SURBAJO Part 5
.
Koda akayi parking aharabar gidan surbajo bata tashi daga baccinba ganin bata tashin bane yasa alameen gyara zamansa a motar Dan cewa Usman yayi da direban su sauka amotar danshide baze fitaba se surbajo ta tashi a bacci sauka sukayi suka barshi Usman yace ah lalle wannan cartoon yana kyau tonide badaniba nashiga ciki inta tashin inajiranka yafadi yanamasa dariya
Mommy dasauran dangi masu jiran karasowar Amarya jin ance motar amaryar takarasone yasasu fita domin taryota
.
Sede ga mamakinsu sojoji ne kewaye da motar rike da bindigu cikin shirin kota kwana abun yabasu mamaki
Tsayawa sukayi suna jiran abude motar
tsawon minti goma baa budeba yasa Momy tambayar daya daga cikin sojojin
Kai wai amaren basu isobane ko bawannan bace motar amaryar
Cike da girmamawa yace madam Amarya taiso amma oga shima yana cikin motar bande san abinda yahanasu fitowaba sede ko zakije ki gani
Murmushi Momy tayi sannan aranta tace dakyau aminullahi wato mu zenunawa yayi Amarya ko zeci uwashi ne dawannan shegen rawar kan
munauwara takira tace taje gurin motar tace injita tace aminullahi yafito da Amaryar haka kota sabamasa
dagudu munauwara tanufi motar abinnema yasamu Dan ita akwai son Amata irin wannan ayken
nurking glass din motar tayi seda tadan jima tana nurking din sannan yasauke glass din motar ganin munauwarace
Yana saukewa idonta yasauka kan surbajo dake ta faman bacci kwance ajikinshi
Dariya tayi sannan tace Bross kana hutawafa to mommy tace Wlh ranka ze baci inbaka fito da amaryaba tafadi Tana dariya takara dacewa su Bross ko kunya juyawa tayi da gudu zata bar gurin dasauri yarukota yace zaki sani wato ninema mara kunyan ko kwacewa tayi taruga gurin mommy Tana dariya
tace mommy Wlh amaryar ma bacci takeyi maybe shine abinda yahanashi fitowa daga motar
bata rufe bakiba taga daya daga cikin sojojin yanufi motar yabude kofar
Alameen ne yafito sannan yamika hannu yadauko surbajo dake bacci
Yanufi su mommy nanfa abokanan wasa suka shiga tsokanarshi masu dauka awaya suna dauka Dan abun koni yaburgeni
.
jin hayaniya da surbajo tayine yasata farkawa ganin abinda kefaruwane yasata Fara kiciniyar kwace kanta Dan gaskiya kunyace takamata sosai
Ganin tanason saukane yasa alameen sauketa
Lafayar dake jikinta takara ja tarufe fuskarta jikinta se rawa yake sabida kunya mommy ce takarasa ta rungumota tana fadin barka da zuwa cikin zuriata Allah yasadamu da alkhairin dake tattare dake yakawar da sharrin
Ameen sauran jamaar suka amsa daganan aka shige da ita cikin gidan falon daddy aka kaita alameen ma yabi bayansu
nasiha sosai daddy yamusu inda akarshe yagargadi alameen akan yarike amanar yar mutane kuma yayi adalci atsakaninsu
daganan akawuce da surbajo part din mommy domin shiryata zuwa gurin dinner shima part dinshi na gidan yanufa
Usman yatarar da wasu abokansa su biyu suna hira dashigarshi suka juyo kanshi suna tsokanarshi babu kamarma Usman harda cewa shi ko alabari betaba jin ango Mara kunya kamar alameenba
dariya alameen yayi sannan yace
Kai alhdllh nagodewa Allah dayasa nazama nafarko atarihi
duka suka kaimasa dukansu suna dariya
daganan suka shiga shirin zuwa gurin dinner wacce zaayi a bafra international hotel dake no11b yakubu avenue off alkali road unguwar rimi kaduna
Sosai suke shiri inda Amarya mommy tadauko me kwalliya tashiga yimata sosai tayi kyau wedding gown akasamata light blue gaskiya bame kallonta yayi zaton wai shekarunta sha hudune sabida surbajo akwai Kira kuma bame zaton tasan hanyar wani abu waishi kauye bare aje ga ruga ita kanta data Kalli kanta a mirror tantama tashigayi akan anya itace kuwa
alameen ma shadda yasa light blue shima yayi kyau sosai yayinda sauran abokansa suka sa farar shadda
kawayen munauwara sune suka zama yanmatan Amarya dangama surbajo baazo da kawarta kodayaba
suma yanmatan Amarya fararan dogayen riguna sukasa yayinda Suka daura head ja takalmi ja
gaskiya sunyi kyau
takwas nadare motoci suka fara dibar mutane zuwa gurin taron
yayinda uwargida Aisha ma tagama shiryawa cikin wani yellow din material doguwar riga takalminta red head dinta ma red Jakarta ma red ce se mayafin Data Dan yafa shima red itama ba laifi tayi kyau aminanta kuma pink din material suka sa da duk wani Wanda yazo ta bangarenta duk pink sukasa
.
Gabadaya jamaa sungama tafiya gurin dinner se Amarya da ango yarage
Motar dazasu tafi aciki ta iso dan haka alameen dakanshi yanufi falon Momy inda surbajo kezaman jira dan babu kowa agidan duk Sun tafi harda su mommyn
Dasallamarsa yashiga falon dakyar surbajo ta amsa gamida dago fuskarta
Wow itace kalmar alameen tafarko jikinshi narawa yakarasa gurinta hannunta yakamo yamikar da ita tsaye yayi hugging dinta kissing dinta yake kokarinyi dasauri surbajo takwace jikinta gamida ballamasa harara tace hoddijan aradu baka isaba yau inma wani asirin akabaka kadunga samin abaki da bakinka to yau takare danni yau KO abinci banajin zanci sabida gudun kar jambakina yagoge shine kai godaigodai dake kawani zo zaka lashe minshi da bakinka ko to Wlh a hir dinka takarasa maganar tana murgudamasa dan bakin dayasha makeup
.
Dariya abun yaba alameen yadda tayi maganar gunta yanufa da niyar kamata nanfa surbajo tasa gudu shima yana binta sunata zagaya dakin wedding gown dinta taja yakamata sabida Jan kasar datakeyi rungumota yayi jikinsa yana kokarin yimata Kiss wayarsa tashiga ruri dasauri yaciro wayar a aljihunsa mommy ce ke kira dasauri yadaga tunkafin yayi mgn mommy tafara fada
Aminu baka da hankaline kuntara jamaa a guri amma har yanzu baku isoba banason shashancin banza fa
Hakuri yashiga bata sannan yakashe wayar danshi ganin surbajo dayayine yasa yamanta akwai dinner da zasuje
Be tsaya bata lokaciba ya dauketa cak bayan yadauko mata fos dinta kai tsaye motar yanufa da ita tun kamin yakaraso wani soja yabude masa murfin bayan zaunar da ita yayi sannan shima yazagaya yashiga direba yaja suka dau hanya yayinda sauran motocin excode dinshi suka sa motar a tsakiya ana jiniya
Dayake ba nisa tsakanin gidan da hotel din so basu wani dauki lokaciba suka iso
Isowarsu keda wuya abokan ango da kawayen Amarya suka fito daga hall din danyima ango da Amarya rakiya zuwa ciki
Fitowa yayi sannan yakamo hannun surbajo itama tafito nanfa masu hoto da video camera suka shiga aykinsu
Kawayen Amarya da abokan ango ne suka sasu atsakiya
Sun fara tafiya surbajo se kokarin faduwa takeyi sabida takalmin kafarta me uban tudune ganin hakan da alameen yayi ne yasa be Bata lokaciba yadauketa kamar jaririya itakuma tasakalo hannunta ta wuyansa
Ihu da tafi kawayen suka sa dan gaskiya koni sunburgeni
Daganan suka fara takowa zuwa cikin hall din yayinda MC yashaida shigowarsu
Nanfa kallo yadawo kofar dazasu shigo
aisha ko wuyanta kamar ze tsinke dan tsawon datake karamasa nason hango ango da Amarya
shigowarsu seda numfashinta ya dauke yadawo bakaramin razana tayiba da ganin alameen dauke da amaryarsa
.
suko sauran jamaar dake gurin tafi kawai suke musu masu daukarsu hoto nayi har suka karasa gurin zamansu zaunar da surbajo yafarayi sannan shima yazauna
surbajo kara rufe fuskarta tayi da mayafinta sabida tasha kunya daukota da alameen yayi daurewa kawai tayi tabarshi yadaukota dan tasan intace dakanta zata tafi faduwa zatayi
nanfa aka shiga gabatar da abinda yakaisu gurin inda MC yabukaci da ango yabude fuskar amarya batare da Bata lokaciba yabude fuskar surbajo
innalillahi wainna ilaihirrajuun itace kalmar da aisha ke furtawa dan ta gigice da ganin kyau irinna surbajo hawayene suka fara biyo fuskarta na bakin ciki dasauri Zuly tasharemata gudun kar wasu sugani rarrashinta suka shigayi amma kosu Sun jinjina dakyau irinna surbajo
.
hankalinta besake tashiba seda taji ana Kiran ango da Amarya sufito su yanka cake
duk abinda ake fadi da turanci akeyi kuma surbajo batajin turancin alameen ne yamike sannan yakamo hannu surbajo yamikar da ita suka nufi gurin cake din dakyar surbajo take tafiya sabida gudun karta sha kasa duk da de rabin jikinta na jikin alameen
tafiyar Tata seta karamata kyau dan wasu dauka sukayi yanga takeyi harsuka karasa gurin cake din alameen besaketaba koda suka tsaya zagayo da hannunsa yayi ta kugunta yariketa ahaka suka yanka cake din aka tafa musu MC yace Amarya taba ango abaki cikin harshen turanci
surbajo batajiba alameen ne yaradamata akunne waigowa tayi tana harararsa akan yace tabashi abaki shikuma yana murmushi wayyo jamaa zokuga yadda wannan kallo da surbajo tayi yakoma na so da kauna ga alameen yanata murmushi
yanko cake din surbajo tayi tanufi bakin alameen kara rungumeta alameen yayi ta kwantar da kanta a kirjinshi ahaka tasa mishi cake din abaki huuuuu kawai mutane ke fadi dan wasu liki suka fara zuwa suna musu agurin dankoni Sun burgeni
shima alameen ahakan yabata cake din tana kwance ajikinshi
.
bayan sunkoma gurin zamansune aka bukaci ango yayi Godiya ga jamaar dasuka taru dominsu nan alameen yayi jawabin cikin harshen turanci bayan yagama aka bukaci Amarya tayi itama alameen ne yafada mata abinda MC yace yakara dacewa tayi da hausa kuma don Allah karta dunga sako aradu à maganar murmushi tamasa Wanda yadauki hankalinsa sannan taamshi loudspeaker tafara magana cikin harshen filatanci
wow bakaramin burge mutane tayiba danko babu Wanda yayi zaton batajin turanci
bayan tagama ne akabukaci ango da Amarya su fito fili su taka
alameen ne yarukota suka fito filin yana rungume da ita aka samusu wakar da Sani slowly yamusu ta auransu suka fara takawa a hankali nanfa kowa yamike yafara yiwa ango da Amarya liki
aisha kuka take harda majina n'a bakinciki da sauri aminanta suka fitar da ita daga cikin hall din gudun karsuyi abin kunya
kai tsaye gida suka nufa da ita suna bata hakuri itako fadi take wayyo Allah alameen yakasheni yacuceni yarasa wacce ze auromin amatsayin kishiya se wannan gogaggiyar Yar bokon nabani ni aisha
sude hakuri suke ta bata
acanko ango da Amarya ne keta cashewa
baa tashi ataronba se goma nadare
suna dawowa aka sa surbajo tayi wanka aka shiryata cikin shigar alfarma aka nufi gidan mijinta da ita
.*
Ankai amarya Lfy inda dangin mahaifiyarta suka kara yimata nasiha game da zaman gidan miji itade surbajo se kuka takeyi
Kamin goma nadare kowa yawatse anbarta ita kadai Bilkisu ce tace mata takulle kofarta karta bude se intaji alameen ne ayko haka tayi kulle kofar tayi duk da bata iyaba seda bilkisun takoyamata
Gefen gado tasamu tazauna tadunga bin dakin da kallo irinna kauyanci komai yamata kyau sede ita wasu abunma batasan menene shiba
Siket da rigane ajikinta nawani material purple colour semayafin data rufa dashi fari takalmin kafarta ma farine kanta ba dankwali sede farin ribom daaka kama mata gashi dashi
Mikewa tayi tacire mayafin dan tagaji tunda aka fara bikinta take rufa mayafi to itade yau tagaji shiyasa tacire
.
Falonta tadawo tazauna akan two sitter sanyin AC naratsata komai na falon yaburgeta
zamanta bajimawa taji ana nurking din kofar mikewa tayi taleka ta ramin da Bilkisu tace tadunga lekawa
Alameen tagani tsaye shikadai bude kofar tayi takoma gurin zamanta tazauna
Da sallamarsa yashigo
Suman tsaye yayi lokacin dayayi arba da surbajo tamasa kyau sosai musamman gashinta daya zuba har gadon bayanta bakikkirin se shining yakeyi
.
Ledar daya shigo da ita yaajiye sannan yasami daya daga cikin kujerun yazauna
surbajo amare kallonshi kawai takeyi ba um ba umum shima itadin yake kallo murmushi yayi yace baby na babu ko gaisuwa irin wannan shan kamshi haka konayi laifi ne
murguda baki tayi tace yoto shikenan sokake insaki baki inta zuba agabanka kaidin daba kunyace gareka ishashshiyaba yanzu kace zaka daukeni kamar wata yarka to aradu kakiyayeni kajide nafadamaka tafadi Tana Kara daure fuska ita ala dole batason raini
dariya zancannata yabashi babu abinda yake burgeshi da ita irin son girmanta
.
mikewa yayi yakoma kujerar datake kai dasauri tamike tana shirin barin gurin cikin zafin nama yarikota tafado kanshi
Riketa yayi tayadda bazata kwaceba sannan yace baby na Wlh bakida kunya ke kodan irin kukannan da amare keyi in antafi anbarsu bakiyiba Dan mayafin dasuke rufe fuskarsu dashi shima bakiyiba kin yiwa ango magana dawuri se ansiyi baki shima duka bakiyiba se rashin kunya kikemin to ki kiyayeni ko yanxu nayi Maganin rashin kunyar taki yafadi yana shafo gashin kanta
Surbajo kokarin mikewa takeyi Amman yahanata ayko budar bakinta se cewa tayi hddijan amma aradu kado akwai raini yo inbanda abunka ko kukan nakeyi aka kawoni gidannan me shegen kyau ay aradu nadena kukan kuma wannan kayan kyalekyalen duniyar inna rufe idona ay bazan gansu da kyauba kuma dakake cewa nayi magana da wuri badole inmaka magana da wuriba gudun kar kace zaka lashemin bakina kamar tsohon Maye ni wallah narasa mekakeji acikin lashewa mutane baki kallonshi tayi sannan tace Don Allah kado mekakeji inkana tsotsewa mutane baki batagama fadin mezata fadaba yahada bakinta danashi yashiga kissing besaketaba seda yaji dakyar take numfashi kallonta yayi yaga jikinta yamutu murmushi yayi yace baby to kinji abinda nakeji inna lashewa mutane bakin
surbajo baki yamutu mikar da ita yayi suka shiga kitchen dinta dake falonta yadauko plate da cup suka dawo falon ledar daya shigo da ita yadauko yajuye naman kaza a plate din sannan ya tsiyayamusu fresh milk a cup yamatso dasu gabanta wayyo surbajo idonki idon nama ay tuni ta watsake daga kasalar da yasamata takai hannu zata dauki naman caraf yarike hannunta yace au ci zakiyi batare danamiki tayiba wani kallon banza tawatsamasa sannan tace aa kallonshi zanyi kamar yadda kaima naga kanayi
murmushi yayi yace inde zakici namannan to akwai sharadi inde kikaci sekin biyani ko ajikinta tace inde biyane me saukine zanbiya koma menene bani naci murmushi yayi sannan yamikamata
seda taji takoshi over sannan tahakura da naman sannan tashanye cup biyu na fresh milk din
.
mikewa alameen yayi sannan yamika mata hannu takama yadagata toilet suka nufa brush yadauko yamiko mata bayan yasa maclean kallonshi tatsayayi danbatasan amfaninshiba mamakine yakama alameen ganin surbajo batasan brush ba Amman bakinta baya wari kwatantamata yadda zatayi yayi wayyo shazumamu aytana gogawa taji zakin maclean tas tashanye kumfan hankalinta kwance tamika masa brush din yakaro mata wani
Kobe tambayaba yasan shanyewa tayi dariya yashiga Yi sannan yasamata wani yacemata inde tasake hadiyewa mutuwa zatayi Dan yaganota mutuwace kawai kebata tsoro ayko bata sha dinba duk da ranta naso haka tadunga zubarwa har suka gama suka dauro alwala suka fito
shiyajasu sallah rakaa biyu ta nafila bayan sun idar yamata tambayoyi gameda addini ga mamakinsa duk tabashi amsa dede sabanin Aisha
mayafinta yabata tarufa yaja hannunta zuwa falonshi zaunar da ita yayi sannan yanufi dakin Aisha
sallama yayi yashiga tanajinshi tamasa banza karasawa yayi yasamu guri yazauna bata gaisheshiba shiya gaisheta sannan yace tazo falonshi
0 comments:
Post a Comment