Ya jima yana tarawa da kwashewa, daga ƙarshe ya yanke shawarar komawa cikin gidan bayan ya kira Khalipha yace idan yaje gidan ya jirasa karya tafi. duk da Khalipha nada nashi uzirin shima sai ya amsa masa da to saboda girmamawa. Dan komai girman uzirin nasa zai iya ajiyewa domin amsa kiran Yayan nasu.
Sai da ya gyara yanayinsa sannan ya tada motar ya ƙarasa gaban gate ɗin da ita. Yayi horn kusan sau huɗu sannan aka buɗe masa. aunty Zakiyya ce da kanta dan gidan babu maigadi tazo ta buɗe masa, hasalima mijinta ya sayesane kawai saboda harkokin siyasarsa idan ta kawosa kano yakan sauka.
Yana gama fakin tana ƙarasowa inda yake, yanda tai wani kicin-kicin da fuska sai ya ƙara ɗaure tasa shima. A ɗage yace mata, “Barka da safiya” yay gaba abinsa batare daya jira amsarta ba. Bayansa ta raka da harara zuciyarta na ƙara mata zafi akan rainin wayonsa. Dama can ita bawani shiri take dashi ba sosai. Ta girmesa sosai amma sam baya bata irin girma ɗin nan yanda take buƙata, wani lokacinma idan yana mata faɗa akan abu sai ka ɗauka shine babba, dan akwai lokacin da mijinta ya taɓa sanar masa wata rigimarsu, daya bincika yaga itace bata da gaskiya ya dinga mata masifa harda cewa zai iya mata dukan tsiya har sai fatar jikinta ta fashe.
Suna gab da shiga falon tace, “Kai yanzu Abdul-Mutallab ka ƙyautama kanka kenan?”.
Batare daya juyo ya kalletaba a daƙile yace, “Da nai mi?”.
Cikin hasala tace, “Aure!. Mi kake buƙata ga mace wanda matarka bata da shi? Wane irin rayuwane wannan mutum yayta tara mata a gidansa kamar wani binsuru.....”
Cak ya tsaya tare da waiwayowa gareta tamkar mai ciwon wuya, ya zuba hannayensa duka cikin aljihu yana jifanta da wani irin shegen kallo da har cikin ranta sai da razani ya kamata, “Masu mata huɗu da ƙwarƙwara su kuma wane matsayi kika basu?”.
“What!?”
Ta faɗa a razane tana kallonsa dan tasan da ubanta yake. Gira ɗaya ya ɗage mata yana ƙara kicin-kicin da fuska. Cikin hayayyaƙo masa itama tace, “Mikake nufi Abdul-Mutallab?”.
“Na baki gundarin baƙin ai, sai ki masa fassarar data dace”. Ya bata amsa da juyawa ya cigaba da tafiya abinsa kamar bashi ya aikata tsiyarba.
Wani irin ƙululun baƙin ciki ya saka idanun Aunty Zakiyya cikowa da ƙwalla, cikin ƙunar rai ta fara zazzaga masa masifa. Ko waiwayenta bai sakeyiba harya shigo falon gidan da sallama.
A kusan tare Mammah da Mahma da Farah suka ɗago suna kallonsu, musamman Zakiyya dake masifa iya iyawarta.
“Ku lafiya kuwa?”.
Mahma ta faɗa tana tsare Abdul-Mutallab da idanu. Zama yay kusa da ita cike da basarwar da ya iya yace, “Mikika gani Mahma?”.
Sosai ta sake zuba masa idanu dan tasan halin Abdul-Mutallab ɗin ya iya manni ya kuma fika tsare gida, sai kuma ta maida ga Zakiyya dake masifa iya iyawa har hawaye na sauka mata a fuska. Kafin ta sake cewa dasu wani abu Mammah tace, “Wai miya faru Zakiyya kike wannan zantukan?”.
Hawayenta ta share da nuna AK dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa, yayinda Farah ta kafesa da ido zuciyarta na harbawa da sauri-sauri akan yanayinsa. “Mammah waini Abdul-Mutallab zai jefa ubana da kalmar suna bunsuru!”.
A kusan tare Mammah da Mahma sukace, “Bunsuru kuma?”.
“Ai gashi nan ku tambayesa mana”. Ta sake faɗa tana fashewa da kuka.
Ganin ko motsi baiyiba yasa Mahma kallonsa da ƙyau tace, “Abdul-Mutallab!”.
Idanunsa ya buɗe a hankali ya kalleta batare daya motsa ba. “Miya kaika wannan zance haka babu daɗin ji? Zakiyya ba yayarka bace?”.
Murmushi ya saki mai ƙayatarwa a karon farko da ɗan yamutsa fuska, kansa tsaye yace, “Mahma ni ƙarya takemin, ita da bakinta ta kirashi hakan”.
Ba mahma ba har Farah sai da ta maida kallonta ga Aunty Zakiyyan da tace, “Kaji munafiki, dagafa na masa magana akan ƙara aurensa nace miyasa zaita tara mata kamar wani bunsuru shine yace wai masu mata huɗu da ƙwarƙwara fa? Kenan yana nufin Abbanmu ko?”.
“To ke miya kaiki faɗa masa haka Zakiyya da girmanki? Aure ba ALLAH ya halasta ayisa ba? Taya za'a danganta wanda yay koyi da MANZON ALLAH (S.A.W) da wannan mummunar kalmar domin ALLAH idan ba neman tada zaune tsaye ba? Dan ALLAH ku ringa sassautama kanku, rayuwarma duka nawa take ALLAH natuba. Kai kuma Abdul-Mutallab baka ƙyautaba daka bata wannan amsar, saika fahimtar da ita kuskurenta ko kai mata shiru”.
“Am sorry Mahma” ya fa ɗa batare da nuna nadamar abinda yay ma aunty Zakiyya ba. Mammah kuwa kasa cewa uffan tayi. Zakiyya ma ƙin cema Mahma komai tayi, dan kai tsaye ta fassara abinda Mahma tayi da son kai. Duk da Mahma ta fahimceta batabi dakantaba ta fara musu nasiha su duka. Sai da ta gama AK ya samu damar gaishesu.
Rai ɓace Mammah tace, “Sai yanzu muke ganinka a gidan? Bayan kasan matarka na cikin halin rashin lafiya, Abdul-Mutallab! Abdul-Mutallab! kana shigarmin hanci fa da yawa”.
Murmushi yayi yana gyara zamansa. Cike da girmamawar da yake bata yace, “To yi haƙuri karki fyatoni Mammah, ba gani nazoba yanzu kuma nama ganta ragal”.
Harara Mammah ta zuba masa kawai dan takaici, zata ƙara magana Mahma tai saurin katseta da faɗin, “Tunda ya nema afuwa basai a sarara masaba a kama wata tashar kuma”.
Dole Mammah ta haɗiye maganar tana marairaice fuska. “Ke kam Addah bakison ace yayi abu saiki fara karesa, to naji yanzu sai ya nema mana ticket ɗin tafiya Morocco”.
“Morocco kuma Mammah? Mizakuyi acan a irin wannan lokacin daba komai akeyi ba?”.
“Eh to lallai ubanmu, sai ana wani abu zamuje tushen uwarmu kenan? To Farah zamu kai ta ƙarasa rainon cikinta acan har sai ta haihu.”
“Kaji kuma wani abu, to banda abinki Mammah sai kace mai cikin fari? sannan wancan karonma bacan tajeba har ya zama sanadin fitar cikin? Ni wannan karonma na yanke shawarar a Nigeria zata haihu babu inda zataj......”
Tassss!!! kakejin sautin fashewar kofin hannun Farah da take shan tea tun shigowarsa. aunty Zakiyya kam a bazata tace, “What!”. Mammah kuma ta ɗan zabura jikin kujera da faɗin, “Baka isaba ko!”.
Yanda sukai ɗin ba ƙaramin mamaki ya bama Mahma ba, shiko sai yay wani shegen murmushi da komawa ya lafe jikin kujera yana zuƙar sassanyan numfashi da iskar ac ke busowa.
Mahma tace, “To minenen abin razana anan? Dan kawai yace a Nigeria matarsa zata haihu? Ai hakan da yay shine dai-dai, kuma shine zai ƙara kawo dai-daito tsakaninta Farah da ƴan uwansa ko?”.
“Adda bazai yuwuba wlhy, karma ki goya bayansa a wannan gaɓar dan tafiya da Farah kamar nayi na gama ne, sannan maganar yarinyar dake gidanka yaya muke ciki?”.
“Ki tayamu addu'a kawai Mammah”. Ya faɗa kansa tsaye.
“Uban addu'a zan tayaku ba addu'a ba Abdul-Mutallab, ni kake gayama na tayaka addu'a akan wannan figaggiyar yarinyar da'a haihuwar kaji ka isa haifarta, to wlhy tunma muna shaida juna ka sakar musu yarinya ko na ɓata maka ranka”..
“To amma Mammah baƙya ganin idan na aikata hakan shima Baffah zai ɓata ran nawa? Kiyi haƙuri kawai kamar yanda nai biyya a zaɓinki shima nayi biyayya anasa. sannan kuma idan ina sonta kuma fa....”
Kafinma ya rufe baki Farah ta fashe da wani irin razanannen kuka sai da Mahma ta daka mata tsawa tasa hannu ta toshe bakinta tana faɗawa kan Mammah.
A zafafe aunty Zakiyya tace, “Wlhy inma baka saketaba da ƙafarta saita bar gidan”.
Banza yay kamar bai jitaba, zata sake magana Mahma ta harareta dole tai shiru tana ƙunƙuni. Cikin rawar murya na alamar jin zafi Mammah tace, “Abdul-Mutallab na rantse zan iya tsine maka akan auren yarinyarnan. Dan haka na baka kwanaki bakwai kacal ka sallameta. Idan kuma ka kuskura ko ɗan yatsanta ka taɓa ALLAH ya is......”
Da sauri yace, “Oh Mammah Please!.....”
Yanda yay maganar cike da ƙosawa ya sata dakatawa tana kallonsa. Cikin ƙunar da zuciyarsa ke masa yace, “Bama sai kinyi wani ALLAH ya isaba haba sweetheart, nifa wasa nake miki kawai dan naga yaya ƴarki zatayi? Tana sona har yanzu kokuwa?, indai nine ki bani wata ɗaya kacal zanyi komai a tsare yanda shima Baffah bazaiga na masa tsageranci ba harya canja wata hanyar da ni dake zamu gaza ganewa kuma ok?”.
A yanda yay maganar seriously yasata yarda dashi, dan tasan halinsa bayason dukkan abinda zai ɓata mata rai, cikin gamsuwa tace, “Idan ka saɓamin alƙawari Abdul-Mutallab bazan maka da sauƙiba fa”.
“Karki wani damu kanki Noorunnisa, sai dai ga shawara, dan akwai abinda naɗan hango idan akace na saketa yanzun, kiɗan sassauta kinsan shima Baffah akwai taurin kai, idan wata ɗaya bataiba zan iya kaiwa biyu ko uku haka, dan dole na haɗa da Granny, kinga hakan na nufin kenan gara ayi sakin cikin hikima yanda zan ɗaura laifin akan wani abu taimin ita yarinyar bawai kece kika saniba. Dan wlhy yanda Baffah ya fusata nace zan saki yarinyarnan yanzu to kuwa zai auramin mata uku rana ɗaya, ya kuma kafamin sharuɗɗan masu tsauri da bazan iya yin wani abuba, kinga kema yaci galaba a kanki kenan, amma idan cikin hikima mukai komai sai a rabu lafiya. Taɓa yarinya kuwa ki ɗauka ko kallo bata ishi Abdul-Mutallab ɗinki ba, na Farah ɗinkine kawai har a aljanna”.
Karan farko ta saki tattausan murmushi da cewa, “To ALLAH yay maka albarka, naɗan gamsu da bayaninka danni shaidace akan Kabeer da halayensa, amma kamar yanda ka faɗa ta wannan hanyarne kawai zamuyi maganinsa da wannan kakar taku sarkin iko wa ƴaƴan wasu”.
“Amin sweet Mammah”. Ya faɗa yana wani shegen murmushi daya zafafa zuciyar aunty Zakiyya ta miƙe fuuu ta shige. dan itakam tsaf ta fahimci shirya rainama uwar tasa hankali yayi kawai.
Mahma kuwa murmushi tayi itama da cewar “Nasan zaka iya Abdul-Mutallab, kamar yanda Hindatu ta faɗa haka mukeson kayi, abinda yasa zan goya bayanka kamar nan da wata ukun saboda dalilan daka faɗa suna akan hanya”.
“Nagode Mahma” ya faɗa yana wani lumshe idanu da komawa jikin kujera ya lafe abinsa.
Sosai dariya kecin zuciyar Mahma tanata ƙoƙarin danneta, a ransa kuwa tanata saka masa albarka da ƙarajin ƙaunar AK ɗin har cikin ranta. A kullum ƙoƙarin sa yaga ya kauce ɓacin ran mahaifiyarsa koda ace ya fita gaskiya, irin wannan ƴaƴan sune abin buƙatar kowa, dan suna ƙoƙarin kiyayewa daga fushin mahaifiya, su kuma kautar da ita faɗawa halaka itama dake zuwa akan dokin fushi kona son zuciya.
Farah ma tashi tai ta shige ɗaki tana rusar kuka. Hakan yasa AK miƙewa yabi bayanta. Mammah zata bisu Mahma ta dakatar da ita.
“Kinga barsu ya lallashi abarsa da kansa. Babu ruwanki a wannan sabgar tunda kinji daɗi yace zai miki abinda kika buƙata saboda ƴar so ɗin taki”.
Ƙaramar dariya kawai Mammah tayi da komawa ta zauna. “Oh Addah kemafa kina bayanmu wannan karon bare kimana wa'azi”.
“Ai nabi bayankunne kawai saboda farin cikinki, sannan nima matar tasa bataminba tayi ƙarama da yawa”.
“To kema dai ƙya faɗa Addah, bandama namiji baida kunya ba, ta ina zai fara nuna wannan ƴar ficilar yarinya matsayin matarsa”.
Dariya sosai Mahma tayi abinta.
AK da Farah kam kusan tare suka shiga ɗakin, ta faɗa saman gado tana sake fashewa da kuka mai cin rai. Shiko yana shigowa ya ɗaure fuskarsa tamau da murzawa ƙofar key sannan ya ƙaraso gaban gadon cikin takun izza da bayyanar ɗacin da zuciyarsa ke masa ƙuru-ƙuru akan fuskarsa. Cikin tsananin kaushin murya yace, “K tashi zaune!”.
Sosai yanda taji muryarsa ya ƙara razanata. Dole ta miƙe zaunen dayace tana kallonsa idanunta cike da tsoronsa. Ƙafarsa ɗaya ya ɗora saman gadon ɗayar na ƙasa yana binta da wani shegen kallo daya saka jikinta fara tsuma tana girgiza masa kanta hawaye na rige-rigen fitowa.
“Share waɗan nan hawayen, kuma ki nutsumin wlhy kona karyaki a ɗakin nan na karya banza”. yay maganar yana matsar da fuskarsa gab da tata da nunata da ɗan yatsansa cikin gargaɗi. Hannu tasa da sauri ta goge hawayen tana magana cikin rawar murya, “Yah Abdul-Mutallab wlhy ba laifina bane, ni bani nace zanzo nan ba, tashi kawai nayi na ganni anan gidan”.
“Bashi na tambayekiba, dan matdalarkice ba tawaba wannan”. Ya katseta a kausashe.
“Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy banason kishiya, zan iya mutuwa ka taimakeni ka barni ni kaɗai, na rantse da ALLAH zan dinga maka duk abinda kake so daga yanzun”.
“Daga baya kenan yarinya. ai kin makaro kuma, dan na baki damammaki bama damaba amma kika cigaba da ɗaukata ɗan iska ko maijin tsoronki ma. Dama na tabbatar miki a randa yaran nan sukaje London inhar kika sakamin ciwon kai sai na baki na zuciya. Koda yake wannan duk bashine a gabanaba yanzu, dan idan na tafi kema kinsan bana waiwaye. Gargaɗi zan miki idan kinbi kin huta, idan kinmin taurin kai da shirya samun ciwon kai wlhy sai na saka miki na jini bayan na zuciyar da kika samu yanzun, kindai sanni sarai. Koda ban miki gargaɗin nanba nasan baki da wata dama ta sake barin ƙasar nan yanzu, amma dole zan miki. Kiyi duk yanda zakiyi ki tabbatarma da Mammah zaki haihu a Nigeria, inba hakaba wlhy ki kuka da kanki, dan inhar ta ɓata ranta a kaina toke zuciyarki da kamanninki zan ɓata gaba ɗaya a rasa ganeki. Ki kuma nutsu akan wannan haukar sumar da kuka da kikema mutane, bake kika jawa kanki kishiyar ba, saurama biyu zan ƙaro bayan wannan shashasha kawai”.
Ya ƙare maganar da sauke ƙafarsa ƙasa yana binta da wasu shegun looks masu riƙe maƙoshi da ƙahon zuciya.
Sai da yaje gab da ƙofa ya juyo cikin wani gargaɗin yace, daga nan zuwa kwana biyu ki dawo inda na ajiyeki, na baki kwana biyunne ma dan banason takurar kowa a cikinsu, idan kuma kin fita yanzu ki sanar musu duk abinda mukai a ɗakin nan, ni kuma na tabbatar miki sunana Abdul-Mutallab Kabeer Shira”.
Daga haka yay ficewarsa. Koda ya fito falon babu wata alamar akan fuskarsa dazai nuna ba lallashin Farah yayba da gaske. Bai zaunaba yay musu sallama akan yana son yin wani uziri ƙilama ya wuce Jigawa duba masu aiki.
Mammah ce ta kallesa cikin harara, “Ban gane zaka wuce Jigawa ba tickets ɗinmu fa?”.
“Oh GOD, Mammah Please kibar maganar zuwa Morocco ɗin nan dan babu ita, idan haihuwarta a london ne baƙyaso nace miki zata haihu anan ne. Zaku iya barmata Mahma su zauna tare kokuma a samo tsohuwa daga Morocco ɗin ta zauna da ita, ke kanki akwai maganar business da nakeson nayi dake wani abokina yanason kaya naga kuma kina dasu. Bye bye ana jirana nikam”.
Daga haka ya fice abinsa dan baiso ta ƙara tofa komai................✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
[10/20, 7:28 PM] Mom Farooq: *_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
_________________________
*Page 56*
..........Sai da ya tsaya yay sallar azhar a hanya sannan ya ƙarasa gidan. Tun daga falon farko yake jiyo dariyar su Meenal da Jamal. Ya ɗanyi shiru na wasu sakanni a wajen amma baiji muryar Zinneerah ba ko sau ɗaya, firar tasu kuma dukta makaranta ce Nawaf na basu labarin makarantarsu ta Turkey shima. Kamar zai nufi can sai kuma ya fasa ya ɗauka hanyar sashensa.
Khalipha dake zaune yana kallon television a falon nasa ya ɗago yana amsa masa sallamar da yayi. Cikin falon ya ƙaraso yana faɗin, “Am sorry besty na barka jira ko?”.
“No babu damuwa Yayanmu, nima ban wani jima da zuwanba sai da na biya ta asibiti”.
“Thanks”.
Yace masa kawai yana nufar hanyar bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sai gashi ya fito sanye da ƙananun kaya da alama waɗan can ɗin sun damesa. Yana zama Khalipha ya miƙe ya buɗe fridge ya ɗakko masa ruwa.
“Thanks Darling”.
Murmushi Khalipha yay kawai ya koma wajen da yake ya sake zauma. Sai da AK yasha ruwan sosai dan ƙishirwar yakeji dama. Kofin ya ajiye yana gyara zamansa ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ƙara komawa serious.
“Khalipha akan maganar da muka farone ranar, inason ka amsa min wasu tambayoyi”.
“Okay Yayanmu kaimin, inhar na sani zan baka amsa insha ALLAH ”.
Kansa ya jinjina masa da kai hannu yaɗan shafo sajensa zuwa gemu. “Yanzu idan nace kamin bayani akan dashen cikin gaba ɗayansa zaka iya?”.
“Zan iya Yayanmu, sai dai zai cimana lokaci matuƙa, kai kuma nasan bakason a cinye maka lokutanka”.
Sassanyan murmushi yayi yana ɗauke kansa daga Khalipha ɗin. “Ai wannan nine na bashi lokacin da kaina, sai dai kuma barsa kawai muje ga tambayoyin zasu wadatar dani insha ALLAH ”.
“Okay Yayanmu ina saurarenka to”.
Ɗan jimm yayi na wani ɗan lokaci kamar mai nazari, kafin ya duba Khalipha da ƙyau, “Bani bayani a taƙaice ta yanda za'a iya dashen cikin?”.
Zama sosai Khalipha ya gyara da nutsuwa. “Abunda kake magana ana ce mishi artificial insemination Yayanmu. Ana daukar maniyyi namiji (semen) a tace, a ɗauki sperms sai a haɗa da Kwan mace (ovum). Shi Kwan mace sai an shirya ake ɗaukan shi shima, anabada magunguna kafin ayi hakan, sannan ba haka kawai ake ɗauka ba sai an duba lokacin da matar take ovulation, ma'ana Kwan yayi girma sai ayi amfani da na'urar scanning a ɗauka. Ta Mara ake ɗauka bata al'aura ba, sai a haɗa a Laboratory (invitro fertilization). Idan anyi sa'a an samu fertilization sai a ɗauki abunda ake cewa fertilized ovum kamar guda biyu a sa a mahaifar matar wannan ta vagina ɗinta za'a saka sai a jira a gani idan dashen ya kama. Idan ban mantaba kuma na fahimci tambayarka wannan itace amsar”.
Sosai AK ke ɗan jinjina kansa yana taunar lip ɗinsa na ƙasa a hankali da haƙiri. “Okay Thanks. Next, za'a iya ɗaukar sperm daga wani ƙasa a kawo wani ƙasa batare daya lalace ba?. Misali kamar daga london zuwa Nigeria?”..
“Eh to Yayanmu za'a iya ɗaukar semen akai wani wuri, amma gaskiya yanada matuƙar wahala saboda sai an sashi a ma'adani na musamman (Google: transport sperm from one place to another). ba kowanne likita banema zai iya maka wannan juriyar kai tsaye”.
“Lallai kam. To amma za'a iya ɗaukar sperm ɗin namiji bada saninsaba aje a aikata dashen?”.
“Yayanmu idan na fahimceka kamar ace matarsa ta ɗauka a ɓoye bada saninsa ba? Dan ko likita sai dai ya saka a kawo, bawai ya ɗiba kai tsaye ba tunda ba kamar jini bane ko fitsari da sauransu”.
“Good, haka nake nufi?”.
“Gaskiya Yayanmu kamar ba zai yiwu ba, saboda idan za'ayi irin wannan abun shi namijin shine zai bada maniyyi asa a kwalba na musamman a tace sannan ayi, ba zai yiyu ayi irin wannna kuskuren ba, kamar yanda na faɗa maka sai an shirya ake ɗaukan Kwan mace, sannan akwalba ake haɗawa sai ya haɗu sannan za'a ɗauka a dasa a mahaifar macen. Sai dai a sakashi ya bada da kansa ta wata sigar batare da shima ya san mi za'ai da shi ba nakega”.
Ɗan jimmm AK yay yana wani tunani da ƙiyasta shekarun Zinneerah a ransa. Kafin ya duba Khalipha ɗin,
“Okay, kenan za'a iyama yarinya ƴar 14years dashen cikin?”.
“Eh Yayanmu za'a iya yi, sai dai kamar yanda na faɗa maka kafin ayi sai an shirya, ma'ana akwai lokacin da akeyinshi sai an duba menstrual cycle ɗin matar, sabida haka idan bata fara al'ada ba, ba zaiyi wuya ba, idanko ta fara zai iya yuwuwa”.
“Akwai ta hanyar da ku likitoci kuke iya gane ɗan na dashe ne?”.
“A iya sanina babu yanda za'a iya gane dashe ne, bandai saniba ko ga wasu manyan likitoci da suka fini ƙwarewa kasan har yanzu ni ɗalibin ilimi ne”.
Ɗan murmushi AK yayi yana sake gyara zamansa. “A nawa tunanin idan har dashen ciki akai ma yarinya, ya kuma kasance cs akai mata bata haihu da kanta ba, kenan zata iya cigaba da kasancewarta cikkakkiyar mace dazai iya bada dukkan amsoshin ko hujja akanta tunda babu wani dalili dazai iya gusar mata da budurci”.
Murmushi ne ya ɗan suɓucema Khalipha, dan sai yanzu ya fahimci dai Yayansu yana magana ne kamar akan Zinneerah, ya dai ƙi fitowa fili ne, zama ya ƙara gyarawa da ƙyau yana faɗin. “Eh to Yayanmu idan dai mace ta haihu ai babu zancen virginity ya kare nake gani ko kuwa?. Sai dai kuma da kace idan ya kasance an mata cs ne. Abunda mutane ke cewa budurci abun ba haka bane, virginity shine idan bata taba saduwa da namiji ba ko an zura wani abu a vagina babu yanda ake ganewa saboda mata da yawa wannan abun mai kama da yaɗi da yake ɗan rufe bakin vagina ba kowa keda shi ba, hasalima idan mace tana manyanta abun yana raguwa, sannan tsallle-tsalle da irinsu hawan doki ko Keke duk yana sawa a rasa shi, haka kuma Koda mace tana dashi ba kowa ke zubar da jini lokacin saduwar farko da ɗa namiji ba. Shi yasa yanzu duk ake hana abubuwa kamarsu vaginity testing. Kaga nauyin ciki zai iya sa ta rasa wannan yaɗin kenan itama inhar tanada, amma ba haka na nufin ta rasa budurci ba, dan dole a kirata virgin inhar bata taɓa sanin ɗa namiji ba, ko kuma wani abu makamancin haka kamar haihuwa bai ratsata ba”.
AK ya ɗan sauke numfashi, “Sannu da ƙoƙari Khalipha. to amma za'a iya yin dashen batare da ta saniba kuwa? Kamar a bugar da ita ko something hakan?”.
“Tabbas za'a iya bata maganin bacci ayi, amma bazai yuwu ayi a gida ba ko ɗakin likita ba, a ɗakin theater akeyi, bai kuma zama lallai a samu nasara ba a yin farko, wasuma sai kaga sunyi sama da sau hudu biyar goma ma basu daceba, ƙwayayen sukan mutu kafinma a dasa ko bayan an dasa cikin yaƙi zama. Idan kana buƙata zan iya baka number wani likita ƙwararre akan wannan fanin kawai dazai maka ƙarin bayani sosai, zaima iya nuna maka yanda akeyin komai insha ALLAHU”.
Murmushi AK yayi da ɗaukar ruwa yasha. “Ai ko haka aka tsaya ma na gamsu Khalipha, na kumaji a raina baka wasa da karatunka, tunda gashi tun a yanzu mun faracin tagomashinsa, inaga nan gaba kuma ka zama cikakke. ALLAH yay maka albarka ya ƙara ƙwaƙwalwa. Akwai wasu bayanai da nakeson sake tattarawa, dana kammala zan baka wani aiki insha ALLAHU”.
“To yayanmu ngd sosai. ALLAH ya ƙara girma da nasarorin rayuwa”.
Murmushi kawai AK yayi da amsawa da amin akan laɓɓansa. Daga haka suka koma wata hirar kuma.
_______★
Sam su Zinneerah basusan da dawowar AK gidanba, tunda su Jamal suka ƙaru sai sukai zaman sake babin sabuwar shafta, sun dai san Khalipha na nan, tunda bayan mai gyaran ya kammala ya sanar mata zai jira dawowar Yayan nasu.
Kiran sallar la'asar ya saka Jamal da Nawaf fitowa massallaci, shine suka haɗu da Khalipha da yayan nasu. Sunata faman sinne kawuna da tunanin zai musu faɗa sai sukaji tsit, tundama ya amsa gaisuwarsu yay gaba bai sake cewa dasu uffanba har aka idar da salla suka fito.
Khalipha ne ya dubesu lokacin da suke shigowa harabar gidan. “Guys kuje ku tattaro waɗan can sauran yan-yan ɗin muwuce gida haka nan”.
Cikin marairaicewa Jamal yace, “Wayyo Yaya Khalipha Please sai anyi magriba zamu dawo fa, can gidan duk mutane, ni wlhy suna takuramin”.
“Ƙaniyarkace mutanen, dalla jeka kirasu mu wuce. Mutanen da kake magana ba duk sun kama gabansu ba, ga aiki can a gida kunzo nan kun zauna”.
Baki cike da iska Jamal ya wuce ciki kiransu Meenal. Duk wannan abin dake faruwa AK na ɗan gefensu kaɗan yana waya, sarai kuma yanajinsu amma sai baima nuna kunnensa na akansun ba. Ba'afi mintuna uku ba sai gasu sun fito harda Zinneerah da fuskarta ke a ƙwaɓe.
Sam bata lura da AK ba, dan haka kai tsaye ta isa gaban Khalipha. “Wayyo Yah Khalipha dan ALLAH ka barsu, hirafa suke tayani”. Ta ƙare maganar hawaye na sakko mata a kumatu.
Tausayi ta bashi dan yasan shaƙuwa da sabon dake a tsakaninsu, sannan kuma akwai rashin sabon nan ɗin tattare da ita. Balle Yayan nasu daba sakewa ya iya da jama'a ba sai yaso dan kansa.
Murya ya kwantar sosai cikin lallashi yace, “Haba auta ai abun sai ya zama rashin hankali kuma. Kiyi haƙuri gobe idan ALLAH ya kaimu sai su dawo ku ɗora daga inda kuka tsaya tunda ku shiririta bata ƙare muku. Kinga yanzu aikine a gidan can sosai, su kuma da zasu taimaka sunzo nan sun zauna aikin yama su Ni'ima yawa.”
“Amma Yah Khalipha zasu koma ai, kaga yanzu suna tayani hira”.
“Indai hirace karki damu ga Yayanmu nan a gida ai zai tayaki”.
Batare da tunanin yana a wajanba tace, “Tab, Yayanmu ne zaiyi hira? Wanda ko dariya yana shekara baiyita ba ma......”
Karaf Bahijja ta katseta da faɗin, “Baya hira, amma ya iya soyayya, nifa nan gidan zanma dawo da zama yasin nasha kallo, dan na taɓa ganin wata zazzafan soyayyar Yayanmu da aunty Farah wani zuwa da sukayi na rakasu gidan Uncle Yusif, ku kunga abu, wlhy Zinneerah zaki sh.......”
“K!”.
Khalipha da abin ya ishesa yay saurin katseta. tun fara sakin zancen nata yake mata alamar tai shiri amma taƙi fahimta. Suko su Jamal hannu suka ɗora bisa kawunansu suna zaro ido da bubbuga bakinsu na mata alamar tai shiru, amma ina yarinyarnan kamar an kunna mata batir. Tsawan da Khalipha yay mata kuwa baki ta turo, cikin ƙunƙuni tace, “Yah Khalipha labarifa nake baku dan kuma ku koya irin ƙwarewan Yayanmu kuma ku dinga yi”.
Kai kawai Khalipha ya girgiza yana ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ganin Yayan nasu ya nufo inda suke yana saka wayarsa aljihu alamar ya gama.
Gyaran murya ya ɗanyi, ba Bahijja mai bada lecture ba hatta Zinneerah sai da hanjin cikinta ya wantsala suka juyo a firgice su uku harda meenal dan sune dai suka juyama inda yake baya.
Kafinma yace dasu wani abu Bahijja da Meenal sun kwasa da gudu hanyar gate, Jamal da Nawaf duk da sunsan dashi a wajen suma dai rufa musu baya sukayi dan hanyar lafiya a bita da shekara.
A bazata dariya ta suɓucema Zinneerah duk da itama fa a tsoracen take. Amma yanda su Jamal suka dafe ƙeya dasu Bahijja ya bata matuƙar dariya. Khalipha da shima dariyar yake dannewa tana kufcewa ya afka mota yana faɗin, “Mu kwana lafiya Yayanmu”.
Kai kawai ya jinjina masa tashi fuskar babu ko ɗigon murmushi ammafa a ransa dariya yake ɗan rainin wayon😂. Dan duk dauriyarka dolene abinda su Meenal sukai ya baka dariya. Maigadi kansa dariya yakeyi dan har bangajesa sukai wajen gudu.
Ganin Khalipha zai wuce Zinneerah ta shirya nata gudun itama amma tana ɗaga ƙafa zata fece taji an cafko mata hannu. Gaba ɗaya ta rikice, dariyar data rage a saman fuskarta ta ɓace ɓat. Baya ya dawo da ita gabansa yana kallonta da birkitattun idanunsa dake neman sakata sakin fitsari dan fuskar ta kuma tsukewa tamau. Shi dai Khalipha motarsa ya harba yana dariyar ƙeta, dan yasan dai Bahijja ta kunno wuta. Kuma gaskiya ta faɗa indai soyayya ce kam Yah Abdul-Mutallab ba'a magana, shi da yake rayuwa a gidansu yake shan kallo.
Cikin tsagwaron marairaicewa Zinneerah da idanunta ke tara ƙwalla tace, “Yayanmu wlhy bance komaiba, ALLAH Bahijja ce ka tambayi Yah Khalipha kuma. Uffan baice mataba, sai jawota da yay a hankali ta faɗa saman jikinsa, rawa jikinta ya fara, batare da yabi takanta ba ya ɗauketa cak a bazata. Babu shiri ta cusa kanta a ƙirjinsa dason sauka amma tama kasa motsawa. Koda suka iso ƙofar falon da ƙafa ya tura, hakama da sukaje ta sashensa da ƙafa ya tura, duk yanda take zame-zame bai direta a ko inaba sai falonsa.
Tanajin ya ajiyeta ta ɗago fuskarta daga jikinsa dajan jikinta dake ɓarin tsoro baya dan catake ko duka zataci, duk da dai bata taɓaji a tarihi ko labarinsa ya taɓa dukan kowaba a gidan nasu, barsa dai da barazana da mazurai, hana rantsuwa marin da yayma matarsa a london sanda ta shaƙeta, shima ba wani lura tai da ƙyauba ranar dan a firgice take sai da su Meenal suka bata labari.
Baya ta dinga ja tana girgiza kanta. “Yayanmu ALLAH bance komaiba, ka tambayi Yah Khalipha”.
Hannayensa ya zuba a aljihu duka biyu yana binta a baya fuska a tamke, sai wani lumshe idanu da buɗewa yakeyi akan lips ɗinda dake motsawa a hankali da yanayin tsoron daya bayyana ƙarara a fuskarta. Tana tafiya yana binta sai ji tai ta dangane da bango, juyawa tai a firgice ta kalli bayanta, ganin dai da gaske tazo ƙarshe hankalinta ya ƙara tashi, ta dubesa da saurin yin ƙasa zata durƙushe ya riƙo hannunta.
“Yayanmu wl.....”
“Shiiii!!!..”
Ya faɗa a hankali yana saka idanunsa da suka canja launi cikin nata, tare da saka duka hannayensa a bangon ya dogareta yanda babu damar kuɓuta kenan. Gashi ya hana kuka dole kuma ta haɗiyesa, sai dai zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito.
A wani irin ƙasa da murya sosai ya fara magana idanunsa cikin nata da takeson janyewa ya hana. “Dama idan kuka zauna gulman mutane kawai kuka iya ko?”.
“Wlhy a'a Yayanmu, bama gulmar kowa ka tambayi Granny”.
“Ni yanzu danaji ana tawa fa?”.
“Y...y...Yayanmu ba gulm...ma bane fa?”.
“To miye sunansa?”
Shiru tai dan batasan mi kuma zatace ba itakam. Hakan datai ya sashi juya idanunsa yana sauke hannunsa ɗaya dake dafe da bango ya maida cikin aljihu. Yace, “Anyhow zan fara hukuntaki kafin ita mai baku lecture ɗin na kamata da sauran ɗaliban nata”.
“Wayyo Yayanmu, wayyo Yayanmu”. Zinneerah ta faɗada iyakar marairaicewar data saka AK cije lip ɗinsa, yana binta da wani irin ƙasalallen kallon daya saka hawayen ƙaryarta ɗaukewa ɗaf ta shiga mar mar da idanu zuciyarta na harbawa da sauri-sauri..........✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
[10/22, 3:27 PM] Queen Meenali👑Mrs Misbah💗: *_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
_________________________
*Page 57*
...........“Nine kuma bana dariya sai shekara-shekara ko?”.
“A'a wlhy Yayanmu bakai nake nufi ba, wani ne acan Danya”. Zinneerah ta faɗa tana duban gefen daya janye hannunsa. Hakan yayi dai-dai da wayarsa ta fara tsuwwa. Aljihunsa ya kalla da ƙoƙarin zira hannunsa zai ɗakko, ‘Alhmdllh’. Zinneerah ta faɗa a zuciyarta tana kwasa da gudu.
Duk yanda AK yaso danne dariya a yanzu kam ya kasa, dole yay murmushi har haƙoransa na fitowa tare da girgiza kansa kawai.
yace, ‘Zan kamaki har inda zakije ɗin ai” daga haka ya kai wayarsa kunnensa dan Hajiya iya ce.
Zinneerah kam bata tsaya a ko inaba sai bedroom ɗinta nacan ciki, ta murzawa ƙofar key tana sauke numfashi da faɗin, ‘ALLAH na godema daka kuɓutar dani, Bahijja taso jamin salalan tsiya yau, dan ƙila zaneni yay niyyar yi ma’.
Sai kuma ta kwashe da dariya saboda tuno su Bahijja, inama tanada waya yau data kirasu taji yanda aka kwashe. Bata taɓajin takaicin rashin wayarta irin yau ba, harta kaita da zama tunanin yanda wayar ta ɓata abin kamar almara
★★★
Tun abinda ya faru Zinneerah da AK basu sake ganin junaba har akai sallar magriba. Sai lokacin ta fito daga ɗakinta ta duba dining ɗin. Tasha mamaki ganin anci abinci data ajiye. Aranta take tunanin ashe ya shigo yaci abincin. Wajen ta tattara tare da falon, ta saka turaren wuta sannan ta koma ɗaki tai wanka. Tana fitowa sallar isha'i ta gabatar, bayan ta idar tai zamar gyara jikinta ranta fal tunanin mmn sadiq dasu Abdull, harma da Little da rabota dashi tun randa zata wuce danya. Tana kewarsa sosai harma da ƴan danya ɗin, yanzu da tanada waya ai da ta kira taji yanda suka sauka lafiya da jikin Tinene kuma. Tsaki ta ɗan ja ranta duk babu daɗi. Doguwar riga kawai ta saka yanda zata sake, tana ɗaure gashinta data taje taji an turo ƙofar ɗakin.
Juyowa tai a hankali tana duban ƙofar aɗan rikice, wanda tayi zaton dai shine, yana sanye cikin wando jeans baƙi da baƙar t-shirt, sosai kayan sukai masa ƙyau duk da alamu sun nuna badan kwalliya ya sakaba.
Ganin yanda idanunsa ke a kanta yasata yin ƙasa da nata, ya ƙaraso cikin ɗakin kansa tsaye da tafiyarnan tasa daba garaje, ga fuskar kuma babu alamar fara'a kamar ko yaushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da kwarjininsa fita ba a bayyane.
“Barka da dare”.
Ta faɗa kanta a ƙasa da ƙoƙarin jan gyalen jallabiyar zata yane kanta duk da bata kamla ɗaure gashin ba. AK da tunda ya shigo idanun nasa ke akan gashin nata ya janyesu yana zama bakin gadon. Batare da yayi mata magana ba ya miƙa mata wayarsa.
Amsa tayi duk da bata fahimci mi yake nufi ba, sai dai ganin sunan Granny da alamar tana online yasata kai wayar kunnenta tai sallama murya a marairaice.
Dariya Granny tayi daga can da cewar, “Inno irin wannan marairaicewa haka?”.
“Granny nayi kewarki ne”.
“Nima haka Inno, shiyyasa nace Moddibo ya banike na karajin muryarki kafin na kwanta”.
A take hawaye suka ziraro a kumatun Zinneerah, muryarta ta fara rawa alamun kuka. Kai kawai AK ya ɗan girgiza da mikewa tsaye, batare da yace komaiba ya zare wayar daka kunnenta....
Da sauri ta kallesa dai-dai yana maida wayar kunnensa. Idanun nasa ya ɗan juya mata da faɗin, “Daga gaisuwa kuma sai ki samin ita kuka Granny? To an fasa gaisuwar dake sai da safe”.
Da alama wata baƙar maganar ta faɗa masa daga can, dan janye wayar yay yana murmushi. Batare da yacema Zinneerah dake sharar ƙwalla uffanba ya raɓata ya wuce inda ta ajiye masa system ɗinsa daya bari a ɗakin jiya. Ɗauka yay tare da nufar ƙofa yana faɗin, “Ki kawomin lipton”.
Baki ta kuma tunzurawa tana matso hawaye da bin bayansa da kallo harya fice, babu yanda ta iya dole bayan ta gama kukanta ta share hawayen da ɗaukar turare ta ƙara a jikinta, hardasu fesa much freshener kamar yanda Hajiya Falmata ta koya mata, ta ɗauka wani ɗan kwalban turare da batasan kona minene ba ta shafa a bayan kinnenta da wuyanta, kamar yanda Hajiya falmatan ta sanar mata ta ringa shafa shi duk dare idan tai wanka, ta kuma ƙara da khumra mai shegen daɗi da narkar da mai shaƙa.
Daga haka ta ɗau hijjab mai hannu jaa ta saka sannan ta fito. Kitchen ta nufa ta ɗaura masa lipton ɗin da ganyen shayin da hajiya Falmata ta bata shima, rashin wayonta yasa batai tunanin ko ganyen shayin na wani abu baneba daban. A wani butar shayi mai azabar ƙyau daya ɗauka hankalinta ta juye tare da kananun kofunansa tasa biyu, sai ɗan bowl ɗin data zuba suger shima ta ɗora da tea spoon guda ɗaya ta ɗauka tray ɗin tana addu'ar ALLAH yasa tayi komai dai-dai.
Yana zaune a doguwar kujera ƙafarsa a miƙe yasa filo da ɗaura lap-top ɗinsa saman filon. Koda tai sallama bai dagoba amma ya amsa mata a saman laɓɓa yana cigaba da aikinsa.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta, a centre table ɗin tsakkiyar falon ta ɗaura ƙaramin tray ɗin da jawosa kusa da shi tace, “Yayanmu gashi”.
Ɗan ɗagowa yay yayi mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, a taƙaice yace, “Zuba”.
Kanta ta jinjina masa kawai ta tsugunna gaban table ɗin tana ƙoƙarin fara zubawar, yanda hijjab ɗinta yay ɗan bula lokacin da take kaiwa tsugunne ya bama hancinsa damar shaƙo fitinannun ƙamshin turarurrukan data sakama jikinta, duk da tun shigowarta ya jisu, sai haka datai ya ƙara ƙarfinsu fiye da farko a cikin hancinsa.
Wani irin harbawa zuciyarsa tayi, har baisan yatsunsa sun kauce wajen tafa saƙon shirme ba a system ɗin. Ya lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta yana ɗan cizar lip dinsa na ƙasa.
Zinneerah da batasan mi yake cikiba ta miƙo masa ɗan mitsilin tea cup ɗin irin na larabawa bayan tasa suga ɗaya dan tasan yanda yake so tunda yasha sata aikin sanda suna gida, tsaf ta gama haddace adadin da yake so.
Idanunsa da suka canja launi lokaci guda ya zuba mata, dai-dai yana amsar shayin muryarsa a ƙasan maƙoshi yace, “Cire wannan hijjab ɗin banaso”.
Mamakin maganar tasa yasata ware idanu sosai tana kallonsa. Sai dai yanda fuskarsa ke a ɗinke ya sata yin ƙasa da kanta ta hau ƙoƙarin cirewa tana haɗiye abinda ya tokare mata maƙoshi, dan duk da doguwar riga ce a jikinta tsananin kunyar zama take a gabansa a haka saboda santsin rigar yasa ta kwanta mata a jiki ta lafe, musamman da yazam ita da kanta ta rage faɗin rigar tun suna gida ita dasu Bahijja.
Hannu ya miƙa mata alamar ta bashi, dole ta miƙa masa, kusa dashi ya ajiye hijjab ɗin dan son tabbatar da shike ƙamshin ko ita?.
“Zauna”. Ya faɗa yana matsar da ƙafafunsa. Yanzun kam kasa haƙuri tayi sai da tace, “Yayanmu zanje na kwanta inajin barci”.
“Nima ba gadin gidan zanyiba ai”. Ya bata amsa a daƙile.
Tashi tai tsam ta zauna inda ya nuna matan har jikinta na neman hayemasa ƙafafu, tai saurin muskutawa kanta a ƙasa.
Idanu ya tsira mata yana kurɓar shayin kaɗan-kaɗan saboda zafinsa. Amma dai haka yafi bukatarsa musamman wannan da yay masa matuƙar daɗi, ga wani irin ƙamshi mai daɗi dake fita a cikinsa.
Ya fahimci ta matuƙar ƙwarewa da iya cuɗa hannunta cikin na juna idan tana waje a takure ko makamancin hakan. Ya danyi gyaran murya nason gusar da shirun nasu. Ɗagowa tai ta kallesa.
Idanunsa a cikin nata yace, “Kin kira su baba ne? Kinji yanda su gwaggo sukaje gida lafiya”.
Ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi, atake idanunta suka ciko da ƙwalla ta girgiza masa kai. “A'a ai bani da waya ta ɓata”.
“Ɓata fa? A ina kenan?”.
Da damuwa sosai a fuskarta tace, “A can gida, tun lokacin da Granny bata da lafiya zaku wuce london”.
Cikin ɗan taɓe baki yace, “Kin dai jefashi wani waje”.
“A'a wlhy Yayanmu, nifa ina gama waya da Mama a ranar daga ajiyewa naje na tarosu na nemeta na rasa. har yanzu kuma ban ganshiba, kuma ko ina su Meenal sun tayani na duba”.
“Uhm to wani ya sace kenan”.
Ya bata amsa cike da basarwa.
Itako tace, “Amma kuma a gidan nan wazai saci waya?”.
Wani ɗan murmushin daya bata mamaki taga yayi yana lunshe idanunsa. Cikin basar da maganar yace, “Ganyen shayin nan yanada daɗi waya baki?”.
Badan taso barin waccan maganarba tace, “Hajiya Falmata”.
“Wacece ita?”.
“Nima sai kwanan nan na santa suna mutuncine da Granny”.
“Uhm! Itace ta baki wannan turaren mai ƙamshi haka?”. Ya faɗa murya a shaƙe dan shayin da yasha ya fara aikinsa.
Rasa amsar da zata bashi tayi, sai ta ɗan jinjina kanta kawai.
“Baki da baki ne?”.
“A'a kayi haƙuri itace ta haɗa, khumrah ne”.
Komai bai sake faɗaba ya sauke lap-top ɗin dan aikin kam bazai iya cigabuwaba, ƙafafunsa ya zaro daga kusa da ita ya ajiye ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar, sake ɗaukar butan shayin yayi ya tsiyaya dasa suga ɗaya a ciki ya motsa. Cigaba da shan abinsa yayi da maida hankalinsa ga television. Itama gyara zamansa da yayi ya sakata jin ɗan sanyi ta koma kallon television ɗin da satar kallonsa. dan ya dage sai ɗora shayin yake hankali kwance. Daya shanye yake karawa, tanata lissafi sai da yasha kusa cups bakwai duk da dai ɗan mitsitsine kofin.
Sai da aka kammala labaran da suke kallo ya miƙe, batare da yayi mata magana ba ya fice gaba ɗaya a sashen har tana mamakin ina zaije? Bata da mai bata amsa dan haka ta ƙudiri aniyar zaman jiransa ya dawo ita dai taje ta kwanta ta farajin barci.
Shiko daya fita kai tsaye sashenta ya nufa, kitchen ya fara shiga ya kaso wutar can ya rufosa. ta Dining ma ya kashe tare da leƙa bedrooms ɗin dake a falon duk yaga akashe sannan ya nufi nacan ciki da take amfani da shi.
Akwatin kayanta ya buɗe, duk da shi ba mutum bane mai buƙatar matarsa tasa kayan barci idan zasu kwanta tare ba, yafi buƙatar tazo masa a natural ɗinta, hakan bai hanashi ɗauka mata suba. Sai dai yau ba kamar jiyaba sai da ya zaɓo dai-dai da ra'ayinsa. Gaban Mirror ɗinta yaje nanma ya shiga shinshina turarurrukan wajen kamar mai neman wani daban. Sai dai abin mamaki ya kasa tantance wanda yake buƙatar jin, har takai ya fara buɗe kwalaben khumra dake wajen kusan kala shidda dan bama a kawo mata sauranba tukunna. Ya ɗan samu wasu a ciki, harya ɗauka biyu sai idonsa ya sauka akan kananun ƙwalabe dake cikin wani haɗaɗɗen kwandon saƙa na kaba da aka zubasu ciki kusan kala goma nanma. Murmushi ya danyi dan shi mutum ne mai son ƙamshi, ƙamshi yana ɗaya daga cikin abinda Farah tai galaba a kansa kenan dan itama gwanace wajen baza turare. Nanma shinshinawa ya ringayi ɗaya bayan ɗaya, sai dai ya kasa tantance wanda yafi daɗi da wanda yaji a jikinta. Sai ma neman rikita masa lissafi sukeyi. Nanma biyu ya zaɓa a ciki ya fice bayan ya kashe komai. falukanma duk kashe komai yayi ya rufe sashen baki ɗaya ya nufi nasa.
Zinneerah da har ta gaji da jiran dawowarsa ta jingina da makarin kujera tana lumshe idanu ta buɗesu a hankali jin sallamarsa. Bataga mike hannunsaba dan kai tsaye bedroom ɗinsa ya nufa. Zamanta ta gyara da ɗaukar hijjab ɗinta ta riƙe a hannu gudun kar tai laifi.
Babu jimawa kuwa sai gashi ya fito, batare da yay mata magana ba ya ɗauka remote ɗin tv ya kashe tare da nufar fridge, yana juyowa ɗauke da fura a hannu tana miƙewa. Fuskarta a marairaice tace, “Yayanmu zanje na kwanta barci nakeji”.
Baiyi maganaba sai da ya karaso, ya ajiye roban furan da kamo hannunta ya zaunar. “Zauna kisha wannan sai kije ki kwanta”.
Cikin langaɓe kai tace, “ALLAH yayanmu na ƙoshi barci nakeji kawai”.
Harar daya zuba mata tasata ɗauka dan harya buɗe mata robar, cokalin dake haɗe da robar furan ta ɗauka ta fara sha a hankali tana lumshe ido dan barci takeji, sosai furan na mata dadi sai dai barci na neman kwafsa mata. Shiko lap-top ɗinsa ya ɗauka yana ƙarasa aikin nasa.
“Yayanmu ALLAH ta isheni barci”.
Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, yaɗan jinjina mata kai kawai yana ajiye lap-top din daya kashe gaba ɗaya. Miƙewa yay hannunsa ɗauke da remote na ac ya kashe. Sannan ya tattara wayoyinsa da nuna mata hanyar ɗakinsa.
Sosai ta ɗan waro masa manyan idanunta dake cike da barci waje. Sai dai yanda ya tsuke fuska dole ta haɗiye abinda ke bakinta ta maida kanta ƙasa. Sum-sum ta fara tafiya hanyar ɗakin da bata taɓa shigaba. Kasancewar ya tsaya kashe fitila ta rigasa shiga ɗakin. Da wani ni'imtaccen ƙamshi tafara cin karo, ta ware idanunta sosai tanabin bedroom ɗin da kallo baki sake. Komai yaji masha ALLAH, white and golden kamar kaci dan ɗaukar idon mai kallo. Ga uban sanyin ac.
Tana tsaye a wajen harya shigo bata saniba. Sai jitai kawai anyi sama da ita gaba dayanta. Sosai ta firgita sai dai babu damar yin magana. Bai direta ko inaba sai toilet ɗinsa da komai yake a tsare kuma a tsaftace. Dan shi kansa kamshi yake na musamman.
“Kiyi alwala”. Ya faɗa kansa tsaye. Sabo da alwalar kwanciya barci yasa bataji komai a rantaba, gashi dama ko shafa'i da wutiri ma bataiba. Alwalar ta ɗaura yana kallonta cike da nazari, da alama yana tabbatar da ingancinta a fannin addinine ne. Sai da ta kammala shima ya ɗaura tasa suka fito tare kamar yanda yay mata alama da ido.
Da kansa ya sa musu abin salla. Ganin yayi tsayuwar alamar jansu salla yasata kallonsa da mamaki. “Yayanmu nayi sallar isha'i”.
“Nima nayi ai”.
Shiru tai bata ƙara maganaba harya tada sallar, itama tayarwar tayi dan bin umarni shine masalaha a gareta. Sunyi salla raka'a biyu suka ɗora da shafa'i da wutiri, sannan ya juyi ya dafa goshinta da ambaton.
*اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ*
*_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._*
_Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._
Lumshe idanunta tayi tana sauraren daddaɗan muryarsa mai cike da kamun kai da nutsuwa. Bayan ya kammala ya juya da ɗaga hannayensa sama ya cigaba da kwararo addu'oi kala-kala da harshen larabci.
Sai da suka kammala addu'ar ya juyo yana fuskantarta da ƙyau. Tambayoyin ya fara mata a fannoni daban-daban daya shafi addini, wasu ta amsa wasu tace bata saniba dan a yanzu take kan neman ilimi, danma Alhmdllh batai wasaba akan hakan tunda ta dawo da zama kano.
Ya gamsu da yanda tayi ɗin, ya kuma karba uzirinta, daga haka ya miƙe yana magana batare daya kalletaba. “Ga kayan barci nan ki canja”.
Yana fa ɗaya yana nufi hanyar toilet. Kaɗan ya rage Zinneerah ta saki kuka amma ta dake ranta fal tsoro. Kenan anan zata kwana tare da shi yau ma?. Ta ayyana a ranta. Sanin bata da mafita kuma baya maimaita magana, gashi batason ya fito ya sameta batai abinda yaceba yasata ƙoƙarin canja kayan. Ganin turarrukanta tare da kayan ta mulke jikinta dasu duk da kuwa ƙamshin take dama. Tana gamawa yana fitowa ɗaure da towel jikinsa nata raɓar ruwa. Ƙasa tai saurin yi da kanta tana gyara zaman hijjab ɗinta data ɗora saman kayan barcin. Komai baice mataba ya hau tsane jikinsa da towel ɗin daya ratayo a wuya.
Da wannan damar ta wuce toilet ɗin nasa sumi-sumi danyin brush tunda taga sabbi a toilet ɗin, dan ta tuna Hajiya Falmata tace duk rintsi karta kwanta batai brush ba, idan da dama ma ta haɗa da much freshener, sannan ta tabbatar duk sanda zata kwanta barci tayi tsarki da ruwan ɗumi koda ace ta yini amfani da shine.
Brush ɗin ta farayi, sannan tai fitsari dayin tsarki da ruwan ɗumi. Much fresheners ɗinsa data gani ajiye a ɗan drawer ɗin glass ɗin toilet ɗin ta ɗauka, dan gasunan kala-kala, banana, cucumber, kai kala-kala ta fannin fruit duk gasu nan. Son da takema S...barry ya sata ɗaukarsa shi da banana ta saka sannan ta fito cikin sanɗa, a ranta tana addu'ar ALLAH yasa ya gama shiryawa dan shiyyasama ta daɗe danta bashi dama.
Tsaye ta iskesa gaban mirror sanye da wando 3quarter iya cinya da riga mai buɗaɗen ƙirji farare tas. Yana fesa turare. Ta madubi yake kallonta harya kammala sannan ya juyo...........✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
[10/22, 3:27 PM] Queen Meenali👑Mrs Misbah💗: *_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 59*
________________________
*_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_*
*_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_*
_Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._
*Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.*
*_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_*
_A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻
Available
_Akwai: herbal whitening black soap 3k_
Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6
Soap
Body cream
Face cream
Body nd face scrub
Cleanser
Glow oil
Location
kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery
WhatsApp 08062991549
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
*_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._*
________________________
*Page 59*
............Koda ya dawo bedroom ɗin wanka kawai ya shiga batare daya tada Zinneerah ba. Harko ya fito ya kammala shirinsa tsaf cikin ƙananun kayan da sukai masa matuƙar ƙyau da ƙara fidda kwarjininsa da ƙuruciya bata farkaba. Yana tsaka da saka turare ya jiyo ana danna door bell, ajiye turaren yayi ya ɗauka wayarsa da ƙarasowa gaban gadon saitin da take kwance. Wani lallausan murmushi yake saki yana ƙarema fuskarta kallo musamman bakin daya tsuƙe. A hankali ya ranƙwafo ya sumbaci bakin da hancinta da goshinta, yana motsa laɓɓansa a hankali wajen ambaton, “ALLAH ya albarkaci rayuwarki”.
Daga haka ya fice abinsa. Yana buɗe ƙofar da Hajiya iya da Moos'ab ya kawo yaci karo. Ta zuba masa harara da faɗin, “Shegen gida kamar na ƴan yankan kai, sai ka danna ƙararrawa an gama yarfaka za'a buɗe maka”.
“Oh-oh daga zuwanki sai neman faɗa, yi haƙuri ni yau bana faɗa”.
“A lallai ai naga alama a goshin ka ma ja'iri mara kunya”. Hajiya iya ta faɗa tana turesa da shigowa cikin falon abinta.
Murmushi ya ɗanyi dakai hannu ya murza goshinsa. A ransa yana faɗin ‘Mi matarnan ke nufi dani?’. Bashi da mai bashi amsa dan haka yay ƙoƙarin bin bayanta. hannunta ya riƙo ganin ta nufi sashen Zinneerah. “Kinga inda zakiyi nan madam”.
“Kai ni sakeni naje na fara ganin Inno tukunna, haka kawai ka wani tattaromu sai kace ƴaƴanka”.
“Uhm ke dama ba'ayi miki dai-dai, ai Innon taki na inda zan kaikin ko”.
“Ato muje naga abuta dan nikam ban yarda da wannan munafurcin nakaba yau Moddibo”.
Murmushi kawai yayi batare da yace mata komaiba suka nufi sashensa. Kamar jira suna isa falon saiga sallamar Haneef. Zaunar da hajiya iya yayi sannan ya amsa da cewa “Shigo da su”.
Kasancewar dama Haneef na tare da Mahma da Gwaggo Maryama da duk hankalinsu ke tashe da wannan kira na AK ɗin sai ya matsa musu alamar su shiga. Shi kuma ya juya.
Cikin girmamawa AK yay zaman gaishesu su duka. Cikin rashin haƙuri Hajiya Iya tace, “Mukam dai duk ka tada hankalinmu Moddibo, mike faruwa ne? Ina Inno kuma?”.
Ɗan dubanta AK yay yana maida kansa gefe da faɗin, “Ku kwantar da hankalinku ba wani abu bane, na saku zuwa nanne domin ku zama na farko dazan fara tabbatarmawa kafin kowama ya sani”.
Hajiya iya dake cikin jimamai tace, “To muna saurarenka, ALLAH ya jishemu alkairi”.
Da amin Mahma da Gwaggo Maryama suka amsa. AK ya gyara zamansa kansa a ƙasa dan nauyin maganar da zaiyi. “Kuyi haƙuri duk da ba magana bace wadda ya kamata kusani, amma saboda wasu dalilai naga ya dace ku sani ku kuma zama hujja akan binciken da zan ƙarasa. Mu dukanmu nan munsan cewar Zinneerah ta haihu a shekarun baya, kuma koda yaushe maganarta shine batasan a inda ta samo ciki ba. Wasu kan ɗauketa mara hankali, wasu na ganin tana wasa da hankalin mutanene kawai ko rainin wayo da makamantan haka. Wasu kuma kan mata uziri da cewar ƙaddara ce ta afka mata. Tabbas ƙaddara ce, da a zahirance zamu iya kiranta *_MAKAUNIYAR ƘADDARA_*. ALLAH shine shaidata ban taɓa taɓa ƴar kowa ba da nufin fasiƙanci. hakkane ya tada hankalina matuƙa akan Zinneerah har takai bana iya barci, a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya cikin shan maganin hawan jini nake saboda tashin hankali da tunanin ta hanyar da aka samar da Abdul-Mutallab, sai da Granny ta kawo wani zance da Khalipha yayi akan dashen ciki sannan ALLAH ya haskamin hanya. A dalilin haka na cigaba da bibiyar abubuwa da dama a ɓoye batare da sanin kowaba, har ALLAH ya tabbatar a yau nakai gaɓar da nine na farko da zan fara tabbatarma duniya lallai dashen cikin Abdul-Mutallab akaima Zinneerah bata hanyar banza ta samoshi ba. Dan bata taɓa tarayya da namiji ba sai daren jiya. Inaji a raina ALLAH ya keɓance tane daga haihuwa da kanta sai cs akai mata domin irin wannan ranar dazai wanketa ga kowa”.
Kallon kallo aka shigayi tsakani Mahma da Granny da Gwaggo Maryama, shi dai AK tunda ya fara bayaninsa harya ƙare bai yarda ya kallesu ba idanunsa a ƙasa.
Cikin karfin hali Mahma ta katse tararrabin su ta hanyar kallon AK da faɗin, “Abdul-Mutallab ka sakamu a duhu nikam, kenan tayaya aka dasama baiwar ALLAH nan gudan jininka?”.
“Wannan ne nakeson sani yanzun, amma Mahma kiyi haƙuri, inaga wannan abin ba kowa bane ya ƙullasa sai Zakiyya, Farah da Mammah, dan naji wasu zantuka nasu da suka rikitani jiya da rana sanda nazo gidan nan, to kafin na shigo na fara samunsu a garden ne amma su basu san na jiba. Sannan idan kin lura duk sanda akai maganar dashen cikin nan sai sun razana. Dalilina na biyu Dr Mahmud ya tabbatar min shi baiga wani alamun mai ciki tattare da Farah ba. Sannan ni kaina idan zanyi aiki da hankalina ai ciki girma yakeyi a jikin mace, amma ace kusan 5months babu wani alamarsa a jikin Farah. Idan baki mantaba cikin farko data samu tun yana wata uku suka matsa sai da ta tafi Morocco, bata dawo London ba sai da tai ɓari kamar yanda suka faɗa. To wannan ma a ƙiyasina tun yana wattani ukun ta shiga damuna zataje, amma zuwan danai da Granny ya sani taka mata birki. Hujja ta biyu a labarin da Zinneerah ta bamu na zuwanta katsina aikatau yayi kama da wadda aka yaudara saboda ƙuruciyarta, bayan an cutar da itane ta gudo batare da saninsu ba. Abinda kawai ban fahimtaba anan shine Mammah tasan hakan kokuwa ita Zakiyya da Farah ne kawai suka sani ko itama Farah bata sani ba? Hujjata ta ƙarshe samun Zinneerah da martabarta ta ƴa mace”.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” Mahma dasu Granny keta ambata, hawaye suka shiga sakkoma Mahma, tasa hannu ta sharesu da faɗin, “Lallai biri zai iyayin kama da mutum Abdul-Mutallab, dan nima kaina ina mamakin rashin tasawar cikin Farah. Sannan akwai wasu abubuwa na rashin gaskiya da zakaga suna shan aikatawa a wani lokaci kuma, lokacin cikin farko na taɓajin wata wayarta da Adilah lokacin tana hostel a makaranta, sai dai ina shiga ta yanke wayar. Indai kuwa hakane sun cutar da yarinyar nan matuƙa, sun ɓata mata suna, sun sakata wahala da ƙarancin shekaru. Wane irin son zuciya ne wannan? Kai kanka damu sun cutar ai”.
Ta kare maganar tana kuka sosai. Gwaggo Maryama ma hawaye takeyi, Granny dai idanunta sunyi matuƙar yin jajur alamar shiga ƙololuwar ɓacin rai. taja numfashi mai zafi da faɗin, “Lallai kayi haƙuri Moddibo, idan har ta kasance wannan zancen ya zama gaskiya sai nayi shari'a da uwarka da matarka. Dan wlhy sai na bima inno kadin haƙƙinta. Yanzu abinda nakeso da kai kar kai musu maganar komai, kuma tabbas inaga Zakiyya itace hajiyar da aka kai Inno gidanta. To karka yarda su haɗu anan gidan yanzun, dan idan suka gane itace zasu iya bin wata hanyar suga sun rufe asirinsu. Abinda nakeso dakai yanzu daganan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ka aika hukuma a kama matar data kai Zinneerah aikatau katsina, itace zata kaimu ga hajiyar farko, ita kuma ta kaimu wajen wadda Zinneerah ta faɗa mana tata jerangiya da ita asibiti, na tabbatar zamu kamo bakin zaren insha ALLAHU.”
Duk da kalaman cewar sai tayi shari'a dasu Mammah ya bashi tsoro dan yasan Granny akan tsayawa wanda aka zalinta hakan bai hanashi ɗaga mata kai ba cikin girmamawa yace, “An gama insha ALLAH, dan yanzu hakama zancen da nake miki tana police station tare da Khalipha. Tun da safe yaje Dayan akanta, ya tatar tana katsina, shine ya zarce can har inda take bisa taimakon wani bawan ALLAH ɗan nan Danya ɗin. Dan da nace a fara kamamin matar baba sai Khalipha ya bani haƙuri akan a barta kodan darajarsa dan yama tarar itama bata da lafiya. Mu kama matar dai kawai tunda ta hanyartane kawai za'a iya bin diddigin abun”.
Mahma tace, “Alhmdllh hakan da kukai shine dai-dai, yanzu yaya akai mi matar tace?”.
“Mahma ba'akai ga tambayarta komai ba, dan inaga ko mintuna goma basuyi da isowaba ma, ina gama waya daku ya kirani yake sanarmin ya dawo harda matarma tana station yanzu haka”.
Gwaggo Maryama dai ta kasa tofa komai, sai hawaye taketa faman zirararwa. Hajiya iya tace, “Kabeer ya san duk wannan?”.
“A'a ban faɗa masa ba”.
“To ya kamata ya sani dagashi har Ahmad da Abubakar (Abba mijin maman sadiq) da baban ita Zinneerah, dan babbar maganace wannan data wuce yinta iya mu kaɗai”.
“Babu damuwa Granny, dama ai dole zasu sani, dama munason mu kammala gano inda mutanen suke tukkuna sai na sanar dasu. Amma tunda kinga ya dace su sani tun yanzu shikenan”.
Mammah ta buɗe baki zatai magana kenan sai ga Zinneerah ta fito tana tafiya a hankali batare da tasan da zamansu a falonba. Ita cama take AK ɗin baya gidan, dan tun ɗazu ta tashi, cikin ƙarfin hali ta gyara masa ɗakin da wanke toilet, yanzuma ta fito ɗaukar kayan sharane.
Tun fitowarta ƙamshin turarenta ya isar masa hanci, dan haka ya waiwayo domin tabbatarwa. sai dai yayi dai-dai da suma duk suka ganta ɗin.
Sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu harta iso kusan tsakkiyar falon, turus taja ta tsaya gabanta na faɗuwa ganin yanda suke mata kallon ƙurulla su duka. Sai duk ta daburce dan gani take kamar duk sun san miya faru da ita a daren jiya. Da sauri ta juya zata koma inda ta fito Hajiya Iya tace, “Inno ba gaisuwa?”.
Matse idanunta tai da cije lips ɗinta waje guda tamkar zata nutse dan kunya. Musamman daya kasance cike da tsokana hajiya iya tai maganar.
AK dake binta da kallo ƙasa-ƙasa yace, “Granny ke baki iya gani ki ƙyale?”.
Dariya duk suka ɗanyi, dai-dai Zinneerah na isowa inda suken kanta a ƙasa. Can jikin kujera ta lafe tana gaishesu, saika rantse wasu baƙin tane da bata saniba ko take matuƙar jin kunyar haɗuwa dasu. Yanda tayi ɗin ya bama AK dariya matuƙa amma ya gimtse baiyiba.
“Oh kajimin ja'ira wa kikema wannan lafe-lafen anan to? Koda yake sai dai idan surukarki Zaliha”. hajiya iya ta faɗa tana nuna Mahma dake kallon Zinneerah ɗin da murmushi a fuskarta tanajin tausayi da ƙaunar yarinyar har cikin bargonta. Itace ta tashi tsam ta kamo hannun Zinneerah data kasa tasowa duk da maganar da Granny tayi.
“Haba ɗiyata minene najin kunya, mufa nan duk iyayenki ne, ga kuma kaka nan. ALLAH yay miki albarka kinji, ya sakanka miki da alkairi mai yawa ta inda bakiyi zatoba. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki ya ƙara ɗaga darajarki a wajen mijinki”.
Babu kunya AK yabi sahun ƴan amsawa da amin, sai dai shi a saman laɓɓa yayi saɓanin su hajiya iya da sukai a fili. Ita dai Zinneerah ta kasa kallonsu koda sau ɗaya dan jitake kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki. Dama kuma ga miskilanci data ƙware kuma ta haddace duk da bataima Hajiya iya yau dai itama ta shafeta kam.
Duk yanda sukaso ta sake hakan ya gagara, hakan yasa hajiya iya cewar, “Tunda yanzu baƙya yayina Inno tashi kije abinki, ai gobema rana ce”.
Tsam ta mike a tunaninsu tafiyar zatai, sai sukaga ta nufi hajiya iya. Tana zuwa a jiki ta faɗa mata hawaye na gangaro mata.
“Oh ashe moddibo ne ya fara koya miki gulmarsa ta basarwa kina yina”. Hajiya iya ta faɗa tana shafa kan Zinneerah ranta fes da so da kaunarta data kara ninkuwa a ranta, ga ɗunbin tausayinta kuma.
Albarka suka dinga saka mata AK na tayata da amsawa. Daga ƙarshe hajiya iya ta sata sake basu labarin abinda ya faru a zuwanta katsina. Suka kuma dora mata da ƴan tambayoyin abinda ya shige musu duhu musamman Mahma da hausar tata ba cika yay ba.
Sallamar Zinneerah sukai su kuma suka cigaba da tattarawa, da wannan damar ta samu kuɓuta ta koma ɗakinsa. Barin batun shara tai ta shige toilet tai wanka da sake gasa jikinta da ƙyau, yunwa takeji sosai ga jikinta da takeji fayau, sai bakinta dake ɗaci amma babu zazzaɓin. Sai dai illahirin gaɓɓanta babu inda baya mata ciwo. Taji daɗin ruwan zafin sosai. Dan sai da ta tabbatar ko wace gaɓa tata ta gamsu kafin tai wanka ta fito ɗaure da towel ɗinsa daya tsaya mata iya cinya. Batai tunanin samunsa a ɗakinba tunda tasan yana tare da baƙi, sai dai kuma tana fitowa tai turus saboda cin karo datai dashi zaune a bakin gado yana waya.
Da baya-baya ta dinga jan ƙafarta zata koma AK ya miƙe yana binta da wani shu'umin kallo daya nema harmutsa hanjin cikinta dan tsoro, dan ita dai harga ALLAH wani irin tsoronsane ya sake tasiri a ranta bayan matsananciyar kunyarsa da bata taɓa ji ga wani ba. Ganin ya taso ɗin ya sata kara sauri, sai dai babu nasara dan taku baifi huɗu yayba ya cafkota. Gaba ɗayanta ya jawo jikinsa yana faɗin, “Okay Baffah sai nazo gidan zuwa anjima ɗin”.
Daga haka ya ajiye wayar a ƴar drawer ɗin wajen da suke gab da ita.
“Anya wannan jikan na Granny zatai jarumta?”.
Ya faɗa cikin wani irin kasalalliyar murya dai-dai yana sa kansa a wuyanta. Duk da wanka tayo hakan bai hana tasirin fitar kamshin mayun khurah ɗinta ba. Ya ƙara tura hancinsa cikin wuyan duk da laimar ruwan dake naso a jikinta. Tare da zagayo duka hannayensa akan cikinta.
Cikin rawar murya kamar mai shirin fasa kuka tace, “Yayanmu su Granny”.
“Su Granny mi? Ba suna falo ba muko muna nan abunmu a ɗakin sirrinmu”.
“Amma zasu ce.....”
Ta kasa ƙarawa saboda nauyin maganar.
Yana cigaba da shin-shinar wuyan nata dake tada mata tsigar jiki yace, “Zasuce ina lalube amaryana?. To ai suma sunsan tunda suka bani komaima zanyi baby girl”.
Zinneerah da kunya ke neman kasheta da mamakinsa, tai saurin cewa “Nifa ba hakaba Yayanmu”.
“To yaya ne?”. Ya faɗa yana ɗagowa da birkitota suna fuskantar juna. Kafafu ta shiga matsewa saboda kunyar cinyoyinta dake waje. Yanda take ɗinne ya sashi kallon cinyoyin, idanu ya ɗan lumshe da sake buɗesu a kansu, kafin ya cije lip ɗinsa muryarsa na canja amo yace, “Karfa kisa nai miki wani sabon aika-aikan ALLAH. Muje ki shirya ga abinci har 2 tana neman yi. Kinyi salla ko?”.
Kanta a ƙasa ta daga masa kawai.
“Magana da baki”.
Dole ta buɗe baki tace, “Eh nayi tunma dana tashi naga lokaci yayi”.
“Good. kije ki shirya to, ko na shiryaki ne?”.
Babu shiri ta waro masa idanunta da har yau ke a ɗan kumbure. Shima waro mata nasa yayi sosai. Hakan sai ya sata jin kunya tai saurin saka tafukan hannaunta ta rufe fuska murmushi na suɓuce mata.
Wannan salon nata na nuna yawan jin kunya na kayatar dashi, dan haka ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa yana faɗin, “Ina son wannan salon naki baby. Da gaske fa kina neman shigama Farah hanci, idan kuma ta tashi fyatoki zakiji jiki”.
Gaban Zinneerah ne ya faɗi dan itakam sai an amfaci sunan aunty Farah take tunawa da ita, tare da tuna cewa Yay Abdull-Mutallab bafa nata bane ita kaɗai, akwai wadda ta fita tsananin sonsa da kishinsa, komai kuma zata iya aikatawa akansa. lallai tana cikin lukutin yanayi duk randa aunty Farah tazo Nigeria (dan itafa batasan suna nan ba har Mammah).
Ganin yanda ta koma saboda ambaton Farah da yayi sai ya ɗauketa cak domin gusar mata da tunanin, saman gadon ya ɗorata yana ƙoƙarin kwance towel ɗin jikin nata ta riƙe gam idanunta na firfitowa waje da jera masa roƙon haƙuri jikinta har rawa yake.
Duk yanda yaso ya danne sai ya kasa sai da ya dara. Ya ɗan dungure mata kai da faɗin, “Matsoraciya kawai. Tashi ki shirya kici abinci inason fita”.
Yana gama faɗa ya nufi hanyar fita dan ya bata damar da zata kimtsa tunda ya fahimci a takure take matuƙa.
Koda ya fita ɗakinta ya nufa, babu jimawa sai gashi da kayanta ya ɗakko mata. Less ne zani da riga kalar milk da kwalliyar coffee. Sai B&F ɗinta daya tuno masa randa ya far ganinta a gidan Granny. Haka kawai ya shiga sakin murmushi shi kaɗai tun a ɗakinta. Tana gyar gashinta ya shigo, ganin duk ta daburce sai baiyi magana ba ya ajiye mata kayan kawai a gado ya fice abinsa zuwa falo.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyowa ta kalla kayan nata. Har cikin ranta tanajin daɗin wannan kulawar tasa na yimata hidima batare da duba cewar ya girme mataba. Sannan inda wani ya bata labarin zata iya samunsa haka da sauƙin kai bazata yardaba. Musamman idan tai dubi da halayyarsa da kowa ke kallonsa da ita na rashin sakewa da barazana da rashin ɗaukar raini. Shiyyasa akace karka yankema mutum hukunci har sai ka zauna da shi sannan. Dan wani ɗan adam ɗin ba'a taɓa karantar shi wanene sai an rayu da shi. Ashe wannan damar Farah ta samu daga garesa take yanda ta gadama. A binda kuma ta fahinta da shi adalcine kawai da sanin darajar mace da son mutuntata ya sashi zama mai sauƙi ga iyalansa badan anfi karginsa bane ko bazai iya motsa ƙwanji ba. Jitai wani natsuwa da kaunarsa na sake saukar mata a rai da bargo, har tana jerama UBANGIJI kalaman godiya da samunsa matsayin abokin rayuwarta batare da yayi shawara da itaba ko dubi da cewar AK ɗin ya ɗarata a komai na darajojin duniya, a lahiran kuma tana fata da addu'ar su kasance a muhalli ɗaya a gurbin gidan aljanna insha ALLAHU rabbi..
Da wannan tunanin ta kammala shiryawa a gurgurguje duk tunaninta su Granny na'a gidan basu tafi ba.............✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
[10/22, 3:27 PM] Queen Meenali👑Mrs Misbah💗: *_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 58*
________________________
*_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_*
*_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_*
_Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._
*Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.*
*_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_*
_A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻
Available
_Akwai: herbal whitening black soap 3k_
Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6
Soap
Body cream
Face cream
Body nd face scrub
Cleanser
Glow oil
Location
kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery
WhatsApp 08062991549
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
*_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._*
________________________
*Page 58*
...........Gabanta ya tako a hankali, ya tsaya tamkar zai shige mata jiki. Baice komaiba sai kama hijjab ɗin jikin nata yay ya zare. Ganin yanda ta duƙar da kai ya sashi saka yatsunsa biyu ya ɗago haɓarta. Ba karamin firgita tai ba da ganin yanda ƙwayoyin idanunsa suka canja launi tamkar wani bugagge. Muryarsa a shaƙe matuƙa tamkar mai mura yace, “Turaren nan naki zai kashe ni kairunnisaa”.
Sosai jikin Zinneerah ya hau rawa saboda kusanto da fuskarsa da yay gab da tata, ya ɗaura hannayensa duka a kafaɗarta ya fara tafiya dasu a hankali zuwa gaban gadon, gwiwar ƙafarsa ɗaya ya ɗaura a bakin gadon, hakan da yay ya daidaita tsahonsu. Ya cusa fuskarsa akan dokin wuyanta yana wani jan numfashi a fisge dan neman ƙwace masa yake.
Yanda ƙamshin turaren ke neman zauta masa ƙwaƙwalwa baima san bakinsa ya suɓuce wajen fallasa asirin zuciyarsaba yace, “Ina ƙaunarki da komanki Neerat”.
Yay maganar da in ina jikinsa na wani ɗan tsumar da shi kaɗai yake jinsa a jininsa. Dan ita Zinneerah ma ruɗewar datai da salon nasa batasan ta fashe masa da kuka ba. Babu alamar ya jita, dan luuuu yayi dasu suka faɗa saman gadon. Babu shiri ta kanƙamesa jikinta na ɗaukar rawa jin harshensa akan kunnenta.
“Na shiga uku Yayanmu Please ”.
Ta faɗa cikin muryar kuka tana ƙoƙarin ture fuskarsa dan neman sakata yin fitsari yake.
Al'amarinne yazo mata a bazata, gashi farko, gashi da mutum mai matukar girma da daraja a idonta, gashi ta sha gyara na musamman da ita kanta ko yaya akai mata wani salo sai jininta ya motsa.
“Shiiiiii!!!”
Ya faɗa a cikin kunnen nata yana zagaya yatsansa saman bakinta. Tsit tai shiru tana haɗiyar zuciya. A nutse ya ɗago fuskarsa yana kallon tata cikin ɗan hasken fitilar ɗakin green.
Kasancewar idanunta a lumshe suke batasan kallonta yakeba, murmushi yayi mai sanyi ganin yanda take rawar jiki da ƙanƙame hannayenta a ƙirji. Kwanciyarsa ya gayara da kife fuskarsa akan tata, ya sumbaci haɓarta da matsar da lips dinsa kan nata da yatsansa ke kai har yanzun. A bazata taji saukar tausasan lips ɗin nasa akan natan. Sosai ta zabura da neman jan fuskarta sai dai babu damar hakan, dan ya tsare ko ina da ina babu wata damar kuɓuta yau sai alƙawarin ALLAH ya cika da izinin mai hukunci da rahama akan bayinsa masu haƙuri da juriyar karɓar ƙaddara da hannaye bibbiyu batare da raki ko ƙosawa ba.
Duk da ya haɗa bayanai masu yawa akanta lokacin da yazo babbar gaɓar mallakarta da iyakar jarumtarsa yaje, sai dai samun hanyarsa ɓam ta sakashi jin wani irin zazzafan tausayinta da ƙaunarta mai tarin yawa da tsanani na shigar gaɓɓansa. Ba tare da tuna son binta a matakin tausayawaba ya ji saukar ƙarar kukanta cikin kunnensa, dan a gigice ta ƙwala kiran hajiya iya da Maman Sadiq tana ƙanƙamesa jikinta na wani irin mahaukacin rawa data sakashi ƙanƙameta shima ya manne bakinsa da nata...........
Da ƙyar take fitar da numfashi hawaye masu matuƙar zafi da tausayin kanta na sakko mata. Bata taɓa sanin Yayansu mugu bane sai yau, ita kanta batasan adadin kuka da roƙon datai masaba, zata iya rantsewa har suma tayi na wucin gadi ta farfaɗo amma bai shirya barintaba sai da yakai inda yake buƙatar zuwa. Hannunsa dake damƙe da nata ya ɗan matsa da mirginowa ya rungumeta gaba ɗayanta a cikin jikinsa yana bata wasu irin hort kissis da ita kanta tasan na tsantsar ƙauna ne a gareta.
“Thanks you, thanks you, thanks you” kawai yake jera mata hawayen tausayinta na taruwar masa a idanunsa. Dan duk da kasancewarsa mutum mai tsananin jarumta da kakan daɗe bakaga kuka daga idaniyarsaba yau yaji tausayi mai tsanani akan Zinneerah, saboda abubuwa masu yawan gaske dake zuwa masa arai game da haihuwa da rainon cikin Little da tayi. Sunanta ya ɓaci ta yanda ba lallai kowa ya yarda da ita ɗari bisa ɗariba koda yayi ƙoƙarin fallasama duniya gaskiyarta. Tayi kuka, tayi wahala, tayi ciwo, ta rabu da garinta, ta rabu da mahaifinta, ta rabu da ƴan uwanta, ta rabu da farin cikinta duk a dalilin cikin ɗansa da batasan mafarinsaba. Dolene ya godema ALLAH daya ƙaddara yarinyarnan kasancewa matarsa ba wani daban can ta auraba. Yayi alƙawarin zai jiyar da ita daɗin duniya gwargwadon ƙwazonsa har sai ta san itaɗin ta musamman ce a garesa kuma mutum mai daraja. Dolene ya sanarma duniya wacece ita? Dolene ya wanketa ga mutane koda bazasu yardaba ya tabbatar musu da *_MAKAUNIYAR ƘADDARAR_* data jefa rayuwarta cikin hajijiyar rayuwa badan ta shiryama zuwanta ko karɓartaba itama. “I'm so sorry Neerat”.
Ya sake faɗa a cikin kunnenta hawayenta na sauka har bisa fuskarsa suna gaurayuwa da nasa na tsananin tausayin da yake mata dajin zafin zalunci mafi muni da akaima rayuwarta.
Cikin kuka tace, “Yayanmu ruwa. Ruwa zansha”.
A hankali ya ɗago kansa yana kallon fuskarta data kacame da hawaye, idanun sunyi luhu-luhu yana kallonta. Goshinta ya sumbata a hankali yace, “Ruwa kike so?”.
Kanta ta ɗan juya masa a hankali itama tana matso wasu sabbin hawayen. Hannu yasa ya share mata su. “Tom ya isa haka kinji, banason kukannan zai saki ciwon kai. ALLAH yay miki albarka uhmyim”.
Kanta ta maida gefe tana ƙoƙarin haɗiye kukan amma ta kasa. Raba jikinsa yay da nata da ƙyar ya jawo rigarsa ya saka, sakkowa yay daga gadon ya fita ɗakko mata ruwa dan yau ko shigowa dashi baiyiba ya manta.
A yanda ya barta haka ya sameta. Zama yay ya jingina da gadon sannan ya ɗagota jikinsa, ta saki karamar ƙarar azabar da wajen ke mata. Ruwan ya saka mata a baki yana ambaton, “Sorry sha ruwan muje ki shiga ruwan zafi”.
Sosai tasha ruwan wata sabuwar zufa na keto mata. Ta lafe a jikinsa tana lumshe idanu da sauke numfarfashin wahala. Idan zata iya tunawa bayan rainon cikin little da naƙudarsa data sha kafin ai mata cs bata taɓa jin abu mai azaba makamancin wanda taji yau a hannun Yah Abdul-Mutallab ba. Ta jigatu matuƙa irin jigatuwar da mantata gareta abune mai wahalar gaske. Tana tausayin mace a rayuwarta, da ace mata zasu nutsu su ajiye duk wani shirme da ruɗanin huɗubar sheɗan da tabbas wasu abubuwa ƙalilian dake zama wajib a rayuwarsu kawai sun isa zama sanadin kaisu aljannah. Yanzu da irin wannan daren kawai aka barka ai ba ƙaramin abin tashin hankali bane, balle akwai rainon ciki, uwa uba naƙuda da babu abinda za'a iya misaltata da shi. Ga fitar rai, Raino, hidimar gidan aure da ƙalubalensa.
(Kai jama'a mata masu duniya, mata sarakan duniya, mata na gaisheku, na gaisheku gaisuwa irin ta girma da mutuntawa dan kun cancanci a yaba muku, ku ƙara haƙuri jaruman duniya, ku cigaba da haƙuri taurarin duniya, kuzama masu haƙuri ALLAH zai sakanka muku da aljannarsa😍😘).
Ruwa AK ya shiga da kansa ya haɗa mata a toilet, sannan ya fito da kansa ya taimaka mata ta sauka a gadon hawaye na rige-rigen sauka mata, ganin tafiyar tasu babu sauri yasashi ɗaukarta kawai. Ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka, dan hakan da yay mata ba ƙaramin taimakonta yayi ba.
Koda suka shiga ba kai tsaye ya tsundumata a ruwanba, cikin dabara da lallashi yay mata. Zinneerah nada dauriya sosai, koshi ya shaida hakan dan ta nuna masa jarumta yau duk da taci kuka, amma tun ihun farko datai lokacin isarsa gareta bata ƙara buɗe baki domin yin kwakwazo ba, sai dai hawayene kam da suna ƙarewa yau da sun ƙare gareta. A yanzunma hawayenne kawai sai ƙanƙamesa da tayi amma ko uhum batace ba.
Hakan ya masa daɗi, dan ya tsani kwakwazo a rayuwarsa da hayaniya, yafison komai a silent kuma da nutsuwa, wannan yana ɗaya daga cikin hallayarta data fara jan hankalinsa gareta batare da ita ta sani ba. Kanta dake kwance a ƙirjinsa ya rinƙa shafawa yana hura mata iskar bakinsa cikin kunne. Hakan ya matuƙar shagaltar da ita har ruwan ya ratsata yanda ya kamata ya ƙara mata wani kuma. Sai da ya tabbatar taji daɗin duka jikintama ba wajen kawai ba sannan yace mata tayi wankan.
Duk da tanajin nauyinsa ga zazzaɓi dake neman rufeta haka tabi umarninsa tayi, dan tsaye yay a kanta da alama yana son tabbatar da ingancin abinda zatayin. Yaji daɗin ganin yanda tayi komai dai-dai, sai kawai ya ɗauka mata bathrobe ya saka mata. Zai ƙara ɗaukarta cikin dasashshiyar muryarta tace,
“Zan iya”
Baice komaiba ya matsa ya bata hanya, cikin dauriya ta fice a toilet ɗin, saida ta fita gaba ɗaya ta cije bakinta da jingina jikin bango tana maida numfashi, tayi hutun kusan minti ɗaya sannan ta ƙarasa kaiwa gadon dake a hargitse. A ranta tace, ‘Dole ka hargitse gado dan nima an hargitsani’.
(😂🤣wayaga mai cikuykuya an zinni😆😝).
Ƙarasawa tai ta fara ƙoƙarin ganin ta gyara don buƙatarta kawai takai kwance. A dai-dai nan boss ya fito yana tsane jikinsa. Ƙarasowa yay inda take yana murmushi tausayinta fal ransa. Batare da sanin fitowar tasa ba taji an rungumeta ta baya da amshe bedsheet ɗin hannunta. “Uhm-uhm waya saki wannan aikin?”.
Sosai tsigar jikinta ta tashi saboda yanda yay maganar a cikin kunnenta. Bai damu da amsawarta ba ya ɗauketa ya dire a saman sofa. Shi kuma ya juya gaban gadon ya kimtsa musu shi, gabanta ya dawo ya durƙusa, tai saurin yin ƙasa da kanta saboda matsananciyar kunyarsa dake neman halakata, gashi yanzu babu riga a jikinsa sai towel daya ɗan yafa a wuyansa ƙarami bayan wanda yake ɗaure da shi. Lallausan murmushi ya saki yana lumshe idanu da sake buɗewa akanta lokacin da yake warware towel ɗin data naɗo gashinta dan ya tsane. Towel ɗin ya warware yana ƙara tsane mata gashin da ƙyau gudun kamuwa da mura.
“Duk zafinsa naƙuda tafisa ko?”. Ya faɗa yana zame towel ɗin daga cikin kanta.
Rashin fahimtar tanbayar tata ya sata ɗago kumburarrun idanunta ta kallesa. Ya sakar mata lallausan murmushi da ɗan jinjina kansa. Kanta ta maida ƙasa kawai gabanta na ɗan faɗuwa da tunanin koya san itace ta haifa little ne?.
Hannunsa ya ziro ta ƙugunta, ɗayan ya ɗago haɓarta sosai suna kallon juna. Duk yanda taso janye idanunta da suka shige cikin nasa hakan ya gagara, dan shu'umin kallon da yake mata tamkar yana zuba mata wasu sinadaraine masu matuƙar daraja da tsada, ta ɗan fara mar-mar da idanunta dake cikowa da ƙwalla.
Kansa ya girgiza mata alamar kartayi, kafin ya saki fuskar tata da matsota jikinsa ya rungumeta a haka suna sauke ajiyar zuciya a tare. “Aure jarabawane kuma ibadace, haƙuri a cikinsa nasarace kuma daraja ce. Riƙe mutunci da kame kai martaba ce, mutuntawace ga iyaye da tarbiyyarsu. Dan duk namijin daya sami mace a yanda yay hasashe ba ita kaɗaice ke samun kima a garesaba har iyayenta ma mutunci da kima suke ƙarawa. Kinsha wahalhalun rayuwa amma hakan baisaki yin gaggawa ba wajen ƴanta kanki har sai da ALLAH ya iyakance miki. Daga yau ke sarauniyace a fadar Abdul-Mutallab, ki ɗauka kin mallakesa shi da komansa. Kin bashi ƙyauta mafi daraja guda biyu da bazai manta da itaba. Kin haifamin Abdul-Mutallab, kin daɗamin da tukiycin budurci. ALLAH yayi miki albarka. ya yalwata rayuwarki da tarin farin ciki, ya share hawayenki ya yaye damuwarki, ya ɗaga darajarki ya cigaba da kare mutuncinki fiye da yanda kika kare nawa”.
Sosai tsoro ya kama Zinneerah jin ya ambaci haihuwar little, sai dai daɗaɗan kalamansa da batasan zai iya kwantar da kai wajen furtasu ga mace ba suna ratsata. Ya ɗago fuskarta yana kallonta. Lumshe nata idanun tayi saboda nauyinsa da kwarninsa.
Ɗan murmusawa yay da miƙewa tsaye, ya kamo hannunta suka nufi gaban mirror batare datasan mi zaiyiba. Dan barci takeji sosai tanada tabbacin kuma asuba ta gabato, ga zazzaɓi jikinta zau, tasan kuma yanajin zafin. Baice mata komaiba ya zaunar da ita a kujerar mirror ɗin, kanta a ƙasa harya jona handryer dake ajiye, gashinta ya fara busar mata sannu a hankali, sannan ya tufƙe matashi da ƙyau yanda bazai takura mataba. Rigarsa ya juya ya ɗakko cikin Wadrobe yazo ya fesheta da turare sannan ya saka mata bayan ya zame bathrobe ɗin tanata noƙe-noƙe dan kunya. Rigan ya kai mata har cinya dan haka ta saki ajiyar zuciya. Sake kamata yay ya kai bakin gado ya zaunar, ya buɗe drawer gefen gadon ya ciro magani dan yaji zazzaɓi a jikinta. Bata yay, babu musu tasha saboda bukatarsa da takeyi. Tana sha yana shafa kanta harta shanye ta miƙa masa ruwan.
“Good girl.”
Ya faɗa yana kamata ya kwantar, tare da ja mata bargo ya lulluɓa mata iya rabi sannan ya sumbaci goshinta da cewa “Good night”.
Kanta kawai taɗan jinjina masa tana lumshe idanu. Wahala tasa barcin ɗaukarta cikin ƙanƙanin lokaci, sai saukar numfashinta ya rinƙaji a hankali. Lip ɗinsa ya cije yana firzar da wani irin huci mai ɗaci dan tabbas bazai bar duk mai hannu a al'amarin nanba. Matakin farko zai fara ajiye hujja ga iyayensu a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu, zai kuma saka bincike na kwanaki biyu zuwa uku domin tabbatarwa da kama masu hannu a ciki dumu-dumu.
Duk da shima barcin yakeji bai kwantaba, alwala yayo da saka jallabiya ya fara nafilfili dan asuba ta gabato ma, yasan idan ya kwanta zasu makarane kawai. Zinneerah kam tasha tarin addu'oi harma da iyayenta, yana a wajen har akai sallar asuba dan bai fita massallaci ba yau bayajin ƙarfin jikinsa sam.
Badan yaso ba ya tada ita da ƙyar domin yin salla. Aiko yasha langaɓe dan sai faman lumshe idanu take, sai da ya taimaka mata zuwa toilet ɗinma tayo alwala sannan. Tanako idar da salar yau babu zancen azkar ta ɓingire a wajen. Ɗagata yay cak ya maida a gadon ya kwantar shima yabi sahunta dan kansa ya fara masa ciwo saboda barci. Cikin so da ƙauna ya rungume matarsa cikin jikinsa suka lula duniyar barci.
*_12:5pm_*
Sai ƙarfe sha biyu da mintuna biyar AK ya farka saboda kiran wayarsa da akayi, ƙaramin tsaki yaja dan barcin sam bai ishesaba. Da ƙyar ya lalubo wayar ya buɗe ido yana kallon mai kiran. Ganin Granny ya sashi gyara kwanciya sannan yakai kunne.
“Assalamu alaiki, Granny barka da asuba”.
“Ai dama barka da dare kacemin, kujimin iya shege da ranar ALLAH kake kiramin barka da asuba. Kai ko moddibo kana lafiya yau kuwa kai da inno? An aiko muku da abinci kusan mutum uku suna zuwa amma an ƙwanƙwasa ƙofa ko motsinku babu”.
“Oh God! Granny sai kin mana kwakwazo duniya tasan bamu tashi ba? To barci mukeyi”.
“Eh lallai ai nafaji barci kukeyi ja'iri, sai ka tashi ka buɗe ƙofa ka amsa ka koma ku cigaba da barcin”.
Murmushi ya saki da ajiye wayar yana faɗin, ‘Hajiyar matsala’. Daga haka ya ɗan leƙa fuskar Zinneerah dake barcinta hankali kwance sannan ya zare jikinsa a hankali ya sauka a gadon. Jallabiya ya ɗauka ya ɗaura saman boxer ɗinsa ya fito.
Haneef ya samu zaune a saman motar da yazo, yana ganinsa ya duro ya nufosa ɗauke da basket. “Yayanmu barka da hantsi?”. Ya faɗa cike da girmamawa.
Amsa masa yay da kulawa yana tambayarsa jama'ar gidan.
“Kowa lafiya yake yayanmu”.
“Alhmdllh, yanzu daga nan ina zaka?”.
“Ba ko'ina zan koma gidane”.
“Okay to kabar zuwa gidan, gidan Abba zan aikeka kaje ka ɗakko min Gwaggo Maryama, sai ka biya ta gidan dasu Mammah suka sauka ka ɗakkomin Mahma. Kafin kaje duk zan kirasu”.
Kai Haneef ya jinjina ransa fal wasiwasin lafiya kuwa?. Rashin mai basa amsa ya sashi miƙa masa basket ɗin kawai ya juya domin cika umarninsa..
Shima ciki ya koma kai tsaye sashensa. a dining ɗin falon nasa ya ajiye basket ɗin ya koma ciki. Wayarsa ya ɗauka yay zaman kiran Hajiya iya, sun ɗanyi magana ya maida kiran ga Mahma kuma sannan ya kira Abba na gidan mmn sadiq...............✍
*_Aunty Farah kina can wagaga da baki za'a mallake mana AK😖😖😬😬😒😒😏😏😏😾😾🙄🙄😑._*
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za'a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
*_ALLAH ka gafartama Iyayenmu🙏🏻😭_*
[10/22, 3:27 PM] Queen Meenali👑Mrs Misbah💗: *_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 60*
________________________
*_KAƊAN YA RAGE SU ƘARE_*
*_MATA ƴan ƙwalisa kuna ina za'aci kasuwar sama babu ku?. Mg's skincare ɗin fa na gab da ƙarewar kaya kuna nan sake da baki baku mallaki naku ba_*
_Mg's SKINCARE nagartattun kayan ne dake gyara jiki da fata cikin sauƙi, sunada inganci da rahusa dai-dai da aljihunku._
*Da kin fito a ringa ga tauraruwar taurarin nan mai fatar da babu kamarta tamkar dinare abin haske da walwali.*
*_Sabulunsu kawai kika ɗana sai kinsan kin kai kuɗinki inda babu asara balle dana sani_*
_A yanzu haka muna jerin kayayyaki da suka rage kamar haka_👇🏻
Available
_Akwai: herbal whitening black soap 3k_
Akwai: beauty kit 11k shi set ne yakunshi Abu 6
Soap
Body cream
Face cream
Body nd face scrub
Cleanser
Glow oil
Location
kaduna buh mn tura Kaya ko Ina saidai inmutum ya amshi kayanshi zebada kudin delivery
WhatsApp 08062991549
Call 08064532391
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
*_Karku bari ayi babu ku guys, siyan nagari maida kuɗi gida._*
________________________
*Page 60*
...........Fitowa tai da sanɗa kanta a ƙasa saboda tunani da kunyar su Granny da take zaton har yanzu suna gidan. Yayinda AK dake zaune a falon shi kaɗai yana latsa waya mayataccen ƙamshin haɗin khumrah ɗinta ya samu nasarar kaiwa ga hancinsa. A hankali ya ɗago yana kallon sashen ƙofar bedroom ɗin nasa zuciyarsa na wani motsawa a cikin ƙirji.
A kan laɓɓansa ya ambaci kalmar “Mash ALLAH” yana wani lumshe idanunsa. Ganin tana nufar hanyar fita da sanɗar da takeyi ya ɗan murmusa, sai da ta ɗan gotashi yace, “Nan zaki zo ai”.
Ina ƙasa Zinneerah ta shige dan kunya, har mamakinsa take ganin shi ko'a jikinsa tamkar bai aikata wani aika-aika ba.
“Kona taso?”.
Taji ya sake ambata. Kafinma ya gama rufe baki ta nufosa dan shi ba abin wasanta bane, abinda ya shiga tsakaninsu kuma bai rage masa kimarsa da girmansa a idanuntaba sai ma ƙaruwa da yayi. Ta ɗanji sanyin ganin babu su Granny, dan haka taso kaiwa tsugunne gabansa.
Bai motsa daga kishin giɗar da yay a kujera yana mata kallon ƙasan ido ba, ya kamo hannunta ganin zata tsugunna. A saman cinyarsa yay mata masauki. Hakan ya sata saurin kallonsa. Da wannan damar yay amfani wajen riƙe idanunta cikin nasa. Duk yanda taso ta janye ta gagara. Sai neman kashe mata jiki yake da wani sakaltaccen kalo dake tada mata tsigar jiki. Babu shiri idanunta suka fara tara hawaye.
Karan farko tun shigowarta falon guntun murmushi ya bayyana a fuskarsa, ya lumshe ido ya buɗe a kanta yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa. “Miyasa ke raguwane?.”
Cikin suɓutar baki tace, “Tsoro kallon yake bani”.
Harga ALLAH ta bashi dariya, duk yanda yaso danneta kar yayi kuma hakan bai yuwuba, sai gashi da sakin murmushin da har haƙwaransa na bayyana. Shagala tai da kallonsa dan tabbas murmushi na masa ƙyau musamman wanda ke bayyana haƙwaransa irin wannan. Nisan da tai a nazari yasa harya iso da fuskarsa gab da tata bama ta saniba. Sai jin saukar laɓɓansa kawai tayi akan nata. Duk yanda taso ta nuna zamewa hakan ya gagara. Dan wani irin sallo da tunda uwarta ta haifeta ba'a taɓa mata shiba yake sarrafa lips ɗinta.
Luf tayi tana amsar rikitaccen karatun na babban yaya data fara haddacewa daga safiyar jiya zuwa yau. Sai da ya tabbatar ya ida zubar da ɗan sauran ƙarfin data samu sannan ya barta yana rungumeta a jikinsa gaba ɗayanta. Yanda yaken sauke numfashinsa mai sanyi da nutsuwa a cikin kunnenta yasata sake lafe masa a jiki tana rumtse idanu. A ranata ko rayawa take, ‘Yayanmu zaka kasheni da wannan salon naka da yafi ƙarfin shekaruna’.
Sun kai kusan mintuna uku a haka kafin ya ɗagota yana kallon fuskarta, duk yanda yaso su haɗa ido yanzun kam taƙi yarda. Yatsunsa biyu ya sa ya ɗago haɓarta, bai damu daƙin yarda su haɗa ido da taiba.
Tana bashi dariya da ƙara birgesa da wannan sanyin nata, dan haka yay wani munafukin murmushi da kamata ya miƙar.
Dining suka nufa yana riƙe da hannunta, sai da ya zaunar da ita sannan shima ya zauna. Da kanta ta miƙe ta haɗa masa abincin yanata faman binta da fitinannen kallon nan nasa dake sakata dabircewa komin jarumtar da taso nunawa.
Shiko fahimtar da yay kallon nasa na mata tasiri tunma suna can gidan yake sakashi kasheta da su. Bata zuba nataba, bai kumayi maganaba, sai da ta gama ta koma ta zauna ta ɗan dubesa. Ganin shima dai kallon nata yake ya sata janye nata idanun gefe.
Komai baice mataba ya fara cin abincin, sai da yay nisa da ci sannan yay magana batare daya kalletaba. “Juyo nan”.
Juyowar tai tana fuskantarsa, sai kawai yay mata alamar ta buɗe bakinta. Ganin yanda fuskar tasa take ya sata buɗewar. Daga haka ya cigaba da ciyar da ita yana ci shima har suka cinye. Godiya yayma UBANGIJI yana miƙewa ya barta a wajen. Hakan ya sata miƙewa itama ta tattare kayan a basket ɗin da aka kawo, sam batajin daɗin jikinta, a yanzu haka tafi buƙatar ta samu waje ta kwanta. Sashen ta bari baki ɗaya zuwa nata, tana shiga ta sauke ajiyar zuciya da nufar kitchen.
Tana cikin wanke kwanikan ya shigo kitchen ɗin, waiwayowa tai ta dubesa. Ya canja kayansa zuwa shadda fara tas da tai masa tsananin ƙyau, ga mayataccen ƙamshinsa mai cika hancin mai shaƙa da bashi nutsuwa. Ya ɗan janye idanunsa daga kanta yana kallon agogon hannunsa. “Bara na gaishe da su Mammah kina buƙatar wani abu ne?”.
Duk da tayi mamakin jin zancen Mammah sai batace komaiba taɗan girgiza masa kanta.
Takowa yay gabanta yana ɗago fuskarta suka kalli juna. “Baza'amin addu'a ba?.” ya faɗa a wani irin sanyin murya.
Tana mamakin a yanda ya iya sarrafa yanayinsa a salo daban-daban, kuma duk cikin kame kansa babu wani rawan kai ko gaggawa tattare da shi. Idan badan ita da take ganin true color ɗinsa a tsakanin jiya zuwa yau ba babu wanda za'a faɗama haka yake ya yarda, dan ko'ita idan yay abu ya basar sai take ganin tamkar ba shine ya aikataba. Ya barta da kunya shiko ko'a jikinsa.......
“ALLAH ya tsare ya dawo da kai lafiya Yayanmu”.
Haɓarta ya saki da tura duka hannayensa a aljihunsa yana kallonta, “Har yanzu matsayin Yayan kawai gareni?”. Ya faɗa yana tsatstsare ta da idanunsa masu kaifi a gareta.
Ɗan ɗago idanu tai ta kallesa, ya wani juya mata nasa manyan idanun yana ƙara tsuke fuska.
“Yanzu ni waye a wajenki?”
Ya faɗa cikin muryarnan tasa ta rashin sakewa.
Mamaki tambayar tasa ta bata, da ɗan rawar murya da kunyarsa ta haifar mata tace, “Yayanmu!”.
“Daga nan fa?”.
Duk da ta fahimci abinda yake son jin sai ta noƙe dan itama ɗin dai gwanace a miskilancin.
“Zaki magantune”. Ya faɗa yana sake kallon agogonsa da juyawa zai fita. Jitai duk babu daɗi,
“Kayi haƙuri idan na ɓata maka rai Yayanmu”.
“Ba haka matata ke bani haƙuri ba, dan haka sai ki shirya ta yanda nafi buƙata kafin na dawo”. Ya faɗa yana ficewa batare da ya waiwayota ba.
Kallo ta bisa da shi zuciyarta na maimaito mata karatun hajiya Falmata daki-daki. Ganin tunanin bazai kaita ko inaba ta cigaba da aikinta cikin dauriya dan wani sabon zazzaɓi ke neman saukar mata, ga wajen itakam har yanzu zafi yake mata kaɗan-kaɗan. Duk da yanda take jin nata haka tai juriyar gyara gidan har sashensa, sauƙintama ba wani datti bane. Turaren wuta ta saka har General falo da ƴar barandar waje. Ta bi kuma da fresheners masu daɗi. Sosai nutsuwa ta ƙara saukar mata jin ko'ina ya ɗauka ƙamshi kamar yanda take buƙata. Daga haka ta taƙarƙara ta koma bedroom ta kwanta kozata samu barci ya ɗauketa kafin sallar la'asar.
Tana kwanciya ana fara knocking, dole ta miƙe kamar zatai kuka. Hijjab ta saka sannan ta fito ta buɗe. Ganin su maman halima yasa fara'arta bayyana tana jera musu sannu da zuwa. Suma cike da kulawa suke amsa mata suna shiga da kayayyakin da sukazo dashi. Akwatinanta ne na lefe da tarkacen ƴan kayayyaki. Sai kayan gara da suka bata mamaki.
Naziru daya kawosu ne yace ta buɗe ƙofar kitchen ta baya a saka tacan zaifi sauƙi. Dan yasan hanyar tunda da shi aka kawo furnitures ɗinta. Cike da girmamawa ta karɓa masa. Taje ta buɗe ƙofar shi da maigadi suka dinga jigilar shiga dasu su Sakina na tayasu da wanda zasu iya. Hardasu kayan cin-cin. Jitai ƙwalla ya cika mata ido najin daɗi da tausayin su baba. Iyaye dabanne, duk da sunsan babu abin AK ɗin ya rasa a rayuwarsa sunyi hoɓɓasa ɗin ganin sun cika mata darajarta akan abinda al'ada ta tanadar. Dan dai gara al'adace da ƙyautatawar iyaye ga miji bawai wajib bace kamar yanda samarin yanzu suke kallo, harma suke samun damar yarfa mace in ba'ai mataba saboda son zuciya.
Sai da aka gama shiga da komai sannan ta kawo musu ruwa da lemo sukai zaman gaisawa. Sakina sai kalle-kalle take da jinjina wannan gida a ranta, duk da da ita aka kawo amarya yau dai tafi kallon komai yanda ya kamata dan shiyyasama ta nace sai tazo. Aiko sai gashi ƙiri-ƙiri tana nuna hassadanta a fili dan sai wani yamutse-yamutsen fuska take ita da uwarta dake ji kamar ta fidda Zinneerah ɗin ta kawo sakina ciki.
Ita dai Zinneerah bama bi takansu taiba, dan akwai sauran ƴan ɗan musa da sukazo tare su uku sai maƙwaftansu mmn sadiq ɗin abokan arziƙinta suma su uku, sai ƴaƴan mmn halima da ita, da matar Naziru.
Kasancewar su mmn halima tsaffin mata ya sasu fahimtar yanayin Zinneerah ɗin, sai mamaki ya kama irinsu mmn sakina da matar Naziru da ita kanta mmn Haliman dan sudai sunsan Zinneerah ba wannan ne aurenta na farko ba, tunda gata harda little. To amma yanayin nata yayi kama da na wadda namiji ya fara taɓawa. Sauran kam dai har ransu gani suke Zinneerah ta kawo mutuncinta, musamman ma ƴan dan musa da babu wanda yasan ƙaddarar data afku ga Zinneerah ɗin har yanzu. Duk da kuwa Inna Asabe ta saki maganganu da sukaje danya sai duk suka kallesu matsayin hassada kawai da sharrin baƙin kishinta da bai ɓoyuwa harga ƴaƴa. Sai da suka shiga ko ina suna mai yabawa da jera addu'oin fatan alkairi.
★★★
Koda Mahma ta koma gida bata yarda ta nunama su Mammah komaiba, hasalima dama basusan inda tajeba. Da sukace zasuzo gidan AK ɗin kuma cikin dabara ta hanasu akan su bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai a maida Farah baki ɗaya dan ya kamata takoma ɗakin mijinta tunda ta samu sauƙi.
Da farko Zakiyya ta tubure akan Farah bazata komaba har sai AK ya saki Zinneerah, zuwa lokacin Farahn ta haihu. Kallonta kawai Mahma tai tana gitgiza kai da sake yarda da zancen AK. Kamar zatai magana akan cikin Farah ɗin sai tai musu shiru kawai. Dan ita Farah ɗince da kanta tace zata koma gidanta saboda tunowa da zafafan gargaɗin AK. Ba aunty Zakiyya da Mammah ba hatta Mahma sai da tai mamakin furicin na Farah, amma sai batace komaiba tai murmushi kawai.
Aunty Zakiyya kuwa wani shegen harara ta watsa mata da faɗin “Saiki koma ballagaza kawai mayyar miji”.
Kaucewa dukan nata tayi tana kumbura baki, dan ita dai wlhy shawarar Adilah da sukai waya jiya da daddare zatabi, gara ta koma koma mi za'ayi ayisa acan.
★★★
Hajiya iya kuwa data koma duk da tana fushi da Uncle Ahmad har yanzu taƙi saurarensa dan ta dage sai ya ƙara aure ya ajiye matar a Nigeria koda zata barsa ya koma. Kokuma ya bar iyalansa anan. Wannan shine zaɓin data bashi kawai ta tsuke bakinta.
Zaunar dasu tai shida Baffah da Mommy ta sanar musu komai daya faru. Baffah dai yasha mamaki wannan al'amari, Uncle Ahmad kuwa da dama gaba ɗaya hasashensa da nazarinsa ya tafi kacokan a wajen ne tunda Baffah ya bashi labarin abinda ya faru da tarihin Zinneerah sai baiji komai ba sai takaici da tausayin Zinneerah ɗin.
Cikin zafinsa yace, “Aiko indai ta tabbata sune suka aikata yanda sukai wasa da rayuwar yarinyarnan suma tasu saita shiga garari wlhy, dan bazamu barsuba sai inda ƙarfinmu ya ƙare. Gatan da suka kalleta da tashinsa a farko har suka aikata mata wannan ta'asar zasu tabbatar da tunaninau gurɓatacce ne kuwa”.
Ɗari bisa ɗari duk suka bashi goyon baya. Suna cikin tattauna yanda zasu ɓulloma al'amarin Khalipha ya shigo gidan, shine ya musu ƙarin bayani akan kamo hajiya lanti da sukai a yanzu haka kuma tana hannun hukuma, Alhmdllh kuma ta bada haɗin kai akan cewar zata sadasu da hajiyar data kaima su Zinneerah dan itama saboda ita taje katsina. Amma sai ta tarar tana saudia dan can ta koma da zama. dama can sana'arta kai yara saudia aikatau, duniyace tai mata gwatson ƙyanwa tunda aka cimimiyota ta dawo kuɗin komawa ya gagareta. To yanzu dai Alhmdllh akwai bikin yaronta da akai a wannan satin rana ɗayama da nasu Zinneerah, itama jira take a gama bikin dama ta sameta dan tazo Nigeria.
Sunji daɗin jin hakan, a take suka yanke zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama a damƙota kawai kafin ta sake tafiya, suma kuma su Mammah karsu bar ƙasar.
A wannan tattaunawar AK da yazo gidan gaishesu ya samesu. Zama yay suka ɗan ƙara tattauna zancen sannan ya shiga ya gaida matan gidan. Daga haka ya ɗauka little daya maƙale masa suka wuce gida dan sai da ya fara zuwa ya gaishe dasu Mammah. Acan ɗinma bai nuna musu komaiba, dan koda Farah tace zata koma gida gobe a taƙaice yace mata, “Ƙofa abuɗe take” daga haka yaja bakinsa ya tsuke. Bai kuma bi takantaba harya baro gidan. Aunty Zakiyya kam bata tanka masaba shima bai tanka mataba dan idan taurin kai ne gidan ta taras.
______________________
*_DANYA_*
Ƴan biki sun dawo gida lafiya, yayinda kowa ya fara ƙoƙarin fesar da maganar daya gumtso akan auren na Zinneerah da daular duniyar da ALLAH ya kaita ciki. Ga miji ɗan gaske acewarsu (🤣ba bily ba😂). Wasuma da biyu suke ƙara kambama zancen dan baƙanta ran Inna data haukace musu da bala'in su fice mata a gida.
Ko'a jikinsu, dan da suka fitanma gaba suka ƙara wajen isar da labarai kala-kala harda waɗanda ba'ayiba ma. Gasu Yaya Gajeje kuwa ga labarin a ransu ga tsoron tunkarar Inna da batun abinda suke hasashe tattare da Tinene, dan tunda suka shigo gidan ɗaki ta shige ta ƙudundune a zani tana rawar sanyi.
Da ƙyar Yaya Gajeje taja ƙafafunta ta nufi gidan saboda yara data bari, gashi yamma nayi tunda tana ƙauyen gaba dasune duk da babu nisa.
Duk da takaici da zafin da inna keji a ranta da labarin ɗaukakar da Zinneerah ta samu hakan bai hanata zaman jin labari a bakinsu Atine dakeyi suna gatsine-gatsine ba kishi fal ransu. Abinda kuma sukazo dashi sai faman ci suke har Inna ɗin dan tace raba mugu da makami ibada ne.. (😂🤣gaskiya kam aunty Asabe)
Shi Baba ma da amaryarsa dake jiyosu daga ƙofar ɗaki dariya suka basu, musamman Inna da baba yasan shegen kwaɗayinta bazai barta ta kasa cin abinda akazo da shi dinba koda kuwa tanaci tana kuka ne.
Washe gari da safe jikin Tinene ya ƙara tsananta, tun dare taketa kwara amai har safiya ta tashi a galabaice. Baba ya ce ta shirya suje asibi maybe dai typhoid ne ke damunta, dan itace kesa zazzaɓi mai zafi haka da naci. Amaryar baba ba sanin ciki tai ba sosai, Inna kuma idanunta ya rufe da damuwar ɗaukakar Zinneerah sam taƙi fahimtar halin da Tinene ke ciki. Su kuma su Karima tsoron faɗar abinda ransu ke raya musu inna ta hau tsinarsu sukeyi.
Ana haka sai ga Gwaggo Laritu tazo domin ai zaman raba alkairin da AK ya basu, bata jima da zama ba Yaya Gajeje ta iso itama. Cikinsu babu wanda yay magana akan shirin kai Tinene asibiti da baba ke shirin yi. Sai da Gwaggo Laritu tai wani tunani sannan tai magana.
“Niko Yaya nakega kai Tinene asibiti bazai jawo komai a garin nanba sai kace nace. Musamman ma daya kasance asibitin garin nan zakuje”.
Da mamaki baba yace, “Kace nace kuma Laritu, akan ciwon?”.
“Tabbas kuwa Yaya, dan banga amfanin aita ɓoye-ɓoye ba akan abinda kowa yasan dama wajib ne. Dan shi dai sharri ɗan aike ne dama shiyyasa ake nusar damu illarsa ga aikama kowa. Asabe tama Zinneerah fata kuma ALLAH ya karɓa mata, sai dai kuma ga sakamakon nan ya dawo ga Tinene. Dan babu wani taifot dake damunta ciki ne jikin wannan yarinyar wlhy”.
Ba baba da amaryarsaba hatta da Inna dake jiran Gwaggo Laritu takai ƙarshe ta sauke mata kwandunan bala'in da take Tattarowa a take ta saki robar ruwan wankan ƴar Karima data ɗauka zata sako ruwan zafi, ALLAH yasotama bata kai ga zubawarba.
Wani irin shuuu taji abu ya gitta mata cikin idanu da ƙwaƙwalwa saboda tsabar razani. Cikin rawar baki tace, “Munahika annamimiya, Laritu kirasa wanda zakima wannan sherin sai ɗiyar zumunki. To wlhy sai dai kiga ciki a jikin jikokinki, ALLAH ya isa kuma sherin da kikaima yarinyata”.
Murmushi kawai Gwaggo Laritu tayi. amma uffan bata sake cewa ba. sai Yaya Gajeje ce tace, “Inna ya kamata ki fahimci zancen Gwaggo, ku kuma nutsu wajen karantar Tinene wlhy cikine da yarinyar nan da gaske”.
Baki sake tabi Gajeje da kallo, sai jitai Atine tace, “Wlhy Inna da gaske ne, ki kalla Tinene da ƙyau zaki tabbatar”.
Tsitt gidan yayi saboda kakarin aman Tinene, Inna ta fashe da kuka jikinta na wani irin rawa lokacin da idonta ya sauka akan Tinene da har ciki ya fara tasawa sama kaɗan, da alama ma ya wuce watannin da suke hasashensa. Baba kansa baya yay sai da amaryarsa ta riƙosa jikinta na rawa itama dan batason damuwa sam, musamman ma yanzu data samu cikin nan. Kafin wani ya samu damar sake cewa uffan sukaji ana rangaɗa sallama daga waje. Da ƙyar baba ya iya amsawa da nufar hanyar ƙofar gidan domin duba wanene. Da Laminu ƙanin Babawo yaci karo, Laminu ya gaishesa da girmamawa yana miƙa masa takardar hannunsa da nuna masa kayan daya sauke a mashin ƙasa. “Baba Sule gashi inji Yayana Babawo, yace a bama Karima tare da waɗan nan kayan. Yace a sanar mata ta tuna yau saura sati biyu wa'adin da kotu ta bata na kai kuɗin sarƙar hajiyar data satamawa ya cika”.
Cikin rashin fahimta baba yace, “Laminu ban fahimcekaba nikam sam, amma kaga shigo daga ciki kai bayani agaban Karimar”.
Babu musu kuwa yabi baba ciki, bayanin daya zayyana masa shiya sake maimaitawa Karima.
Gani kawai sukai ta saki ƴar sai da Atine tai azamar tarota tana ambaton, “Na shiga uku Karima baki da hankaline?”.
Ina Karima ba saurarenta takeba, dan atakema gani sukai ta yanke jiki ta faɗi, Inna ma da tun fara bayanin garin ke juya mata da wata irin hajijiya sai tabi bayan Karima ta zube ƙasa.
Ƙarar da Atine da Sa'a suka ƙwalla na firgici ya saka amaryar baba dafe bango saboda wani irin murɗawa da mararta tayi alamar tahowar naƙuda.........
____________________
*_KANO_*
Bayan wucewar su mmn Halima
salla kawai Zinneerah ta samu tayi ta la'asar. Duk yanda taso daurewa da zazzaɓin daya rufeta kasawa tai, dole ta rrrafa saman gado ta kwanta dajan bargo ta lulluɓe tana rawar ɗari.
Cikin barcin daya ɗan fara figarta little ya faɗo mata a jiki yana faɗin, “Aunty!” cike da farin cikin ganinta. Buɗe idanu tayi da ƙyar tana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar yaron mai tsananin kama da mahaifinsa. Ta ɗan lumshe ta buɗe da ciro hannunta a bargon da ƙyar ta shafa kansa.
“Kaga ka tadani daga ɗan barcin dana fara sweetheart, waye ya kawoka?”.
“Abbana”.
Ya bata amsa kansa tsaye yana ƙara daka tsalle akanta.
“Wai ALLAH little karka ƙarasani dan ALLAH, ka tausaya mani”. Ta faɗa tana yunƙurin miƙewa zaune. Idontane suka sauka akan AK dake bakin ƙifa tsaye kawai yana binsu da kallo tamkar ya samu television.
“Barka da dawowa” tai maganar da maida idonta ƙasa. Batare daya amsaba ya tako ciki sosai, a kusa da ita ya zauna da kamo little dake ɗane mata wuya...........✍
*_Na gode da addu'oinku, na samu sauki Alhmdllh. Asha hutun weekend lafiya😘😍😍_*

*_TYPING📲_*
*_LIttafin nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH karki karanta sai kin biya. Idan kuma kin saya, muna haɗaki da ALLAH karki fitar mana. Dan ALLAH ku zama masu riƙon amana da adalci a garemu🙏🏻😢_*
*Page 61*

0 comments:
Post a Comment