CIWON IDANUNA Part 18-21 (THE END)
=== CIWON IDANUNA 18=== . Akwai randa nayi operation a TH na shigo a gajiye, ga yunwa ga bacci da gajiya duk ya taru mun Allah -Allah nake yi naga na mike na kwanta amma da na shigo wani wari da naji gidan yakeyi, ba'ayi shara ba tana sanye da rigan bacci sai chatting take yi, nayi tsaki na wuce daki na na rufo kofan, amma hankalina bai kwanta ba kar wani bakon kunya yazo ni zanji kunya don nasan zarah ba kunya zata jiba, kuma yanzu da zan mata fada kiran hajiya zata yi ta fara kuka hajiya yanzu zata fara kwashe min albarka,cire rigan nayi na iso cikin gidan na dauki tsintsiya na share gidan tsaf, nayi mopping dukka zahrah na zaune tana kallona kaman kishiyanta, ina gamawa na dauko turaren wuta na kunna sannan na kunna A.C bana son kazanta ko kadan, idona na jajur naje nayi wanka sannan nayi sallah nabi lafiyan gado, ji nayi kawai ana shafani agefe bude idona naga Zahrah, lallaima yarinyannan bata da hankali don tsabar rashin kunya tana gani nagama aiki amma tsabar iskanci tazo min don ta biya bukatarta bansan lokacin da na tunkude ta ta fadi akasa ba, " in ke jahila ce toh naje makaranta, ki fita min daga daki kafin na miki rashin mutunci wallahi" janta nayi na fidda ta da karfi na koma na kwanta sai bacci mai dadi, acikin baccin ana buga min kofa da karfi kaman zai fadi na mike da sauri don wallahi hannu nakai ina budewa na kwasheta da mari " don ubanki ba nace ki rabu dani ba? ke mahaukaciyar wacce gari ce?, banza kazama ba zaki kasheni ba" gani nayi ba ta dago fuska ba sannan halittanta kaman ba itaba, kafin nace me naji ankai min wani wawan mari "ashe baka da hankali ban sani ba Aliyu? dama saka ta kakeyi kayita duka? shine yau ni zaka dau hannu ka mareni? ni na tsuguna na haifeka? lallaima kana so in tsine maka ne? innalilahi wainna ilaihi rajiun na haifi yaro dan cikina yazo ya mareni" yadda ta maren tsugunawa kasa nayi don jikina na bari, yau nine na mari mahaifiyata oh God i deserve to die, kuka ta farayi tana cewa dama nayi niyyan kasheta, tunda nake bantaba ganin mahaifiyata haka ba, haka ta saka zahrah agaba suka fita suka barmin gidan, daga office aka fara kirana akwai aikin da zamuyi bansan lokacin da na kashe wayan gaba daya ba . Bazan iya misalta tashin hankalin dana shiga ba domin ji nayi dama na mutu akan wannan bakin cikin, gida naje har lokacin Zahra tana makale agefenta yadda nake ji kamar na tashi na kasheta amma ya zanyi mahaifiyata tana tsaye akan magananta , ji nayi kaman na ce na saketa domin na tsaneta, na tsani ganinta ba tsani zama da ita amma nasan akan maganan zahrah hajiya zata iya tsinemin albarka don dama tana barazanan, nayi zaman roko da ban hakuri amma hajiya ko kallona batayi ba zahra na makale agefenta harda kukana amma hajiya bata kulani ba ,Amrah ma tazo ta sa baki duk a banza amma zahra na bada hakuri ta bugamun sharudda tace ta hakura na dau matana mutafi gida, a hanya kaman in wurgata a rami in wuce sai dai na tuna bayanin hajiya da sharuddanta na farko ma shine karna batawa zahra rai, duk abunda take so zan mata ko inaso ko bana so , babu tsawa balle harara balle tsangwama duk bakin ciki nake hadiya wallahi zuciyata kaman nayi hauka, ban kulata ba haka itama bata kulani ba, washegari da sassafe nabar mata gidan, a asibiti aka kawo emergency wata za'a mata aiki nine zanyi aikin, a tarihi nayi aiki atleast guda sha uku successfully ko fiye da haka amma ban taba jin aikin danayi babu karfin gwiwa ba sai wannan, damuwa sai cina yakeyi, ina fitowa daga aikin na yanki jiki na fadi, tuni suka bani gado. Abokan aikina ne ya dubani nan yaji mamaki sosai " meya sameka ne? yau kai ne mai son daurawa kanka pressure, ka daina fa its so risky" nayi murmushi domin ni kadai nasan me yake damuna, Amrah ce ta shigo da sauri dakin tana haki kaman wacce kare ya koro " Hamma ya jikinka?" tana fada tana kare min kallo, " Kalli yadda kayi baki ka rame, meya sameka?" likitan ya fita ya bamu guri nikuma na tashi na dan zauna na jinginu da pillow sannan nace " ya hajiya?" "lafiyanta lao ta damu wallahi taso tazo amma ankai mata Junainah shi yasa ma ta turo ni, kayi hakuri don Allah yaya" shiru nayi natuno da Nadrah da ace tana raye na tabbata babu abu makammancin haka da zai faru, " Amrah sakayya nake gani na ubangiji, duk abunda nayiwa Nadrah shine Allah yake mata sakayya, wallahi nayi nadaman abunda nayi, arayuwata yanzu Nadrah nakeso Amrah, duk zama idan na zauna, duk motsi duk dakika dare da da rana sai nayi tunanin irin wulakancin da na yi mata, na jahilce kaina dana wulakantata, samun mace kaman Nadrah awannan zamanin ba abune mai sauki ba, kiga abunda zahra take mun, babu tausayi asalima ni jikina na bani bata sona, don da tana sona ba zata taba min wannan wulakancin da takeyi ba, ta hadani da mahaifana" jikina a sanyaye nake fada mata abunda ke damuna, tayi shiru tayi tagumi sannan ta shiga bani hakuri, ni dai haka na danne domin kuka naji yana son fito min kuma abun kunya ne nayi agaban kanwata, har ta gaji da zama sannan ta tafi nima mikewa nayi na koma office ina hada wasu takardu, amma kirjina ciwo yakeyi, damuwan Nadrah shine araina, da na gama hada komi na tattara na koma gida, junainah na wasa da ball a hannunta, naga wata sanye da abaya sai da gabana ta fadi domin idan sama da kasa zata hade na zata Nadrah ce, jikina na rawa na matso kusa da ita kawai naga fido ne ta katse min tunani da " ina wuni Hamma" ban samu daman ansa ta ba na juya zan dau junaina amma kukan da ta sakamin kaman na caketa da wuka da sauri fido ta zo ta dauketa sannan ta matso da ita kusa da ni, tana ta cusa kanta cikin gyalenta yayinda fido ta fito da hannayenta ta mika min, nasa hannu na rike duk da tana kukan tuni take jijjigata, hakan yasa tayi shiru, tana dan rera mata waka, har raina naji dadi sosai na zura mata ido kaman bazan daga idona akanta ba, har ta tsargu taja Junainah suka koma cikin gidan na bi bayansu, falo suka shiga nima haka naje na zauna agefe, tana mata wasa nikuma ina kallonta, ban taba nutsuwa na kallo Fido ba sai ranan, suna asalin kama da Nadrah don gizo take min, Hajiya data sauko tamin ya jiki ma ban bi takanta ba, damuwa na Junainah ta kulani duk da banajin kwarin jikina. Abinci naci da kyar na mike nabar gidan. Zahrah na kwance akan kujera yau anyi shara an dan kimtsa gidan duk da haka ban kulata ba nayi daki, domin idan akwai halittan dana tsani gani to yabiyo bayan zarah, ina kwance ta shigo, rike da kwankwaso " Hamma ka dubani banda lafiya" keyn mota na wurga mata, " kije asibiti" tayi shiru sannan ta dauka ta fice, tunda ta fita zahra bata dawo gida ba sai goma sha dayan dare, alokacin na kulu iya kuluwa jira nakeyi kawai ta dawo naji, tunda gashi nakira asibitin ance bata je ba, tana shigowa ina zaune a falo " daga ina kika fito?" "asibiti" "wani asibiti?" bata kulani ba tayi hanyar daki, a harzuke na mike na janyo ta ina sauke numfashi, fizgewa tayi tamin kallon sama da kasa sannan ta shige dakin tana jan tsaki ta rufo kofar, wani wawiyar yawun bakin ciki na hadiye sannan na dawo na zauna, kaina har ya fara jiri, if not saboda hajiya zan iya marinta na mata duka sannan na turata gidansu, wannan ai karamin karuwanci take min agida, daki naje na kunna A.c amma bashi zaisa ban hada zufa ba, ranan banyi baccin arziki ba ina tunanin hanyan bullowa Zahra, laifin da tayi bai isheta ba washegari da sassafe ta kunna waka ta hau rawa, daga ita sai rigan bacci, tun ina jan tsaki har na mike na shiga toilet nayi wankan dole na fito, har lokacin bata daina ba, na ja tsaki na fito anan na tuna ashe keyn motan na hannunta,da akan na koma nace ta bani na gwammace na hau machine na tafi gun aikin haka, ina zuwa asibiti akace directorn mu na kirana, na nufi office dinshi bayan mun gaisa yake cemin " na lura kwana biyu kana cikin damuwa, me zai hana kaje ka huta na kwana biyu ko? in ka dawo sai ka cigaba" shiru nayi sannan nayi godiya na fice, sai dana shiga office din anan ake sanar min wacce nayiwa aiki jiya ta rasu, surgeryn wasnt a success, shiru nayi naje office na kwanta kaina , na tuna lokacin nadrah tana raye duk lokacin da nake cikin damuwa a office idan ta ganni bata zama, snacks zata nemo min bayan kwaliyya da kamshin da takeyi, tana mun tattausan lafazi duk da bana kulata sai dai na mata tsawa. === CIWON IDANUNA 19=== . Irin abunda Nadrah take min nake tunawa kaman in dawo da baya, Allah sarki, dama baka sanin amfanin abu sai bayanan, zuciyata na radadi ina lumshewa ina ganin Nadrah da murmushinta, ko meye na mata bata jin haushi , bata zuciya sannan bata min rashin kunya. Atakaice nadawo banda aiki kenan tunda ance naje na huta na kwana biyu, nikam gwara na tattara natafi abuja, toh nan ma hajiya tace ban isa ba sai dai na tafi da zahra, ni kuwa da inje da zahra ta kutsa min bakin ciki gwara na zauna anan dukkanmun mu zauna haka, zan jira har su kara kirana na koma tunda ma anci sa'a ba'a karbi license dina ba, zirga zirgan Junainah nasa agaba alokacin ana son sata a makaranta, zuwa nayi na bada dubu dari uku nace gashi duk makarantan da akeso a bauchi a sata,Ammi tace yayi yawa amma nace ta barshi sauran ayi mata shopping, Fido bata nan alokacin don haka sai na zauna akan zan ga junaina while ita nakeson gani, ni kaina bansan dalilin da yasa na keson ganin fidon ba, bata fito ba sai can yamma, tayi kyau sosai , sanye da dogon riga kore yasha aiki ta tumbuke gashinta ta gefe , daurin dankwalin ya zauna dam dam,sai kawai naga kamar Nadrah, zuciyata tana bugawa sosai na tsorata, Ammi har ta gane tayi gyran murya da sauri na sunkuya kaina akasa ina sosawa nayi murmushi itama murmushin tayi alokacin fido ta gaishen na amsa cikin ladabi sannan ta nemi guri ta zauna, ni kuwa nabi ta da kallo gabana yana fadi wanda ni kaina narasa meyasa ne, Ammi ce ta lura da hakan tace " yau kanwarka gizo take maka?" na sosa keya sannan nace "wallahi ,Nadrah nake gani fa suna kama sosai" tayi murmushi sannan tace " haka mutane ke cewa, wai kaman yan biyu, bayan kaine kake kama da fahad ko tambayansa baka yi" na girgiza kai ina murmushi nace "" tun rasuwan Nadrah ya daina min magana, dashi da kamal kaman su kasheni haka suke ji, bayan abunda ya faru da Nadrah wallahi kaddara ce, ni kaina ina Nadama sosai, Allah yayi hanyan ajalinta kenan amma nayi Nadama Ammi har yau ina ganin sakamako, bana ganin farin ciki arayuwata tunda ta rasu sai sakkaya" Dukkansu shiru sukayi inbanda Junainah da take ta wasa da Ammin, hakuri dai tayita bani, yayinda Fido ke kara gayamun yadda Nadrah ke sona , tace lokacin da Nadrah ta fara shaye shaye ba wanda yasani, ita dai ta taba ganin wiwi ne shima batayi tunanin sha takeyi ba tayi zaton zata saka a gashi kaman yadda mata ke hada man gashi daga baya tazo taga ba haka ba, tace lokacin da Nadrah ta ganni da zahra a mota tana bin mu abaya, tsabar sauri sai data buge motanta ita kanta taji ciwo sosai amma bata damu ba, abubuwa da dama wanda ya narkan min da zuciya ina kallon fidon gaba daya yanayin jikina ya canja. Ban bar gidan ba sai tara na dare cikin ikon Allah na nufi gida, kofan gidan arufe don haka na ciro mukullai na bude na shiga, shiru naji alamun babu kowa sai dai tunda naga mota awaje nasan tana ciki, har na je zan bude dakina naji nishi kaman mutum kaman ba mutum ba, na juya ahankali sannan na nufi inda na ke jin karan, murda hannun kofan nayi na bude ba tare da nayi wani tunani ba, Zahrah ce akwance da wata haihuwar iyaye, salatin da nayi yasa suka juyo suna kallon na, na koma dakyar ina jan kafana babu mafi munin gani irin abunda na gani yau, numfashi na daukewa ya farayi na fara rike kujera na zauna duk ina numfashin sama sama, ta fito dasauri tabar gidan bansan lokacin da na mike naji karfi ajikina ba na ha wayan cable na shiga dakin na rufo kofar, da na fizgota da karfi na fara dukanta wallahi sai da cable dinnan ya tsinke, na cire belt shima ya tsinke, sai da na tabbatar numfashi ma dakyar takeyi sannan na rubuta mata saki uku na damka mata nace tabar min gida adaren kuma idan ta kuskura ta waiwaye hajiyata ta tabbata sai na kasheta. Yadda naga dare haka naga safiya, sai juyi nake akan gado can dai na dauro alwala nayi masallaci, a wajen gidan nake ganin maigadin sai gyangyadi shima yake kofar a wangale hakan ya tabbatar min da Zahra ta bar gidan, da na idar da sallah na dawo anan bacci yadam dibeni. Wayata ce tayi kara hakan ya tasar dani daga baccin da nake na dauka na saka a kunnena ba tare da duba sunan naga waye ba, "kazo gida yanzu ka sameni" tana gama fada ta kashe wayan, yayinda ba shiri na fado daga kan gado na shiga toilet, gabana sai fadi yake ina tunanin me zanje na tarar a gidanmu, minti sha biyar yakaini gida tun daga bakin gate naci karo da motan drrivern hajiyan Zahra, dama nasan zaa rina, na shiga nayi sallama dukkansu suna zaune tamkar wanda suke jirana, na tsuguna na gaishesu hajiyan zahrah ta amsa ba yabo ba fallasa yayinda Hajiya ta kam ko kallona batayi ba, "Me ya hada ka da Zahrah?" idona na kai kanta na zura mata ido, tana sanye da hijabi , munafukar yarinya su suke batawa masu hijab suna, Allah sarki saboda wannan kucakar na wulakanta Nadrah wayyo Nadrah, "Tambayanka na keyi meya hadaku?" hajiya ta katseni daga dogon tunanin da nakeyi kafin na bada amsa zahra ta cabe baki tace "Hajiya da gaske ni nace ya sake ni, naga kaman ina takurashi har yanzu yana kewar tsohuwar matarsa" "maganan banza maganan wofi, yaushe ka fara son Nadrah? yarinyar da ka wulakanta, ai ba kaga komi ba, kadan kenan daga rayuwarka har kukan jini sai kayi akanta, ina kai wasa da soyayyan wata? tsabar ka raina min hankali shine bazaka zauna da matar taka ba? toh ka mayar da ita" Harara na sakewa Zahra jin karyar da tayi babu alwala balle sallah sannan nace " hajiya saki uku ne ba daya ba" wani naushi ta sakemin sai da hajiyan zahra ta riko ta " ka tashi ka bani wuri, kanaso ka kasheni ne? Haba Aliyu!" jiki tsum tsum na mike na bar musu falon, waje nazo amma na gagara nutsuwa, abu daya nake tunani yadda zan lallabata tayi hakuri hanya daya ne, ta ganni da mata babu abunda ta tsana kaman ganina haka, to yazanyi yanzu kam bazan taba yin aure ba sai auren so. Gidan Ammi na nufa don ganin Ya ta ko zanji sanyin rayuwa, a tsakar gida na tsince su,Fido na turata a keke sai da gabana ya fadi da ta juyo tana min murmushi,Nadrah na gani sak a fuskanta, Junainah na ganina ta tafara buya abayan fido tamkar taga dodo, jiki a sanyaye na karasa muka gaisa na mika mata hannu amma sai "a'a" take cewa "unma fido kay ki kaini gun dodo! unma fido kay ki kaini gun dodo!!" tana fada tana buya, fido ta janyo ta tana murmushi " ba dodo bane abbanki ne!" amma ganin zata miko ta guna ta saka wani irin kuka mai tsanani dole ta janyeta suka shiga ciki ni kuma na bisu abaya na gaida Ammi kaina akasa tana ta murmushi ni kuwa na zurawa Fido ido ina sosa keya, Ammi lura da hakan yasa ta mike tabar falon, duk kokarina na janta da hira taki sakewa alamun na takurata da kallo har aka kira sallah kafin na bar gida, Abbanmu ne yakiran yanemi yaji dalilin sakin zahra nace masa ita tace na saketa, tunda ita ta fadi hakan zan rufa mata asiri, acikin kwana biyu akazo aka tattara kayanta Allah yasa babu rabo a tsakaninmu, ni haushi da kyama take bani, nanma tunanin Nadrah ne araina da Nadrah nada rai da duk wannan bai faru ba duk da hajiyata gani takeyi tamkar wani mugunta nayiwa zahran nace karta fada. Na mayar da gidan Ammi gidan zuwana, sai na fake da zuwa ganin junaina amma zahiri fido nake gani, bata da surutu akwai ta kamun kai ga kunya duk abubuwan da takeyi yasa na kamu da sonta fiyeda yadda nake zato, gun aikina ma dana koma duk da an dakatar dani dayin surgery akan zasu turani wani course naje nayi nafara processing, ina fitowa daga gun aiki gidan Ammi nake zuwa anan nake cin abincin dare nayi sallah ina zuwa gida sai dai nayi bacci, wata ran mukan hadu dasu Amir ko usman ko Kamal, akwai randa na hadu da Abamama shi kanshi yayi mamakin ganina anan Ammi tace masa ai kullum ina zuwa ganin junainah, itama junyn yau da gobe sai Allah ta rage tsorona sai dai har lokacin bata kaunar tsayawa kusa dani kullum ta gefen Ammi ko Fido, Nayi iya kokarina in gwadawa fido tsananin son da nake mata amma baiwar Allahn nan ta matar dani baho, gwadamin takeyi ba ta masan meye nakeyi ba balle ita kanta soyayyar, gata da ado da kwaliyya, ranar nayi kokari zan sanar mata nasha wanka na bayan na dawo daga aiki naje gidan, junainah na bacci don haka kawai na zauna muna gaisawa ta kawomin abinci tana murmushi har ta tashi zata wuce nace "Firdausi ji mana" ta tsorata sosai daga yadda ta kallen domin kuwa na gani a fuskanta tace "toh" sannan ta sallami su abakkar da muhd kabeer suje suyi wasa don suma kullum suna gefenta in ba wai in sun koma makarantan boardn ban, "Akwai abunda nakeson ssnar miki kuma ya damen hakan yasa nace gwara na sanar miki ko zanji sanyi araina" kanta akasa ta gyada kai sannan naci gaba " Kinga tsakanin mu babu boye boye sai gaskiya, kinga junainah ta saba da ke sosai tamkar mahaifiyarta kuma anci sa'a ni mahaifinta na ganki na fara sonki, So da bana tsamannin na taba yiwa wata mace ina miko kokon barata ki taimaka ki amince ki soni" murmushi tayi wanda ya fara bani hope sannan tace "Da gaggawa zanyi hanzarin kin amince maka, kamanta bahaushe na cewa in kaga gemun danuwanka na ci da wuta ka shafa wa na ka ruwa? kayi hakuri banjin zan iya zaman aure da kai, Junainah ta girma tace meye?" "hmn, Firdausi Karki min illah, ban taba wasa da so ba, bakuma zanfara akanki ba, nasan inada mummunan kaddara a tattare dani don Allah ki manta da wannan, kinga gani gaki ga Juny, kuma ba haramun bane " " uhm, Hamma kenan! bar ganin Allura kankanuwa karfe ce, wannan junainah da kake wa kallon ba tasan komi ba inta girma taji labarin yadda kukayi da mahaifiyarta me zata ce akaina?" " ni ki daina min magana da karin magana bana ganewa, yanzu dai kije kiyi tunani, koma meye don Allah" "babu tunanin da zanyi, na yanke shawara ta kuma shine bazan iya zama da kai ba" tana gama fada tabar min falon, shinkafar dake gabana naji duk ta fitamin akai, mikewa nayi nabar gidan. Tun daga ranan naga sauyi agun fido, ta daina zama a inda nake da zaran nazo zata hada Junainah dasu muhd kabeer ta shige daki ko basa nanma sai dai ta hadota da mai aiki, duk jikina yayi sanyi yayinda alokacin nakejin wani irin tsantsan son Fido araina , kyakywar numfashi nayi sai na tuna da ita, gaba daya nayi loosing control, ciwon zuciya zai iya kama ni ahalin da nake ciki gashi dama jinina yahau, akwai randa adaki ina zaune kawai naji na fara hawaye, abun ya matukar bani mamaki na danna wayan fido tana jin nine ta kashe wayan, ni ko ganinta na samu nayi naji dadin rayuwata amma babu hali. Randa naje nasa araina sai na ganta na aika mai aiki taje tace tazo taki fitowa, nasan abu daya zaisa tazo shine junainah tafara kuka sikuwa na danne raina duk da abunda na tsana kenan naji kukan ta na dauketa, kukan data farayi kaman taga malaikan mutuwa ba shiri saiga fido ta fado a falon ko dankwali babu da sauri na rufo kofan ta karbi junainah tana lallashi nikuma na tsaya abakin kofan, kallonta kawai da nakeyi wani sanyi nakeji araina, ashe haka so yake da dadi? haka so yake da daci? haka so yake da radadi? " ka matsamin" "don Allah kiyi hakuri wallahi ina sonki, bantaba furtawa wata mace wannan kalamun ba sai ke" ficewa naga zatayi na riko hannunta da karfi ta fizge sannan tace cikin bacin rai "Don't!! karka kuskura ka fara ina ganin mutuncinka, ko giyan hauka kasha don't you dare touch me" ta bankade kofan ta fita, bantaba jin zafin nadaman shan giya ba sai ranan, ashe skwai ranan nadama , duk wanda yamin gori bana damuwa amma akan na fido sai dana zubar da hawaye.Nafi minti talatin a zaune can dai na yanke shawaran samin Ammi ko zata tsawata mata, ina zuwa na tarar da ita a falonta na gaisheta cikin ladabi sannan nace "Ammi nazo neman alfarma duk da nasan ban cancanci wannan alfarma ba" "ina sauraronka, Allah yasa alheri ne" "sosai ma, Ammi ki aura min Fido wallahi na yi alkawarin yi mata duk abunda takeso, bazan cuceta ba, wallahi tallahi Ammi ina sonta" murmushin da tayi sai daya fadar mun da gaba sannan tace " kai kuwa Aliyu ka taba ganin An ciji mumini a ramo sau biyu? ai da zaran an cijeshi na farko in har shi mumini ne bazai kuskura yace zai koma ba". === CIWON IDANUNA 20=== . Yayi Murmushi sannan yace "Na baka, duk abinda na mallaka ai na Danuwa nane" Yadda Ammi ta bata rai ta mike sannan tace " bangane abun danuwanka ba, jiya na gama maka bayanin dalilin da yasa ba naso ahada aurennan" hannu ya saka mata alamun ta masa shiru hakan yasa ta juya kanta tana jan numfashi shi kuwa yace " zanyi magana da alhaji gobe , Fido ta zama naka insha Allah, ni na isa in hanaka wani abu da kakeso aguna? bayan mahaifinka shine silan duk abunda na mallaka a duniya in ita ta manta ni ban manta ba" farin ciki ya zo min na mike cikin gaggawa ina godiya gidanmu na nufa domin babban daron yana gun hajiyata yanzu nasan sai ta hanani auren Fido tace zan wulakantata kamar sauran matan, dakinta na nufa tana kan sallaya na gaisheta ta amsa sama sama dama tunda na saki zahra dama ta daina min murmushi ko sake fuska kam tunda Nadrah ta rasu ta fara tamke fuska sakewan kadan ne shima acikin mutane, "Hajiya nazo neman alfarma ne" "inaji" "Na roki mahaifin Fido ya bani aurenta ya amince inaso don Allah ko Alhaji yakiraki akan maganan kisa albarka shine nace barin fada miki" Kallona ba tayi ba sai data idar da adduanta sannan ta juyo tace " so kake yi itama ka aurota sai ka wulakantata ka raba mutuncin dake tsakani? ko ka manta mahaifinta danuwan Alhaji ne? ba zaka cuci yarinya ba ingaya maka in har kaga ka aureta toh na mutu ne" Yadda tayi maganan babu alamun wasa a tattare da ita don haka nasan ba wasa take yi ba jiki a sanyaye nabar mata dakin kafin ta kara harzuka, gidanana na nufa sai gani ina sallah tsakar dare ina rokon Allah ya bani fido har da kuka na, anan na tabbatar da ina sonta tunda abunda ban taba yi ba kenan, nasan ko da duniya da yayanta zasu taru suce zan auri fido idan hajiya ta tace a'a babu wanda zai aura min ita, abu daya nasan anyi shima bata so daga baya da aka lallabeta ta yarda wato aurena da Nadrah, yadda aka bata labarin yadda take sona aka lallabeta yasa ta amince amma bayan haka sai dai batace abu ba toh ya zauna, mutum daya ne zai iya juya min ita shine Allahn da ya halliceta na yarda komi baya gagaransa. Rikici sosai akayi akan maganan auren domin kowa ya amince amma Hajiyata da Fido sunce basusan batu ba haka Ammi ma, wannan mutane uku kadai sun isa su hanani kwanciyan hankali ko da ace andaura, Ammi ta dage bazaa yi auren cin amanar yaruwar ta ba, Hajiya tace bazan raba zumunci ba haka zalika fido tace bazata ci amanan nadrah ba, Ni abun da ya damen shine na kasa ganewa tana sona ne ko ba ta sona? dukka hayaninyansu baisa na hakura ko na daina addua ba tuni na dukufa agaban ubangijina na rokeshi na kuma kai kuka na agareshi, Alhaji yayi iya kokarinsa ganin ya shawo kan hajiya amma batu yaki ci yaki cinyewa, tun ina azumin har nazo na fara ramewa , kana ganina kaga tsantsan damuwa ga idona yafito guli guli inbanda kasusuwa babu abunda mutum zai tsinta ajikina, na dawo kaman dan maula kullum ina kofan dakin hajiya ko zata amince mini amma kaman bawa haka hajiya ke yi dani, ta koreni na dawo na zagen dukka naki zuciya, wataran haka nake zama akofan dakinta inta kuka amma ko ajikinta rufe ma kofanta take, Amrah tun bata kulani ko jin tausayina tadawo itama tana tayani zama toh haka hajiya ke hadamu ta koremu, tace bazamu mayar da ita tsohouwar banza ba, " yaushe yaushe zahra tagama Idda? zaka kawo min batun mace, kai kenan sai kace bunsuru? kabi wannan kabi wancan? daga karshe ka wulakantasu toh ban isa karaba zumunci yadda kayi afarko ba inaji ina gani nida hajiyan zahra mun daina mutunci kaman da saboda kai dan iskan yaro maras ta ido!" kullum mitan kullum daban ban taba zuciya ba, akwai randa tun safe dana dawo daga asibiti nake zaune akofar dakinta ba ci ba sha, sallah ma agun nakeyi kuma dama kwanana uku banci abinci ba, asali abinci rabona dashi tunda ta hanani fido,haka ma zauna ina jingine da bango ga wani sanyi da akeyi jikina na bari amma naki tashi karshe suma nayi awajen. ko da farkawata ganin hajiya nayi tana kuka cikin damuwa, duk da bansan meye ba nariga nasan nadama takeyi akan abunda tamun, lallabani ta rinka yi nikuwa na kara langwabewa domin samun biyan bukata nace "Hajiya ki taimaka ki aura min fido, wallahi nayi alkawarin Riketa amana" shiru tayi ba taban amsa ba sai dai nasan da sauki ba kaman da ba bata rai zatayi ta zagen, a gidan na kwana aranan washegari Amrah da gudu tazo daki take sanar mun hajiya ta amince da batun aurena da Fido acewarta tace kar ma rabone yake so yazo duniya ta hana Allah ya kasheta kuma ayi auren, sujjada nayi ina godiya wa Allah da ya nuna min wannan rana don wani dadi naji araina karshen wahala ta tazo ko ince karshen sakayyar Nadrah kaman yadda mutane suke fada, wanda ni ayanzu gani nakeyi duk da nine ajalinta, rabo ne ya kasheta domin da tana raye bazan taba auren Fido ba, Allah shine masani akan al'amuransa, duk da haka ban nuna na watsake a damuwata ba danaje gaishesu a falo alhaji ya kallen cikin tausayi yace "sannu ko! kaman ba Aliyun da na sani ba dan gaye dan kwalisa, yanzu duk kayi baki ka fita hayyacinka" sosa kaina nayi ina murmushin karfin hali hajiya kuwa sai tura min sakon harara takeyi kaman ba itace take ta shekan kuka ba, " Ka ce kai sai yar'uwarka dama mahaifiyar ka ce taki amincewa amma yanzu ta amince yanzu zamu garzaya zuwa neman aure, sai dai inaso Aliyu kayi hankali kaji? ka nutsu, mata da kake gani ba'a biyewa yarintarsu, har yau bamusan rabuwarka da zahra akan meye bane amma ni ina kyautata zaton gajen hakurinka ne kawai, ka koyi hakuri da fahimtar mace kaji? kowa daka gani da haka yake rayuwa in baka fahimcesu ba toh an rinka rabuwa dasu kenan" Shiru nayi har ya gama waazinsa wanda na dauki kowanne nasaka araina, don ni yanzu jina nakeyi kaman ban taba aure ba yanzu zan fara. Acikin satin aka kai gaisuwa aka bada sadaki akasa rana har lokacin bana ganin sassauci agun Fido, asalima ita kam tattarawa tayi tabar gidan wai taje gidan Hajiyati kakarsu, yadda bazan iya zuwa ba tunda tasan yas kamal na gun haka sauran yanuwan Nadrah, Ni da kaina nasiyo kayan gyran gida ina tsaye suna gyra, dakaina naje na hado kayan aurenta wanda daga Nadrah har zahra babu wacce ta samu irinshi, na tura mata kudi a account dinta duk da bata tambaya ba, ba ta kuma nemeni ba illa sako da ta bayar abani na nude takardan cikin zumudi duk da ga waya amma ta tsallake tayi a takarda jiki na bari na bude na fara karantawa kamar haka Daina farin cikin ganin wasikata don nasan yanzu haka jikinka bari yakeyi, na yine na sanar maka cewa bana son rawan kai ban kuma ce ka samin dukiyarka a account ba, idan dashi kake sayan zuciyan yanmata to kasani nawa yafi karfin dukiyarka , magana ta biyu bar farin cikin burin ka yacika zaka aureni kaiconka! ashe har zaka manta laifin da ka aikata wa yaruwata? kana tsammani zan manta ne? kayi shirin taron bakin ciki a rayuwarka! acikin gidanka! a mafarkinka! a duk yanayin da kake ciki, . Yaga wasikar nayi ko ajikina domin babban burina na aureta, kuma tunda an amince komi zaizo cikin sauki, Haka dai aka fara shirye shiryen biki, ba yabo ba fallasa tayi biyayya duk da bansan yanda iyayenta suka saka ta amince ta kuma daina damuwa ba har na fara tunanin ko tana sona boyewa takeyi? walima akayi sannan aka daura aure, mummy wannan karon taki yin dinner acewarta kunyan jama'a kadai ma ya isheta , Randa aka daura aure tazo ta zaunar dani kaman karamin yaro "Aliyu wannan karon ba doka nake baka ba rokonka nakeyi, don girman Allah ko bayan raina ko firdausi yanka fatarta takeyi tana ci ban yarda ka saketa ba saboda zaka raba zumunci, in kasancutar baiwar Allah zakayi ka fada tunda wuri musan makomar mu, in har ka saketa ban yafe maka ba, Allah ya isa tsakanina dakai kuma" wannan ne karo na farko da hajiya tamin kashedi mafi ban tsoro kaina akasa nace "Hajiya wallahi ina sonta kiyi hakuri don Allah insha Allah ba abunda zai faru ma" jiki a sanyaye na koma falon alhaji shima haka ya ajiyeni kaman karamin yaro yamin waazi sosai, ya gwada min rayuwar mata da yadda ake tafiya dasu yace " Su mata da kake gani rauni garesu, kuma kai zaka tarbiyartar da mace yadda kakeso arayuwa, hakuri da mace dole ne, kar kace zaka yiwa mace dole baayi musu, raayi da dai sauransu, kuma kayi HAKURI, kayi HAKURI, sannan kayi HAKURI! ka kai zuciya nesa ka jini ko babana?" na gyada kai sannan yasamin albarka na tashi na fito jiki a sanyaye. Aranan aka kai amarya dare-dare wannan karon ba'ayi wani bidi'an kaita gidanmu ba tukunna, kai tsaye gidanta aka kaita har lokacin gabana fadi yakeyi haka kawai nake bala'in fido, kajina naje na siyo da fresh milk, dakina na nufa nayi wanka na canja kaya sannan na nufi hanyan dakinta, ina murdawa naji ansaka key , na buga amma shiru akeji, nakira sunan fido kaman muryata zata tafiya amma baiwar Allahn nan ko motsinta ban jiba, na ajiye kajin na jingina da bakin kofan na rasa me zanyi, anan bacci ya kwashen ban tashi ba sai asuba, ina farkawa kawai na ganni a yashe kaman kayan wanki , na janye jikina nayi daki na dauro alwala na nufi masallaci, dawowa ta naga dakin abude na leka naganta akan sallaya na isa gun na zauna na jira naga ko zata idar, baiwar Allahn nan data fara sallah sai dana kai sawun wani baccin kafin ta idar, na farka na samu tayi wanka tana zaune tana danna wayanta, gaisheta nayi sama sama ta amsa tare da cewa "zan gyra dakina ka fita don Allah" jiki a sanyaye na fice na yi wanka sannan na fito. Wunin ranan tayi shi a daki da zaran na shiga zata ce min na takura ta haka nake fita tsumtsum, duk yadda naso ta kulani ta nuna bata san batu ba dama daga gidanmu ake kawo abinci, sai ta dibi nata tabar min nawa. === CIWON IDANUNA 21=== ****** KARSHE ****** . Sati daya muka jera da fido muna wasan kura, da zaran na zauna agu sai ta tashi asalima sai inaga kaman kyankyami na takeyi, Da zaran na fita sallahn magrib toh kafin na dawo zata danna sakata wa kofanta sai kuma da safe, ranan da na gaji tun daga asuba agida na fara sallah naki matsawa balle ta samu hanyan kulle kofa, magrib nayi na tattara sallayan na shiga dakin ta dashi da kayan tea na da kajin da nasa akawo min duk na ajiye, ta shigo tana kallona rike da kunkumi " ka fita min adaki" ina zaune agefen gado ban kalleta ba balle nasan tana wani abu, ta kara matsowa " magana nake maka" na kalleta idona yayi jajur wanda ni kaina bansan halin da nake ciki ba, tsorata tayi ta juya ta dauki pillow daya zata fita hakan ya tabbatar min da lallai tana da niyyan barmin dakin, hannunta na riko da karfi ta juya zata fizge tamin yadda ta saba yi da sauri na rike dayan hannun na zura mata ido, duk matsifan idonta sai da ya tafi babu shiri, juya kanta tayi na sa hannuna na juyo da kan nata sannan nace "ki kalleni kimin rashin kunyan, kinsan hukuncin macen da ta gujewa mijinta ko baki saniba" duk jikinta yayi sanyi hakan ya tabbatar min da lallai tana sona ko da kuwa son kadan ne, domin da bata sona zata fizge jikinta ne tabarni agun, " kin wahalar dani fido, nasan nayi kuskure amma ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mai yasa ke bazaki yafe ba? ki na amfani da Nadrah ne ki bata min rai amma na tabbata kinada hujjanki daban, kiyi hakuri wlh na azabtu da yawa, kece mace ta farko dana fara so kuma kece ta karshe da yardan Allah kiyi hakuri Fido", sauran hawayen dake makale a idona ne ya zubo,janta nayi ahankali nace muyi sallah a sanyaye ta saka hijab , na jamu sallahn isha sannan mukayi nafila, na juyo zan mata addua naga hawaye fam a idonta, atake na rikice " me ya sameki don Allah? kiyi hakuri idan na bata miki rai" na janyota ina rarrashinta a hankali , kuka tayi sosai, harda shesheka abun har ya fara bani tsoro na rasa dalili gashi taki magana, dakyar na lallabata na tofa mata addua sannan na shimfida ta akan gado. Washegari da sassafe da rawar jiki na tashi na daura mata ruwan wanka, na tasheta a hankali amma kunya yasa gaba daya ta gagara fitowa ganin haka yasa nabar mata dakin don ta samu ta kimtsa, jiki na rawa na hada mana abun karyawa na jera a dining ina jira tazo muci, ashe haka aure yake da dadi idan kana so kuma ana sonka, masha Allah yanzu nasan nayi dace, Bayan samun fido a cikakkiyar mace, na samu fido mace mai hakuri, kunya da ilmi, hangen nesa da zurfin tunani, ta dawo abun alfahari ga dangina, Ashe ta dade tana sona tun Nadrah na raye sai dai kasancewwar yaruwarts na sona yasa ta hakura, tabbas nayi dace, da wuri naje na dauko junainah, Fido taci gaba da riketa tamkar yar cikinta wannan karon Juny ta daina tsorona ba kamar da ba kasancewar kullum tana ganina kuma ina hadawa da adduoi Allah ya jikan mahaifiyarta. BAYAN SHEKARA BIYU Shigowa gida nayi don na gaji mun fito daga wani surgery na tarar da Junainah a tsakar gida , tana ganina tazo da gudunta "Abamama oyoyo" nayi dariya sosai ina janta har muka shiga jiki aikuwa Fido ce ta fado ajikina itama da salon nata oyoyon, "wayyo zaki kasheni " " kana mutuwa zan bika" " ina kika bar Rahama da Amira?" " suna daki" "muje, nikam bana hanaki barin min yan biyu su kadai ba, don kin samu Allah ya baki su? wannan baiwa haka?" tana murmushi ta riko junainah mukaje har dakin na zurawa yan biyun da Allah ya bani kyauta ido, suna mugun kama dani , hawaye naji sun fito min nasa hannu na goge, fido ta kallen sannan tace " zaka fara ko?" " uhm! ba abunda zan fara,Allah ya jikan Nadrah Allah yasan dalilin daukan ranta, rabon wannan yan biyun domin kuwa da ina aurenta bazan taba aurenki ba, Allah yabar wa kansa sani,Allah ya barmin ke matata" na rungumo ta ina goge hawayen da suka makale. BISSALAM*** Na gode da kukayi hakuri da nayi har na gama wannan littafin, i just hope fadakarwan dake ciki mutane zasu gani GAREKU SAMARI DA YANMATAN YANZU MASU WULAKANTA MASU SONKU , MAI KUDI, TALAKA, MAI KYAU KO MARAR KYAU DUK DAGA ALLAH NE , MUBAR WULAKANTA MASU SONMU DOMIN BA MUSAN INA GOBE ZATAJE DAMU BA. . Jinjina ga marubuciyan wannan littafi Haj. BINAZEER UMMAR . sai kuma ni da nakawo muku Abdullah yahaya saad nake cewa sai mun hadu a wani littafin anjima. . ADMIN Abdullahi yahaya saad zaria (AYS) 07066508080
0 comments:
Post a Comment