DAGA TAIMAKO Page 1-5
.
Wata matashiyar buduruwa na hango a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba,"
.
Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata "bismillah ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"?
.
Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna daga taimako zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace.
,
Rik'e hanun juna sukayi suka nufi gidan gabansu in banda fad'uwa babu abinda yake,Dan Muhibba har wani gumi take,suna zuwa k'ofar gidan,Surayya tayi sauri ta koma bayan muhibba,muhibba ita kuma taja da baya da sauri ta juyo tana kallon surayya "Haba Dan Allah surayya mai yasa kike min haka ne ko bazaki rakani bane"?
.
Muhibba tace cikin rawar baki dan kiris take jira ta zuba aguje sabida tsananin tsoro,Surayya cewa tayi " kijiki da wani zance in bazan rakaki ba zan biyoki ne,kawai dai tsoro nakeji dan wlh Matan nan dak'yar in ba aljana bace kinga tsayinta kuwa",katseta Muhibba tayi da sauri tana k'ara ja da baya tace "haba Surayya ya kike kuma tsoratamu Dan Allah muje ki rakani insha Allahu ba aljana bace,muyi addua kafin mushiga ciki," na yarda zamu shiga ciki amma ke zakiyi gaba in biki abaya, Surayya tace tana k'ara lab'ewa abayan Muhibba,hanunta Muhibba ta rik'e gam, suka fara adduoi sai sun je zasu shiga sai su dawo aguje,sai da sukayi haka sau uku ana hud'u Muhibba ta d'aure suka shiga gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suna kallon band'akin,yana nan arufe kamar yanda yake,cikin tsananin tsoro Muhibba tace " baiwar Allah Dan Allah ki fito har yanzu baki gama bane karki cuceni daga taimako miki" motsi suka jiyo daga band'akin sukayi waje dagudu,
,.
Surayya kuwa cikin kiftawar ido ta shige gidanta tana k'ok'arin rufo k'ofa Muhibba ce tayi saurin shigewa tace " Surayya wai mai haka ne mai yasa
Kika gudu kika barni ai da kin tsaya munga fitowarta inkece kinsan bazan miki haka ba ko" d'aga wuya Surayya tayi tana kallo k'ofar gidan Muhibba tace "kiyi hak'uri Muhibba wlh tunda naga wanan matar na rasa nutsuwata,wlh wani irin tsoro nakeji kinga bari mu samu namiji ya shiga ya dubo mana ita" kuka Muhibba ta fashe dashi tana " innalillahi wa inna ilahi rajiun nashiga uku ni Ummi( sunan da iyayenta suke kiranta dashi) daga taimako na janyowa kaina masifa," tsayuwar lifan a k'ofar gidan Surayyan ne ya katse mata maganar da takeyi,Ayuba mijin Surayya ne ya dawo,da sauri Surayya tayi waje ta gayawa Mijinta abinda ya faru sallati yayi ya kalli Muhibba dake tsaye abakin k'ofa tana ta kuka,tambayarta yayi yanda akayi,ta kuma bashi labarin abinda ya faru, addu'a yayi aransa yace su biyoshi abaya,tsoron da sukeji ya d'an ragu sakamakon sun samu mai taimaka musu,Muhibba tana daga bayansa Surayya kuma tana daga bayanta ahaka suka shiga gidan,Band'akin ta nuna mishi ya nufi band'akin yana addu'a su kuma suka tsaya daga bakin k'ofa suna kallon band'akin,in banda fad'uwa babu abinda gaban muhibba keyi,"Auzibikalimati tamaaa
••••••
Ayuba ya karanta har karshe ya tura k'ofar ahankali tura k'ofar yayi gabad'aya yaga ba kowa,juyowa yayi ya kalli su Muhibba dake Neman sakin Fitsari a wando sabida tsananin tsoro,durk'ushewa tayi a lokacin data ga ba kowa a band'akin kuka ta fashe dashi tana nuna band'akin " Wlh Aljana ce ta shiga band'akin nan,ta ina ta fita,oooo ni Ummi daga taimako na Janyo wa kaina" Mijin Surayya rufo k'ofar band'akin yayi,yayi hanyar waje, suka bishi dasauri,Dan Surayya har tayi gaba,Ayuba tsayawa yayi yacewa Muhibba "ki kwantar da hankalinki babu kowa a gidanki watak'ila ma idonki ne yake gane miki kinga wata ta shiga band'akinki" dasauri Surayya ta katse shi tana "Wlh Ayuba Aljanace Nima naganta da idona Dan gidana tafara zuwa,Ina ganinta na rufe k'ofata Dan wlh Baka ganta ba kana ganinta kasan ba mutum bace,bansan tsautsayin daya sa Muhibba ta barta ta shigar mata gida ba"jikin Ayuban ne yayi sanyi daya ji abinda Surayya tace, Muhibba kuwa ta k'ara rushewa da kuka tana " Allah yasani Taimakonta nayi bansan Aljana bace ni yanzu mai zancewa Abdul,gashi ya kusa dawowa ko girki ban d'ora ba" Ayuba kwantar mata da hankali yafa yi yana "karki damu muhibba ai Allah yaga zuciyarki Taimako kika yi niyyar yi,Insha Allahu Allah bazai bata ikon cutar dake ba",juyawa yayi ya kalli Surayya dake zare ido yace mata "jeki rakata ta d'ora abincin lokaci na tafiya,", da sauri Surayya taja da baya "Ayuba wlh ni tsoro nakeji Dan baka ga matar bane" wani kallo ya watsa mata taja bakinta tayi shiru,"wuce ki rakata bana San shashanci ke kin isa ki ga aljana da idonki" "Nima fa ban d'ora girki ba"
.
"eee wuce kije zan d'ora mana ai Nima na iya girkin" Ayuba yace yana janyo hanunta,Muhibba ita dai tana tsaye,tana kallonsu,a zuciyarya kuma tana tunanin yanda zata kwashe da Abdulmajeed Dan yana da tsatsauran raayi Dan yasha yi mata warning akan kwashe kwashe,Dan lokacin da take amarya yaran makota haka suke cika mata gida,ita kuwa dayake ba ruwanta murna takeyi ta Shiga tsakiyarsu suyi ta hira sai da Abdulmajeed ya taka mata birki tukuna,dan ko kawayenta daina zuwa gidanta sukayi Dan sunce Mijinta baya San mutane,Yanzu idan ya dawo ta bashi labarin abinda yafaru batasan wane irin mataki zai d'auka akanta ba,"ki wuce mu tafi ki d'ora girkin" Surayya tace a lokacin da ta tsaya a gefen Muhibba,gaba Muhibba tayi Surayya ta bita abaya,sai da tafara lek'a band'akin taga a rufe yake tayi sauri ta shiga gidan,tana addu'a k ayan data goge tafara kwashewa ta kai d'aki ta nad'e tabarmar data shimfid'a tasa abayan k'ofa,ta rufo d'akin,Kitchen ta shiga da sauri ta kunna risho ta d'ora ruwa,duk abinda ta keyi idonta na kan band'akin Surayya dake tsaye abakin k'ofa itama band'akin take kallo Dan jira take taji motsi ta d'iba aguje,Muhibba ruwan da ta d'ora ko zafi bai yi ba ta wanke shinkafa ta zuba,Dan gabad'aya a tsorace take,Allahn daya taimaketa tun safe tayi miyarta,Salad da tumatir ta d'auko Dan ta yanka,Surayya motsi taji asaman kwanun gidan tayi waje da gudu,Muhibba wurgi tayi da wuk'a da salad d'in Hanunta itama tayi waje da gudu,atsakar gida ta Tarar da Surayya tana maida numfashi Ayuba dake k'ok'arin d'ora musu jellof d'in taliya na tambayarta mai ya faru,ce mishi tayi motsi taji asaman kwanu,tsaki yayi yace ta wuce su koma Muhibba ta gama girkin,k'in tafiya tayi atakaice sai da Ayuba ya rakasu ya tsaya abakin k'ofa,Muhibba tasamu ta gama abincin,aranar Dan turaren data ke yiwa gidan bata samu tayi ba,ballantana azo ga wankan da takeyi tayi kwalliya ta jira dawowar Abdulmajeed kamar yanda ta saba,gidan ta kulle bayan ta gama abincin ta tafi gidan Surayya Dan ta jira dawowar Abdulmajeed Dan bazata iya zama a gidan it a kad'ai ba, Dan taga alamar Surayya a takure take.
.
Ana kiraye kirayen Sallahr Magriba Abdulmajeed ya dawo,Muhibba fitowa tayi daga gidan Surayya Dan tagane k'arar Lifan d'inshi,binta yayi da kallo a lokacin daya ke sauk'owa daga lifan d'in,had'e rai yayi yace " ke kuma mai kike jeyi a gidan mutane da magriban nan,share tambayar daya yi mata tayi tace " Sannu da zuwa" "tambayarki nake mai kika je yi agidan mutane da magriban nan kinsan na hanaki shige shigen nan banaso," itama had'e rai tayi tace "
.
yanzun nan fa na shiga gidan abinci na kai mata dan batajin dadi" tsaki yayi yace "uwar San gwaninta ni bud'e min k'ofa na Shiga da machine d'ina,nufar k'ofar tayi gabanta na fad'uwa sai addu'oi takeyi a zuciyarta,Shigar da lifan d'in yayi ta bishi abaya,sai da yayi parking a tsakar gida,ya nufi inda generator yake ya tayar,Muhibba tunda suka shigo ta tsaya daga bakin k'ofa tana kallon Band'akin Dan gani take kamar matar tana ciki,Abdulmajeed ganin ta kame awaje d'aya ne yasa ya zuba mata ido, " keeeee" wani irin tsalle tayi ta nufeshi a firgice,"kallon mamaki ya bita dashi yace ", ke lafiyarki kuwa mai yake damunki?dasauri ta daidaita nutsuwarta dan bataso Yagane halin da take ciki,tace "bakomai mai kagani," binta ya k'arayi da kallo tunda daga sama har kasa,yace " Kin ganki fa da kayan dana fita nabarki sune ajikinki har yanzu,gidan ma wani iri ba kamshin daya saba well ke kika sani tunda kince ba komai,zuba min ruwa inyi wanka zafi nakeji" Abdulmajeed yace yana shiga d'akinsa,da Sauri tabi bayansa Dan wani irin tsoro ne ya rufeta dayace asa mishi ruwa a band'aki,Abdulmajeed juyawa yayi yana kallonta a lokacin da yake k'ok'arin cire rigar jikinsa, "wai bakiji mai nace bane ki zuba min ruwan zanyi wanka,wai yau Muhibba mai ke damunki ne?", juyawa tayi, tayi hanyar waje gabanta na mugun fad'uwa,adduoi taringa yi ta nufi band'akin Dan ta d'auko bokitin wanka, tura k'ofar tayi bakinta d'auke da addu'ar Shiga band'aki, wani irin razananan k'ara ta saki tayi baya da gudu sakamakon ganin rigar da matan nan ta sa atsaye,babu alamar mutum acikin rigar.
.
KUNA TARE DA NI MU CI GABA?
0 comments:
Post a Comment