Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Thursday, August 24, 2017

SURBAJO Part 14 (THE END)

 August 24, 2017     SURBAJO 1-END     No comments   

SURBAJO Part 14 (THE END)
.

Allahu gafurur raheem watansu biyu da dawowa Allah yaba Aisha ciki zokuga Surbajo har azumi tayi na nuna godiyarta ga Allah daya amshi addua'rsu,Al-ameen yayi murna sosai itako Aisha harda kukanta gurin nuna godiyarta ga Allah.

kulawar da Surbajo take bata abin gwanin Sha'awa dole su burgeka duk abinda Aisha takeson ci shizata bata ko menene, dayake cikin Aishan me kwad'ayine abubuwa da dama se anbar kaduna za'a samo mata shi in kwad'ayin abunda ba lokacinshi bane a kadunar ya motsa mata.ko kad'an basa gajiyawa da hidimarta wanda ita godiya kawai take musu da fatan alkhairi.
.
Cikin Aisha se girma yake wanda girman cikin har tsoro yake ba su Surbajo sabida girmane na sose,gashi lafiyarta k'alau ba
ciwon komai se na kwad'ayi gashi yanzu tazama rumbu cin abinci kamar hauka intaci kuma takasa tashi  sesun d'agata.

Watan cikin bakwai suka kwasheta zuwa scanning dan su girman cikin ya tsoratasu,koda sukaje cemusu akayi komai normal kawai de twins ne a cikin.

Wayyo dad'i  Surbajo sujjada take yi tana k'arawa ga ubangiji shiko Al-ameen duk girman Aisha da cikinta be hanashi d'agata ba yana murna.

Daga gurin scanning kasuwa suka wuce suka barta a mota suka shiga wani boutique na babycare suka shiga jidar kaya kamar hauka,daganan gida suka nufa.
Har walima seda sukayi dan murna inda akai addu'ar Allah ya sauketa lfy.

Watan haihuwarta yatsaya kullum cikin addu'a suke Allah ya raba Lfy, wata jumma'a Aisha ta tashi da ciwon nak'uda da sauri suka d'auketa zuwa asibiti.
.
Da isarsu labour room akasata, Surbajo kamar zatayi hauka dan tausayin Aisha, addu'a kawai sukeyi dan shima oga hankalinshi atashe yake.

Suna nan tsaye wata nurse tafito tamusu albishir data haihu Lfy ansamu twins duka mata,rungume juna sukayi Surbajo da Al-ameen suna nuna farincikinsu ga Allah.

Bajimawa aka fito da me jego da twins d'inta kyawawa dasu aka kaisu d'akin hutu.Surbajo tunda ta d'auki yaran kasa ajiyesu tayi sabida kyan da Allah yay musu kuma abin mamakin yaran da Surbajo suke kama kowa seda yayi mamakin hakan.
.
Aisha kallon Surbajo tayi murya araunane tace,

"Sister nagode da addu'ar ki gareni,wlh base kin ce kina k'aunataba inda banyarda ke me sona bace yanzu dole nayarda duba da kammanin da yarannan sukeyi dake, nayi imani inba nagartacciyar soyayya hakan bazata yiwuba,nagode miki sister da addu'ar ki gareni Allah ya rabaki da bak'incikin duniya da Lahira,"tafashe da kuka da sauri Surbajo tamik'awa Al-ameen yaran tarungume Aisha tace,
.
"Haba Aunty yau ranar murnace agaremu ba kukaba Allah ya amshi addu'ar damuka dad'e munayi danhaka godiya kawai zamuyi masa, kimance da komai Aunty na ni mesonkice."

Koda aka Sallamosu Surbajo ce d'auke da yaran tun kan su k'araso gida gidan yacika da y'an uwa kowa murnar haihuwar su twins yake.

Al-ameen yanajin son yaran har zuciyarshi badan komaiba sedan Kama da Surbajo dasukeyi bame kallonsu yace ba ita ta haifesuba, Allah Kenan.

Ranar Suna Surbajo ba k'aramin mamaki tayiba,
   dataji yaran duka sunanta Aisha tace asa musu d'aya Zahra d'aya fatima suna kiransu da mamah da mimah, amman Al-ameen me suna zahran Surbajo yake ce mata yayinda ita kuma yaci gaba da kiranta Babynsa.Surbajo godiya tadunga yiwa Al-ameen da Aisha abisa karar dasuka yimata.

.
Rayuwa taci gaba da tafiya inda Ahalin yanzu Surbajo tagama university d'inta Amman Al-ameen yace bazatayi aykiba,bata musaba ta hak'ura,Aisha nakan nata karatun dan itama tuni takoma makaranta,Yaransu gwanin Sha'awa bame gane wannance Mamana acikinsu sabida duk kulawa d'aya suke basu.

Al-ameen hankalinshi akwance na iyalanshi ma haka so da k'aunar dake tsakaninshi da Surbajo se son barka duk da yana b'oyewa gudun kar ran Aisha ya b'aci,amman son da yakewa Surbajo gagara misaline.

ina labarin su Ruky?
.
Ruky tunda suka bar gidan Aisha da wata uku tafara jin canje canje ajikinta dan haka ta nufi asibiti gwajin farko aka bata sakamakon HIV,yanke jiki tayi tafad'i sumammiya Gado aka bata a asibitin.Zuly nasamun labari tazo asibitin tagaida Ruky kamar abin arzik'i daga k'arshe se cewa tayi.

" Wannan k'awance  namu ina sonshi tunda gashi nayi nasarar saka miki ciwon danake d'auke dashi."daganan takwashe labarin komai tafad'a musu tana dariya, Maman Ruky shak'e Zuly tayi kamar zata kasheta tana yimata Allah ya isa,likitoci sunkasa kwaceta a hannunta dan haka suka kira police sukayi gaba da Zulyn.

Ruky ko kuka take me tsanani tashiga barin wasiyya tace ma mamarta tanemarmata yafiyar Aisha tasan hakkintane yake bibiyarsu don Allah tayafemata,ranar Ruky bata sake kwanan duniyaba tace ga garinku bayan tayi kalmar shahada.Allahu akbar Allah nason masu tuba Allah kasadamu da rahamarka dan darajar Annabi da alqur'ani Ameen.

Zuly ko kotu aka shigar da ita k'ara inda aka yanke mata d'aurin rai da rai agidan kaso,gamida horo me tsanani har iya k'arshen rayuwarta. Duniya kenan shiyasa akace abinda kashuka shi zaka girba Allah yasa mudace Ameen.

.
Su Aisha dasuka sami labarin mutuwar Ruky har gida sukaje gaisuwa ananne mamar Ruky take sanar da Aishan sak'on Rukyn,kuka Aisha tasa tace,

"Wlh nayafe mata duniya da lahira Allah yajik'anta yakyauta namu zuwan,"
godiya yan uwan Ruky sukai tayiwa Aishan.

To Ruky Allah yajik'anki yasa kin huta ya yafemiki kurakuranki.

Surbajo uwar biyu yanzu haka wani cikinne ajikin Surbajo tsoho yafi na Aisha girma scanning na farko aka shaida musu yan biyu ne duka mace da namiji,fad'in murna da farincikin da Al-ameen da Aisha sukayi page din yayi kad'an se fatan Allah ya sauketa Lfy.

Tahaihu  Lfy inda yaran suka ci sunan iyayen Al-ameen. So da k'auna agurin Al-ameen da Surbajo abin fatane ga kowacce mace agidan mijinta.

.
*Godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya bani ikon kammala wannan littafi nawa me suna Surbajo.ya Allah kuskuran danayi kagafartamin wa'azin dake ciki gamu mata masu zafafa k'iyayyar kishiya Allah yasa mata sund'auki darasin, maza mata masoyana ako ina kuke afad'in duniya me surbajo na k'aunarku harcikin ranta Allah yabarmu damasu son mu ameen wandama baya sonmu Allah ka jarabceshi da sonmu,Allah yazaunar damu cikin aminci.*

NGD

Jinjina ga mawallafiyan wannan littafin wato zahara muhammad (Maman Yusuf)
.
Naku akoda yaushe Abdullahi Yahaya Sa'ad zaria (AYS)
.
CALL or SMS
07066508080
.
Whatsapp
07066656752

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MIWASMITI Page 31 to 40
    Kuka ta Kuma saki gamida kamo hannushi ta matse a tsakiyar qirjinta Dan jin wani irin suka da yake mata Ga jiri da takeji gaba daya bata gan...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam