'YA'YA DA KUDI Page 6-10
.
Ana kiran sallah tayi d’akin su ta kwanta, kasanewan garin da sanyi lokacin hunturu ne. Addu’a tayi ta kwanta ga yunwar da ke addabarta. Haka har bacci b’arawo yayi awon gaba da ita. Dukun-kune take a yar ta barmata gefe kuma katifar Beeba ne yar k’arama wanda mutum d’aya zai d’auka. Bacci take amma sanyi ya dameta. Kiran Sallah asuba ya farkar da ita da kyar ta mik’e ta d’ibo ruwa a randa sai d’ari take yi. Alwala tayi ta koma d’aki tayi sallah bayan ta idar ta fara azkar d’in safiya wani bacci ne ya d’auketa kamar daga sama taji an shek’a mata ruwa mai sanyi nan take ta fara d’ari-d’ari, duk da haka Gwaggo bata kyaleta ba wani ruwan ta k’ara kwara mata. Barin da takeyi ya tsananta, Gwaggo tace”ke har kimsami daman da zaki kwanta bacin safe, uban wa ya baki dama?.
.
Malam yana karatun Al-qur’ani mai girma sai yaji kamar ana hayaniya jin maganan yayi yawa ya fito, yaji d’akin su Khadi ne da sauri ya sa kai cikin d’akin ganin Khadi ta fi luuuu zata fad’i yaje da sauri yana”Salati ya tare ta fad’a a hannunsa cikin k’unan rai ya d’ago ya kalli Gwaggo yace” in kin kasheta ae kin huta, kin san yarinya tana fama da Pneumonia kuma yayi mata yawa zaki kwara mata ruwan sanyi, haba hauwa anya kina tsoron Allah kuwa ae d’a ko ba kai ka haifeshi ba, bai kamata kina wula kanta ta ba.( Yan uwa mata kira gareku, kune jigon gida duk lokacin da gida yayi kyau kune, kusani Ya’ya da Dukiya, da Dabba ba’a mugun tar su. A rauwa ba kasan wanda zai taimake ba, sai kaga d’an da ka haifa da cikin ka wani lokacin bai jik’anka ba, wanda baka san zafin sa ba ya taimake ka kuma Ya’ya Rahmane dan Allah kuna kyautata ma yara ba sai naka ba ku d’auka duk d’aya suke a gunku). Gwaggo ko a jikinta tayi waje tana cewa”ni dai dole ta fito ta min aiki yau ko ta ji a jikinta. Malam ya kali Khadi ta idanunta suka kafe a sama da sauri ya d’auketa ya fita waje da ita. Beba da ta fito daga d’aki ganin halinda Adda ta ke ciki yasa tayi gun Malam da hanzari suka fita dake garin da sanyi da kyar suka samu mai Napep yace”Yaro Asibitin Murtala zaka kai mu, Malam da Beeba suka shigar da ita ciki suka d’au hanyar Asibitñ, sun d’anyi tafiya kafin suka iso asibitin, kud’in mai napep ya basa kafin ya d’auki Khadi suka shiga cikin Asibitin nurse suna hango su, suka tahoda sauri suka karb’eta. Emergency aka nufa da ita, Dr Abdul ke bakin aiki, da sauri “nurse suka sanar masa an kawo patient. Yace “ok! I’m coming now”. Bata dad’e da isa gun su Malam sai ga Dr Abdul nan ya iso.
.
Dubata ya soma yi yaga tana wani yanayi numfashinta na shirin d’aukewa, tai makon gaggawa aka bata cikin ikon Allah suka samu numfashinta ya dai-daita. Magunguna ya rubuta ya mika wa Malam yace”Baba gashi kaje Pharmacy ka sayo, in ka dawo ka bawa nurse sai ka same ni a office d’ina. Malam ya amsa da rawar jiki ya nufi pharmacy. Malam suna hira da Khadi Gwaggo ta fito wani sak’on kalon da Gwaggo ta aika ma Khadi, yasa ta mike ba sh’iri ta nufi kitchen ta d’aura girkin dare, sai da ta magama aiki Gwaggo tazo ta d’auke tukunyan d’akinta ta sh’iga dash’i duk abun da suke Malam na kalon su bai ce mata komai ba. A zuciyansa ya na mai jin-jina bak’in hali irin na Gwaggo, Malam ya mike ya fita waje zuwa gurin da suke d’aukan karatu. Rabi ce ta sh’igo tayi d’akinsu ta nufa ta dau naira goman Gwaggo tasa a wando ta fita waje, alawa ta siya sai da ta shanye kafin ta dawo gida. Gwaggo tazo d’aukan raina gomanta don a siyo mata sikari ta saka a surki, taga babu kud’i cike da masifa tazo ta danki Khadi tace”ke barauniya bani kud’i na da kika d’aukar min wato satan ma gadonsa kikayi a gun uwar ki. Khadi tace”Gwaggo ko d’akin ma ban sh’iga ba ina zaune a nan gurin fa. Gwaggo tace”oh! Sharri zan miki ko?. Ni a ya’ya na babu b’arawo ba mu gaji sata ba sai dai ko gun uwarki ne zuri’an barayi. Nan take Khadi ta soma hawaye jin takaicin yanda ake kiran iyayenta da suke kasa. Eyeh lalle kin samu gu dan ban dakaki ba shine kike kuka ko?. Gwaggo ta d’auko dorina tazane Khadi sai da taji hannu ta ya gaji tace”naira goman da kika d’auka a madadin abinciki na yau da kuma karin safiya. Gwaggo ta juya zata tafi sai ta dawo ta rike kunne Khadi tace”saura in Malam ya baki abunci ki karb’a ki gani ni dake yau a gidan nan. Ina son ana kiran Sallah ki sh’iga d’aki ban yarda ki leko waje ba, ina ga munanan kafarki a guri kin san sauran ta nufi d’aki. Taku a kullum mai k’aunar ku Malam ya sayi maganin dubu buyu da d’ari biyar ya nufo k’ofan Emergency ya mika ma nurse “Malam ya tambayi office d’in Dr Abdul nurse ce ta gwada masa, godiya ya mata nufi office d’in, da Sallaman sa ya tura k’ofar aka bashi izinin shigowa, Dr ya nuna masa gun zama Malam ya zauna. Sai da Dr ya gama yan rubuce-rubucen sa tukun ya d’ago da fuskansa tare da zare yar faran glass d’in da ke manne a kyakyawan fuskansa.
.
Malam ya msa sannu da aiki,Cikin girmamawa ya amsa, kali Malam yace”Baba jikin Khadeeja yayi tsanani sosai, mai yasa kuke barinta tana aiki da ruwan sanyi?, kuma tana zama a inda ke da sanyi, mai ya kawo hakan bacin na sha fad’a muku illar hakan amma kun kasa koyayewa. Malam da jikinsa yayi sanyi yace”Dr in Allah ya yarda wanan karon zamu kiyaye fatan mu kawai yanzu ta samu lfy. Dr Abdul ya kallesa sosai tabbas ya gano damuwa a cikin idonsa ga alamar magana a bakinsa, amma tunda bai fad’a ba “ni dai zanyi iya kokarina ganin na taimaka mata, ya Allah kabata lfy ameen. Ya kalli Malam yace”shikenan zaka iya tafiya amma akula mata da shan magani. Kai Malam ya d’aga masa alamar eh!. ‘Dakin da aka kwantar ta ya yashiga Beeba ya gani a bakin gadon ta zuba mata ido ga alamar tayi kuka sosai. Da Sallama ya shigo Beeba ta masa sannu ya amsa tare da zama a d’aya daga cikin plastic chairs d’in dake d’akin. Yace”Beeba ya jikin Addah ki?. tace” da sauki amma har yanzu bata tashi ba, bacci take ya kalli Khadi yace”Allah ya baki lfy, cikin zuciyar shi kuwa cewa yake” ya zama dole in d’auki mata ki akan Gwaggo bazai yiwu Khadi taci gaba da wahala haka ba. Ya mike ya nufi k’ofar Asibiti ya sayo musu abinci ya dawo ya kawo musu nan Beeba ta karya, shima sama- sama yaci abincin. Gwaggo ne tafito daga bayi ta na zuwa d’aki taga ba Beeba ta duba d’akin su Khadi taga bata nan d’akin Malam ma baya nan, Rabi ta tambaya tace”kee ina Beebalo?. Rabi ta kalli ina tace” ba sun fita da Malam ba naga ya riko Adda Khadi, tsaki tayi ta leko titi basa nan, nan takama bala’i yau zaizo ya sameta akan me zai fita mata da yarta don wata marar galihu, ita yarta na galihu, cikin gida ta koma sai surutu take ita d’aya.
,
WACECE KHADIJA?.
khadijatu~Kubrah shine asalin sunan Khadi ya d’aya tilo ga Malam Adam. Malam Adam haifafen garin kano cikin unguwan Dakata gurin fire service. Yayan Malam Ahmad ne Ubansu d’aya ne. Tun Malam Ahmad na karami Allah yayi rasuwa Mahaifiyar sa, ya koma hannun Maman Adam wato Kakan Khadi kenan, ta yi musu rikon tsakani da Allah har suka girma. Adam shiya fara yin Aure kasan cewan shine babba sun shekara da yawa da matar sa Balkisu Allah bai basu haihuwa ba, sai daga baya ta samu ciki ya zo mata da laulayi haka tayi ta fama har tazo haihuwa, ta kwana biyi tana na kuda, kafin rannan ukun har ana shirin shiga da ita operation ta haihu ko juyawa batayi ba Allah ya karbi abunsa. Malam Adam yayi kukan rashin matarsa mai hankali da kirki, watan ta shida da rasuwa Baba Ahmad yayi Aure, ya auri matar sa Hauwa amma auren dangi sukayi yar kwan war Maman sa ne,(danganta karsu ta gun uwa kenan da haiwa). Hauwa macece mai masifa tun tana budurwa ta ki jinin Balkisu Maman Khadi ganin yanda Ahmad ke zama a d’akinta hakan yana bata haushi sosai.
.
Cikin ikon Allah Khadi ta samu kulawa in ka ganta bazaka ce bata sha nono ba madara take sha bul-bul da ita ga ta da gashi ga kyau sosai, gwanin burgewa. Hauwa shekaranta 3 da Aure ta haifi yarta Beeba kar kuso kuga murna gunta, ta d’au son duniya ta d’aura ma Beeba, ta taso cikin kulawa ga hankali, in ka ganta sak Malam Ahmad kamar kakinta yayi, yarinya mai hankali da nutsuwa, jinin su ya had’u da Khadi tun Beeba na karama Khadi ke mata wasa komai ta samu zata kawo mata, amma in Gwaggo ta gani ta kwace ta yar ta daki Khadi, ana cikin haka wata ranan talata Malam Adam ya tashi da ciwon Ajali kwanasa biyar Allah ya karbi abunsa tun daga wannan rana Khadi ta dawo hannun Malam Ahmad da zama, nan Gwaggo ta samu daman galla za mata, sam bata kaunar ganin Khadi da Beeba sun zauna gu d’aya. Sam Gwaggo bata ‘kaunar ganin Khadik, da Beeba sun zauna gu d’aya. A kwai wani rana, da Khadi na wasa ma Beeba, Gwaggo na zuwa ta saka k’afarta ta shure Khadi, ta fad’i akan hannu ta, sai da ta gurd’e. Ranan ran Malam ba ‘karamin b’aci yayi ba, har sai da ya mari Gwaggo. Tun daga lokacin ta ‘kara tsanar Khadi, har zuwa girmanta, sam bata tausaya mata, duk aikin gidan Khadi keyi, Beeba kuwa bata son ganin Khadi cikin damuwa, in Gwaggo ta bata ma Khadi aiki, sai ta faki idon Gwaggo ta zo ta tayata su gama. Haka rayuwansu ya kasance dad’i da ba dad’i, Malam ya sanya su a Makaranta Khadi da Beeba suna ‘ko’kari, amma Rabee kam in ban da niman tsokana ba abunda take.
.
A hakan har Khadi ta kammala Secondary school d’inta, ta barsu Beeba yanzu ke karatu har islamiya an yaye ta. Matsalar ta d’aya ne sam bata kula saurayi, ko sunzo Gwaggo koran kare take musu, wai baa su nimi mayya ba. Tana lashe zuciyar mutane, har ta lashe na Malam da yarta Beeba. Hakan sam bai damun Khadi,ita kulum da Malam addu’a su, Allah ya shiryi Gwaggo yasa ta gane. Wankin Gwaggo dana Ya’yanta Khadi ke yi, in tafara sai ta gama, bata isa tace”ta gaji ba Gwaggo zata fara mata bala’i, wani lokacin, abimci ma hana ta take. Back to lbr. Khadi bata farka ba, sai kusan k’arfe sha biyu, sai da Malam ya ga tasamu ta ci abinci, kafin ya musu sallama, akan zaije shi gd ya dawo, Beeba ta mishi adawo lfy, ya fita. Yana isa gd, Gwaggo ta taso cikin masifa, tana tambayar sa ina ya kai mata yarta?. Ko dun bai damu da ita ba ne, yana son wannan mayyar ta lashe mata kurwa, kamar yarda uwarta ta lashe zuciyan mutane. Sai da ta gama sababinta Malam bai bi ta kanta ba, abincin sa ya d’auka, ya fita tare da tabarma da pillow. Gwaggo na ganin ya fita, gyale ta d’auko ta fara binsa a baya, har taga ya nufi Asibitin Murtala, itama tace”ma me Napep su bi Malam, haka ko akayi, har ya shiga cikin asibitin, ta bisa a baya, har ‘kofan Ward d’in da aka kwantar da Khadi. Ta na labe taga ya shiga d’akin bai dad’e ba ya fito, ya nufi wani guri a cikin asibitin. ta na shiga, gadajen ta rink’a bi, har ta iso na su Khadi, wani mugun kalo ta sakar ma Khadi,da ke jin gine da pillow, tace”mayya kin lashe zuciyar mijina da yata, to bakiyi sa’a ba, tana zuwa kusa da ita, ta wanke ta da kyakyawan mari, nan take yan d’akin suka yi mata caaa. Kafin ka ce me, guri ya d’auka da hayaniya.
.
Dr Abdul ne ya fito daga Ward d’in dake, kusa da na su Khadi, hannunsa rike da waya, da alamar waya yakeyi. A hankali ya ke tafiya, tun daga nesa ya ke jin hayaniya, yace”Dr Umar ina zuwa, naga kamar female ward na lfy, bai karasa ba ya iso gun hayaniya, yayi yawa, da kyar ya kutsa zuwa cikin gun, sam ya manta bai kashe wayar ba. Dr Umar shima bai kashe ba, dai-dai lokacin Malam ya iso gurin, ganin abunda ke faruwa ya soma jan Gwaggo da ta rufe Khadi da duka, sai zuba bala’in take. Dr Abdul ya iso yana “tan bayan lfy?. Gwaggo sai wani fin cikewa take, Malam ya d’auke ta da mari. Ta d’ago tana kalon Malam tace”ka mare ni a kan wannan banzan, mayyan mai kod’ade’en fuska. Ba zan yarda ba, sai na rama ta sake yin kan Khadi, itakam in banda kuka ita da Beeba sun rike juna. Dr Umar da ke jin duk abunda ya faro, duk da baya gurin amma ransa ya baci sosai, cikin zuciyarsa yace”duk da bansan maike faruwa ba amma wata irin macece haka?. Malam ya ransa ya baci mari ya sake wanke Gwaggo da shi, zafin yasa ta nutsu sosai, sai ta dawo ta fara jan Beeba, ita ko gadon ta rike, security aka kira suka fita da ita. Sai da guri ya lafa, Dr Abdul yace”Baba ka sameni a office d’ina ya fita, Malam ya nufi office d’in sa.
0 comments:
Post a Comment