Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Saturday, August 19, 2017

SURBAJO Part 2

 August 19, 2017     SURBAJO 1-END     No comments   

SURBAJO Part 02
.
Basu tambayeshi meyasa baze tafi da Aishan ba sabida zuwa yanzu sungama fahimtar dannasu beyi dacen mataba

Tunda yatafi kullum seya kirata awaya intayi raayi tadauka inbatayiba kuwa inze kira so dari bazata dagaba
Haka inyasamu Hutu yazo gida sotari hutun baya karewa yake komawa sabida balain aisha
Rayuwa tayiwa alameen zafi awaje mutane yisuke kamar su goyashi sabida kulawa amma cikin gidanshi masaima yafishi daraja wannan wacce irin rayuwace  gashide yanada mata amma bata da amfani agareshi Allah kakawomin agaji.

*cigaban labari*
.
Haka Aisha taci gaba da musgunawa alameen kullum Sabida shimutumne me hkr kuma dama duk soja seka sameshi da sanyi akan mace

Zuwa yanzu hakurin shi yasoma karewa dama dagamata kafa yake tunda yakoma ayki besake dawowaba seda yakwashe shekara guda sannan yadawo
Yauma bata gidan kuma tasan zedawo tatafi yawonta tunda yake daita betaba jin bacin rai irinnayauba kuma yasha alwashin yau seyayi maganinta

Yanazaune afalo tadawo kokallo be ishetaba tawuce dakinta. Seda tajima dashiga dakin sannan yamike yabi bayanta yanashiga kamar kullum yauma wayar take da kawayenta
Daga gidan ubanwa kike alameen yawurgamata tambayar
Seda tambayar tafirgitata amma dayake Kai na hayaki setace daga gidan ubanka nake ubana
wani wawan Mari yakifeta Dashi seda tafado daga gadon
Belt din jikinshi yacire yashiga dukanta takoina ran yanmaza yabaci haba ay yayi kokari tsawon shekara biyar yana hakuri
Aisha tun Tana ihu harseda ihunma yagagara seda yatabbatar da tayi laushi dankanshi yakyaleta
Sannan yadakamata tsawa Tana kwance akasa jikinta duk jini sabida tadoku ahannun soja Dan dukan kato yamata
yaci gaba dacewa cikin fushi anfadamiki tsoron ki nakeji ne dazaki dunga yimin abinda kika dama ina kyaleki wallahi Aisha nayi danasanin auranki danasani nabarki kinsake shan fiya fiyar ki mutu wlh daan rage mugun irin
Damutuncina agari amma agidana bandashi to wlh kinyi kadan dama nasamiki idone banza kazamiya kuma wlh kitashi yanzu ki gyaramin gida awa guda nabaki inba hakaba nalahira seyafiki jin dadi yafadi yayin dayayi kwallo da ita yafice daga dakin

Jikinta narawa tamike tafara aykin dukda ciwon dake jikinta besa tabar aykinba tanayi jiri nadibarta Dan yanzu wani mugun tsoronshi takeyi hhhhhh nace su aee anji maza

kafin lokacin yacika tuni gidan yayi clear dattinko data kwashe seda yacika katon dustbin
gidan se kamshi yakeyi komai yayi normal araina nace oh Aisha tazama zuma seda wuta
.
alameen tunda yafito daga dakinta garden din gidan yashiga seda yatabbatar lokacin daya dibamata yacika sannan yashiga cikin gidan mamakine yakamashi ganin yadda gidan lokaci kadan yasauya sewani kamshi yakeyi dakinshi yaleka komai normal harda sabon bedsheet tashimfidamasa har cikin ranshi yaji dadin ganin gidan ahaka sabida rabonshi daganin sa hakan tunranar daaka kawota gidan

dakinta yanufa yana shiga yaga Tana morping a tsugunne tana kuka tausayintane yakamashi  amma yayi saurin kawar dashi sabida sanadin tausayinne yajefa kanshi acikin halin dayake yanzu
Tsawa yadakamata sannan yace Dan rashin mutunci a tsugunne kike moping din dalla malama tashi
Jikinta se Bari yake tace Dan Allah Yaya kayi hkr bazan sakeba
Mamakine yakama alameen sabida rabonshi dajin irin wannan kalaman abakinta tun sati biyu da auransu
.
dalla yimin shuru sumumu kasau kawai bacemin dagani Jikunta narawa tadauki ruwan moping din taje toilet tazubar tawanke toilet din fitowa tayi tana rabe rabe inda alameen yakorata taje tayi wanka da gudu tashige bayin Dan tadauka yabiyota abayane
so uku Tana fitowa bayan tayi wankan yana maida ita tasake wani wai bata fitaba hakama brush seda makilin oral b yakusa karewa dan seda bakinta yasoma jini sabida brush sannan yakyaleta kantama adaren tatsefeshi tawanke shi tas haka ma shaving duka seda tayi
ita dakanta taji dadin kanta Dan har wata iskace take ratsata nace oh ji yiwa Kai mugunta

rigar vacci kawai tazira tahaye gado tuni bacci yayi gaba da ita dayake alameen yabar dakin
dawowa yayi yaga Tana bacci duka yakaimata abaya afirgice tafarka tadiro agadon
ubanwa yabaki damar bacci bayan baki sallameniba hkr tashiga bashi Tana hawaye alameen bakunya yakamota yashiga sarrafata bata hanashiba Dan Tana gudun shan duka
yau cikin nishadi yabiya bukatarsa inda besauraramataba se asuba nace Kai alameen batausayi

wanka yayi yafice masallaci Tana kuka tamike tashiga toilet tayi wankan tazo tayi sallah sabida kafin yatafi masallaci seda yamata worning akan ta tabvatar kamin yadawo tahada break fast sannan tayi gyaran gida tayi wanka tayi kwalliya idan yadawo yaga batayi daya acikiba zatasani
shiyasa tamike tafarayi jiri nadaukarta  sabida rashin bacci ga jikinta dake mata ciwo ahaka tadaure tayi komai kamar yadda yabukata har girkinma tayi duk da ba wani dadi yayiba amma yafi babu
dayadawo abun yaburgeshi har wani nishadi yakeji amma idan yatuno tilastata yayi seyaji duk ranshi yabaci

.

Tundaga wannan rana Aisha take tsoron Alameen Dan ko fita bata sakeyiba sosai take jin maganarshi
Bangaren rayuwar aurema ko tanaso ko bataso inde shi yanaso anwuce gurin

.
Yau alameen ze koma bakin ayki inda yakafamata dokoki yakuma ce muddun ta karya daya takuka da kanta

Har airport Tamushi rakiya kamar gaske
Ay tundaga airport dinnan bata wuce gidaba kaitsaye gidansu Ruky tasauka kamar fadi Tana zama Sega zuly tazo nan suka shiga hirar yaushe gamo daga karshe Aisha tabasu labarin abinda alameen yamata
Dariya suka samata harda hawaye
Zuly tace dankari amma wlh Aisha kinbada mata yanzu tsayawa kikayi yadakeki tabdi ayko inde baki dauki matakiba wlh kinzama filin training dinshi

Ruky taamsa ay yana cewa zedokeki gabansa zaki rike iya karfinki inyaji zemutu wlh zedena ko ki dunga ajiye wuka agefenki dazaran yamiki wani wargi kinuna zaki masa kachiya wlh denawa zeyi amma taya zaki sakarmasa jiki yadunga labta wlh kin rikito

nande sukasata agaba suna huremata kunne basu bartaba seda suka tabbatar shawararsu taamsu agurinta Dan har haushin kanta tadunga ji amma bata baciba tasha alwashin inyadawo zegane kurensa.

.
      *Photacot*
.
Alameen ne zaune a office dinshi shida amininshi Usman fira suke gameda rayuwar duniya ananne alameen yashaida mishi labarinshi da Aisha harda dukan dayamata
.
Major Usman ne yace haba abokina meyakaika dukanta gaskiya baka kyautaba aysu mata insuna iskanci irin wannan akwai dukan daake musu yasasu haukacema gaba daya
dasauri alameen yamatso yace Kai haba abokina
wlh yabashi amsa

to wanne irine shi dukan alameen yabukata

ka kara aure shine mafita

ajiyar zuciya yayi sannan yace major kafi kowa sanin raayin mace daya ne Dani arayuwata so gashi nakuma Aura bandaceba baka tunanin yin wani auran ze Kara daga hankalinane

haba abokina wancan auran dakayi aurene bana soyayyaba maana aurene natausayi so yanzu inzaka sake wani wacce kakeso takesonka zaka Aura wlh inde kadace sekayimin godiyar shawarar Dana baka amma taya zaka tsaya mace tana gasaka bakadauki matakiba aywasu matan zumane seda wuta
dariya sukayi gabadaya suka tafa inda daga karshe alameen yace zeyi nazari akan zancan Usman

haka kwanaki sukai ta tafiya har Allah yadawo da alameen gida koda yazo yaga Aisha tayi fatali da dokokinshi be kulataba
anata bangaren tayi shirin ko ta kwana Amman ga mamakinta setaga ko kallo bata isheshiba
hakan bemata dadiba taso yakulata tace zata masa kaciya  shiko bawan Allah bata ita yakeyiba
.
shurun dayamatane yasa tasake Mike kafa ita adole taci dubu se Ceto kawayenta nakara zugata

     *RUGAR YALLI*

.
wata rugace ta fulani agarin makarfi ta jahar kaduna  jamaa dayawa basu San rugarba sabida Tana cikin dajine sosai ko yan garin se tsofaffin zamane sukasan da rugar sabida rugar gida ukune kawai acikinta gidan alhaji babba dagidan alhaji jume se gidan ardon rugar wato gidan alhaji yalli

duka gidajen Manyan gidajene sabida kowa dashi da zuriarshi yake zaune agurin
.
zahrau wacce akafi saninta da surbajo "ya ce agurin alhaji yalli wato ardon garin  Wanda aynihin sunanshi muhammadu Mahmuda asalinsu yangarin gwangolane dayake su fulanin tashine shine suka dawo wannan guri dazama
matanshi biyu sumaye wacce itace uwargida se amina wacce itace Amarya
yaranshi takwas inda sumaye takeda guda bakwai duka Mazda ita Kumar amina takeda guda daya wato zahrau
amina asalinta yar garin kadunace awata anguwa mesuna tudun wada layin kosai anan aka haifeta kaddarar aurece takaita ga auren ardo dakuma rabo danginta Sam basason aurannata dashi kasancewarta marainiya shiyasa tunda taaureshi danginta suka tsameta acikinsu

bayan haihuwar zahraune da shekara  biyar Allah yama amina rasuwa  ardo yayi kuka  kamr ranshi zefita
yanuwantama dasuka sami labarin rasuwarta sunyi kukan rashinta dasuka zo gaisuwa suka bukaci ardo yabasu zahrau sutafi da ita fafur ardo yahanasu yace meze dunga kallo  amatsayin amina idan yabasu ita
ransu besoba amma yafisu iko da ita haka suka tafi suna danasanin watsi da aminan dasukayi

.

Zahrau ta taso cikin tsana da tsangwama  irinna kishiyar Uwa

Sumaye ganamata azaba takeyi tun tana karama aka fara sata zuwa kiwo zuwa yanzu taiya sosai dama ga aladar gidan insun fita kiwo dare yamusu to acan suke kwana ingari yawaye su cigaba da kiwon sede laasar nayi zasu komo gida
.
Shiyasa inzasu tafi suke tafiya da kanzo Wanda aka daka da gishiri da yaji da man shanu da tukunya sabida koda dare yamusu acan sugirka suci

Kokadan zahrau batajin dadin zaman gidan inde mahaifinta bayanan sabida inyananan bame dukanta sosai yake jida ita kuma gata sunan mahaifiyarshi yasamata shiyasa ake kiranta da surbajo

Yauma kamar kullum surbajo tafita kiwo ita da ya'u yayantane
Suna zuwa rafi suka hadu da arera yar gidan alhaji jume itama tafito kiwon itada yaynta saidu

Suna ganin juna suka rungume juna ita da areran sabida murnar ganin juna guri suka samu suka zauna suna hira

surbajo ayko inada wani albishir dazan miki inji arera

dagaske wanne irin albishir ne wannan kekuwa arera inji surbajo

Aradu dama jae ne dan gidan alhaji Babba jiya yazo gurin yayana zubairu danaganshi muka gaisa shine yace wai ince miki yana gaisheki

ihu surbajo tasa sannan tarungume arera tace

kai madallah aradun Allah naji dadin wannan albishir

Aydama nasan zakiji dadin shiyasa nafadamiki

Ranar agurin kiwo wuni surbajo tayi tanajin dadi Dan harga Allah sakon gaisuwar da jae ya ayko mata ta sanyaya zuciyarta

          *JA'E*
.
dane agurin alhaji babbah Dan kimanin shekara ashirin
kyakkyawane naajin farko dan duk mazan garin bawanda yakaishi kyau shiyasa kowacce mace take kaunarsa gashida da kyauta dan inde yace yanasonki to ko zakici soyayyar gyada da burodi kimore gashi ranar kasuwa kullin kosanki da yar yau na musammanne
Shiyasa kowacce mace burinta yace yana sonta
to surbajo ma Tana cikin jerin masu sonnasa

yau akwai biki agidan alhaji babba inda yake aurar da yarsa Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya
Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu sha dayanne

ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar
Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta yalo da kafarta yin hakan nanufin  tanason yafito suyi rawa kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take shiga tsakani hartakai ga aure

.
to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan
Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada tabbacin jae ze zo gurin
haka yanmata sukai tazuwa suna hawa layi sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri kuyi mgn

fili yacika bamazanba ba yanmatanba
su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau

anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se kyakkyawa

bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan yaloshin datayi

hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka gama

itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata dantasan yau tafi kowa saa a duniya

koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya

shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata sannan yafara mgn

wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do Allah do annabijjo kishe kina shona.nide  aradu ina shonki

kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare takoma gurin arera

gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa
.

Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo da jae ko kadan basa son rabuwa da juna

Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo

Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya sabida kunya
Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar
Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata

Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu dukan tsiya
.
dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki

Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito

hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi yawa

****************************

Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa

alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan

Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai
Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan  take tsulawa agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena

Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata da wadataccen hankali

     ***************

surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda nononba
.
Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin ta iso rugarsu goma tayi
haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka

wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin wainda suke zuwa tallan tare

duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take Rufe bakinshi

insuka koma daki ita da surbajo tashaketa takuma ce wlh inkika kuskura kika dawo gidannan baki siyarba yankaki zanyi
itade sede tayi kuka tafadawa Allah

jae yasha yimata juyen nonon yabiya kudin Dan kawai tasamu taje gida dawuri to yau da gobe tafi wasa
ba koyaushene yake da kudin juyenba seyafara rakata tallan sui ta yawo agari har su samu asiye haka sukeyi sunfi karfin wata guda suna zuwa tallan tare kwatsam rannan se sukayi kwantai basu sayar da wuriba ranar basu dawo gidaba se goman dare
lokacin Baffa yafito yabi hanya yagani meyasa bata dawo da wuriba dayake basu San jae narakata tallanba seganinsu yayi tare suna tahowa tsawa yadaka musu yace daga ina kuke cikin darennan
tsugunnawa sukayi sannan sukace daga talla wankesu yayi da Mari duka lokaci daya sannan yace nizaku maidar yaro wato dama abinda innarki take fadamin akan maza kikebi Ashe da gaskene to wlh yau zaki gane kurenki kaikuma zanga baffan nakane wawa kawai kekuma munafuka shige mutafi dagudu tamike tayi gaba Tana kuka koda isarsu gidan yaba sumaye labarin abinda yafaru cewa tayi ay gwanda dakagani da idonka Dan Dana fada baka yardaba aygashinan

ranar seda yama surbajo jinajina inda yakara da fadin  gobema ki kuma kaiwa dare awaje wlh Sena yankaki na huta kuma tallan nono bazaa Dena doramiki ba sabida aladarmuce kowacce yarinya tanayi Danhaka yazama dole kema kiyi daga yanzu in magaruba tamiki awaje ki kuka dakanki

haka taci gaba da Kukanta har zuwa washe gari batayi bacciba

.*

Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano zasu tafi gaisuwa duka family dinsu

Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar acikin ayarin

Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu

Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da karramawa
  Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana zasuyiba

**************

Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon mutane zata dungayi akan su siya

Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin kwalli gaba daya  dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne yasa baa siyan kayanta

sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce

.
Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane akan su siya

haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa

haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta tayi Don Allah  Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan Allah kifadamini

Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau mota naira dari zaa kaiki a  akori kura
Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah  aradun Allah zani
Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata hau motar
.
Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka tafi

**************

Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya tafiyar wahainiya ba

suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska yasamusu suwuce

agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor dasuke ciki
1k alameen yabashi mutumin se godiya yake
karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri tace sannu bawan Allah  Don Allah kataimakeni dasauri alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn
.
arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah  kataimakamin kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka

alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta har rawa yakeyi
mommy ce tafara mgn dacewa  yanmata Lfy cikin harshen fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace
cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa dukana zeyi Don Allah  kutaimakamin
.
tausayintane yakama mommy
bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace
tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga muyadace damu taimakeki
share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan wancam  tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi sabida batamusu lkcn datayi
taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda amaimakon naira talatin shiyasa
dariya sukayi harda sumunauwara

daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar yalli tabashi amsa

jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin wato ardon

ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya
ni yar gidan ardoce
mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace

washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman innata ta rasu
.
no wonder inji mommy shiyasa ake doramata talla inbata siyarba adoketa

shigo mota inji daddy yayinda yace munauwara dake gaban motor tadawo baya surbajo tashiga gaban

arude alameen yawaigo yace haba daddy time is going fa inakuma zamu da ita
gidansu zamu daddy yabashi amsa

dakyar surbajo tayarda tashiga motar Dan gani take guduwa daita zasuyi seda sukasha fama da ita tayarda tashiga

utone alameen yayi sannan yadauki haryar makarfin daddy kemasa kwatance
dan surbajo tunda tashiga tarungume kwaryar nononta sanyin ac yafara dukanta tafara bacci yin baccinnata seda yabasu daddy dariya ita me gudun asaceta gata Tana bacci
harsukazo makarfi surbajo baccinta take sha.

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MACIJINE SHI Page 31 to 40
    _________________Kai tsaye part ɗin nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai ƙamshi ke tashi,dakin fattu suka...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam