Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Tuesday, November 14, 2017

HIBBAH Part 16-20 (THE END)

 November 14, 2017     HIBBAH 1-END     No comments   

HIBBA Part 16-20 (THE END)
.
Umma ta haifin d'anta k'ato duk suna cikin k'oshin lafiya, yaci sunan Muktar.   Muna zaune mukaga Baffa Kalla sunshigo da wasu manyan mutane su uku da takardu ahannunsu, yanunamusu ko ina na gidan da muke ciki suka fita, mudai anbarmu da tunanin ko lfy? Ohh.  Bayan ya rakasu ya dawo yake fadima matan nashi cewar "yasai da gidan kud'i yasai wani gida a karofi nanda wata biyu zasu tashi idan angama gyaran gidan." acewarshi "yagaji da yadda mutanen wannan unguwar suke damunshi da k'ananun magana akan yakasa rik'e amanar y'ay'an d'an'uwananshi."   Umma kam zama sam yak'i dad'i gashi yanzu bata samun aikinyi sai ayi kwanaki basu sami abunda zasu sa'a bakin salatiba daga k'arshe dai ahaka auren ya rabu, ga yara har biyar awajenta tunda auren ya k'are mijin ya kwashi yaranshi suka k'ara gaba bata kumajin d'uriyarshiba, dama kuma zaman gidan haka suke, mutanen daya gwada matasu amatsayin y'an'uwanshi ashe duk k'aryane zaman mutunci kawai ya had'asu, dole tanemi alfarma wajen masu gidan sumata hak'uri zasu gyara gidansu kafin kud'in hayar ya k'are.   Su Hibbah ankoma sabuwar unguwa yau kusan watansu uku da dawowa, saidai gidan dasuke yanzu bawani fasali d'akunane guda hud'u ciki d'ai_d'ai, sai bayan gida da kitchen, sai filin tsakar gida wanda yaci a d'aga d'akuna ciki da falo da bayan gida guda biyu awajen. 

HIBBATULLAH!
HIBBATULLAH! 
HIBBATULLAH!  
Sau uku tana k'wala mata kira a rikice ta fito daga wankan da take jiki duk kumfa ta d'auro zani ta fito, da sauri ta isa k'ofar d'akin ta durk'usa gabanta na dukan tara tara.  Tace "gani Mama."  Wani kallo ta mata saidata kusa zama cikin masifa tace "rami kika shigane da nake k'iranki bazaki amsaba?"   "Ahh! ki hakuri wanka nashiga"   "kin kad'amana miyanne dazaki shiga wani wanka?"
.
  "bai karasa nuna bane shiyasa nashiga wankan, naga lokacin islamiya yayi su Ahmad suntafi tun d'azun"  "ina ruwana? Idan kinga kinje Islamiya yau toh kin gama miya kin d'auramana ruwan tuwo, idan kin dawo ki k'arasa don kinsan ko wuta bamai iza miki" Kwallace ta taru a idonta don tasan yauma saitasha dukan latti, haka ta wuce kitchen ta samu wutan ya mutu ga iccen d'anye ruwa duk yagama jik'ashi, ledodi da roba tayita bankamai har ya kama miyar ya k'arasa nuna ta kad'a ta sauk'e ta d'aura ruwan tuwo da sauri ta fito sau warin hayak'i take gashi ko wankan bata gamaba, kayan makarantarta kawai tasa tafito tabiya dakunansu ta musu sallama ta wuce kamar kullum ba wacce ta takata.   Sanda tazo fita saidata lek'a k'ofar gidan taga ba kowa tayi ajiyar zuciya tajin jin dad'i sannan ta fito, sauri take tayi don tasan tagama latti bama dukan lattin take tunaniba burinta kar Allah ya had'ata da y'an cikin unguwar don tasan saitasha kuka.   Ta isa makarantarta karfe biyar dai_dai ta iso.  Tana shigowa y'an aji suka fara "Hajiya babbah" suna murnar ganinta.   HIBBAH yarince mai fara'a son mutane ga uwa uba ilmi, shiyasa malamai da d'alibai ke sonta. tana aji shida a boko, islamiya kuma tana aji biyar Malamansu na k'iranta da Mace mai kamar maza. Itace minitor, ita kecin na d'aya duk jarabawa duk lokacin da zasuyi gasar karatu ita ke cinyewa, shiyasa kowa ke sonta.
.
   Allah ya taimaketa yau malamai suna meeting bata sami kowaba, nan suka fara bitar karatunsu, bayan ta koma gida ko kayan makarantar bata cireba jaka kawai ta ajiye tayi kitchen tahau had'a wuta tana had'awa taje tai sallar magrib tana idawa koma kan girki, kafinta gama tagama shan wuya da iccen damina wanda ruwa ya gama dokarsu, ga yara sunata kukan yunwa.  Tana gamawa ko ci bataiba ta sunkuya wankin kayan makarantarsu nata dana yara biyar tagama k'arfe tara lokacin kowa na d'aki da yaranshi alola tayi aje tai sallar Isha'i, tana idarwa ko batabi takan abincinba ta d'auki yar tabarmar kwanciyarta tayi d'akin Mamansu Ahmad don kwanciya tana shiga tasamu duk sunyi bcc kan gado, gefe tasamu tashinfid'a tabarmanta ta kwanta, tama gama mantawa mai gidan anan d'akin yake, chan cikin dare taji magana sama_sama kamar masifa Mamansu Ahmad kecewa "wallahi saitabar d'akinnan"  "habba ke kuwa inaga ta mantane kibarta tunda tayi bacci" "bacci fa kace ina ruwana da baccinta" "babu ruwanki, amma amata hak'urin yau tunda kinga sauran yaran suma baki koresu a d'akinba."  "saurankam ai yaranane itako bani na haifetaba uwarta bansan wani gantalin takeyi agariba"   Hak'uri yayita bata dak'ar ta hak'ura   Hibbah dake kwance ba abunda takeyi sai kuka, Wai yau ita akema gorin wajen kwana har akema mahaifiyarta mai yawace_yawace, Allah sarki Ummanah, Allah yasa kuna cikin k'ishin lafiya da kwanciyar hankali aduk inda kuke.
.
*  Cikin dare Hibbah ta tashi da sand'uwa ta bud'e k'ofar d'akin ta fita, d'akin da da suke ajiye wasu shirgin da kayanta aciki nan ta nufa ta ciro zani cikin kayanta ta shimfid'a ta kwanta acan gefe hijabin jikinta kuma ta rufu dashi.  Asubar fari ta tashi tanayin sallah tahau gyara gidan ta nufi kitchen, sauri take tagama yau ta tafi makaranta da wuri ga yunwa Amma ko kad'an bata shawa'ar zama taci abincin zuwa shida da rabi ta gama komai saura gyara d'akin matan gidan, gashi har yanzun basu fitowa tunda sukayi sallah suka koma.     Sai wajen k'arfe bakwai suka fito lokacin duk yaransu sun shirya a gurguje ta shiga ta gyara musu d'akunan, kwanukan dasuka ci abinci ta had'a waje guda ta rufe sai ta dawo zata wanke don ta riga tayi wanke wanke.  dubawa tayi taga har bakwai da kwata da sauri taje ta kar'bi naira hamsin kud'in mashin d'inta tayi gaba yaran sun jima da tafiya makaratar gwamnati take sukuma sunata kud'i, idan anbata kud'in abun hawa na zuwa da k'afa take dawowa kafin ta iso gida duk yunwa ya gama da ita wani lokacin ma idan ta dawo sai ace abinci ya k'are anba yara, dolenta zata hak'ura ta d'aura na dare idan ta gama akayi rabo ad'an yafa mata.   
.
_wacce rayuwa su Umma suke ciki bara mu lek'asu_  Cikin yaddar Allah su Umma har sun koma gidansu dake yanzu unguwar tafara samun mutane, da taimakon Alhaji Isma'il aminin mahaifinsu Hibbah suka d'an gyara gidan.   Gidane mai d'auke da hud'u ciki d'ai_d'ai, sai bayan gida.  'Dakunan duk rufin kwanone, ko arzikin silin babu mafi yawan rufin d'akin a'bule suke, dabaraakayi aka d'an lik'esu, sai filin tsakar gida wanda zai iya fidda d'akuna kamar wad'ancan, ya fidda kitchen dakuma bayan gida.  Wad'ancan d'akunanma manyane sosai Umma ta sa kayanta a daki d'aya yaran suna d'aya ahan kali zata sami y'an haya su shiga saura biyun.  Gidan ko katanga babu sai kara aka samu aka kawaye gidan dashi, ahaka suke rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da rufin asiri.   Hibbah nagani zaune can gefe rik'e da k'irjinata da ciki, sauran d'alibai kuwa wasu na gyad'a, wasu tambo, wasu nacin abinci, wasu na filin break, dake lokacin sun fito  break ne, kad'awa akayi don komawa aji d'alibai sai rige_rigen shiga aji suke don gudun duka, Hibbah ma mik'ewa tayi don shiga aji saida tana fara tafiya wani girine ya kwasheta ta fad'i k'asa warwas numfashinta sai sama_sama yake kafin kace me d'alibai yan'uwanta sun rufeta, Ko ganinta ba'ayi.   _Nayi iya k'okarina don ganin na kutsa tsakanin yaran na kasa,dole na koma gefe ina tunanin me yasami HIBBAH baiwar Allah_             *
.
Duk sun rufeta ko ganinta ba'ayi, wasu daga cikin d'aliban sukace "kodai aljanu gareta?" aidajin an ambaci aljanu kanemi yaran ka rasa, saiy'an kad'an, kamata sukayi suka kaita aji aka dukufa karatun (Alqur'ani), ko gezau bataiba, don abundaya ragu. 
.
   Wata malamace tashigo don yimusu karatu, Saidai mafi yawan d'aliban ajin hankalinsu ya raja'a wani wajen da taga sun kewaye wajen,  Tambaya tayi "meke faruwane?"  Wata d'alibace taimata bayanin komai tace"shine zaku barta anan? Clinic yadace ku kaita baku cika akantaba da zafin ciwo zataji koda rufeta da kukayi ga zafi."    "malama bazata iya tafiyabane."    Har wajen malama tasu ta iso tana kallonta tace "dama Hibbace ba lafiya? Subhanallah! Yadda taganta rik'e da k'irji ga numfashi na fita da kyar gashi tana rik'e da ciki tasan yunwace."  Tace ma yaran "kowa ya koma wajen zamanahi ya zauna mutum d'aya ta tsaya ta mata firfita."  Fita tayi daga ajin, zuwa can sagata da y'ar k'aramin kwando d'auke da k'aramin flaks da kofuna biyu da gwangwamin madarar ruwa sai sugar.  Da kanta ta had'amata lafiyayyar shayi ta d'agota tabata abaki tanasha ta kwaro amai, ajiyewa tayi ta tafi Clinic din cikin makarantar ta ma ma'aikaciyar wajen bayani tace "ga dukkan alamu ulcer keneman samun muhalli jikin yarinyarna.
.
malama tace  "nima tunanin danake kenan." magunguna ta dauka da allurai guda biyu suka fita, allurai biyu akamata zuwa anjima in yad'an lafa  mata taci wani abun sai tasha maganin.   Ahankali takejin ciwon na tafiya ga wani zufa na sauk'omata.   Shayin aka kuma had'a mata tashi aka bata magani, kafin atashi taware kamar ba'itaba, Saidai rashin k'arfin jiki, tana tunanin yadda zata taka har zuwa gida a k'afa cikin ikon Allah malamar ta bata kud'in abun hawa. 
.
  Hadarine yau sosai ya had'o cikin dare, Hibbah duk sanda ake ruwa hankalinta na gidansu wajen Ummanta tunda taje ta kwana biyu taga yadda suke ana ruwa ba karamin tausaya masu Ummah da k'annenta, yanzu haka zaune take tana tunanin idan ruwannan ya sauk'o kwana zaune zasuyi atak'ure, bata gama tunaniba taji wani iska mai k'afi had'eda ruwa ai batasan sanda ta fara kukaba tana addu'ar Allah takaita ruwan kar yayi yawa.    Nima gidansu Ummah na garzaya don ganin wani yanayi sukeciki da yasa Hibbah kuka haka.   Ummah na hango ita da yayanta mak'ale can gefen d'akinsu wajen da baya zubarda ruwa, wasu sunyi bacci wasu kuma sai gyagyad'i suke,  Fita nayi daga d'akin don idona bazai iya cigaba da kallon yanayin da suke cikiba  Allah sarki rayuwa jarabawarta takanzo ma bawa ta ko wani fanni fatanmu Allah yabamu ikon cinye jarabawar.
.
   Yau asabar ba boko Hibba sai sauri take tagama wanke_wanken datake ta tafi islamiya don yanzu wajen takwas da rabi, tana gamawa taje ta sa kayan makaranta kira taji ankwala mata matar Baffan nata da sauri ta fita taga Maman Shahida ke kiranta kudi ta mik'a mata Wai tayi sauru ta sayoma Shahida k'osai amsa tayi tana Addu'ar Allah yasa gidan ba layi fitowa tayi sai sauri take bugawa, daban y'an unguwar tagani zaune kan dakalin k'ofar wani gida, tunda ta hangosu gabanta ke fad'i jitake kamar ta juya amma bata isaba jiki sanyaye taci gaba da tafiya aiko tana isowa waje duka d'au ihu suna k'irantada sunan data tsana.          
.
*Cigaba tayida tafiya, sukuma sukaci gabada tsokanarta, kwallar data taru idonta ne ya zubo, kukan zuci kawai take zuciyarta kamar wuta take jinshi, nan  take kanta ya fara sarawa, haka ta isa gidan sayan k'osan, Allah ya taimaketa ba layi akabata tayi gaba tare da fatan kar Allah yakuma had'ata da mutanennan saidai tana isowa sukaci cigaba daga yadda suka tsaya, kukane yakuma kwanamata, tasa bayan hannunta tana sharewa.   Tana isa gidan tamik'amata ta d'au y' ar ledan littattafanta tayi gaba, ga kanta dake tsananin ciwo ta gwammace taje makarantar data zauna gida don idan ta zauna aiki saita rasa yadda zatayi idantace batada lafiya ace k'aryane aikine bataso,shiyasa ta gwammace ta tafi makarantar datai zaman gidan.   Haka rayuwa taita tafiya da jarabawa kala daban daban.   Har noman kud'i Umma keyi, wanki, surfe da daka na kud'i don kawai tasami abunda za'arufama kai asiri, daga baya tasami aiki a ma'aikatan kula da marayu da marasa galihu basuda matsala yanzu sosai, yaranta duk tamaidasu makarantar kud'i yaya Sadeeq kawai ke makarantar gwamnati, d'akuna biyun tasa haya, balaifi suna rayuwa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali.    Cikin ikon Allah Hibbah sun zana jarabawar aji shida a primary ta fito da kyakkyawar sakamako, har anmata register a makarantar gaba primary aji d'aya, saidai k'arfe sha biyu zuwa biyar da rabi suke tashi, tundaga lokacin aikin gida ya k'aru mata don saitayi girkin rana idan ta gama ta d'aura miyar dare kafin ta dawo gida magrib yayi,sai kicin.    Haka rayuwa taci gabada tafiya, kwatsam aka rufe ma'aikatardasu Umma suke aiki, lokacin aka turo mata mahaifiyarta ba lafiya  nan take ta tafi don dubata, kwana biyu da zuwanta Allah ya kar'bi abunshi, kwana bakwai tayi ta dawo, akaci gaba daga inda aka tsaya.          ~
.
*  Rayuwa taci gaba da tafiya lokacin Umma duk sama ma yaranta wajen aiki, dagamai kafinta, d'inki,gyaran wuta, makanikanci, gakuma karatu ta ko wani fanni sunayi tukuru na addini da boko,   Hibbah ma tun wani ciwo datayi Umma tazo ta d'auketa bata kuma komawa gidanba suma basu nemetaba, haka suka Cigaba da rayuwa kowa abundaya samo wajen aikinshi dashi suke had'awa su biya buk'atunsu.  
.
*BAYAN SHEKARU MASU YAWA*  
Gidan Umma nazo amma gaba 'baya na kasa gane gidan don duk layin wasu had' ad'd'un gidaje nagani, da tambaya nasami gidan.    Ummu na hango zaune kan wani rantsatsen kujera rik'eda wata yarinya dagani suna kamada yaya Sadeeq, can naga wata y'ar duma dumar mata tashigo ta kar'beta tana cewa "ai Umma Zarah akwai kuka tundaga gefenmu nake jiyo kukanta."  kafin Umma tayi magana akai sallama aka shigo wani k'aton Alhaji nagani, har gaban Umma ya wuce ya tsugunna ya gaidata sannan yace "Umma zamu wuce gidan Hibbah muduba ya jikin nata."    "toh saikun dawo Allah tsare hanya, agaidata da yaran."      "zataji insha Allah."      Maman Zarah matar ya Sadeeq tace "Umma sai mundawo, ko inbar miki abokiyar hira."      "waaa! jeki da abunki adawo lafiya."   Suka fita suna dariya Umma dariya take.   Hibbah tayi aure harda yaranata biyu, suna zaman lafiya,so da K'aunar junansu.  Ya Sadeeq ma yayi aure da y'a d'aya   Sauranko duk karatu suke.   Baffah kallah ananan ana fuskantar jarabawar rayuwa, ga mata hud'u ga tarin iyalai ga gida kullum cikin rikici.   Y'an'uwa yanzu kowa rububin zuwa wajemsu Ummah ake.   Komai yayi farko zaiyi k'arshe.   Mahak'urci mawadaci.    
.
   *ALHAMDULILLAH*         _NAN NA KAWO K'ARSHEN WANNAN NOVEL NAWA_  *INAMAIBA MASOYA WANNAN NOVEL HAK'URIN YANKEWA DANAYI HAYAN YA FARU SABIDA WANI DALILI*

.
CALL or SMS
07066508080
.
Whatsapp
07066656752

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* 👉🏻1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaɗo se kuka takeyi,prince kasa...
  • MIWASMITI Page 31 to 40
    Kuka ta Kuma saki gamida kamo hannushi ta matse a tsakiyar qirjinta Dan jin wani irin suka da yake mata Ga jiri da takeji gaba daya bata gan...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam