SURBAJO Part 03
.
Daddy ne yace alameen yatashi surbajo Dan takarasa kwatancen gidan
Wani uban duka Al Ameena yakaimata acinya
Hande in bonide itace kalmar da surbajo tafadi da karfi asakamakon zafin dukan dataji
Arude tadago Tana kallonshi sannan tace Kai kado menayimka Kake buguna da zafi haka aradun Allah ka kuma senasa jae yabugemin kai
Dariya gaba daya motar akasa banda alameen Dan yaji haushin maganar
Kwatance surbajo taci gaba damusu har suka iso kofar gidan ardo
.
Ardo ganin motane yasashi tasowa yaiso gurin ga mamakinsa seyaga surbajo tafito daga gaban motar
Begama mmkb yaga daddy yafito shima Wanda shi alhajin burni yake cemishi
Dasauri yakarasa gurin daddy yana fadin ikon Allah alhaji kaine agidana yau Kai lale lale
Mommy ce tafito itama Tagaida ardo tace nashori yace jam sago
Iso yamusu zuwa cikin gidan sumaye jiki na Bari tafito Tana lalelale kodo jabbama anan jabbeko
Ruwa takawo musu bayan sungaisa tabasu guri
daddy yace haba ardo yanzu mene amfanin dukiyarka dazaka Bari ana dorawa yarka tallah harda samata dokar inbata siyarba se anyankata daganan yakwashe labarin yarda suka hadu da surbajo yafadawa ardo
.
mamakine yakama ardo jin ashe sumayece kecewa seta siyar zata dawo gida amma munafukar tace ba ita bace tasa yana dukan marainiyar Allah
shima fadawa daddy yayi abinda yasani danshi vashida masaniya akan sumayece take cewa kar tadawo seta siyar
Nande daddy yayta mishi waazi akan yadena bari ana dorawa surbajo tallah kuma yamasa alkawarin bazaa sakeba
da daddy zasu tafi dubu dari yaba ardo sannan yaba surbajo dubu hamsin akan tasiyi kayan sawa ay surbajo dukawa tayi kamar zatayi sujada Dan godiya duk da batasan yawan kudinba ammade tasan masu yawane
sumayema daddy yabata murna kamar tayada zani
Rakosu sukayi bayan ardo yasa daya daga cikin yayanshi me suna sammani yadebowa su daddy kwarya biyu ta Kwai sannan jarka guda ta zuma me kyau
Sumaye ma kwaryar manshanu tabasu duka akasa abooth din motor
Su daddy suka shiga duk abinnan daake alameen betako kafarsa kasaba sabida takaici shi koda excode dinshi bayason tafiyar dare bare yanzu shinema driver ranshi yagama baci ko ardon daga cikin motar yagaisheshi
sungama shiga yayi ribar's yajuya kan motar dagudu surbajo tazagayo setin window dayake tace
kado arage mugun hali aradu bacin baffanka yabani kudi dase na kira jae yabugeka tafadi Tana murguda masa baki afusace yaja motar suka wuce ranshi namishi zafi suko su daddy se dariya suke masa babu kamar munauwara gurin tsokanarshi abu kadan tace kado aradu jae seya bugeka shide be tankamusuba
.se Tara nadare suka iso kaduna agidan yakwana yaki zuwa gidanshi Wanda ita Aishan ko ajikinta Dan itama tafiya gidansu tayi takwana acan
kodasafe dayaje gidan bata dawoba se wajen tara sannan tashigo ko ta tambayeshi ina yakwana kawai hidimar gabanta taci gaba dayi
kuyi hakuri dawannan banida lfy ne
.
Tundaga wannan rana vaa sake dorawa surbajo tallah ba sede taje kiwo
Ardo Dan Yi yayi kamar ze saki sumaye seda yaranta sukai tabashi hkr sannan yahakura
Sosai sumaye tayi nadamar abinda taaykata tai taba ardon hkr kuma tace bazata sakeba
.
Abangaren soyayyar surbajo da jae kuwa se abinda yayi gaba Dan yanzu ma intaje kiwo shima yaje to hirarsu suke sha har cikin zukatansu suke son junansu Dan yanzu jae yace zefadama baffanshi aje nemarmasa auran surbajo Wanda hakan bakaramin farinciki yasa surbajo ba danji take tafi kowacce mace saa aduniya araina nace Anya surbajo harda Aisha kuwa
***************
Alameen bejimaba yakoma bakin aykin Dan zamannashi baida amfani tunda matar gidan batasan darajarshiba Dan ahalayenta kaf babu abinda yasauya
Gidanshi kuwa inda kazanta nasawa gini yafadi datuni nashi yajima da faduwa
.
Aisha ce zaune itada aminanta suna gulmar wata kawarsu anmata kishiya carab Aisha ta amshe zancan dacewa kan ubancan nahango alameen yamin kishiya Wlh dase nakonata kurmus Dan alameen Danni kadai akayishi shiyasa koda wasa betaba attempting Kara aureba Danni kadai naisheshi rayuwa dariya suka samata Dan zancan nata dole Adara su sungama kokarin alameen da har yanzu besaki Aisha ba dansu burinsu yasaketa tadawo gida suzama daya tunda su har yanzu basuda mashinshini amma ita dayake ballagazace bata gane nufinsu akantaba
Haka de taita cika bakin alameen be isa yamata kishiyaba koze mutu inko yayi seta kona matar
aminan nata nazugata dacewa shi yama isa ay baze ma faraba
.
Babbar sallah ta taho Dan haka ana saura sati daya Al ameen yanufi gida danyin bikini sallah agida
.
wannan Karon Aisha tayi murna dazuwanshi Dan gaba daya shaawarshi takeji kuma ita bata iya zinaba shiyasa takosa yadawo Dan tasamu karbuwa agurinshi gyara ko ina nagidan tayi har kudi taware takira masu yin penty sukayiwa ciki dawajen Gidan turaruka kalakala haka tadunga sawa gidan duk Dan tafaranta mishi rai ga abinci yakai kala goma Data siyomishi a restaurant duk Dan yaji dadi. Itama wani gurin gyaran gashi taje me suna maman Izzuddeen beauty Saloon sukayimata gyaran kai hardasu eye lashes suka samata dayake Maman Izzuddeen taiya aykinta shiyasa Aisha sosai tayi kyau
Daga Saloon gurin wata Hajiya me gyaran jiki taje wacce ake Kira da Maman Gidado tamata gyaran jiki sannan tamata lalle wayyo fans naso kuna gurin dakunsha kallo araina nace ikon Allah wato Ashe Aishan tasan abinda yadace Amman batayi se yanzu datake dawata manufa tadaban aranta lalle taamsa sunanta ballagaza
Bata dawo gidaba ranar se laasar Tana zuwa wanka tashiga Wanda seda takusan share awa guda a toilet Dan rabonta da wankan takusa sati guda sede tayi ciki tsami tafita Tana fitowa kwalliya akasoma ba batun sallah danko alwala batayoba haka tagama Kwalliyar ta ta cakare a wasu tsinannun English wears masu bayyana surar jikinta
falon kasa tadawo ta harde zamanta ba jimawa taji alamar bude get wani sanyine yaratsata Dan tuni magungunan data shashsha dawanda ta matsa sunfara ayki🙄
dasallamarshi yashigo Dan tundaga kofar gida kanshi yafara kwancewa daganin sabon penty
yanashigowa falo faduwa yakusan Yi sabida arba da Aishan dayayi Tana takowa zuwa gareshi se girgiza kirji takeyi abinda yafi tsolewa alameen ido suman tsaye yayi rungumar da Aishan tamasace tafarko dashi kallonta yakeyi cike da matsanancin mamaki Dan tunda yake da ita bata taba rungumeshi Dan yadawo ba sede shi yarungumeta mamakinshi be karuba seda Yaji muryarta Tana fadin sannu da zuwa Rabin Raina
.
wani dadine yalullube alameen tabvas yanzu ya yarda Allah yashirya mishi Aishan shi rungumeta yayi shima nanfa suka shiga kissing din juna dakyar alameen yakwace kansa danta Aisha bataki komai ayishi agurinba kan kujera suka nufa suka zauna yayinda Aishan tahaye kan cinyarshi tazauna Tana masa wani malalacin murmushi
sannan tace sannu dazuwa hubby na ya hanya cike da farinciki yace hanya Lfy baby na yana sameki Lafiya tabashi amsa gamida fari da idanuwanta
janshi tayi tarakashi toilet danyayi wanka ga mamakinsa Aisha yau harda tayashi yin wankan
.
yana fitowa ta tayashi shiryawa sannan tajashi zuwa dinning
alameen murna kamar ta kasheshi ganin kulolin abinci kalakala nande yashiga dibar gara yana samata alvarka bayan yagama alwala yayi zefita masallaci sallar magrib dasauri Aishan Tasha gabanshi tace haa hubby ina zuwa kuma
sallah zanyi Gimbiyata yanzu zandawo kema jeki kiyi sallar yana gama fadin hakan yamata kiss agoshi yazagayeta yawuce
tsaki Aishan taja Wlh Dan karta ja yafasa biyamata bukatane da tamasa rashin mutunci Dan tsabagen rainin wayo yasan abinda take nufi amma shine harda wani tafiya masallaci sallah
dakinta tawuce tazauna Dan sallar cewa tayi tahada da asuba danko azahar batayiba
alameen bedawoba seda yayi sallar ishai sannan yashigo gida
bata falo danhaka dakinta yanufa Yatura kofar yashiga hasbunallahu waniimal wakeel itace tafito abakinsa sabida arba dayayi da Aishan haihuwar uwarta babu kaya ajikinta jikinshi ne yafara Bari dasauri yaje yarungumeta yashiga ayka mata da sakwanni masu wuyar fassara to abinka daya jima beyiba jinshi yake kamar ango ajan gado suka yada Zango sosai suka Raya wannan dare Wanda se asuba alameen yasaurara mata yayi farinciki sosai da canjin dayaji Aishan tayi Danjinta yayi takara test
.
dasafe yashirya zeje gidansu gaida iyayensa yanemi Aishan datamasa rakiya wata uwar harara ta wurga masa sannan tace
Bainda zani kajimu da mutum shikenan daga Dan sakar maka fuska se raini yanemi yashigo to contract ne kuma yakare bukatar maje hajji sallah Dan haka karka nemi ka takuramin amfaninka nawannan lokacin agurina yawuce sewani jikon tawuce tabarshi agurin
jiri ne yafara daukar alameen dasauri yazauna yadafe kanshi yana karanta adduar datazo bakinsa wato Aisha tayaudareshine da duk abinda tayi Dan yabiyamata bukata badan Allah ba wannan wanne irin balaine
dakyar yasamu zuciyarshi tadena zafi yana zaune agurin tazo tawuceshi tafita yawonta
mikewa yayi jiki bakwari yanufi gidan iyayensa sosai sukayi murna dazuwanshi
daddy ne TaiwanYauwa aminullahi dama Kabir nake jira yazo na aykeshi tunda gaka kazo sekai kaje
cikin ladabi da biyayya yace to daddy ina zanje
rugar yalli inda muka taba zuwa muka Kai wata yarinya gidansu can Zan aykeka kasiyo shanu dazaa rabawa mutane
carab munauwara taamshe daddy cewa zakayi gidansu me kiranshi kado budurwar jae zaka aykeshi gabadaya falon sukasa dariya duka alameen yakaimata ta gudu
kudi daddyn Tamiko Yamiko masa a ledar viva yace gasu miliyan ukune kasiyo yadda yakama murmushi alameen yayi sannan yaajiyewa daddy kudinsa yace ze siyomasa danashi kudin inda sabo daddy sunsaba da kyautatawa daga alameen din albarka sukai tasamasa yamusu sallama yatafi bayan daddy yatambayeshi zegane gidan yace eh zegane har munauwara nacewa kode tazo tarakashine yamata banza yawuce
.
da azahar ya iso garin yana faking surbajo nafitowa zata tafi kitso tsayawa tayi Tana kallonshi yayinda shima tsayawar yayi yana kallonta
cike da TaiwanTsiwa tace aradu wannan kadon bayan bakin halin har maita gareka yoto inba mayeba taya zaka tsaya kana kallona kamar nacimaka bashi nagade kudin daaka bani kyauta aka bani kuma bakai kabaniba baffankane bare kace sukazo ansa sede idan bakin halin nakane zaka gwadamin aradu ko dakasha sanda Danni bani daukar raini tafadi harda murguda baki
alameen dariyace takwacemasa tabbas ya yarda da zancan mutane dasuke cewa yanfulani Nada katobara
surbajo ganin yanamata dariyane yasa takwance dankwalin kanta tasake Damara dashi dama akwai wata damarar daure akugunta karasowa tayi gabanshi tatsaya taruke kugu ita ala dole zatayi maganinsa tunda yake mata dariya wata dariyarce tasake kamashi yace ikon Allah yau nahadu da gamona inba hakaba taya daga zuwana bancimikiba
ban shamikiba kitareni da balai
.
surbajo tsayawa tayi Tana kallonshi tunda yafara dariya dimples dinshi suka lotsa hankalinta yakoma kanshi aranta tace Ashe akwai Wanda yafi jae kyau dama bansaniba hannunta takai dede setin dimples din ta taba dariyar dayakeyine tatsaya sakamakon jin antabashi afusace yajuyo zekaimata duka dagudu takwasa Tana cewa woo nacuceshi nataba ramin nacuceshi nataba ramin harta kule yadena ganota
haba alameen mezeyi inba dariyaba shi tunda yake betaba nishadi irinnayauba yana dariyar ne ardo yafito yasameshi
ganinshine yasa yadena dariyar da faraa yanufeshi suka gaisa ardo yamasa iso zuwa cikin gidan anan alameen yafadamasa abinda yakawosa zagayawa dashi ardo yayi gardengarken shanun yagama zaba yabiyashi kudinsa inda harda ihsani yamasa sannan yabaShi kudin daze dauko motor dazaa zuba shanun akawo musu kaduna Dan dama inaka siya ardonne yake kaimusu sallama yamasa yatafi bayadda ardo beyi dashiba yatsaya yatafi da nono amma yaki .
yafara rakiyatafiya kenan yahadu da surbajo tadawo daga kitson tsayawa yayi Dan yaga tanufoshi soyake tasake bashi dariya Dan duk wani bacin ran da Aishaaisha tasashi dariya da surbajo tabashi dazu yakawar masa dashi
karasowa tayi tace kado zaka tafine kai yadagamata yana murmushi tace to Dan Allah kabarni nasake taba ramin fuskarka aradu bazan fadawa kowaba inma bazaka Bari nataba Dan Allah ba togashi kabarni nataba a naira goma tafadi tana kwance habar zaninta tadauko naira goman dariya alameen yakeyi danshi Wlh yanzu kallonta yake tamkar katoon
Mika hannu yayi yaamshi kudin sannan yatada motarshi yatafi yabarta dagudu tabi bayan motor Tana cewa kado katsaya kabani kudina gudu take iya karfinta alameen na kallonta ta mirror yana dariya dataga bazata iya kamoshibane tace kaci wuta balbal ban bakaba tadauki dutse tawurga ma motar dayake surbajo ta iya jifa seda tasamu motor
Alameen Allah ne kawai yakaishi gida Lfy Sabida daya tuno surbjo dariya yakeyi lalle ya yarda fillo akwai wowta baabinda kebashi dariya irin nacuceshi nataba ramin wannan Abu nabashi dariya ahaka har yaiso gida
itako surbajo Allah yaisa tajata yafi kwando dubu sabida naira gomanta Dan kudin da daddy yabata gona ardo yasiyamata dasu goman data ba alameen ardone kullum yake bata goma takashe toshine tayau alameen yagudu da ita har kuka tayi akan naira goman koda sukaje makarantar dare kasa karatu tayi sabida gomanta yayinda tasha alwashin duk randa taga kado seya sani
taku har kullum
.
Alameen tunda yadawo gida ko Aisha tabata masa rai baya damuwa sabida yanashiga damuwar surbajo take fadomasa arai yayita dariya shikadai
Naira gomanta ko duk inda zashi da ita sabida inya Kalli kudin suna sashi nishadi yanason komawa rugar Dan yaga irin bidirin da zaayi in suka hadu da ita Dan yasan tabbas akwai artabu
.
Anyi sallah da sati guda alameen yakoma bakin ayki
Sosai wannan Karon yakejin dadin aykinnasa sabida baya tare da damuwa ko kadan Dan daya tuno surbajo yake samun natsuwa
yauma tafe suke a mota shida amininsa Usman tambayarshi yayi yace yadai mutumin naga tunda kadawo daga pass gaba daya kasauwa dariya bata maka wiya kode madamce tasamu twins ne
Murmushi alameen yayi Sannan yace hmm Usman kenan wanne irin twins Aisha zata samu abinda ranar dazan dawo naje mata sallama naga wasu tablet a kan mirror dinta a time din tana toilet nadauka nakaranta naga nahana daukar cikine abun yadauremin kai banmata maganaba sabida nasan kanta ta cuta Danni Wlh aure zan kara kwanannan
Kai haba mutumina Usman yatambaya cike da murna
Wallahi kuwa aure zan kara inji alameen
tokodai soyayyace take saka yawan nishadi
dariya sukayi gabadaya
sannan alameen yaba Usman labarin surbajo Usman harda hawaye Dan dariya
Alameen yaci gaba Usman Wlh bawai sonta nakeba sabida yarinyace gaba dayanta kawai drama dinta nakeso shiyasa nake ganin auranta kawai zanyi tazo gidana amatsayin cartoon inkalla inyi dariya
Kokuma takalleka tayi dariya ba darabon kaine zaka zama cartoon din agurinta inji Usman yafadi yana dariya
Haba Usman nidin yarone dazan tsaya ina shirme kawai nafadamaka for personal use zan ajiyeta
dariya usman yakeyi sosai sannan yace Allah yabada saa amma Wlh zakace nafadamaka kaine zaka koma cartoon din at the end of the day
Dariya alameen yayi yace zanko baka labari ni dannayi dariya kawai Zan auri yarinyarnan Wanda kaima intayi wani shirmen agabanka seka dara
**********
Seda alameen yakwashe wata uku sannan yazo hutu wannan Karon besamu tarba daga gimbiyarsa ba shima bedamuba sabida badan ita yazo hutunba Dan madam surbajo yazo
.
Iyayensa sunyi murna dazuwansa dama kuma sungaji da ganin shi a halin dayake sunason subashi shawara agameda rayuwar gidanshi
Bayan yagaishesu mahaifinsa yace yanzu aminullahi haka kazabawa kanka rayuwa da macen dabatasan ciwon kantaba bazaka iya daukar matakiba duk Inda nafita labarinka Akeyi mace tamallakeka ko haka kaga Dan uwanka nayi anasa gidan haba aminullahi kasanifa mace itace mutum amma Kai ga irin wacce kazabowa kanka kayi tunani kagyara rayuwarka
mahaifiyarsama fadan Tamasa dama kuma sunbarshine badan komaiba sedan kar ace suncika sa ido arayuwar yayansu
godiya alameen yayi sosai sannan yashaida musu aure yakeson karawa
sosai sukai farinciki dajin zancan dansuma abinda ke ransu kenan
mahaifinshine yace aina kasamo matar aminullahi
murmushi yayi yana sosa keya yace daddy kumma santafa
faraace takaru afuskokinsu inda daddy yace Kai alhdllh wacece
surbajo yabasu amsa gabadaya sukasamasa dariya
mommy tace ikon Allah tagida ma kana fama ina zaka iya da shirmen surbajo ban hanakaba amma Allah yasanya alkhairi Kai kaji kagani
daddy da tun dazu dariya yake seyanzu yace aminullahi na yar fillo to iyayenta sunsan dazancan
aa yabasu amsa inade so daddy kaje kanemarmin aurannata
badamuwa aminullahi daddy yafadi yana dariya
sallama yamusu yatafi Dan dama yakosa sugama magana yatafi Dan surbajo yakeson gani
yana fitowa yadauki hanyar makarfi shikadai dan bako inane yakeson excode Dinshi subishiba bare irin wannan tafiyar tazuwa yada manufa
.
da azahar yaiso garin makarfi lokacin surbajo taje yo icce
parking yayi akofar gidan dayake yau larabace mazan gidan suntafi cin kasuwa Dan kasuwar makarfi ranar laraba take ci
surbajo ce tashawo kwana da iccen datayo akanta kamar amafarki taganshi atsaye ajikin motarshi
habawa xubar da iccen tayi ta runtuma da gudu gurinshi Tana zuwa rigarshi takama Tana fadin yauwa wana Kama ay dama nafadi aradu nakamaka sekaji jiki gashiko yau kaida kanka ka kawo kanka har gida tabadi Tana kokarin gyara damararta da hannunta daya daya kuma Tana rike dashi Dan kar yagudu
shiko alameen dariya abun yabashi Dan yasan zaa rina
surbajo dataga yana dariya naushi ta dirka masa aciki sannan tacigaba da kaimishi duka takoina ba abinda keba alameen dariya seganin itace ke dukan Amman itace ke kuka Tana aradu Seka bani kudina bazan yardaba gashi dukan datakeyi ko zafi babu kamar badukannasa takeyiba
be hanataba seda tagaji Dan kanta sannan takyaleshi Tana haki
sannu alameen yamata yana dariya yace ammafa kinsha ayki
.
dagowa tayi da jajayen idanuwanta datasha kuka tace jiki kamar karfe dukanka nakeyi amma ninakejin zafi aradu senamaka abinda koda wasa akace ka kuma yimin rashin kunya bazaka kumaba tafadi harda nunashi da hannu shide binta kawai yake da ido yayinda gefe daya kuma yana daukarta awayarshi
shigewa gida tayi Takai iccen sannan tadawo ga mamakinsa tsugunnawa tayi agabanshi tanacewa Dan Allah kado kayi hakuri kabani kudina aradu nasha kuka sabida kudina daka gudu dashi danhaka seka karamin akan nera gomata kaji kado
murmushi yayi sannan yace naji zanbaki kuma zan karamiki akan nakin tonikuma dukan dakikamin anawa dannima biyana zakiyi inba hakaba inje inkiramiki sojoji sukamaki
akidime surbajo tamike Tana shirin guduwa jin yaambaci sojoji rukota yayi dasauri yace ina zaki muna magana kuma
cikin barin jiki tace aradu nayafemaka kudin kuma Don Allah karka kiramin wainnan mugayen mutanan niko ganinsu banaso yin sabida nataba ganin yadda sukayiwa wani mutumi dukan tsiya akasuwa suka ciremishi kaya aradu mutumin yabani tausayi Danhaka kayafemin aradu bazan kumaba
ganin ta tsoratane yasa alameen kwantar mata da hankali tahanyar cewa haba surbajo ayko nakirasu bazasu iya yimiki komaiba sabida kyanki
ay surbajo najin haka tahau dariya sannan tace dagaske kakeyi basa Kama mekyau
ehmana dagaske nakeyi
kwace hannunta tayi daga rukon dayamata sannan tace to aradu nafasa yafemaka kudina seka bayani
dariya alameen yayi yace ayko bazan bakiba sabida ke kikace kin yafemin
kallonshi surbajo tayi sannan tace zaka biyanine tun biya nada dadi
.
sunanan Ardo yadawo dafaraarsa ya tarbi alameen Yayinda yarufe surbajo da fadan meyasa bata kawomasa ruwa da shimfidaba alameen ne yace nine nace tabarshi base takawoba
sannan Ardo yadena fadan
mamakine yarufe surbajo tace a zuciyarta hoddijan aradu kado ko a makaryata shinadabanne kato dashi amma baya kunyar karya
cikin gida ardo yaja alameen suka zauna suna hira
sato jiki surbajo tayi tafito inda motarshi take tsinke tasa acikin tayoyin tasacemusu iska gabadaya Tana gamawa ta ruga gidansu arera Tana dariyar mugunta ita atunaninta hakan datayi baze Hana. motor tafiyaba sede yahanata yin sauri dalilin dayasa tasacemishi iskar kenan
.
alameen hira tayi dadi Shina Shida Ardo besan magaruba takusaba seda yakalli agogon hannunshi mikewa yayi domin tafiya ardo nata samishi albarka kyauta yayiwa ardo metsoka sannan yafito daga gidan tsayawa yayi yana waigen ta ina ze hango cartoon dinsa tazo suyi sallama amma be hangotaba ardo yace aykawai kayi tafiyarka inde surbajoce takai takwas nadare bata dawoba tanacan suna wasa da saointa
bahaka alameen yasoba Amman bashida zabin dayawuce yatafi sabida dare yafara Yi ga hadari yahadu sosai
shiga motarsa yayi batare daya Lura da barnar da surbajo tamasaba seda yakunna motar security dake jikin motar yafara kara alamun akwai Matsala amotar fitowa yayi danganin meyasami motar
innalillahi wainna ilaihi rajuun ita kawai yake maimaitawa ganin tayoyin motarshi a sace kobaa fada masaba yasan aykin surbajone dafe kanshi kawai yayi yana kallon motar yama rasa abinyi dama daya tasace dase yadauko spare din tayar dake boot yasa to duka hudunne gashi garin ko mashin babu me ita bare asamu Mesa iska wayarsa yadauko babu network sam
kamin yagama yanke abinyi ruwan sama yafara sakkowa
ardone yakaraso kusa dashi yace Aminu akwai matsalane
kai yadagamasa sannan yamasa bayanin abinda yafaru da motar amma befada masa surbajo ce tamasa ba Dan yasan tsaf ze iya Zaneta
.
suna nan tsaye ruwan yakarasa tsugewa kamar da bakin kwarya dasauri ardo yajashi zuwa wata bukka wacce dama anyitane sabida baki
zama yayi akan gadon karan dake ajiye adakin ardone yajawo kofar bukkar yakare wacce take ajiye agefe itama takarace
sunanan zaune ruwan betsayaba se misalin bakwai da Rabi nadare
ruwan alwala ardo yaje yakawomasa yayi alwala yay sallah sannan ardo yakawomasa barguna guda biyu da fitilar aci balbal yace gashi yashimfida daya yarufa da daya yayi hkr yakwana anan inyaso gobe da safe ardon zeje cikin gari yakira mesa iskar yasamasa
alameen bakinciki yagama rufeshi bakomai yake bashi haushiba se irin yadda ze kwana Abukka batare da wani tsaroba ko kofar arziki babu ga sanyi daaka fara kamar jaura tawuce shiyama zeyine gurin bacci akan gadon kara amma ya yaiya bashida zabin daya wuce hakan
komawa motarshi yayi yadauko bindigarshi da touch light Wanda yaajiye amotar sabida tsaro
surbajo se takwas tanufo gida itadasu arera dasuka rakota tabayan gida tashigo gidan Dan haka batasan alameen betafiba alwala tayi sallah sannan tafara tunanin oh kado koyaje gida yanzu oho sumayece takirata tace tazo takaiwa
bako abinci yana dakin baki mamakine yakamata nayaushe sukayi bakon daukar abinci tayi tuwan dawane da miyar kuka danya yasha manshanu Wanda aka zuba a akushi na musamman tanufi bukkar bakin dayake motor alameen bakace kuma akasan bishiyar mangwaro yayi parking dinta surbajo bata Lura da itaba sallama tayi kofar bukkar daga ciki aka amsa shiga tayi taajiye kwanon abincin tajuya zata fito fisgota yayi da karfi tafada jikinshi zata samasa ihu yarufe bakin da hannunshi haska Mata fuskarshi yayi sannan yasakarmata baki arude tace kado meya hanaka tafiya gida kallonta yayi sannan yace haba surbajo meyasa Zaki sacemin iskar tayakinsan motar kuma bazata tafiba inba iska tausayinsane yakamata hawayene suka fara zubowa daga idonta cikin kuka tace Dan Allah kado kayi hkr aradu bansan motor bazata tafiba nadauka saurine bazatayiba Dan Allah kayafemin nasa Zaka kwana a inda baka saba
tausayinta alameen yaji amma hakan baze hanashi hukuntata ba danyayi alkawarin yimata hukunci bindigarsa yazaro ya saitata kan surbajo .
0 comments:
Post a Comment