=== CIWON IDANUNA 10 === .
A yadda yake maganan cikin tsananin damuwa yasa ita kanta hajiyati tana damuwa daukan wayanta tayi ta fara kiran Abamama yana dauka tace yayi sauri yazo,
cikin minti ashirin sai gashi aikuwa tana kuka tace dr.Hisham ya masa bayani shikuwa dama kaman jira yakeyi ya zauna nan yace masa " Baba zan yi magana ne ba a matsayin likitan Nadrah ba zanyi magana ne a matsayin abokinta sannan kuma mai sonta" Abamama ya zaro ido don yanayin da Hisham yake magana dole jikin mutum yayi sanyi anan ya cigaba da cewa " Baba Nadrah tana da damuwa bansan ko ka sani ba, Amma akwai likitan mu anan likitan zuciya ne, Nadrah tana sonshi sosai amma baba baya sonta, son da take mishi yasa yanzu gaba daya ta dawo haka, wani zai dauka ko rasuwan mammy ne amma acikin dari kashi saba'in saboda shi ne, idan batayi hankali ba zata iya rasa ranta, kaga tsantsan nuna kaunar da take masa gudunta yake yi, nayi iya kokarina in janye hankalinta akanshi amma na kasa" dukka dakin kowa tsit yayi Abamama ya kallen amma na rasa gane kallon meye daya , gyran murya yayi sannan yace " wato Hisham na gode sosai da wannan labarin da ka bani, nayi sake sosai akan y'ata tun rasuwar mahaifiyata, Amma naji dadin wannan bayani insha Allah zan dau mataki da gaggawa" yana gama fada ya fice yabar dakin, ya kamal kuwa kaina ya iso alokacin sakon harara nake turawa Hisham shi kuwa ko ajikinsa ya fice yabarni irin wato na ci kaina kawai, yaa kamal yayi murmushi sannan yace " me ya hanaki fada mun tuntuni?" juya kaina nayi domin shi kanshi ya sani da ace fada masa nayi in bai makeni ba toh zansha mari cikin biyu za'ayi daya, ummi aisha kuwa jugum tayi tana ganin ikon Allah. Tun ranan Abamama bai dawo cikin asibitin ba, haka zalika ban hada ido da Haidar ba, hajiyati kadai ke jinyata sai yayuna idan sun zo, duk na jime na dawo abun tausayi, Ammati kullum tana cikin yimin test a makaranta, sati na na biyu Abamama ya shigo da Visa a hannunsa ga kuma epassport wanda ina tsammani nawa yayi renewing don tayi expire , jiki a sanyaye na zauna ina kokarin gaisheshi nan ya katseni " na saka kamal ya hada kayanki dukka zamu hadu a airport, ki wuce dubai kije gun Ammi(kanwar Mammy da take zama acan) , skul nan zanmiki differing ko kuma na nema miki transfer idan zai yiwu" tun da ya fara kallonsa nakeyi har ya idda yana gamawa nace "Abamama ba zanje ba". wani kallon mamaki yamin daga shi har hajiyati domin yadda na fada da confidence dina babu tsoro aikuwa ya gyra tsayuwa sannan yace " Nadrah idan zaki mutu anan sai an dauki gawanki ankai can don haka ki tashi ki zo ki wuce na karba miki ticket ki wuce abuja jirginku zai tashi karfe biyun dare. . Tashi nayi na mike na riko kafarsa ina kuka "Abamama kayi hakuri bazanje ba " ko kulani baiyiba, ya fice yana goge gefen idonsa alamun share hawaye a fuskarsa,kowa sai da ya tausaya min kukan da nakeyi agun, Yaa kamal ne yasa nurse din ta min wanka na shirya tsaf asibitin suka sallamen mukayi sallama da hajiyati da kuka, airport muka nufa cikin minti arbain da biyar muka isa abuja, muka yi zaman awa biyar, awannan zaman dr.Hisham yakirani mukayi sallama, muryarsa duk ta dishe alamun yana cikin bakin ciki, ni dai ko ajikina tunanina duk shine Aliyu, na kira numbanshi bai dauka ba don haka nakira Amrah nace mata zanyi tafiya amma zandawo don Allah ta gaishemin da yaa Aliyu tayi dariya kafin ta amsamin. Anan ma take sanar dani cewan yana abuja, rokonta nayi ta turo min address dinshi yana zaune a maitama har dadu house number nayi murmushi sannan na kashe wayan.
Anan muka shiga ethopian airline nan ma muka tsaya a addis baba wanda ke birnini ethopia, mukayi awa uku kafin muka wuce dubai duk wannan lokacin yaa kamal bai tanka min ba kaman kishiyoyi waya san meyake damunsa, oho nidai ina kissa yadda zan gudu,daga airport dinsu muka zauna jiran Motan gidan Ammi da zai zo yakaimu sharjah inda suke da zama, Yaa kamal yaje nemo mana coffee duk kayanmu na ajiye anan na mike sadaf sadaf na bar kayan agun sannan na koma cikin airport din na tambayi yaushe zansamu jirign zuwa nigeria a daren mutumin ya kallen yace nan da awa biyu, na ce to inaso na biya, yayi dariya sannan yace "ai bazai yiwu ba" duk cikin harshen turanci muke magana, a gigice nace masa " me yasa?" ya kallen yace " wannan fa international airport ne ba state zakije ba" duk da haka ban yarda ba nace " toh duba ko akwai wanda sukayi cancelling flight dinsu" yayi murmushi ganin yadda na rikice kuma nake juyawa in kalli bayana in kalleshi,nan ma yace babu, wayata na ciro na kunna dama mtn dina ne akai, tuni na kunna wifi dina a gigice na hau whatsapp ganin asiri na zai tonu yasa na shiga ladies tsaf tsaf babu kazanta daga masu shiga sai masu gyra makeup dinsu da masu gulma wasu turanci wasu larabci dama ladies ya gaji haka, na hau whatsapp dina sannan na ga iby, iby kuma abokina ne sosai anan natuna yana zama a dubai, a gigice na mishi magana, na ce masa gani a kasarsu amma inason komawa, tambayata yayi da wani layi nake amfani nace masa da wanda nake whatsapp kawai ganin wayansa nayi , na dauka ya tambayeni me ya faru, nan na masa bayanin komi dama asali yasan Aliyu don haka kawai da na masa bayani yace ina ina? na sanar masa da gani a airport , nan ya bani hakuri yace na nemi hotel na kwana yana da mutane a embassy zai roka ko za'asami mai zuwa gobe, nan ma nafara kuka don Alah yagani bazan iya kai gobe ba, haka nan dai nafito ina share hawayena rike da wayata a hannu sai jakata, aikuwa ganin yaa kamal nayi agabana, idonsa tayi jajur alamun yana cikin tashin hankali yace " daga ina kike?" cikin rikicewa dan zufa har ya ketomin nasan kalan ubana da zanci, nace " toilet naje" bai ce komi ba yayi gaba nayi bayansa ina waige kamar barauniya, nikam na shiga uku idan ban koma ba, ya zanyi da hamma Aliyu , mota muka shiga muka wuce sharjah cikin minti arbain muka isa gidan Ammi, buga kofan mukayi aka bude numfashina ne ya tsaya cak ganin wanda idona ke nunamin.
=== CIWON IDANUNA 11 === .
Ido na a zazzare nace "Hamma!" ya lumshe idonsa a hankali sannan yayi murmushi yace "Hamma kuma?, ku shigo daga ciki" harshensa a juye, alamun hausan ba ta zauna ba,ya wangale kofan , rike da jakakkunan mu muka shiga bani kadai ba hatta yaa kamal sai daya bisa da ido, Ammi ce ta sauko biye da Fido(yarta ta fari, wacce muke sa'oni da ita) da sauri ta rungumoni nikuwa abun al'ajabi yamin yawa sai kallonshi nake nace mata "Ammi yaushe Hamma Aliyu yazo nan?" ta kalleshi sannan ta juyo ta cemin " Hamma Aliyu kuma? Fahad dai ko?" na saki jakar hannuna bakina a sake, inaaa ai raina mun hankali zasuyi da hankalina, ya za'ayi ina ganin Hamma Aliyu acemin Fahad, nace "Ammi kina gani kuwa da kyau? Hamma ne fa!" ta yi murmushi sannan tace " Fahad taimaka kaje ka haura mata da kayannan sama, inaga stress ke damunta kasan da sauran ciwonnan ajikinta" tafiya yayi yabarni nikuma Fido ta rikoni mukaje dakin da aka sauken, wanda shine dakinta, babban dakine komi pink kana gani kasan dakin yan'mata ne ya sha ado da komi, muka zauna ta kunnamin heater na shiga nayi wanka na samu tafito min da dogon riga na sanya nayi sallah sannan muka sauko kasa, duk da riga da wando ne ajikinta ta tumbuke gashin kanta, Yaa kamal na kan dining yana aika sakon abinci abunka da mai ci, ya kallen sannan yacewa Ammi " Ta zauna anan tunda zamanta acan rikici take janyo mana da kayan kunya, idan tasamu makarantan ma dukka, ni dai gobe zan wuce" ina zama na riko cokali sannan nace " idan na tabbatar da Hamma Aliyu ne na gani dazu bazan bika ba, Amma idan bashi bane zan bika" zura min ido sukayi a lokacin shima ya sauko jallabiya ce a jikinsa tayi matukar yi masa kyau, ya zauna akan dinning din sannan ya fara cin abinci yana danna wayan hannunsa, idona kyam a kansa ina kokarin fitar da cewa shi dinne Hamma Aliyu ba wani ba, Amma ina duk abunda nagani ajikinsa tsak na Hamma, sai dai shi yafi Hamma manyan ido da kuma ginin jiki( wato six packs) daga gani baya wasa da lafiyarsa, namiji ne a zube, hannu fido ta sakamun na juyo sai da naji kunya domin duk idonsu na kaina tace " kinsawa Bappah na ido" na harareta ta gefe sannan naci gaba da jefa shinkafar da ke gabana duk da bawai tamin dadi irinna gida nja bane. ******** Washegarin ranan Yaa kamal ya bar dubai ya koma nja ya barni da jimami da kuma ganin ikon Allah, duk ya ajiye min magunguna na da komi da zan bukata, ko da iby yakirani nace masa a a nafasa tafiya, Fido na zuwa makaranta da sauran yaran Ammi guda hudu dukkansu maza, Mubarak,Alhassan,kabir, da Abbakar sai ita fido dukkansu suna makaranta acan haka zalika Ammi na da shago a cikin kasuwansu don haka takan fita tace , Fahad yana aiki shima duk da bansan gun aikin ba gidan anwatse anbarni ni kadai kamar mayya sai masu aiki, na kimtsa kayana na ajiye sannan na sauko na kunna tv, bana gane yaren nasu don haka na kashe na dauko wayata. Ina kewar gida don haka nakira Abamama, ya dauka cikin sanyin jiki na gaisheshi ya amsa sannan yasamin albarka " Kiyi hakuri ki cire ranki akanshi kinji? ina nan muna miki adduan wanda yafishi alheri, zaki gani kema kiyi addua Allah zai musanya miki shi da wani" "Amma Abamama shi nakeso fa" "kina wasa da ikon Allah ne? ke kam kiyita addua kinji?" da haka na kashe, na kira hajiyati, Ammaty da kuma su yaa Amir da su yaa ahmed, dukkansu yayuna sai dana kira, kowannensu wa'azi daya yake min na nutsu nayi karatu sannan nacire Hamma Araina, wanda idan sun fada dariya nakeyi banjin akwai halittan da nakeso fiye dashi alokacin arayuwata. kwankwasa kofan akayi da sauri na sauka naje na bude a zatona Fido ce ko Ammi saikuma na ganshi, gabana yayi mummunan fadi sannan nace " Ina wuni" bai amsa ba sai murmushi da yake min yashigo ya rufo kofan sannan yace " baki gaji da zama ke kadai ba?" " na gaji mana, gobe zanbi ammi kawai" ya yi murmushi sannan yace " zo kiga" na tsaya ina kallon shi dasauri ya janyo abayata sannan yayi dani ta bayan gidan, wani irin teddy bears na gani ajere a ajiye, juyowa nayi na kalleshi sannan nace " na waye haka?" " wata budurwa ta ce, kullum idan na kai mata sai tasa adawomin dashi, shine nake ajiyewa ko akwai wacce zata dauka wataran" na dauko daya na rike wani irin kamshi teddyn yakeyi na rungume ina lumshe ido tunanina aina nasan turaren, gabana tayi Dam ta fadi dana tuna cewa na Hamma ne, dago idon da zanyi na ga shima kallo na yakeyi nan ma gabana ta kara fadi dasauri na bar wajen, yau nikam nashiga uku bugun zuciya zata kasheni a gidannan idan banfice ba, falon na koma shima sai ya nemi gu yazauna ya hade kafansa daya kan daya yana danna waya, nashiga uku haka Hamma yakeyi idan zai zauna shima, zura masa ido nayi ko kyaftawa banyi "wannan kallon ba zaisa na shake ba kuwa?" muryarsa ce ta katseni a razane na kawar da fuskata sannan nace " wani kallo fa, tunani nakeyi" "tunanin Hamma ko?" na gagara amsawa shikuwa ya tashi yabarni a falon, nan ma nabishi da kallo tabbas idan ban tattara kayana na bar wannan gidan ba zan iya karamin hauka.
***** Sati na daya agidan Ammi na dawo tamkar yar gida, don asai munsaba dasu zuwansu dubai ne last year yasa bama haduwa, shima aiki yazo yi mijin nata na shekara biyu yana gamawa zasu koma acewar Ammi domin ita batason zaman can tafison zaman nan musamman ma da Mammy ta rasu hankalinta yadawo nja, kauna duk sun gwadamin banda abun cewa sai godiya, Abu daya ke cimin kwarya a tuwo, ko cin abinci Fahad yakeyi sai naga kaman Hamma ne, gashi sai shigemin yakeyi mutum ne mai son mutane, fara'a dakuma saukin kai, haka zai jamu nida fido muyi yawo mu dawo gida, sannan duk fita sai yadawo mana da kunshin leda, ina matukar jin dadin zaman gidan Ammi sannu a hankali na fara mantawa da duk wani abu dake faruwa dani haka zalika shakuwa ta shiga tsakanina da Fahad, ko chewing gum naci sai na ajiye masa, haka zalika shima ko me ya samu sai ya ajyemin, hankalin Abamama ya kwanta sosai atunaninsa bazanyi maraicin uwa ba kuma hakanne sai dai kuma a duk lokacin da na ga yadda Ammi take dasu fido sai na tuna da Mammy ko Hamma na kan shiga toilet nayi kuka har sai kuka yafita araina, in rarrashe kaina, babu wanda yasani har wata rana da Fahad yashigo kirana kawai yaji shishikan kuka dasauri yarinka buga toilet din na bude yaga yadda idona ta kumbura tayi jajur, tuni ya lallaboni muka zauna akan kujeran dakin, zuramin ido yayi yana jira na masa bayani amma na kasa nan ma wani sabon kuka na farayi don tuna min da Hamma da yayi zuciyata na ciwo, wani irin kaikayi nakeji aran nawa, ina zansa kaina naji dadi , wayyo Allah na Hamma, wayata naciro da sauri na fara kiran numbanshi duk da nasan ba dauka zaiyi ba tunda naje kusan kullum sai nakira numbanshi amma baya dauka, nakira bugun farko ya dauka a razane na tashi sannan nace "Hamma!" bai ce komi ba sai dana kara kiran sunan nasa "Hamma!!" " i taught nace ki daina kirana, ke wacce irin mutum ce?" ji nayi an fizge wayan , juyowan da zanyi kawai na ga Fahad yadda yakarba haka yakarba ya tika wayan a kasa, Tasssss ya fasata idonshi tayi jajur tunda nake ban taba ganin shi awannan yanayin ba, nashiga uku. Ba tare da ya kalleni ba yajuya yafice nikuwa na tsugunna na tattara wayan sannan na koma daki, bakin ciki da takaici wayata mai uban tsada ya kama ya fasamin wallahi zai ga madarar rashin mutunci, zuciyata ta cigaba da kuna shi kuwa ban kara ganinsa ba aranan.
***************** BAYAN SHEKARA DAYA Lafiya akace uwar jiki toh haka ta kasance dani, domin kwanciyar hankali na samu nayi bulbul kwata kwata bana da damuwa, na so shiganakaranta, don har transfer na nema anma bansamu ba domin cgpa na ya sauka sosai, American university dinsu na cika , gashi kuma archictecture and art desighn shima almost shekara biyar, Ammi tace na bari kawai tunda mun kusa dawowa nja,don haka sai dai na raka Ammi shago, muyi yawo mu ga duniya , shakuwar dake tsakanina da Fahad ya zama hatta abinci tare mukeci, bana ci idan baya nan safe idan yafita aiki haka nake zama jugum sai dai mu wuni muna chatting, wani lokacin har skype mukeyi , ni nake gyra masa daki sannan na wanke masa a machine idan sunyi datti mu hada akai guga, yayuna kuma mu kanyi waya dasu, su hajiyati da Abamama duk hankalinsu ya kwanta ganin ina cikin kwanciyan hankali, alokacin har na fara jin haushin kaina , meye na gani ajikin Hamma? idan kammanine gashinan sak ajikin Fahad , hallayar da nake nema ajikin namiji kuwa shima gashinan, saukin kai, kyauta, fara'a ga ilmin addini domin Fahad har karatu yana kara min, duk munayi to ahaka na shaku dashi shakuwan da yasa na kanyi sati biyu zuwa uku ban tuna da Hamma Aliyu ba, ga Adduoi da Hajiyati da Abamama suka dade suna min , Hajiyati kam saukan alqurani ta saka aka rinka min Alhamdulilah na dawo asalin Nadrah ta, kwanciyan hankali saikuma maraicin uwa duk banyi shi ba sai dai na tuna da ita.
****** Mijin Ammi ya gama aikin da yazo, don haka tuni muka tattaro muka dawo gida nja, gidansu na bauchi kerarriya a gra wanda duk wanda zai wuce gidan dole ya juyo yakara ganin wannan gidan, mun tarar da gidan tsaf tsaf ga mamakina na ga Amrah da wata dattijuwa yar gayu daga gani ita ta haifi Amrah, na gaisheta tana da fara'a sosai naga sai barkwanci sukeyi abun yaban mamaki sosai, sun san juna ne? sannan aina suka san juna da su Ammi? na kalli Fido na ce mata "meye alakarsu? " abun ya matukar bata dariya, don haka sai kawai tace " ki bincika da kanki zaki sani" nayi mamakin ganin gidan, domin kuwa kowa da dakinta nida fido sai dai fanninmu daya ne, haka sauran yaran Ammi. kayan mu kawai muka ajiye amma gidan babu abunda babu, sanin garin fiye da Fido yasa muka fito da ita na tambayi Ammi mota ta kuma bamu akan zamu je ko jifatu mu siyo abubuwan da muke bukata su tootthbrush da sauransu, sanye da abaya duk muka fito munyi matukar kyau idan aka cire kyan fatanmu da kuma kyalli da mukeyi , duk inda muka wuce sai an juyo an kalle mu, muka shiga cikin jifatu muka tsinci abubuwan da zai mana amfani , sannan muka fito muka dawo gida, shigowar motata yayi dai dai da lokacin shigowar motarshi , Gabana ne ya tsinke ya fadi haka kawai amma kuma murmushi ne a fuskata, sauke glass din motar yayi ganin fido yana murmushi ita kuwa tace "Cousin!" annurin fiskata gaba daya naji ta dauke don sai alokacin na tabbatar da cewa ba fahad bane Hamma ne, hannuna na rawa na dawo baya kadan duk da glass din dake idona baisa na gagara mishi kallon muzurai ba, suka gaisa da fido sannan ya juyo yace " daga ina?" tace " mun fito jifatu" kallona yayi amma jikina ya na bani baigane ni ba to ko ya ganeni ma kadan daga aikinsa yayi banza dani, ya ja yawuce nima na shige ciki , ina shirin parking motan tace " baki gane shi bane?" "na ganeshi mana" " na ga kin shareshi" " banda case da shi" mamakine ya ciko fuskanta don dai tasan cewa inba mafarki take ba hotonsa nake damunta ada dashi nace inasonshi, tasan tarihin soyayyata bawai bata sani bane, gashi ina nema na raina mata hankali. Har dare ban ga Fahad ba nima dama na gaji sosai don haka wanka nayi na sauko kasa gun Ammi tana kan dinning tana gyra plate na ce mata "Ammi meye alakar Fahad da Hamma?" ba taso na mata wannan tambayan ba don haka ajiye cokalin hannunta tayi sannan tace " Nadrah! dawowan mu banso shi ba saboda ke, nayi iya kokarina na hana fido ko duk wani acikinsu su fada miki wani abu dangane da Aliyu, tunda ga halin da kike shiga akansa don haka kawai kiyi hakuri kibar maganan nan kicire ranki kinga kin samu lafiya yanzu hankalin kowa ya kwanta,
Abamama ma baya garine da kin ganshi yanzu amma su kamal ma suna tahowa don haka bana so ki tayar musu da hankali" na gane me take nufi don haka kawai nace mata " wallahi Ammi na hakura da Hamma , na daina sonshi ni yanzu ba ruwana na miki alkwarin ba zakiji wani matsala a tattare da ni ba, don Allah ki fadamin kinga yanzu na ganshi a waje, kuma ban kulashi ba" "Nasan zaki yi mamakin kammaninsa, kammaninsa da Fahad yayi yawa, duk da cewa kanin Babansu fido ne wannan kam kin sani ai amma da Hameed tofi wato mahaifin Aliyu da kuma Babansu fido,Uncle Usman, da Fahad uwarsu daya Ubansu daya, ma'ana dai a takaice Fahad yana matsayin Bappah wa Aliyu" tsananin mamaki ya kamani, haba mana dole mana, kammanin yayi yawa ace kuma munyi zaman sama da shekara amma ba'ataba fada mun ba, lallaima Ammi sannunta da kokari, na girgiza kai cikin mamaki sannan nace "Ammi da gaske kar ki damu ni dai ba zaki kara jin wani abu daga gareni ba" ina gama fadin haka na mike na koma daki ina tsananin tunani duk da cewa ina jin dar-dar araina ayanzu shakuwar da nayi da Fahad yafi karfin tunanin mutum, akashi dari cikin son da nakeyi wa Hamma kashi 60 yanzu wa Fahad nake wa, Allah ya gani yanzu son da nake masa ba kaman da ba, na manta da al'amarinsa duk godiya wa Allah da taimakon adduan yan'uwa yasa yanzu ni kaina na huta. damuwata da addua'na shine tunda ina cikin kwanciyan hankali Allah yasa na dauwama ahaka tunda ni ban iya controlling love life dina ba, Ashe ni kam Nadrah ina nawa Allah na nashi tashin hankali rikici da kuma damuwa na dawo cikinta kenan. (zan ci gaba insha Alah jibi, kada ku manta its a true life story) . #ays
0 comments:
Post a Comment