๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina rokon allah ya bani daman rubuta dede, ya hani hannuwa nah d rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page....1
Hayaniyace take tashi tako ta'ina, mutane na kaiwa da komowa kowa Yana harkan gaban sa, ga ababen hawa wasu na natafiya wasu Na dawowa, seda na duba sose se naga Ashe kasuwa ce.......
๐ Can Na hango wata dattijuwa duke agaban wani matashin saurayi, hannunta rike da wata Riga da alamade ciniki suke yi fadi take, "haba dan nan ina lefima ka siyar min a naira hamsin, nima de karambani zanyi Na siya ahaka, don wlh ladidi naira talatin ta bani, gashi nazo kasuwan naga kome ya kara kudi, matashin yaron nan yace "haba goggo kudin rigan nan yafi haka gaskiya ,tace "toh bazaka siyar min ahaka bake nan? dan nan yace "goggo nima Kayan banawa bane Inde nasiyar ahaka me gidana Zemin fada, Inde zaki siya d'ari da hamsin ba toh gaskia bazan siyar haka ba, dattijuwan nan ta'ijiye rigan hannunta, tana mitan bazata siya ba, a kud'in nan ba, dubanta takai gefan hannunta Na dama, wata matashiyar yarin ya ce tsaye da'alama duk surutun dattijuwan nan d me Kaya tana saurara, rai bace tace "shige muje banga amfanin zuwa dake bama, kin barni inata surutu ni d'aya, kila da kinsa baki ma da yabari, su yaran nan na zamani Inde yaran mata suka gani sumfi barin Kaya a banza, ammah ke kin tsaya abaya na, kaman kurma,gaskiya kede halinki ba kyau,wannan matashiya dake biye da dattijuwan nan Bata ce da ita kome ba, sede Binta take tana tafiya cikin natsuwa, da'alama de Bata cikin Mata masu tafiya cikin sauri ,dattijuwan nan ta juyo ta kalleta tace "kinga wancan satin da mukazo da 'yar uwark,i kome arha muka samu, Inba cin Bata da lafiya, wlh ban zuwa dake ,dukar da kanta 'kasa tayi, tana mai cewa "ALLAH ya baku hakuri baba" wan nan dattijuwa da aka Kira baba, tace "aikin kenan kina kasa dakai kaman kinga surukanki, ni shige gaba mutafi, shigewa gaban baba tayi suka cigaba d tafiya ....
"Uncle "uncle wani yaro me kimanin shekara 13 ne yajuyo da sauri, Yana cewa "lafiya kuwa yusura? wan nan yarinya me suna yusura "tace uncle kazo ayyah nakiranka, yace "toh jeki bari na'amshi littafina wajen usman ina zuwa, yarinyan nan ta tafi d gudu tanace wa "toh$ ta'isa wani matsakaicin gida, wan da shide ba nama su Shiba, kuma baza muce musu basu da Shiba, da sallama tashiga gidan tana cewa, "ayyah" ayyah wata mace fara me jiki wan da a shekaru bazata wuce 40, ba tafito tana cewa "kai yusura meyasa baki Abu a natsuwa ne? yusura na sauke nunfashi saboda gudun da tayi tace "ayyah sauri nake kar abinci nah ya huce, ayyah tace "to" aeh gayinan sekici, ina uncle din? kafin yusura ta Bata amsa uncle ya shigo, da sallama Yana cewa "mahmah gani, natsaya amsan littafi nane, tace toh" na d'auka kamance, yau akwai makaranta ne? yace "a'a" mahmah tace "ga abincinka Can a kwanonka kayi sauri Kaci, ga ruwa nan nasan yayi d'umi ka watsa ka tafi, yace "toh mahmah, ya d'auko abincin nashi ya wanke hannunshi, da butan kofar dakin mahmah, ya bude kwanon yayi Bismillah Yana me kai loman danbun shinkafa cikin kwanciyan hankali ......
"Gafaranku de masu gida" cewar baba dake tafe da Kaya aduka, hannayenta kafin mahmah ta amsa sallaman, matashiyar yarin Yannan ya ratsa kunnuwan mahmah dake duke gaban murhu, tana fifita ruwan wankan uncle, amsa sallaman tayi tana me mikewa daga gaban murhun, tare da fad'in "yaya har kun dawo? "aeh asiya sannu da gida, mahmah da ta d'ibo ruwa a kofi, tana mi kama baba, tare da fad'in "yauwa yaya aeh kunsha Rana, tace ke de Bari asiya aeh ba'a magana, ya me jiki kuma? mahmah dake zaune kusa da baba tayi murmushi, "tace yaya lafiyan munubiya kalau fa, bawani ciwo da take yi son zuwa kasuwan ne batayi, ๐คbaba tayi tana cewa "hakane ma, toh ta kyauta, uncle dake 'ko'karin shan ruwa da alama ya, gama cin abincinsa ne yayi dariya Yana cewa(...baba sannou moun bรฉ lawoul..) baba sannu da hanya, tace yauwa jabir, kallonta yayi Yana cewa "addah munu nad'au kin dad'e, a makaranta, wannan matashiyar da akakira munu cikin magana a hankali kaman yaddah naga hakan dabi'arta ne "tace (mi dofti baba loumo woun) naraka baba kasuwa ne, yace toh addah, ki jirani nafitoh mu tafi tare, Yana d'aukan bokatin da ya juye ruwansa yana tafiya bandaki.....
Munu batace kome ba, se sannu da gida da tayi ma mahmah, "yauwa sannu, je ga abincin ku can ki d'auka, tace "toh tana mi'kewa, ita ma baba dake zaune tana jinsu ta raka munu da harara, tana "cewa asiya wannan 'ya taki sekin tashi tsaye akanta............
Please COMMENT'S and SHARE in other group's
๐๐ป๐๐ป boddo ๐๐ป๐๐ป ce ๐ง๐ง๐ง
๐ RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kir'kirarrene labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa,ina rokon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwa nah d rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page.....2
Mahmah dake 'ko'karin tashi don kawo ma baba abinci ''tace yaya wani abun( boddo baffah...).. kyakkyawan baffah tayi,? baba ta'amsa abincin tana 'ko'karin kaiwa baki ''tace ke asiya ban san kalanki bama ke duk abun da wan nan yarinya take yi baki kulane yarinya babu wani kazar kazar kome tana yi kaman ana mata dole ๐ค ke baki lura da 'yar uwar haihuwan ta bane ,mahmah da tayi shiru tana sauraran baban tace toh yaya insha allah za'anemo tace nide nafad'a Miki ah toh in ba nid'in bama babu me fad'a Miki haka yarinya zata taso babu kuzari mahmah tayi murmushi tana mi'kewa don ganin lokacin la'asar ya gabato......
Isan ta d'akin kenan sllm d'auke abakinta jin ba'a amsa bane yasata d'ago kanta tana me kallon kan katifan dake malale a 'kasan d'akin idonta ya fad'a kan wata matashiyar yarinyar dake kan katifan tana latsan wayan dake hannunta,girgiza kanta tayi tana me ajiye kwanon a tsakar d'akin, tace munubiya...wace aka Kira da munibiya Na kallah, bansan sanda nace Masha ALLAH ba kyakkyawan matashi yar budurwa wan da a shekaru bazata haura 16 ba kana kallonta kaga bafulatanan asali, d'ago idonta farare tayi tass ta sauke akan wan nan budurwa da naji ankira da munu tayi mata kallon sakanni tamaida du banta akan wayanta ''tace lafiya munu ''tace yau bazaki makaranta bane tace kaina na ciwo in kinje ki sanar wa ya ''sayyadinmu munu ta girgiza kanta tana kwance ni'kaf din dake d'aure a fuskanta munubiya dake hararanta ta 'kasan ido tace ''ustaziya'' toh bazanje ba ta ciga ba d latsa wayanta ko a jikinta, munu dabata san abunda muna take yi ba tace ga abinci nan mahmah tagama tace ci ni se anjima juyowa tayi don kallon muna wow Masha ALLAH nace allah ya halicci mace anan ๐dole ta sa niqaf kar ta hada goslow a hanya๐คญ kyakkyawa ce wan da Na hango shigen kama tsakaninta da Wanda naji an Kira da muna, sede munu ta fita haske don'ita farace Tass ''ita kuma muna choculate ce ita ba fara ba bakuma za musata a jerin ba'ka'ke ba ''takalleta cikin kulawa da alama hankalinta ya fara tashi cikin mareraice murya tace...(bandou maiy nah dardam...?) jikin ne 'yar uwata? ''tace (oho) aeh cikin nuna kula muna ''tace (allah hoynou) ALLah ya'kara lafiya, ameyn ''tace tana me bin muna da kallo waddah ke 'ko'karin, shirin makaranta......
mahmah nafitoh cewan jabir Daya fitoh cikin shirin shi n'a islamiyyah dogon jallabiya choculate color da farar hula akan sa hannunsa ri'ke da jakansa me dauke d littafansa, mahmah dake saka ma yusura Safa a 'kafanta ''tace toh jabir, ga yusura ma ta gama Nata shirin dubo ''hammanku ko ya shirya yace toh mahmah ya tafi d'akin da ke cikin zauren gidan ya tsaya bakin 'kofar d'akin Yana sallama jin amsawa da me dakin yayi ne yasa shi isar da sa'kon mahmah Yace nashirya kufitoh dawowa jabir yayi Yana me fad'ama mahmah sa'kon hammah ''tace toh je ka Kira (addirabe ma) ..yayunka ku tafi da toh ya 'amsa yanufi d'akin su munu, munu dakรฉ d'aukan littafin ''min hajjil Muslim'' tana sakawa a jakan ta ''tace mun tafi muna Bata amsata ba ta d'auka bacci ne ya d'auketa se ta fita tana fatan samun sau'ki ga 'yar uwantata wacce Bata da kamar ta had'uwa sukayi d jabir a hanya 'yace addah munu ina addah muna ''tace Bata da lafiya ๐ณido yayi Yana me cewa......
Please COMMENT'S and SHARE in other group's
๐๐BODDO ๐๐CE ๐ง๐ง๐ง
๐ RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwa nah d rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page......3
Addah munu jikin nata d sauki ko? kallon shi tayi na d'an sakanni ''tace karka damu ta samu bacci, sauke numfashi yayi yace ALLAH yabata lafiya , ameyn muje ko, da toh ya'amsa suka cigaba da tafiya mahmah dake jiran iso wan su ce ta ke tambayan ina muna ? tana bacci.cewar munu dake daura gilas d'in ido akan ni'kap d'inta, bacci ? Mahmah tayi tambayan fuskanta na nuna alaman mamaki, aeh mahmah, makarantar fa? Mahmah bata da lafiya ne cewar jabir, kafin mahmah tayi magana baba dake idar da sllanta kenan tana tana lazimi ''tace koda naji dama nasan wan nan 'ya ba lafiya ba tunda fa nadawo banganta ba asiya mahmah da ta kaici ya 'isheta ''tace yaya lafiyan muna 'kalau fa niyyar zuwa ne bata dashi, ri'ke baki๐ค baba tayi ''tace asiya yanzu lafiyar usaina 'kalau ta'ki zuwa min barka d dawowa ni Bana son haka asiya yanzu ma in yarinyan nan lafiyan ta 'kalau tace bazatajeba aeh yakamata abarta suke nan yara kullum ahanya ba hutu, mahmah bata ce kome ba se kallon hammah Ali da iso wan sa kenan don yayita jira bega fitoh wansu ba yashigo ya ga me ya tsayar da su se yaga Ashe baban tasu ne tafara mitan ta da ta Saba in da sabo duk wan nan abun sunsa ba dashi ita de baba Bata son ganin abun da ze ta'ba mata muna ko kadan don 'yar gaban goshinta ne, se kun dawo karku manta da addu'ah ALLAH ya Bada ilimi me albarka wan nan shine addu'an mahmah aduk Sanda zasu tafi neman ilimi kuma ba'karamin tasiri addu'an yake a garesu ba da ameyn duk suka amsa suna kama hanya mahmah da duk Bata ji dadi ba ta shige d'aki tana addu'an shiriya ga duka 'ya'yan Nata baba dake tsaye ''tace min jimin mata da neman ba'asi buri in idar da lazimi mah naje kemis d'in d'an asabe na amso mata panadol......
Fitan su a gida da addu'ah abakin dukansu kaman yaddah mahmah ta umurce su kaman tana wajen ๐ฅฐhakan yasa ni ce wa Masha ALLAH ๐ฅฐcikin natsuwa ta ''yan islamiyyah tafiyan minti 15 ya'iso dasu wani kofar makaranta waddah naga anyi rubutu da kalman larabci ''nurul ala nurul'' tura kofar sukayi suka shiga Masha ALLAH makaranta ce babbah me shashi uku ne acikin katafaren filin makarantar akwai b'arayin ''raudha'' akwai ''iftida'iyyah'' akwai ''sanawiyyah'' Masha ALLAH babu wani b'ata lokaci yusura da jabir ke ri'ke da hannuwanta, tabi b'arayin nasu sashin raudha take Daru abdallah, inda jabir ma ya tafi nasu b'arayin shikuma barayin iftida'iyyah yabi inda yake, Daru d'alhat munu dake biye da hamman nasu ne suka shiga bangaren sanawiyyah inda ya Shiga Daru Oumar ita kuma dashiga Daru abubakar, sllm tayi tana me mi 'kama mutanen da basu fi biyar ba hannu don musabaha duk suka amsa cikin nuna kula ta 'katshen da ta bama hannune ta Na murmushi ''tace yau de Na rigaki zuwa zama tayi kusa da ita tana cewa mun shiga kasuwa ne ๐คmamaki Na bayyana asaman fuskanta ''tace kasuwa ? Cire idonta tayi akanta ''tace Na raka baba ne dariya tayi ''tace baban mu Na gargajiya Bata ce mata kome ba se littafin da tafitoh da shi ta mi'ka mata shukran tace mata magana Wanda aka ba littafin nan take shirin yi munu tace rabi'at muyi musaffah toh ''tace tami'ke gaban ajin ta nufa, da kallo munu ta bita rabi'at ba 'kawa bace kawai a wajen ta 'kalman 'kawa yayi kadan da matsayinta 'yar uwa ce don daga mahmah se rabi'at cikin Wanda ze 'iya cewa wacece ''munu'', dede wajen da aka jera littatafai taje Masha ALLAH wurin ya tsaru littafai ne kala kala manya da alama ajin Yana cikin manyan a jujuwa dake cikin makarantar al'qur'an ta d'au ko cikin natsuwa da girmama qur'anin da ta d'au ko iso wanta wajen Zaman nasune ya katse munu a tunanin da ta tafi Bismillah tace da munu tana mi'kamata Al qur'an din dake hannunta amsa tayi tana maida duk wani hankali da natsuwanta akai......
Sallm tayi Bata jira amsawan na ciki ba ta fad'a d'akin tana ''cewa wan nan shegen sauro de be kyau ta min.. Bata 'karika maganan da take niyyah fad'i ba ta hango muna da ke kwance kamar me bacci ''tace ALLAH sarkiiii ''tafa d'a tana me jan kalman 'karke muna da ke kwance kamar me bacci ta 'kara lafewa akan katifar tasu baba ta 'karaso tana ta'ba wuyan Nata ''tace ayyee daga ni zazza'bin yafara sauka sannu 'yar gidan baba, bud'e ido tayi tana me yatsina fuska tana mar mar da ido ๐ฅน baba ta rud'e se sannu take mata muna na d'aga kai ''tace tashi kisha magani kinji, imhim'' tace tana tashi da gyar baba 'kara rud'ewa tayi tana Anya baza' a tafi asibiti ba kuwa ๐คmahmah dake jiyosu ta ta'be baki tana fatan shiriya ga yarin yar tata......
Please COMMENT'S and SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'DDO๐๐CE ๐ง๐ง๐ง
๐RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kit'kirarrenen labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa,ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwa nah d rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page......4
''karatu suke cikin bama ko wanne harafi ha'kkinsa ahankali suke don kar su shiga ha'kkin ma'koftan Zaman su a'ajin ahankali d'aliban suke shigowa suna musabaha da juna ๐Sun burge ni sose, sllmn mlm isma'il ne ya ratsa ajin dede in da rabi'at ''take kai 'kar ken ayan shafi na biyu na cikin suratul ''ankabut'' rufe al'qur'an d'in sukayi suna masu maida hankali ga mlmin nasu, bayani yafara musu gabaki d'aya hankalin su suka maida ga mlmin don son fahimtar sa da kyau ''toh a watan sha'aban za'ayi amsan da mlm isma'il ya ba ma wani d'alibi da yayi tambayan da su basusan yaushe aka yita ba, yacigaba da cewa yakamata ku maida hankalinku sose akan abunda ke gaba toku ku ababen alfaharine agare mu, imam yace Mazan ku zasu d'inka jallabiyyah farare da hirami ba'ka'ke da hula shima fari ake bu'katan ko wannen ku ya mallaka, matan kuma Yana me juyowa 'barayin matan ''yacigaba da cewa hijjab fari Safan hannu fari ni'kap ba'ki safan 'kafama ba'ki , kowa yau yakoma gida ya sanar don walimar taku saura sati uku kenan a lissafi muna bu'katan ko wannen ku ya mallaki abunda akace mashi, da toh suka amsa mashi ''yace Masha ALLAH, muhammd bello, Wanda aka Kira da wan nan sunan ''yace na'am mu'allim ''yace zaku tafi bangaren raudha a tabbatar ko wani, dar an shiga don basu karatu ''yace insha ALLAH ya mu'allim, juyawa yayi Yana me fita ajin don meeting d'in gaggawa ne dashi da wasu tsirarun wasu daga mlman makarantar, ''tashi muhammd yayi Yana me karanta kaffaratul majalis ya juya ''yace yakamata mu'isa da wuri don lokacin yafara ja mi'kewa sukayi Dukan su mazanne suka fara fita da kaman minti 5 matan su ka bisu bangaran raudha suka nufa ko wanne ya Shiga ajin da ya kamata suka fara Bada darasi cikin 'kwarewa Wanda aka horar dasu aciki .......
Futoh wa d'akin su munu baba tayi tana cewa asiya zo kiga jikin yarinyar nan, ina ga se munje asibiti mahmah bata 'kiba ta tashi tabi bayan baba don rudewar da taga baban tayi yafara samata fargaba d'akin suka shiga muna na zaune gefen katifan mahmah ta kalleta fuska a d'aure ''tace kunci abincin murya na rawa muna ''tace a'a bud'e kwanon tayi taga abincin na yaddah ta zuba kenan munu ma Bata ciba cikin rai tace, dama nasan za'ayi haka yaddah yaga lokaci ya ja bazata tsaya ci ba, d'ago kai tayi ''tace d'auka kici jiki na rawa muna ta jawo kwanon abinci tayi Bismillah ta fara ci wan nan ita ce mahmah bata d'aukan sakarci da shashanci shiyasa yaranta suke shakkanta don Bata yarda araina naga baba Na gaba kuma baze taka 'karami ba shiyasa yaran ta suke da girmama junansu, fita tayi a d'akin, baba ta bita da kallo tana maganan zuci ๐คoh asiya de bazata canza ba, du banta ta maida kan muna ''tace sannu 'yar baba ci ko yaya ne ki sha magani ciwo ba dadi tana magana fuskanta na bayyana halin Al hini da zuciyarta yake ciki......
Karatun muryoyi da yawa ne yake tashi cikin ajin d munu take karantarwa yarane suke karatu cikin had'a baki ๐muna dake tsaye agaban ajin tana kallon su sukuma suna biya mata cikin nuna zumud'in don kowa so yake yaga yafi d'an uwansa iya wa, le'kowan da suraiyyah Adam tayine tana ''cewa ''munaya'' yasata d'aga kai ta kalleta, nuna mata agogon dake d'aure a hannunta tayi, d'aga mata kai kawai tayi ta juya d kallonta ga yaran ''tace, kowa ya fitoh da littafinsa da pencil d'insa ku rubuta huruful hijja'iyyah banda surutu amsawa sukayi da toh d'aukan jakarta tayi tana cemusu ilal liqa suka hada baki suna cewa bi amanillah jinjina musu kai tayi tana jin dadi sose a ranta ,suraiyyah dake tsaye ne tace lokacin tashin ma yakusa muyi sauri kafin abubakar ya buga 'kararrawa kin san mlm Yahya Inde aka buga baze amsa takardan nan ba, ba tace da'ita kome ba har suka isa bangaren iftida'iyya daru zubair suka shiga da sllm abakunan su amsawa mlmin dake zaune akan kujera yayi gaishesa sukayi cikin ladabi. amsawa yayi cikin nuna kulah gare su ciro takardan da tayi rubutoh don nemawa muna alfarma tayi, mi'ka masa tayi ya amsa, bud'ewa yayi yafara bin rubutun da kallo, d'agowa yayi Yana cewa ALLAH yabata lafiya da ameyn suka amsa suna me fita a ajin, tsayawa sukayi don jiran rabi'at dake ajin da aka Bata jin 'kararrawa yayi 'kara yasa suraiyyah cewa, ALLAH ya temake mu da yau muna se ta had'iye mu d'anye, murmushi kawai munu tayi ๐คda alama murmushi d'abi artace ๐suna tsaye rabi'at ta iso bayan ta yusura ce da 'kanninta biyu siyama da sadiq , jabir ne ya'karaso wajen Yana cewa na'iso, hararansa rabi'at tayi tana cewa aeh mun ganka, dariya yayi yana cewa addah Rabi problem, juyowa tayi afusace da niyyar kai mai bugu, matsawa yayi da sauri Yana mata๐คช'kwafa tayi tana cewa da katsaya, suraiyyah ne tace aeh jabir shine maganinki muda Kika shanya bamuyi 'korafi ba se ke da zuwan ki kenan Zaki matsa mishi, dariya jabir yayi Yana cewa shiyasa nake yinki addah suraiyyah ๐ฅฐ.....
Aslm alkm sllmn ladidi ne da taga ji da jiran sakon ta tabiyo sahu amsa sllmnta mahmah tayi tana mata maraba, yauwa (dada fad'i am ) maman fad'i ''sunan da ake Kiran mahmah dashi kenan a anguwan su inkiya ake mata da sunan yarinyar ta ta farko'' zama tayi tana cewa ina yaran ko basu dawoba mahmah dake mi'kamata ruwa a cup tace aeh kin san nasu ba 'atashinsu da wuti, tace baya fiba aeh nace ma baabansu Na gaji da makarantar cikin anguwa kullum yara Na gida mahmah tace kuma karatu de anayi yaran ne suke sa wasa saboda suna ganin suna kusa da gida, ladidi tace toh kinga in sunyi nisa aeh zasu Natsu acan mahmah ''tace toh ALLAH ya temaka, ameyn ladidi ''tace tana duba gidan d kyau, dada fad'i har yanzu yayar taki Bata dawo bane mahmah ''tace ta dawo tana daki, daga murya ladidi tayi ''tace ( oun loreke baba bikkoy) kin dawo baban yara, baba sakรฉ zaune Zaman jinyar da babu ciwo ta ja tsaki tace fitinanniya๐คฃmi'kewa tayi tana cewa ( jaumirawo yardi ) ubangiji ya yarda fitoh wa tayi murmushin ya'ke dauke a fuskan ta tana mata maraba, amsawa tayi tana mata sannu d gajiyan hanya amsawa tayi tana zama kusa da mahmah ๐คtace ke ladidi kin san Riga ba haka kud'in shi yake ba Kika barni naje ina rage murya yaro na wula'kantani, ladidi ''tace wlh ban san yaushe suka'kara ma Kayan kud'i ba waccen satin da mukaje d suwaiban lurwanu a haka muka siya don ma bakud'i a hannu nah ne ban siya ba sannu baba bikkoy kunsha wahala, baba ''tace aeh ga kud'inki in kinje kya siyo a hakan, ladidi amsan kud'in tayi tana masu se anjima mahmah ce kawai ta amsa baba ko da ta rakata da harara tace ji wai a haka suka siya a'a kyauta suka baku tunda tsoron ku suke mitsww๐คฃ๐คฃ๐คฃ๐คฃladรฎdi de ta ta'bo baba se de muce baba ALLAH ya huci zuciyan kรฎ.....
Please COMMENT'S and SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'DDO๐๐CE๐ง๐ง๐ง
๐ RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwana da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page.....5
Murmushi mahmah tayi tana cewa yaya 'kila de ba Wanda ta kwatanta maki Kika gani ba, baba da take ta mitar ta a zuci ta kalli mahmah ''tace ๐คasiya wai ke me 'kawa ko, mahmah tace a'a yaya bahaka bane ALLAH ya baki hakuri tashi tayi tana cewa, oho nide baruwana ana magana seki ce wani ayi hakuri, mahmah dake jin duk abun da babar take cewa, duk da yanayin maganar 'kasa 'kasa tayi shi, murmushi tayi me fad'i Arai ''tace yaya rikici,๐คฃ sllmn 'yan makaranta da dawo wansu kenan ya shiga kunnuwan mahmah amsawa tayi, tana me fad'ad'a murmushin da baba ta sanya ta sakanni kad'an da suka wuce, yusura ta, tafi da gudu tana me rungumar mahmah, tana cewa ''ayyah Na dawo, mahamah dake shirin ciro ta a jikinta, tace 'yar nema ke kad'ai Kika dawo kenan, dariya yusura tayi irin ta yara, tana girgiza kai, toh jeki ki cire unifoam d'in kuma ki ninke Kayan karki bar su a wargaje, da toh yusura ta amsa tana me shigewa d'akin mahmah, dawo da kallonta kan yaran Nata dake tsaye tayi ''tace kun dawo da aeh suka amsa suna masu had'a baki wajen fad'a, d'aki munu tashiga don 'ijiye jakarta da sllm d'auke a bakin ta amsawa baba tayi wacce ke zau ne kusa da muna suna hira ๐ค to fa muna anji sauki kenan kode maganan, mahmah ne ya tabbata ๐คญ(sannou moun bรฉ sare baba) sannunku da gida baba, baba dake zaune tana jiran abokin kuka don de me tayata yau Na kwance ba lafiya ๐คญbaba ne tace Haka bani ba๐คฃyauwa 'yan nan, munu dake shirin wuce wa wajen wedrobe d'in su don canza Kaya ta tsinkayii maganan babar, ke kijimin wan nan matar tazo se fi'ili take wai sunsiyo rigar nan a 30n ita kuma asiya me 'kawa har da ban duba da kyau bane, munu da Bata fahimci inda maganar Babar ya nufa ba don Bata kawo da ita take ba, cigaba tayi da cire unifoam d'in Nata baba da tayi magana taji shiru ba amsa ''tace jimin wula'kanci ๐คyanzu wan nan 'ya ina magana kina share ni, juyo wa munu tayi tana cewa baba ,dani kuke harara baba ta ballara mata tace a'a da kai na nake, kede ba'a abun arzi'ki dake mstww baba ta buga tsaki, ta juya wajen muna tace 'yar gidan baba ko Na siyo Miki 'kosan manja ne? don Na san ''gaje ta fara suya, d'aga kai muna tayi tana cewa aeh da sauri baba ta d'au fallen atanfa ta d'aura bisa kanta ta nace wa yauwa 'yar baba fita baba tayi tana d'aga murya Na fita asiya, da toh mahmah ta amsa tana me ๐ค mamaki ina kuma yaya zata da Al murun nan iso War munu wajen ne ya yanke wa mahmah zance zuci da take yi, mahmah me zan kar 'ba maki, cikin jin dadi da kulawar da 'yar tata ta nuna a gareta ''tace bakome (bod'd'o baffa)jeki ki taso 'yar uwar taki kuyi alola lokaci yagaba toh, da toh ta 'amsa tana me koma wa d'akin dan sanar da muna maganar mahmahn.....
Idar da sllansu kenan Na isha'i zaune suke suna azkhar Na idar da sllh, tashi muna tayi Yana ijiye sallayar da ta ninke a saman kujera me Zaman mutum d'aya dake d'akin, kin Bada takar dan kuwa ?ta fad'a tana me zama saman kujeran, aeh munu tace tana me dubanta da kyau, bece kome ba? yace ALLAH ya'kara lafiya, cikin nuna jin dadi muna ''tace nagode munu tayi murmushinta me kyau, ''tace ya jikin naki? da sauki da kikaje ajin kinga sumaiyyah Umar ? a'a ban kula ba, toh muje muci abinci da toh munu ta amsa tana me mikewa daga kan sallaya fita sukayi a tare ๐abun gunun burgewa, haka rayuwan muna da munu suke a 'bata a shirya 'yan tagwayen mahmah masu abun mamaki๐๐.....
Tsakar gida suka isa inda suka tarar da hammah ali kusa da mahmah Yana latsa wayarsa ta hannu, jabir da ke zaune Yana nuna ma yusura dake zaune kusa dashi assingment d'inta ya d'aga kai yace sannunku addah yauwa sukace suna maida ma yusura tata sannun da tayi, zama sukayi suna ma mahmah sannu d dare ta amsa cikin nuna kula tana mah muna ya sau'kin jiki, yadena ciwo muna tayi saurin cewa tana amsan littafin dake hannun yusura tana dubawa, h (hammah oun hirti jam ?....)...hammah ka uni lafiya ? Ijiye wayan hร nnun sa yayi Yana cewa (djam)lafiya, kabir yace an fitar maku da unifoam d'in walimar taku ko, aeh ''tace tana 'kara nutsuwa don Bada hankalinta ga yayan nasu kuma uba a garesu don hammah ali ba matakin yaya bane kade suka bashi ba harda matsayi na uba don ya cancanta, kad'a kai yayi Yana cewa ALLAH yanuna mana lokacin ameyn mahmah tace dake sauraran su tana jin dad'i da alfahari da yaran nata, lokacin ya gabatoh ne? Jabir dake gefe yace aeh mahmah yau sheikh Adam ya fad'a mana muma hammah sannu da dare, yauwa me ya sameki ne? In inah ta fara cikin alaman rashin gsky muna ''tace kai nane yayi min ciwo hammah, kinsha magani? aeh tace tana fatan tamvayoyin su tsaya haka kar hammah ya gano gsky, in kinji bรฉ dena ba kiyi magana, toh hammah tace tana sauke nunfashi na ku'buta๐คฃ๐คฃhajรฎya muna 'yar gidan baba๐tashi sukayi suka d'auko abinci suka jera su muna ta d'ibo ruwa munu tashin fid'a kyallen da suke saka farantin abincin akai, zama sukayi a jere gunun burgewa mahmah,muna, munu, se yusura inda gefen su hammah ali da jabir ke zaune suma Masha ALLAH Bismillah ko wannen su yayi Yana me mai da hankali akan abincin gabansa๐ฅฐ๐ฅฐ.......
Please COMMENT'S ans SHARE in other group's
๐๐BO'D'DO๐๐CE๐ง๐ง๐ง
๐RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan kabari nawa 'ki'kirarrrnen labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwana da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page....6
Cin abinci suke cikin kwanciyar hankali kamande ko yaushe , wan nan yanayi na cin abinci yazama kaman al'adar ko d'abi'a ta wan nan ahali atare suke ci abincin su musamman na dare don kowa ya Na nan a gida, suna gama ci sukayi addu'ar gama cin abinci kamar yaddah manzon tsira ya koya mana ako da yaushe , ruwan da muna ta ajiye a gefene ta tsiyayo ta mi'kama mahmah ''kar'ba mahmah tayi tana me godiya ga 'yar tata ruwan wanke hannu ta ijiye agaban mahmah ''juyawa tayi tana ba hamman nasu ruwa a cup ''amsa yayi Yana godiya tare da kai ruwan bakinsa, mi'koma munu da ke gefan sa cup d'in yayi Yana me gyara zama sose alamu de yanuna magana ne abakinsa, mahmah da ta kula da yanayin d'an Nata ne ''ta umurci jabir da yusura da su kawar da kwanonin da akaci abinci a wajen, tashi sukayi suna tattara kome da aka yi amfani dashi suka kai ke'bantaccen wajen da aka killace don wanke wanke muna da munu suka tsaftace wajen da aka 'bata, Tass wajen yayi kaman ba yanzu aka gama cin abinci a wajen ba , dawowa sukayi suka zauna don ta'ba hira kad'an kamar yaddah aka Saba ko wacce dare, ''wan nan shine mahmah tasaba wa 'ya'yanta duk dare sukan zauna don hira da sanin halinda yaranta suka kasance a unin ranar Zaman nasu ba wuya, baba da tun fitarta sayo 'kosan manja ta dawo, sllm tayi tana Zaman kan ta barman dake shinfid'e a tsakar gdn, wash ta fad'a tana me sauke nunfashi, sannu yaya cewar mahmah da take Binta da kallo, yauwa asiya kinganni se yanzu ko, aeh cewar mahmah har ina shirin aiken jabir gidan ''azumi ya dubo ku, hum kede Bari asiya ๐คAshe haka yarinyar nan gajeje ta bun'kasa, mahmah da Bata gane me yayar tata take son cewa ba ''tace wata gajeje yusura dake dariya ita da jabir ''tace ayyah gaje fa me 'kosen manja, mahmah tace oh Can kikajene yaya, aeh wlh Can naje munubiyace ''tace zataci kinsan abunki da me masassara baki duk ba dadi shine fa nace buri in amso mata ko Na hamsin ne, ingaya Miki asiya layi naga anbuga akaban kaskon yarinyar nan ๐คkud'i kawai take amsa baki ba gani gsky yarinyar nan ta sanu ba kad'an ba, hammah Ali dake girgiza kai Yana danne dariyar sa ''yace Masha ALLAH tana gyara sana'arta kam, baba data samu me tayi ''tace kaide bari 'kusan ya'ki, wan nan shine sunan da take Kiran hamman dashi, aeh ninaga Abu kai har sha'awar fara soyawa nima nayi๐คฃ๐คฃ๐คฃjabir da muna suka kwashe da dariya, jabir da bรฉ jiyayi shiru yace ''kuma baba custumer zaki samu ba kad'an ba ๐คญtace kaide bari jabiru aeh goben nan Zan shiga kasuwa in suyi wake ko kwano biyu ne In gwada kaga idan naga abun da nasibi aeh se in 'kara kwano d'aya akai, dariyan da muna ta saki me d'an karfi ne ya ankarar da baba da ita bilhakki da gsky take maganan ta ''tace kaga wani rashin hankali ke yanzu usaina ni Kika tasa agaba kike ta 'bab'bakan dariya ๐ค da gyar muna ta tsayar da dariyan ta tana ''cewa wlh baba jabir zugaki yake, 'bata rai tayi tana hararanta tace ke ni bansan iya shege yanzu dan ya bani shawara ne zakice wani Yana zugani aeh yafiki ke da Kika sani agaba kina 'bab'bakan dariya kamar wata sabon kamu munu dake jinsu tayi murmushi tana du'kar dakai 'kasa tana me zancen zuci yau baba d muna ne ake fad'a ita da Bata son jin lefin muna d'in ko kad'an, maganan da hammah Ali yafara ne awaya ya hana firar ci gaba, (jam alhmdllh oho mid'on sira ma'b'be toh yafendo) lafiya alhmdllh aeh ina kusa da'ita toh yafendo, mi'kama mahmah wayan da yayine ya katsesu tunanin waye ne yayi kiran, aslm alkm mahmaha ''tace fara'ar fuskarta ne ya fad'ad'a saboda jin wacce tayi magana (maimounatou hande a noumtiyam nah?) Maimunatu yau kin tuna dani ne? dariya ta kan wayar ta sanya daga Can ''tace (addah miyajjitai moun dey) anty ban manta kuba dey ''dariya mahmah tayi tana me jin sanyi har zuciyarta 'yar uwanta guda daya da batada kamanta wacce tayi nesa da ita sose ko muryร rta wuyan ji yake mata se in ita ta nemeta saboda nisa datayi ko 'kรนdin Kira ma abune dake zaune d kansa, gaisawa suka fara cikin nuna 'kauna metarin yawa acikin hirar yasu ce take fad'ama mahmah Sun dawo suna ita da iyalinta babu zance yin nisa kuma , murna sose mahmah tayi, san nan ta d'ora da fad'amata walimar yarinyar tasu sose fendo maimounatou tanuna farin cikinta tana cewa zata zo insha ALLAH, ALLAH ya yarda mahmah tace, tambaya jama'ar gida tayi ,duk suna lafiya mahmah ''tace, amarya har yanzu Bata da wo bane aeh mahmah ''tace, toh bikin da saura kenan? Toh kร d'an zamuce don ya gabatรด, wata nร wa yayi saura addร h? Mahmah ''tace bร zรฉ wuce uku ba, aeh kode yakamata ta dawo haka don shirya wa sose ''mรนrmushi mahmah tayi tana cewa toh insha ALLAH zan Kira naji yaushe zasu barta ta taso, a'a addah kawai kice yarinya ta taso don anan ma akwai inda yakamata taje duk Bata jeba, toh mahmah tace don hakan kad'e ne zesa fendo tayi shiru, ita fendo Bata da hakurin mahmah don kome Nata Bata boye boye sam , sllm sukayi da juna fendo Na jajjadah kalman dawowar amarya don kar mahmah tayi shiru kamar yaddah tasaba ako dร yaushe ana nuna mata iko akan yaran da ta Raina da dukkan 'karfinta yayin da su masu nuna ikon Sun cire hannunsu sun saka ido saboda Wanda ya had'an ya tafi inda kowa zeje (zumunci igiyace me girma 'yan uwa mu ri'keta da kyau don tsira a gobe )....
Mikama hammah wayar mahmah tayi tana me sauke nunfashi, amsa hammah yayi ya ijiye agefenshi ya maida hankalinsa ga mahmah ''mahmah nima maganar da nake son yi keanna don yakamata ta dawo haka in zumuncin ne yayi wata biyu kenan da kwanaki, kome ta tsaya mata acan ita ba makaranta take zuwa ba acan bare muce ba kome gsky yakamata Akira ta dawo haka koya kika gani baba ya juyo da Duban sa ga baba da ke cin abinci Wanda muna ta d'auko mata lokacin da mahmah tafara waya, ta'be baki bab tayi ''tace oho tunda de ba amsar shawara uwar taku take ba ita ma maimunatun da ta dena 'bata miyan bakinta don naji asiya zatayi ba ni nan na zaunar da asiya lokacin da yarinyar nan tayi wata d'aya nace yakamata Akira ace su saka ta amota insu bazasu iya dawo da'ita ba don de ni nayi rantsuwa bazan kola d'auko taba don yaddah mammadou yarufe ido yayita fad'amin magana don nace da'ita zan dawo, ammah asiya tayi kunnen uwar shegu dani, har yau shiru kakeji toh ni mezan ce mata aeh ita tahaifi abarta, sekaga yaddah yarinyar nan ''nafi'' tayi lkcin da zan taho, ammah ace har yanzu ba a dawo da yarinya ba seka ce wata tsiyar zasu mata d zasuce abarta, rai a'bace baba ta gama magana, mahmah datayi shiru tana sauranta ''tace wlh yaya bakome yasa na'kiyin magana ba kinsan hammah usumanou da yaddah yake, mstww baba taja tsaki tana cewa aeh tunda tunda ga Amadou ko aeh ko amadoun da yayi sanadin zuwan wan nan 'ya duniya ba ya si yaganta a yanayin damuwa ba , taja tuwon ta tacigaba da ci tana cigaba da mitann anbar yarinya tana cutuwa kawai,hammah da yagama jin maganan kowa acikinsu ya sauke numfashi '' yace baba ( baba joni kam d'ume hani in gad'ata ?) Baba yanzu kam me yakama muyi? Kallon shi tayi ''tace kasan de su bazasu yi hankalin dawo da yarinyar nan ba toh kakira baffanku jafaru don de yafisu dama dama kuyi magana kanuna mashi yarinyar nan krt take aka yanke mata shi tazo yimusu sallama yakamata su dakota a mota ta dawo kar ma kanuna masa kanaso sudawo da'ita don bame wan nan kasadar, toh yace Yana 'kara jinjina hali irin Na nasu dangin kowa nasa da kansa yasani ALLAH ya kyauta yace Yana me mikewa don tafiya d'akinsa , in kakira kafad'a musu walimar su manaya, da toh ya amsata Yana me musu se da safe Dukan su, amsawa sukayi suna mai masa addu'ar tashi cikin masu Imani ameyn yace Yana cema jabir ya yabbatar yayi alola kafin ya shigo d'aki, asawa yayi da toh hammah , tashi mahmah tayi hannunta dauke da yusura da tayi bacci tun d'azu don Bata hira me tsayi, tashi munu tayi ita da muna suna ma baba se da safe Miko ma muna kosai tayi tana kinga ni nama mance dashi gashi yamayi sanyi kya dangwalashi da yajin don yajin Bade dad'i ba dariya muna tayi tana (miyatti baba am) nagode babata , mahmah da ta fitoh daga shin fid'ar da yusura tace karku mance da alola da toh suka amsa suka wuce, jabir da rai yabiya da 'kosan gaje ya taso da sauri Yana cewa (addah hami dofta moun๐คฃ) addah buri Na rakaku๐ค๐ค๐คoh malam jabiru kwad'ayi.....
Shin wan nan family dake cike da natsuwa sanin yakamata waye su?
Zamuji su waye su a page nagaba ngd๐
Please COMMENT'S ans SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'D'DO๐๐CE๐ง๐ง๐ง
๐RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa 'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwa na da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page......7
(ASALIN SU)
Modibo ''lawwali'' haifaffan kasar Nigeria ne a wani gari da akakira jimeta watoh yola anan aka haifesa anan yataso, agaban mahaifinsa ya d'auki ilimin addinin mudulunci, shida 'yan uwanshi, ilimi me zurfi bodibo lawwali yayi don har tafiyye tafiyye yayi don 'karota lkcin da yayi tafiyane ALLAH yayi ma mahaifinsa rasuwa dalilin dawo wansa gida kenan ya hau kan kujerar mahaifinsa Na bada ilimi ga d'alibai, Modibo lawwali yayi aure sose don seda ya rufe 'kofa allah kuma ya albarkacesa da samun yara sose, mata da Maza inda ya d'orasu akan hanyan neman ilimi naji ba gani toh sede kuma kowa da yanda allah ya rubuta ze rayu kula ze kasance acikin yaran Modibo ansamu wan da basa ra'ayin zama a zaure don Bada ilimi burinsu su tafi neman nakai watoh fatauci aciki akwai, ''nuhu'' Wanda akafi sani da mlm nuhu, mlm nuhu d'ane Na biyar ga modibo, taso Wansa gidan ilimi hankan yabashi daman krt dede yanda ze'iya domin shi harkan kasuwancine a gabansa, duk da bahaka bodibo yaso ba ammah yabasa dama don cika burinsa mlm nuhu ya fara harkan kasuwancin sa Yana fatauci gari zuwa gari, allah yasaka masa nasibi ya samu cigaba yakoma bin makoftan kasashe nakusa, lokacine ALLAH yabasa ikon aure ya auro matarsa ta fari wato larai, larai de macece 'yan baruwa na Nata kawai ta sani bayan wan nan Bata san nawani ba, ALLAH ya a zurta mlm nuhu da larai da yara har biyu cikin Na ukun ne da'ita ALLAH ya'kara bama mlm nuhu ikon 'kara aure Na biyu inda ya auri ''mariya'' mariya itama 'yar jimeta ce kamar larai kuma yarinyar abokin Modibo ne don su suka had'a abun ma , ALHMDLLH gidan mlm nuhu ya had'u itama mariya tasamu Nata rabon tanada yara uku larai nada hudu, tafiya tataso ma mlm nuhu zeyi fatauci zuwa 'kasar camaru, yatafi yabar larai da mari da yaransu cike da kewansa....
Ya isa 'kasar camaru ya sauka a (waila) arewa wata gari da ake Kira da ''Marwa'' awata 'karamar 'kauye me suna '' 'bogo'' garin bogo garine Wanda zamuce garin ni'ima da arzi'ki, mlm nuhu ya sauka a fadan ''jauro'' me gari ya gabatar da kansa da abunda yakawosa watoh fatauci jauro yayi maraba dashi yayinda aka basa masauki a nan kusa da fadan jauro mlm nuhu ya cigaba da gudanar da rayuwan sa a garin bogo, Abu Na farko da ya lura shine ilimin addini islam bรฉ gama ishan su ba Yako d'au niyyan temaka masu kamar yaddah aka temaka masa yatashi tsaye akan jansu sllh da yi musu wa'azi aduk san da aka idar da sllh ai kuwa gari yasoma gyaruwa, kowa na girmama mlm nuhu Hatta me gari ba'abarsa abaya ba , shawara jauro ya yanke shida mutanen fadan sa yaddah mlmin nasu yake zaune ba mata sam hakan bรฉ musu dadi, aeh kuwa jauro ya samu mlm nuhu da maganan Zaman shi haka beyiba Inde bawata matsala shi ze bashi 'yarsa ya aura mlm nuhu ya kar'bi kyautan jauro da hannu biyu, ranar wata juma'ah bayan saukowa sllhr juma'ah aka daura ma mlm nuhu aure da amaryar sa ''salaha'' sose mlm nuhu yanuna farin cikinsa akan wan nan auran, salaha yarinyar jauro ce waddah ALLAH yayi ma mahaifiyar ta rasuwa wajen haihuwarta ita kad'e ne a wajen mahaifiyarta lkcin da dangin mahaifiyarta sukace zasu d'auketa jauro ''yace besan wan nan maganan ba don ita ze kallah yaji dad'i don zata d'ebe mai kewan mahaifiyarta ba yaddah zasuyi suka hakura donde yafisu isa da yarinyar, salaha haka ta rayu a tsakiyar gidan jauro donde ba Wanda yake damuwa da'ita se in jauro na nan ne yake kula abarsa, lkcin da yaga mlm nuhu natsuwarsa da ilimin sa da hankalinsa se yayi ma salaha kwad'ayin sa....
mlm nuhu da amaryarsa salaha suna zaune lafiya 'kalau, mlm nuhu Yana Binta ayaddah take wato na 'karama shi kuma tana masa biyayyah da girmamasa maysayinsa Na abun girmamawa a duk garin bogo zama suke me ban sha'awa don de Zaman kana gani kasan namasu ilimine da sanin yakamata, lkcin da ALLAH ya azurta salaha da ciki a lkcin ne mlm nuhu yatafi ganin gida koda yatafi bรฉ samu dawowa ta Can ba har seda salaha ta haihu yaro ya fara takawa da 'kafarsa, yadawo yaga d'ansa yaji dad'i koda yatambayi sunan da akayima yaro hud'uba dashi tace aeh ance ajira ko yaushe in yadawo yasa, yanuna farin cikinsa inda ya sama yaro ''amadou'' Amadou yanada shekara biyu salaha ta 'kara haihuwa yarinya Mace inda itakuma taci ''safiya'' tunda ga lkcin salaha Bata 'kara haihuwaba ta cigaba da rainon yaranta guda biyu lkcin da mlm nuhu ya samu wasi'kan mutuwar mahaifinsa ne yasa shi tafiya babu shiri, yatafi gida inda ya taraddah anata Zaman makokin mahaifinsa watoh Modibo haka ya rungumi jarabawasa Na rashin mahaifi lkcinda akayi arba'in yaje gida da maganan yanason komowa camaru iyayensa suka mi'ke sukace basusan wan nan zancen ba inyanason cigaba da zama da salaha sede ta dawo Nigeria saboda shine ze gaji modibo, duk da rashin Zaman mlm nuhu da rashin sonsa da Zaman zaure Yana Bada krt shine akaga yafi cancanta da ya gaji modibon, be'ki tasu ba ya shirya tafiya aka ce sede yaje da d'an uwansa d'aya don karyayi zamansa ya'ki dawowa, anan ma be'kiba suka tafi tare lkcin da suka isa bogo kai tsaye fadan jauro suka nufa ya zayyane masa bu'katan 'yan uwansa agaresa san nan ya d'aura da cewa yanaso ze kwashe iyalinsa su koma tare ai kuwa jauro ya rufe ido yace besan da wan nan magana ba, babu inda yarinyar sa zataje tana kusa dashi ransu mlm nuhu beyi dad'i ba haka suka'isa gida ya fad'a ma salaha kome duk da salaha tana son mijinta ammah ta daure don Bata da kaman jauro a rayuwarta, tace nataso tun'ina yarinya a RAYUWA TA baffana kawai nasani shine komai nah babu Wanda ya damu da naci ko banci ba se baffana kayi hakuri zanbi umurninsa, mlm nuhu ya girgiza dajin abinda salaha tace Na bazata bishiba, haka suka gama ro'ko da kama 'kafa wajen mutanen da yasani shida d'an uwansa ammah jauro ya'ki sam haka mlm nuhu ya hakura, ammah yana fata watarana jauro yayi hkr yabasa matarsa , tafiya sukayi salaha taci kuka har ta gaji inta ke'be ita kad'e tayita kuka ammah in tafitoh cikin jama'ar gida se tanuna kaman Bata damuba, bayan tafiyan su mlm nuhu jauro ya dawo da salaha cikin gida wajen 'yan uwanta, abunda salaha Bata saniba jauro yana lura da ita sose kuma Yana jin lallai bema 'yar tashi adalci ba, ahaka rayuwa tacigaba da turawa da dad'i ba dad'i har yara suka fara girma kuma har ya zuwa yanzu salaha na son mijinta da begensa, ahaka ALLAH ya jarabci jauro da jinya haka yayita jinya me tsayi a lkcinne ya Kira salaha ya Bata hkr Akan rashin adalcin da yayi mata kuma yace ko yanzu mlm nuhu ya dawo ya yarda ta bishi, taji dadi sose har se da tayi kukan murna haka taciga ba da jiran tsammani Na zuwan mlm nuhu tare da jinyar ma haifinta har ta ALLAH taka sance akansa yace ga garinku nan, salaha tashiga wani hali don de gata guda d'aya da take dashi ya tafi shima ga gida ba dad'in shi take jiba ma koda jauro bare yanzu babu shi, haka ta cigaba da rayuwa cikin wani irin hali, kwazam ranar Sega wani dan 'kauyen kusa dasu yace lallai yaga mlm nuhu a jimeta Yana Bada krt, sose salaha taji dad'i haka aka had'a mata Kaya ita da yaranta suka tafi tare da wan nan bawan ALLAHn koda suka isa jimeta kai tsaye gidan Modibo lawwali suka isa, tabbas salaha yau tasan tayi kewan mijin Nata sose ,haka aka amshesu cikin mutumci, aka gyarama salaha d'aki ta shiga, toh salaha de zama acikin gidan yawa ba farko bane awajen ta don de tasaba da nasu gidan ammah abunda yake damunta ware ta da'ake yi gefe sose ake nuna mata wariya ammah Bata ta'ba fad'ama mlm nuhu ba, yaranta ko sunyi lefi ko basuyi ba dukane kawai, ita de kullum cikin kawaici da cire fuska take, haka rayuwa ta cigaba da turawa inda salaha da yanzu yaranta suke Kira da dada tacigaba da fuskantar abubuwa kala kala ana haka salaha ta kwanta masassarace ta kwana biyu, tace ga garinku nan mlm nuhu ya girgiza da wan nan rashi da akamasa ya firgita sose yaji wan nan mutuwa, bayan kwana bakwai iyalan jauro da suka zo sukace zasu tafi da yara mlm nuhu yace sam bรฉ yarda ba yaransa ahannunsa zasu cigaba da zama basu ja maganar ba suka bar masa yaransa.......
Amadou da safiya wata rayuwa suke na ban tausayi duk wani me Imani ya gani se ya tausaya musu basu isa ra'ban d'akin kowa ba amatan mlm nuhu ko wacce Nata tasani a d'akin mahaifiyar su suke kwana anan suke kome su biyu babu Wanda ze tambayi lfynsu ko yaya suka kwana kaman ba yaran gida ba tun suna saka ran dawowar dadar su har suka fara hakura su ka tabbatar tayi nisan da bazata iya jin kiransu ba๐ญ a hk mlm nuhu ya daukeshi yakai shi wajen abokinsa karatu a garin zariya ranar rabuwa haka suke kuka shida safiyyah ri'keshi tayi tana zata bishi shima kuka yake Yana bazejeba haka mlm yunusa ya ri'keshi mlm nuhu ya cire safiyya a jikin amadoun , haka aka tafi dashi suna kuka da d'agama juna hannu , sabon rayuwa me 'yanci Amadou ya ci karo dashi a garin zaria a gidan mlm yunusa d'a yake ba almajiri ba baya bara baya kome da duk wani almajiri yake krt kawai yake babu wasa matar mlm yunusa ta d'aukeshi matsayin d'a ne mlm hauwa'u son sa take har ranta haka yataso Yana krtnsa cikin kwanciyar hankali duk lkcin da akayi hutu ze je jimeta yaga ''yar uwansa suyita murna ranar rabuwa kuma ayita kuka haka rayuwa ta cigaba da tafiya yayinda lkc yake gudun wucewa, yau gashi Amadou yayi sauka mlm nuhu dakansa yazo tare da safiyyah suka tayasa murna suka dawo suka barsa alokacinne mlm yunusa ya nema masa aikin kanikanci san nan yasa masa littafai Na karatu san nan yafara haddah sose yake maida hankali a karatu da aikinsa , kuma ALLAH ya samasa albarka aciki ana hakane kuma safiyyah ta samu mijin aure inda ta auri almajirin mlm nuhu wan da shi da kansa yanuna bu'katan haka mlm nuhu kuma yabashi sose Amadou yaji dad'in auren 'yar uwar tasa don dama kullum tunaninshi yanayin da take rayuwa acikin gidan mlm d'in, duniya sabuwa zamu'iya cewa donde Amadou rayuwa ta samu cigaba duniya ta bud'e Yana ganin haske akome Na rayuwarsa inda yabar harkan kanikanci ya koma kasuwa, yafara da jiran shago daga nan kuma ALLAH ya temake shi ubangidanshi me kirki ya bud'e masa nasa , ahakn Yana temakon mlminsa don har ce fane ya d'auke masa san nan ta Can gida jimeta ma Yana iya 'ko'karinsa tare da tallafama 'kanwarsa da ba abunda ta nema ta rasa arayuwarta miji yatsaya mata ga kuma yayanta shima haka lokaci ya dunga gudu inda ALLAHh ya had'a Amadou da wata ba fulatana me suna ''asiya'' asiya mafulatanan jimeta ce ita ma awata ruga da Al Kira rugal maman anan iyayenta suka haifesu ita da 'kanwarta maimounatou suna dauko nono su shigo dashi cikin jimeta in sunsiyar sukoma gida, wata Rana Amadou yaje jimeta suka Had'u da asiya ta d'auko nono, Yako yaba batare da 'bata lkciba ya samu mlm yunusa da magana da yakama zaria shi kuma mlm yunusa yayima mlm nuhu bayani, ba'bata lokaci suka nemi rugar su yarinya suka je don nema ma Amadou aure , toh kowa de yasan waye mlm nuhu a jimeta nasabace garesa me kyau ba 'bata lkci baffan asiyz ya amince.....
Please COMMENT'S and SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'D'DO๐๐CE ๐ง๐ง๐ง
๐ RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwa na da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page.....8
Ansha biki sose inda bayan biki ango Amadou ya dau amaryarsa asiya suka koma garin zariya da zama, Can wani anguwa ya kama haya inda suka kasance su uku a cikin, gidan, kuma dukansu zamuce yarane duk da acikinsu akwai me yaro d'aya, zaman asiya a zaria kokari kawai take dan kar mijin Nata ya fahimci halin da take ciki donde ba sabawa tayi ba taka sakin jikinta a cikin mutanen gida tana baya baya dasu duk da zamu 'iya cewa wan nan d'abi'ar fulanine kafin suyi sabo dakai akan dad'e ๐ hakan da sauran matan gidan suka ganine se suka soma ja baya da'ita suka koma suka had'a kansu ita kuma takoma gefe tana kallon su da 'ido kawai, asiya yarinya ce me hankali natsuwa ilimi don ta sauke awajen baffanta ta karanta wasu daga cikin littafan addini, lokacin da Amadou ya farga da kaman tana cikin damuwa ne ya kirata ya zaunar da ita akan ta fad'amishi meyake damunta, se kawai ta fashe masa da kuka tace ita kewan baffanta da dadanta da 'kanwarta take, ๐คcikin mmk yake kallonta Yana juya maganan a zuciyar sa toh yaushe akayi daren ma ๐คฃkunji de abunda Amadou yace.
rarrashinta yayi har ta samu nutsuwa tare da alqawarin ze saka iro 'kaninsa d'an wajen baba mari da yakai waya Can rugan maman d'in tayi magana da baffanta, aeh ko ba'karamin dadi asiya taji ba ranar har su maman sadiq seda suka lura da hakan, aeh ko basuyi shiru ba suka tambaye ta dalilin farin cikinta tace babu kome, toh wan nan yanadaga cikin d'abi arta da yake basu ta kaici don de asiya baka isa kaji cikinta ba tanada zurfin ciki sose sirrinta kam Bata fitarwa ga kowa daga ita se cikinta, duk da zamu 'iya cewa harda hud'ubar dadanta da ta ri'keshi kam a 'kwa'kawalwa ta zuciya, samun mlm yunusa Amadou yayi da maganan asiya Na Yana kewan iyayenta tana son ganinsu, gyara zama mlm yunusa yayi Yana me murmushin yaro de yaro ne, yanzu kai Amadou me kake So ayi kenan , ya 'kara du'kar da kanshi cikin nuna ladabinsa ga mlm d'in ''yace mlm duk hukuncin da ka yanke yayi, cikin nuna farin ciki da biyayyan da Amadou ke masa kaman yaddah yake ma mahaifin da ya haifesa ''yace toh inaga kad'aici ne ya ke damunta kasamu mkrnta namasu aure ka Sakata zata dunga rage lkci acan, sose Amadou yayi murna da umurnin mlmin nasa, aeh kuwa yafara nema mata mkrnt aka samu cikin yardar ALLAH yazo ma da asiya da albishir d'in fara zuwa mkrnt, ba'karamin dad'i asiya taji ba tayi murna san nan a ranar iro yakai ma su baffanta waya, zokaga dad'i wajen asiya tayi magana da iyayen Nata tare da fad'a musu zata fara zuwa mkrnta baffanta yayi mata nasiha sose Na ta kama kanta ita matar aurece sose ita ma dada tayi mata Nata nasihan tare da jan kunne, se kuka asiya take haka suka gama wayan nan cikin farin ciki da kewar 'yar tasu itama ta wajen asiyan hakan ne ke d'awai niya da'ita ๐ฅนtoh ya zakiyi asiya aeh aure ya'kin mata ne๐....
Asiya tafara zuwa mkrnt sose ta maida hankalinta akan karatu wan da ya shige mata ga mijinta kome Nata a garin zarian ta tambayeshi, shima dayake Masha ALLAH anyi karatun sose, haka asiya tafara sabawa da garin, tuni gari yasoma ma asiya dad'i ga shi gefe d'aya tana ta fama da laulayin cikin da ba ze wuce wata biyu ba haka rayuwa ta cigaba da turama wa''yan nan bayin ALLAHn inda allah ya sauki asiya lfy ta haifi yarinyar ta Macรฉ kyakkyawa kamar mahaifiyarta don de kamar su d'aya da asiya Bata d'au kome na amadoun ba asiya ce babu sirki๐ranar suna yarinya taci suna fad'imatou ana kiranta da fad'i Masha ALLAH haka Amadou da asiya suke rainar yarin yarsu cikin so da kulawa, inda ALLAH ya 'kara bud'ama Amadou sose a harkan sana'arsa Yana ganin bud'i, ta bangaren asiya kuma krt se nisa yake haddah take Bada wasa ba mijinta waddah ayanzu take jin babu kamarsa a duniyarta, yatsaya mata sose don cika burinta Na haddace al'qur an haka rayuwan take turawa Sega fad'i an cika shekara d'aya aduniya babu inda ba ta takawa yarinya abun so ga kowa 'yar gatan baffanta, lkcin da fad'i ta cika shekara asiya taso zuwa jimeta ammah su baffanta da dakansu suka hana zuwan Nata don bikin ''yar uwarta maimunatou da'aka sa ba da dadewa ba sukace ta Bari se bikin ya gabatoh se tazo gaba d'aya, duk da ba haka asiya tasoba ta hakura don anan ma akwai matar mlm yunusa ta tsaya masu sose kamar uwa don duk abunda ya dace uwa tayi shi take masu.....
Haka asiya taciga ba da karatu tare da jiran lkcin bikin maimunatou, don de a matse take da son ganin iyayen nata da a yanzu tacika shekara biyu da wasu watanni Bata sasu a idonta ba, ana haka asiya tafara sabon laulayi da alama de An'kara samun rabo ne ๐คญtoh sede muce asiya ALLAH ya inganta ciki na da wata biyar bikin maimunatou ya taso, aeh kuwa asiya ta ci kuka da aka hanata zuwa bikin 'yar uwar tata donde Amadou rufe ido yayi yace se ta haihu zataje, lkcin sa ya fad'i mata hakan ta tada hankalinta sose, ganin hakan da yayi ne yasa sa Tura iro rugan su asiyan don tayi magana da su baffan 'kila ta sassauta ma kanta kodan abunda ke cikinta, sose baffa da dada suka had'u suka yi mata tass sukace in tayi wasa ma zasu hanasa barinta zuwa ko da ta haihu, haka asiya ta saka ma kanta dangana da hakuri tanaji tana gani akayi bikin 'yar uwar ta ta, Masha ALLAH maimunatou kam me hannu da mai 'ko de ALLAH yabata donde ya ijiye a bank๐ana gama shagalin biki ya d'au matarsa suka shilla canada, toh ta 'barayin asiya de tana nan tana ti tsawa, cikinta Na da wata bakwai ne, akayi walimar tabbatar dasu a mahaddata al'qur'an Masha ALLAH kowa yaganta se yaji sha'awan zama kaman 'ita, sose matar mlm d mlm yunusa da sauran yaranshi suka yi musu kara kai in ba a fad'a maka bama zaka ce yarinyar mlm d'ince, .....
Masha ALLAH haka asiya ta haifi yarinyar ta ta biyu itama kyakkyawa da 'ita donde wan nan karan camaru muka tafi yarinya kamarta d'aya da amadou๐ ranar suna yarinya taci sunan matar mlm yunusa hauwa'u ana kiranta da ''Dali'' Masha ALLAH haihuwan Dali yazo da wata sabon Salo donde bayan suna da kwana shida Amadou ya tare a 'kerarran sabon gidan sa da yayi asabon anguwa gida naji na fad'a, sose asiya tayi mmk don ko a mafarki Bata kawai hakan ba, bayan arba'in d'in Dali ne Amadou ya shirya musu zuwa jimeta a sabuwar dalleliyar motarsa da yasiya kwanaki biyu da suka wuce haka suka tafi jimeta cikin d'in bin Na sarori, kowa ya Gansu se san barka, ammah ta bangaren 'yan uwa da iyayen su hassada ne cike a rayukansu toh dama ance zakaran da ALLAH yanufa da cara....๐sose mlm nuhu yaji dad'in ganin d'an nasu cikin Rufin asiri, kwanan asiya biyu a gidan su amadou, taga dangi Sun ganta, Amadou ya tattarata ita da yara ta kaisu rugan mamman sose asiya tayi farin ciki suma su dada da baffah hakan take, suna cikin farin ciki ga su ga 'yan jikokin su, sose asiya tayi ziyara don amadou ko mawa zaria yayi ta barta tagama ziyaranta a natse, aeh kuwa asiya ta sha ziyara taje gidan 'yan uwa sose haka ta tattaro tadawo jimeta zuciya cike d kewan 'iyayenta, dasuma tasan dauriya kawai suke alkcin ne ta san safiya watoh 'kanwa d'aya tall ga mijinta sose suka sha'ku da juna don de safiyya ta ji dad'i Na ganin asiya amatsayin matar yayan Nata haka Amadou ya zo ya kwashesu suka koma zariya zuciya cike da kewan ahalin nasu....
Tunda suka koma zaria asiya ta koma mkrnt don son fad'ad'a iliminta shi kuma Amadou ya'kara 'kaimi akan sana'ar tasa Masha ALLAH kuma sose suke ganin cigaba haka asiya ta'kara haihuwa a wan nan karan d'a namiji ta samu sose ita da amadou sukayi murna tare da abokan arzi'ka yaro yaci suna aliyu haka asiya da amadou suka cigaba da kula da yaransu ciki amincin ALLAH , awan nan lkcin ne asiya taji haihuwar 'yar uwarta maimunatou tayi murna sose duk da ba daman zuwa haka rayuwa yayita juya wa haka asiya ta 'kara haihuwa inda ta haifi Macรฉ awan nan karan taci suna ''nafisa''ana ce mata nafi Masha ALLAH awan nan lkcin ne amadou yakai ziyara d'akin ALLAH ya sauke farali rayuwa tayita juyawa inda amadou se bun'kasa yake, yakai mlm nuhu da mlm yunusa suma Sun sauke farali se sam barka suke yi da aduu'ar nasara a rayuwar sa 'yan uwansa ma bรฉ barsu a baya ba duk da zallar hassadan da yake gani a idanunsu ya dan ne Yana temaka masu iya yaddah ze iya, shiri ziyaran gida asiya take donde wan nan karon ma ta dad'e Bata jeba, taga ma had'a kome da zasu nema ita da yara har an sasu a mota, amadou ya samu Kira daga mlm nuhu inda yake sanar masa da ALLAH yayi ma baffan asiya rasuwa jinyan kwana d'aya allahu Akbar rai ba'a bakin kome take ba, gashi de baffa shima yatafi inda kowa yake jiran ranar tafiyarsa, sose amadou yarasa tayaddah ze fad'ama asiya wan nan al'amari haka de da asubayi bayan Sun 'idar da sllh ya daure ya fad'a mata sose asiya ta girgiza tayi kuka sose haka suka kama hanyan jimeta cikin damuwa da d'imuwa sose asiya dataga da gaske baffanta yatafi ta rikice jikinta ya rikice har seda ta kaita da kwanciyar asibiti anan ne aka gano cikin da ke ma'kale a jikinta, likitoci da kyar suka 'iya tsaida cikin do damuwar da tashiga yaso yayima cikin 'illah haka aka sallameta tare da Bata shawar wari kan ta rage damuwa, haka aka cigaba da kar bar makokin baffan lkcin da baffa yayi kwana bakwai ne maimunatou ta'iso itama da tsohon ciki tare da'ita Haka mutuwa ya dawo musu sabo, suka rungume juna suna kuka me ta'ba rai kowa yagansu seya tausa ya masu, bayan arba'in ne 'yan uwan dada suka ce zasu tafi da'ita dake 'ita mutuniyar ''mali'' ce haka suna ji suna gani dada ta ke ta shirin bin 'yan uwanta toh suma de Sun amince don de anan babu kowa Nata se abokan ar'zu'ka haka suma suka shirya tafiya, maimunatou zata sauka gidan surikanta dake garin Kano har seta haihu zata koma Canada inda asiya zata wuce zaria haka rayuwa yake baffade tasa ta 'kare, koma wansu babu dad'e wa ne maimunatou ta haihu yaranta uku kenan don da biyu ta taho se ciki, asiya har Can Kanon taje, bayan suna ta dawo , maimunatou ita ma ta kawo ziyara gidan addar tata a garin zaria bayan tayi arba'in sose ta ji dad'in yaddah yaga addar tata tana cikin wadata da kwanciyar hankali, bayan koma War maimunatou Canada ne itama asiya ta sauka a wan nan karon 'yan biyu ALLAH yabata duka mata yara kyawawa inda usainan ta kasance fara Tass ita kuma hasanan chocolate ce ita ba ba'kaba ba kuma fara ba sose masoyan su asiya suka tayasu murna ranar suna kuwa amadou da yakoma alhaji amadou ya taka rawar gani sose ya fitoh da 'yan biyu da mahaifiyarsu har da 'yan uwarsu kowa se sam barka, yara aka bar musu sunan su Na ''hassana'' da ''usaina'' anakiransu da ''munaya'' da ''munubiya'' bayan 'yan biyu asiya ta'kara haihuwar Na miji inda yaci suna jabir Masha ALLAH asiya da alhaji amadou sede suce alhamdllh ala kulli halin๐ฅฐ๐ฅฐ๐ฅฐ .....
Please COMMENT'S ans SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'D'DO๐๐CE๐ง๐ง๐ง
๐RUYUWA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancinsa, ina ro'kon allah yabani daman rubuta dede ya hani hannuwana da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page.....9
Rainon yaransu suke, cikin so da 'kauna, kwanciyar hankali da had'in kai shike wan zuwa a cikin wan nan ahali na alhaji Amadou da matarsa asiya, haka rayuwa take Tura ma wan nan ahali yaransu suna zuwa makaranta ingattattu daga boko har islamiyyah sede muce Masha ALLAH cikin wan nan yanayine mlm nuhu ya kwanta ciwo, tun ana d'aukan abun da sau'ki Abu fa se gaba yake da farko an hana alhaji Amadou zuwa don yaddah ake gani Yana iya tashi har ya Bada krt d yammah ga magidanta toh abude yafi 'karfi gida an dangana mlm nuhun zuwa asibiti, dole aka Kira mlm yunusa aka sanar masa yanayin jikin aminin nasa sose ya girgiza dajin mlm nuhu sede an kwantar a ta yar, hakan yasa shi zaunar da alhaji Amadou ya fad'amasa cikin hikima da fasaha kamar yaddah ALLAH ya horema mlmanmu fasahan harshe, sose ya fahimcesa, cikin mutuwar jiki alhaji Amadou ya koma gida Yana jimami da fargaban yaddah jikin baffan nasu yake don de shi yasani jikin ya tsananta, don de in bรฉ tsananta ba mlm yunusa baze zaunar dashi akan maganan ba, sauke zuciya yayi da d'an 'karfi har seda asiya da ta'ijiye masa lemo a kusa dashi tajishi, cikin nuna kulawanta ga mijin Nata fuska cikin damuwa, ''tace ( baffa fad'i a jamo? ) baffan fad'i kana lfy, kallonsa ya sauke akanta Yana d'aga mata kai, ya d'au lemon da ta'ijiye masa ya sha kad'an ya ijiye, 'kara kallonshi tayi cikin kulawa ''tace akawo abinci ne ko zaka watsa ruwa kafin nan, dubanta yayi dakyau, se yaji duk beji dad'i ba burin asiya ne kawar masa da dukkan damuwar sa ko kad'an Bata son ganin shi cikin wani hali, 'kara sauke ajiyan zuciya yayi yari'ko hannunta shima cikin 'karfafa ma kansa gwiwa ''yace dada fad'i ba kome kaina ne yayi min nauyi ammah da sau'ki don kallon wan nan kwalliyar taki ma ya war kar da shi ya 'karike fad'a Yana d'an murmushin 'karfin hali donde da gaske hankalin sa ya koma jimeta so yake yasan wank hali baffahnsa yake ciki, ita ma murmushin tayi duk da tana hango damuwa a idanun mijin Nata don de tasan ya fad'i hakan ne don kar 'itama yasata a damuwa, tashi ki had'amin ruwan wanka, yafad'a Yana maida cup d'in lemon d'azu a bakinsa, mi'kewa asiya tayi jiki duk a sanyaye ta nufi toilet, fitoh wa tayi tana sanar masa da ta had'a masa ruwan mi'kewa yayi Yana tambayan ta 'yan islamiyyah basu dawo bane? da aeh ta amsa tana me bud'e wajen ajiyar kayansa don ciro masa Wanda ze sa, lkcin da yafitoh ya kimtsa ya nufo parlor, fitoh warsa ba dad'ewa ne sllmn 'yan mkrnt ya ratsa parlon, sannu da gida suka ma iyayen nasu, binsu da kallo alhaji Amadou yayi, Yana 'kara gode ma UBANGIJI game da kyautar sa garesa donde yasan babu wayo ko dubara ko isa acikin wan nan kyauta, yanatuna yaddah suka rayu daga shi se 'kanwarsa kad'e ammah yau gashi cikin wata ni'ima na ALLAH ko ina ya juya cikin gidan sa motsin yaransa ne ketashi ALHMDLLH ya furta Yana binsu da kallon so da 'kauna, amsawa yayi Yana umurtan aliyu da yayi sauri ya d'auro alola don sutafi msslc, don anfara Kiran sllhr magrib da toh ya amsa Yana Shiga d'akin sa don bin umurnin baffan nasa, suma matan tashi sukayi suna nufan nasu d'akin don shirin sllh, bayan dawowan baffah da aliyu gida bayan sauke farali suka zauna cin abinci, bayan Sun gama fad'i da tafara zama budurwa ne ta tashi tare da Dali wacce itama anfara girma suka tattara wajen, san nan suka dawo suka zazzauna don hira da iyayen nasu....
munu dake zaune kusa da Dali tana kallon yaddah, take assingment d'inta ne baffah, '' ya yafitoh ta da hannu Yana cewa( War ) zo 'yar gidan baffah, ''tashi tayi taje kusa dashi d'agata yayi yasa ajikinshi Ya mi'kama muna hannu ita ma ta taso ya sata ita ma a gefe yafara musu tambaya akan mkratar da suka je yau cikin haza'ka da nuna suna fahimtar abunda ake masu suke Bada amsa sose, wan nan abun ya burge baffah har ya d'an fara jin sassauci akan damuwar da yake ciki, kukan jabir da yake son ture muna ya zauna a jikin baffah ne ya dawo da shi acikin tunanin da ya tafi na 'yan sakanni, dariya yayi yana, a'a auta ya haka me ne usainan tayi maka kuma? Mahmah asiya dake kallon su , ''tace so yake ta tashi shi ya zauna, baffah ''yace toh๐คba'ayi haka ba kaima matso ga naka wajen nan, zau Nar dashi yayi Yana kallon ko wannen su ''ya bud'e taro da addu'ah, ya dawo da kallonshi akan mahmah ''yace (dada fad'i 'bandu baffah oummi) dada fad'i jikin baffah yatashi, sose mahmah ta shiga damuwa, ba'ita kad'eba har su fad'i sunshiga saboda 'kaunar kakan nasu a garesu don ba kad'an ba mlm nuhu Yana nuna kula agaresu don har bore su mama mari sukayi masa ammah be bi takan suba ya nuna ma besan sunayiba, addu'ah suka fara yi baffan nasu na amsawa da ameyn yajira suka kammala ya cigaba da magana kamar haka, ''yakamata gobe in ALLAH ya nufa in tafi don dubo jikin nasu, da toh mahmah ta amsa tana gyara zama, baffan fad'i kafad'a ma baba mlm kuwa, haka suke Kiran mlm yunusa aeh yace ya 'kara da cewa shine ma ya sanarmin, tare zaku tafi ne? mahmah tayi tambayan tana kallon mijinta a'a yace Yana gyara ma jabir kwanciyarsa, gobe Yana da zuwa saukan d'alibai da aka gyayyaceshi, inaga de ze biyo bayana sauke numfashi mahmah tayi hankalinta ya kasa kwanciyar da Bata san ko me ya kawo hakan ba, tunda baba mlm baze je gobe ba me ze Hana mutafi tare, kallonta yayi yana karantar damuwanta, ''in muntafi yaran su zauna da wa tunda ba hutu akayiba bare mu tafi duka tare, hum mahmah tace donde ita ma Bata san duk dalilin damuwar tataba akan tafiyan mijin Nata ba yanzu yafara zuwa jimeta ba shi kad'e, saurin kauda kome tayi tana allah ya kaimu goben, ameyn yace Yana kallon munu dake zaune shiru ba'ajin ko motsinta ''yace bod'd'o baffah azo ayimin krt yau da wuri don gobe akwai tafiya da sassafe a gabana natsuwa kowa yayi don sauraran krtun munu don munu tun tana 'karamanta Inde zatayi maka karatu sekaji kamar karta dena, me 'kira ar manya sunanta a mkrntar su tashi tayi ta jingina da jikin baffan ta tafara krt baffah Na kallonta cikin alfahari da soyayyarsa wacce baya 'boyuwa a lokuta da dama Yana murmushi wacce da'alama tunda ga 'kasar zuciya yake fitoh wa suratul ''AHA'KAAF take karantawa cikin nuna syyrt ga karatun Nata lkcin da ta kai 'karken suranne ta d'ago ta kalleshi cikin muryan ta me sanyi ''tace (baffah ALLAH findi'in jam) baffah ALLAH ya tashemu lfy ameyn 'yar baffah ya fad'a Yana shafa kanta mi'kewa tayi ta tafi, murmushi be bar fuskan sa ba har seda yaga shiganta d'aki, kallon muna yayi ''yace usaina tashi jeki ki kwanta (se fajiri baffah ) se da safe baffah ''tace ita ma tana tafiya, d'aukan jabir Dali tayi tana kaishi d'akin kwanansu....
shirin, kunnah tv baffah yayi don kallon labarai 'biradam d'in da mahmah ta tafaso masa ya d'auka Yana sha, me kike kallo ga rayuwar 'yar ki nan gaba mahmah tasan aka. Wa ne yake magana ''murmushi tayi tace inaga de zata yi gado ne murmushi shima baffan yayi yace le kenan zata gada ๐ณmahmah tayi tace tsola ko ''yace a'a gsky de girgiza kai tayi ''tace buri Na had'a maka kayanka tun yanzu nasan fitar asuba zakayi, kede kice de dama kin 'kosa Na baku iska ๐ค''tace yaushe nafad'a ''yace kinsan de ina karantar zuciyarki ko ''tace yau de baka karanta dede ba yace 'kila tazaran dake tsakaninmu ne yasa igiyoyin sadarwan yayi sanyi ๐mรนrmushรฎ mahmah tayi tana me 'kara gode ma UBANGIJI akan kyautar miji me hankali sanin yakamata me kula da iyali da yabata Inde zega damuwa a idon d'aya daga cikinsu ita ko yaranta baze hutaba har se ya kau da wan nan dร muwar, kinga bar had'a Kayan nan ko da asuba zaki'iya ba gagawa ake ba hajjiya asiyan alhaji amadi ya 'karike Yana kashe mata ido ๐'kasa mahmah tayi da ido tana ''cewa kร de kusa yin siriki shima dariya yayi yana ''cewa toh se akace don zanyรฎ suriki in zama dutse ๐คya'karike mgnan Yana ri'kรฉ ha'ba, dariya mร hmah ta 'kyalkyace dร shi tana ''cewa nide bance ba dungure kanta yayi Yana cewa dama kice kigani ina dawowa daga jรฎmeta in dauko 'yar cass dedeni ya 'karike mgnan Yana danne dariyarsa ๐คญsbd yaddah yaga fuskan mahmah yayi....
jawota yayi kusa dashi ''yace ba wata da zata samu gurbi anan Yana nuna saitin zuciyarshi seke, kece kad'ai sirrina kece kad'e Matata insha ALLAH kin bani kyawawan yara kamar ke masu tarbiyyah da natsuwa bayan safiyya ban ta'ba tunanin 'kara samun ahaliba se gaki kinshigo RAYUWATA ke kyau tace daga UBANGIJI nah gdy ta garesa shine barinki ki rayu a gdn ba tare da wata kalma ta kishiya ba.....
Please COMMENT'S and SHARE in other group's๐๐๐
๐๐BO'D'DO๐๐CE ๐ง๐ง๐ง
๐ RAYUWATA๐
๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ๐ซ
Wan nan labari nawa'kir'kirarren labari ne, ina fata ya amfani duk wani makarancisa, ina ro'kon Allah ya bani daman rubuta dede ya hani habnuwa nah da rubuta ba Dรฉdรฉ ba akafta๐๐๐
Page.....10
Misalin 'karfe 6 Na safiyar washe gari, baffah da yafitoh tsaff cikin shirin shi na tafiya, ya zauna a d'aya daga cikin jerin kujerun da ke parlor Yana kur ban tea, wacce mahmah ce ta matsa akan se ya sha ba ze fita babu kome a cikinsa ba, duk da yace mata ze za'a a wudil ya karya ammah tace sede yasha tea d'in, kallon agogon dake manne da bangon parlorn ya'kara yi Yaga lkci fa Na tafiya ijiye cup d'in yayi ya mi'ke Yana fad'in, kiramin yaran nan muyi sllm, tashi mahmah tayi ta nufi d'aku nan su, Kiran ko wannen su tayi, suka fitoh a tare mi'kama ko wannesu hannu baffan nasu yayi suna musabaha wan nan d'abi'ar sane Inde tafiya ta taso masa me nisa ze yi sllm da yaransa cikin musabaha da ko wannensu, ri'ke hannu aliyu yayi ya matse sose ''yace zan tafi a kula da gida a kula da mutanen cikinta kar inji wata magana bayan nadawo girgiza masa kai yayi Yana fad'in insha ALLAH baffah, haka suka fitoh su Dukan su suka nufi filin da baffah yake ajiye motar sa, fad'i da ta d'akko karamin a'kwatin da mahmah ta shirya masa Kayan sa a cikine ta bud'e bayan motar tasaka, dukan su suka matso bakin motar da baffah ya Shiga Yana zaune gaban motar yana amsa waya wacce yaddah yake amsata ne nagane da mlm yunusa yake saboda yaddah yake amsa wayan cikin girmamawa, ameyn allah ya saka maku, shine 'karshen abunda sukaji yafad'a ya kashe wayan, ya juyo da kallon sa kansu ya sakar musu murmushi yaddah yaga duk sunyi shiru suna kallonsa, ''yace akula da gida ( dada bikkoy) maman yara, daga masa kai tayi tana me ''cewa toh insha ALLAH ya jinjina kansa, ya mi'ko ma munu hannu ita da muna yace tagwayen baffah kuzo, tafiya sukayi wajensa da sauri ya shafa kawunan su ''yace a dage da krt kar asaka wasa baffah zeyi alfahari daku amsawa sukayi suna kallonsa, yasakar masu murmushi, ''yace toh ku tashi kar inyi daren hanya tashi sukayi ya mi'kama jabir hannu da gudu ya zo shima shafa masa kai yayi Yana me saka masa albarka a zuciyar sa, sweet d'inka Yana hannun mahmahnku, banda rigima, daga masa kai jabir d'in yayi kafin baffan ya sauke sa, ya kalli fad'i, da Dali, da nafi, ''yace banda wasa, suka ce toh ya kalli fad'i yace kud'in shahadar ki Yana hannun mahmahnku, tuni murmushi ya bayyana a saman fuskan ta tafa ra jero addu'o'in da iyayen su suka d'au rasu akai na idan wani ya kyautata maka ka tabbatar ka godema sa se yaji dad'in 'kara faranta maka sose kuwa baffan yaji dad'in addu'o'in d'iyar tasa, mahmah ce ta kallesu Dukan su ''tace toh ayima baffah addu'ah a je a fara shirin skull sose suka yi masa addu'ar da ya faranta masa Yana me 'kara alfahari dasu a ransa, ameyn ya ke ce musu cikin nuna kulawar shi garesu, juyawa sukayi suka shiga cikin gida kowa najin kewan baffan nasa a ransa, kallon mahmah yayi bayan tafiyar yaran nasu ''yace toh asiyen amadi zamu d'au hanya ga amanata nan de har kullum ina 'kara barmi ki a kuladasu kamar ina nan, ki dunga tuna hadisin ma'aikin Allah aduk sanda kikaji kin gaza mata rahmane , kuma ta sana dinsu zamu 'iya Shiga aljannar Allah, toh Inde da sabo mahmah ta Saba da wan nan mgn nan don kusan kullum maganan baffan ne hakan, murmushi tayi me fad'in ta ri'ko hannunsa ta fara masa Nata addu'oh'in cikin shau'kin so da 'kauna yake amsawa Yana kallon cikin idon ta, ameyn Allah ya dawwamar maku da farin ciki ke da 'ya'yana, ita ma ameyn d'in tace tana me matsawa a jikin motar addu'an hawa abun hawa yayi, Yana me kunnah motar me gadin sa da yasa babu dad'ewa ne ya fitoh daga d'akinsa ya bud'e masa get d'in 'karuso wa yayi me gadi yafara masa addu'an sauka lfy, saka hannunsa yayi a aljihun gefe Na rigarsa ya ciro kud'in da bazan ce ga yawan sa ba ya mi'ka masa Yana 'kara jadda da masa kalman a kula da aiki da kyau, sose me gadin da yaran gida ke Kira da baba ado ya kai har 'kasa Yana godiya tare da tabbatar da insha ALLAH yaddah kabar gd lfy haka zaka dawo ka taraddah shi lafiya, Masha ALLAH ''yace Yana me gangarawa da motarsa kan titi Yana me gyara Zaman sa ya d'au hanyar jimeta......
Tafiya yake sannu a hankali krtun qur'an natashi amotar yayin da baffan yake bama motar wuta, Masha ALLAH ana shirye shirye shiga sllhr magrib baffah yashiga anguwar su dake cikin garin jimetan parking yayi a 'kofar gidan nasu yara dake wasa a gefe suka taso a guje suna fad'in ga baffan zaria ga baffan zaria suna ihu suna murna da alamade suna farin ciki da zuwan baffan nasu, sau kowa yayi Yana ''cewa ku matsa gefe kar kuji ciwo, ina su yara Bata ciwo suke ba tuni wasu Sun ruga da gudu sunyi cikin gd suna sanar da zuwan baffan, safiyyah da yara suke Kira da baba yanzu ne ta fitoh daga d'akin dake a matsayin na dada hajara cikin nuna farin cikinta tace Masha ALLAH hammah ya iso kenan baba mari dake kwashe tuwon dare ne ta ta'be baki tana cewa kya tambayeni abunda ina nan kina nan yaran suka fad'a, baba safiyyah da yanzu tabar yin shiru ga duk Wanda ta tanka mata ko tashiga hanyanta don Zaman duniya ya karantar da'ita rashin d'aukan raini da cin kashin da ahalin nasu suke masu ita da d'an uwarta ''tace a'a ''yadikko'' ba dake nake ba harar 'kasan ido ta bita dashi tana fad'in kima yi danin ita bama tasan tanayi ba tuni tayi hanyar wajen dan gasgata maganan yaran, tana fitoh wa kuwa suka kusa buga karo dashi shi Yana shirin shigowa, ja'b'bama hammah, ''tace tana shirin amsar ledan fruits d'in da ya siya akan hanya, Bata yayi Yana mi ja'bi yaushe Kika zo nan d'in ''tace aeh hammah na kusa sati da zuwa, jinjina kai yayi yace madallah turo min da ruwa nayi sallah se na shigo ciki da toh ta amsa tana Shiga cikin gidan, bayan idar da sllhn isha'i ne ya shigo cikin gidan, shida su iro da jafaru baba da taji shigowar tasu tafitoh da sauri Yana shinfid'a masu dar duma a'kasan simintin tsakar gidan, zauna wa sukayi aka fara gaishe gaishe, kallon iroh baffaj yayi ''yace inaga ya kamata mu tafi asibitin yanzu ko, a'a hammah ga abinci nan an kawo Kaci ka huta se mu tafi, aa jafaru muje naga yanayin jikin baffah tukun, toh hamamah duka suka ce suna mi'kewa baba ta tashi ta d'auko girkin da tayi na 'yan asibiti jikinta sanye da hijjab tana fad'in hammah muje nima ku nake jira dama da toh ya amsa Yana shirin kar'ba mata kulan a'a hammah bashshi, kai da ka shawo hanya gashi ko hutu baka samu ba har yanzu, bece mata komeba shiga motarsa yayi suka d'au hanyar asibitin.....
Isar su asibiti ne hankalin baffan ya 'kara tashi duk hasashen da yake akan jikin baffan ya wuce nan domin baffan nasa Yana cikin wani mawuyacin hali, hankali tashe ya kai dubansa ga iro dake kusa dashi ''yace iro ya Haka ya zaku barshi acikin wan nan hali batare da wata kulawa ba iro ''yace hammah wan nan ma don addah safiyyah ta taimaka ne ammah da a gida ake ta jinyar sa ya 'ki yarda da a kaishi asibiti, su kuma hammah ashiru basuce kome akan hakan ba, girgiza kai kawai yayi, mlm nuhu da yake jin su ammah babu daman motsi bare magana , 'kura masa ido yayi hawaye nacika a idanunsa, sose hankalin baffan ya'kara tashi yace ya kamata muga likitan da yake kulada shi batare da wata matsala ba suka isa office d'in sa ya basu umurni suka fara tattauna wa akan laluran mlm nuhun, sose baffan ya girgiza jin ciwon 'barin jikine ya same baffansa, salati yafara tare da tasbihi ga sarkin da ya hallicci halittu dukansu, likita muna bu'katan samun sllm don canza ma baffa asibiti, ba tare da ja ko wani gardama ba likita ya amince don shima ya tabbatar halin da mlm nuhun yake yafi bu'katan kulawa fiye da waddah yake samu yanzu, canza ma mlm nuhu asibiti da akayi anfara ganin cigaba akan jikin nasa sose don yanzu karka cewar kan nasa ya fara daidaita bakaman daba, sose mlm yunusa da yazo shima ya jajanta lamarin jikin aboki kuma Aminin nasa, kwanansa biyu ya koma saboda yanayi na d'alibai, sose baffah ya kula da yaddah gidan nasu ya ke tafiya a yanzu don yaga kaman kowa RAYUWARSA yake, zaunar da iro da jafaru yayi ya tambayesu me nene matsalan, aeh kuwa batare da wata kwana kwana ba suka fara fad'amasa halin da ake ciki dama suma abun ya dad'e Yana damunsu ba yaddah za suyine saboda sude 'kana nah ne san nan ba wani abun hannu ne da suba sukuma manyan da yakamata su yi Sun koma gefe kowa kan sa da 'ya'yansa ya sani, sose ran baffan ya 'baci batare da ya Bari 'bacin ran nasa yafitoh fili ba, ''yace yanzu menene babban matsalan jafaru yace tunda mlm yakwanta ciwo gidan nan ba'a girki donde kowa in ya nemo d'akinsu yake kaiwa daga shi se dadarsa girgiza kai kawai baffah yayi ''yace toh Allah ya kyauta ameyn baba ''tace waddah ke zaune awajen kuma taji kome, fitoh da 'kud'i yayi yami'kama iro yace suje ayi cefane asiyo kome da yakamata a cigaba da girki kamar yaddah ake yi da a gidan, batare da 'bata lkci ba su iro sukaje suka siyo kome a ka kawo, sose suka nuna farin du duk da zamuce na ciki Na ciki, kwanan baffah shida a jimeta, yafara shirin koma wa gida zaria duk da ba wata damuwa kome yake wuce wa a Can d'in yanaji sose kamar Yana Can ma toh ammah wani abun dole se kana nan ana gani idon ka, ta 'barayin mlm nuhu kuma jiki yayi sau'ki sose, baffah ya tafi yi masa sallama don kama hanyan dawowa gida sose yanuna alhininsa a fuska, ri'ke hannun baffan nasa yayi Yana masa addu'ah dafatan samun lafiya, motsa hannun da yayi ne ya sa baffan d'aga ido da sauri Yana kallon mlmn d'in murmushi na sbuce masa baba dake kusa tana kallon komai ita ma farin ciki ya bayyana a fuskanta iro ne ''yace (Alhmdllh baffah jamo he'bama) Alhmdllh baffah ya samu lfy sose kowa dake wajen yayi murna , da gyar mlm nuhu ya saki hannun baffah har abun yayi ta basu mmk 'addu'ar samun lfy me d'orewa yakara ma baffan nasa san nan yafitoh duk jikinsa yayi sanyi, kallon su yayi yaga kowa yana tsaye suna kallonsa, se ya sakar masu murmushi ''yace yakama ta kudunga sanar min da yanayin jikin nasu, kar ku 'kara gangancin da kukayi abaya don lafiyarsa nada mahimmaci a garemu insha ALLAH sukace safiyyah yakira su iro sukayi gefe don barin sa yayi sllm da'ita don Sun san matsayinta a wajen sa, yakamata ki koma gd kema haka , kin bar yara su kad'e a gd duk da kina da abokiyar zama ammah kema yakamata ki koma, alabashshi ko bayan sati se ki rin'ka dawowa kina ganin yanayin jikin nashi, da toh ta amsa ya mi'kamata wani abu a d'aure a takarda wan da bansan ko menene ba, gdy ta yita masa da addu'o'i Yana amsawa ya fad'a mota su jafaru suka matso suma suna masa fatan sauka lfy, kama hanya yayi Yana me karanta addu'ahn hawa abin hawa, dede ya shigo cikin zaria dede d'an magaji Kiran mahmah ya shigo wayar sa d'auka yayi Yana fad'in na fasa se gobe zan taso mahmah dake ta Can 'batayin ta fara magana fuskanta na sauyawa ''tace yanzu baffah fad'i shine baka Kira ka sanarmin tun d'azu ba se yanzu ☹️ta 'karike magana tana me jin haushin maganan, dariya baffah yayi yace toh mai da wu'kan asiyen amadi Na kusa gida ma, dariya mahmah tayi ''tace toh aeh kaine duk mungama shirin tar banka zaka ce kafas be gama jin me zata ceba yaji wani 'kara 'kuuuuuu kafin ya gama sauraran wan nan 'kara yaji motar ta fara ju yamasa Gamm motar ya bugi wata mota dake kusa dasu juya wa motar tafara a tsakiyan titin nan, kafin mutane su fara tasowa dan Bada temako tuni baffah yafita a cikin hankalinshi salati yake tun farkon faruwar abun har lkcin da yafara jigata dagyar aka samu motar ta tsaya da gudu mutane na rige rigen fitoh da baffan don cecen rayuwar sa, dasuri wani waddah da alama aikin temako aikin sane cikin zafin nama ya ciro baffah da duk jikinsa ya sake sa sauri yake cela wani matashi ya kunnah machine d'insa sukai baffan asibiti, cikin rudani wani dattijo da tunda aka fitoh da baffan yake kallon Yana yinsa, ya girgiza kai yace kabiru wan nan bawan Allahn fa baya nunfashi da'alama rai yayi halinsa.......
Please COMMENT'S and SHARE in other geoup's ๐๐๐
๐๐BO'D'DO๐๐CE๐ง๐ง๐ง
0 comments:
Post a Comment