Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Wednesday, October 25, 2017

JUWAIRIYYA Page 4

 October 25, 2017     JUWAIRIYYA 1-END     No comments   

JUWAIRIYYA Part 4
.
A falo Ju ta hadu da Mami da Ya Sagir suna hira. Mami tace wa ya taba min ke naga kina ta kumbura bakin nan na tsiwa. Ju tace Ya Rayyan ne ya koro ni, Mami a gabansa fa ya hauni da fada. Ya Sagir da bai gane me akeyi ba yace gaban wa am confused. Ya Rayyan daya shigo a lokacin yace gaban Lawal mai shago mana. Cikin fushi ya cigaba da kallon Ju yace wai ni waye ma ya baki izinin fita. Ya Sagir yace Mami Ju zance take yi ban sani ba. Mami taga yara zasu mata taron dangi tace kwana hudu kenan yana turowa kiranta ina hanawa dazu Hajja tace kada na sake hanata fita don dole tayi aure wata rana. Ya Sagir yace to ni zan mata magana ai su bata gama secondary ba. Ya Rayyan kwance akan gado yana kallon hotunan Amal cikin zuciyarsa yana dada tausayin halin data shiga dalilin auren su amma abinda yafi damunsa yadda Ju ke neman zama centre of his thoughts. Wai shine har yake fadawa wani shine mijin yarinyar nan mai tsiwa. Ya tashi ya dauko papers din jarabawar da aka yi mata farkon shigarta makaranta ya sha dariya. Karshe dai alwala yayi ya sallah tare dadewa yana addua musamman ga matarsa Amal.
.
  Lokacin WAEC ya matso su Ju an maida hankali ga karatu don ita bata da burin da ya wuce ta zama likitan ido ta taimakawa babanta. Ita da Yasmin sun dage da karatu cikin ikon Allah sunyi sun gama lafiya. Result din Jamb ne ya fara fitowa ita tana da 214 Yasmin kuma 221. Kowa ya tayasu murna. Kanwar Ju ma Nafisa wadda saboda demotion din da akayi mata tare suka gama itama ta sami 187.
***********************
  Hajja tasa 'ya'yanta maza a gaba tace shawara na ke son kawo muku wadda kuma zancen gaskiya da Umma muka fara yi don ita tazo da maganar. Abba yace Hajja mu ai umarni zaki bamu ba shawara ba. Tace hmm kaji shi bayan ku akan 'ya'yanku sai anbi a hankali.
Baba yayi dariya yace to muna sauraronki. Hajja ta gyara zama tace to ba wani abu bane akan yarinyar nan Juwairiyya ne, idan banyi kuskure ba ta kusa cika shekara hudu a gidan nan kuma duk tsahon lokacin nan a kula da yarmu tayi. Baba yace hakane nima kaina ina tunanin me zamuyi mu saka mata da alkhairi. Hajja maida kallonta ga Abba tace Bashir kana ganin zaka yarda Rayyan ya auri juwairiyya? Gaba dayansu basuyi tunanin jin wannan maganar ba. Hajja bata kula da yadda suka razana ba ta cigaba da cewa yarinyar nan taci kashi da fitsarin yayarta ba tare da ta taba bata rai ba. Allah Ya sani ina tausayin Habiba amma kuma har yanzu bata sami lafiya ba. Idan Juwairiyya tayi aure a wani gidan wa zata yarda ya taba ta. Duk kunsan yadda take kuka idan Juwairiyyan ta tafi makaranta. Abba yayi shiru sai kawai hawaye ya digo daga fuskarsa ya kalli dan uwansa yace Yaya abinda Hajja ta fada gaskiya ne. Shi kanshi Rayyan har kunyarsa nake ji ya gina gida ya kasa tarewa kullum sai dai yaje aiki ya dawo ga shekaru na karuwa. Yaya indai ka aminci to ni bani da matsala akan hadin nan. 
**************************
Kowa ya tashi da tunani a ransa amma Abba tsoronsa daya yadda Mami zata karbi maganar. Kwana biyu yana ta juya zancen a ransa karshe dai ya sami dama da ta kawo masa zancen taga alamun Sagir fa yana son Ju. Abba yace ya fada mata ne tace a'a naga alamu ne dai sai ya fada mata shawarar da Hajja ta kawo. Mami sai kuka wiwi kamar yarinya tace yanzu Abban Sagir haka Amal zata kare rayuwarta? Ni bana kin ya auri Ju domin yata ce amma misali Amal ta warke fa. Ni Asiya na shiga uku Abba yace haba yaushe zaki rinka maganar kin shiga uku bayan kinsan babu tsumi ko dabara idan ba abinda Allah Ya tsara ba. Kada muso kanmu mu cutar da wasu. Ki duba yadda yaron nan hatta da abincin da Amal take ci shi yake siya kuma baya tunanin wani aure ya hakura ya zauna da ita a haka. Kada muyi zalunci saboda son yarmu idan hakan alkhairi ne to muyi fatan Allah Ya tabbatar da faruwar sa. Daren ranar dai Abba da Mami kusan kwana suka yi sallah Allah maji rokon bawa sai Ya sassauta musu al amarin a zukatan su..
*************************
Yau Ju an tashi da farin ciki domin kuwa wudil zata ta kwana biyu. Sai da tazo tafiya da kyar aka rabata da Amal duk suna kuka Ju har waje tana jin muryar Amal tana kiranta. Ya Sagir ne zai kaita dasu Yasmin yan rakiya. Fauza ana exams a buk tana karanta Economics bata sami zuwa ba. Koda ta isa gida murna take taga Yaya Najib sarkin cin zali don ta kwana biyu basu hadu ba saboda yana aiki a kaduna. Ya yi musu gyara a gida harda fenti Ya Ismail kuma yana bautar kasa a Kwara state. Gida dai sai murna ake da zuwan Ju.
.
Washegari abin mamaki sai ga Abba da Baba da wani Kawun su kanin babansu. Bayan sun gaisa da Baba suka gabatar da abinda ya kawo su na son nemarwa Rayyan auren Ju. Baba yace Alhaji Bashir ban tari numfashinka ba amma yaron nan ba shine mijin Amal ba. Abba ya amsa da shine...sai baba yace to don Allah ku bani mintuna kadan ina zuwa. Sandarsa yasa ya shiga cikin gida ya nufi daki tunda yau da gobe tasa yana iya yawoba gidansa. A daki sautin kukan mama yaji yace Mariya me ya faru? Tace yanzu muka gama magana da yaya da kuma Dada akan abinda ya kawo su Alh. Baba yace to me kuka yanke tace ka amince don duk shawarar da suka bani kenan saboda tunda aka fara maganar auren nan idan ma munki to zasu nema masa wata karshenta ya rabu da Amal din. Kuka yaci karfinta tace ko kadan ba irin rayuwar danake wa Juwairiyya fata ba kenan amma wai mahaifiyarsa ce ta kawo shawarar kada mu aurar da ita a rabasu. Ta share hawaye tace kuna kasan ina tausayawa Yaya kafin najib ya kawo karfi duk dawainiyarsu ta karatu ta dauke mana. Fatana Allah Yasa abin nan ya kara mana zumunci. Yace amin nagode Mariya da dukkan abinda kuke yi min ke da yar uwarki. . Baba ya fita ya koma falon waje yace da bakinsa yaushe kuke son a daura auren kunga ni banyi wani shiri ba ko zaku bani lokaci. Abba yace haba Alhaji Idris juwairiyya ai yata ce don nafi ka morarta idan ka amince a yau zas daura auren. Bidaya Baba ya kira yace ta kira masa Najib da yazo ya tura shi kiran mal Yau da Liman da wasu yan uwansu da abokan arziki.
.
Bayan sallar laasar aka daura auren Rayyan Umar Tafida wanda wurin aikinsu aka tura shi Germany na sati biyu da Juwairiyya Idris Muhammad wadda ke daki suna hira da su Nafisa bata san me yake faruwa ba. Akwai rigima a gaba daga dukkan alamu  . Rayyan tsaye a reception yana ta kallon agogo ya gaji da jiran abokinsa Abbas wanda suka yi alkawarin haduwa a reception din hotel din da akayi musu masauki zasu je shopping domin sun gama abinda ya kawo a germany saura kwana biyu su koma gida nigeria. Da gudu Abbas ya fito daga elevator yana bashi hakuri. Rayyan sanye yake da wani ash din wando da riga light blue kayan sun masa kyau. Fuskar nan tasha gyara don shi baya aske gemu duka yana barin kadan wanda ya hade da gashin bakinsa. Da yake shi fari ne sai gashin yake masa kyau. Suna tafiya Abbas wanda tuni ya kawo kudin auren Fauza yace mu shiga kantin kayan matan can kasan mai hada lefe idonsa idon kayan mata. Rayyan yayi dariya to bana son rashin kunya dai kanwata ce. Dukkansu sunyi siyayya shi Rayyan banda Amal harda kannensa ya hada. Zai je wurin biyan kudi ya hangi wata farar night gown sleeveless wadda bazata wuce gwiwa ba kawai sai yayi imagining Ju a cikinta nan da nan yayi tsaki Abbas yace mutumina lfy. Rayyan wanda hannunsa har ya kai kan rigar yace yarinyar nan is getting under my skin and I don't like it. Abbas yace Ju ko. Cikin mamaki yace what do you mean..Abbas Yace ni kaina I cant remember when it started amma baka da zance sai na yarinyar nan tayi kaza ko tayi kaza kana fada kana wani lumshe ido. Rayyan ya kai masa duka yace to tunda ban ambaci suna ba ya akayi kasan da ita nake. Abbas yace sau biyu muna tare da kai zata wuce gaba daya hankalinka sai ya koma gareta. Ka siyo rigar baccin don nasan zata yi rana very sooooon. (fauza ta tsegunta masa auren da aka daura amma tace yayi shiru kada ya fada). Rayyan dai ya dauko irin rigar har biyu duk tsiyar da Abbas ke yi masa sai ya share kawai. Yau kwana biyu Ju tana aikin kuka ko abinci bata ci tunda Baba ya fada mata zancen auren da aka daura mata da Rayya.  
.
Mama tun tana bada hakuri har abin ya fara bata haushi tana fada. Baba ma yayi nasihar har ya fara fada shi da babu wanda yake jin kansa da Ju. Gidan Baba Idris dai ya zama kamar ana zaman makoki Ju data zo kwana biyu sai gashi tayi kwana takwas. A kwana na taran Ya Najib yasa Ju a gaba yana ta lallabata tayi hakuri don duk fadansa yana son kanwarsa kuma yana tausaya mata. Suna cikin magana sai kawai suka ji sallamar Mami da Umma . Ju tana kokarin tashi ta gudu daki sai taji an kira sunanta. Amal ce fuskarta duk hawaye da gudu Ju taje ta rungumo ta taja hannunta dakinsu Nafisa. Umma tace lallai ana fushi damu yau ko kallo bamu ishi Juwairiyya ba. A falo dai ta barsu tare da Mama suka shiga daki tace da Amal abinci tana mata nuni da baki Amal tace gyada kai alamar tana so, Ju ta tashi zata debo mata sai ta biyota har ta debo iyayensu dai suna kallo. Sai a lokacin Ju ta gaishesu bayan ta dan huce da fushin tace Mami ko kwalĺi baa sawa Yaya ba kuma wannan siket din bata jin dadin tafiya dashi ni bana sa mata. Umma tace to Juwairiyya idan baki amince da auren nan ba wace mace kike tunanin zata kula miki da yayarki kamar yadda kike yi. Kuma kina jin akwai mijin da zai yarda ki rinka zuwa kula da ita kullum? Ta cigaba da cewa mu da muka hada auren nan munyi ne bayan tunaninku duk ku ukun kuma da yardar Allah alkhairi muka kulla. Mami tace Ju kiyi hakuri da bamu baki hakkinki na sanar dake ba nayi tunanin bazaki amince bane. Ganin yadda suka taru suna lallaba ta sai taji ba dadi tayi murmushi ta kama hannun Amal suka koma dakin. Hakan ya tabbatar wa da iyayen nata zaa sami nasara a hankali.
************************
Al'amarin Ya Rayyan kuwa tun ranar da ya dawo ya sami labari a wurin iyayensa. Bayan duk iyayen sun taru a gaban Hajja sai Abba yace Rayyan bayan tafiyarka fa an daurawa Juwairiyya aure ai kafin ya kai karshe jikin Rayyan ya fara gumi yace Abba aure kuma? Dama tana da saurayi ne? Ko na dole akayi mata? Baba yace kai wannan irin tambayoyi haka da kai aka daura. Rayyan wani yanayi ya tsinci kansa shi bai gane ba murna ce ko kishiyata. Nan dai iyayen nasa suka yi masa bayanin komai tare da nasiha. A dakin Umma Rayyan yana nuna mata sayyayyar da yayiwa kowa tana yabawa tace banga ta amarya ba. Rayyan ya wani bata rai ai bansan da maganar ba. Ni an rinka daura min aure a haka kenan babu ko katin gayyata. Umma dai dariya ma take tace zaka iya bagarar da kowa banda ni ba tun yau nake lura da yadda ka damu da yarinyar nan ba sai ka rinka nuna halin ko in kula. Rashin zancen da take ma maigadi ya fada min kai kace duk wanda yazo nemanta ace tana da miji. Shiru yayi don yasan gaskiya ta fada. Can dai yace Umma ko ke kika bada shawarar auren tace eh don nafi kowa sanin meye a zuciyarka. Zai fita ya waigo to nagode tace ba godiya ba itama kayi mata tata tsarabar na gani.
************************* 
Sai da su Umma sukayi sallar magrib sannan sukayi shirin tafiya tare da Ju. Sai da ta dake sabon kuka Baba ya dai bata hakuri yace banda abinki ai ba yau zaa kaiki ba abinda ance sai bikin Fauza yazo nan da wata hudu. Kije Allah Yayi albarka. A soro sukayi kicibis da Ya Sagir da Nafisa suna zance tana ganinsu ta gudu shi kuma ya fita yana sosa keya. Umma tace almuri shiyasa kullum Juwairiyya zata zo kake cewa zaka kawota. Mami kuwa a ranta tace ashe naso yin kuskure ba yar yake so ba.
***********************
  Kan Amal ne a cinyar Ju tana yi mata tsifa washegarin da suka dawo a dakin Hajja su Yasmin suna ta tsokanar Ju wai tazama dauko wando ita kuma sai kumbura baki take taki kula su. Hajja tace zanci kaniyarku yaran nan. Suna haka Ya Rayyan yayi sallama duk suka yi shiru sai aka fara gaishe shi banda Ju data sunkuyar da kai sai hawaye Hajja tace su Yasmin su fita. Ta juya ga Juwairiyya tace baki gaishe da yayanki ba Ju still bata dago ba tace ina yini bai amsa ba ya dauko kitkat nan da nan Amal ta tafi wurinsa ya bare mata. Hajja tace bazaka amsa ba yace sai da kika rokar min fa Hajja to lafiya tunda kin rokar mata itama. Wannan zama akwai kallo

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MACIJINE SHI Page 31 to 40
    _________________Kai tsaye part ɗin nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai ƙamshi ke tashi,dakin fattu suka...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam