BINTU Part 007 (THE END)
Tana lek'ensa ta windo har ya bar gidan sannan ta sauke labulen gami da zubewa kan kujera tana dariyar farinciki. "Na sameshi!" Ta fad'a a fili kafin ta dauki ragowar tea din ta saita daidai saitin da ta ga ya sha ta hau korawa a cikinta tana mai lumshe idanu, wani irin soyayyarsa na k'aruwa a ranta. Ta dire kofin bayan ta kammala, sai kuma jikinta yayi sanyi. Baifa furta yana sonta ba? "Sannu bata hana zuwa." Ta ayyana hakan a ranta. Cike da nishad'i ta tattara kayan karin ta mayar kicin domin ji tayi gaba d'aya yunwarta ta kau. Ranar yini tayi da wani nishad'i marar misaltuwa. To shi d'inma hakan ce gareshi, don har Abba saida ya tambayeshi ko anyimishi albishir da aljanna. Dariya kawai yayi. Itama a ranar sunyi waya da Aisha, wacce shirye-shiryen biki ya 6oyeta don alokacin sauran watanni biyu da kwanaki. Nan Aisha ta sanarmata lallai a wannan daren tayi kokarin kyautatawa mijinta. Tayi shiri, irin shirin da tasan zaiyi saurin birkita tunaninsa. Sukayi dariya. "Kinsan fa har yanzu ya k'i furtamin yana sona?" Tsaki Aisha ta ja. "Kedai ki bada kai, wannan kuma sadda zai furta ma bakisani ba, kuma na gayamaki wallahi Yaya yana sonki. Ki bi dai shawarwarina. Na yarda zaki iya fin haka." Suka k'ara darawa kafin suyi sallama. Misalin d'aya na rana, ta dauki waya tayi kiransa kamar yanda Aisha ta gayamata. Saida ta kammala dariyar sunan (Angrybird) da ta sanyamishi. Saidai har ya kammala rurinsa baki d'aga ba. Bata sauke wayar data kunnenta ba sai gashinan ya kira. Ta shige d'akinta tana goye da Hanif wanda yayi bacci a bayanta. "Assalamu alaikum." Yayi sallama cikin tattausan muryarsa. Ta lumshe ido ta bude tana murmushi. "Waalaikumussalam, Barka da rana Yaya." "Bintunaa! Ya dace a chanjawa Yaya suna, a k'ara mishi matsayi please." Tayi shiru batace komai ba, ya d'ora da fad'in. "To gayamin ya kike? Ina bebina?" "Lafiya lau, gashinan yayi bacci." Ya jinjina kai kamar tana ganinsa. "Masha Allah. Kinsan ina nake kuwa?" "A'a " "Gamunan tare da Abba munzo daurin aure Katsina." Ta zaro ido. "Katsina?" Yayi 'yar dariya. "Hey, kin tsorata ko? Ba kwana zanyi ba ai, zanzo ki bani karfin mata goma." Ai tuni ta kashe wayar tana dariya, shima dariyar yayi cikin jin wani irin nishadi marar misaltuwa. Bata motsa daga inda take tsaye ba ta ji shigowar sak'o. Ta bud'o. "Kina k'ara burgeni Bintuna, miss you! Ayi mana addu'ar dawowa lafiya." Ta karanta yafi sau biyar da wani, k'arshe ta zauna gefen gado tana cigaba da karatun. Wani sanyi ne takeji yana ratsa zuciyarta, wai kuwa dagaske Yayanta Ma'aruf d'inne kuwa? Wannan Ma'aruf din da suke yawan samun sa6ani har Mami kan kirasu mage da 6era? Sai kuma ta ji tanason ba shi amsa. "Miss you too, Allah Ya maidoku lafiya YAYANA." Ya saki ajiyar zuciya. Wai meke faruwa haka? Da ace ba gida guda suka task da Bintu ba, kuma baisan soyayya ba, zai iya rantsewa ko wani abin tayi mishi ya soma sonta har haka, irin son da babu wacce ya ta6a yiwa sai Ma'unsa. Ita kuwa Bintu da wuri ta kammala ayyukanta don wajejan hudu na yamma ya shaida mata sun taho. Ta k'ara gyara Hanif ta shiryashi cikin kana kaya marasa nauyi. Itama ta shiga da zummar wanka, ta zaro ido ganin abinda bata zata ba. Tayi shiru, ashe fa tuni aka shiga sabon wata. Hakanan ta hakura ta kimtsa jikinta ta fito. Batayi wani shiga mai birkitarwa ba kawai ta sanya yadinta marar nauyi mai hannu (3quater) dinkin doguwar riga, saidai ya kamata. Haka ya dawo gidan har da ledarsa ta kaza a hannu. Dariya ta ciyota alokacin da ta sanya hannu tana kar6ar ledar. Ya matso da ita. "Ya akayi?" Ta sunkuyar da kanta tana girgiza kai. "Bakomai." Tayi furucin a hankali. Yayi 'yar dariya. "Ashe inada maganin tsiwarki? Lallai nayi sake a baya. Yau dai (the game will be over). Daga haka ya shige dali yana wani takun kasaita har batasan sadda tayi dariyar mugunta ba (Kuyi maneji da wannan ..kuyi hkr wlh ba da son raina yake kadan ba.!!) Bayan sallar Magriba, suna zaune yana wasa da Hanif ita kuwa ta dukufa tana zubamishi abinci kana ganin fuskokinsu kasan suna cike da jin nishad'i. Shi nasa na murnar yau zai samu abinda ya jima cikin tsananin so da bukata, yayinda ita kuma ya had'e mata biyu, ga hirar da sukeyi cike da nishad'i ga kuma na muguntar da Ma'aruf baisan da zamansa ba, har sai kuma ta ji ya bata tausayi. "Wai Bintuna duk me ya sanyaki wannan fara'ar?" Ta dubeshi ta kauda kai tana murmushi. "Bakomai." Murmusawar shima yayi, zuwa yanzu ya gama fahimtar ita dinma tana sonshi, kawai dai jan aji ne irin na mata. Misalin goma da rabi na dare, suna zaune daga shi sai ita a falo, Sarah da Hanif sunyi nisa da bacci. Ta mik'e tsaye, ya rik'o hannunta wanda ta jishi har kwanyarta. Ta dubeshi, idanunsa a lumshe. "Ina zaki?" Ya nemi sani da muryarsa wacce ta chanja sanadin tunaninta da ya fad'a. Ta kuramishi idanu. "Zanyi shirin kwanciya ne." Ya saki hannun bayan ya sauke idanunsa akanta, ta kauda nata da sauri sai kuma ta shige. Bayan ya shirya ya sanya hannu ya dauki wayarsa ya kirata, tana gani ta k'i amsawa saboda wani nauyinsa da takeji. Ta zubawa wayar ido yanata ruri, alokacin ne kuma ta ji shigowarsa dakin. Ta mik'e tsaye da sauri, sai kuma tayi k'as da kanta ganin ko riga babu a jikinsa. Ya dubeta daga sama har k'asa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ganin irin shigar da tayi wanda shi kadai Allah Ya yarjewa gani. "Meyasa bakya amsa kirana? Sai ma ido da kika zubawa wayar?" Ta girgiza kai, baki bari tayi magana ba ya soma abinda ya matsu da shi. Har saida ta kaisu da zubewa a k'asa. Alokacin kuma ya d'ago ha6anta har numfashinsu na bugun hancinansu da sauri-sauri. "Tashi muyi sallah." Shaf, ta mance da batun rashin sallarta sai alokacin. Ta lumshe idanunta, murya na rawa ta amsa. "Bani da sallah." Ya saki ha6anta yana murmushi, duk a zatonsa wasa takeyi. "Bari na gani." Ya d'ago ya dubeta kamar yayi kuka, sai kuma ya mik'e ya fita kawai. Tausayinsa ya kamata, da kyar ta iya mikewa ta kashe fitilu ta kwanta. Babu jimawa da kwanciyarta, ta ji shigowarsa hakan yasa ta saurin rufe ido. Kwanciya yayi ya juyota jikinsa ya sumbaci goshinta. "Allah Ya tashemu lafiya." Ta amsa a hankali. Cikin dare ya kasa saita kansa, haka yayita juyata son rai yana yanda yaso, kafin a karshe ya mike ya bar mata dakin. Ta bishi da kallon tausayi yanda yayi mata da kuma kalaminsa gareta har yana furucin bazai iya rayuwa babu ita ba. Ta lumshe ido tana murmushi a haka sabon bacci yayi awon gaba da ita. Shi kuwa tun daga ranar ya rage ra6arta hakanan ya rok'eta da suturta jikinta duk sadda suke tare kada ya sa6a umarnin Mahaliccinsa. Idan kuma ya fita aiki, ta fita makaranta suna tare a waya, bini-bini ya kirata har itama ta saba da kiransa idan ta ji shiru. Baya dawowa gidan sai magriba, haka zasu zauna suyita hira, gaba d'aya yanzu ya sakar mata har ta daina kunyarsa. Hirarsu a yanzun ya bambanta da na baya don hirar soyayya ce da mutunta juna. Kamar dai a yau, tana kwance saman doguwar kujera tana lissafa kwanakin period dinta, a goben ne take da kwana bakwai cif wanda a kwanan zatayi wanka. Ta ji shigowar motarsa da tsayuwarsa. Saidai kafin ta motsa wayarta ta hau k'ara, ta dauka ta duba. Tayi mamakin ganin yayannata ne. Ta d'aga da sallama, ya amsa. "Ki fito, yau zance nazo." Abin ya bata dariya. Ta amsa da toh. Dakinta ta shiga ta k'ara kallon kanta. Riga da siket na brown lace ne a jikinta, tayi kyau ya zauna d'as a jikinta. Ta k'ara feshe jikinta da turare ta murza jan baki. Mayafinta ta dauka marar nauyi ta yafa a kafad'arta, sannan ta zura takalminta mai tsini ta fita. Hanif na tare da Sarah a d'aki, bata bi ta kansu ba ta fita. Yana sanye da shadda sky blue, hularsa kuma dark blue. Dinkin boda, ya zauna sosai jikinsa, yayi kyau har ya gaji. Kafarsa d'aya ya tankwashe saman kujera, kansa kwance a kujerar ya zubawa hanya ido, a sannu kuma yana sauraron kid'an dake tashi a rediyon motarsa. Ido ya zubamata sadda ta fito tana wani irin taku na jan hankali, bata ganinsa sakamakon gilashin ba haske, saidai jikinta ya bata ita din yake kallo. Yasa hannu ya bud'e mata gaban motar tun kafin ta k'araso. Ta shigo ta rufe. Tayi mishi sallama. Ya sauke ajiyar zuciya don baisan Bintu na da kyau haka ba saida ya soma sonta. Ya amsa yana tambayarta mutan gida Abin ya sanyata dariya. "Wai Yayana menene haka?" Hannunta ya rik'o. "K'ara'i, sonki ya sanyani Bintuna." Ta zaro ido tana dubansa, baki ta6a cewa yana sonta ba, zataso a yau ya furta. Ya hura idanun. "Bakya sona ne? Yau fa baki zaki bude malama, hira ta kawoni, zan bayyana miki sirrin dake raina." Tayi farr da ido, ya kauda kai yana wani irin murmushi, ya kar6i wannan sak'on. "A baya, nayi zaton mace d'aya ce ta dace da ni, mace d'aya ta dace na mallakawa komai nawa. Nayi zaton yanda nake, ni d'in MIJIN MACE D'AYA ne, banyi aune ba, mutuwa tayi min YANKAR KAUNA da matar da na so na kuma fi sonta fiye da kowace mace a duniya." Ya d'an tsagaita kafin ya cigaba da magana. "Na zo nayi biyayya bayan da na jajircewa zuciyata na yarda da KADDARA, na aureki." Ya k'ara matse yatsunta yana dubanta duk kuwa da cewar idanunta baya gareshi. "Bintun Mami, Bintun Ma'aruf. Kinsan me yafi had'ani dake?" Sai lokacin ta dubeshi ta girgiza kai gami da turo baki. Yayi 'yar dariya. "Bakya ji, na lura kina da fitina da tsokanar fad'a. Ba kuma sai na fad'amaki wanene Ma'aruf ba. Wannan shine ya kawo rashin jituwarmu. Kafin kuma na zo na had'u da jarabta ta sonki. Ban k'ara sanin ina sonki ba, sai bayan da na nisanta gareki har na kwanaki talatin da d'aya, zuwana Lagos kenan. Bayan na dawo nayi kokarin soma janyoki a jikina domin nuna miki irin so da kaunar da nakeyi miki a aikace batare da na furta ba." Ya d'anyi shiru yana mai cigaba da murza yatsunta, ta sauke ajiyar zuciyar tana kar6ar sak'on a sannu-sannu. "My Queen." Yayi furucin da wata muryar da ta ji kamar ba ta shi ba. "Ina sonki, ina kaunar na kasance tare da ke har abada. Kin shirya kar6ata matsayin miji kuma uba ga 'ya'yanki?" Ta sunkuyar da kanta k'asa. Gaskiya ne, da ba'ason zurfafa k'iyayya a addini, bakasan sadda zaka soma son abinda kake k'i ba. Ya d'ago ha6anta. "A'a my queen, you have to answer me." Ta lumshe idanunta. Murya na rawa ta furta a hankali. "Na amince, ina sonka." Haka yayita aika sak'o kafin ya barta yana murmushi ya soma da bud'e kofofin. "Nagode my queen." Daga haka suka shiga ciki, ran kowannensu k'al. Ranar ma basu raba shimfid'a ba. Washegari kuwa da Magriba, yana shigowa ya risketa tana sallah a d'akinta. Ai baisan sadda ya washe hak'ora ba don farinciko sannan ya juya zuwa d'akinsa. Abincin daren nan dakyar ya ci. Ita kuwa gaba d'aya ta tsorata da yanda ya soma nunamata. Haka dai ta daurewa zuciyarta ganin ya riga ya gama matowa. A daren bayan sunyi sallar nuna godiya ga Mahaliccinsu yayi musu dogon adduoi. DAREN ALKHAIRI KENAN...! * * * Kuka takeyi sosai, yana rarrashinta, dole tayi shiru ganin yanda duk ya bi ya damu kansa da kukannata. Da kansa ya taimaka mata ta tsarkake jikinta kafin ya barta ta k'arasa. Ranar ya tsinci kansa da wani irin farinciki marar misaltuwa. Lallai Allah Ya mishi babbar kyauta, a yau gashinan ga madadin Asma'u. Yau shi ya taimakawa Sauda da d'awainiyar gidan, ita kuwa kunya ce ta hanata fitowa ma. Tana jin shigowarsa d'akin tayi saurin ture kanta k'ark'ashin filo. Ya k'arasa yana dariya ya hau yi mata cakulkuli, babu shiri ta hau dariya gami da ture filon. Ya sumbaci goshinta, ta lura yanason yin hakan kafin ya kwanta ya soma yi mata wasu nauyayyun zantuttuka acikin kunnenta. Zata mik'e cikin zafin nama ya janyota, tayi narai-narai da ido, kwalla suka cikamata idon. "Don Allah kayi hakuri." Ya kwaikwayi muryarta. "Don Allah ki nunamin karfinki na mata goma." Ai sai ta tura kanta jikinsa tana dariya. Yayi mata kyakkyawan runguma. * * * Acikin wannan satin, ba'a cewa komai. Da ka gansu kasan suna cike da more rayuwa babu wata matsala a gabansu. Sai gashi wata muguwar shakuwa ta daban ta shiga tsakanin Bintu da Ma'aruf wanda ta bawa kowa mamaki. Akwai sadda da yamma suna zaune gaba d'aya a falon Mami ana hira har Hashim da Sally wadanda suka kawowa Mamin ziyara, lokacin sauran kwanaki biyar ya rage bikin Aisha. 'Yar kwarewa Ma'aruf yayi, nan da nan Bintu ta rikice ta mance a inda suke ta hau shafa bayansa tana mai mik'a mishi ruwa. Cike sa tausayawa tace. "Sorry my king." Ya amsa, gyaran muryar da Rufa'i yayi ta farkar da su. Mami dai kauda kanta tayi kawai tana murmushi, yayinda Rufa'i da su Hajara suka sanya dariya. Ma'aruf ko a jikinsa sai ma ita Bintun ce ta dan ji nauyi. "Oh, Allah Hakim, yau 'yar Mami ce ke wannan rikicewar akan abin gudunta? Soyayya lallai tana dadi " Mami ta mike don sai alokacin ta ji kunya. Daman ita Bintu ke kunyar, ai kuwa tana bada baya ta dubi Yaya Rufa'i. "To meye? Wasu ma suyi mana." "Lah, ni kike gayawa haka? Eh lallai, kinmanta sadda yake bulale ki nake yare miki? Aisha kinga halin d'an adam." Bintu na dariya ta zauna gefen mijinta wanda ke sauraronsu da murmushi dauke saman fuskarsa. "To ai bulala ce ta soyayya, yanzu ba gashinan tayi rana ba, ai hakane ko my king?" Suka tuntsire da dariya har Ma'aruf din. "Yes my queen, ashe kingane. Ku dai ku rike girmanku ba'a shiga tsakaninmu da queen, ko harshe da hak'ori ma haka suka ganmu suka kyale. Ato." Dariyar aka k'ara. Hashim ya d'ora da fad'in. "To d'an iska, dadin abin dai..." "Ya isa." Ma'aruf ya dakatar da shi ta hanyar mik'ewa yana dariya gudun kada yayi mishi iskanci. "Malam tashi muje ku gaisa da Abba." Haka suka wuni cike da jin wani irin annashuwa. * * * BIKI BUDURI....! ((SAIRAN POST DAYA KO BIYU IN SHA ALLAH..!) A yau ake bikin sanya Aisha a lalle. Wannan yasa gidan nasu yake a cike da 'yan uwa, cikinsu kuwa har da mutanen Rano. Wannan karon har Umma abokiyar zaman Inna itama ba'a barta a baya ba wajen halartar bikin autar Mami. Bintu babu zama, sune wancan babban shagon na kayan kicin, sune acan shagon gyaran gashi. Ya zamana ta dawo gidan da zama, duk yanda Ma'aruf yaso hanawa bai samu hakan ba kasancewar ta samu daurin gindi wajen Mami. A daren da akayi kamun Aisha, suna zaune a can d'akinsu tare da su Atika harma da Hafsa kanwar Ma'u wacce itama takanas ta zo kwana adalilin mijinta yayi tafiya, kasancewar gidansu basu da sa ido ballantana har abin ya zama wani babban al'amarin da zai shafi ZUMUNCI A YAU. Sai hira sukeyi suna kyalkyala dariya. Rabin hirar kuwa Atika ke basu akan matar saurayinta. Yanda yake bala'in shakkar daukar koda wayarta a gaban matar. Wayar Bintu da tayi k'ara ya sanyasu dubanta suna tsokana. "Toh sarakan soyayya." Ta murgud'a baki tana dariya kafin tace suyi shiru ta d'aga da sallamarta. "My king, fatan dai ka bar fushin?" "Idan kinaso na daina, zo ki sameni anan d'akina. Ta zaro ido. "Lah, baka tafi gida ba? Karfe goma fa " Yayi 'yar dariya. "Kina wasa, ai na gayawa Mami saidai nima na kwana a gidannata." Ta hadiye dariyarta, suma tasu suka gimtse don kuwa a hands free wayar take. "Allah Sarki My King, shikenan ai, da safe Dan dolo sai ya mik'o maka kayan karinka. Allah Ya tashemu lafiya." Ta kashe wayar gaba d'ayanta, me zasuyi banda dariya. Aisha ta d'akamata duka a cinyarta. "Wallahi kina daukar alhakin yayana, kinsan dai abinda yake nema." "Ai idan batayi hakan ba, babu mai kiranta da Bintu." Cewar Hafsa cikin dariya. Ta zaro ido. "Lallai ma, kunyi zaton nima ina iskanci ko? Ba abinda na iya." Sukayi dariya. Kasancewar basusan labarin ba yasa Aisha fesa musu. Ai kuwa nan sukayita tuntsire dariya. Ranar kwanan farinciki sukayi, ita kuwa tana sane ta k'ular da Ma'aruf. Har washegari daurin aure da yini, babu abinda ya sake hadasu, koda tayi kiransa a waya sai ya k'i dauka. Hakanan ko sun hadu d'akin Mami bai ko kallonta. Jikinta yayi sanyi, da kanta ta soma neman shiri. Don haka ana ta shirye-shiryen tafiya dinner, itama ta shirya cikin ankon da sukayi kalar pink, ta ci ado har ta gaji da haduwa, jikinta babu dadi, daurewa kawai takeyi don tana bala'in son zuwa fatin. Ta dubi Aisha, "Kuna iya tafiya, kinsan ni tare da King dina zan taho." Sukayi murmushi kafin ta fita zuwa sashensa na gidan. Saidai yayanta Saifu ta iske, shi ke sanarmata yana can gidansa. Haka Mami ta saka aka kaita don ta tafi kafe saidai su tafi tare. Da shigarta ta iskeshi saman doguwar kujera a kishingide yana amsa waya. Sam baiji shigowarta ba, ta karaso da sallamarta, alokacin ya ji ya amsa saidai bai ko dubeta ba. Ta zauna da sauri sanadin jiri-jiri da ke kwasarta, jikinta yayi zafi, ta tuna rabonta da abinci tun wajen k'arfe d'aya na rana da ta ci. Bayan ya kammala wayar ya mik'e zaune. Sai lokacin ya dubeta, tayi mishi kyau kwarai. Ya yi kamar bai ga kwalliyar ba ya kauda kansa. Ta marairaice fuska gami da mik'ewa tsaye. Babu shiri ta soma kokarin zubewa awajen, da azama ya tarbota. "Lafiya?" Ta soma kukan shagwa6a. "Kaine kake fushi da ni, duk ka tayarmin da hankali." Ya dagota. "Abar wannan maganar, jikinki fa da zafi, kin kuwa ci abinci?" Ta girgiza kai. Ya mike yana fad'in "Ina zuwa." Ta kwanta a saman kujerar tayi lamo tana tunanin yanzu watakil ansoma shagalin fatin. Can sai gashinan ya fito cikin kananun kaya. Ya dagata zaune yana jan tsaki. "Wannan kayan ma ai k'arawa kanki wani nauyin ne Queen." Zai ragemata ta nok'e har da hawayenta. "Nifa wajen Dinner na biyo mu tafi." Ya zaro ido. "Kina a wannan halin? A'a muje dai na nema miki abinci sai mu wuce asibiti." Ya nace, itama ta kafe harda kukanta, ya zaayi ma bataje dinar nan ba bayan ta ci buri akansa? Haka ya amince suka tafi, tayi-tayi ya chanja kaya ya k'i. Ta lafiyarta yakeyi. Yaso su soma zuwa asibitin, ganin haka nan da nan ta mike ta daure tace ita fa ta samu sauki daman yunwa ce. Ya girgiza kai kawai. Bintu akwai k'arfin hali. Sun shiga yana rik'e da ita har mazauni. Bayan sun zauna, ya sanya aka kawomata abinci tun kafin ma a soma ciye-ciye. Ta ci tayi nak ta ture, sai lalla6ata yakeyi, sun burge mutane da yawa musamman sarakan soyayya, wato 'yan ROF whatsapp.(lol). Fauza kasa jurewa tayi ta isa wajensu ta daukesu hoto, tana fatan kasancewa da habib dinta haka wataran. Sally ta k'ara kankame hannun Hashim dinta a kunne ta radamishi. "I love you." Shima ya ji sanyi, don soyayyar abokinsa da Bintu na burgesa. Ba'a je ko'ina ba ta soma shek'a amai. Hankulan mutane ya dawo kansu, Ma'aruf ya ja ta sukayi waje, ma'aikatan wurin suka gyare wajen tsaf aka cigaba da shagali kowa hankalinsa yana ga Bintu. Ko meke damunta? Kai tsaye shi kuma yana kaita mota suka nufi asibiti harda Atika wacce yasa ta hau su je. Likita ya aunata ya buk'aci fitsarinta, ai kuwa result ya nuna tana da ciki. Hamdala kawai Ma'aruf yayi ta yi har suka fito hannunsa cikin nata. Suna shiga mota ya sumbaci goshinta. Hawaye suka zubomata na farinciki. Nan dai zance ya cika gidan ta bakin Atika cewar Bintu na dauke da juna biyu. Kowannensu ya hau murna, Bintu bata da masaniyar wainar da ake toyawa don yayannata cewa yayi gidanta zata kwana ta huta. Har aka kai Aisha babu inda ta fita, Mami ma ta goyi bayan Ma'aruf a wannan karon. * * * SANNU BATA HANA ZUWA...! A yau har ga Bintu ta cika watanni tara cif dauke da cikin bebinsu da Ma'aruf. Sai kuma a wannan lokacin ne ta shiga damuwa sosai, ba na komai ba sai na tsoron haihuwa. Sau da yawa Mami ke kwantar mata da hankali don tuni ta komo gidan Mamin duk kuwa da ba da son ran mijinnata ba wanda yaso ta zauna gabansa ta haihu. Takan ce, tana tsoron mutuwa kamar yanda Ma'u ta rasu. Ma'aruf da zarar ta soma zantuka haka har ma ta hau rok'on gafararsa, sai ya ji hankalinsa ya tashi, akwai sadda ya zubda hawaye yana rok'onta akan ta bar sanyamishi damuwa. Haka dai har wata ranar litinin da daddare nak'uda ta taho gadan-gadan. Babu shiri Mami ta kwasheta sai asibiti. Cikin ikon Allah, mintuna baifi arba'in ba da zuwansu, ta haifo d'iyarta mace santaleliya. Ma'aruf wanda ya zo tun wayar da Mami tayi mishi, suna tare da Mamin a tsaye suka ji kukan jaririyar. Sai kuma nos ta fito ta sanar dasu haihuwar. "Ya lafiyar uwar?" Shine farkon abinda Ma'aruf ya nemi sani. Hankalinsa ya kwanta jin tana cikin koshin lafiya. Murna kam ba'a cewa komai, washegari haka yan uwa sukayita zuwa gidan Mami don a washegari aka sallamesu. Abinda ya burge Ma'aruf ga Bintu, bai wuce ganin da kanta ta nemi a sanya sunan Ma'u ba, shi kam ya so sanya sunan Innarta. Haka nan aka yiwa yarinya hud'uba da Asma'u suna kiranta BINGEL(lol). * * * BAYAN WASU SHEKARU...! Barrister Fatima Bintu bakinta ya k'i rufuwa adalilin yau ake bikin yayesu daga makaranta. Tana rik'e da hannun Hanif da Bingel ta rungumosu Yaya Rufa'i ya daukesi a hoto. Ta k'arasa ta sumbaci goshin bebinta Amir mai sunan mahaifinta Muhammad dake rik'e a hannun Abida sabuwar 'yar aikinta. Nan ma ta kar6eshi akayi musu hoto, kafin ta k'arasa ta rungume Maminta tana hawayen farinciki. "Yau ga Bintunki ta fito a yanda kikeso, I am now a Barrister.' Sukayi dariya, itama Mamin ta sharce hawayenta na farinciki. "Allah Shine abin godiya." Sukayi dariya. Ta janyo Aisha wacce ke rik'e da d'anta Mustapha suka had'u suka sanya Mami a tsakiya aka dauki hoton. Daga bisani kuma gaba dayansu har Abba suka dauka. Bintu ta cika tayi fum saboda rashin zuwan Ma'aruf akan lokaci. Har da hawayenta. Koda Abba yayi niyyar kiran wayarsa, hanawa tayi. Har suka bar wajen suka dunguma zuwa gida babu shi da labarinsa. Ganin an nufi gidan Abba bata damu ba ko kad'an, fushin da takeyi da mijinta yasa ta yanke koda kwana ta kama ta kwana anan ba zata k'i ba. Saidai ta cika da mamakin yanda aka faka motoci a kofar gidan, su d'inma anan sukayi fakin suka fito cike da mamaki tattare da su. Fitowar Saifu yayan Bintu dauke da d'ansa a hannu ne ya basu mamaki. Ya gaidasu Abba da fara'arsa, baice komai na daga tambayoyin da suke mishi ba yayita musu iso zuwa ciki. A babban falon na Mami suka tarar da mutane cike, Ma'aruf na tsaye gaban wani k'aton cake yana kunna kendir. Ya dago ya sakarwa matarsa murmushi, tuni dukkan wani 6acin ranta ya gushe. Nan fa bakin kowa ya gaza rufuwa ana ta murnar ganin juna. Bayan Bintu ta yanka cake tayi kamar zata sanyawa Ma'aruf sai tayi azamar turashi bakin Hanif, akayi dariya. Duk da iyayen dake a falon, baisa yayi dabarar yi mata magana ba. "Ina sonki fiye da kullum. Babbar kyautarki shine, na biyamiki umrah." Ta dago dara-daran idanunta ta dubeshi tana dariyar farinciki. Da ace akwai hali da ta rungume mijinta, kawai sai ta soma fidda hawayen farinciki tana dubansa. A haka Rufa'i ya daukesu hoto ana dariya. TAMMAT BI HAMDULILLAH Inda mukayi kuskure a gafarcemu. Nagode sosai yan uwana masoyana, shakka babu kun nunamin kauna, fatana Allah Ya hadamu haka a aljannarSa. Amin. Godiya ta musamman ga Ummu Abdool, Bingel. Kun zamo wasu jigo a rayuwata, Allah Ya bar zumunci, amin
0 comments:
Post a Comment