SURBAJO Part 9
.
Watan haihuwar surbajo yatsaya kuma taje àmmata scaning ance namijine dan haka alameen Baya nisa da ita gudun kar haihuwa tazo bayanan
.
Wata ranar jummaa dasafe surbajo tafara jin ciwon nakuda amma basosaiba haka tadunga daurewa gudun karta dagawa alameen hankali hardare bata denajiba ciwonma sekaruwa yake
Ahaka harsuka kwanta tana ganin yayi bacci tamike tasoma safa da marwa dan ciwon sosai take jinshi sewajen karfe hudu na asuba alameen yafarka yaga bata kan gado dasauri yadiro daga gadon akasa yaganta atsugune se gumi takeyi tana nishi hannunta rike da kwankwasonta
Dasauri yarukota yana tambayar Lafiya
Mararta take nunamasa dasauri yasaka jallabiya itama yasamata hijab yakinkimeta yakai mota sannan yadawo yadauki kayan haihuwa asibiti yakaita mafi kusa dasu dan gani yake gidan Usman yamasa nisa
likitocine suka rufu akanta yayinda alameen addua kawai yakeyi Allah yasauketa Lafiya
Karfe shida nasafe Allah yasauki surbajo Lafiya yayinda tahaifo danta kyakkyawa mekama da alameen komai nasa na alameen ne
nurse ce tazo tama alameen albisheer gamida mikomasa yaron
allahu akbar Allah megirma alameen har hawaye yayi nafarincikin samun dan dayayi yaronko sekallonsa yakeyi idonsa tar akan ubansa
Alameen tambayar surbajo yayi nurse din tace tashiga wankane yanzu zaa fito da ita dakin hutu kosawa yayi yaganta Yaga irin murnar dazatayi
.
Baajimaba aka fito da ita tana zaune akan keken daake tura marasa Lafiya tana ganin alameen tasoma murmushi shima shiyakeyi rikemata hannu yayi da hannu daya dayan hannun kuma yana rungume da dansa
Dakin hutun aka kaita tadan huta amma lafiyarta kalau babu mecewa ita tahaihu ga yaron kato dashi masha Allah
alameen mikamata yaron yayi yace baby kinga kyautar Allah ko karbar yaron tayi tana kallo harda hawayenta lokacin da yaron yasoma dariyar kuda da jarirai sukeyi alameen dasauri yadaukeshi hoto
Nande sukasa yaron atsakiya suna kallo surbajo takaiwa alameen duka tace Wlh dear kayimin wayo duk wahalar nan danasha amma babyn dakai yake kama
Dariya yayi yarungumota yace haba baby daga jikinafa yafito kinga ko ay dole yamin kara yasan nima wahalar nayi nande sukai ta abin dariyarsu karfe takwas likita yasallamesu kai tsaye gida suka nufa
Da isarsu yafara kiraye kirayen waya yana sanarwa surbajo tahaihu yan kaduna har hoton babyn yadunga turamusu
Usman jiyayi kamar shi akayiwa haihuwar dan tausayin alameen yakeji ace ashekarunsa KO haihuwar fari beyiba
kayan barka suka siyo shida Hafsat cikin bayan motarsa harda kayan wasa suka nufo gidan masu jego
nanfa Hafsat tadunga yiwa surbajo tsiya wuni sukayi agidan har Usman yayinda su Fatee benee sune kan gaba kawa tahaihu
daga kaduna daddy yakira alameen yace gobe yadawo da surbajo gida sabida akula daita dakyau amsawa yayi cike dajin dadin irin soyayyar da iyayensa kema surbajo
.
washe gari dasafe dakanshi yashirya iyalinshi suka daga zuwa kaduna
Sun Isa Lafiya suna shiga falon gidan aisha ce zaune itada aminanta seganinshi sukayi yashigo rungume da jariri surbajo nabiye dashi abaya
dasauri aisha tamike bakinta har rawa yakeyi gurin tambayarsa
horney yaron waye wannan tana leka fuskar yaron dasauri taja da baya tanafadin pls alameen karka cemin yaronkane pls murmushi yayi yace why not zan ki fadamiki he is my son danane da babyna tahaifamin jiya
wata gigitacciyar kara tayi tayanke jiki tafadi dasauri aminannata sukayo kanta shima alameen gunta yanufa
surbajo ko amshe danta tayi tawuce part dinta hankalinta kwance
itako aisha Sun yafa mata ruwa amma abanza Bata farkaba dasauri suka sata amota suka nufi asibiti
seda likitoci suka jima akanta tafarko se kuka takeyi tana fadin wlh baze yiwuba dole nima kamin ciki nahaihu taya yarinya zatazo daga bayana amma ace harta haihu so biyu ni ko bari bantaba yiba
wuni Aishan tayi a asibitin sannan suka sallamota shiko alameen dama tun rana yabar asibitin sabida Mommy takirashi tace gidansu zekai surbajo kuma haka yayi zuwa yayi yadauketa yakaita gidan iyayensa
murnar dasukayi daganin jikansu nagurin alameen tanada yawa ga yaron har yafi alameen kyau daddy dakansa yamasa huduba
dangin mamanta ma baabarsu abayaba sunzo barka kuma kullum se sunzo wata mata aka dauko tanama surbajo wankan jego
gata bairin Wanda baa nunamata
alameen yakoma gurin ayki se ana gobe suna yaduro
ranar suna yaro yaamsa sunan Yusuf sabida daddy yace kyan yaron yakai asamasa sunan Yusuf sabida aynihin me sunan shima kyakkyawane fatansu Allah yasa yabiyo halin mesunan
fadin irin shagalin daakayi ranar sunan se data 1gb takare bangamaba
su Fatee sune agaba dan itama tazo sunan dan itama har gayya tayo na kawayenta masoya surbajo. su Eshat,maryam Taheer, Juwairiyyatu,zahra,hafsat daheer, lawisa,hameeda,ummu Yusura, Aunty Nafeesat Aliyu,maman Muallim,mrs lukman,ruky Afeshe, Ussaina m lawan kai suna dayawa dan motoci sukayo sukazo taron sunan anci ansha anyi danasha inda taro yawatse cike da farinciki
se fatan Allah yaba mejego Lfy da yusuf
.
Alameen daze koma bakin ayki kuka sosai suka dungayi shida surbajo bayason barinsu ga yaronsu meshiga rai shiyasa yaji duk garin yamasa zafi
.
Itako surbajo kukanta harda kishi sabida yace mata da aisha zetafi shiyasa abun yadunga damunta
Daukar Yusuf yayi yadunga masa wasa yanajin son yaron harcikin bargonshi
Haka sukai sallama ita kuka shi kuka
Haka yashirya aisha suka tafi tare murna gurinta kamar me. Shiko alameen haushinta yakeji Tunda taki Zuwa taga babynshi ahakade Suka tafi
Satinsu biyu dazuwa rivers yaga aisha nason kashemishi gida da kazanta kamar yadda takeyi akaduna
Bashiri yatarkatota suka dawo kaduna
Balai ko Da masifa yashasu agurinta kamar hauka
Shiko kota kanta bebiba dayake bakwana zeyiba shiyasa yana ajiyeta gida yawuce gurin sanyin idaniyarsa
Lokacin suna falo gaba daya mutanen gidan suna kallo kuma bawanda yasan da zuwanshi Yusuf nahannun daddy danshima son yaron yakeyi sosai
sallamar alameence takatsemusu kallon
.
Wata uwar Kara surbajo tasaki gamida kwasa da gudu tarungume alameen shima rungumeta yayi daga karshe yadagata yana jujjuyawa dariya suke cike da nishadi shaf sunmance agaban suwa suke murnar ganin junansu ta makantar dasu
Tana rungume ajikinshi tasoma shagwabarta fadi take dear shine katafi kamanta damuko sabida kana tare da katafilar matarka shine kotamu bakayi ko
Kara rungumota yayi yace who told you that my baby
Keda Legend Yusuf kullum kuna nan yanuna setin zuciyarshi
Kara rukota yayi yayi kasa da murya yace meyasa kike cewa Matata katafila dariya tayi sannan tace katafilace mana sarkin barna inban kirata katafilaba balama kakeson inkirata dariya sukayi gaba daya yayinda su munawwara ketayasu
Hankalinsune yadawo jin dariyarsu munawwara dasauri surbajo tajuyo ita Da alameen durkushewa tayi agurin tarufe fuskarta sabida kunyarsu daddy data kamata
Shiko alameen ko ajikinshi karasawa cikin falon yayi yana murmushi gaida iyayensa yayi cike da girmamawa suka amsa fuskarsu dauke da faraa
Daddy yace amunullahi zamu bata dakai shine kasamin ya jin kunyako maza kajata kubar nan Tunda kasa tanajin kunyarmu
Dariya sukayimata dukansu
.
mikewa yayi yaje inda take durkushe bejira komaiba yadauketa cak
Kuka tasamishi ita yasauketa Tana dukan bayanshi kokulata beyiba yawuce da ita dakin mommy
Kan gado yasauketa kuka take bilhaqqi da gaske ita wai yabata kunya
Kamota yayi yana fadin to sannu mekunya bakiji medaddy yacebane kinga so nagaskiya baa kunyar idon kowa nunashi ake aduk inda yakama kuma mu nan gidan baruwanmu da wannan kunyar taki muna rayuwane so simple
nande suka buge da romancing din juna
Kwankwasa kofar akayi suka bada izinin shigowa amal ce dauke da Yusuf yafara kuka
dasauri alameen yaamsheshi yasoma yimai wasa Dena Kukan yayi alameen yace that's good my resemble
Dariya surbajo tayi tace ah lallefa su resemble anji jiki
nima zanhaifo my resemble dinne ingata iko
se bayan laasar alameen yabar kaduna cike da kewar surbajo da yaronshi
itama surbajo kuka taitayi bayan yatafi sabida har ga Allah batason tanayin nisa da mijinta sabida bukatunsa
madam Aisha kuwa bakincikin abinda alameen yamata yasa takasa ko cin abinci aminanta tafadawa suko abun yamusu dadi Amman afili nunawa sukayi suna tausayinta harda cemata zasu dauki mataki takwantar da hankalinta
.
rayuwa tacigaba da tafiya inda har surbajo tayi arbain tambayar alameen tayi zata ruga ganin gida cewa yayi tabari yazo tukuna sesuje tare bayadda batayiba amma yaki har mommy tasa baki fafur yace sujira yazo tukuna shida kanshi ze kaisu abin yama surbajo zafi
tsawon shekara biyu da auransu bata taba zuwa gidaba Amman yanxu tace zata shine zece tajirashi
Kiranta alameen yayi yanamata gargadi akan karta sake tatafi seyazo ayko rufe ido tayi tanata fada hardacewa in akan babynkane kahanani zuwa asalina tozanbarmakashi agida inje nikadai danna fahimci kana gudun innaje dashi ruga ze cutu ne to ni kabarni inje tunda ni dama acan nataso maganganude marasa dadi tafadamasa
alameen runtse ido kawai yayi yana sauraronta ranshi namishi kuna
kashe wayar yayi yahiga tunani
tabbas surbajo tayi gaskiya beso taje da Yusuf rigar gudun yakamu da wani ciwon shiyasa beson taje sedashi to amma ay Tunda befadamataba bedace tafadamasa maganaba har haka
itama surbajo sebayan yakashe wayarne hankalinta yatashi tuno irin maganganun data fadamasa tabbas bata kyautaba kiranshi tashigayi tabashi hakuri Amman fafur yaki daukar wayar
tamasa text shima baamsa
.hankalinta tashi yayi tashiga rusa kuka har mommy tashigo dakin tasameta tambayarta abinda yafaru tayi bata boyemataba tafadamata abinda tayimasa murmushi mommy tayi tacr baki kyautabs surbajo Amman kibari zanmasa mgn konan gaba Karki sake yimasa irin haka kinjiko
sosai surbajo tagamsu da zancan mommy itade burinta abashi hkr
.
Waya mommy tadauka takira al-ameen,bayan sungaisa, hakuri tabashi akan abunda surbajo tamasa.
Godiya yayiwa mahaifiyartashi, sannan sukayi sallama bayan yatabbatarmata da yahakura.
Surbajo murna tayi dajin yahakuran, sabida duk abinda sukecewa taji don wayar a speaker take.itama godiya tayiwa mommy tare da alkawarin bazata kumaba.
Tundaga ranar,surbajo kotakirashi awaya,baya sakin jiki suyi hira kamarda, sede yatambayi lafiyar danshi shikenan.
Abun yanama surbajo zafi Dan bata Saba irin hakan dashiba.
.
Yauma kamar kullum,kiranshi tayi awaya suna gama gaisawa yafara kokarin kashe wayar,dasauri surbajo tace,
"Abban Yusuf Don girman Allah kayimin afuwa, nasan namaka laifi amma zuwa yanzu yadace kayimin afuwa kodan darajar mommy datasa baki please"
Karashe zancan tayi Tana kuka.
Al-ameen baze iya jure jin kukantaba,zuciyarshi zafi takeyi jin kukan surbajo akunnensa.dasauri yakashe water.
Surbajo kifewa tayi agurin Tana kuka,kukantane yatashi Yusuf dake baccinsa hankali kwance. Mika hannu tayi tadaukoshi tasamishi nono abaki yafara sha itakuma taci gaba da kukanta.
.
Al-ameen jiyayi gaba daya garin yaisheshi, dama next week yake saran zaa bashi hutu, Dan haka jiyayi kamar tayi tsuntsuwa yaje gareta yakeji.
Ranar jummaa dawuri yashirya yabar garin, Dan karfe takwas ta Safiya a kaduna tamasa, besanar Dakowa zuwanshiba Illa driver dinsa,kaitsaye gidan iyayensa yanusa, sunyi mamakin ganinsa,bayan yagaishesune yawuce dakin da madam take.
.
Tana kwance Tana kuka, yayinda yusuf keta bacci. karasawa yayi gurinta yazauna agefenta.
jin motsin mutum ne yasata fara goge hawayenta dasauri Dan tadauka mommy ce kosu munawwara.
Suman kwance tayi da ganinsa, fuskarta take mitsikewa Dan Tana zaton gizo yakemata
"kukan mekikeyi?
shuru tayi masa Tana goge hawayenta .
Kamota yayi yarungume,aykamar jira take ,rushemishi tayi dakuka Tana fadin
" haba dear,Ashe nangabama zaka iya rabuwa Dani har abada kenan,nace kayi hkr amma kaki Kayi, yakakeso inyi da raina?
.
Bakinsa yasa acikinnata, dan bayason maganar datakeyi, soyake yamantar da ita bacin ran,kuma dama yamata hakanne gudun karta samu kafar rainashi, tadunga fadamasa magana son ranta kamar Aisha.
surbajo jin bakinsa acikin bakinta yasa kukanta yatsaya, tuni gyaran da mommy taimata yafara ayki, dan sosai mommy take gyaratada magunguna masu kyau, shiyasa itama yana fara yimata kiss din, itama Tashiga maidarmishi da martani.
ganin suna neman wuce gurine yasa takwace kanta dakyar Tana maida numfashi.
shiko Al-ameen rasa yazeyi yayi, Dan gabadaya hankalinshi yagama tashi burinshi yakeba da matarshi.
.
Mikewa yayi yadauki Yusuf sannan yace mata
"dauko gyalenki mutafi gida"
surbajo jiki har Bari yake gurin neman gyalen, Dan harga Allah tagaji dazama gidan iyayensa,wajen watansu uku agidan.
jakar kayansu tajawo,yana gaba Tana biye dashi abaya har zuwa falo,boyewa tayi abayan Al-ameen, Dan abun da kunya,Amman bata da zabin dayawuce tabi mijinta.
gabadaya falon kallonsu kawai sukeyi,bakunya Al-ameen yace
"mu munwuce gida seda safenku"
dariya gabadaya falon akasa,itade surbajo Tana boye abayanshi tarufe fuska tamkar Amarya.
.
mommy tace "to Allah yabamu alkhairi shugaban marasa kunya,matar tazo wanka shine bazaka jira amaidatabako?
dariya yayi,sannan yace "mommy to aydama nine nakawota dakaina,kinga balaifibane danmuntafi kuma tare yanzu".
daddy dariya yayi sannan yace "baruwanki dasu, aminullahi kuje abinku Allah yatashemu Lfy".
Dagudu surbajo tafice afalon, mommy nacewa tatsaya suyi sallama, amma ina tuni tafice Dan batason Su hada ido da mommyn.
Al-ameen jakar kayan da surbajo tagudu tabari yaja da hannu daya, dayan hannun kuma yana dauke da Yusuf,yamusu sallama yafice yabarsu sunata faman tsokanarshi.
Amota yasameta,direbansa yasamasa jakar abaya, sannan yabude masa baya yashiga inda surbajo take,direban yazagayo yatada motar suka fice.
.
Seda taji anfara tafiya tadago fuskarta, Dan Tunda tafito take rufe da fuska. Murmushi tayi Tana kallon Al-ameen Wanda yadage dayiwa Yusuf wasa.dagowa yayi yakalleta sannan shima yayi dariya ,sannan yace,
"wallahi ko alabari bantaba cin Karo da mara kunyar mejego irinkiba.kubiyu kawai nasani, daga ke se indon kauye ta Ali nuhu, masu gudowa daga gida tunkamin amaidosu dakunan mazajensu .yafadi yana dariya.cuno bakinta tayi alamar shagwaba tace,
"au hakama zakaceminko? nagode .baka ma barni da kunyar su mommy ba, shine zaka soma yimin tsiya, ay gwanda ni akan indon kauyen, ni mijinane yaje yadaukoni,itako gudowa tayi,
Kuma ba laifinkabane, laifinane dana biyoka, Danhaka ni asaukeni Nakoma. Tafadi Tana shirin yin kuka.
Dasauri yarungumota tagefe, fadi yake,"kirufamin asiri my baby don Allah, inkika koma can kuma yakikeso inyi dawannan nauyin?
"kaje matarka tasaukemaka"
Tabashi amsa.
kara rukota yayi sannan yaradamata akunne," no baby wannan lodin nakine, Dan haka dole kece me saukeshi .
duka takaimasa nawasa hakade suketafaman raha a motar har suka iso gida
.
Suna isa gida,afalo suka tarar da uwargidan.ganinsu atare bakaramin mamaki yabataba,dan zatonta daga patakot din suke.
Sallama suka mata,amma bata samu damar amsawaba.
"daga ina kuma akuya da dantaure"?itace maganar aisha tafarko.
Amsa surbajo tabata dacewa
"daga yawon Barbara muke balama"
"kan bala'i,dan ubanki nice balamar ?wlh yau senayi maganinki agidannan shegiyar yarinya Mara kunya kawai"cewar Aisha Tana kokarin cakumo surbajon.
Dasauri surbajo taja baya,
"tace wai nufinki dambe zakiyi Dani,?haba wuce nan Wlh, toke inbanda abinki inban girma yanzuba seyaushe zangirma?ace har haihuwa biyu Amman bandena dambe da yar wrestling ba, kinga, rufamin asiri, akan tarbiyyar Dana nake ,ina gudun yataso yaga ina hada kashi dake yadauka abune mekyau,kema nasan kinayi ne sabida ko kashi me tauri baki taba yiba bare ace kinsan zafin haihuwa, Dan haka ni banida lokacinki nayi nan. Tana gama fadamata tajuya zata bar gurin.
Azafafe aisha tabi bayanta,dasauri Al-ameen yasha gabanta Wanda tun dazu tsaye kawai yake yana kallonsu,kokarin tureshi takeyi,Amman ina yafi gaban wannan rainin.tsawa yadakamata,
Sannan Yancey,
.
"is enough Aisha,i say is enough, yafadi cikin tsawa Wanda ba Aishan ba har surbajo seda ta tsorata, shiko Yusuf dake hannunshi, farkawa yayi agigice yana kuka.
surbajo dasauri taje taamshi danta ahannunshi,gudun kar yayarmata dashi garin fadan.
cigaba yayi da fadannasa,tainda yashiga batanan yake fitaba, Aisha ce takatseshi dacewa,
"dalla yaisa haka mijin tace, Tunda tariga data wanke tabaka kasha ay dole kazo kaina kana balai.surbajoce takatseta dacewa,
"lalle keko Aisha andade da baroki abaya,ayni nafi karfin nawanke nabashi yasha sede yasa bakinshi yasha.hala ke wankewar kikeyi shiyasa kika dauka kowama garane irinki. Tsaki tayi tawuce dakinta, tabarsu tsaye baki bude.
Aisha kuka tarushe dashi agurin,wai surbajo tamata gorin haihuwa,sosai take kuka,Dan bata taba jin ciwon rashin haihuwartaba se yau.
.
Al-ameen ko dakinshi yawuce,bebi takan kowaba, dan gaskiya abinda suke yafara kaishi bango, badama suhadu sesunyi fada,kuma laifin na aisha ne, Tunda ita take fara tsokanar surbajo. Ranshi yabaci sosai yau dinnan duk wata shaawar surbajon tagudu sabida bacin rai.
Wanka yayi yashirya, sannan yafice agidan,restaurant yanufa,yasiyo abinci ,sannan yadawo gidan.
tunshigar surbajo dakinta,gado tafara gyarawa, yayinda Yusuf ke goye abayanta ,bayan tagama gyaran gadon, kwantar da Yusuf tayi akai, sannan taci gaba dasauran ayyukan.
fes tagyara koina takunna turaren wuta,koina se kamshi yakeyi,kitchen tashiga taduba store taga komai akwai nabukata, refrigerator tabude taga awai nama Kala Kala duk sunyi kankara sabida rashin amfani dasu,
girki tashiga hadawa Wanda tasan Al-ameen naso ,se kamshi yake tashi, Tana gamawa,tajera kulolin abincin akan dinning table, sannan tanufi toilet tayi wanka,tana fitinanniyar tashirya acikin wasu ubansun English wears, tayi kyau sosai,barin turare tayiwa jikinta sannan tanufi dakin Al-ameen.
.
sallama tayi tatura kofar tashiga, fuskarta dauke da faraa,
Faraarce tagudu daga kan fuskartata,yayinda taci Karo da al-ameen zaune yanacin takeaway din dayasiyo dazu,
rai abace taje takwace abincin agabansa,dagowa yayi dasauri danyaga wacece,yawun bakinshine yakafe,sanda yay arba da amaryarsa wacce bata laifi kota wanke plasma da laptop.
itako Fara magana tayi Tana diddire kafa, kamarde yadda yara sukeyi inzasuyi rigima.
"haba dear, yanzu kamin adalci kenan?Tunda nadawo ban zaunaba, seda natabbatar nahada maka abinci, shine kaje kasiyo awaje ,salon kajamana zagi, ace babban mutum kamarka baa girkamasa abinda yakeso agidansa,kuka tamasa na shagwaba juyawa tayi zata bar dakin dasauri yakamota tafado jikinshi,tana cigaba da kukannata.
shiko Al-ameen mamakin kanshi ne yakamashi,ganin tun baaje koinaba yadena fushin, shida da cewa yayi seyayi wata bekulasuba.
rarrashin gimbiyarsa yashiga Yi,dakyar tahakura, sannan tace yataso suje suci abincin,ba musu yarukota suka nufi dakinta,
sun fito kenan, suka ci Karo da Aisha tafito cikin shirin fita anguwa, kallonsu tayi tawatsar tafice agidan.
.
Al-ameen kada kai kawai yayi, sabida kobaa fadamasaba, yasan gidan aminanta tanufa.
Janshi surbajo tayi,ganin yabi Aishan dakallo,
sunci abincin sun koshi,kuma abincin yamasa dadi, Dan dakyar yaiya hakura da abincin badan bakinshi yagajiba sedan cikinsa daya cika.
daganan duniyar maaurata suka fada,Al-ameen jiyayi kamar kanshi zejuye,sabida sabon test din dayaji game da ita.
bayan komai yanatsa, sunyi wanka,lokacin Yusuf yatashi, wanka tamasa tashiryashi taba Al-ameen shi yarike ,
Itakuma tanufi dakin Al-ameen din domin tagyara
0 comments:
Post a Comment