Karfe takwas da wani abu ya iso hostel dinsu cikin motan aunty sumy don yasan idan yazo da motarshi masu gadi suna iya ganewa shi kuma baiso su ganshi sbd dare yayi shiyasa yayi disguising kanshi da motarta..so yayi ma ya hakura da ganin nata sai gobe sai kuma yaji bazai iya ba at leat ko ganinta ya samu yayi ya danyi mgn da ita yasan zai samu bacci mai kyau shiyasa baiyi ka sa a guiwa ba..yana gama parking yayi dialing number dinta..lokacin suna zaune sun hadu a room 1a gaba dayansu sai labari suke suna daria kowa tana bada labarin hutunda tayi a gida...Lamido na zaune daga gefe tana sauraronsu tana sakin smile ita nata holidays din dai la ba’asa zatace don kwata kwata ba wani enjoying dinshi tayi sosai ba..suna tsaka da wnn hira wayanta ya fara ringing ta dauka da sauri tana zare ido ganin Proprietor akan screen..mikewa tayi ta fita daga dakin sbd hayaniyarsu bazai bari taji ba..kiran na katsewa wani ya sake shigowa dan tayi picking tareda cewa"sir ina yini"..bai amsa gaisuwar ba sai yace mata"ki fito in ganki ina bakin gate dinku plss"..dan tura baki tayi kmr yana ganinta tace"sir dare fa yayi"..a hankali yace"i know..bazan iya bacci bane tunda nasama taina saina ganki nasan matsala zan samu idan ba ganin naki nayi ba..ki daure kizo kinji"...bata sake mgn ba ta kashe wayarta tareda dora babban hijab akan three quarter da rigan dake jikinta..wayanta na rike hannunta ta fita daga hostel din..idanunshi na kanta yana kallo kmr bai taba ganinta ba har ta karaso inda yake..da sauri ya bude mata kofa ta shiga snn ta rufe kofar..kanta a kasa tana wasa da fingers dinta tace"ina yini"..maimakon ya amsa sai ji tayi yace"i missed u"..sake sinne kanta kasa tayi tanajin wani irin yanayi tattare da ita..shi kuma kallonta yakeyi kmr an aikoshi..wani abu yakeji mai kamada magnet ko kuma ince maganadisu yana kokarin janshi gareta amma bai bari yayi tasiri ba ya dan janye jikinshi kadan ya sauke wani ajiyar zuciya mai karfi tareda relaxing jikin kujera yana cigaba da kallonta..shi baiqi su kwana a haka yana kallonta ba wlh..he can’t get enough of her..komai nata abun kallo ne a wurinshi shiyasa wani lokaci shi kanshi yakan ba kanshi mamaki...ganin yanda suke zaman kurame yayi breaking silence ta hanyar kiran sunanta"Aysher"..amsawa tayi da"na’am"..ba tareda ta yadda ta dago idonta ba..shikuma yana cigaba da kallonta murya kasa kasa yace"i missed u so much..can i hug u plss"..da sauri ta shiga girgiza kai tace"Noo"..hannunshi ya daga alaman surrender yace mata"shknn i wont touch u tunda bakiso..amma da gaske am missing u sosai..ko bacci bana iyayi"..lumshe idanunta tayi tanajin wnn baqon yanayin daya tsiri bijiro mata a duk sanda take tare dashi..gabanta har wani faduwa yake na rashin dalili...sake matsowa yayi yana kallon cute face dinta da kyau har breathe dinshi na sauka direct akan fuskan nata sbd kusancinsu yayi mata wispering"i love u"..sake runtse idanun tayi tanajin faduwar gabanta na sake tsananta..wai wane irin mutum ne shi kam?..yana gama fadin haka ya sake komawa ya kafe jikin seat din da yake har yanxun yana kallonta yace"bari in barki ki tafi saida safe..dama kawai nace izo in ganki sbd in samu bacci sosai"..kai kawai ta iya gyada mashi ta kasa cewa komai..dan marairaicewa yayi yana dubanta yace"Aysher this is not fair mana..kin kulle idanunki kin hanani ganinsu snn mgn ma bazan samu ayimun ba?.."da kyar ta iya bude bakinta tace"saida..safe"..kallon bakinta kawai ya tsaya yi and he couldn’t help it but closed his eyes sbd yanda yakejin kmr ya kama dan bakin yayita sha..hannunshi ya mika baya ya dauko wani shopping bag mai kyau ya mika mata ganin idanunta a kulle ne yace mata"take mana"..sai yanxu ta bude idanun tana kallon bag da yake miko mata..sbd tsabar bazata iya masa musu ba don ko bude baki bata sonyi ta amsa bag din kawai batareda tace komai ba..bayan ta amsa yace"Mummy tace in kawo maki"..gyada kai ta shigayi kafin a hankali ta sake cewa"nagode"..yayi murmushi tareda daga mata kai kawai duk mood dinshi ya sauya wanda har yayi affecting idanunshi...cire mata lock yayi ta bude motar ta fita snn ta sake sukuyowa ba tareda ta yadda sun hada ido dashi ba tace"thank u..saida safe"..yana kallonta kasa kasa shima yace"saida safe..love u"..bata sake gigin cewa wani abu ba ta bar wurin da sauri rikeda bag din daya bata..shiko lumshe ido yua sakeyi kafin ya bude ya tayar da motar snn yayi reverse ya fita daga hostel din.
The next morning da wuri suka gama shiryawa kowa cikin well ironed uniform dinta da dan mini hijab dinsu as usual..kafin su fita daga room dinsu Lamido ta dauki wani pink veil dinta mai dan girma ta yafa akan uniform din nata don tasan idan ma bata sa ba saiya mata mgn..Billy sai daria take mata itama tana rama tsokanarta da taitayi jiya haka su fita daga dakin..kmr kllum yauma school bus dinsu ne ya kwashesu kowa za’ayi dropping nashi hospital da akai posting dinshi..Freedom suka fara zuwa and abun da ya basu mamaki bai wuce ganin su biyu kadai akai posting Freedom din ba dan gaba daya sauran dake cikin bus din ba wanda take a nan...suna fita suka nufi cikin asibitin kai tsaye...office din CNO suka nufa as usual don yayi masu posting sai yace suje office din Dr Bobby yace shi da kanshi zaiyi musu posting bashi ba..wani irin kallon juna sukai suka hada ido suna fita Billy ta sake rushewa da daria..Lamido bata kulata ba har suka isa office dinshi..kafin suyi knocking wani messenger dinshi dake zaune gefe da alaman su yake jira ya tashi ya bude musu office din yana cewa"doctor yace ace ku shiga ciki ku jirashi..sun shiga theater ne tun daxu"..basuyi masa musu ba suka shiga office din Lamido sai binshi takeyi da kallo tana tuna abubuwa a dama da suka faru cikin office din nan nashi..ta tuna ranar farko data fara shigowa office din lokacinda sukaje bikin Aneesa ta bar ward dinsu ba kowa har hakan yayi sanadin rasuwar wata mata..ranar ne ta fara shigowa office dinshi yayita sata aiki snn ya hanata zama for almost 5 hours..ta tuna lokacinda batada lafia ya kawota nan ya dubata sai kuma lokacinda Provost ya kawota sbd yayi fushi da ita..she remembers how he hugged her at that time..how he wrapped her with his hands..batasan lokacinda ta lumshe ido tareda zaunawa nan kujeran dake kusada ita ba..nan take komai daya taba faruwa a office din ya shiga dawo mata daga masu dadi har masaru dadin..ta tuna randa yake cewa bazaiyi posting nata inda takeso ba until she promised to stay far away from doctors da duk wani staff namiji and her reply was"bazan kulasu ba ai dama bana da interest kan doctors da health workers sbd son matansu yayi yawa"..sake lumshe ido tayi tana tuna yanda komai ya faru a office din...bit by bit ta shiga remembering duk wani moment da ta taba spending a office din har zuwa time dinda taji ciwo a kafa..how he treated her..da yanda ya daukota cak tun daga parking space zuwa cikin office din..tayi nisa sosai cikin tunani har batasan wayanta dake cikin bag dinta nata ringing ba saida Billy ta daddage ta kwada mata duka a cinya snn firgigit ta dawo hayyacinta..ta wani hade rai tana kallon Billy yace"wnn wane irin mugunta ne..kinji zafinda naji kuwa?.."murmushi Billy ta saki tana fadin"yi hakuri Ammi keta kiranki tun daxu fa kina can kina tunani"...daukan wayan tayi da sauri taga two missed calls from Ammi dan haka tayi dialing number dinta tana kara wayar a kunne...Ammi na dagawa tace"ina kika shigane naketa kira baki dauka?.."da sauri tace"Ammi ban ganiba wlh..ina kwana"..Ammi tace"lafia lau..ya makarantan"..tace"fine Ammi..yau mukayi reporting asibiti"..Ammi tace"to Allah ya taimaka..dama tuna maki zanyi karki yadda kiyi abunda bashi knn ba..ki nustu ki kama kanki yanxu kinga dai mgnr aure ne tsakaninki da mutumin nan idan kikaje kikayi abunda mutuncinki zai zube a wurinsa ke zakizo daga baya kinajin kunya sbd haka ki kula sosia"..gyada kai takeyi tace"insha Allah Ammi zan kula..i will be a goo girl"..Ammi tace"to Allah yayi albarka..ina Bilkisu?.."tace"gata"..snn ta mika mata wayar..Billy na amsa itama ta gaisheta kafin ta amsa da fadin"so nakd kisamun ido akanta sosai duk kikaga zatayi wani abu daba shknn ba ki kira ki fadamin"..da sauri Billy tace"zanyi haka inshaAllah Ammi"..daga haka sukayi sallama ta mikama ma Aysha wayarta..ta karba tana sake dinke fuska tace"sbd mugunta kika dakeni Billy..kinji zafin da nakeji kuwa"..kallonta Billy keyi tana kunshe daria tace"to Allah baki hakuri nidai"..ta daddage zata fara masifa aka turo kofar office din aka shigo nan take ta hadiye masifar da takeson saukewa tareda kasa da kanta kmr mara gaskia..kamshin perfume dinshi kawai taji ta gane shine don a jikinshi kadai tasan irin wnn kamshin...shigowa cikin office din yayi waya kare a kunnenshi idanuwanshi kuma kyam akanta har ya isa seat dinshi ya zauna..kallonta yacigaba dayi yana sauraron abunda ake fada mai ta wayar banda gyada kai ba abunda yake itadai Lamido tayi wani tsit ko numfashi ma a nutse take daukanshi sbd kada ace tayi ba daidai ba...muryanshi taji yace"abunda zai faru yanxu ki turota tazo ta sameni zuwa anjima sai ik duba maki ita inyaso duk yanda ake ciki i’ll let u know"..shiru ya sakeyi kafin kuma yace"alright sai anjima"..daga haka ya ajiye wayar yana kallon yanda ta dage wasa da fingers dinta kmr ‘yar yarinya..juyawa yayi yana kallon Billy da ido ya tambayeta"what happened to her"..Billy ta bude hannayenta alaman she have no idea..sake juyawa yayi gareta still kanta a kasa Billy ta gaisheshi ya amsa ba tareda ya dauke idon daga kanta ba.."Aysher"..ya kira sunanta a hankali..maimakon ta amsa sai cewa tayi"ina kwana"..komawa yayi yai relaxing kan kujera yana dan rotating dinshi yace"yau bazan amsa gaisuwan nan idan baki dago kin kalleni ba"..sake sunkuyar da kanta tayi tana turo baki..yace"bazaki kalleni ba?.."kin dagowa tayi shi kuma yacigaba da kallonta yana shafa gemu zuwa sajenshi yace"then yau zamu yini office din nan knn"..juyawa yayi ga Billy dake kallon love iya love yace mata"kice ta bude idonta idan baso take mu kwana office din nan ba"..ajiyar zucia Billy ta sauke before saying"Lamido open ur eyes mana"..banza itama tayi mata taki dago kan nata..ganin haka ya juya ga Billy ya sake cewa"ina kikeso ayi posting dinki tunda naga ita zaman office din nawa takeso"..da sauri ta dago idanunta tace"ni ba zaman nan nakeso ba"..yace"then look into my eyes"..shoulder ta makale mashi tace"ni banason kallonsu"..yace"why?.."tace"suna sani jin wani iri"..murmushi kawai ya saki tareda gyara zama yace"to ku fadi inda kukeso ayi posting naku"..da sauri Billy tace"sir ni theater nakeso"..tana rufe baki Lamido tace"nidai bazanjd theatr ba gaskia"..bai sake mgn ba yayi posting Billy theater ta tashi ta tafi..ita kuma yace ta fadi inda takeso yayi posting dinta tace maternity..baiyi musu ba yayi posting dinta can itama ta mike zata tafi yace"banda mgn da maza dan Allah"..kai kawai ta gyada mashi ta fita tana sakin ajiyar zucia..batasan meyasa these days duk take taredashi take jinta kaman a prison ba..hatta numfashinta ba daidai yake tafia ba ta kuma rasa dalilin wnn abu haka..mutuminda ba tun yau ta sanshi ba ta rasa meyasa sai yanxu takejin wnn bala’i a kanshi..shikam da kallo ya bita har ta fita snn ya janyo wasu files dake kan desk dinshi ya fara dubawa yanata zabga murmushi..saida ya gama going through the files snn ya ajiyesu ya fita daga office din zuwa maternity don yin ward round.
Kwanaki nata tafia yayinda Dr Bobby ke gwada mata tsantsar soyayya..gaban kowa nuna mata so yake babu ruwanshi saida ita ya barta dajin kunya..har mamakin yanda baida kunya take wlh..koda yake ba abun mamaki bane idan akayi duba da ya hada jini da inyamurai...kullum ta shigo asibiti sai ta fara zuwa office dinshi don idanma bata je ba shi zuwa yake har inda take ya bata kunya..haka zai ajiye duk wani abu da yakeyi ya tashi ya rakata har maternity tun abun na bata kunya har tazo ta denaji..daga karshe ma hanata bin school bus yayi yasa driver dinshi ke zuwa ya daukosu daga hostel snn ya maidasu idan sun tashi aiki..Lamido tun tana ignoring abunda takeji game dashi har ta fara saduda..soyayyan da yake gwada mai tsayawa a rai ne don kullum ta koma hostel tayita tunaninshi knn har wani lokacin ta tsinci kanta tana murmushi..tana jin dadin yanda yake kulada ita sosai da kuma yanda bai iya 6oye abunda yake feeling gameda ita..duk wanda yayi zama 10 mins dasu saiya fahimci ba dan karamin so yakeyi mata ba...abu daya da watarana yake bata haushi shine kishinshi da yayi yawa..gaba daya yabi ya takureta a asibitin ta yanda ko mgn yaga tanayi da namiji shknn ta shiga uku don saiya mata fada..har mamakin yanda yake daure face dinshi take sai kace bashine ke mata mahaukacin so ba amma kan kishi gaba daya idanunshi rufewa suke..snn ga dokar saka hijab daya kafa mata shima ba karamin takura bane a wurinta amma haka nan ta hakura take sakawa dan ko by mistake ya ganta ba tareda hijab din nan ba sai an samu matsala..a 6angaren Billy da Hammanta kuwa soyayya ce mai karfi suke yinta don yanda suke son juna abun har mamaki yake bata..wani lokaci idan Billy na waya dashi saidai tayi zaune tana kallonta a daidai lokacin sai itama soyayyan da sukayi da Prof ya shiga ya dawo mata..ta tuna itama fa da haka takeyi da saurayinta amma with Proprietor komai ya canxa mata..dukda zuwa yanxu ta rage jik kunyanshi amma har yanxun bata iya sakewa tayi mashi mgnr daya shafi love kmr yanda shi yake mata..bata sani ba ko har yanxu bata fara sonshi bane amma dai ta tabbata ya samar ma kanshi special place a cikin zuciyarta.
Yau Friday da safe ta shigo asibitin ita kadai kasancewar Billy evening duty gareta..bata je office dinshi ba kai tsaye ta wuce maternity sbd ta danyi latti..tana shiga ta cire hijab dake jikinta ta bar iya na uniform dinta snn ta shiga cikin labour room bayan ta gaisa da sauran staff dake dakin..Nurses station ta shiga ta ajiye bag dinta snn ta shiga ciki..mutum biyu ta samu kwance a dakin..daya daga cikinsu nata fama don har anyi rupturing membrane..karasawa tayi tana dubata sai taga head ya fara tahowa dan haka tayi saurin daukan hand glove ta saka snn ta shiga assisting matar..cikin ikon Allah ta haifi yaronta lafi..bayan tayi musu duk wani necessary abu tace ma matar ta fadi sunanta wanda suka kawota aje a karbo kayan baby a wurinsu..ba musu matar ta fadi sunan mijinta ita kuma ta fita don sawa a karbo kayan sai bataga ko daya daga cikin messengers dinsu ba dole ta fita da kanta ta amsa kayan ta dawo..tana cikin shirya babyn ya shiga cikin labour room din sbd kiranshi da akayi ya duba daya matar dake cikin dakin..abunda ya bata mamaki shine yanda yayi kamar bai ganta ba ya wuce inda matar take fuskan nan nashi a daure kmr an aiko mashi da saqon mutuwa..dakatawa tayi da abunda take ta juya tana kallonshi still taga ko inda take baya kallo ya fara aikin gabanshi..ranta taji ya 6aci sosai..to uban me tayi kuma da zai wani dinga shareta dan rainin hankali kawai.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
49
Kallonshi ta tsaya yi da mamaki bayan ta gama shirya yaron ya dorashi jikin mamanshi da aka wuce da ita post natal..yanxu laifin me tayi kuma?..ko dan sbd bataje office dinshi bane yau?..karasawa tayi inda yake bayan sauran Midwives din sun fita..murya can kasa tace mishi"ina kwana"..wani kallo daya sakar mata saura kiris ta fadi kasa sbd tsabar rudata da yayi..ta tabbata wnn fushin ba iya na rashin zuwa office dinshi bane dole da akwai wani abu to amma menene?..duk jikinta yayi sanyi taji bataji dadin wnn cold treatment dinba tunda ba haka ya saba mata ba..tafiso yacigaba da kulawa da ita yana nuna mata so kmr dai yanda yakeyi a baya..ganin har yanxu bai kalli inda take ba aikin gabanshi kawai yake sai ta juya ta fita daga labour room jiki a sanyaye..lumshe ido yayi bayan fitan nata yana sauke numfashi..jiya ko baccin kirki kasawa yayi sbd labarin da aka bashi wai tsohon saurayinta yaje har hostel wurinta kuma ta fito ta sameshi sbd batada hankali..abun yayi mashi ciwo sosai ta yanda har zata iya zuwa ta kula wani bayan alqawarin aure dake tsakaninsu..snn kuma da zai shigo nan ya hangeta tareda wani suna mgn kuma ko hijab babu a jikinta haka ta gama nuna mishi jikinta ta juya ta tafi yana ganin yanda mutumin yabita da kallo..a yanda yasan halinta da shegen rashin jin mgn tabbas idan ba zafi zafi yayi mata ba bazata shiga hankalinka ba shiyasa dole ya dake ya nuna mata abunda tayi ba daidai bane sbd ta kiyaye gaba amma shi kanshi bajin dadin fushin da yakeyi da ita yake ba..kawai dauriya yake amma Allah kadai yasan halinda yake ciki...a takaice har ya gama aikinshi ya bar ward din baibi ta kanta ba hakan kuma ya sake daga mata hankali fiyeda tunani..lokacin tashi nayi ya tura mata text saying tazo office dinshi idan ta tashi ya maidata hostel..ba bata lokaci ta nifi office din nashi bayan tasa katoton hijab dinta..tana shiga ko zama batayi ba ya dauki wayoyinshi dake kan desk dinshi ya bude kofa yana kallonta fuska daure yace"muje"..kai a kasa ta ra6a ta fita daga office din shima ya fita suka wuce parking space..amsan key yayi hannun drivernshi snn ya bude mata front seat ta shiga shima ya shiga snn ya tada motar suka wuce..ko a hanya sai satar kallonshi take taga fuskan nan a cunkushe kamar na shanu..sun danyi nisa da tafia wayanta ya fara ringing ta duba screen sai taga thesame number ne da baby ya kirata dashi jiya dan haka tayi daurin silencing wayar tareda turata cikin jaka tana rarraba ido..Bobby dake ankare da duk abunda take hannu yakai ya dauki bag din nata tareda zaro wayar daga ciki snn ya ajiye mata jakar ta..kallon wayar ya tsayayi kafin wani kiran ya sake shigowa bai tsaya wata wata ba kuwa yayi answering tareda sawa a speaker..on the other hand Prof na jin tayi picking call din ya fara cewa"baby girl listen to me plss..i will explain everything..lokacinda.."kitt Bobby ya katse kiran tareda kashe wayar gaba daya yasa a aljihunshi saura kiris kan motar ya kwace mashi Allah ya taimaka yayi saurin daidaitashi..Lamido kuwa banda kwalo ido ba abunda take shknn ya gama tona mata asiri..kodai ya samu labarin yazo hostel jiya?..tunanin hakan yasa taji kaman fever na neman rufeta..yanxu idan ya fadawa daddy ai ta shiga uku..shidai yana driving yana kokarin cooling temper dinshi don idan ta zuciyarshi zai bi yana iya gaura mata mari a wurin..kawai zafi yakeji na wnn tsohon mutumin da bazai bar mashi ita ya huta ba..idan ba iskanci bama baiga dalilinda zaisa yace yana son ‘yar cikinshi ba wlh..duk ranshi ya sake 6aci kafin su isa hostel ya cika yayi fam kiris yake jira ya fashema wanda keda rabon shan masifa..daurewa tayi ta tattaro duk karfin halin da take dashi ta kira sunanshi a hankali"Sir"..bai kulata ba kuma bai kalli inda take ba..ta sake juyawa taga yanda yake cin kuna sai kawai ta kauda kanta tana turo baki..tun asali fa wnn baqin halin nashi ne yasa bata wani so aurenshi ba..kan a very minor abu zaizo ya nemi daga mata hankali..har suka karasa hostel batace ba shima baice mata ba..bayan ya gama parking ta juya tana kallonshi kafin tayi mgn taji yace"sauka"..ko minti daya bata kara na cikin motar ba ta bude tayi ficewarta ko sallama bata yi dashi ba..da kallo ya bita zuciyarshi na tafasa yayi reverse ya bar hostel din..direct gida ya koma don yana bukatar mgn da Mummy a halin yanxu..ya fuskanci idan ba wani mataki ya dauka ba tsaf tsohon mutumin nan zaiyi snatching dan attention dinta daya fara samu yanxu..direct bedroom din Mummy ya shiga ya sameta zaune tana karatun Qur’ani ya karasa da sauri ya zauna kusada ita yana kallonta kmr wanda ke shirin fashewa da kuka..Alqur’anin hannunta ta ajiye bayan takai ayah snn ta shiga dubanshi tace"kai lafia kuwa?..why zaka shigomin daki a zabure haka?.."kama hannayenta yayi yanayi mata puppy eyes yace"Mummy akwai matsala wlh"..kallonshi Mummy keyi tace"matsalar me?.."yace"Mummy so nake ayi mgn da Lamido ya tsayar mun da rana nidai..bazan iya jira har saita gama karatu ba wlh"..zare idanu Mummy tayi tana kallonshi tace"rashin kunya Bobby?.."girgiza kai ya shiga yi yace"ba mgnr rashin kunya ba..wani mayen mutumi ne ya makale ma yarinyar nan yake kokarin rabani da ita ni kuma hankalina bazai kwanta ba tunda kinga ba wani sona takeyi ba har yanxu"..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace"sai kaje kayi mgn da Waziri sune masu nema maka aure bani ba"..da sauri yace"kunyarshi nakeji wlh..kiyi masa mgn da kanki"..girgiza kai Mummy ta shigayi tana murmushi..ya sake kama hannunta yace"Mummy please mana..ba tuntuni kikeso inyi aure ba?.."kai ta gyada alamar eh..yace"to yanxu nakeso nayi auren Mummy kiyi wani abu plss"..kai ta gyada mashi tareda fadin"zanyi mgn da wazirin"..da sauri ya rungumeta yana cewa"nagode sosai mother..Allah ya baki aljannah"..kai kawai ta iya gyadawa tana shafa kanshi..har yanxu bata dena mamakin wnn so da Bobby kema yarinyar ba...sallama yayi da ita ya sake komawa hospital don bai kammala aiyukanshi ba.
Bai baro hospital din ba sai after magrib..yaso ya wuce gida amma yaji bazai iyaba sai yaje yayi mgn da ita..so yake fushin nashi ya dore amma yasan bazai iyaba don wahalar da kanshi zaiyi..gashi ita ko text message batayi masa irin na bada hakuri ba balle yasa ran kira..jikinshi duk yayi sanyi yasan dama shi kadai yake sonta ita ba sonshi take ba..bayan driver ya gama parking ya bude motar ya fita shi kuma ya kira wayarta tana dauka yace ta fito waje yana jiranta...hijab ta dora akan dogon rigan dake jikinta ta fita..kafin ta karaso ya bude mata kofa dan haka tana zuwa ta shiga tareda maida kofar ta rufe..kamshinshi duk ya cika motar ga kuma sanyin ac da driver ya bari a kunne..kallonta Bobby yake yanajin ciwon tsayawa da tayi kula tsohon saurayinta..kmr tasan tunanin da yake knn tayi kasa da murya tana dan kallonshi a hankali tace"sir nidai dan Allah kayi hakuri"..kallonta yacigaba dayi kafin yace"why are u doing this?.."a hankali ta sake cewa"am sorry"...lumshe ido yayi tareda jingina kanshi jikin seat din da yake yana sauke numfashi..dama yasan wnn fushin ba wani wurin zaije ba tunda ba iya fushi zaiyi da ita na lokaci mai tsaho ba..bude idon yayi yana kallonta ita kuma ta sake narkewa cikin shagwa6an da ta manta yaushe rabonta dashi tace"nidai kayi hakuri bazan kara ba"..kallonta kawai Bobby yake gabanshi har wani faduwa yake..yau dai itama ta tsayar da idonta a kanshi tana kallonshi da puppy eyes don da gaske bata son yana fushi da ita..wani irin sanyi da kasala Bobby yaji sun dirar mashi at once..gaba daya joints din jikinshi sukayi wani irin weak kaman wanda yayi shekara da shekaru ba lafia..lumshe ido yayi ya bude yana sake kallon yanda har yanxu bata dauke idanu akanshi ba..baisan wane force of attraction ne ya matsar dashi kusada ita ba kawai shidai yaji yana iya zaucewa yau idan baiji yarinyar nan a jikinshi ba..Allah kadai yasan yanda yake kokarin fighting wnn feeling dake bijiro mishi duk yake tareda ita amma wnn is different and beyond his control..a hankali yakai hands dinshi yayi cupping fuskanta dasu yana sauke numfashi da sauri kmr wanda yayi aikin karfi..da sauri ta lumshe eyes dinta gabanta na faduwa..fuskanshi ya dora kan nata yana kallon the most cutest and attractive lips daya taba coming across duk rayuwarshi..a hankali ya bude bakinshi yace"i..i..want"..kasa karasawa yayi kawai saiya rungumeta a jikinshi yana sauke ajiyar zucia..wani irin azababben so da qaunarta suna sake zaga kowane kafa na jikinshi..shidai yasan yarinyar nan idan bata soshi ba mutuwa zaiyi for sure..wnn son da yake mata bana lafia bane ya sani..wani irin dif Lamido tayi tanajin yanda heart dinshi ke beating da karfi..ga wani irin force da yayi applying a hug din kaman zai maidata jikinshi...batayi mosti ba kmr yanda batayi kokarin kwace kanta ba..heart beat dinshi da taji kadai ya isa ya tabbatar mata da ba karamin so yake mata ba..wani tausayinshi taji ya kamata...shiko Bobby har yanxun eyes dinshi lumshe yanajin wani extra hot feeling na sake rushing into him..gashi duk kokarinshi na yaga ya rabata da jikinshi ya kasa sbd ko energy baidashi..saida ya daddage snn ya iya raba jikin nata da nashi idanunshi kumshe ya jingina kanshi da kujera..kallonshi Aysha keyi ba tareda tace komai ba har ya dan samu nutsuwarshi snn ya bude idonshi da sukayi jaa sbd abunda yakeji voice dinshi na fita da kyar yace mata"i will die without u..i love u"..kallonshi kawai Aysha keyi batace komai ba..shi kuma yana dubanta ya gyada mata kai yace"yes..i love u to the core..duk wnn abunda kike ba karamin daga hankalina yake ba..am sure yanxu if za’ayi diagnosing dina baza’a rasani da high blood pressure ko kuma cardiac problems ba and it’s all because of u"..kallonshi har yanxu takeyi fana langabar da kai kmr zata sa kuka..hannunta ya kama ya dora saitin heart dinshi yace"zafi nakeji a ciki duk lokacinda namiji ya ra6eki..inajin kmr zata fasa kirjina ta fito idan kika fita ba tareda covering jikinki completely ba..snn inajin ciwo idan kika nuna baki damu dani ba"..shiru ya sakeyi yana sauke numfashi..itama tayi tsit tana sauraran heart beat din nashi..hannun nata ya cire daga chest dinshi ya rikeshi gam da nashi hannun yana yi mata kallon da ya kusa tafia da imaninta in a pleading tone yace"i beg u in the name of almighty ki bar wahalar dani haka..all i want from u is love and care..ko baki soni yanda nake sonki ba i will manage and i will live a happy life for as long as ina tareda ke..i love u so so very much Aysher..i love u to the moon"..kai kawai ta shiga gyada mashi hawaye har ya ciko idonta tace"kayi hakuri ban karawa"..dan murmushi ya saki tareda matsawa ya manna mata peck a forehead dinta yace"thanks love..i love u"..lumshe ido tayi hawayen dake cikeda idon suka zubo kan fuskanta..kmr an fizgi mgnr daga bakinta tace"and i..i..i.."kasa karasawa tayi ta sake lumshe ido..da sauri Bobby ya sake kama hannayenta yana kallonta cikeda son yaji abunda zata fada"say it..say it plss it’s what i have been longing to hear from u..please say it in samu saukin zuciata"..sake runtse idanu tayi voice dinta na rawa tace"i..love..u"..tun kafin ta karasa ya cike gap din dake tsakaninsu ta hanyar yi mata kyakykyawar runguma...wani irin bright smile ne kwance kan fuskanshi yaji kalmar i love u din nan tafi diamond da gold a wurinshi..wani irin sanyin dadi yaji yana kamashi ashe haka akeji idan masoyi ya furta kalmar so?..ashe haka feeling din yake?.."oh Allah thank u..Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah yaa rabb"..sun dauki lokaci mai tsaho a haka kafin yayi breaking hug din ya dagota sai yaga hawaye take wani nabin wani..hannu yakai yana share mata hawayen yace"don’t cry okay?..stop crying i love u"..kai ta gyada mashi tana wani turo baki..ita kanta batasan wai ita zata iya bude baki tacema proprietor she loves him ba amma gashi tayi..it happened all of a sudden..kawai batasan yaushe ta fara sonshi ba amma for sure yau ta tabbata she loves him too and she doesn’t want to share him with any other woman..ido ya kuma lumshewa tareda pecking forehead dinta yana dubanta da bright smile nasa yace"thank u so much love..thanks for loving me"..murmushi kawai ta saki dimples dinta suka fito..Bobby dake kallonta yau dai yakai fingers dinshi ya aza bisa dimples din nata..hannunta tasa ta dafe nashi hannayen snn ta dan bude ido kadan ta kalleshi sai kuma ta sake maidawa ta rufe..sunkuyawa yayi ya hade fuskanshi da nata yace"open ur eyes mana ki sake maimaitawa inji"..shoulder ta makale tana wani turo baki tace"oh oh"..daria sosai Bobby ya saki har yanxu fuskanshi hade da nata..wani irin mashahurin nishadi yaji yana saukan mishi ta ko ina kmr bashine dazu kunci suka mai zucia ba..wato Allah dai shine mai yanda yaso kuma a lokacinda yaso..bayan ya gama dariarshi ya raba jikinshi da nata tareda duba agogon hannunshi nan take ya wara ido cikeda mamaki ganin time ya wuce har haka..juyawa ya sakeyi yana kallonta har yanxu bata bude eyes dinta ba..shi duk bai gaji da ganinta ba wlh..ya zama dole ma yaje ya hura wuta shidai asa rana ayi ayi a daura a kawo mashi ita gidanshi don bazai iya jurewa ba anymore..hakurinshi ya kare don haka kawai asan yanda za’ayi dashi shidai..hannunta ya kama yana kallon yanda har yanxu eyes dinta ke rufe yace"love to ki bude idon naki muyi sallama mana"..shoulder ta sake makalewa tana girgiza kai..hands dinshi ya hada wuri daya alaman begging yace"Aysher please mana..ki tausaya min please"..bude idanun tayi a hankali tana kallonshi sai kuma ta bude kofar da sauri ta fita daga motar har tana hada hanya..wani kunyanshi taji ya rufeta wlh..sam bazata iya hada idanuwa dashi ba ita dai..Bobby kam relaxing yayi nan cikin motar yana binta da kallo har ta shige gate dinsu...ajiyar zucia mai karfi ya sauke yana sake godia wa Allah daya nuna mashi wnn rana..shikam babu abunda zaima Allah sai godia..hakika an gama mashi komai na dunia saidai fatan cikawa da imani kuma..driver na ganin fitarta ya koma ciki ya tada motar suka tafi yayinda Bobby ke jingine da seat yana ayyana yanda zaije ya takurama kowa har ansa mashi ranarshi..kuma bada nisa yakeso asa ba shi in ta nashi ne ma nan da two months yakeso ayi komai a kawo mashi matarshi.
Yana shiga gida ko flat dinshi bai shiga ba ya fara shiga flat din Mummy..har ta fara bacci shigowan nashi ta farka ta shiga dubanshi da mamaki tace"lafia dai koh?.."zama yayi a gefenta yace"ba lafia ba Mummy..mgnr sa ranar nan ne dai"..da mamaki Mummy take kallonshi tace"Bobby yaushe ka zama mara kunya ne wai?.."turo baki yayi yace"Mummy ba rashin kunya bane kawai nidai na gaji da jira ne..nidai dan Allah kiyi mgn dasu in two months time nakeso ayi komai plss"..tace"shi kuma ginin gidanka daka ajiye ka denayi fa?..kana ganin zaka iya karasa shi in two months time?.."da sauri yace"Mummy ai finishing ne kadai ya rage and in 4 weeks time nasan za’a gama kawai kice musu nidai banaso ya wuce two weeks"..ha6a Mummy ta kama tace"innalillahi wainna ilaihi rajiun"..sake marairaice mata yayi yace"Mummy please"..kallonshi kawai Mummy keyi tace"ikon Allah"..ya sake bude baki zaiyi mgn tace"tashi ka barmin daki kafin ranka ya 6aci wlh..yaushe ka zama mara kunya haka ne"..mikewa yayi yana turo baki yace"Mummy ni ba rashin kunya nake ba"..tace"to wuce ka barmin daki idan ba haka ba ince shekara guda za’a sa ba wata biyu ba"..ya sake bude baki zaiyi mgn tace"nace ka fita daga dakina Bobby"..sum sum ya juya ya fita daga dakin yana kunkuni..shifa duk basu san halinda yake ciki bane..da sun san abunda yake going through da basu tsaya yi masa kwane kwane ba wlh..he’s kind of desperate..he’s eager..shi gane yakeyi idan ba’ayi komai da wuri ba tana iya dawowa nan gaba tace bata sonshi kuma..har yanxun there is this insecurity a tare dashi amma sun kasa ganewa.
Lamido kuwa da gudu gudu ta koma hostel kai tsaye ta shige room dinsu tareda fadawa gado tanata doka murmushi kai kace mahaukaciya ce sabon kamu..wani irin excitement taji ta tsinci kanta a ciki all of a sudden..wato Allah yayi ma Proprietor baiwar iya kalamai sai kace abunda ya karanta knn..yanda yake tsara mata love words abun har mamaki yake bata yanda baya taba running out of them..gashi da kirki da iya kula da mace snn kuma uwa uba yana yi mata sonda tasan duk dunia babu maiyi mata irinshi idan aka dauke parents dinta..bata san how and when ta fara sonshi ba kawai lokaci daya taji tana sonshi itama kuma zata iya auranshi ko don sbd wnn son da yake mata..ta lura he is super romantic dan yanda yayi wrapping dinta a chest dinshi daxun kadai ma abun tsayawa a rai ne balle kuma wnn maganganun da yayita fada mata wanda sune suka bijiro da nata son itama har ta kasa rikewa ta sanar dashi..she remember the smile on his face lokcinda ta furta tana sonshi..she remember how he pecked her kawai saita saki murmushi mai sauti..gaskia Dr Bobby is amazing..he is one in a billion and duk macen data aureshi will be considered as a lucky girl..tayi zurfi sosai cikin tunaninta har bata san yaushe Billy ta shigo dakin tana mata mgn ba..saida ta daddage ta daka mata duka snn ta dawo hayyacinta..ta mike zaune tana waji daure fuska tace"meye haka?.."zama Billy tayi nan kusa da ita tana kallonta with smile tace"bestie bani labari dan Allah..what’s the good news?.."murmushi Aysha ta saki tana wani kallonta ta gefen ido tace"who is ur bestie?.."Billy tace"to yi hakuri bestyn Sa’eed..bani labari inji what’s the secret behind wnn beautiful smile din naki?.."gyara zama Lamido tayi tana dubanta still face dinta da murmushi tace"hmm Billy u wont believe this..wai nice yau da kaina na bude baki nace ma proprietor ina sonshi..can u believe this?.."tagumi Billy tayi tana dubanta da murmushi tace"ai dama kin dade da fara sonshi ganewa ne bakiyi ba..bani labari in de tadail plss"..Lamido tace"aikam dai daxu bansan ya akai ba kawai sai jin bakina nayi yana furta i love u..kuma wlh Billy da gaske sonshi nake..ya samar ma kanshi special wuri a cikin zuciyata har mamakin abun nake..it happen so fast"..murmushi Billy ke saki kai kace itace Proprietor tace"ai dama na fada maki mutumin nan karshe ne..ni tun daga yanda naga yana miki a hospital nasan ba karamin sonki yake ba sbd bai iya 6oyewa a ko ina"..zama Lamido ta gyara ta shiga bata labarin komai daya faru in detail..Billy tayi tsit tana sauraronta banda murmushi ba abunda take saki..Allah ya sani ita dama ta dade tanama qawat tata sha’awar auren proprietor sbd mutum neshi na kwarai..yanada duk wasu qualities da mace take nema a wurin namiji and above all yana sonta fiyeda yanda yake son kanshi..labari sosai Aysha ke bata tana yi tana blushing ita kanta mamakin yanda farat daya ya mamaye ilahirin zuciyarta take..ko daxu da safe bataji wnn feeling din game dashi ba amma yanxu gasu nan sai rushing sukeyi zuwa heart dinta kmr zasu fasa ta..so sosai taji tana mashi kusan fiyeda wanda tayi ma Professor Ahmad...saida ta gama labarinta tsaf Billy ta dauki waya tana searching contact din Sa’eed tace"Sa’eed needs to hear this..i cant believe Lamido is in love with Proprietor..what a miracle!.."
Jama’a biki dai ya kusa sbd haka kowa ya fara shiri zamuje har Gombe mu gwangwaje💃🏻💃🏻💃🏻
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
50
Soyayya mai karfi ya shiga tsakaninsu tun daga wnn ranan..Lamido har mamakin yanda take mugun sonshi take..she loves him to the moon and back kmr yanda yake fada mata..kawai gani take babu macen da ta kaita sa’a data sameshi..yana sonta sosai and ya iya kula da mace sosai ba kadan ba..yanda yake treating nata yasa ko kusa bataso taga wata ta ra6eshi don yanxun zasu samu matsala..kulawa takeyi da abunta yanda ya kamata don da gaske bazata so ta rasashi ko tayi sharing dinshi da wata ba..duk wani abu da tasan bayaso ta bar yinshi wanda yakeso kuma tanayi don ta faranta mishi..sbd tsabar nutsuwa yanxu su Lamido kullum hijab ake sawa babba idan an shigo school ta cire..tana sonshi sosai kusan duk wanda ke tareda ita sun san da haka ga kuma kishi da take dashi don akwai ranar da kiri kiri tace bazai duba wata mata ba wai tunda ta shigo sai kallonshi takeyi..haka nan ya hakura bai dubatan ba saida ta bar office yasa aka sake kiranta..farin ciki sosai yake ciki na samun soyayyarta da yayi shiyasa har kullum bazai gaji da yima Allah godia ba...before su gaka Clinical Posting kusan yan asibitin kadan ne basu san Dr Bobby zai auri Lamido ba sbd yanda suke nuna tsantsar caring wa junansu is something else..wani lokaci kota rigashi tashi bata tafia har saiya gama da patients dinshi snn ya maidata hostel..abun nasu is so so interesting sai ma wanda ya gani..a haka har suka kammala posting suka koma makaranta.
A hankali ta turo office dinshi ta shiga fuskan nan ba fus ganin yana tareda secretary dinshi da kuma wata da bata san wacece ba a office din..sake tamke fuska tayi ta karasa ciki rungume da hannayenta ta karasa ciki..tunda ya dago idonshi ya kalleta yasan akwai daru yau..yanda ta hade ran nan yasan drama ne zasuyi shi ba karami ba..File dake hannunshi ya mikawa matar dake gabanshi tareda sallamarta yace suje zai sake namants..ba musu suka bar office din Lamido ta shiga karasowa ciki har yanxun fuskan nan ba sarari..tsayawa tayi gaban desk dinshi tana mishi kallon tuhuma tace"who are they?.."dan wara ido yayi yana kokarin danne daria yace"secretary dina ce baki gane ba kuma?.."yana rufe baki tace"to na meye zasu wani shigo office dinka su zauna?.."kallonta kawai yake yana kunshe daria yace"to yi hakuri"..harara ta watsa mashi mai kyau tana sake dinke fuska tace"Kuma dayar hadda wani zuwa da dingilallen skirt..nidai bana so kana tara irin wayan nan mutanen a office dinka bakasan ‘yan iska bane koh?.."yana kallonta yace"baby ba tarasu nakeyi bafa..bakiga aiki ne ya kawosu ba?.."sake rungume hannu tayi ta zauna tana turo baki tace"nidai banaso..dama da aiki suke fakewa suzo suyita kallonka mana"..daria sosai ya saki jin kalamanta..har gobe wani extraordinary farin ciki yakeji idan yaga tana kishinshi haka..abun na qayatar dashi sosai..yanxu matsalanshi daya shine bikinsu da akace dole saita gama makaranta za'ayi..waziri da kanshi yace bazai ma jema da Lamido mgnr ba sbd yasan amincewa zaiyi bayan kuma ba haka sukaso ba..kokarin dakatar da dariyarshi yayi yana kallon yanda saura kiris ta fashe ya kama hannunta yace"to kiyi hakuri baby insha Allah bazasu sake zuwa ba..babu mai sake kallon miki ni kinji"..baki ta murguda tana hararanshi shi kuma yacigaba da kallonta full of affection yace mata"C'mon smile mana..da gaske sun dena zuwa daga yau and ko suna zuwa ma babu ruwana dasu you'll always be my one and only woman..baby I love u so so very much..i love u alot"..murmushi itama ta saki dimples dinta suka fito sai wani blushing take tace"nima da gaske Ina sonka..ban ta6a son wani namiji kaman yanda nake sonka ba Allah..i love u sosai"..gyara zama yayi yana marairaice mata yace"yanxu ya mgnr mu na daxu?.."itama marairaicewa tayi kafin tace"Sir ni bazan iyaba"..tun kafin ta karasa ta katseta da fadin"i told u ki bar kirana da sir din nan bakiji koh..am not ur sir for God's sake am ur partner..ur life partner so please ki bar kirana da wnn sir din is so irritating"..murmushi ta saki tana kallonshi ta wani kashe murya tana karkata kai tace"can i call u partner then?.."murmushi ya saki shima yana kallon eyeballs dinta yace"U can call me anything amma banda sir"..yana rufe baki tace"alright then daga yau ka zama partner kuma kaima dole kace mun partner"..makale mata shoulder dinshi yayi yace"No u are my baby..yanxun enough talking about that..ya mgnr mu na daxu?.."sake langabewa tayi tace"partner bazan iya bafa..kawai sai inje incema Lamido ayimun aure kafin na gama school"..tasowa yayi daga inda yake ya dawo kusada ita ya zauna suna facing din juna yace mata"partner yanxu bazaki tausaymin ba?..for how many months kikeso muyita zama a haka for God’s sake..if ke zaki iya jurewa ni bazan iya ba pls..na gaji da zama wothout u i want to get married"..baki ta rufe tana daria tace"partner rashin kunya fa"..yace"ba wani rashin kunya am saying the truth..ke baki ganin kokarina ma?.."..kama hannunshi tayi tana kallonshi in a pleading tone tace"nidai kayi hakuri dan Allah..bazan iya ba"..hannunshi ya zame daga nata tareda mikewa ya koma seat dinshi..kawai bazata gane bane shi kadai yasan halinda yake ciki..idan saita gama makaranta nan da almost four months fa ake mgn..dole ma yasan matakinda zai dauka gaskia..ita Mummy da anyi mgn kullum sai tace bai gama gidanshi ba amma yanxu ai ya gama gidan nashi tunda dama fininshing kadai ya rage to me ake jira kuma idan dai baso suke another sugar daddy yazo ya sake mishi gaba da ita ba..marairaicewa ta sakeyi itama kafin tayi mgn Nur ya shigo office din da files a hannunshi..yana ganinta nan zaune yayi wani saurin juya baya kmr wanda yaga abun kunya yace"A’uzubillahi Subhanallahi na shigo at the wrong time"..wani kallo Bobby ya bishi dashi yanajin kmr yaje ya rufeshi da duka..Lamido dai na zaune tana daria dan da gaske draman dake tsakaninshi da abokin nashi ba karamin daria yake bata ba..sake juyowa Nur yayi yana kallon Bobby da wani shegen smile yace"sorry for the interruption guys..will come back some later"..har ya juya zai fita Aysha tace"Sir ka dawo plss..dama ni tafia zanyi"..tana rufe baki Bobby yace"you won’t go anywhere until we finished our discussion"..kallonshi tayi taga ya hade giran sama dana kasa dan haka bata sake mgn ba ta gyara zama tana kallonsu..ta fuskanci shima ba karamin rigimamme bane wlh..at times ma sai taga kmr yafita rigima..juyawa yayi ga Nur da har yanxun yake tsaye rikeda files a hannu shi bai shigo ciki ba kuma bai koma waje ba..saida ya sakar mashi wani harara kafin yace"if u like ka karaso muyi abunda zamuyi as u can see ba zaman banza nakeyi ba"..da sauri Nur yace"ni din banza ince kana zaman banza bayan da idona naga babban aikin da kakeyi..ai ka wuce a kiraka da mai zaman banxa mr romeo"..sake daure fuska Bobby yayi baice mishi komai ba har ya karaso seat dake opposite to her ya zauna ita dai kanta na kasa sai ji tayi gogan nata yace ta koma kan sofa ta jirasu..dan dagowa tayi ta kalleshi tace"sir please..sorry i mean partner please inje anjima sai in dawo"..kallonta yayi yana jajjada mata ki dawo fa da idanunshi..murmushi ta saki tareda gyada kai hadi da lumshe ido meaning she will definitely come back..daga haka tayi sallama da Nur ta bar office din..tana fita Nur ya sauke wani ajiyar zucia yana shafa gemunshi yace"muma dai muzo mu fara love din nan..very soon zakaji nima na hau network wlh..bazanyita zama kuna kasheni da salon love dinku ba kaida Lamido"..harara Bobby ya watsa mashi kafin yace"abunda ya kawoka knn dama?.."girgiza kai Nur yayi tareda daukan files daya shigo dasu ya mika masa ya fara dubawa..shi Kuma Nur banda kallonshi yana murmushi ba abunda yakeyi..mamaki sosai yake na yanda abokinshi ya zama mastern soyayya kmr dai ba shine da yake cewa bazai iya soyayya da diyar kowa ba wai it's a waste of time and resources..yanxun sai gashi tsumu tsumu yana soyayya da Lamido kmr ba Dr Bobby ba shiyasa har kullum bazai dena mamakin yanda ta shigo rayuwarshi farat daya kuma ta canxa mishi ita ba.
Da dare ya shigo parlon Mummy cikin wani baqin yadi daya haska skin dinshi sosai sai baza qamshi yake abunshi...Mummy da aunty sumy na zaune sai faman listing abubuwan da zasu fara siya na lefe suke don shirye shirye sosai sukeyi na biki da baifi saura few months ba..ya karaso ciki ya zauna yana kallon list din da suke yace"Mummy har yanxu list din bai kare bane?.."Mummy tace"ai list bazai kare ba Bobby kasan sha'ani irin wnn wahala ne dashi..idan ba list din akayi ba sai kaga anxo an manta da wasu abun ba'a siyo ba"..dakatawa tayi tareda dagowa tana kallonshi kafin tacigaba"wait..tun yaushe ma nace ka kawota inason mgn da ita kaki?.."shafa kanshi yayi yace"Mummy ba laifina bane bafa..wai kunya takeji bazata iya zuwa ba"..girgiza Kai Mummy tayi tace"to zan kirata da kaina in fada mata"..mikewa yayi ya zuba hannunshi cikin aljihu yace"zan dan fita Mummy"..Mummy tace"to a dawo lafia"..aunty sumy dake ta sauraronsu tun daxun tace"duk wnn wankan nata ne knn?.."dan 6ata rai yayi yana kallonta yace"ke waya fada maki haka?..ni ba wurinta zanje ba"..aunty sumy ta dago tana kallonshi da murmushi tace"ai ba zama zanyi har sai kazo kace aunty na tafi wajen Lamido snn zan gane wajenta zakaje ba"..zuyawa tayi tana duban Mummy tace"dan Allah Mummy baki lura duk yasa manyan kaya wajenta yake zuwa ba?.."dagowa Mummy tayi tana murmushi tace"nima dai na lura Sumayya..ni bansan yaushe ma ya fara sa manyan kaya ba shida kullum cikin suits yake kaman ba bahaushe ba"..Mummy na rufe baki Bobby daketa faman smiling ya dan kwabe face dinshi yace"Mummy ni ba bahaushe bane mana..am Igbo"..hararanshi Mummy tayi tace"for where?..kai bafulatani ne"..aunty sumy tace"rabu dashi Mummy..kaje ka fadawa Aysha haka kaga idan bata fasa aurenka ba"..murmushi yake yana girgiza kai yace"nasan maganinki ai..babansu Miemie kawai zan kira ince ya dawo daga England ya daukeki ku koma gidanku tunda takura mana kikeyi"..daria kawai tasa tacigaba da aikin gabanta jin ya ambaci baban su Miemie..Mummy ma bata sake mgn ba shi Kuma yayi musu sallama ya fita yanata smiling..da mgn daya yayi maganinsu...yana fita ya nufi motarshi da yasha car wash sai kyalle yake ya bude driver seat ya shiga tareda tayar da ita ya fita daga gidan..these driver dinshi ba karamin hutawa yake ba sbd almost everyday shi yake driving kanshi yanxu especially idan yasan wajenta zaije..shifa gani yake ana daura musu aure ma driver office kadai zan dinga kaishi amma duk wani personal al'amuranshi da kanshi zai dinga zuwa yanayi ko don sbd matarshi..shi bazai iya bari driver ya tuka mashi mata ba har ga Allah..kawai gani yake zaiyita kallonta ne ta mirror shi kuma da wani namiji ya kalleta gwara shi a kwana ana kallonshi bai damu ba...driving yake yana murmushi gami da shafa Kai sbd tunowa da ita da yayi..har kullum sonta karuwa yake a cikin ranshi musamman yanxu da yake receiving equal treatment daga wurinta..daxun rigima sukayi sosai sbd tayi mgn a sauko musu da biki tace bazata iya ba shine yayi zucia har ya baro school din bai nemeta ba yasan tana can ta cika fal tana jiran yaje ta sauke mashi...har ya isa college dinsu bai bar tunawa da ita yana murmushi ba..daidai gate dinsu yayi parking snn ya dauki waya yayi dialing numberta don ko sanar da ita zaizo baiyi ba..tana dauka ko jira tayi mgn baiyi ba yace"baby am outside"..ta wani hade rai ita bata yadda ba ya 6ata mata rai tace"ni banida lafia"..murmushi yakeyi yace"eyya meya sameki?.."a shagwabe tace"fever"..yace"alright let me come inside in dubaki"..tun kafin ya rufe baki tace mishi"nidai No..salon ka shigo duk suyita kallonka"..yace"then indai bakiso in shigo ki fito..na baki 3 mins idan ban ganki ba am coming inside"..daga haka ya kashe wayar yana cigaba da murmushin wnn rigiman nata...suna gama wayar ta juya tana kallon Billy dake kunshe daria tace"munafuka"..daria Billy ta fashe dashi harda su tafa hannaye tace"munafurcin me Kuma nayi Lamido?.."harara ta watsa mata tareda mikewa zuwa wardrobe dinsu ta dauko zumbulelen hijab ta dora kan jean da Jessy dake jikinta as always snn ta fita daga dakin bayan ta Maka ma Billy harara..ita dai da kallo ta bita tana cigaba da murmushi tace"wai Ina matsayin matar yayanta takemun wnn iskancin..Lamido Allah ya shiryeki".
Tana fita Kai tsaye inda ta hango motarshi ta nufa..shi Kuma yana zaune ciki yana kare mata kallo don wurin akwai haske dal kmr ba dare ba..hijabinta yakai qasa amma Saida ya fahimci jean da riga ne a jikinta sbd fitowa da wandon yayi ta kasa..lumshe Ido yayi ya bude tareda jingina kanshi da kujera yana cigaba da kallonta har ta iso inda yake..ta bude motar ta shigo snn ta maidashi ta rufe tanata wani ciccin magani ta juya tana kallonshi..murmushi ya Kara saki tareda kama both hands dinta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace"menene?."turo baki tayi tace"Pogba"..idanu ya ware da kyau a kanta cikin mamaki yace"Pogba Kuma?.."Kai ta daga mishi akamar eh nan take kuma ranshi yaji ya 6aci..shi duk tunaninshi sbd ya wuce bai nemeta bane daxun take fushi ashe abun nata ne ya motsa bai saniba..sake hannunta dake cikin nashi yayi snn ya sake dubanta cikin kokarin 6oye 6acin ranshi yace"what about him?.."a dan fusace tace"wai mutumin nan mu zai wani tozarta ya bar Manchester United..kasan yanxu wai Juventus..."bata samu sararin karasawa ba sbd wani kallo da ya shiga binta dashi ita sai yanxu ma ta tuna ashe fa tayi kato6ara..innalillahi wainna ilaihi rajiun ta fada cikin ranta.."wane ruwa na kuntowa kaina ni Aisha?.."ta fada a hankali yayinda take kallon yanda yanayinshi ya sauya lokaci daya..dunia idan akwai abunda ya tsana bai wuce wnn Pogban ba..ya tsaneshi to the extent that yakejin duk wani dan Manchester da Yan ball din ma kaf ya tsanesu..dukda cewa shi Pogban musulmi ne amma da gaske tsanarshi yakeji sbd wnn son da yaga tana mashi.. marairaicewa tayi sosai kmr wadda ke dab da fashewa da kuka tace"partner am sor"..bata karasa ba ya dora finger dinshi kan lips dinta yana kallon cikin Idonta yace"u don't have to apologize"..girgiza kai ta shigayi tana kallon 6acin rai Karara kan fuskanshi tace"nidan am sorry plss..wlh mancewa nayi"..baice mata kala ba ya dauke finger dinshi daga bakinta tareda komawa yayi relaxing kan seat din da yake..hankalinta taji ya tashi sosai tasan duk yayi irin wnn fushin da ita to abu ba karamin 6ata ranshi yayi ba..shaf mancewa tayi da wnn kishin nashi wlh da bata ma fara ambaton Pogba a gabanshi ba sbd yanda ya tsaneshi..matsawa tayi jikinshi sosai tareda Kai hannu ta kama left hand dinshi murya can kasa tace"partner"..banza yayi mata baice komai ba..ta sake cewa"partner talk to me manaa..nace am sorry fa"..still baiyi mgn ba sai ma hannunshi daya zare daga cikin nata ya shiga kokarin bude motar zai sauka kawai yaji ta rungumoshi ta baya tana cewa"partner am so very sorry plss..am sorry I hurt u amma ba da gangan nayi haka ba kasan I love u"..lumshe Ido Bobby yayi yanajin heart beat dinshi na sauyawa lokaci guda..kawai sai yaji wasu irin abubuwa sun shiga zagayawa cikin jini da tsokar jikinshi baisan lokacida ya sauke wani gauron numfashi ba..yana jinta a jikinshi yaji duk 6acin ran nashi yayi disappearing sai Kuma wani shauki daya tsinci kanshi a ciki na musamman...tunda yake da ita bata ta6a hugging dinshi haka ba sai yau..this very moment..wani additional sonta yaji yana sake ciko zuciarshi kawai sai ya juya tareda dagota daga jikinshi yayi cupping fuskanta yace"Love why plss..why do u always wants to talk about him..why do u love him this much?.."hannu takai itama tayi cupping nashi face din tana girgiza mashi Kai tace"I do not love him..I love u..only u baby..I love u more than any other person in this whole wide world..u are my soul partner,my future husband,my babies daddy and I love u so much"..sbd tsabar jin dadin kalamanta baisan lokacida ya sake maidata jikinshi yana sauke ajiyar zucia da mugun karfin gaske ba..wani irin sanyin dadi yaji yana ratsa zuciarshi tamkar an sauke mashi mountain daga ciki..these words means the entire world to him..it means a lot to him and he wouldn't mind tacigaba da fada mashi irinsu daga nan har mahdi ya bayyana..kawai baiso ta dena fada ba..sai yaji kaman su dawwama nan wurin tana fada mashi the most sweetest words daya taba saurara all his life..rumgumeta yayi sosai sai sauke numfashi yake kafin ya dagota a hankali yakai lips dinshi ya manna mata peck a forehead dinta yana kallonta wearing a very wide smile kan fuskanshi yace"I love u more baby..I love u like..."kasa karasawa yayi sbd gani yake babu wata kalma da zatayi daidai da son da yakejin yanayi mata a mizani saidai in zuciyarshi zai bude mata ta shiga ta gani kawai idan ba hakaba duk yanda zaiyi bayani bazata ta6a ganewa ba..hade fuskanshi yayi da nata idanunshi rufe yace"I beg u in the..."bata bari ya karasa ba itama ta dora two fingers dinta akan lips dinshi tana kallonshi tace"I promise not to talk about him ever again..am sorry"..sake rungumeta yayi yana sauke ajiyar zucia..bayan few minutes ya rabata da jikinshi yanata doka murmushi ya kalleta kafin yayi mgn tace"I love u"..ya lumshe Ido ya bude shima yace"I love u more baby..and ba na hanaki fitowa da wando ba?.."kallonshi tayi ta kalli jikinta tanaso taga ta Ina ya gane wando ne a jikinta amma bata ganiba don hijabinta ya rufe har kasa ne.. dan marairaicewa tayi tana dubanshi tace"partner naga ba wani wajen zanje ba ai..wajenka zanzo"..yace"ko wurina ban yadda kina zuwa anyhow ba manaa.. don't u know u have this beauty and figure da bai kamata kina fita da anyhow dressing ba?.."langa6e Kai tayi a hankali tace"to kayi hakuri na dena"..sake pecking goshinta yayi tareda komawa seat dinshi ya zauna yana cigaba da kallonta with a smile yace"thank u so much love..I love u"..murmushin takeyi itama kafin tace"I love u more"..girgiza kai yayi yana kallonta yace"no I love u more"..itama ta makale shoulder dinta tace"nima I love u more"..murmushi kadai Bobby keyi ya kasa dena kallonta..itama kallonshi takeyi this time around ba tareda wani tsoro ko fargaba ba..bayan almost 10 mins of silence and starring yace mata"Mummy nata damuna fa in kaiki wajenta..yaushe zaki shirya muje?.."dan karya wuta tayi tana dubanshi har yanxu tace"partner kunyanta nakeji nidai"..yace"then kiyi mgn da Billy kuje tare amma da gaske Mummy tace she wants to see u..kilan akwai abunda takeso kuyi discussing da ita"..gyada mishi kai tayi a hankali alamar ta amince.
Sorry for the late update pls..kunsan sallah ya kusa so ina can ina kujiba kujiba😅
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
51
Washegari da around 4 ya gama shiri tsaf don zuwa daukosu kamar yanda sukayi da ita jiya..tun daxun yake tsaye gaban mirror sai faman kalkale yakeyi kamar mace..wayanshi ne ya shiga ringing yana dubawa yaga Rayhan kan screen dan haka ya saki tsaki tareda ignoring call din har ya gama ringinshi dinshi bai dauka ba..wani kiran ya sake shigowa still bai dauka ba yana gama ringing ya dauki wayan da nufin sawa a silent sai kuma kiran Nur ya shigo..fasa sawa silent din yayi tareda answering call din yana cewa"what?.."daga daya 6angaren Nur yace"dole kace haka mana dan rainin hankali kaman ba kaine Lamido tayita ladabtar mana da kai ba"..tsaki Bobby ya saki yana ta6e baki yace"is this why u called?.."da sauri Nur yace"no plss..ina cikin matsala ne wlh almos similar to wanda ka shiga a kwanakin baya and i need ur help"..ajiye comb dake hannunshi yayi tareda daukan keys dinshi ya fita daga dakin kafin yace"then ka bari idan hadu gobe sai muyi mgn amma ba a waya ba"..yana rufe baki Nur yace"no plss nidai kayi alqawari zaka taimakamin"..dan girgiza kai yayi yana mamakin wnn sudden behavior na abokinshi yace"wai kayi gamo ne hala?..wane irin alqawari zan daukan maka kuma?.."Nur yace"alqawari dai kmr yanda kaji na fada"..gyada kai yayi yace"then nayi alqawari shknn?.."Nur yace"shknn sai munyi mgn tomorrow"..yace"ohk"..snn ya kashe wayar yana girgiza kai..wani lokacin Nur sai yayita behaving kaman wani karamin yaro wlh..kai tsaye yana fita parlon Mummy ya shiga yayi sallama da ita snn ya fita don zuwa dauko su Aysha daga hostel..yana hanya ya kira ya sanar da ita tahowarshi don haka kafin ya karasa sun gama shiryawa tsaf shi kawai suke jira..bayan ya isa ya sske kira ya sanar mata ya iso basu 6ata lokaci ba suka fito tareda Billy..relaxing yayi nan cikin mota yana kare mata kallo as usual duk yazo wurinta dama kafin ta isa gareshi sai ya gama kalleta tsaf shiyasa ko hijab tasa yake iya gane abunda take sanye dashi ta ciki..doguwar riga ne a jikinsu iri daya saidai color daya banbanta amma daidai da hulunan dake kansu iri daya ne likewise takalmansu..ya fuskanci qawance ne tsakaninsu na gaske bana wasa ba and suna son juna tsakani da Allah ba wani mai zucia biyu a cikinsu..kafin su karaso as usual ya bude mata front seat suna karasowa ta shiga Billy kuma ta shiga backe seat bayan sun rufe kofa ya sake tada mota suka bar cikin hostel din...suna daukan haya ta juya tana kallonshi da wani smile daya kusa sashi zubar dasu a titi sbd tsabar rikitashi da yayi tace"partner kayi kyau"..kallonta ya danyi sai kuma ya saki murmushi yana cigaba da driving dinshi ita baima san yanda zai bayyana irin kyawun da tayi mashi bane..kawai shidai baison tana yin shiga irin haka tace zataje wani wurin amma bazai iya hanata ba yau tunda anko yaga sunyi ita da Billy amma ko Allah yasan shidai baso yakeyi ba..sam baison tana fita babu hijab sbd yanda yake ganin kmr idanun kowa kanta zasu dawo don a ganinshi babu namijin da zai kalleta baiji ta birgeshi ba ko don kyawun fuskarta ko kuma surar jikinta...dan turo baki tayi tana kallonshi tace"bazaka ce nima nayi kyau ba koh?.."juyawa yayi ya kalleta for like 2 secs kafin ya sake maida hankalinshi ga driving da yakeyi yace"kinyi more than kyau"..harara ta dan watsa mashi alaman bata gamsu da abunda ya fada kuma har yanxu bata bar turo mishi baki ba..Billy dake sauraronsu tana murmushi tace"sir ina yini"..kallonta ya danyi ta mirror kafin yace"lafia lau Bilkisu meyasa bakiyi mata fada ne?.."Billy tace"Allah inayi mata sir kawai dai halin nata ne sai ita..batajin mgn wlh"..tana rufe baki Aysha ta juya tana kallonta tace"kiji tsoron Allah wlh..haka kikaje kika hadani da Ammi ma kikasa taitamun fada ba tareda laifin komai ba"..murmushi kawai Billy tayi batace mata komai ba shima murmushin yayi hade da girgiza kai ba tareda cewa wani abu ba..ganin yanda suka maidata kamar wata yar iska tayi mgn sunyi banza da ita sai taja bakinta ta tsuke itama tana harare harare ita a dole anyi mata ba daidai ba..har suka isa gida ba wanda ya sake mgn cikinsu..ciki ya shiga yayi parking kmr ko yaushe snn Billy ta fara budewa ta fita don ta basu space..itama tana kokarin budewa ta fita ya kama hannunta da sauri yana langabar mata da kanshi yace"bana hanaki fitowa a haka ba?.."langabar da nata kan tayi itama kafin tace"kaga anko fa mukayi da Billy ai babu dadi ince mata bazan sa ba"..janyota yayi jikinshi sosai yana kallon eyeballs dinta yace"sai kice mata na hanaki fita a haka ai zata fahimta amma kin kama kin fito a haka yanxu Allah kadai yasan adadin mazan da zasu kalleki kafin mu koma"..kallonshi take a hankali tace"partner kaima fa dan bakaga kyau da kayi bane nima sai ince mata zasuna kallonka mana"..hannunta ya kama ya dora saitin heart dinshi yace"ko sun kalleni it won’t change a thing sbd my heart beats for only u and u alone..i don’t think har dunia ta tashi zan samu macen da zan sota kmr yanda nake sonki..ina sonki sosai nefa..try and understand mana"..kallonshi kawai Aysha keyi tana sakin murmushi cikin ranta kuma tana godia wa Allah daya bata shi a matsayin miji..dukda basu riga sunyi aure ba tana da tabbacin za’a jima ba’a samu macen da tayi dacen miji dake sonta irin yanda yake sonta ba..soyayyanshi is genuine wanda ta tabbata yafi wanda ita take mashi nesa ba kusa ba...ganin kallon da take mishi tana smiling ya dan hura mata iska a ido yana kallonta yace"what are y thinking about?.."a hankali tayi pointing nashi da finger dinta tace"you"..kallonta yayi kafin ya samu damar cewa wani abu yaji saukan warm lips dinta akan forehead dinshi ta manna mishi kiss that last for almost 3 mins kafin ta janye bakin a hankali tareda bude motar ta fita tana sake kasheshi da wnn smile din nata...Bobby mutuwan zaune yayi a wurin yana bin bayanta da kallo har suka shiga cikin gidan itada Billy..lokaci guda moo dinshi ya sauya gaba daya sai kace wanda yasha wani abun...wnn kiss da tayi mashi ba karamin hargitsa mashi lissafi yayi ba..jikinshi ya mutu murus wanda hatta numfashi da kyar yake shaqansa..lumshe ido yayi tareda komawa yayi relaxing kan kujera yana sauke ajiyar zucia..wani irin yanayi yakeji tattare dashi wanda yafi duk wanda yasan yanaji a baya..jikinshi yayi sanyi qalau da har ya kasa daga legs dinshi balle ya samu ya fita daga motar..haka yake fama da wnn desire din these days ko kallonta ya fiye yi saiya samu matsala ballantana kuma yanxu da tayi mashi abunda bata ta6a yi mashi ba tunda suke tare..kawai addu’a yake Allah yasa bata ta6a yiwa wani namiji haka ba don a yanda yakeji tsaf zai iya kauce hanya sbd yanda dan abu karami daga gareta yake kai mishi karo..effect sosai wadan nan abubuwan suke dashi a kanshi wanda ya zama mishi dole yayi baya baya da ita don gudun kada azo ana samun matsala..saida ya gama tattara sauran energy dinshi kaf snn ya bude motar ya fita yana takawa a hankali ya nufi cikin gidan..a central parlor suke zaune da Mummy da friend dinta maman Rayhan sai kuma Rayhan din dake zaune gefen Mom dinta tana karema su Aysha dake gaisawa da Mummy kallo...karasowa cikin parlon yayi a hankali bayan ya daure fuska ya shiga gaida Mom din Rayhan kafin itama Rayhan din ta mike da sauri tana kallonshi da wani murmushi tace"Uncle Bobby sannu da zuwa..tun daxun nake jiranka"..kai kawai ta iya gyada mata yana satar kallon Aysha da ko ba’a fada ba yasan kallonsu take..Mom dinta na murmushi itama tace"tun tuni take damuna da mgnrka Bobby kusan kullum haka zamu yini tana kiran Uncle Bobby shiyasa yau dai nace bari mu samu muzo dan ni kaina rabona da mahaifiyarka tun bikin Zahraddeen"..murmushin yake ya iya saki yana gyada kai duk yabi ya diririce sbd presence na Aysha a wurin..Mummy ma ba karamin kunya maganganunsu suka bata ba gashi ta rasa yanda zatayi tayi stopping nasu don haka da sauri tace"to ka wuce ciki idan mun gama gaisawa sai ka maidasu"..kmr abunda yake jira knn ya kama hanyar flat dinshi da sauri..Itama Rayhan da saurin ta mike tabi bayanshi tana cewa"Mommy bari inyi mgn dashi plss"..daga haka itama ta shiga flat din nashi..Mummy ta juya a hankali tana kallon Aysha data kasa jurewa ta shiga binsu da kallo har suka shiga flat din nashi kawai saiji tayi hawaye sun ciko idanunta..wnn kuma wace irin masifa ce?..da sauri tayi kasa da kanta tana kokarin maida hawayen da suka ciko mata ido amma Mummy ta riga ta gani and hakan kuma ya bala’in tada mata hankali..kada fa yaran nan suzo suna samun matsala ta dalilin wnn abun..mikewa tayi da nufin binsu flat din nashi sai ga Miemie da aunty sumy sun shigo parlon tareda ilham da alama unguwa sukaje...Miemie na ganinsu ta karasa kusa dasu da fara’arta tana gaishesu haka ma ilham da hugging Aysha saida tayi sbd farin cikin ganinta..ganin haka Mummy ta dubi aunty sumy dake gaisawa da Mom din Rayhan tace"wuce dasu parlonki su samu su huta kafin na shigo"..ba musu aunty sumy ta kwashesu zuwa flat dinta tareda su Miemie da suketa murna kamar basu ta6a ganinta ba..Billy dai sai kallonsu takeyi tana sake yabawa da kirki irin nasu..ta tabbata Lamido ba karamin dacen samunsu matsayin dangin miji tayi ba basuda matsala ko kadan..Lamido kuwa ji take kaman ana hura mata wuta a cikin jikinta sbd tsabar zafin da taji ya rufeta..ita bataso suka bar parlon ba so tayi su zauna taga iya tsahon lokacin da zasu dauka a dakin nashi basu fito ba..har wani jiri taji kaman zai dauketa sbd tashin hankali..bata ta6a sanin haka takeda kishi ba sai this very moment..kawai ayyanosu takeyi wai suna can suna abunda bai kamata ba kilan ma har kissing juna zasuyi and iya tunanin haka kadai yasa ta kware da yawun bakinta nan take kuma tari ya sarketa kmr zata shide..Miemie daketa faman zuba ma Billy surutu hankalinsu yayi kanta gaba daya suka shiga kokarin taimaka mata..aunty sumy ta dauko ruwa da sauri ta kawo musu Billy ta amsa ruwan ta bata a baki tasha sai kuma tarin ya sake karuwa sbd another kwarewa da tayi da ruwan data sha din..nan take hawaye suka shiga kwararowa fuskanta wanda ko kusa bana kwarewa da tayi bane kawai na ciwon ganin wata mayya tareda namijin da duk dunia batada kamarsa a yanxun idan aka dauke iyayenta...yayi mata ciwo sosai yanda yarinyar ta iya binshi har flat dinshi kuma bai koreta ba..da sauri aunty sumy ta dauko waya ta shiga dialing number dinshi sbd batason dagawa Mummy hankali tunda tana tareda bakuwa..kamar jiran kiran nata yakeyi yana dagawa tace mishi"come to my parlor plss..ur Aysha bansan meya sameta ba"..ai tun bata kai karshe ba ya katse wayar tareda fitowa zuwa flat din nata da sauri..tana shiga yayi toxali da yanda take shaqan numfashi da kyar baisan lokacinda ya karasa tareda zaunawa nan kusa da ita ba..yakai hannu yana kakarin janyota jikinshi da karfi tace"don’t..touch..me"..tsayawa kawai yayi yana kallonta kmr bai gane me tace ba..hannu ya sake kaiwa zai zare nata hannun data rufe hanci da bakinta dashi still ta sake cewa"i said don’t touch me"..kama hannun nata yayi ya janyeshi daga fuskar ita kuma ta daddage ta make hannun nashi tana wani sauke numfashi tana muzurai tarin kuma sai ya tsaya cak kmr dama dai zuwanshi yaje jira..kallonta ya shiga da puppy eyes dinshi ita kuma ta dauke kai tana kokarin maida hawayen da suke sake ciko mata idon..kawai gani take kilan ya dade yana raina mata hankali akan yarinyar...aunty sumy da batasan dawar garin ba sakin baki tayi tana kallonsu da mamaki haka ma su Miemie..kallonta yayi yana marairaicewa yace"aunty kice tayi hakuri plss"..yana rufe baki itama tace"aunty baimin laifin komai ba"..galala aunty sumy ta tsaya tana kallonsu da sabon mamaki..Bobby ya kori su Miemie da yaga sun wani tsaresu da ido kafin ya sake maida dubanshi ga aunty sumy da ido ya shiga yi mata alamar ta rokar mishi ita aunty sumy kawai tasa daria..daria suka bata daga shi har Ayshan wlh..idan akace kuruciya na damun mutum dai sai a hankali wlh..juyawa tayi da nufin ta basu wuri suyi rigimarsu su gama Mummy ta shigo parlon hankalinta gaba daya kan Aysha tace"daughter meya sameki?.."dan murmushi ta kakalo kai a kasa ta girgiza kai alamar ba komai..Mummy tayi shiru tana kallonta kafin tace"to ku taso mu koma parlor tuna baqin sun tafi"..mikewa sukayi ba musu suka sake komawa wancan parlon..shidai Bobby har yanxu hankalinshi bai bar kanta ba...bayan sun zauna Mummy ta danyi kasa da muryanta tace"kiyi hakuri da abunda ya faru kinji?..ba abunda kike tunani bane"..kai kawai ta iya gyadawa Mummy amma Allah kadai yasan me takeji..Allah Allah take kawai su tafi yanda zata samu wankeshi tas da soso da sabulu..nasiha sosai Mummy ta shiga yi musu wanda duk akan abunda ya faru ne tana sake assuring dinta cewar ba komai ba wani abu ne tsakaninta da Bobby ba amma kishi ya rufe mata ido kwata kwata bata yadda ba kawai gani take itama Mummyn yana raina mata hankali ne kmr yanda itama ya raina mata kilan yana soyayya da ita a bayan idanunsu..idan ba haka ba why zai bata such freedom?..why zata samu damar binshi har flat dinshi kuma ba tareda wani shakku ko tsoro ba idan har ba soyayya suke ba?..a takaice sun 6ata lokaci sosai Mummy nata faman musu nasiha ko dalilin da yasa tace tana son ganin nata ma bata fada mata ba..shidai Bobby yana zaune yana kallonta yasan duk wnn 6a6atun da Mummy take da kyar idan tanaji don a yanda yake ganin fuskanta kadai ya isa yasa yasan yau fa mai rabata dashi sai Allah...bayan ta gama musu nasihan da suka zo tafia har ita akayi musu rakiya bakin mota su A’i sai yake ake ana washe hakora irin komai normal din nan nan kuwa basu san ta ciki na ciki ba..ta bude front seat ta shiga Billy ta shiga back seat kafin shima ya shiga ya tada motar su tafi gabanshi har wani faduwa yake sbd tunanin yanda zaiyi ya fitar da kanshi daga wnn gundumemen zargi...har suka isa hostel babu Wanda yayi mgn cikinsu..ita Billy tana zaune back seat tana danna waya yayinda Lamido da Bobby ake kallon kallo a tsakanin juna shi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita yanda yaga tana hade rai ita Kuma tana tunanin Kalan rashin mutuncin da zata mashi sbd raina mata hankali da yayi...yana gama parking a gate din hostel Billy ta bude motar ta fita bayan tayi sallama dashi ta shiga cikin hostel din shi Kuma ya juya a hankali yana kallon Aysha data shiga kici kicin bude motar zata fita amma yasa lock don haka ta kasa budewa..matsowa yayi yana dubanta a hankali yace"baby listen to me plss..I will explain"..tun bai rufe baki ba ta kama masa wani kallo Idonta har ya ciko da hawaye tace"ka cuceni"..juyawa tayi zata fita yayi saurin janyota ya sakata jikinshi murya can kasa yake ce mata"am sorry..am so sorry ki bari inyi maki bayani plss"tureshi ta shigayi tana dukan chest dinshi da duk karfin da Allah ya hore mata ta kasa cewa komai..ganin ba sakinta zaiyi ba kawai ta sake kankameshi tana fashewa da matsanancin kuka..kishi takeji sosai na wnn shegiyar inyamurar yarinyar..bata ta6a sanin kishi bala'i bane sai yanxu..knn shima haka yayita ji duk lokacinda yake ganinta tareda wani?..idan haka ne ma yayi kokari sosai dan ko Allah ya San ita bai zama lallai ta iya irin wancan hakuri da yayi da ita a baya ba..wani irin zafi takeji tamkar an dau zuciarta ansa shi cikin frying pan ana soya mata shi...Bobby dai banda shafa bayanta ba abunda yakeyi..bashi yake kukan ba amma zai iya rantsuwa yana jin sautin kukan da zuciarshi takeyi sbd nata kukan da takeyi..hankalinshi tashi yakeyi sosai..yasan yanda mutum keji idan irin wnn kishin ya motsa and ko kadan baya mata fatan sake experiencing wnn feeling din sbd yasan exactly how it feels..ba fatanshi ta dena kuka kadai ba fatanshi kada Allah ya sake kawo dalilinda zai tada kishinta haka sbd ciwo yakeji idan yana ganinta a irin wnn halin..he loves her to the extent that duk wani abu da zai daga mata hankali baya son yazo kusada ita..gashi dai yanxu ita take kukanta amma yanda yakeji yasan ko ita dake kukan bazata kaishi shiga damuwa ba...dagota yayi a hankali yana share mata hawaye gami da girgiza kai shima kmr zaisa mata kukan yace"stop crying plss..nace maki ba wani abu nefa tsakanina da ita ba"..ture hannunshi tana sauke ajiyar zucia sbd kukan da taci ta sake juyawa zata bude motar yayi saurin dawo da ita yana kallon tsakiyar idanunta a hankali yace"please!..please I beg u"..lumshe Idonta tayi tana goge hawayenta shi Kuma ya matsa jikinta sosai har suna shaqan numfashi juna yace mata"when i say u i mean u baby..only u..duk dunia idan kina tunanin akwai wata mace cikin rayuwata apart from u then u are mistaken..I love only u and u alone..you are the best of all the precious things that have ever happened to me..you owns my heart completely and I love u so much..please allow me to explain things to u"..tunda ya fara mgn kawai ta lumshe Ido tana sauraran yanda yake pouring mata love words din nan ya kamata taji dadi amma Sam kishin dake cinta ya hana mata jin dadin kalaman nashi..kawai imagining take dama sun dade tana shiga flat dinshi kilan har ganinshi ta ta6ayi babu kaya ajikinshi..tunanin haka yasa ta sake kwa6e fuska hade da tale baki zata fara kuka kawai taji saukan warm and cute lips dinshi akan bakinta..ta kwalo idanuwa waje da sauri tana rarraba su kmr dai shege a rabon gado..lokaci daya ta hadiye kukan nata tsaf ta zuba ma face dinshi Ido yanda ya lumshe nashi idon yayi holding dinta da two hands dinshi makes him loos so cute a Idonta..lumshe idon ta sakeyi tanajin yanda ya kasa raba lips dinshi da nata ga heart dinshi dake bugawa very fast kawai saita daddage iya karfinta ta janye bakinta daga nashi tana sauke numfashi...bata sake yadda ko kallon inda yake tayi ba ta bude motar ta fita da sauri har tana hadawa da gudu...Bobby ya dafe head dinshi tareda hada Kai da starring yana sauke numfashi da sauri kmr Wanda yayi tsere..lokaci daya regretting abunda ya aikata ya shigeshi..baisan yanda akayi har hakan ya faru ba kawai shidai yaji bakinshi cikin nata anda daga nan Kuma bai sake tantance komai ba sai abunda yakeyi...shknn yanxu kilan kallon dan iska zata fara mishi amma ba laifinshi bane..Allah ya gani he tried his best abun ne yafi karfin tunaninshi..shi da yake kokari bata hakuri ya sake aikata wani laifin da kilan sai yasha wahala kafin ya damu kanta again...lumshe Idonshi yayi yana furta"innalillahi wainna ilaihi rajiun"a hankali..gaba daya yama kasa tashi balle ya tayar da motar ya tafi..driver dinshi ya kira da kyar yayi mashi bayanin inda yake yace yazo yayi picking dinshi..babu wasting of time yazo wurin Bobby ya bashi keys tareda komawa back seat shi Kuma driver ya tashi motar suka tafi bayan yace gida yskeso ya kaishi.
To habibties ina ganin zamu dakata a nan sai Allah ya kaimu bayan sallah.
Ina ma kowa barka da sallah in advance Allah ya maimaita mana..Allah kuma yasa muyi azumin arfah lafia mu gama lafia.❤️💫
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan diya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
52
Driver na gama parking a gida ya bude motar ya fita yana takawa a hankali zuwa cikin gidan..bai ko lura da Mummy da aunty sumy dake parlor ba yayi wucewarshi flat dinshi..yana shiga ya fada kan gado ba tareda ko takalman kafanshi ya cire ba..haushin kanshi yakeji sosai na abun da yayi..Sam bai kamata yayi hakan ba yanxun gashi baisan ta Ina ya kamata ya fara bata hakuri ba...yana cikin wnn tunani kiran Nur ya shigo wayanshi..ya dauka tareda sashi a speaker ya ajiye daidai face dinshi kafin yace"what?.."tsaki Nur yaja before yace"kaidai kanada matsala wlh banza..are u at home?.."Kai ya gyada tareda cewa"yes"..katse wayar Nur yayi ba tareda yace komai ba shi Kuma ya sake gyara kwanciya tana tunanin abunyi..yasan da kyar idan Nur ba zuwa zaiyi ba tunda ya tambayi ko yana gida amma yasan idan ya fada masa abunda ya faru shknn ya shiga uku da walakancinsa dan tsona ne zaisha a wajenshi tunda yasan halin kayanshi.
Lokacinda Nur ya shigo dakin ya fito daga wanka knn ya shiga closet zai canxa kaya..yana jinshi baice mishi kala ba har ya gama shiryawa ya fito..Nur ya juya yana kallonshi da wani murmushi yace"na Lamido bada kanka a sare idan kaje gida kacewa Mummy ya Fadi"..murmushi Bobby ya saki tareda zama nan kusa dashi yana dubanshi yace"bansan a inda kaji Hausa ba Nur.. duk wani mgn na hausawa ka iya sai kace dai ba inyamuri bane Kai"..daria shima Nur din ya saki yana shafa Kai yace"sai kace dai ba inyamurai bane mu..kaima ba kace kai ba bahaushe bane?.."harara Bobby ya watsa mashi yace"to yanxu nace bahaushe ne ni.. bafulatani ma kuwa"..tun kafin ya rufe baki Nur ya kwashe da daria kmr ta6a66e.. Bobby na jinshi bai kulashi ba Saida ya gaji don kanshi ya bari snn ya sake dubanshi yana cewa"wai Dr Bobby ne yau yake kiran kanshi bafulatani..wonders shall never end"..banza Bobby ya sake yi dashi yanata danna wayarshi..Saida Nur ya gaji da iskancinshi don kanshi snn ya dan rage murya yace"sorry abokina wasa nake Maka"..shidai baice dashi komai ba..shi Kuma Nur dan nustuwa yayi tareda maida hankali gareshi yace"wata yarinya ce nake tsananin sonta wlh Kuma na kasa fada mata"..kallonshi Bobby ya danyi for like 3 secs kafin ya maida duba ga wayarshi dake hannunshi yace"Ina jinka"..dan shiru Nur yayi kmr bazai ce komai ba sai can yace"Bobby pretty nakeso"..dagowa Bobby yayi da sauri yana dubanshi cikeda mamaki sosai yace"are u even listening to ur self?..kaji abunda kace kuwa?.."Nur yace"na sani mana..ce Maka nayi Ina son pretty and I want to marry her"..girgiza Kai Bobby ya shigayi har yanxun yana binshi da kallo irin na mamaki yace"yanxun of all mata dake garin nan ka rasa wadda zakace kanaso sai Miemie da ko secondary school bata gama ba?.."dan daure fuska Nur yayi yace"kasan I don't tell my heart whom to love..kawai idan bazaka taimakamin ba its ok ba sai ka biyo ta wnn hanyan ba"..murmushi Bobby ya saki ya sake duban Nur da mamaki yace"ikon Allah..when did i say that?.."Nur yace"gashi nan ka fara cewa bata gama secondary school ba..ai ba cewa nayi zan fada mata Ina sonta tun yanxu ba..I just want u to know sbd kada a samu matsala nan gaba amma its ok".. daria sosai Bobby ya fashe dashi Wanda rabon da yayi irinshi har ya manta...he can't believe Nur da gaske yake..yanxu of all yammatan Kano ya rasa warce zaiso sai yar karamar yarinyar da batafi 17 years ba..abun ba karamin daria bane..shi Kuma Nur ya cika yayi fal kiris yake jira ya fashe ganin sbd rainin hankali daria ma yake mashi...Saida ya gaji da daria dan kanshi snn ya dan dakata ya kama hannun Nur kafin yace wani abu Nur ya fizge hannunshi yana zabga mashi harara..daria Bobby ya sake yi kafin yace"C'mon sorry mana abokina..sorry sirikin aunty sumy"..yana gama fadan haka ya sake kwashewa da daria..Nur dai na zaune yana kallon tsabar walakanci kawai sai ya mike ya kama hanyar fita daga dakin Bobby yayi saurin mikewa ya isa inda yake suka fita dakin a tare yana cigaba da murmushi yace"to ka tsaya mu karasa mgn mana"..girgiza Kai Nur yayi ba tareda ya tsaya da tafiyar da yakeyi ba yace"don't bother"..kama hannunshi Bobby yayi ya dawo dashi cikin parlor suka zauna snn ya dan daidaita dariar da yakeyi yace"to yanxu ya kakeso ayi?.."marairaicewa Nur yayi yana dubanshi yace"kawai nidai kayimin kokari akan mgnr..ba sai ka fadama kowa Ina sonta ba amma daga nan zuwa ta gama secondary school kada a bari ta kula kowa dan Allah sbd banaso wani yazo ya rigani"..murmushi Bobby keyi yana gyada kai yace"baka da matsala da wnn..dama bata kula kowa and bazata fara ba har ta kammala secondary school din"..ajiyar zucia Nur ya sauke tareda fadin"thank u..wnn year din zata gama Koh?.."Bobby yace"mene?.."Nur yace"secondary school din mana?.."murmushi ya Kara saki yace"yeah this year zata gama"..Nur ya sake cewa"ohk Allah ya kaimu..and thanks for ur understanding"..murmushi kawai Bobby keyi yana shafa kanshi..har yanxun mamakin abun yakeyi ne..saidai Kuma ba abun mamaki bane idan akayi duba da how love is..kwata kwata baisan wani dacewa ko cancanta ba..snn Kuma baya duba kan abunda ke iya zuwa ya dawo duk kan wanda yaga dama kawai fadawa yake..yasan Nur husband material ne sosai and tunda har ya furta yana son to lallai fa gaske son nata yake..shi Kuma zaiyi bakin kokarinshi wajen ganin itama Miemien ta soshi ko don sbd abotar dake tsakaninshi dashi.
Da dare yayi dialing number dinta praying Allah yasa ta dauka sai Kuma gashi ta dauka din..ya lankwasa muryanshi in a pleading tone yace mata"Love am sorry"..shiru tayi bata amsa mashi ba shi Kuma ya sake cewa"Aysher"..a hankali tace"umhum"..yace"am sorry for kissing u..nasan I shouldn't have done that amma ba laifina bane..u couldn't control my self am sorry"..ajiyar zucia yaji ta sauke ita bama wnn ne damuwarta ba..Kai tsaye tace"wacece ita?.."yace"Mom dinta friend din Mummy ne..and.."kasa karasawa yayi yai shiru tana tunanin yanda zaiyi mata bayani...jin yayi shiru tace"and?.."a hankali yacigaba"tana Sona sosai amma believe me I never loved her..infact na tsaneta"..dan daure fuska tayi kmr yana ganinta tace"i don't believe that..baka sonta shine kake bata daman binka har flat dinka?.."tana rufe baki yace"wlh da gaske nake maki Aysher bana sonta..koda ta shiga flat din nawa explaining mata nayi cewa ni ke nakeso Kuma kece zan aura..dan Allah kiyi hakuri mana plss..u are the only person that matters to me and i love only u"..shiru tayi batace komai ba..shi Kuma ya sake marairace mata yace"love please!.."ajiyar zucia ta Kara saki before saying"nidai wlh ta sake zuwa inda kake ban yafe ba..and I mean it"..ya saki wani murmushi yana cewa"baza ma ta sake zuwa ba believe me..I Love u"..shiru ta sakeyi kafin yace"Love say u love me too mana plss..i want to hear that"..dan turo bakinta tayi kafin tace"I love u too".. tun kafin ta rufe baki ya shiga blowing mata kisses ta cikin wayar yana cewa"thank u..thank u..thank u so very much baby..thank u".
Tun daga wnn rana masoyan suka shirya abunsu..soyayya Kuma sai sake karfi yakeyi a tsakaninsu ta yanda basa iya complete 2 days ba tareda ganin juna ba..abun har mamaki yake bata yanda takejin sonshi a kowane lungu da saqo na zuciarta..kullum yana kan hanyan zuwa ganinta don kullum sai ta fara shiga college ya ganta kafin ya wuce hospital..zuwa yanxu hatta students daidai ne basu san irin soyayyan dake tsakaninsu ba...a daya 6angaren kuma shirye shiryen council sukeyi sosai don few months yanxu ya rage musu su fara..kowa ya maida hankali matuka wajen karatu sbd yayi passing...specialist aka dauko ta fannoni daban daban suke musu extra lesson kullum a cikin college din kan duk wani abu daya shafi council exam tun daga kan theory har zuwa kan practical..sosai Kuma suka maida hankalinsu suna koya wnn dalilin yasa har weekends suna shiga school sbd lessons din da sukeyi.
A 6angaren shirye shiryen bikinsu nan na ba'a cewa komai don both bangarori nata shiri sosai na bikin da baifi saura 4 weeks ba yanxu...su Mummy sun gama hada lefe lokaci kadai suke jira su dauka su kaisu wajen waziri da yace har ita Mummyn yakeso suzo wai da akwai mgnr da zaiyi da ita.
A 6angaren bride and groom Kuma za'a iya cewa ba wani shiri da suke don ita tana fama da karatu exams dinta dake sake approaching yayinda shi Kuma ya maida hankali sosai wajen ganin tayi passing exams din nata..har extra lesson yakeyi musu ita da Billy kan duk wani abu daya shige musu duhu..sosai Kuma suke fahimta dan da gaske ya iya koyarwa..wani lokaci har class din nasu yake zuwa yana koyar dasu wani abun during weekends haka sbd ya taimakawa Nur da shima duk wani attention dinshi ya dawo garesu.
Yau ma kmr kullum bayan sun gama lesson da yayi musu office dinshi Billy tayi sallama dashi ta fita ita Kuma Aysha na zaune tana kallonshi ganin ya zuba mata ido ya kasa cewa komai..turo baki tayi tana rufe fuska da hannaye ta tace"ni ka dena kallona"..dan murmushi ya saki yana shafa gashin kanshi yace mata"gobe zamuje Gombe"..bude idon tayi da sauri tana kallonshi lokaci daya ta kwabe fuska kmr zata sa mishi kuka tace"partner nima inaso inje plss"..girgiza Kai yayi yana cewa"kiyi focussing kan exams dinki dan Allah"..tun bai rufe baki ta make kafada tana turo baki tace"nidai i want to follow u plss"..kama hannunta yayi ya dawo da ita kusa dashi ta zauna yana facing dinta yace"kinga fa bani kadai zanje ba..tare dasu Mummy zamuje..Kuma ba daddy yace ki bari ki gama exams dinki ba"..baki ta sake turowa tace"to shine Kai zakaje ka barni?.."yace"ai ba jimawa zamuyi ba love believe me..ba dan Waziri da kanshi yace yana nemanmu ba da bazan iya zuwa in kyaleki a nan ba kema kin sani"..kallonshi kawai takeyi hawaye na ciko idonta ta dora kanta a shoulder dinshi tana rikeda hannunshi tace"am going to miss u"..shafa kanta yayi yace"nima i will miss u amma ko kwana biyu bazanyi ba zan dawo trust me"..Kai kawai ta gyada mishi tana sake lafewa a jikinshi..hannu yakai ya dagota daga jikin nashi sbd wasu abubuwa da suka fara kai kawo a cikin jinin jikinshi ya shiga goge mata tears dinta yace"to yaushe zamuje kiga kayan naki?.."makale kafada tayi alaman bazata jeba..yace"to gidanki fa shima bazaki je ki gani ba?.."sake makale kafada tayi tana wani turo baki..Bobby daketa kallonta with adoration lumshe ido yayi tareda matsawa yayi pecking forehead dinta kafin ya dago yana rike da hannayenta yace"I love u so much"..murmushi ta saki itama da wet face dinta tace"i love u too"..kallon dimples dinta yayi kafin yakai fingers dinshi a dora both dimples din nata yana kallon tsakiyar idanunta yace"suma ina sonsu sosai"..murmushi ta kara saki dimples din ya sake fitowa baisan time din da ya lumshe ido ya sake pecking cheeks din nata ba..he loves this girl to the core..yana jin sonta a duk wani numfashi da yake shaqa a doron kasa..soyayyarta a cikin jininshi yake.
Washegari da safe suka dauki hanyan Gombe su uku..Mummy,Bobby sai aunty sumy..sai da suka fara tsayawa Police Academy Wudil wajen Sab snn suka wuce Gomben...lokacinda suka isa was around 12..bayan sun isa gidan Waziri yasa aka fito da kayan da suma mota guda akayi musu suka shiga dasu parlonshi..Saida ya gama ganin uban kayan snn yace da Mummy"kunyi kokari sosai Allah ya saka da alkhairi..amma banaso ku sake yin komai kan harkar bikin nan..duk wani abu da yayi saura tun daga kan sadaki har zuwa duk wani abu da za'ayi spending lokacin biki ni na dauki nauyinshi..kaima Attahiru ban yadda ka sake yin komai ba ni da kaina zanyi maka duk abunda ya kama in Allah ya nuna mana"..cikeda farin ciki Mummy tace"Muna godia Baffa Allah ya saka da aljanna"..Waziri yace"Ameen..mgnr kai lefe kuma nayi mgn da Baffaninka da kansu zasu dauki kayan su kaiwa Lamido dan haka ba sai mata sun shiga lamarin ba"..nan ma godia suke sakeyi Bobby ji yayi ya rasa inda zai sa kanshi sbd farin ciki..wato dai zumunchi ba karamin abu bane a rayuwa..dunia mutum baya da tamkar 'yan uwanshi shiyasa no matter the situation bazaka ta6ajin ance wane ya canxa 'yan uwa ba..dan uwanka dole dan uwanka ne komai rigimar da zakuyi dai bazai canxa wnn suna ba shiyasa ake son mutum ya kasance mai juria da Kuma hakuri da 'dan uwanshi..(Allah ka bamu ikon rike zumunchi har karshen rayuwarmu).
Bayan sun dan nisa Waziri ya sake cewa"sai Kuma mgn ta biyu da nakeso muyi"..Mummy ce tace"Muna sauraronka"..Waziri ya gyara zama tareda maida duba ga aunty sumy ya kira sunanta"Sumayya"..a hankali tace"na'am"..yace"kinada masaniyar zuwan tsohon mijinki wajena kan batun maida aurenku?.."girgiza kai aunty sumy tayi alamar aah..Waziri yace"to yazo nan ya sameni tareda wani kawunshi..ya sanar dani duk abunda suka faru a tsakaninku ya kuma bani hakuri tareda neman alfarmar in roka masa ke ki amince ki koma dakinki..nace masa bazan yanke hukunci ba saina farajin ta bakinku dan haka kuje kuyi shawara a tsakaninku idan kun amince ta koma Alhamdulillah idan kuma baku amince ba wanda zaiyi mata dole"..gaba daya shiru sukayi tamkar basuji abunda yace ba..Mummy ce ta fara breaking silence din da cewa"nidai ta 6angarena banida wani matsala da haka domin mahaifiyarshi har gida tazo ta nemi gafarar mu kuma muka yafe mata..dan haka indai taga zata koma din nima zanfi son haka ko don sbd zuri'a dake tsakaninsu"..gyada kai Waziri ya shiga yi yace"wnn haka yake..kai kuma Attahiru menene shawararka akan haka?.."dan murmusawa yayi yana shafa kanshi yace"Baffa nima indai ta amince shknn"..da mamaki aunty sumy ta juya tana kallonshi jin yace ya amince kmr dai ba Bobby da har sim card yake canxa mata sbd Isma'il din ba..lallai Bobby ya canxa sosai ba kadan ba..ta tabbata da ada ne akayi mashi wnn tambayar kanshi tsaye zaice bai amince ba amma wai shine da cewa in ta amince shknn..lallai wonders shall never end..har gobe bata dena mamakin sudden change din nan nashi ba..ta fuskanci tun da ya fara son Lamido zuwa haduwa da Waziri ya sauya daga Bobby mai kafiya,taurin kai da kuma riqo zuwa Bobby mai sauki da kuma sanyin hali kan abubuwa da dama ciki hadda yafiya da kuma mancewa da tarin laifukan mutun da tunawa da alkhairinsa komai qanqantarshi...ganin tayi shiru ta kasa cewa komai Waziri ya sake Kiran sunanta..ta amsa kanta a kasa duk bata San ma amsar daya kamata ta bashi ba..shi Isma'il din na meye zai wani xo har wajen waziri ba tareda ya fara mgn da ita yaji ta bakinta ba..Waziri yace"na baki nan da sati biyu kiyi tunani akai..idan kin amince sai a hada auren naki dana 'dan uwanki a daura rana daya"..ba tareda ta dago kanta ba tace"na amince Baffah..Allah yasa haka shine yafi alkhairi"..cikeda farin ciki Waziri yace"Ameen Allah ya maku albarka..Allah Kuma yasa ayi lafia a gama lafia"..duk suka amsa da Ameen..daga nan kuma suka shiga cikin gidan don su huta kafin gobe kuma su sake daukan hanya su koma Kanon Dabo.
Kmr yanda Waziri ya fada Baffanin Bobby su hudu tareda shi wazirin na biyar sukaje suka kai lefe wa Lamido inda shima ya kar6a tareda saura uncles dinta..farin ciki sosai sukayi da ganin uban kayan kowa yana Allah sambarka..daga nan Kuma suka tsaida biki bayan sati hudu da gama council exam dinsu..sosai su waziri sukayi na'am da da ranar sbd ita kanta amaryar tabada buqatar hutawa kafin lokacin bikin nata...dukda Lamido yaso hada bikin dana Hamma Najeeb amma hakan bai yiwu ba sbd wani special assignment da aka turashi yi a Cameroon and bazai gama ba sai bayan shekara daya..wnn dalilin yasa dole suka bar nashi bikin har zuwa lokacinda zai dawo shi kuma Bobby tunda ya matsa lallai so yake ayi nashi sai a fara yinshi kafin zuwan na Najeeb din..lokacin da labarin sa ranar ya iske Bobby Saida yaji ba dadi..yanxu bayan duk wnn jiran da yayi so suke ya kara cinye wani month bayan exams dinsu snn ayi biki?..Sam baiji dadin wnn four weeks din ba..shi da zasu gane ma da dawo da bikin sukayi ya dawo one month din amma ba su sake Kara mishi another month akai ba...yana zaune office dinshi tun daxu sai jujjuya mgnr yake yanajin haushi kmr tasan halinda yake ciki saiga kiranta ya shigo wayarshi..daukan wayan yayi tareda relaxing kan kujera yayi answering call din ba tareda yace komai ba..a daya 6angaren Lamido najin yayi picking ta wani kashe murya tace"partner nah"..dan turo baki yayi exactly yanda take tura mishi nata bakin yace"stop calling me that"..wara ido tayi da mamaki tace"why?..what happened?.."sake marairaicewa yayi kmr zaisa mata kuka yace"wai bakiji ma abunda ke faruwa ba?.."dan rausayar da Kai tayi itama kmr yana ganinta tace"meya faru?.."tun bata rufe baki ba yace"two months..sbd Allah wane hutawa akeso kiyi har na tsahon one month bayan kammala exams..ya kamata aji tausayina mana"..Saida ta bari ya gama haqilonshi snn ta saki wani murmushi tana cewa"Partner its just four weeks fa..before u know it zakaga har lokacin yazo"..girgiza kai kawai yake yana dafa head dinshi alaman she won't understand..ita Kuma jin baice komai ba ta sake lankwasa murya tace"sati hudu ai kaman yau n..."bata karasa ba katseta da fadin"idan kika sake kiramin four weeks din nan zakiga other side of me wlh..a tunaninki four weeks din kmr four days yake?.."dan daure fuskanta tayi tana turo baki tace"nidai kayi hakuri..ai bani nasa maka biki ba zaka wuce a kaina"..shiru yayi kmr bazai sake mgn ba yace"haka kikace?.."with full confidence dinta tace"yes"..yace"ohk then"..sai kuma ya dakata ya shiga sakin murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi murya can kasa yace"don't worry my turn will soon come..and yes ya kamata ki samu enough hutu sosai for what u are about to face"..dan daure fuska tayi tana muzurai tace"what are u insinuating?.."yana cigaba da shafa uban gashin kanshi yace"nothing oo..it's nothing"..shiru tayi tana ture turen baki sai kace ganinta yake..shi kuma har yanxu bai dena smiling ba ya sake cewa"kullum Ina cewa zakiga other side of me baki ta6a gani ba koh?..to a wnn ranan zakiga the real definition of my other side"..tun kafin ya rufe baki tace"banaso"..yace"badai ni kike cema its just four weeks ba?..zakiga it's just four weeks duk ranan da kika shigo hannuna..a ranan zaki gane Attahir nake ba proprietor ko Dr Bobby ba"..ya karasa mgnr da wani killer smile a fuskanshi..yanda yake mgn kadai says it all domin duk wanda yaga how he's talking yana lumshe ido zai gane da mace ne yake waya..kawai baqin cikin da yake na Kara mishi one month duk yayi disappearing sbd tunawa da wani abu da yayi..hakan kuma yasa yaketa sakin murmushi yana shafa kai kmr wani sabon kamu...Alhajia indo kuwa jikinta ba karamin sanyi yayi da wnn kalaman nashi ba..ta lura fa dama these days wani sabon iskanci yakeji dashi haka zaiyita 6aro mata mgn yana sata jin kunya shi kuma ko a jikinshi..ita bata ta6a sanin there is this side of him ba sai yanxu..duk ya wani dawo mai dabi'un 'yan iska shiyasa yake bata tsoro ma...jin yanda tayi dif kmr bata jinshi ya sake relaxing yana lumshe ido kafin yace"baby"..banza tayi mishi tana turo baki kmr yana gabanta..ya sake cewa"partner"..still taki tankashi kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai yace mata"duk wnn abun fa love wasa nake maki..ke bakisan wasa bane?.."murguda baki tayi tana sake dinke fuska tace"ba wani wasa..Allah idan kacigaba da tsokana na fasawa zanyi"..Bobby ya dan wara ido yana sake murmusawa yace"baby idan kika fasa kuma ai mutuwa zanyi"..tace"to ka dena tsokana na nidai"..tun kafin ta rufe baki yace"na bari..ban karawa believe me"..ajiyar zucia ta sauke kafin tace"shknn"..ajiyar zuciyar shima ya sauke tareda lumshe ido yana sake relaxing kan seat dinshi yace"I..love..you..and i can't wait to..marry you".
Bayan sati hudu...
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
53
Bayan sati hudu...
Yau Friday sukayi final laper dinsu and tun da suka fito daga exam hall around 11 kowa yaje ya sake shiri cikin sign out shirts da sukayi iri daya kowa nashi dauke da sunanshi a jiki..hall da suka saba gabatar da celebrations aka bude musu suka shiga nan sukaita celebrating kammala exams dinsu saura fitowa results kuma..har dj suka kira yaketa playing musu waqoqi iri iri masu rawa nayi masu daukan pictures ma sunayi...a extreme end of the hall Lamido zaune tana kallon su Billy daketa dirkan rawa kan stage da sunga wani da bai musu signing jikin shirts dinsu ba zasu bar rawan suje ayi musu signing din suma suyima wanda basuma ba snn su sake komawa dance floor..haka suketa yi tun daxun ita tana nan zaune tana kallonsu..kawai tunanin yanda zasu kwashe da Bobby takeyi idan yaga shirt dinta da signing musamman ma signing na namiji sai kuma rawa Kiri kiri da takeso tayi amma sbd tsoron kishi irin nashi ta kasayi..har sha'awan Billy da sauran colleagues dinta dake wurin takeyi sai taji inama ba'a college din nan yake ba itama da ba abunda zai hana mata enjoying wnn ranan amma yanxu bata isa ba...Billy ce ta nufo inda take zaune da sauri tana zuwa ta Mika mata wayanta dake hannunta tana cewa"Ur Hamma wants to speak to u"..ba musu Aysha ta karbi waya suka fara mgn dashi ita Kuma Billy ta dauki bottled water dake ajiye nan kusa da ita ta zauna tana sipping ruwan tana sauke numfashi...after like 4 mins suka gama mgn da Hamma Aysha ta shiga mikawa Billy wayanta kafin tace"Billy dan Allah zan danyi rawa ko kadan ne kinga fa ba zuwa zaiyi ba nasan yana hospital wlh"..girgiza kai Billy ta shigayi tace"aah fa ba ruwana Lamido bazaki hadani da wnn rigimammen mijin naki ba..haka nan kisa yazo yana tsareni da idon nan nashi da dadine dasu ba"..langa6ewa tayi tana kallonta kmr zata sa kuka tace"yanxu knn kinfi sonshi akaina Billy?..dan girman Allah in dan shiga inyi Allah ba dadewa zanyi ba"..girgiza Kai Billy ta sakeyi saidai kafin tace wani abu Aysha da ta riga tazo wuya sbd haushi tace"ko baki yadda ba sai nayi wlh saidai kije kiyita fada masa din i don't care"..daga haka ta mike zata bar wurin Billy ta dawo da ita da sauri tareda mikewa itama tana kallonta tace"amma banda signing kou?..kinsan fa halin mutumin nan Lamido banson kuxo kuna samun matsala akan haka"..kwace hannunta Aysha tayi ta bude bag dinta ta fito da wani shirt din sabuwa sak irin na jikinta tana nunawa Billy rigan tace"indai ba kece munafukar da zaki fada masa ba ba yanda za'ayi ya sani..ana gama min signing kafin mu fita hall din nan ma zan cire in saka wnn"..kallonta kawai Billy keyi ita wnn abun bai gamsheta ba..a yanda taga yake mgn jiya tasan wlh da kyar idan basu samu matsala kan haka ba tunda he made it clear cewar bayason wnn abun...ganin har ta kama hanyan dance floor ta daga shoulder alaman ba ruwanta snn itama ta bita a baya...tana hawa kan stage din sai kuma ta juya zata sauka da sauri colleagues dinta suka kamata suka maidata wurin..daya daga cikinsu taje ta samu dj tace mishi class rep dinsu ta shigo don haka ya samu Waqar favorite dinta mai azabar dadi yayi playing musu zasu cashe yanxun nan..dj kuwa ba musu ya sakar musu waqa mai dadi nan suka shiga rawa suna janta wai itama dole sai tayi..tun tana nokewa tanajin tsoro har dai daga baya ta saki jiki ta dilliqi rawar ta son ranta..at that moment gaba daya mantawa ma tayi da wani warning dinshi na jiya kan baiso tayi rawa and bai yadda wani ya taba rigarta da sunan signing ba..enjoying dinta takeyi kawai tana cashiya kmr ba Lamido ba...saida tayi me isarta snn ta fara zuwa ana mata signing jikin shirt dinta duk wanda ta gani da sauri take zuwa wurinshi yanayi mata zatayi sauri ta rufe wurin da kimono din jikinta wai duk sbd kada ya samu labari idan yazo...a takaice har after five suna cikin hall din nan suna abu daya..ganin yamma ya farayi hankalinta ya dawo jikinta tasan yanxu duk inda yake ya kusa shigowa college din don haka baki alekum ta fita daga cikin hall din zuwa wani dan small room dake kusada wurin ta shiga ciki da sauri ta zare kimono dinta tana kokarin cire sign out shirt din kawai taga mutum a gabanta..batasan sanda gabanta yayi wani irin yankewa ya fadi ba..lokaci daya ta saki rigar tana yarfa hannayenta hawaye har ya ciko eyes dinta tace"wayyo Allah na"..kala bai ce mata ba sai kimono daya dauka ya mika mata..da sauri ta kar6a ta maidata jikinta tana kallonshi..tana gamawa ya kama hannunta a fusace suka fita daga room din..direct office dinshi ya nufa da ita mutane nata kallon yanda ya riko hannunta amma kobi ta kansu baiyi ba don abunda ya dameshi kadai ma ya isheshi..yana bude office din ya turata ciki snn shima ya shiga ya maida kofar ya rufe ya shiga kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd bacin rai...kuka sosai ta fara tana yarfe hannayenta shi Kuma baice mata komai ba sai tsareta da yayi da eyes dinshi da taji sun dawo mata eyes dinshi data sani a baya masu sanya mata firgici da nutsuwa ba tareda ta shirya ba..da sauri ta matsa zuwa kusa dashi ta dan daga Kai tana kallonshi sbd yafita tsayi sosai kawai sai ya lumshe eyes dinshi don bazai iya juran kallonta a haka ba karyar mishi da zucia zatayi...ba zato ba tsammani kawai yajita fada jikinshi ta kankameshi tana sakin wani kukan da koshi yasan na shagwa6a ne kawai muryanta na rawa tace"am so..rry"..lumshe idanu ya sakeyi yana sauke ajiyar zucia..baisan ya zaiyi da rashin jin Aysha ba amma ko Allah yasan ba karamin wahalar dashi take ba..bude idanunshi yayi tareda dagota daga jikinshi ba tareda ya kalleta ba yakai hannu ya bude kimono dake jikinta nan take uban signings din dake jikin riganta suka bayyana..kallonsu kawai Bobby keyi ranshi na sake 6aci..duk Wanda yayi signing din nn yasan ya ta6a masa jikinta Kuma shidai Allah ya isanshi wlh..da iya class mates dinta ne ma da sauki tunda mata ne amma yasan baza'a rasa 'yan nursing a cikin Wanda sukayi mata signing din ba...runtse Ido yayi da karfi da yaga har wurin chest dinta saida akayi signing..ya juya bayanta nan ma yaga har waist dinta signing ne kaca kace kawai sai ya juya tareda zaunawa kan sofa yana date head dinshi da yaji kaman zai 6alle sbd ciwo..karasawa tayi ta zauna kusa dashi tareda dora kanta a shoulder dinshi tana hawaye sosai tace mishi"dan Allah kayi hakuri partner..zaka iya punishing dina da any kind of punishment amma don't be mad at me plss..am sorry"..hannunshi yakai a hankali yana shafa kanta sbd yanda kukan ke ta6a zuciarshi kwarai...sake langabewa tayi tana sauke numfashi..shi Kuma murya can kasa yace mata"you danced right?.."shiru tayi tana rarraba ido kmr munafuka shi Kuma ya saki murmushi mai ciwo dama ya tambaya ne wai ko hasashenshi zai zama ba gaskia ba amma shirun da tayi ya tabbatar mishi da cewa tayi rawa..zafi sosai yakeji cikin ranshi Wanda inda zai fito dashi ya nuna mata yanda yakeji kilan tsorata zatayi ta gudu shiyasa yake kokarin dannewa kawai..zuwa yanxu ya fuskanci zafi da takura babu abunda zai kara mata sai kangarewa so it's better ya fara binta da lallami da nasiha kilan Allah yasa ya dace..sake Kai hannayenta tayi ta zagaya bayanshi zuwa stomach dinshi dasu dukda ba gama zagayawa sukayi ba tace"partner am sorry please"..Kai kawai ya iya gyadawa yana shafa kanta a hankali yana karanta duk addu'an da yazo bakinshi..inshort sun duki lokaci mai tsaho a haka tana bashi hakuri kafin ya samu saukin abunda yakeji..Saida ya dan nustu snn ya shiga nata nasiha sosai Wanda har kusan kuka yasata sbd yanda yake mgnr shows ba karamin zafin abun da tayi yakeji ba..bata bar office din ba saida ta tabbata he is no longer upset with her snn yayi dropping nasu a hostel da kanshi bayan sun sha love dinsu.
Washegari da safe bayan sun gama 'yan koke kokensu na rabuwa da juna Hamma Najeeb yazo ya kwashesu dasu da komai nasu sai jihar Gombawa diban fari..ba'a kwana daku ba wai sai a tashi daku.
Wnn knn..
Kwananta biyu da komawa small mom dinta tazo ta dauketa suka wuce Bauchi wai za'a fara mata gyaran jiki and stuffs dai da akeyi na gyaran amarya..dukda Ammi bataso haka ba sbd zaman Fiddausi da Aysha a cewarta ba abunda yake karawa sai lalata Ayshan sbd ba wani fada take iya mata ba..amma da daddy yasa baki haka nan ta hakura suka tafi Bauchin bada son ranta ba..ita fa so tayi a dan zaman nn da zatayi ta gyara mata zama sosai ta yanda bazata je gidan miji tana basu kunya ba don tasan halin kayarta tsaf har yanxu ba cikakken hankali ne da ita ba.
Tunda ranan da suka isa Bauchi ko kofar gida bata sake fitowa ba wai idan ana gyara ba'a son shiga rana...mai gyaran jiki sosai auntyn nata ta dauko takanas take gyara mata ita ciki da waje don komai daya danganci gyaran amarya ana mata and ita da kanta ta fara ji da kuma ganin canji a jikinta..biki ya rage saura 3 weeks Billy ta dawo gidan aunty Fiddausi da zama sbd shirye shiryen biki da suka fara ka'in da na'in...events sosai Billy suke shiryawa ita da Provost don sune Organizers na komai da zasuyi a bikin..dama Kuma halinsu ya kusa zuwa daya dan haka suketa planning events kala kala hadda na shirme dan kusan week guda za'a kwashe ana bikin..ko Lamido da take mayyar biki Saida tace ma Billy events din sunyi yawa da taga uban abubuwan da suka rubuta za'ayi amma sai Billy tace mata babu ruwanta nata kawai zuwa ne amma ko event guda baza suyi cancelling ba.
Shirye shirye sosai akeyi ta kowane 6angare..baga ahalin Lamido da Waziri ba..ba Kuma ga ahalin hajia Mummy da aunty Sumayya ba...bride and groom dai nasu Ido ne kawai almost komai na bikin shirya musu akeyi so nasu kawai suyi attending ne..lokacinda aunty sumy ta fada mishi events da zasuyi cewa yayi a rage that shi bayason big wedding wai gajia zaiyi ma da attending events din..amma aunty sumy tace ko event daya bazasuyi cancelling ba idan yaga dama kar yazo su zasuyi abunsu tareda amarya...murmushi kawai ya iya sakar mata ya wuce flat dinshi yana dialing number amaryarshi da rabonshi da sanyata a ido tun ranar da tabar Kano..kiri kiri yanason zuwa ya ganta yarinyar nan ta hanashi wani wai aunty Fiddausi bazata bari ba which he knows she's lying of course..kawai shima sai ya rabu da ita cikin ranshi yace zaiyi maganinta ne idan ta shigo hannunshi..ganin har Kiran ta katse bata dauka ba ya ajiye wayar ya shiga wanka don dawowarshi knn daga clinic.
Aunty Fiddausi ta shigo dakin da take kwance hannunta rikeda bottled water mai sanyi sai sachet na inflanil a hannunta ta karaso ciki ta zauna gefen Aysha dake kudundune cikin bargo tace"oya mike ki samu Kisha maganin nn yanxu zaki samu sauki inshaAllah"..dan bude Ido Aysha tayi tana ganin magani a hannunta ta wani yatsine fuska tana marairaicewa tace"aunty dan Allah kiyi hakuri da kanshi zai dena wlh"..a fusace aunty Fiddausi tace"kinsan Allah zan kira Adda in fada mata wnn iskancin da kikeyi..Shan magani kawai ya gagareki kuma don walakanci har likita na kira tazo ta dubaki kememe kina hana ta maki allura yanxu maganin ma Kuma bazaki Sha ba sbd kin maidani yar iska"..sake marairaicewa tayi tana duban small mom din tata tace"aunty na rantse da Allah idan nasha bakina sai yayi sati yanamin daci..shi Kuma allura fa kinsan dai yanda yakemun ba saina fada maki ba"..a fusace aunty Fiddausi ta ajiye drug da ruwa dake hannunta tace"sai kiyita zama da ciwonki har bikin naki yazo ni ba ruwana"..daga haka ta mike tayi ficewarta daga dakin..a waje suka kusa karo da Billy zata Kai mata tea tasha..ganin yanda ta fito rai a 6ace Billy tace"bata Sha maganinba Koh?.."aunty Fiddausi tace"inafa tasha..yarinya dai shege taurin kai kmr mutanen farko"..girgiza kai Billy tayi tace"bari in kai mata tea din nan inzo aunty nasan wanda ko bataso zai iya mata allura"..daga haka ta wuce dakin ta dire mata tea din gabanta ko kallonta batayi ba ta juya ta fita Aysha ta bita da harara kmr Idonta zasu Fadi kasa..kawai batada lafia ma bazasu daga mata kafa ba kowa sai yayita nata masifa kmr an gaji da ita...Billy na fita ta iske aunty Fiddausi zaune a parlor samun wuri tayi itama ta zauna snn ta dauko wayanta tana searching contact dinshi tace"aunty proprietor ne kadai zai iya mata allura komai isakancin da zatayi"..kallonta aunty Fiddausi tayi kafin tace"sai Kuma mu tasoshi tun daga Kano sbd yazo ya mata allura Bilkisu"..Billy tace"zaizo wlh aunty shima nasan da kyar idan ba son ganinta yake ba yanxu..rabonshi da ita fa tun da mukayi graduation"..ajiyar zucia aunty Fiddausi ta sauke tana cewa"to kirashi ki fada mishi yazo yasan yanda zaiyi da ita nidai..dan wlh idan ta kaini bango ubanta zanci babu ruwana da ita amarya ce tunda batada mutunci"..Billy na murmushi tayi dialing number dinshi tana fadin"bama za'a Kai ga hakaba zaizo yayi maganin kayarshi"..yana daukan waya bayan ta gaisheshi tace mishi aunty Fiddausi tace idan zai iya zuwa Bauchi yazo ya duba musu ita batada lafia as usual Kuma taki yadda ayi mata allura snn taki tasha magani..Bobby da yaji abun kmr gaba ta kaishi nan take yace zai taho yanxun nn don shima son ganinta yakeyi musamman yanxu da akace batada lafia yasan ko yace sai gobe ma ba iya baccin kirki zaiyi ba so gwara ya taho yanxun..suna gama waya ta sanar da aunty Fiddausi yanda sukayi dashi dan haka tasa aka fara shirya mishi abinci kala kala yayinda hajia Ai ke kwance daki tana bacci bata ma San abunda ke faruwa ba.
Bobby na gama waya da Billy ya shirya kanshi sharp sharp ya dauki duk wani abu da yasan zai bukata tareda key din mota ya fita ka tsaye ya shiga flat din Mummy ya mata sallama kan zaije Bauchi wai Aysha batada lafia..Mummy batayi yunkurin hanashi ba ta bishi da addu'an dawowa lafia don tasan yanda duk ya rikice din nn idan ma ba'a barshi ya tafi ba hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba...yana fita ya fada mota direct ya wuce gidan su Nur haka ya azalzaleshi ya shirya sharp sharp snn suka shiga motanshi suka kama hanyan Bauchi..Nur sai mita yake mishi wai daga dawowa gida ko hutawa bai barshi yayi ba yazo ya wani jajibeshi zuwa Bauchi sbd rashin hakuri ba yanda baiyi dashi akan ya bari sai gobe ba amma ya dage sai yau sai kace dai a kanshi aka fara soyayya.
Karfe hudu da wani abu suka shigo cikin Bauchi..driver aunty Fiddausi ta tura ya taho dasu daga inda suke har zuwa gidanta..shi ya fara shiga ciki kafin suma su shiga da nasu motan..parking Bobby ya karasa ciki yayi yayinda driver daya rakosu ta shiga cikin gidan ya sanar da aunty Fiddausi karasowarsu..Jim kadan ya dawo yace musu tace su shiga ciki..basuyi musu ba suka fita daga mota dukabi bayanshi har zuwa cikin gidan..a main parlor suka zauna shi Kuma driver ya fita..bayan few minutes Billy ta shigo parlon rikeda tray din su juice a hannunta..ta karaso ciki ta ajiye tray akan table snn ta zauna kan one seater tana dan sunkuyar da kanta tace"barkanku da zuwa"..Nur ya fara cewa"barka Bilkisu..ya jikin Lamidon?.."tace"da sauki sosai"..juyawa tayi tana kallon Bobby ya sakar mata murmushi..murmushin itama ta saki snn ta shiga gaishesu..bayan sun gaisa ta mike ta bar parlon can sai gata ta sake dawowa da wasu dirka dirkan warmers ta ajiye snn ta sake komawa ta kawo wasu ta kuma ajiyewa snn ta wuce don kiran aunty Fiddausi..tare suka dawo da ita parlon ta karaso ciki ta zauna opposite to them tana dubansu da murmushi sosai fuskanta tace"sannunku da hanya"..durkusawa sukayi har kasa suka gaisheta dukda ko zata girmesu ba irin sosai din nan ba..aunty Fiddausi ta amsa gaisuwarsu tana murmushi bayan sun zauna tace"ku fara cin abinci sai raka ku inda take..bacci ma takeyi don batasan da zuwanku ba"..tana rufe baki Bobby da ya matsu ya sanyata Idonshi yace"am..ni bana tareda yunwa aunty"..dan murmushi aunty Fiddausi ta saki kafin tace ma Billy"ki rakashi dakinda take"..ba musu Billy ta amsa da toh ta juya ta kama hanyar dakin Bobby yabi bayanta yayinda oga Nuruddeen ya baje ya shiga bama cikinshi haqqinshi don a cewarshi soyayyar Bobby bazai hanashi cin abinci ba shikam...Billy na nuna mashi dakin ta juya ta bar wurin yayinda shi Kuma ya tura kofar dakin a hankali ya shiga da sallama...wani irin sanyi dakin ya dauka sosai sbd ac dake kure ita Kuma tana kwance can karshen gado ta kudundune kanta cikin blanket tana bacci peacefully kmr ba mara lafia ba..a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin gadon ya tsaya yana kallon yanda tayi coiling kanta a kan gadon kmr ba mutum ba..stool ya janyo ya zauna dab da gadon yana facing dinta kafin yakai hannunshi a hankali ya janye blanket din..da uban gashin kanta dake tsefe ya fara cin karo sai kuma cute and beautiful face dinta da yaga har wani glowing yakeyi a Idonshi..baisan ko sbd ya jima bai ganta bane amma yaga ta Kara kyau sosai ba kadan ba...janye blanket din yayi daidai stomach dinta sai yaga tayi motsi tareda jan blanket din zata sake rufewa dashi yayi saurin janyeshi tareda daukan remote ya kashe air condition din dakin gaba daya...kallonta yacigaba dayi yanajin wani abu mai matukar karfi yana kokarin fizgarshi zuwa gareta baisan lokacinda ya lumshe ido tareda sunkuyawa yayi pecking forehead dinta ba..hannunta ya kama ya rike yana cigaba da kallonta kmr Wanda keson gano wani abun..left hand dinshi da yake free ya mika yayi feeling temperature dinta yaji jikinta normal babu wani zafi kawai sai ya saki wani hadadden murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi Kuma still hannunshi na cikin nata..a hankali ta fara motsawa sbd zafi data faraji as a result of kashe ac da yayi..lokaci daya Kuma ta bude Idonta tar tana kallonshi shima sai ya tsayar da nashi idon a kanta yana kallonta...mikewa tayi zaune da sauri tana Mirza idonta to make sure ba dreaming take ba Kuma sai taga its real ba mafarki bane..wara idon tayi da kyau tana kallonshi kallo irin na mamaki kafin tace wani abu ya rigata da fadin"ya jikinki?.."hadiye yawu tayi da sauri tana gyada kanta tace"naji..sauqi..amma ya akayi kazo nan?.."murmushi ya saki yana kallonta yace"kirana sukayi wai bakida lafia kuma kinqi yadda ayi allura and kinqi shan magani"..turo baki tayi tana hade rai lokaci guda tace"to nidai bazaka mun allura ba wlh"..murmushi yakeyi har yanxu yace"baby bakida lafia fa?.."rau rau tayi da Ido kmr zata fara kuka tace"Allah kamun allura fasawa zanyi"..daria ta bashi sosai jin abunda ta fada..ya fuskanci these days rigima takeji dashi dan abu kadan zata ce mishi fasawa zatayi..Saida ya gaji da dariarshi kafin yaja dogon hancinta yana cigaba smiling yace"da yake fasawan a hannunki yake Koh?.."turo baki tayi tace"nidai kada kamin allura dan Allah"..gyada mata kai yayi alamar bazaiyi ba..dan kura mata ido yayi for like 3 mins sai Kuma ya saki murmushi yana kallon eyeballs dinta yace"meke damunki?.."a hankali tace"fever"..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai yana cigaba da kallonta yace"ba fever ba dai..ki fadi gaskia"..daure fuska tayi tana harare harare tace"nidai fever ne ke damuna"..shiru yayi yana kallonta kawai sai ya girgiza kai..Aysha da gaba daya ta gama tsarguwa da wnn abun nashi tace"and what does that mean?.."shoulder ya daga mata alamar nothing..da sauri tace"ban yadda ba wlh..da akwai wani abu cikin ranka"..girgiza mata kai yayi alamar ba komai ita kuma ta wani hade rai zata kwanta baisan lokacinda ya janyota jikinshi yana danne dariarshi ba..murya can kasa yace"kawai ki fadamun period kike ba sai kina wani 6oye 6oye ba mana..am ur soon to be husband"..tun kafin ya rufe baki ta daddage ta tureshi daga jikinta ta sake juyawa zata kwanta yayi saurin dawo da ita jikinshi yana cigaba da dariarshi yace"nifa bada wani abu na fada ba..am sorry"..banza tayi dashi ta shiga kokarin kwace kanta..ya dagota tareda cupping fuskanta still yana murmushi yace"bafa laifi kukayi ba ni kyautamun ma kukayi keda period din naki da kukeyin abunku tun yanxu ba sai..."bata bari ya karasa ba ta toshe mishi bakin da hannu daya tana dukan chest dinshi da dayan hannun tace"banaso..banasoo"..sake rungumeta yayi yana sakin daria sosai yace"to kuyi hakuri na dena"..sake dukan chest din nashi tayi yace"to kiyi hakuri love..am sorry ba period kike ba"..daga haka ya dagota daga jikin nahi yana kallonta da kyau yace"yanxu kici abinci sai muyi allura"..girgiza kai ta shigayi tana cewa"No pls"..da sauri yace"ohk to ki samu kici wani abu sai kisha magani"..gyada mishi Kai tayi alamar toh..shi Kuma ya mike daga inda yake zaune ya mika mata hannunshi yace"tashi muje parlor kici abinci"..girgiza kai ta sakeyi tace"rigana baida tsayi kaje zan fito"..yace"U sure?.."Kai ta gyada mishi meaning she's sure..bai sake cewa komai ba ya fita daga dakin ita Kuma ta mike da kyar ta janyo hijab ta zura snn ta shiga takawa a hankali ta fita zuwa parlon..itadai tsoronta Allah tsoronta kada yace zaiyi mata allura dan bataso wlh..haka kawai salon azo bikinta allura nayi mata ciwo.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
54
Biki ya rage sati daya Aunty Fiddausi ta tattara su gaba daya suka wuce Gombe sbd preparation na biki da zata taya yayarta...zuwa lokacin sosai amarya Aysha ta canxa tayi wani 6ul 6ul da ita kaman ba amarya ba don ba wani stress na biki data daurama kanta..duk wani abu daya kamata ayi Billy ce takeyi tareda sauran cousins dinta sai kuma Aunty Fiddausi...sbd cika fa gidansu ya farayi da mutane na nesa da suka fara zuwa Ammi tace ita da Billy suje can gidan wani small uncle dinta da bai dade da aure ba su zauna tareda sauran friends dinsu da zasuzo idan an fara biki...haka kuwa akayi suka tattara duk wani abu da sukasan zasuyi amfani dashi har a kammala biki suka wuce can gidan uncle din nata dake few houses away from nasu gidan...sun rage yawan events da suka tsara zasuyi sbd Lamido ne yace lallai lallai duk yawan events dinsu kada ya wuce kwana uku dan haka sun bar Henna Party ranar Wednesday.. Thursday Cocktail party..Friday kuma Kamu da Mother's Eve wanda Ammi ta shirya..Saturday ayi daurin Aure by 11 daga nan kuma a wuce da amarya Kano inda zasu gabatar da nasu events din a can.
Yau Tuesday tun safe sukayi shirin tafia saloon Billy na zaune parlor tana waya da Hamma bai Kai ga dawowa Gombe ba ita kuma amarya Aysha tana daki tana karasa shiryawa don su wuce saloon din da wuri..tana zaune gaban mirror tana kokarin parking gashinta kiran ango ya shigo wayarta..ajiye comb dake hannunta tayi tareda daukan wayan tana marairaicewa tayi picking tana cewa"partner dan Allah kayi hakuri mu tafi plss..wlh daga ni sai Billy zamu tafi ba wani ne zai kaimu ba"..girgiza kai Bobby yayi kmr tana gabanshi yace"baby i told u Sab is coming to take u guys ku Kara hakuri mana..ban yadda ki shiga motar wani ya fita dake ba wlh"..da mamaki sosai tace"u mean tun daga kano ka tasoshi sbd yazo ya kaimu saloon?.."girgiza kai ya sakeyi yana shafa kanshi yace"no yana Gomben dama tun jiya Mummy ta aikoshi bai dawo ba..yanxun yacemin ya fito daga gida so u guys should wait for him"..a hankali tace"partner kishinka yayi yawa mana..an kusa bikin ma bazaka dena wnn abun ba"..tun kafin ta rufe baki yace"duk abunda zaki fada ki fada amma da gaske bazan saki matata sakaka kowane Kato yana kallon min ita ba..ubangiji da kanshi yace ya tsine ma wanda bai kishin matarshi so bazan zama among wayanda tsinuwan Allah zai tabbata a kansu ba"..murmushi tayi tana girgiza kai tace"dukda haka naka yayi yawa partner..ya kamata ka rage plss"..shiru taji yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can taji yace"kinsan wani abu?.."girgiza mishi before saying"aah"..wani munafukin murmushi ya saki yana shafa gemunshi murya can kasa yace"i can't wait to be with you..Allah kadai yasan yanda nakeji kaman in janyo Saturday ya dawo yau"..ya karasa mgn yana lumshe ido kai kace a gabanta yake..Lamido dai diff tayi tana sauraronshi jin ya fara sauka daga layi..ita ta rasa dalilinda yasa ya dawo bashida kunya yanxu..gaya mata duk maganan da yazo bakinshi yake ita ya barta da jin kunya..turo baki tayi tareda mikewa daga inda take zaune tace"nidai tafia zanyi Ammi na kirana"..da sauri yace mata"hang on plss"..shiru tayi tana sauraronshi..shi kuma ya wani kwantar da murya yace"bakice kina Sona bafa"..murmushi mai kyau ta saki tana kallon kanta ta mirror kafin a hankali tace"Partner"..murya can kasa shima yace"yes partner"..sake kashe murya tayi tana wani kashe ido cikin wani irin siga tace"Ina sonka sosai..i love u"..lumshe ido Bobby yayi yana safe chest dinshi still smiling yace"i love u more wlh..son da nake maki Allah kadai yasan amount dinshi"..har yanxu bata bar smiling ba itama tana lumshe ido..batasan why har yanxu bata gajia da sauraron words din nn nashi ba..she loves him to the extent that duk wani word da zai furta mata means the entire world to her..she loves him to the core...kafin wani cikinsu ya sake mgn kiran Ammi ya shigo wayanta..tana dubawa taga itace sai tayi saurin maidawa kunnenta tana cewa"partner excuse me plss..Ammi naga ke kira tun daxu bansan ko nemana take ba"..gyada kai yayi tareda kashe kiran ita Kuma tayi saurin daukan call din Ammi tana cewa"hello Ammi"..a fusace Ammi tace"wai zaman uban me kukeyi a gida baku fito ba tun daxu?.."da sauri tace"yi hakuri Ammi cewa yayi ya turo Sab yazo ya kaimu shiyasa bamu fito ba"..tsaki Ammi taja kafin tace"to yana zuwa ku tafi and ki tabbata kin biyo ta nan don akwai baqin da zaku gaisa dasu"..a hankali tace"to Ammi"..daga haka Ammi ta kashe wayarta ita kuma tayi saurin karasa parking gashinta ta dauki bag dinta da veil dinta a hannu ta fita daga dakin..har yanxu Billy na nan parlor suna waya da Hamma..Aysha ta karasa ciki tana yafa veil dinta akai tace"su Laila da Majnoon har yanxu ba'a gama wayan bane?.."harara Billy ta watsa mata before tace"inace kema wayan kika gamayi da Romeo dinki yanxu?.."girgiza kai Aysha tayi tana karasa veiling dinta..daidai nan Kuma kiran Sag ya shigo wayarta and ko bata dauka ba tasan karasowa yayi dan haka a hanakli ta isa inda Billy ke zaune ta fizge wayar hannunta tareda kaishi kunnenta tana cewa"Hamma a dan daga mana kafa plss..zamuje saloon"..murmushi Hamman nata ya saki tareda kashe wayarshi..Billy da already ta gama shirinta kafin ta fito ta mike tana rataya bag dinta a shoulder dinta tace"to muje amaryar proprietor"..murmushi kawai Aysha ta saki tareda juyawa suka fita daga gidan..suna fita ta hango motar Sab Parke a gefe dan haka suka nufi can direct..yana hangosu ya fito daga motar ya bude musu kofa yana kallonsu da murmushi har suka karaso..Aysha na kallonshi with a smile tace"haka nan ya tasoka daga aikinka Koh?.."girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi shima yace"duk aikin da nake ai muhimmancinshi baikai wnn ba aunty"..murmushi ta kara saki ta shiga cikin motar Billy ma ta shiga snn shima ya zaga ya shiga ya tayar da ita suka bar wurin..Saida suka hau titi Lamido tace"dukda haka nidai banji dadin tasoka da yayi kana zaman zamanka ba..Saida fa nace mishi daga ni sai Billy zamu tafi amma bai yadda ba"..Sab dake jinjina zafin kishi irin na dan uwanshi yace"haka nan fa yake aunty..tareda wani cousin dina da zamu zo yace bai yadda in tahoda kowa ya kalleki ba shine na saukeshi a gidan Waziri nace mishi yanxu zanje in dawo"..murmushi Aysha keyi tana girgiza kai tasan halin kayanta tsaf zai aikata hakan shiyasa batayi mamaki ba..har yanxu tana murmushi tace"ni kaina kishin Partner har tsoro yake bani fa..inaga shi baiqi ace babu wanda zai sake kallona ba har karshen rayuwa"..daria Sab ya saki yana cigaba da driving dinshi yace"zai iya aikata hakan wlh"..Billy dai na zaune baya tana jin conversation dinsu..tun bata sa baki ba har daga baya itama ta shiga suka farayi da ita..bayan ya saukesu yace idan sun gama sai su kirashi ya maida su gida shi Kuma ya juya kan motarshi ya koma gidan Waziri.
Lokacin da Sab ya maidosu gida was around 3..kofar gidansu tace yayi parking sbd amsan da kiran da Ammi keyi mata tun safe dan haka daga nan sukayi sallama dashi ya wuce su kuma suka shiga cikin gidan da yake nan taf da mutane...saida suka tsaya suka gama gaishe gaishe a parlor na baqin dake ciki kafin suka wuce bedroom din Ammi..daga ita sai aunty Fiddausi a dakin sai wata cousin dinsu suna lissafa cards din mother's eve da dole Ammi tasa aka karo sbd wanda akayi da farko har ya kare..karasowa ciki sukayi suka zauna suna gaisawa dasu..cousin din Ammi mai suna Rahina tace"aah su amare an samu shigowa knn"..Lamido tayi kasa da kai tana sake gaisheta..Aunty Fiddausi ta debo cards kusan guda 40 ta mikama Billy tace"ungo wnn koda na hannunku zaku kare sai kuyi amfani dasu"..Billy tasa hannu ta amsa tana counting dinsu tace"wlh kuwa kmr kinsan wanda kika bani har sun kare"..Aunty Fiddausi tace"nasan za'ayi hakan ai shiyasa na kwasan maku wnn"..daga haka ta kwashi wasu da suka ware na 'yan uwan daddy ta fita daga dakin don kai musu nasu..Ammi ta gyara zama tana duban Aysha tace"zauna muyi mgn"..ba musu ta zauna kusa da Billy tana kallonta..daure fuska Ammi tayi tana cewa"mgn dama zanyi Miki akan African time..wlh Aysha kika sake na tara jama'a a wuri kikaje kikayi zamanki bakizo da wuri ba da sunan make up zakiga yanda zanyi dake a gidan nan..dama da wuri ku fara make up dinku don bazan dauki a 6ata mana lokaci ba kin sani"..gyada kai tayi tana dan marairaicewa tace"wlh da wuri zamu fara Ammi"..Ammi tace"good..saura kuma kiqi nutsuwa kizo kina wnn raye rayen naki da kika saba"..sake marairaicewa tayi tana duban Ammin nata bata dai ce komai ba..Ammi tace"kika wani tsareni da ido ko bakiji abunda na fada bane?.."kasa tayi da kanta kafin a hankali tace"naji..amma to Ammi nidai dan Allah kice kar asa waqoqin gwanja kinga bansan sanda zanyi rawar bafa"..rai a 6ace Ammi ke kallonta tace"qanin ubanki ne Ado Gwanjan?.."da sauri ta girgiza kai tana turo baki..Ammi tace"to kije kiyi rawar kiga idan banci mutuncinki ba..ki bar ganin aurenki za'ayi wlh idan kikayi ba daidai ba Ina iya zuwa har gidan mijin naki inyi maganinki"..har yanxun kanta na kasa tace"to kiyi hakuri"..Ammi bata sake tankata ba ta dauki wasu cards cikin wanda ke xube gabanta ta mikama Billy tace"idan Kun fita ki nemi Husna ki bata..kuma kice mata idan batayi sauri ta kawomun abunda na aiketa ba itama zataci ubanta"..murmushi Billy ta saki tareda mikewa ta amsa cards din Aysha ta mike suka fita..suna fita cousin din Ammi dake sauraron draman nasu tana daria tace"yanxu Maimuna har yanxu baki dena wnn fadan naki ba..yarinya tana amarya kin wani sanyata a gaba da fada bayan ba laifin komai tayi ba"..murmushi Ammi tayi tareda mikewa daga kan gadon da take zaune tace"Adda bakisan halinta bane idan ba haka nayi mata kunya zatazo tana bani a gaban jama'a..shegen rawar kai gareta kmr ba bafulatana ba".
Suna bar gidan direct gidan uncle dinta suka wuce da kafa tunda ba wani nisa ke tsakaninshinda nasu gidan ba..suna shiga ta hadu da wata cousin dinta ta 6angaren Ammi mai suna Walida da taba dade da zuwa ba..aikam suna ganinta suka rungume juna suna murnan zuwanta..abinci kadai sukaci bayan sallahn la'asar wanda zatayi musu red henna tazo tunda gobe iya black za'ayi a wajen henna party..daga ita sai Jessy da gajeren wando ta zauna aka fara mata lallen yayinda Billy da Walida keta faman dirkan hira kaman wanda suka shekara da sanin junansu..kafin a gama mata wasu daga cikin cousins dinta dake nan cikin estate din suma duk sun karaso dan haka sukayi reras sunata hira da labari abunsu sai tsokanar amarya suke Billy na tare mata...bayan ita suma duk sauran wanda suke son red din akayi musu ciki harda su Hajia Bilkisu kirjin biki da kuma wasu daga cousins dinta na wurin...har matar gidan saida mai lallen tayima daga nan kuma Ammi ta turo aka dauketa zuwa can gidan nasu don tayi musu nasu lallen suma.
Henna Party...
Tun safe mutane keta shirin tafia henna party da za'ayi a makeken compound din gidan wani uncle dinta dake nan cikin estate din..anyi decorating wajen in a traditional way wurin yayi kyau sosai da gani traditional event za'ayi a wurin...masu kidan kwarya tuni sun fara aikinsu yayinda wasu da suka fara zuwa wurin suketa tikar rawa.
Amarya Aysha bata iso wurin ba sai around 5 tayi matukar kyau cikin wani saqi army green kasancewarta fara sai duhun kayan ya sake fito da ainihin hasken skin dinta..dinkin straight gown akai mata da head dinta da aka daura ya tashi sosai kmr dai na amare..tun daga kan shoes har purse dinta duk sunyi matching da kayan jikinta...tayi kyau sosai da light make up dinta daya sake fito da kyan nata..su Billy da sauran cousins dinta sai few friends dinta ne sukayo mata rakiya har zuwa wurin event din...kafin su shiga da ita ciki Billy dake sanye da ankonsu na bridesmaids tayi kyau sosai itama kasancewarta best friend din amarya ta matso kusada ita da sauri tana daga musu hannu tace"you people should wait inyi video din shigan nan in turama angonta don da gaske idan bai ga wankan nan ba yau da kyar zai iya bacci"..daria gaba daya suka saka itadai Billy ta dauko wayanta ta shiga yi mata pictures da videos saida ta gama snn ta maida wayarta cikin jaka daga nan Kuma suka sake jeruwa suka shigo da ita ciki bayan an sakar musu kida na musamman domin shigo da amarya..bayan sun kaita inda aka tanadar mata ta zauna sai suka koma tsakiyar fili suka dan taka rawa daga nan kuma kowa ta nemi wuri ta zauna..su Billy table guda suka cika na yan FCNM da suka zamu zuwa bikin kowacce tayi shar da ita exactly yanda qawayen amarya keyi idan ana bikin qawar su..each table yana cike da kayan ciye ciye iri iri na gargajia bayan sun gama ciye ciyen henna artists da sukazo suka fara aikinsu...lalle sosai akeyi musu baqi kusan duk Wanda tazo wurin babu wanda hannunta ba lalle a jiki..amarya dai na zaune inda aka ajiyeta duk zaman wurin ma ya isheta kafin a gama nata lallen...tun kafin a gama photographers keta aikinsu..masu daukan pictures nayi masu video coverage suna suna nasu..a takaice har akayi sallahn magrib suna abu daya..dakatawa akayi sukai sallah bayan sun dawo Kuma aka sake sakar musu kida suka cigaba da rawa wnn karon har amarya Lamido kasa cigaba da zama tayi don haka ta taso ta shiga cikin qawayenta sukaita rawa suna nishadinsu a cewarta dai Ammi ba zuwa zatayi wurin ba...bayan wani lokaci su Aunty Fiddausi da sauran aunties da mata uncles dinta suka zo wurin nan ma kida aka sake sa musu sukaita rawa suna 6arar da kudi kmr basu sa zafin nemansu..Aunty Fiddausi ta kama hannun Aysha sukaita rawa abunsu kmr wasu qawaye aikuwa yan uwan Ammi sukayi caa a kansu suna watsa musu kudi..inshort dai basu suka tashi taron ba sai after 8..zuwa lokacin kowa jiki yayi liqis don rawar da sukayi a wurin bana wasa bane..motoci aka kawo musu suka dauki amarya da friends dinta zuwa gidan uncle dinta yayinda su Aunty Fiddausi suma suka nashi motocin da sukazo dasu suka wuce.
Suna komawa gida Aysha ta cire kayan jikinta ta shiga wanka don yanda takejin kayan duk sun takura mata..tana fitowa ta dauki sabon jessy dinta na Man u as usual ta saka ta hada da gajeren wandon rigan snn ta zura katon hijab ta tayar da sallah..tana idarwa ta cire hijabin kanta ko hula babu ta dauki waya ta fita parlor inda qawayenta suke sunata maida zance suna daria...gaba dayansu suma sun canxa shiga zuwa na bacci kowa kuma ta gabatar da sallahn da ake binta kafin su zauna..tsakiyarsu ta shiga ta zauna Billy dake kallon wayarta tace"Lamido kinsan ya mukayi da mijinki kuwa?.."girgiza kai tayi tana kallonta meaning bata sani ba..Billy tace"hmm ai Ina tura masa videos din nan na daxu ya kirani wai amma bamuyi masa adalci ba..nace sir rashin adalcin me mukayi wai da muka bar masa ke kika fita a haka nace dole fa yayi mana hakuri har a gama bikin nan"..daria gaba daya suka saka suna tsokanarta ita dai tayi gum babu bakin mgn.. kmr kuwa yasan mgnrshi sukeyi sai ga kiranshi ya shigo..ta mike da sauri ta fada daki hadda su rufe kofa snn ta zauna kan gado ta dauki wayar..ko sallama baiyi ba yace mata"lets video call"..tace"ohk"..shi Kuma ya kaste Kiran sai gashi ya kirata video call..dauka tayi tana kallon screen sai ta ganshi zaune a bedroom dinshi yana sanye da white shirt da three quarter fuskan nn nashi a shagwabe kmr zaisa mata kuka..kallon yanda yayi da face dinshi tayi sai ta saki smile tana karema beard dinshi da yayi mata kyau sosai sbd gyaran fuska da akai mashi kallo..kawai sai taji dama kusa da ita yake yaudai takai hannu ta taba wnn sajen nashi da take ganin kmr duk dunia babu wanda gemu da saje kema kyau kamarshi..lumshe ido tayi tana sake fadada smile dinta..yayinda take kallonshi shima kallon nata yakeyi ganin jessy a jikinta ya dan bata ranshi yace"love meye wnn kike wearing?.."kallon jikinta tayi kafin ta maida kallon gareshi tace"riga ne mana partner"..tana rufe baki"of all rigunan da kike dasu ki rasa Wanda zaki sa sai na 'yan ball..what is wrong with you?.."kallonshi ta tsaya yi har ya gama mgn snn tace"ka cika rigima wlh..riga ne fa kawai ba wani abu ba"..tana rufe baki yace"nidai banasonki da kayan Manchester din nan seriously"..gyada kai tayi tana cewa"to na dena sawa daga yau..are u happy now?.."girgiza mata kanshi yayi yana turo baki yace"Kuma gashinki a bude"..murmushi tayi tareda mikewa ta ajiye wayar jikin mirror yanda zai na kallota daga nan tace"to bari in dauko hula in sa"..daga haka ta juya zuwa wardrobe ta shiga neman hula ko dankwali da zata rufe gashin nata dashi..tana juyawa ya bita da kallo ganin dan wandon dake jikinta ya lumshe ido jin gabanshi har faduwa saida yayi..wandon ya kamata ne sosai gashi kuma gajere baifi iya guiwarta ba..sake bude idon yayi daidai lokacinda tayi bending tana kokarin zaro hula daga cikin kayan Billy kawai sai ya kashe kiran da sauri yana sauke numfashi..tana gama daukan hulan ta juya tana kallon wayan sai taga ya kashe dan haka ta saka hulan a kanta da sauri snn ta sake kiranshi video call din amma har ya katse bai dauka ba..sake kira tayi still no answer tana shirin sake kira sai kuma kiranshi ya shigo amma voice call ba video call..picking tayi ta Kai kunnenta kafin tayi mgn yace"let's not video call again plss..matsala za'a samu"..wara idanunta tayi tace"matsala kuma partner"..gyada kanshi yayi tareda fadin"yes ko a yanxu nasan na gama samun matsala..Allah yasa dai ba haka kike fita kowa yana kallonki ba"..sauke ajiyar zucia tayi kafin tace"da hijab nake fita..amma what's wrong naji kace ka samu matsala"..shiru yayi kmr bazaice komai ba sai can yayi kasa da murya ya shiga furta mata mgnr da tunda suke dashi bata ta6ajin such words daga bakinshi ba..ai da sauri ta kashe wayar tana kwalo idanu waje kmr munafuka..har wani seizing taji numfashinta nayi kmr zai dauke..wai meyake damunshi ne these days?..gaba daya ya canxa mata wlh..sai yayita furta mata duk abunda yazo bakinshi shi ko kunya bai dashi...Billy ce ta shigo dakin taga yanda take kwalo idanu waje tace"what?.."girgiza mata kai tayi alamar ba komai..Billy ta saki smile tareda karasawa ta dauki charger dinta ta juya kafin ta bar dakin tace"yarinya ta kusa jin mazaaa..wlh har tausayi kike bani Lamido"..harara ta Maka mata mai kyau tana wani daure fuska tace"kinga banason irin haka Billy..meye wani na kusa naji maza sai kace yar iska"..juyowa Billy tayi tana kallonta da wani dan iskan murmushi a fuskanta tace"wnn mijin naki dai da gani ba hakuri zaiyi ba yaseen..Proprietor da ko kallonki yakeyi sai an fahimci wani abu..yarinya idan ma zaki shirya ki shirya don aiki ne gagarumi yake tunkaroki"..tana gama fadin haka ta fice daga dakin tana kyalkyala mata daria ita Kuma Aysha komawa da baya tayi ta zauna gefen gadon tareda dafe chest dinta idanu a waje sosai tace"na shiga uku ni Aisha..anya kuwa ba fasawa zanyi ba?.."
0 comments:
Post a Comment