SURBAJO Part 10
.
Tunda Al-ameen yadawo da surbajo gidan kullum ba
ranar banza da Aisha bazata nemi surbajo da rigimaba. Itako bata kulata ko kadan,lokuta da yawa dakinta take shigewa tabarta Tana 'ba'batu.
Yau asabar tun safe surbajo keta shiri,sabida Al-ameen yace, tashirya suje makarfi,murna gurin surbajo baa magana,kamin Tara tayi tuni tagama shiryawa ita Da Yusuf,oga kawai take jira yafito,dayake ba girkinta bane Aisha ce dashi,
.
Se karfe goma Al-ameen yafito cikin shirinshi na tafiya,lokacin surbajo duk tagama kosawa,koda yashigo dakinta, kauda kanta tayi gefe, ita ala dole tayi fushi.
Karasawa yayi kusa daita,yaruko hannunta yace,
"haba my charming princess, menayi kuma ake fushi Dani?
Turo bakinta tayi gaba, alamun shagwaba,tace,
"ay bandauka yanzu zaka fitoba,nadauka se wata safiyar,
Dariya yayi kawai,azuciyarshi yasan kishine yamotsa nanko batasan shikadai yakwanaba.amma afili cewa yayi,"am so sorry baby it will never happen again OK, yadaga mata gira daya ya kashe ido daya.
Murmushi tayimasa, metafiya da hankalinsa,sannan,tamike tadauki jakar kayansu,shikuma yarungumo Yusuf suka nufi mota.
.
Tafiyace sukayi mecike daso da kaunar junansu,Al-ameen ne ke driving din dakansa.
Se wajan shabiyu na rana suka isa garin,wayyo dadi, surbajo rasa inda zatasa kanta Tayi,suma 'yan gidansu kowa se tattalinta yakeyi,Yusuf ko, tuni ardo yaamsheshi yanamasa wasa,sosai kowa ke murna da zuwansu,kankice me gari yadauka duka surbajo tazo da mijinta harda Danta,nanfa jama'a sukaita zuwa ganinta,kowa yazo da tsarabarsa yake fita.
Al-ameen har mamakin farinjinin surbajo agurin yan garinsu yake,yaga kowa da farincikinsa yake zuwa ganinta.
Surbajo babu inda batajeba acikin garinnasu,tagaida kowa kuma tamusu abin Alheri.
Shide Al-ameen behanataba,yana zaune tare da ardo da Yusuf,Dan ardo hana surbajo tafiya yawon gidajen yayi da Yusuf din,wannan Abu da ardo yayi,yafaranta ran Al-ameen sosai.
Se magaruba suka baro garin,dan fafur yahanata kwana, ba irin magiyar dabatayiba amma yaki,ardo ma kuma yagoyamasa baya,shiyasa suka tafi.
Karfe takwas na dare suka shiga gida,dayake girkin surbajone sallama kawai yaje yayiwa Aisha yadawo bangaren surbajon, adaren, tamusu girkin abinda zasuci, Dan ta tsani siyan abinci awaje.
***********
Bayan shekara daya,
.
Rayuwa taci gaba da tafiya, inda abubuwa da dama suka faru,aciki harda auran munawwara inda ta auri wani custom suna zaune a Legos.
Bangaren Al-ameen ko, sauyin gurin ayki yasamu gamida Karin girma ,yanzu andawo dashi Abuja da Ayki,
Da surbajo yatafi, Inda yanemar mata university anan abujan, tafara zuwa, Tana karantar low. Tuni ta yaye yusuf sabida yaron akwai girman jiki, ga wayo sosai bame zaton shekararsa daya Da wata biyar sabida girmansa,a kaduna tabaroshi, gurin iyayen Al-ameen din,tundaga yaye suka rikeshi.
sede duk sanda al-ameen yasamu dama,yazo kaduna gurin Aisha, yay sati biyu Yakoma Abuja,
Bangaren soyayyarshi da surbajo se abinda yayi gaba, kullum burin kowa yafaranta ran Dan uwansa. Surbajo takara gogewa, yanzu tayi kiba, ga wani haske datayi, bame cewa tahaihu har so biyu.
.
wani zuwa kaduna da Al-ameen yayine yatarar da Aisha kwance afalo ba Lafiya duk tayi amai tabata guri,arude yadauketa yamata wanka yashiryata suka nufi asibiti,
Bayan aune aune daaka matane likita yamusu albishir dacewa Tana da ciki natsawon wata uku,murnar dasukayi fadinta bata lokacine,koda suka dawo gida tattalinta yakeyi kamar kwai, su Aisha abunnema yasamu,se kara narkemasa takeyi,shikuma yana biyemata.sati biyu yazo da niyar yi,amma seda yayi sati hudu,dan kulawa da Aishan, sabida cikin me laulayine sosai,
Koda yafadawa surbajo,murna tayimusu gamida fatan Allah yasauketa Lfy, itace ma tabashi shawarar yakara kwanaki,dan yakula musu da baby da kyau,
Ranar daze tafine, yaje gidansu Aishan yadauko mata kanwarta danta tayata Zama,su Aisha harda kuka,dan taji dadin zaman dayayi da ita,rarrashinta yayi yace takwantar da hankalinta baze dadeba ze dawo,dakyar tasakeshi yatafi.
Tarba ta musamman yasamu agurin surbajo Dan har airport taje tarboshi,tareda bodyguard dinsa.
Suna zuwa gida,taimakamasa tayi, yayi wanka yashirya, suka dawo dinning yaci abinci.kara yimasa Allah yasanya alkhai'ri tayi game da samun cikin Aisha,sannan tace yakiramata ita tamata yajiki.bamusu yaciro wayarshi yakira Aishan bayan sungaisa yace ga surbajo zata gaisheta, da kamar tace a'a sekuma ta tuna yadace taba surbajo amsa,gameda gorin data Mara. Tace to abata sugaisan, kamar abun arziki, surbajo tagaisheta gami da mata fatan Allah yasauketa Lfy, ay kamar jira take,tace, "ameen idan takai zuci, kinki Allah yaso,da kindauka kekadaice me rabon haihuwa?tonima gashi nasamu,kuma Wlh ko kece shugabar matsafa na duniya, sede kiyi kibari wannan cikin yafi karfinki, yargidan masu tallan nono.
Dasauri surbajo tamikawa Al-ameen wayarshi,tana danasanin cewa akirata sugaisa.*.
.
Yanzu Aisha laulayi yayi sauki,bakamar da ba,iskanci kuma da takama da cikin se abunda yayi gaba,musamman datayi scanning,akace mata namiji zata haifa, karkuso kuga rawar kafa, kawayenta kullum suna gidanta wai sunje jinyarta,abun namata dadi,yadda kawayennata ke bata kulawa,
.
Al-ameen tuni yagama siyayyar kayan baby,haihuwar kawai suke Jira,yanzu duk weekend a kaduna yakeyi sabida cikin Aisha daya tsufa,
Surbajo tamaida hankalinta kan karatunta, Sam bata wasa dashi ko kadan,shiyasa al-ameen kekara sonta,dan har cikin ranshi yana takaicin rashin karatun Aisha,Wanda ita ko ko ajikinta.
Wata safiyace aisha ta tashi da ciwon nakuda, Allah yataimaka lokacin Al-ameen yazo weekend,
Ihu tadunga yimasa kamar zatayi hauka, duk yabi yarude,agigice yayi asibiti da ita,suna zuwa aka shiga da ita dakin labour.
.
waya yaciro yakira mamanta, bajimawa tazo asibitin,shuru har yanzu Aisha bata haihuba,se addu'a sukeyi,zuwacan likitan ta fito dasauri,gurinta suka nufa suna tambayarta ya Aishan take,zufa tashare sannan tace musu bleeding takeyi ,dan haka Tana bukatar jini da gaggawa, inba hakaba anything can be happen,
Tahaihune? suka tambayeta arude, as tabasu amsa kuyi sauri kukawo Jinin ko kuma ku biya akwai nasiyarwa,
bamason nasiyarwa muje adebi nawa am group o±,
Donor ne ni,
Bamusu suka nufi lab dashi, bayan sun aunashi suka tabbatar bawata matsala, sannan suka dibi jinin,akaje akasawa Aisha,
Allah gamu gareka,aishafa nacikin mawuyacin hali, duk me imani yaganta ze tausaya ,likitoci sunyi iya yinsu wajen ganin tahaihu da kanta,amma ina dole se ammata cs.
.
Gurin al-ameen sukazo,wanda yazuba uban tagumi hankalinshi atashe,burinshi Allah yasauketa Lafiya,kiranshi office doctor din tayi,tayimasa bayanin abinda ke faruwa,ba musu yasa hannu a takardar cs din gami da fatan Allah yasa ayi asa'a.
Gurin mamanta yazo yamata bayani,kuka tasa, Tana adduar Allah yafito da Aishan Lfy,
Sunanan zaune akafito da Aishan fuskarta dauke da oxygen a hanci alamun numfashinta be wadataba,zaa kaita dakin operation,mamanta kuka tasa Tana mata addu'a,duk juriya irinta soja,Al-ameen komawa yayi kamar yaro, kuka yake sosai yana mikawa Allah rokonshi,
Ankwashe sama da awa biyu,sannan likitocin suka fito,dasauri,su al-ameen suka nufesu,tamvayarsu Al-ameen yake ya aisha take,daya daga cikin likitocinne yace,she is fine,but am sorry to say,we lost the baby,
Godiya ga Allah Al-ameen yayi, daya tsallakar da Aishan siratsi,yayinda agefe daya kuma yanajin dacin mutuwar babyn,gamida tausayawa Aishan duba da ganin yadda ta dora buri akan dan.
.
doctor ne yakatseshi dacewa yanason ganinsu a office akwai magana,dasauri suka bi bayanshi zuwa office din,hakuri yasoma basu sannan yace Aisha tawahala da yawa wanda hakan baason faruwarsa ga me nakuda, kuma hakan yafarune sakamakon shan kwayoyin hana daukar ciki datayi amfani dasu acan baya, sanadin hakanne yajawo mahaifarta tasamu matsala inde bawani ikon Allah ba ze wuya tasake haihuwa arayuwarta,
Al-ameen gaba daya rikicewa yayi ,dajin zancan likitan,haka mamantama,hakuri doctor din yadunga basu daga karshe yabasu takardar data tabbatar da bincikennasu,
Bayan Sun baro office din doctor, dakin daaka kwantar da Aishan bayan anfito da ita daga operation din suka shiga,tana kwance Tana bacci, har yanzu akwai oxygen din a hancinta,tausayintane yakamasu duka,
suna nan zaune aka kawo musu gawar babyn Rufe cikin shawul kamar me rai, Al-ameen ne yaamsheshi yabudeshi,wasu hawayen ne suka zubomasa, ganin babyn ba inda yabaro Yusuf, maana shima dashi yake kama,mamanta yaba itama tagani tamasa addu'a,wayarsa yaciro yadunga daukar babyn hoto,sannan yaamsheshi yatafi gida domin amasa sutura,
gidan iyayensa yakai gawar suma suntausayawa Aishan gamida yimata fatan samun sauki, shikuma Allah yajikansa, bayan sun shirya yaron suka masa sallah,makabarta suka nufa domin birneshi,itakuma Momy ita Da amal,da matar kabeer asibitin suka nufa,domin dubo Aishan.
.*
Su mommy sun iso asibitin Lfy, sede suma suna ganin Aisha sunyi matukar tausayamata,har kuka sukayi sabida tausayinta.
Surbajo Al-ameen ne yakirata yasanar daita abinda yafaru,Allah sarki baiwar Allah kuka tadunga yi kamar ita abun Yasama, rokonshi tashiga yi akan zatasa driver yakawota tadubata,kin amincewa yayi yace tabari zezo sutaho tare,haka dole tahakura Dan tasanshi kaifi dayane,
.
Kwanan Aisha daya a asibitin tafarka, abinda tahaifa tafara tambaya, duk cikinsu anrasa mebata ansa se al-ameen,shima daurewa yayi yamata bayanin,kuka tasamusu tana fadin "Wlh bazan yardaba wato takashemin shi hankalinta yakwanta,inna yarda Allah yatsinemin dole seta biyani yarona. Hakade taita zage zage dasauri suka Kira likita yasake yimata allurar bacci.
Al-ameen ko ranshi yabaci dajin zantukannata,wato ita har yanzu bazatayi hklb kenan.
satinta daya aka sallameta,koda tadawo gida kullum zancanta surbajo takashe mata da ita bazata yardaba,kawayenta se Kara zugata sukeyi akan lalle surbajo ce takashemata yaro.
Kwanan Aisha goma da haihuwa al-ameen yakawo surbajo ta dubata,
Tana ganin surbajo wani ihu tayi tayo kanta,dasauri al-ameen yariketa, kokarin kwacewa take amma takasa sabida jikinta ba kwari masifa ce kawai irinta Aisha,
magana yafara dacewa,
"aisha yakamata ace yanzu kingirma Don Allah yaushe zaki Dena batamin raine?sama da shekara goma kullum da bacin ranki nake kwana menayimiki haka Aisha kike burin kasheni? why Aisha?dama Ashe bada gaske kike sonaba kin aurenine domin kikasheni da bakinciki? Ina son dakike ikrarin kinayimin? Seyaushene zanfara jin dadin zama dake iye Aisha ninefa Aminu amma nikikewa tozarci irin haka ngd,
yana gama fadamata haka yasaketa yabarsu agurin yawuce dakinshi, jikin Aisha gaba daya yagama mutuwa dajin kalaman al-ameen,kuka tarushe dashi agurin tarasa meyadace Tayi, Tunda suke da al-ameen yaune yamata kalaman dasuka dagula mata lissafi Amman batajin zata yafewa surbajo abinda tamata,surbajoce ta katsemata tunani dacewa, "aunty Don Allah kiyi hkr inna batamikine Allah yahuci zuciyarki, Allah kuma yabaki Lfy yajikan babyn yasa masu cetonmune, ko kulata
Aisha batayiba bare tayi tunanin zata amsa,surbajo mikewa tayi tafice daga dakin.
.
dakinsa tanufa tasameshi yana zuba kaya a wadrop,tayashi tayi suka gama zuba kayan, Lura datayi ranshi abace yake yasa tashiga kwantar mishi da hankali harseda yasamu natsuwa, daganan aka fada rayuwa medadi.
Da daddare daukar surbajo yayi suka tafi gidan iyayensa,
Sunyi murna sosai da ganinta, suma tamusu gaisuwar rashin dasukayi, dazasu wucene mommy tace suwuce da Yusuf Dan tasan sunfisu bukatarshi akusa dasu kawaici kawai suke musu, wayyo dadi,surbajo jitayi kamar ta goya mommy, godiya sukamusu sosai daganan suka musu sallama, Dan gobe surbajo zata koma Abuja sabida Tana da exam,
daga gidansu gidan Yan uwan Maman surbajo sukaje,
Sunyi murna daganinta sosai, sunjima agidan sannan sukayo gida .
washe gari da safe al-ameen yahadasu da driver yamaidasu Abuja,sabida shi ba yanzu ze tahoba se jikin aisha yakara sauki,duk da mamantace ke zaune da ita, se aminan ta dakullum suke gidan.
sannu ahankali Aisha kesamun sauki harta warke gaba daya,lokacin tuni al-ameen yakoma Abuja gurin aykinshi.komawarshi bajimawa akasa Yusuf amakaranta, sabida Yusuf inyafado wata maganar zaka dauka bashine yayitaba.
*jama'a albishirinku*
aminan aisha de lokaci yayi inda kowaccensu tasamu mijin aure, kuma duka mazajen a kaduna suke sede anguwace kowa datashi.
Se anriga yin bikin zuly da sati biyu zaayi na Ruky,wayyo rawarkai, ay Aisha ce tadauki nauyin yimusu setin kujeru dukansu, abun yamusu dadi sosai.yayinda azuciyarsu ko mugun fata suke mata.
Anfara hidimar biki su aisha bazama sune can sune nan,
ranar asabar aka daura auran zuly da mijinta Musa,sosai akayi bidiri abikin inda aka Kai Amarya gidanta dake makarfi road can hayin rigasa, layin tattali blocks, semuce Allah yabada zaman Lfy.
haka lokacin bikin Ruky ma yazo aka sha biki inda ta auri wani mesuna baballe itama ankaita gidan mijinta dake unguwar dosa layin commissiona road.
.
Al-ameen ne zaune, yayinda surbajo Tay matashin kai da cinyarsa, Suna hira.
Al-ameen ne Yace,
"madam yaushe zaki bani new baby ne?yafadi yana shafo cikinta,dariya tayi medaukar hankali,hannu tasa Tana wasa da dimples dinshi,sannan tace,
"lalle ma my dear nan,nafahimceka sokake inyi saurin tsufa, inbanda abinka ay yanzu hutawa yadace inyi Dan haihuwa barkatai seyajawo natashi ayki dawuri,cuno baki tayi sannan tacigaba,dan haka ni kadena wannan maganar yanzu kabari sena gama karatu.
Al-ameen mamakine yacikashi naganin zallar kuruciyar surbajo, wacce yafahimci dole seya setamata hankali,magana yafara da cewa,
"baby yakike magana kamar bakida ilimi,menene aybu inkin haihu yanzu,karki sawa kanki akida tawasu mutane marasa tunani,tonide soyayyar dazaki nunamin itace kihaifamin yara,taya yaro daya kawai kice kinaso ki huta,hutun jaki da kaya ko?.itade Tunda yasoma mgn kallonshi take Tana murmushi, Dan dama tafadine taji mezece.
Kallonta yayi yaga Tana dariya,dakatar da maganar yayi yana dubanta,rungumoshi tayi Tana dariya tace,my Legend kenan maida wukar surbajo tsokanarka takeyi,haifa maka yara inde Allah yabamu yanzu nafara so no need to be worry, rumgumeta shima yanada dariya yace,
"lalle baby wato kinmaidani kakanki ko,seki fadi maganar dakikasan dole Sena tada jijiyar wuya ko?to daga yanzu naganoki bazan Kara bata bakina gurin maganaba wannanne hukuncinki, yana fadin haka yasureta yay cikin daki daita suna dariya.
Muleka gidan amaranmu.
Zuly da angonta Musa, soyayyace akashata bata wasaba har ta tsawon wata guda.bayaga haka,
.
Yau tun safe Musa yafita yabar gida shuru bedawoba har karfe goma nadare,hankalin zuly inyayi dubu yatashi,gashi wayarshi takira Tana ringing Amman baa dagaba, Tana nan zaune afalo taji alamun bude get lekawa tayi ta window ganin motarshi ke shigowane yasa hankalinta yakwanta dasauri taje ta bude kofar, sannan tajuya dakinta takara gyara makeup dinta tafesa turare,sannan tadawo falon, sede me? Tana zuwa falon Musa tagani dawata yarinya maana karuwa tarukoshi yana tangadi ga kwalbar gulder ahannunshi yana korawa,
Salati tayi Tana fadin,
"nashiga uku Musa mezan gani acikin gidana,giya da karuwa , innalillahi wainna ilaihirrajuun, Wlh baze yiwuba,
kan budurwar tayi tana fadin,
"wlh yau se zina tazamemiki karshen aykinki aduniya matsiyaciya tsinanniya,
Musane yakatseta dacewa cikin muryarsa ta me Maye,
"narantse da girman Allah kika kuskura kika tabamin blessing Wlh Sena fafemiki ciki, kuka tasa tace,
" musa yanzu akan karuwa zaka hallakani?
amsa yabata dacewa,"eh karuwar kuma Wlh tafiki daraja a idona, ke!bakebama uwarki wannan tafita mutunci a idona, Dan haka ki kula,yana gama fadin haka yaja hannun blessing suka shige dakinsa suka kullo kofa.
Kai ta dafe tafada kan kujera Tana kuka iya karfinta.
Tuge dankwalinta tayi Tana Ta share hawayenta dashi.
ranar zuly bata runtsaba Tana zaune afalo, Tana jiyo sautin bidirin da akeyi akan gadonta na Sunnah .
Washe gari da safe haka musa yasata agaba dole ta dafamusu ruwan wanka, kuma yace ta tabbatar ta hada musu breakfast kamin su fito,bata da zabin daya wuce tayi abinda yasata,dan bakaramin so takewa musaba Tana tsaron yasaketa takoma gidansu da zama, dama gashi ta juma batayi auranba.
haka rayuwar zuly taci gaba da tafiya agidan Musa,zuwa yanzu bakoyaushe yake kwana agidaba,wanda hakan ita yafimata dadi Dan in agida ze kwana toko da 'yan tayan kwana yake zuwa biyu ko uku Dan yanzu likkafa taci gaba yafi karfin mace daya sede biyu zuwa uku, kuma ingari yawaye duk kayansu itace me wankewa inba hakaba taci duka,koda wasa bata taba ba kawayenta labariba bare takai kararsa gidansu.
yau da wuri Aisha tashirya, sabida tanason zuwa gidan zuly tawuni,sabida Tunda akayi auran so biyu taje shima lokacin ko wata batayiba.
.
karfe takwas na safiya a gidan zuly tamata,wanda zulyn seda ta firgita da ganinta,afalo tasauketa,Aisha ko mamakin abinda yaramar da zuly tayi baki takeyi,kasa daurewa tayi seda ta tambayeta tace,
"kawas meke faruwane dake haka kika Yi baki kuma kika rame, kamin tabata amsane suka jiyo karar bude kofar dakin zulyn. Musane yafito shida 'yanmatansa guda biyu,kowacce ta rungumeshi gashi kayan jikinsu kadai yaisa yasanar dasuwaye su ,
Arude Aisha take kallonshi, takalleshi ta Kalli zuly wacce tasunkuyar dakai Tana kuka,
Kasa cewa komai tayi se ido, Musa ko bakunya ya Kalli Aisha yace "madam ykk? ya gida kwana dayawa kinyi wuyar gani ,mamaki ne da tsoro suka hana Aisha bashi amsa, ko ajikinshi Illa ajiye panties and bras na yanmatanshi Wanda suka cire agaban zuly yace "gasunan washing and drying and then ironing kamin mudawo .bejira amsartaba suka fice shida 'yanmatanshi.
Azabire Aisha takai dubanta gurin zuly, tace,
"today I saw the thing that I have never think it will be happen to you ever in your life,please zuly wake me up kice mafarki nakeyi please, tafadi Tana girgiza zulyn wacce inbanda kuka baabinda takeyi.
Dakyar Aisha tashawo kanta tabata labarin abinda ke faruwa, zugata Aisha tashigayi kamarde yadda sukemata, ga mamakinta seji tayi zuly ta dakatar da ita dacewa, "Aisha waimeyasa kika dauka kowama banzane irinki,tobari kiji infadamiki kinga halinde danake cikiko,to wlh har gobe inason mijina kuma babu wani dalili dazesa inbarshi, zugarki gareni ki adanata kibari inkin samu wata shasha irinki seki bata tadauka Amman bani zuly ba, uhm Bari kiga inje inyi aykin lada tamike gamida kwasar kayan da Musa yaajiyemata na'yanmatanshi ta tafi wankewa.
kwakwalwar Aisha seda tadena ayki na 'yanmintina, zuciyartace take harbawa da karfi yayin da wasu hawayen bakin ciki suka fara biyo fuskarta,bata da sauran magana Jakarta tadauka tabar gidan zuciyarta na mata kuna.
0 comments:
Post a Comment