Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Sunday, September 24, 2017

BAKAR MACE Part 1-5

 September 24, 2017     BAKAR MACE 1-END     No comments   

BAKAR MACE Part 1
.
Haba mana Farouq try to undrstnd me mana! Why can't you open your eyes and see what i'm trying to tell you?? Nifa i'm not rediculing her, i just want you..... Farouq ne ya tsaida shi ta hanyar daura hannun sa bisa lips dinsa. Farouq yace Ishaq nifa idan ba xaka bani goyon baya ba akan wannan yarinyar toh wallahi ka gyale ni. Ishaq yace nikam banga abnda ka gani jikin wannan BAQAR MACEN BA! Gata BAQA ga Muni, kai nifa wallahi na rasa gane kan wannan yarinyar. Kuma ni abnda yafi bani haushi, yadda take da wani irin jan aji kamar wata mai kyau. Farouq juyowa yayi da manyan idanun sa, yace jan aji ay abu ne mai kyau. Duk macen da bata da jan aji ay ba mace bace. Ishaq dafa kafadar Farouq yayi, sannan yace Farouq dan Allah ka dubi kanka. Ka duba kaga dame Allah ya rage ka. Amma ka rasa wacce xaka ce kana so sai wannan BAQAR halittar. BAQAR MACE! Kafa duba kaga yadda mata masu class kyawawa suke sonka. Some of them are even crying for your love while some are begging. Amma duk baka ga wannan abun ba. Sai ka rasa inda xaka mace saiga BAQAR MACE. Farouq buge hannun Ishaq yayi daga kafadar sa. Sannan yace mata marar sa class dai, duk macen dake liqe ma namiji ay bata da class. Ishaq yace toh ay ba haramun bane, domin Annabin mu yace mace tana da right din da xata fadi ma wanda take so cewar tana son sa. Is just that wannan xamanin da muke ciki mutane sun maida abn wani abu daban. Farouq yace maganar ka gaskia ne, amma kaima kasan yanxu mace tace tana sonka saika raina ta. Kai nifa kada ka isheni da wasu surutun banxa. Kawai ka samo mani wata idea yadda xan samo kan Farida. Ishaq daria yayi sannan yace kai yanxu dan Allah ba xaka ji kunyar nuna ta cikin friends dinmu ba??
.
Ka dube kafa! Babu ta inda Allah ya rage maka kamala. Amma ka rasa.... Farouq yace kai dallah Malam rufe mani baki. Taya xanji kunyar nuna abnda nake so?? Idan kana tunanin xanji kunyar nuna Farida idan na aure ta. Toh wallahi kayi kuskure, domim idan akwai abnda nake qauna sosai toh Farida ce. Kuma babu abnda xai hanani nuna ta ga abokai na da duk wani wanda ya dace yasan ta. Idan ma kana tunanin nam toh garama ka daina. Ishaq yace yayi maka kyau, amma nidai.... Farouq yace my dear please kindly get out of my room! Kama hannun Ishaq yayi, saida ya fidda shi daga dakin sannan ya kulle qofar dakin ya koma hisa gado ya kwanta. Rufe idon sa keda wuya, ya fara tunanin Farida. Addu'a yake cikin ransa Allah yasa Farida ta fara sonsa. Kamar yadda shima yake sonta. Da wannan tunanin bacci yayi gaba dashi.
.
Farida ce xaune ita da Umman ta suna cin abnci! Bayan sun gama Farida ta kauda komai ta dawo wurin Umma ta xauna. Daura kanta tayi bisa qafar Umma yayin da Umma ta kira sunan ta..... Farida amsawa tayi, Umma ta shafa kanta tare da fadin. Farida ya kamata ki nutsu ki daina ma Farouq abnda kike masa. Nifa wallahi ina son yaron nan, yaro mai hankali ga nutsuwa. Amma ki tsaya kiyi ta ja masa aji, ki lura da abnda hausawa ke fada idan jan aji yayi yawa. Toh fa ajin tsinkewa yake. Dan haka ki daina masa abjda kike masa kada Allah ua jarrabe ki kema. Kifa duba kiga yaron nan kamar balarabe, Barakallahu! Amma ya tsaya ya nace akan shidai ke yake so. Ke kanki kinsan idan dan ta kyau ne da koh kadan Farouq baxai taba cewa tana sonki ba. Ke kanki kin san gaskia, Farouq baku ma dace dashi ba. Domin yayi miki nisa, kawai dai Allah ya dora mishi sonki. Toh Umma In Shaa Allahu xan gyara hali na. Amma wallahi.... Umma tace nidai ban son jin wata magana. Ki gyara halin ki! Ki gyara halin ki!! Ki gyara halin ki!!! Farida cewa tayi toh Umma, baxan sake yi masa abnda nake ba In Shaa Allahu. Umma tace toh shikenan Allah yayi miki albarka. Bayan sun gama maganar ne Farida tace Umma bari naje nayi wanka. Umma tace Allah yasa a fito lafia kedai Allah ya daura miki yawan wanka. Farida daria tayi ta wuce daki, bayan ta gama wankan ta. Ta shirya cikin wata atamfa riga da skirt! Kayan sunyi mata kyau ta sha uban jan baki. Abun ka ga
.
kwalliyar fuskar tata ba wani fice tayi ba. Duk da uban jan bakin da tasha . Sai qamshi ke tashi daga jikin ta, domin Farida akwai son qamshi. Har fatar jikin ta qamshi take ko ta saka turare koh bata saka ba. Ita Umma abn har mamaki yake bata. Wani lokaci kuma abn ya daure mata kai.

! Bayan ta dawo parlour ta xauna! Taji wayar ta na ringing. Tasan koh baa fadi mata ba tasan cewar Farouq ne. Umma kallon ta tayi sannan tace ba xaki dauki wayar bane koh yaya? Farida tace aa Umma dauka xanyi, Umma tace kedai jan aji yayi kyau dake. Daukar wayar tayi, yau da sauki domin ta saki fuskar ta. Gaishe dashi tayi, nan yake gaya mata cewar yana qofar gida. Ce mashi tayi ya shigo kasan cewar Abba ya hanata xance qofar gida. Bayan sun gama maganar ta kashe wayar, Umma tace toh saura ki kwada masa baqin hali. Farida daria tayi tace kai Umma bafa ni da Baqin hali kema kin sani. Umma tace toh ay Baqin hali kike kwadawa Farouq. Farida tace ay Umma baxan sake ba. Umma daki ta wuce yayin da Farida itama ta koma daki domin qara gyarawa. Duk da cewar babu abnda kwalliyar fuskar ta tayi. Amma saida ta sake feshe jikin ta da turare, sannan ta dauki gyalenta ta yafa. Saida taje kitchen ta dauki trey ta hada masa duk abnda ya dace sannan ta nufi parlourn baqi.
.
Da sallamar ta tashiga parlour, shi kadae ta tarar hakan yasa taji wani dadi. Domin dama bata son ganin Ishaq domin tasu bata xo daya. Da xaran yaxo tofa dama kafin ya tafi sai sunyi fada. Ta gaishe da Farouq cike da ladabi, domin yau ta saki fuskar ta. Farouq ganin smiling dinda yake afuskar Farida ba qaramin dadi yake ji ba. Dan ya lura da canjin da aka samu daga fuskar ta. Ya lura yau duk maganar da yayi mata cikin ruwan sanyi take maida masa sabanin yadda suka saba firar tasu. Farouq cikin jin dadi ya kalli Farida yace please Farida will you marry me?? Daria idan da sabo ta saba jin wannan kalmar daga bakin Farouq. Yanxu kam Farida rufe fuskar ta tayi sannan ta ruga da gudu ciikin gida. Farouq smiling yayi tare da fadin why the sudden changed from my Fari? Daga hannu yayi sama ya roqi Allah akan ya daura sa bisa Farida. Tashi yayi ya nufi parlour wajen Umma. Da sallama ya shiga, ya kuwa ci saa Umma tana xaune.
.
Waje ya samu kusa da qafar Umma ya xauna. Bayan ya gaishe ta sunyi fira kamar yadda suka saba. Farida ta fito parlour, abn ya daurewa Farouq kai daga shi har Umma. Dan bata taba xuwa parlour ba idan Farouq yana xaune da Umma. Yau kuwa gashi har tana dan saka musu baki cikin firar tasu. Ahankali take kai idonta kan Farouq. Cikin ranta take fadin, Allah yayi halitta, Umma dai ta lura da yadda Farida take satar kallon Farouq. Farouq shima tun bai lura ba, har takai sun saida suka hada ido da Farouq sau 2. Kunya ta kama Farida hakan yasa akaro na biyi da suka, hada ido saita ruga daki. Shi Farouq abn daria ya bashi, haka Umma!. Umma ce take ta qara kwantar masa da hankali! Aranar haka Farouq yabar gidan, cike da farin ciki! Driving yake amma hankalin sa yana kan Farida da yadda tayi behaving infront of him! Dadi yaji sosai harya qagara ya koma gida domin sanar da Ammi abnda yake faruwa.a
.
Farouq ne xaune gaban Umma sai labari yake bata akan yadda Farida ta canxa. Suna cikin wannan maganar Ishaq ya shigo. Da sallamar sa ya isa wajen Umma. Waje ya samu ya xauna bayan sun gaisa yaji labarin da Farouq yake bama Umma. Ishaq wani irin kallo yayi masa! Sannan yace Umma wannan yarinyar fa ashe bayan Munin ta har Aljanu ke gare ta. Umma tace Aljanu fa kace?? Farouq wani mugun kallo yayi masa tare da fadin Ishaq i don't want to see your face again in my whole life time. Please get out of dix house, i really don't know your problem, why are poking your nose into my affairs? Umma ce tace Farouq keep your mouth shut! Farouq komawa yayi ta xauna sannan yace Umma wallahi Ishaq haushi yake bani yanxu. Wai bai san babi kyau xuga cikim aure bane koh yaya? Kuma abnda yafi bani haushi wannan yarinyar babu abnda tayi masa. Infact bata da wani baqin hali wanda xaisa mutum yaqi auren ta.

.
Amma kawai yabi ya dame ni, kamar shi xai xauna mani da ita. Bayan dubun kushe ta da yake kuma yanxu yaxo mani da wata magana wai tana da aljanu. What's there dan tana da aljanu? Shi mai aljanu ba mutum bane? Koh ba haka Allah yake son ganin mutum ba? Look Ishaq macen da nake da ra'ayi xan aure not your choice. Dan haka kada ka sake kawo mano wata magana akan Farida. Ba Aljani ba koma miye In Shaa Allahi xan aure ta. Umma ce tace Farouq tashi ka shiga daga ciki and i don't want to hear a word from you again. Bai sake cewa komao ba ya fita kamar yadda Umma tace. Bayan ya fita Umma ta kalli Ishaq ta kira sunan sa. Umma tace Ishaq tunda Farouq Allah ya daura masa son wannan yarinyar bana son kana sage masa qafa. As his best friend kamata yayi ace kai kake bashi goyon baya.
.
Umma tace kuma kai waye ya fadi maka cewar Farida tana da Aljanu?? Ishaq yace wani dan anguwar sune yake fadi mani. That's why nace bari na fadi may be koh ya fasa auren nata. Umma tace ka taba ganin inda lalurar Aljanu ta hana aure?? Nidai ina ganin it will be better idan ka daina kushe Farida tunda itace Choice dinsa. Kasan it hurts a lot abnda mutum yake striving akan sa. Ya xamana ana sage masa guiwa! Bare yanxu daya samu yadan fara shawo kanta. Ishaq yace toh shikenan Umma In Shaa Allahu baxan sake ba. Dama gani nayi duk kyaun Farouq yace yana son wannan. Umma tace babu komai ka dai taya shi da addu'a Allah yasa ta xame masa abokiyar kwarai. Ishaq yace toh ameen Umma. Haka Umma tayi ta masa nasiha, daga qarshe suka yi sallama. Umma tunani take yi wanda ita addu'ar ta Allah yasa Farida taso Farouq kamar yadda yake sonta. Umma na cikin maganar Ibrahim ya shigo, ya xauna kusa da ita. Umma tace Auta harka dawo... Ibrahim yace eh Umma.... Umma tace toh kaje kaci abnci saika dawo. Miqewa yayi ya qara gaba, tare da cewa Umma ina big Brother? Umma tace yana daga ciki.......

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MIWASMITI Page 31 to 40
    Kuka ta Kuma saki gamida kamo hannushi ta matse a tsakiyar qirjinta Dan jin wani irin suka da yake mata Ga jiri da takeji gaba daya bata gan...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam