JUWAIRIYYA Part 7 (THE END)
.
Kamar muryar Fauza nake ji fa Ju ta ce da Samira. Sallamar suka sake ji Samira ta je ta bude kofa. Fauza ce tare da Yasmin da Nafisa. Su hudun rungume juna suka yi suna kuka. Bayan sun gama bata labarin duk abinda ya faru bayan tafiyarta harda rashin lafiyar Ya Rayyan ,Ju ta share hawaye tace ni ya zanyi ne da raina? Idan na aka bar auren nan zumunci sai ya tabu haka ma idan aka raba. Nafisa tace kiyi hakuri mu koma gidan Dada wallahi Mama ko abinci bata iya ci. Yasmin tace amma dai zaki zo duba Ya Rayyan ko. Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace in sha Allah. Yaya mun nemo Ju tana gidan Dada abinda Fauza ta radawa Rayyan kenan a kunne. Yayi kokarin tashi zaune amma jikinsa babu kwari yace kin tabbata ta gyada masa kai. Alhamdulillah yace da har Mami da Ya Sagir suka ji Mami tace me ya faru? Bai iya bata amsa ba sai Fauza ce tace Mami mun nemo Ju dazu mun kaita gidan Dada. Mama Allah lafiyata kalau abinda Ju ke ta fadawa mamanta kenan wadda tun shigowarsu gidan take ta juyata tana shafa mata jiki tare da tambayar babu inda ke miki ciwo ko. Dada tana daga gefe ta kalli Baba wanda sai murmushi yake tace kaga rashin kunya ko? Da sai ka zata bata son yarta she dai tana zuci.

*********************
Mami da Amal ne suka shigo gidan Dada kowa ya bisu da kallo. Ju ce tayi kokarin gaishe da Mami. Amal sai taje ta rike hannun kanwarta tace Ju kiyi hakuri da abinda ya faru nasan ban kyauta ba. Dama nasan bazan taba iya saka miki ba wannan sai Allah amma yanzu a gaban iyayenmu nayi miki alkawarin bazan taba zama silar mutuwar aurenki ba. Idan har akayi kokarin raba aurenki da Ya Rayyan to nima nayi alkawarin bazan taba zaman aure dashi ba. Iyayensu mata harma da Dada sai kuka. Mami tace Mariya kiyi hakuri naso na biyewa sharrin zuciya na watsa zumuncin mu. Itama Mama tace nima ki yafe min Yaya. Dada cikin murna tace Allah Yayi muku albarka. Baba Idris baki har kunne don farinciki yace Alhamdulillah tunda Allah Ya korar mana shedan Allah Ya kara hada kawunan mu. . Mami dai ta kawo shawarar a hada su duka ayi biki tare nan Baba yace a'a Haj Asiya ni tawa shawarar shine a fara bikin da Amal bayan shekara daya sai Juwairiyya ta tare hakan zaifi. Mami tace dama abinda Baba likita yace zai fada maka kenan idan ka yarda. Baba yace ni na amince. Allah Ya basu zaman lafiya. Ju da Amal da suke cikin daki suna jin hirar iyayen nasu. Amal tace Ju kin amince da hakan? Ju tace kai yaya ba dole ba Allah Yasa kafin nan ma kin haihu. Nan Amal tayi mata dundu a baya. Ju ta kwalla kara Mama tayi saurin cewa lafiya? Suna shiga suka gansu suna dariya. Har zuciyarta Mami taji dadi sosai yadda suka hade kansu. Ita kuwa Mama murde musu kunne tayi.
*******************
Yau dai falon Hajja alkhairi aka kulla aka tashi cikin farin ciki da annashuwa. Kamar yadda Baba ya fada Amal ce zata fara tarewa. Gaban Ju har faduwa yake ta tsaya kofar dakin da aka kwantar da Ya Rayyan. Amal ce ta fito tace to ni zan tafi nayi kanwata na bashi hakuri tare da tabbatar masa mun hada kanmu. Ju ta tsaya kamar an kafe ta don wata irin kunya take ji. Amal kuwa tura ta tayi tace anjima zan dawo sai mu tafi gida yanzu wurin neman venue zamu da Fauza da anti Habiba. Ju tana shiga dakin taji an rufe kofar an rungumeta ta baya. Tana kokarin gudu taji ya rada mata a kunne keep still. Tsayawa tayi kamar yadda ya umarceta. Sunyi kusan 5 mins a haka sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin gado. Duk kunya ta rufe Ju yace ba gaisuwa? Tayi saurin sauka tace ina yini ya jiki? Da sauki tunda kinga damar zuwa dubani. Ju bata ce komai ba ya cigaba da maganarsa da baki dawo ba da aurena zaki mutu ko ina zaki a duniya don bazan sake ki ba. Allah Ya sa na iya hakuri har sai an shekara kafin a kawoki.
.
Bata ce komai ba yana ta surutunsa shi kadai. Wai dama haka Ya Rayyan yake ta fada a zuci. Sai yayi ta wani shiru shiru kamar baya magana. A nan ta yini abinci ma ranar a plate daya suka ci don cewa yayi bazai ci ba idan bata sa hannu ba. Amal ta dawo tare da Fauza suka dan taba hira sannan suka tafi. Yau saura kwana uku bikin su Amal gida ya cika da 'yan uwa na nesa harda su Mama. Dinkunan amare duk iri daya akayi ita kuma Ju da su Yasmin da kannenta nasu dinkin iri daya. Mami wani special kulawa take bawa Ju. Ya Rayyan dai ba karamin farinciki yake ba domin yadda yaga matan nasa sun cigaba da rayuwa kamar yan uwa. . Anyi kamu a gidan Hajja ranar ba karamin kyau amaren sukayi ba. Itama Ju tayi kyau sosai tasha gwaggwaro ga kunshi mai kyau kafa da hannu. Washegari yini akayi sannan aka kai amare wadanda suka sha kukan rabuwa da gida. Ju a gayyar Fauza ta tafi daga nan suka shirya zuwa wurin dinner wadda Ya Rayyan da Abbas suka shirya. Kaya Bidaya tazo dasu a leda ta bawa Ju inji Rayyan. Wani lace ne white and purple anyi masa dinkin skirt da riga sai dankwalinsa, mayafi fari mai kyau da takalmi da jaka purple. Ju tana juya kayan tace ya akayi Yaya yasan size dina? Fauza wadda akeyi wa kwalliya tace ni na kai dinkin i hope yayi kyau. Shoe and bag kuwa zabinsa ne.
.
Ju tace to ankon mu dasu Yasmin fa. Fauza tayi dariya zaki fara sabawa miji akan anko ko? To dai an daura miki aure don haka dole abi Yaya da kannen yaya ma ta fada tana kanne mata ido. Taro ya kayatar sosai musamman shigowar angwayen da amaren su. Ju dake tsaye bayan amaren yau itama taji kishi a ranta amma tayi saurin kawar da abin ta hanyar neman tsari daga sharrin shedan. anyi taro an gama lafiya sunfito duk zasu tafi Abdul ne zai ja motar su Ju. Amal ce ta kula Ya Rayyan duk bashi da sukuni tace Yayana kaje kayi sallama da Ju mana zan jira ka. Harararta yayi kyaleta kawai mu tafi. Kaga dai ka fita nasan kana son zuwa am not that selfish fa. Waya yayi mata tana dauka yace karaso wurin mota ina jiranki. Tana zuwa tace Ya Amal kinyi kyau sosai Amal tace nagode bari na karbi sako wurin Yasmin. Tana fita ta share kwalla gaskiya kishi sai an daure. Ya Rayyan kallon Ju yayi yace sweet Ju Allah Ya kaimu ranar da zaki tare duk da bana jin zanyi hakurin shekara daya. A zuci tace amin amma ya kamata ku tafi haka sai da safe. Korata kike ko? Nagode kada ki kashe waya dai. Tana juya baya taji yace I love you tace me too a hankali sannan ta tafi. Ju ta fara karatunta a saa tana degree a Nursing sabon department din da aka bude a buk. Ya Rayyan kuwa kullum zai zo gida ya ganta. Ko kadan ta dena bari su hadu inda ba mutane don yana ganinta sai ya taba ko da hannunta ne. Duk dare kuma zai mata waya ko suyi chatting a whatsapp. . Ju an gama exams tun safe yau ta hada kaya zata tafi Wudil. Ya Rayyan yace zai kaita ya gaisa dasu Mama. Supermarket ya fara kaita yayi wa iyayenta siyayya sannan suka dau hanya. karatu ya kunna musu Ju ta fara rufe ido yace sweet Ju a hankali ta amsa da kyar don bacci ya fara daukarta. Parking yayi a gaba kadan da wani kauye yana kallonta. Jin alamar sun dena tafiya yasa ta farka yaya lafiya kuwa. Yace ina fa lafiya sweet Ju zata haukata ni. Ta zare idanu me nayi maka yace sace min zuciya mana cikin karamar murya. Tace Allah yaya ka fiye shagwaba haka ka koma magana kuma. Yace yarinya ban fara komai ba ma amma bari kiga kadan. Matso da fuskarsa yayi daf da tata tayi saurin rufe ido ya kama hannunta ya dora kan kirjinsa bude idonki tace a'a, musu da miji ko sai ta bude a hankali yace sweet Ju kinji yadda zuciyata ke bugawa akanki? Don Allah kice kina sona ko sau daya ne duk ya marairaice mata. Tausayi ya bata duk da tanajin kunya tace I love you Ya Ràyyan. Kissing din hannunta yayi yace kinga yadda ake shagwaba kasa mutum yayi abu ko baiyi niyya ba. Lallai yaya kayi min 1-0 amma zan rama. Ya ce eyye ramuwa akan miji tace eh. Dariya yayi suka tafi cikin nishadi. Sweet Ju ta Ya Rayyan
.
Yau watan Amal takwas da tarewa amma an hana Ju zuwa gidan sai ranar tarewarta. Sai dai kullum suna waya balle da Amal din ta sami ciki. A gajiye take tana cin abinci bayan ta dawo daga makaranta Mami ta shigo dakin ta zauna bakin gado tace Juwairiyya wane kalar curtain kike so a falo. Ju ta sunkuyar da kai kai Mami ni kowanne ma. Bikin ma ai akwai lokaci Mami tace mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka Juwairiyya ko kin manta ranar asabar zaa kai kayan yayanki Sagir gara ma hada bikin ke da Nafisan kawai. Ranar asabar ana ta shirye shiryen tafiya Wudil kai kaya Amal ma ta dage zata je Ya Rayyan ya hanata da kuka ta shigo gidan Umma na bata hakuri karshe dai dole aka tafi da ita. Zata shiga mota harda yi ma Ya Rayyan gwalo. Sunje Wudil lafiya sai a hanyar dawowa ne Ya Aliyu ya fada wani rami. Nan fa cikin Amal ya fara murdawa kafin su iso kano jini ya balle mata.

A asibiti Rayyan ya same su an samu jinin ya tsaya sai dai kuma Amal ta fara nakuda gashi cikin watansa bakwai. Hankalin kowa a tashe yake musamman Rayyan fita akayi aka barsu a gaban gadon ya durkusa ya rike mata hannu tana cizon lebe. Tace Sweet Yaya yana dago kai yaga ta rike kunnuwanta biyu. Nan hawayen da yake rikewa suka zubo tace kayi hakuri banbi umarnin ka ba daga yau dan ba kara. Da hawayen yayi murmushi yace sweet Amal ai ba fushi nayi ba. Allah Ya saukeki lafiya kuma Ya baki lafiya. Tace amin ka fita kuyi ta min addua yanzu zaa kaini dakin gashi,wani murmushin yayi ya ja mata hanci I want a beautiful baby like you Habiba. . Jikin Ju har rawa yake da taga yadda Amal ke gumi ta taba Mami tace haka ake haihuwar to ni na yafe. Mami tayi karfin halin murmushi eh mana Juwairiyya ke da zaki haifo mana dozen. Nurses biyu ne da wata doctor akan Amal ana ta kokarin ceton ranta dana abinda ke cikin. Da gudu nurse ta fito daga dakin Rayyan yana tambayar lafiya bata kula shi ba ta wuce. Jinin da Ju ta gani a jikin hand gloves din nurse din yasa ta fadi kasa a sume nan Rayyan ya kwasheta ya kaita wani dakin abin duniya yayi mada yawa. Tare da Baba nurse din ta dawo shima baiyi musu magana ba ya shige. Sunyi kusan minti talatin da shiga sai ga nurses sun fito kowacce da baby daya a hannunta. Umma da sauri tazo karba tace dama biyu ne nurse tace eh duk mata ne daya ce bata kwanta daidai ba shiyasa muka kira Baba. Baba shima ya fito yace a wuce da yara SCBU inda ake ajiye jarirai bakwaini ko marasa lafiya. Sai da Amal tayi kamar awa daya da haihuwa aka turo ta waje dakin hutu. Jikinta duk a mace ba kwari ana ta yi mata sannu. Ya Rayyan ta kalla harda harara tace daga wannan bazan kara ba. Hajja wadda bata zo asibitin ba sai da aka haihu tace haka kowa take fada sai kuma badi a ganta da wani. . Sai da kowa ya fita Ya Rayyan yace Sweet Amal sannu da aiki. Allah Ya baki lafiya Yayi miki albarka. Tace amin amma dai daga wannan sai an kwana biyu na barwa Ju. Dariya yayi sosai su Amal an horu fa wai anyi dinkin nan da kike tsoro yana fada yana cewa bari na gani ta doke masa hanne wallahi anyi baka ji ina ta kiranka ba? Yau Baba yaji zance kala kala don ni daga yau ya zama siriki na.
*******************
Sai bayan sati biyu aka sallami Amal da twins wadanda suka ci sunan Mami da Umma wato Asiya da Aisha. Mama ce tayi jinyarta a asibitin bayan anyi sallama ta koma wudil. Sai da sukayi wata daya sannan akayi taron suna Abba yana ta fada wai son bidiarsu yayi yawa ace suna bayan wata daya. Ju tana zaune bakin gado dauke da Minal ( Aisha) ita kuma Manal (Asiya) ta bacci sai Ya Rayyan ya shigo yace sweet Ju da babies dinta ina Sweet maijego? Ju tayi dariya tace wanka takeyi. Yauwa to dan matso kiji wata magana tace anya Yaya nifa tuni na dena trusting dinka. Ya kashe ido daya ke bakya cin ribar zance baki ma tsaya kinji me zan fada ba. Daga bayansu suka ji Amal tana cewa gulmata zaku yi ko? Ju tace Allah ban saurare shi ba Yaya. Dariya suka yi mata Ya Rayyan yace wai dama cewa zanyi itama ta haifi biyu next year ke kuma ki haifi gambo. Amal tace Sweet Yaya yace naam ta dauki takalmi tace sweetly go out tana fada ta bishi da takalmi ya fita Ju tana dariya. . Ance rana bata karya sai dai uwar 'ya taji kunya. Yau ne ake bikin Juwairyya da angonta Rayyan sai kuma Nafisa da angonta Sagir. Taro kam yayi kyau Mami tayi rawar gani sosai don a daki Mama ta sameta bayan an gama jeren Ju taga irin abinda sukayi mata cikin hawaye tace Yaya Allah Ya kara mana zumunci Ya basu zaman lafiya da juna. Babu abinda bakiyi wa Juwairiyya ba mu da muka haifeta ma gudunmawar mu a auren nan kadan ce. Mami tace Mariya kinsan dai kullum nasihar Baba gare mu kenan kafin ya rasu saboda haka muyi kokarin bawa yaranmu shawara mai kyau ta zaman lafiya. Mami ce ta bada shawarar ayi delaying komawar Amal da sati biyu saboda amarya Ju. Amal din bata musa ba don tasan kazantar da baka gani ba tsafta ce kuma ita ai Ju ta yarda ta bata watanni ma duk da cewa da aure a kanta. An kai amare dakunan su gidan Rayyan babba ne ba laifi domin kuwa banda falon tsakiya kowace mace harda shi tana da ciki da falo, harda kitchen da toilet. Sai dinning area a falon da wani toilet din guda daya da dakin baki. Gida dai yayi kyau sai fatan zaman lafiya.
*******************
Tunda Ya Rayyan ya fita raka baki da kawayen Ju cikinta ya fara kadawa. Samira tace mata ana shan wahala gashi Anti Hassana ta sata zama cikin bagaruwa wadda samiran tace kara matse mace takeyi. Yana taba kofar dakin ta sake jin cikinta na kuka ai nan da nan ta fada toilet na shiga uku tace a ranta. Ni kuma da gudawa na tare a gidan miji. Sai da ta gama fitowa ta gagara kawai tonu ranar data shigar masa toilet tayi a gida. Yana ta knocking taki magana can da ya gaji yace zan bude fa. Tana jin haka ta fara tube kaya tace ina zuwa wanka nake. Ba yadda zata yi haka watsawa kanta ruwan sanyi tana da rawar dari tayi alwala...da muguwar rawa gwamma kin tashi. A zaune kan gado ta sameshi yace ana kawo amare sunyi wanka ke daga zuwa zaki karar mana da ruwa. Gabanta ya fadi ba dai yaji tana flushing ba. Ya cigaba to kazamar amarya by the way akwai ruwan zafi ma kuwa? Ga sanyi ya fara zuwa. Sai ta basar ni zafi nake ji shiyasa nayi. Yace to zo na shafa miki mai tace ai zafin dai nake ji amma yanzu da gaske take tunda ya shigo wani gumi ya karyo mata. To dai duk wayon amarya...........

******************
Amal ta fito daga kitchen ta tarar da Ju tayi tagumi a falo tana goye da Manal. Amal tace Ju lafiya kuwa ko result ya fito ne nasanki da zulumi kije ki duba kawai. Ju ta share kwallar data fito mata Amal hankalinta ya kara tashi sai taje ta yiwa Ya Rayyan waya. Bai dade ba ya iso ya dauki Minal dake hannun Amal. Yace lafiya sweet Amal tace tambayi Ju sai sharar kwalla take. Yace sweet Ju ya akayi bata kulashi ba ta tashi ta tafi daki. Amal ta ce Yaya bita i think something is wrong. Sweet Ju dina wa ya taba ki cikin kuka tace tunda nazo gidan nan wata uku banyi period ba kullum jiransa nake. Yanzu idan ciki ne dani haka zanyi irin na Ya Amal? Da kyar fa ta rinka tafiya gashi harda dinki. Fita yayi ya kira Amal suka rinka mata dariya Amal tace kin fiye tsoro Ju to sauke goyon nan daga yau an yafe miki kada ki matse musu kanne. . Ju ce a labor room tana ta kiraye kirayen neman taimako. Idan tayi adduar sai ta fara kiran Mami da Mama. Amal har kuka tayi don tace ita bazata taba manta ciwon ba. Kusan awarta biyu a ciki ta haifo katon jaririnta ana kokarin yanke cibiya tace wa nurse din anyi min kari ne nurse tace eh amma ba yawa uku ne Ju tace a garinku uky ba yawa ko. ta ce na ma dena kiranka sweet Yaya tana fada tana kuka. Sister Rabi wato nurse din tace maigidan ne ko? Ai daga yau ki kira sunansa kawai. A haka aka gama aka fito da ita. . Rayyan dai ba karamin dadi yaji ba. Yaro kamar shi yayi yakinsa. Amal tace Ju yaya kika ji akwai zafi... hmmm Yaya ke dai bari sai godiyar Allah gashi nasha dinki. Ranar suna yaro yaci suna Idris abinda Ju bata zata ba. Ba karamin farinciki tayi ba tace Sweet Yaya ka fadi duk abinda kake so tukwici banda haihuwa next year. Ya rungume ta sannan ya rada mata a kunne ni ke nake so da dan bakin tsiwar nan ya fada yana shafa mata lips.
*****************
Minal da Manal ke rike hannun Baba karami wai yayi tata-ta Amal tace kaji iyayin yaran nan ko yaushe tasu kafar ta gama mikewa Ya Rayyan yace ai gara duk su mike tunda akwai wasu a hanya yana kallon cikinsu ita da Ju. Duk dariya suke Amal tace ni dai daga wannan na dena itama Ju tace ai nima haka. Ya Rayyan yace to sweet matana ai kunsan akwai fili a gidan nan sai na karo biyu. Tare suka rufe masa baki Amal tace Sweet yaya sai sweet Ju ita kuma Ju tace da Sweet Yaya Amal. Ya juya hagu da dama ya kare musu kallo ga yaransa suna wasa yace Allah Ya bamu zaman lafiya da zuria dayyiba. Tare suka amsa da amin.
.
ALHAMDULLAH
Copied By
Abdullahi Yahaya Saad (AYS)
Dandalin Ays
Hausa Novel
Dandalin Nishadi
.
ALHAMDULLAH
Copied By
Abdullahi Yahaya Saad (AYS)
Dandalin Ays
Hausa Novel
Dandalin Nishadi
Dandalin Hikayoyi Da Hausa Novels
.
CALL or SMS
+2347066508080
.
WHATSAPP NO:
+2347066656752
.
CALL or SMS
+2347066508080
.
WHATSAPP NO:
+2347066656752
0 comments:
Post a Comment