HIBBAH Part 11-15
.
Lokacin Ummah tayi shirin tafiya k'auyensu don duba mahaifiyarta ba lfy, kwana biyu da tafiyarta matar Baffah tazo ta d'aukeni Wai idan Ummanah ta dawo zata dawo dani Lokacin dana koma gidan da zama ba laifi ina samun kulawa duk inda zata tare muke zuwa kullum cikin ado nake. Lokacin da Umma ta dawo bata taga ana kula dani bata nemi indawo garetaba Tunda taga banda wata matsala. Kud'in data kaima aminin mijinta dubu talatin da biyar ya cika dubu biyar yazama arba'in yasamusu gida Saidai unguwar ba mutane sosai kuma yawancinsu ba musulmai bane, tace bazasu koma yanzunba sai wajen ya cika da mutane,tasami Kawu Usman akan tanaso ta nemi gidan haya ta koma sabida nauyi yayi yawa a kanshi, ba yadda baiyiba da ita akan ta hakura taci gaba da zama Amma taki tace "gara yaje ko wankin kud'i da wanke_wanke zatayi don rik'e yaranta" haka ya hakura ta nemi gidan haya a unguwar Dutsen Tanshi, ta kwashi yaranta suka koma chan da zama. Bayan komawarsu tasamama Sadeeq wajen gyaran mashin idan yadawo makarantar boko yakanje wajen gyaranshi da yammaci kuma su tafi Islamiya, ita kuma tana d'an sana'arta tana samin abunda zasusa abaka.
*YARAYUWAR HIBBAH YAKE CIKI*
.
Tsawon wata biyu *HIBBAH* nashan gata ashe duk kiwonta suke daga baya komai ya chanza ta dawo tamkar baiwa, itake share share daga d'akuna har cikin gida ga lodin wanke_wanke ga aika kamar me duk nisan aika ita kezuwa ga yaransu ba abunda suke akatawa. Umma tana kokari sosai wajen kula da yaranta da basu tarbiya wani lokacin abunda zasucima gagararsu take, yadda Allah ya taimakesu mutanen dasuke hayar sunada kirki suna d'an taimaka musu.
.
Lokacin da yara suka sami hutu duk ta tattarasu suka tafi kyauye hutu, sanda taje taga sauyi sosai wajen mahaifinta, abun ya mugun bata mamaki Amma sam bata nunaba, bayan dare yayi sun ke'be da mahaifiyarta take tambayarta meke faruwa taga mugun sauyi gurin mahaifinta. Nan take gayamata sharrin da kishiyoyinta suka mata "iyayenkine suka sami Babanku Wai ninama yaransu asiri shiyasa sukaki auruwa, Tunda ga nawa yara mata uku sunyi aure don haka dole inje in karya asirindana na musu, namasu rantsuwar 'ba sanin gurin wani mai asiriba balle har inje in musu, munyi rikici sosai har maigari saida yashiga zancen tukunna nasamu sukuni." "Lallai mama kina cikin ukuba" "Humm! "kedai bari Allah ne kawai zai fiddani, domin yanzu zaman rashin y'anci nake a gidannan, ace Tunda yarantarmu bamuyi hakanba da mahaifinku saida tsufa yazo mana, danasa abun araina Amma daga baya na cire don nasan bayin kanshibaba k'ullaliya akamai." "Amma wannan abun da tashin hankali, ina tunanin baba yaje dahar zai zauna mata su shiryama wannan kullin? Allah tona asirinsu kekuma yakara miki hakuri da juriya." "Ameen" Sundau lokaci mai tsawo suna hirarsu daga baya suka kwanta. *Washe gari* Bayan umma taje gaida mahaifinta da k'ar ya amsa yana cin magani, hakadai ta bashi tsarabar data kawomai, shaddace yadi biyar da takalmi da hula ko kallonsu baiba yace ajiye acan "idan kin karya kizo zamuyi magana" "toh" Saidatabi kowani d'aki ta gaidasu har makwabtansu duk tashiga ta gaidasu sanda ta dawo tasamu ancikasu da abun karyawa, bayan tad'an taba ta nufi d'akin mahaifin nata, yace "takoma ta kira mahaifiyarta yanason ganinsu" Juyawa tayi taje ta kirata sannan suka dawo, gyaran murya yayi sannan yafara magana "Hadiza! Saida Umma taji wani iri don baisaba kiranta da sunantaba kasancewar itace d'iyarshi ta fari, " Naam baba" Inaso yaran dake hannunki ki maidasu wa dangin mahaifinsu don anfara kawomin korafin kinabin maza acan, Atare Umma da mahaifiyarta sukad'au salati INNALILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJI'U
.
Daga Mama har Umma kuka kawai sukayi, Wai yau mahaifintane da kanshi yake gayamata tanabin maza, yau Mahaifintane kece tana zina, mahaifindaya bata tarbiya tundaga tsumman goyonta har yazuwa yanzu Amma shike mata wannan mummunan zato. _innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un_ wannan wacce irin jarabawar rayuwace take shirin fuskanta. Haka yagama maganganunshi wani zancenma dagaji had'ine, saida yagama tsaf sannan ya sallamesu. Abun mamaki sukagani lokacin da suka fito daga d'akin Matan Baban Umma su biyu suna la'be agefen k'ofar sai murna suka ga dukkan alamu sunji me akace. Wucesu kawai sukayi aiko Umma suna bada baya suka kwasheda dariya sukace "kad'an kuka gani" Mama tace "ALLAH yafiku dashi muka dogara." Wunin ranar Umma a d'aki tayishi don data fito za'a mata habaici. *
.
*CIKIN DARE* Ummane da Mama ke magana Mama tace "Saidai ki hakuri don yanzun saikin toshe kunnenki don zakisha maganganu, tunda kina zaman gdn hayane ba tare da wani nakira don Allah idan kinkoma kiyi k'ok'arin fidda miji cikin manemanki ki aure hakan zaisa ki fita zargi. " Nifa ba aurenne bansoba wanda zai rik'eni da yarana hud'u shine abun tunani tunda kinga duk dagin mahaifinsu ba wanda yakuma waiwayansu badon kuma basunan ba suna raye kuma dukkansu sunada rufin asiri daida gwargwado. " " kidainasa damuwarsu aranki kedai ki kula da yaranki koda wasa ban yarda kibasu yarankiba" "Insha Allahu zan sadauk'ar da rayuwata don kula dasu, ran Monday insha Allah zamu koma don zamanmu zai zame miki 'bacin rai tunda wunin yau bak'ak'en maganganu kawai suke jifarki dashi a dalilina" "Allah yakaimu gobe asabar da lahadi saiki zazzaga gidajen y'an' uwa" Saida sukasha hirarsu sannan sukayi bacci dama yaran sun jima da bacci. *Washe gari* Umma taje ta gaida mahaifinta sannan tabiya d'akin matan Baban nata biyu ta gaidasu da kyar suka amsa gaisuwar, yaranma sunje sungaida kowa, wanka sukayi sukafice ziyara gidan y'an'uwa. Basu suka dawoba saidare suka dawo gida, washe garima haka suka sake ficewa Saidai yau da wuri suka dawo don shirye_shiryen tafiya. 'Dakin Mama cike yake da kayan abinci irinsu Wake, gyad'a, gero, dawa, masara, bushashshen ku'baiwa, Kuka, daddawa, shinkafa, tsintsiya duk mutunene suka turo musu dashi a hakanma harda basu hak'uri.
.
Da daddare saida Umma tabari kowa ya rufe k'ofa ta nufi d'akin Baba ahankali ta tura k'ofar tareda sallama tashiga zaune yake kan kujera yana saurarar Radi'o amsa sallamar yayi tare da fad'in "lafiya da darennan" "lafiya lau Baba. " waja tasamu ta zauna tafara magana "nazone dama inbaka hak'uri kan abunda ake fad'a game dani, nasan sharri akamin kuma kowaye nabarshi da Allah. Da sannu Allah zaimin sakayya, nayi mamakin yarda da kayi akan maganar kafi kowa sanin wace ceni, kafikowa sanin irin tarbiyar da kamin, tunda yarintana banyi Zinaba saida girma yazomin ribar mezanci, bayan nasan girman zunubi irinna mazaunai. Tayaya zanciyar da yarana da haram bayan nasa dukkan jikin da aka raimeshi da haram bazai shiga Aljannahba."kukane yaci k'arfinta tace "gobe insha Allah zamu koma ina mai neman afwarka ka gafarceni Insha Allahu dana koma zanyi Aure domin kare kaina da zargi." batajira amsarshiba ta tashi tayi gaba shikam yayi mutuwar zaune tana fitowa taga kishiyar Mama mak'ale da alama taji duk abunda tace, wucewa tayi tare damata addu'ar shiriya ita kuma ta shige d'akin Baba. ~
.
*WASHE GARI* Umma sungama shirin tafiya zuwa k'arfe takwas motarsu zai tashi, yanzu wajen karfe takwas da minti hamsin tana jiran Baba ya dawo suyi sallama amma bashi ba labarinshi, tun asuba daya fita sallah bai dawoba, k'arshe dai tafiya sukayi ba tareda sallamabah. _
.
Su Ummah Allah kiyaye hanya, yabada hak'uri_ Tun dawowarsu Umma taje taga Hibbah takuma basu tsarabarsu, bata kuma komawa gidanba, don randa ta koma gida tayi kuka sosai yadda taga Hibbah ta dawo, duk wani aikin gidan ita keyi hatta gjrkin gidan itace bata da wani lokacin kanta, da zarar ta tashi tun asuba tayi sallah zata fara sharan gida tana gamawa ta fara abun karyawa sai ta sallami kowa sau tari haka take tafiya makaranta ba tare data karyaba, tana aji biyar na primary Allah yabata baiwar ilmi na boko da arabic. _(ba doleba tunda Umma da Abba ba dama wajen ilmi ta kowani fanni)_ Haka rayuwa tacigaba da tafiya wani lokacin asamu wani lokacin arasa, Umma sun daidaita da wani bawan Allah yanada yara Uku biyu mata d'aya na miji, Allah yama mahaifiyarsu rasuwa. Lokacin da suka daidai tamai maganar yaranta guda hud'u yace "ba komai d'a na kowane." Lokacin da sukayi aure komai yana tafiya daidai daga baya kuma halinshi na asali ya nuna, ba abinci, sutura, duk wani hak'k'i daya rataya kan miji baya baya badawa, da Umma taga haka tuni ta ware ta fara wankin kud'i shima ba kullum ake samuba gashi lokacin tana da ciki, haka suke rayuwa idan tasamu tayi wankau kud'i suci abinci inbabu su hak'ura daga baya ya tsiri sabon salon iskanci idan yadawo aiki saiya siyo abinci yashige d'aki ya k'ira yaranshi suci, da Umma ta fuskanci hakan bata nuna damuwartaba don tasan ba wanda zai iya mata d'awainiya da yaranta tunda dangin ubansuma sun gaza balle wanda bai had'a jini da suba.
.
Haka Umma ta ware tana neman abun rufin asirinsu ita da yaranta.
0 comments:
Post a Comment