Hausa novels 2023

  • Home
  • Ciwon Idanuna
    • Internet
    • Market
    • Stock
  • Agola
    • Dvd
    • Games
    • Software
      • Office
  • Mijin Biza
    • Child Category 1
      • Sub Child Category 1
      • Sub Child Category 2
      • Sub Child Category 3
    • Child Category 2
    • Child Category 3
    • Child Category 4
  • Kwarata
  • Health
    • Childcare
    • Doctors
  • Inda Ranka

Monday, March 13, 2023

UMURNIN IYAYE Page 1 to 10

 March 13, 2023     UMURNIN IYAYE 1-END     No comments   

*I dedicate dix buk to a special frnd she's not only a frnd she's a sister to me luv yuh so vry mch*

 1⃣ ↗ 5⃣

Wata yarinya na hango akan royal bed dinta yar kimanin shekara 17
Laptop ne a gabanta me kirar apple ta sa headphone ga iphone 7 dinta me pink pauch ansa *AG* ma'ana *ARIANA GRANDE* tayi connecting da laptop din
Acan gefe kuma ga ipad dinta me pink jacket ansa *kylie jenner* a jiki

Sannan ga tv a kunne tasa *SCREAM QUEENS* duk da ba kallo takeyi bah
Daga ita se pink night gown a jikinta dede cinyanta da pink and white sucks a kafanta 

Hakeem ne keta knocking kofanta amma bata bude bah dan headphone ne a kunnanta ta kure wakan side to side na Ariana grande 
Da yaji shiru yasan waka takeji se ya shiga dakin mami ya dauko spare-key din dakin *Ameenah* ya bude kofan dakin yana shiga ya ganta kwance batama ganshi bah dan ta juyama kofan baya

Ya shiga a hankali ya dauke ipad dinta yasa hannu xe dauki iphone dinne se ta juyo tayi ihu danta tsorata shima yayi ihu se yayi waje agoje ta tashi ta bishi yayi hanyan parlo tana ta binshi tana kiran Abbah!! Abbah!!!

Abbah da Mami suna parlor
Abbah ya tashi ya tare hakeem ya kwantar dashi a kasa yace ma Ameenah meyafaru 

Da muryan shagwaba take magana tace
Abbah ina kwance a daki na kawai yazo yasatan min iphone dina 
Abbah yace bata abunta
Hakeem yace toh Abbah dagani in bata

Tace Abbah wlh karka dagashi ze gudu
Abbah na dagashi ya tashi aguje ya boye bayan mami yace wlh senayi deleting vedio kafin kiyi posting

Ta fashe da kuka tace Abbah kamai magana karyamin deleting

Mami tace wai vedio meye
Hakeem yace mami jiyane ina cikin dakina zanshiga toilet naga wani katon snake a toilet dina 

Ameenah tana dariya tace karyane barin baku labarin
Hakeem yace wlh idan kikayi magana zan sake wayamnan a kasa yanzin nan

Tayi shiru 
Abbah yace toh abamu mu kalla vedio 
Tace yawwa Abbah amsa ka gani
Hakeem yace ae na gane wayon 

Mami tace toh ni bani na kalla 
Yace amma se kinyi promising baza kiyi daruya bah and kina kalla zaki ban nayi deleting 
Tace toh
Yace no se kince i promise

Mami tace *I PROMISE*
Sannan ya bata 
Tana budewa Abbah ya matso shima ya kalla

Hakeem ne daga shi se towel yasa waka dakinshi yana bi ya bude toilet ze shiga yayi wanka yaga wani katon snake a kasan toilet din yayi ihu ya rungume kofan toilet din yanata ihu kaman mace kuma ya kasa motsawa daga wajan 
Se yaji muryan Ameenah tana dariya yana juyawa ya ganta da camera a hannu tanata dariya
[07:20, 05/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Mami tasa hannu a baki Hakeem yace Mami kince fa baza kiyi dariya bah
Abbah kam daya ringa dariya hadda hawaye itama Ameenah se dariya takeyi

Abun yaba hakeem haushi ya amsa iphone din yayi deleting 
Ameenah tace too late tayi hanyan daki a guje shima ya bita 
Tana zuwa tasa keyy a dakinta yanata buga kofan 

Haka ya hakura ya tafi yana shiga parlo yaga su Mami sunata dariya ya daure fuska ya tafi dakinshi yana shiga ya dauki wayanshi ya hau instagram se yaga Ameenah tayi sabon post yana budewa ae kuwa yaga vedio tayi posting
Se comment akeyi

Yace am gonna kill you



Mami da Abbah suna zaune a parlo Mami tace nifa wallahi bansan ta inda zan gayan ma Ameenah zancen nan bah
Abbah yace toh ki bari gobe se na kirata da daddare na gayan mata nasan baza tayi musu bah
Mami tace idan baka san ranta ya bace sosai kayi mata ordering designers din kylie su handbag da kayan kwalliya dade sauran su
Yace toh babu damuwa zan gayan ma assistant dina tayi

Mami tace yauwa hakan zefi sauki

Shi kam hakeem yana kan gado ya rasa mezeyi mata ta cire post dinda tayi sannan yana tunanin muguntan daze mata

Ameenah tana dakinta phone dinta yayi ringing ta duba taga Ameerah ce tayi murmushi ta daga suna cikin magana se taji muryan fatye a ciki ta mugun tsorata tace ke kuma daga ina 

Tace banza confrence call ne 
Tace awww 
Ameerah tace gobene fa zamuje gidansu maryam dazin amina ta kirani wai babban abokin ango ze zo se muyi maganan event dinda za'a 

A lokacin ne Ameerah ke gayan masu ta sama admission a nasarawa
Itama Ameenah ta sama a Abuja 
Fatye kuma ta sama a ABU 
Suka taya junan su murya sannan sukayi sallama
[08:28, 05/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Ta kunnaa karatun Qur'an sannan ta kashe wutan dakin tayi addu'a ta kwanta

Washe gari asuba nayi ta tashi tayi alwala sannan tayi brush tayi sallah ta 
Sannan ta dan karanta Qur'ani ta kuma gado ta cigaba da baccinta
Goma da rabi ta tashi tayi salati ta kunna heater toilet taje tayi wanka ta wanke gashinta ta daure da towel sannan ta fito ta hada drier tayi drying din gashinta tayi oiling sannan tayi stretching gashin tayi packing ta gefe ta zubo gashin a kirginta ta shafa mai sannan sannan tasa powder da eye pencil tasa maron lipstick

Ta shiga closet dinta tana budewa haka na sake bakina 
Kayane kala kala da takarma da handbags
Na tabbata hadda wanda bata taba sakawa bah

Kana shiga ga wani katon wajan takarma ban hawa hawa akayi su layin farko pink takalma ne dukka se na biyu purple na uka red na hudu black
Sega wajan handbags dinta gasunan kala-kala bazan iya maku bayani bah

Ga wani katin mirror nan a jefanshi akwai drower data bude na farkon yan kunne ne da sarkuna na buyu rist-watch ne kala kala na uku glasses (jikina ya fara rawa )
Ta kulle can kuma ta bude wajan kayan sawa dukkansu *GOD* ba'a magana shiru kawai
Dan dugayan riguna ne gaba daya babu atanfa babu wani riga da wando gasunan daban-daban ta ja daya daga ciki 

Ta bude wani karamin drawer inner wears ne a ciki
Can kuma ga wani karamin wadrop na tight ne da wist

Nace masha Allah

Tana fitowa da wani dogowan riga a jikinta red da black blet a jiki se black handbag da black veil ta daurashi ga kuma black takalmi amma flat

Tana fitowa sannnan karfe sha biyu yayi ta fito zuwa dinning ta sama Mami da Abbah se hakeem suna karyawa

Abbah yace my princess kinyi kyau fah tayi murmushi tayi mai peck shida Mami sannan ta gaidasu 
Ta gaida hakeem ya galla mata harara 
Tayi dariya dan tasan abunda ta mai

Mami tace ina zaki tace zamuje maganan bikin maryam ne 
Tace amma se kinyi break-fast koh tace wlh na kushi
Mami tace to ba inda zaki se kin karya
Ta farayi kaman zatayi kuka tace Abbah in tafi koh 
Yace na goya bayan Mami yau
Ta fara hawaye tace nifa slimming nakeyi
Hakeem ya bude baki yace me zakiyi ma slimming anan abu duk kashi

Ta harareshi ya mata gwalo kaman tayi hauka tace ji

Daddy yace ya isa haka kisha golden morn kawai se ki tafi 
Tace daddy akwai milk fa a ciki
Haka ya ringa lallamanta sannan tasha hakeem se gwalo yake mata tana gamawa ta tashi zata fita Mami tace driver ne fa ze kaiki
Tace Mami am 17 fah se na zauna driver yana tukani 
Abbah yace toh kina da drivers licence ne
Ta zumbura baki tace ba sunce baxa suyi min ba sena kai 18
Yace toh se kinkai 18 zaki fara fita da mota for now driver ya kaiki

Hakeem yace Abbah to ni na kaita mana 
Ta zara ido tace wlh ban yarda ba driver ze kaini
Mami tace yawwa tashi ka kaita 
Tace wlh na fisin driver nina fasa ma zuwan 
Hakeem yace haba little sis dina zo na kaiki mana 
Abbah yace kije ya kaiki mana 
Tace Abbah wurgar dani a daji zeyi fah 

Hakeem ya tashi yaja hannunta suka fita ita kuma se ihu takeyi wai ita driver xe kaita


*TYETYELORH'S NOVELX*✍🏻
[11:22, 06/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ *UMARNIN IYAYE*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Na tyetyelorh*

*NOTE:*
             *MUTANE DAYAWA SUNA MIN MAGANA TA PRIVATE WAI DANA BARI NA GAMA ZULAIHATOU KAFIN NA CIGABA DA UMARNIN IYAYE NI NACE ZANYI AND I KNOW I CAN DO IT AND FOR DOES DAT ARE PRAYING FOR ME THANKS SO MCH AND I LUV YOU ALL*😘

*LUV U SO MCH MUMMY KAMEELA*

0⃣5⃣ ↗ 1⃣0⃣

Suna shiga mota hakeem yace am gonna kill you
Ta fara kukarin bude motan 
Yace wlh karki ballamin door din mota na
Ya tada motan suka fara tafiya
Tace please ka bari sena dawo daga gidan su maryam sannan kamin duk abunda zakamin
Yayi murmushi yace ae idan na kaiki gidan frnd dinki na yafe maki ni yanxin ma gidansu Ahmed zani 
Ta fashe da kuka da kuka tace you are gonna regreat dix 

Hakeem yace if you jst apologize i might forgive you
Ta kalleshi tace ban taba ba mutum hakuri bah and am not gonna start from you
Yace we shall see

Can se fatye ta kirata tace mata gashi fa kowa ya hadu ita kadai ake jira ta fashe da kuka tace wannan mugun ya hana ni zuwa wai mun fito daga gida yace shi gisan frnd dinshi zashi
Hakeembya fuzga wayan ya kashe call din 
Tace give it back 

Yace idan kina da karfi ki kwata
Ta cire sit belt ta fara kukarun amsan wayan hannu daya kawai yasa ya tureta ta sake fashewa da wani kukan

Suna isa gidan gateman ya bude mai gate dayake yasanshi 
Suna shiga yayi packing ya fito itama tana kukarin fitowa ya zagaya ya bude kofanta ya fusga jakanta ya bude ya dauka ipad inta daman wayanta yana hannunshi ya wulla mata jakan 
  
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[18:00, 06/12/2016] Tyetyelorh-❣: Ya kulleta a cikin motan ya tafi abunshi se bubbuga window motan take amma dayake yasha teens 
Is very dark ba me jinta

Yana shiga cikin gida yaga mommy Ahmed yayi sallama ya tsoguna ya gaidata 
Ta amsa yace ina mutumin ne tace yana dakishi ya tashi xe shga dakin sega Ameerah ta fito daga kitchen da pancake a hannunta tasa earpice daga ita se three quater da wani top ansa *JB* a jiki

Hakeem yace dake da kawan naki halinku daya se son wanda basu san kunayi 
Tace wlh yaya hakeem sunsan munayi tunda ni nayi following justin bieber a instagram kuma yayi following dina back
Yace mistake de yayi besan ku bane 

Tace ina Ameenah yace tana cikin mota na kulleta 
Tayi dariya tace wlh ka iya fadan bakar magana yayi murmushi ya wuce
Yana shiga dakin yaga Ahmed ya baje akan gado yanata waya
Yana isa gunshi ya fusga wayan yayi eanding call din yace kasa yarinyan mutane ta fara sanka alhalin playing dinta kakeyi

Ahmed yace amma kasan wani abu wlh na fara sonta dan naga tanada hankali 
Yace kaide ka sani 

Suka kwashe awa daya da rabi suna hira sannan yace shi ze tafi ya bar mutum a mota
[18:24, 06/12/2016] Tyetyelorh-❣: Ahmed ya rike baki yace wa ka bari a mota na tsahun lokacin nan 
Ya tashi yace ina ruwanka ya kama hanyan fita yana zuwa parlo ya kira Ameerah yace mata tazo yana da present daya kawo mata yana mota tazo ya bata

Tace yeeyy yaya Hakeem shiyasa nake sanka wlh 
Suna fita ya bude motan yace ga present dinki 
Tana lekawa taga Ameenah ta gaji da kuka tace yaya hakeem daman da ita kazo shine ka barta a mota 
Ya bude motan ya shiga yace punishment na bata yaja motan ko sallama be masu bah
Suna tsaye suna kallonsu kawai Ahmed yace kai abokina mugune 

Ameerah tace ae nasan itama tana nan tana planing mai wani abu 

Suna cikin motan ku ufffn bata cemai bah ya fito da wayanta ya hau inatagram ya cire post dinda tayi sannan yahe gellery yayi deleting vedio ya wulla mata wayan 
Batace komai bah ta amsa tasa cikin jaka 
Tace Hakeem please ga wani store nan dan tsaya na saya ruwa 
Yace tab na tsaya ki gudo tace wlh ba haka bane kishi nakeji for how many hours ka barni a cikin motan nan please tsaya na saya 

Ya hango wani store ya tsaya ta shiga ze saya ruwa amma kuskuran da yayi se ya bar key din a jikin motan 
Ita daman abunda ta shirya kenan tasan baxe barta taje ta sayo bah

Yana fita ta dawo sit dinshi tasa sit belt ta fusga motan 
Shi kuma yana jin tashin mota ya juyo yaga ta tafi da motan yayi jifa da ruwan hannunshi yace fck
Ya tsayarda keke napep abunda be taba hawa ba kenan a rayuwanshi 
Ya tsayda ya hau
Ita kuma data fusga motan bata ko tsaya bah seda ta isa gida tana isa gateman ya bude mata gate ta shiga tayi packing ta fito
Tana shiga parlo taga su Mami a zaune 
Abbah yace princess ina Hakeem yake tace yana baya tayi shigewanta daki tasa keyy tahau gado yayi kukanta iya san ranta 

Can sega Hakeem ya shigo Abbah yace kaikuma ina ka tsaya
Yace i had something to take care of shima ya shiga dakinshi

Mami ta juyo ta kalla Abbah shima ya kalleta suka girgiza kai 
Maminta tashi yaje tayi knocking dakin Ameenah 
Ita kuma tana can tanata kuka tanajin anyi knocking tayi ajiyan zuciya ta gyara murya tace waye 
Mami tace nice idan kika yi sallah kizo Abbah nasan maki magana
Kawai setaji gabanta ya fadi batasan dalili bah
Tace toh
[16:38, 07/12/2016] Tyetyelorh-❣: [12:57, 07/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ *UMARNIN IYAYE*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Na tyetyelorh*

*IN DEDICATION TO A VERY SPECIAL FRND I WILL OLWAYS LUV YUH*😘

1⃣0⃣ ↗ 1⃣5⃣

Kawai setaji gabanta ya fadi batasan dalili bah 
Tace toh
Seda ta karasa kukanta sannan ta tashi taje ta sake wanka tayi sallah sannan ta dauko riga da wando ta sa ta zauna gaban mirror tayi kwalliya tayi lining idonta sosai dan kar a gane tayi kuka ta fesa turare sannan ta fito ta tarar da Abbah da Mami a parlo se hakeem 
Tana zuwa ta zauna ku kallon hakeem batayi bah tace Mami gani 
Abbah yace hakeem tashi ka tafi
Hakeem yace kai Abbah wlh zakasa yarinya nan ta rainani a gabanta kana kurana

Mami tace hakeem zo muje inada magana da kai ta tashi tayi dakinta shima ya mike se suka hada ido da ameenah yayi mata gwalo ita kuma ta murguda mai baki 
 
Yana tafiya Abbah ya miko mata wani jaka irin shopping bag dinnan amma na tagarda da murna ta amsa tana budewa taga wani designer bag na kylie a ciki ta fito dashi se tayi ihu tayi huging daddy tanata murna ta gwada se kuma tayi shiru ta kuma ta zauna tace daddy me kake so dan tasan idan ya mata irin wannan kyautan yana bukatar wani abu a gunta 
Yayi murmushi yace zauna tukunna tace yawwa aena sani.

Abbah yace ameenah gabanta ya sake fadi dan tunda take a rayuwanta Abbah ba taba kiranta ba sede yace princess dina koh baby nah
Taji wani ladabi yazo mata tace na'am Abbah

Yace mama na inason nayi wata magana dakene me mahimmanci ne kuma nasan bazan nema abu a gunki na rasa ba dan haka inason kiyi mana biyayya nida mahaifiyarki
Tace Abbah inajinka
Ya cigaba Ameenah na saman maki miji ina son.....
Kafin ya karasa tace Abbah miji Abbah are yuo serious miji fa kace Aurwn dole zaku min seta fashe da kuka
Abbah yayi mata wani irin tsawa da ku shi be taba tsammanin ya iya bah
Ameenah kam wani firgita tayi seta hadiya kukan 
Ya dawo kujeran da take kai ya zauna ya dafata yayi my princess am so srry kinji ta daga mai kai 

Sannan tace daddy na yarda dan nasan baza ku zaban min abunda ze cutar dani bah amma daddy plxz ka bari sena shiga 20 kafin kamin aure yace nanda 3yrs kenan fa 
Ta daga kai
[16:34, 07/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Yace Ameenah please kiyi hakuri kinji da muryanshi yana rawa ya ce idan kika yimin wannan abun i promise you zan kaiki kiga kylie da arian

Tace Abbah karka damu na amince kuma badan zaka kaini naga kylie bane yasa na amince saboda nasan duk abunda kuka zaban min baze cutar dani bah
Amma karka manta you promise zaka kaini naganta 
Ya daga hannu daya yana murmushi yace i promise tayi mai peck tace i luv you so mch yace i luv you my princess thank you so mch
Tace Abbah ka bar gode mun *THIS IS MY WAY FOR SAYING THANK YOU DA ABUNDA KUKA YI MANA A RAYUWAN MU NIDA HAKEEM DUKDA HE'S ANOYING SOMETIMES BUT I LUV YOU ALL SO MCH*

Daddy ya sake huging dinta se yaji ya kara sonta 
Harta tashi zata tafi se ta dawo tace Abbah waye mijin 
Abbah yace *ADEEL*

Tace *OMG* Abbah karkace min adeel dinda na sani 
Ya daga kanshi yace shi

Ta dawo ta durkusa tace Abbah dan Allah ka zaban min duk wanda kake so amma banda Adeel wlh Abbah yanada girman kan tsiya gashi bamu taba magana dashi bah
Abbah ya share mata hawaye yace amma ba yanxin kika yarda ba 
Tace Abba na yarda amma Abbah dan Allah ka changer wlh bansan Adeel he is irritating 

Abbah yace kiyi hakuri kinji insha Allah zaku zauna lafiya dashi
Tace toh shi kenan Abbah ta mike se kuma tace amma Abbah shi yace yana sona 
Abbah yace *GOD* wlh kina da matsala

Ta fara shagwaba tace kai Abbah ae ya kamata na sani yace toh jeki zaki sani 
Tace amma Abbah you promise zaka kaini na ganta yace i promise tayi tsalle seta tafi

*ASALINSU*

Alhaji siraj asalinshi mutumin kano ne babban dan kasuwa ne tun suna yara Allah ya hada jininsu da Alhaji Musa kuma abunda ya fara hada su shine fada suna makaranta su kullun cikin fada suke kullum danbe 
Shine ranan nan iyayen su suka hada plan su kullesu a daki harse sun gaji da dambe
Haka kuwa akayi duk suna cikin bacci aka kinkimu su aka ajiye su a dakin suna tashi suka gansu tare suka ringa fada gashi babu me raba su sukayi2 har suka gaji suka hakura kuwa yana haki
Shine sukayi dabara suka fito daga dakin tundaga ranan suka fara shiri har suka girma kansu a tare 
A rana daya ma aka daura masu aure shi Alhaji siraj sunan matanshi khadija while Alhaji musa sunan matanshi fatyemah
A rana daya suka haihu duk suna haifa maza dan Alhaji siraj aka sa mashi hakeem while dan Alhaji musa aka sa mashi *Adeel* 
Bayan shekaru 5 Allah ya kara ma Alhaji yarinya kyakkyawa san kuwa kin wanda ya rasa aka sa mata *AMEENAH* sunan mahaifiyar Alhaji siraj kenan suna ji da ita amma su kullum suna cikin fada da hakeem dan shi ya iya neman ita kuma baza ka mata ta bari a kwana bah dukda tanada kamin kai batasan hayaniya kuma gata butty tanaji da weight dinta kwata2 bata cin abu me nauyi dan a ganinta mutum me kiba loser ne πŸ˜‚

Bayan watanni bakwai da haihuwanta matan Alhaji musa itama ta haihu aka sa mata safieyarh sunan mahaifiyar Alhaji musa kenan 

Haka rayuwa ta ringa tafiya Allah ya hada kan hakeem da *Adeel*
Se *Ameenah* da safieyarh gaba dayansu suna shiri suna son junansu amma ita Ameenah ta tsana adeel dan yanada dan banxan girman kai itama tana da nata wanda ma yafi nashi toh shiyasa ta cireshi ta ajiye a gefe guda 

*BCK TO OUR STORY*
[17:07, 07/12/2016] Tyetyelorh-❣: Sanda mami taja hakeem zuwa daki ta bashi labarin hadin da suke son shiyi yayi dariya yace ashe akwai showw zamuga abu
Mami ta bejeshi tace Insha Allah zasu baka kunya 

Mami ta fito taje gun Abbah ta tambayeshi ya akayi yace ta yarda amma da kyar ya bata labarin su uku tana dawowa tace bata yarda bah
Mami tace ae nasan za'a runa amma Alhamdulillah tunda ta yarda semu kira Alhaji musa mu fadan masu tunda sunce shi adeel din ya yarda se asa rana kawai
Abbah yace hakan za'ayi 

*TYETYELORH'S NOVELX*
[08:35, 08/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ *UMARNIN IYAYE*πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*Na tyetyelorh*

*IN DEDICATION TO A VRY SPECIAL FRND LUV YUH SO MCH*😘

1⃣5⃣ ↗ 2⃣0⃣

*GIDAN SU ADEEL*

Adeel ne dunkushe a gaban iyayenshi 
Daddy yace toh Adeel kai muke jira kasa ranan da za'ayi daurin aure
Adeel yace daddy kawai kasa ranan da kanka
Daddy yace toh shikenan Allah yama albarka yace ameen
Yanxin ka fara hada kayan akwati nan da one month za'a daura aure 
Adeel yayi sauri ya daga kai yace haba daddy kaman kun gaji da ganina ne a gidan

Mommy tace ba dole mu gaji da ganin ka ba ta cigaba yau da yamma ina son kaje gunta 
Zeyi magana kenan ta dakatar dashi tace ba alfarma nake nema ba umarni nake bah

Yace toh shikenan insha Allah zanje amma mommy kinsan yarinyan da girman kai ku gaidani fa batayi idan tazo gidan nan
Mommy tace wannnan kuma ba ruwana bane
A cikin satin nan daddyn ku xekai gaisuwa sannan akai sadaki kai kuma kaje ka hadu akwati a dubai

Yace shikenan Insha Allah zanbi umarnin ku Allah sa shine mafi alkairi
Daddy yace ameen Allah ma albarka 
Yace ameen ya tashi ya tafi dakinshi
Yace zanje gidansu amma wlh yarinya ta kawo min raini zan zubar mata da hakuri

Ashe safieyarh tana jinshi tazo dakinshi neman headphone dinta dan tasan shine ze dauke mata danshi kwata2 besan yajita tana jin waka 
Tace lalala yaya Adeel Ameenah zaka fasa ma baki chabb wlh zaku fasa ma juna baki 
Ya juyo yace dan uwarki me kikeyi a nan 
Tace haba yayana yau ni kuma kake zagi

Yace srry little sis Wlh yau gabadaya haushi nakeji ta matso kusa dashi tace yaya idan de saboda auren Ameenah da su daddy suka ce se kayi wlh karka samu damuwa idan kuka saba da ita wlh tana da saukin kai tana da kirki

Adeel yace shikenan yanxin me kika zo yi
Tace yaya Adeel plxx headphone dina zaka bani yanxin nayi downloading sabon track inason naji ne 
Yace idande headphone dinki ne toh banzan bada bah
Nxt ma wayan zan dauke gaba daya bansan ma meyasa ake baku manyan phone bah tun kuna yara
Tace yara 3 month fa ya rage na shiga 17
Tace yauwa yaya Adeel plxx idan zaka je gidansu Ameenah zan raka ka
Yace ki bari se wata rana se muje tare
Ya tashi ya bude wani drawer ya dauko twist ya mika mata 
Ta ringa jin dadi ta tashi taje gun mommy
[13:15, 08/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
Bayan magrib Amrenah tana kan gado tanata tunani abunda bata tabayi ba a rayuwanta 
Se Mami ta shigo bata yi mata magana ba ta shiga closet dinta ta dauko mata wani dogowan riga tace mata tasa Adeel yana hanya 

Ameenah ta fashe da kuka Mami tazo ta rungumeta tace mata Ameenah kiyi hakuri please ki bar kuka Insha Allah wannan auren alkairi ne tunda har *UMARNIN IYAYE* zaku bi

Ameenah tace Mami wai yaushe ne bikin tace nanda one month 
Ameenah tace dan Allah ku bari na na shiga university tukun na kafin kuyi min aure wlh idan na gama nayi maku alkawari zan zauna da duk wanda kuke so

Mami tace yanxin de tashi ki sirya yana hanya ta ajiye mata rigan ta fita hawaye a cike a idonta se suka ci karo da Hakeem ashe yana labe yana sauraran su
Ya kalleta yace Mami kuka kikeyi 
Yace yanxin nan wani kwaro ya shigan min ido 
Yace toh tsaya na hura maki 
Tace banso ta wuce 
Yayi murmushi dan yasan kuka takeson yi ita kuka be mata wuya 

Ya sake leka dakin ya hango Ameenah ta dauko rigan zata je tasa yayi wani murmushin mugunta ya tafi dakinshi ya dauko wani karamin bucket din penty yazo kufan dakin Ameenah ya leka be ganta bah yasan tana closet dinta
Se ya dan bude kufan dakin kaman half se ya ajiye bucket din akai inda ana sake jan kufan ze kifo ma mutum yaji motsin bude kofn closet din seya gudu

Data fito tayi kyau sosai ta dauko wani silk ta daura batayi wani kwalliya bah tasaka chapet da eye-pencil a ido ta feshe jikinta da turare se taji wayanta yana ringing tana dubawa taga Mami ta dauka Mami tace mata ta sauko kasa tace toh
Tana bude kofanta ta fito se taji wani abu ya zubu mata a kai ta kulle idonta tace *HAKEEM* da karfi shi dama yana zaune a dakinshi yana jiran yaji ihunta ae kam yana ji ya dauka keyy din motanshi yabi ta kofan baya yashiga mota ya tafi yawonshi se dariya yake mata
[17:08, 08/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Ita kuma Ameenah kuka ta fara tanata kwallama Mamai kira 

Mami tana zuwa ta ganta a cikin penty tace meyafaru haka 
Cikin kuka tace Mami Hakeem ne mana 
Mami tace Hakeem dinda ya fita tin dazin ta dauke waya tayi dailing number shi
Yana cikin mota yaga number mami yayi murmushin mugunta 
Ya daga yace hello Mami tace kana inane yanxin yace ina gidan frnd dina ba tun dazin na gayan maki zan fita bah yace Mami meya faru
Tace babu komai tayi ending call din 
Mami tace toh idan bashi bane waye yanxin a bar mgn nan Adeel fa yana can parlo yana jiranki
Tace Mami kawai kice mai banda lafiya tace noh yanxin je ki sake wani wankan
Ta kuma daki tanata kunkuni a zuciyanta kuma tanata shirya abunda zata ma Hakeem dan ta san shine 

Ta shiga toilet ta sake ma kanta shower bayan ta gama fitar da pent din a gashinta tayi wanka ta fito tayi drying gashinta ta shafa man ta sake dauko wani duguwan rigan ta saka sannan ta fito zata bude kofan kenan se kuma ta kuma baya ta samo dugan abu ta tura kofan taga ba abunda ya fado se ta fito.

Adeel yana zaune a parlo baki shida Abbah se aka kirashi a waya ze fito yayi answering call din kenan ita kuma zata shiga parlon se sukayi karo dayake be riga ya daga labulen ba
Ita ta aza Hakeem ne se ta kaimai ciro a hannu 

Adeel yace auch
[17:18, 08/12/2016] Tyetyelorh-❣: Ya daga labulan yaga waye ya cijeshi
Kawai se yaga Ameenah har call din ya tsinke be daga bah


Ita kuma data ga Adeel ne tayi baya tace ewwww kai na taba *OMG* se tayi sama da gudo 

Shi kuma yana tsaye kawai yana kallonta se ya girgiza kai ya shiga parlo yace ma Abbah ze tafi sun hadu da Ameenah Abbah yace toh shikenan Allah yayi maku albarka yace Ameen ya bari yaje yama Mami sallama ya fito daga parlo sega Mami ya dan rage tsayi yace Mata ze tafi
Tace har Ameenah tazo
Yace a tazo mun gaisa tace toh shikenan ka gaida mutan gidan Allah maku albarka 
Yace Ameen ya tashi ya tafi


*TYETYELORH'S NOVELX*✍🏻
[12:27, 13/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹ UMARNIN IYAYEπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

WRITTEN BY:
        TYETYELORH

EDITED BY:
       AMEENATOU


IN DEDICATION TO A VRY SPECIAL LUVING CARING SISTER AND SHE'S ALSO A BST FRND TO ME LUV YUH SO VRY MCH HAWWATIEE HAPPY ANNIVERSIRY😘

2⃣0⃣ ↗ 2⃣5⃣

Ita kuma Ameenah data shiga daki ta cire veil din kanta ta shiga toilet a guje ta dauki brush ta ringa brush kaman zata cire hakuri

Shi kuma hakeem bayan ya gama yawonshi ya dawo gida shi gaba daya ya manta muguntan da yayi ma Ameenah ya tafi dakinta stregth 
Ji kake suuuuuuuuuuuuu
Hakeem ya zamule akan pent dinda ya rubama Ameenah timm ya fadi 
Ya juya yaga bame kallonshi ya mike rike da kugunshi ya sauko kasa se suka ci karo da Mami yacr Mami kinga abunda Ameenah tayi min koh toh wlh nima sena rama ya tafi dakinshi 
Mami ta kalleshi tace toh waya zuba pentin nan

WASHE GARI

MISALIN KARFE 3:00PM
 
Magaba tan Adeel suka zo suka kawo kayan gaisuwan Ameenah ita bata ma san anayi bah dan tana dakinta tasa key tasa waka se tikan rawa 

Adeel

Matashi ne me jini a jika irin namijin nan ne masu jijiyoyi a jiki amma ba irin sosai dinnan ba koma ga gashi ta ku ina a jikinshi yana da saje amma ba sosai bah sannan yana da packs 
Shi packs dinshi is natural tun yana yaro yake dashi
Be murmushi kwata kwata haka yake tun yana yaro shi bameson hayaniya bane da mutum daya yake hira amma ba sosai bah da safieyarh

Shi Hakeem mutum ne me saurin sabo amma wani sain yanada girman kai kuma ga surutu da tsokana idan yaje gidansu adeel da safieyarh suke hira sosai idan kingan shida Adeel suna hira toh Hakeem ne me surutun 
Shi kawai aikinshi ya daga mai kai ku murmushi

Kuma duk abunda yakeyi duk sonda yake ma abun nan iyayen shi suna hana shi ze bari
Shiyasa da suka ce ya aure Ameenah beyi masu musu bah
Dukda ya mugun tsanan Ameenah sabuda iyayinta ga dan banzan girman kai ga kaudi (A ganinshi)



Mimi ta je dakin Ameenah taji kida na tashi ta taba kofan taji shi akulle tayita knocking amma bata bude bah dan bata jinta 

Seta koma dakinta ta shirya 
Dama zasuje da Ameenah ta sayo mata kayan da zata sa idan danjin Adeel sunzo ganinta

Ta sirya taje ta sake knocking kofan amma still bata bude ba dan haka kawai seta sauka kasa ta kira driver yazo ya kaita
[12:39, 13/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Taje wani shopping mool ta sayo mata wani duguwan riga dan ta san idan ba duguwan riga ta sayo mata bah toh bazata sa bah
Rigan maroon ne da stone work a gabanta ta biya kudin sannan ta dawo gida 
Data dawo ta tafi dakin Ameenah ta ganshi a bude
Taga Ameenah akan gado daga ita se wani top zuwa cinyanta da plate a hannunta 
Cucumber ne a ciki an yanka shi kanan tana ci da fork a gefe kuma glass cup ne da water melon a ciki anyi blending dinshi

Mami ta shigo tace wai ke bazaki ringa cin abincin kirki bah a rayuwanki
Da muryan shagwaba tace Mami yanxin wannan ba abinci bane

Mami ta zauna bakin gadon tace yanxin wannan a grinku abinci na ta zumbura baki

Mami ta mika mata bag din tace gashi 
Tayi saurin ajiye plate din a gefe ta amsa tana bude wa 
Tace OMG Mami thank you kin iya zaban kaya tayi hugging dinta 
Tace ba kaman Abbah ba
Mami tace lalala aekam sena fadan mai

Ta rike baki tace seriously bansan sanda ya fito bah
Mami tayi murmushi ta tashi har zata fita se ta dawo tace ma Ameenah gobe da yamma Mommy Adeel zata zo da yamma seta fita

Ameenah tayi wurgi da kayan tace daman na sani akwai wani abu a kasa 
Wai dan Allah ni zan aura wannan yaron shi kwata kwata be dariya ga dan banan girman kai bala'i ni wlh da badan Abbah yace ze kaini ganin kylie ba da bazan aureshi bah
Tayi shiru can kuma ta dauki wayanta ta hada confrence call da bst frnds dinta Ameerah da fatye tace masu su kunna laptop dinsu zata hada masu video call

Ta dauko system dinta ta hada tana kallon fuskansu se kuma ta fashe da kuka
[19:58, 13/12/2016] Tyetyelorh-❣: Duk suka rude dan suna ji da ita saboda itace karama a cikinsu

Ameerah tace Meenah meyafaru plxx stop crying and tell us ku zamu iya baki shawara

Sukayi sukayi tayi shiru ra fadan masu abunda ya faru taki
Can se fatye itama ta fashe da kuka itama Ameerah ta kama suka ringa kuka mara dalili 
Bayan kaman minti goma Ameenah ta share hawaye tace meya saku kuka 
Ameerah tace ke mana tun dazin kinki magana se kuka kikeyi 
Ta kwashr komai ta gayan masu gameda gada aurensu tana magana tana kuka 

Ameerah taja wani tsaki abunda yasaki kuka kenan muma muka biye maki
Daman a cikinsu itace me basu shawara saboda duk ta girme su
Ta cigaba ni na aza yaya hakeem nema wlh amma kin ban haushi

Ameenah ta sake fashewa da kuka
Hakeem yazo wucewa se yaji kukanta se ya leko dakin ya hangota kan gado da laptop a gabanta 
Ya karaso yace little sis meyafaru kike kuka ta juyo ta dauki pillo ta wulla ma tana kuka tana cewa ka fitan min daga daki
Ya kama pillo ya karaso gunta yace habah little sis****
Be karasa magana bah yaji muryan fatye tana cewa yaya hakeem ya leka jikin laptop din se ya hangosu su biyu
Yace dama tare kuke kukan mstewww wlh harkun ban haushi kadde ace saboda auren ne kuke kuka

Ameenah tace get out from my room 
Yayi kaman be jita bah 
Se kuma ta sake fashewa da kuka tace hakeem dan Allah ka tashi ka tafi
Yace bazan fa fita na barki kina kuka bah besan sanda ya furta kalman nan bah

Fatye tace awwwwn 😊 beson yaga little sister shi na kuka 
Ya juya ya kalla laptop din yace wlh sena jefeki 
Yace she will call you guyx later 
Be jira sunyi magana bah ya kulle laptop din
[20:11, 13/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Ya juya ya kalla Ameenah yace habah Ameenah ki dena kuka muyi magana 
Tace maganan me zamuyi yace share hawayanki first
Ya cira toilet paper ya mika mata ta amsa 
Bayan ta gama share hawayen yace yanzin gayan min kina son auren ku baki so

Tace ni banso yace toh shikenan meyasa bakison ki aureshi

Tace shiya cika gigi da kai ga miskilanci and his not my type ni ban taba imaging mijina haka bah

Hakeem yace ba gi da kai bane shi be cika haya niya bah sannan idan kika saba dashi beda matsala 
Tace taya ka sani yace saboda na saba dashi
Ameenah tace wani sabo idan fa kuna zaune kaine me surutun shi kawai kallonka yakeyi

Hakeem ya susa keya yace toh naji
Amma ki dena kuka akan abun nan kinsan iyayanki ne suka zaba maki shi kuma i promise you zaki ji dadin zama dashi
So plzzz ki dena kuka bansan inganki kina kuka 
Ta rike baki tace da gaske hakeem ne a gabana shi yake cewa beson kuka na 

Ya dauki pillo ya jefeta dashi yace toh karya nakeyi ya fita daga dakin
Tana murmushi tace I LUV YOU BRO
Ya dawo yace me kika ce 
Tace ina ruwanka fitan min daga daki
Yayi murmushi ya fita seda yayi nisa sannan yace I LUV YOU TOO







TYETYELORH'S NOVELX
[20:34, 15/12/2016] Tyetyelorh-❣: πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹UMARNIN IYAYEπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

WITTEN BY:
                   TYETYELORH
EDITED BY:
                   AMEENATOU

IN DEDICATION TO A SPECIAL AND LUVING PERSON LUV YUH

2⃣5⃣ ↗ 3⃣0⃣

WASHE GARI

Misalin karfe bakwai na yamma Mami tasa Ameenah a gaba wai seta shirya 
Ita kuma se zumbure2 takeyi
Bayan ta shirya tasa babban veil tasa powder da maroon lipstick sannan tasa eye liner ta feshe jikinta da turare 
Tayi masifan kyau

Mami tace princess din Abbah tayi kyau fa 
Ta hada fuska
Mami tayi murmushi tace barinje na dawo 
Tana sauka ta tarar da mommy da wasu mata suna zaune a parlor ta shiga ta zauna suka gaisa sosai sannan ta tashi ta dauko masu drinks snacks da kuma ruwa ta kawo masu ta ajiye 
Ta dan zauna sukayi dan hira irin tasu na manyan mata 
Sannan ta mike ta tafi dakin Ameenah ta sameta a zaune da wayanta a hannu tanata selfie 
Tace toh uwar selfie taso muje
Tace Mami dan tsaya na kara wani
Ta fuzge wayan tayi wurgi dashi kan gadon tace idan kin dawo kya cigaba
Ameenah ta rike baki tace Mami zaki tarwatsamin wayan 
Mami taja hannunta ita kuma se surutai takeyi wai Mami idan kika kashewayan nan kin kasheni 
Suna isa bakin kofan parlon Mami ta tsaya tace ina shiga ki rusuna ki gaidasu

Tayi murmushi tace yau kuma hadda gaisuwa zaki koya min Mami kaman karamar yarinya
Ta dungure mata kai da dan yatsanta ta shiga 
Ita kuma tayi murmushi ta girgiza kai sannan ta shiga da sallama cikin nutsuwa

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Duk suka amsa mommy adeel ta kanta ta mike ta kamo ta suka shigo tare tace zauna kusa dani diyata 
Amma Ameenah taki ta zauna a kasa 
Tace noh diyata tashi ki zauna kusa dani
Ta dukar da kanta kasa taki tashi 
Ta gaidasu cikin girmamawa suka amsa 

Ita kuwa Mami dadi ya isheta se jin dadi takeyi a zuciyanta abunda Ameenah tayi 

Ameenah tana zaune a kasa duk ta kusa ta tashi ta tafi dakinta dan maranta wani ciwo yake mata
Idonta ya cika da hawaye dan azaba

Ta dago ta kalla Mami tace Mami barin shiga daki cikina yana ciwo 
Tace toh shikenan 
Mommy tace Allah kara sauki 
Tace Ameen ta mike ta futa 
Da kyar take tafiya tana rike da maranta 

Mami tace toh Allah sa ba maran bane
Mommy tace ameen sukace toh su zasu tafi Allah kara sauki suka tashi suka tafi Mami ta rakasu suka shiga mota suka tafi

Da sauri ta kuma ciki dakin Ameenah ta wuce direct tana shiga taganta akan gado tanata juyi hannunta a mari ta shigo a rude ta riketa tace maran ne 
Ta daga mata kai
Tace toh barin kira Hakeem ya kaimu hospital
Mami na fita Ameenah ta mike daga kan gadon ta wani kwalla kara seta zube a kasa 
Ta dawo a guje ta ganta akasa ta riketa ta dauka waya ta kira Hakeem tace kazo ga Ameenah ba lafiya 
Nan da nan se gashi a guje ya kinki meta yayi waje da ita Mami ta biyo shi ko mayafi babu 
Yana zuwa zun mota ya bude yasata a baya ya juya ya kalla Mami
Yace Mami mayafi fa
Sannan ne ta tuna babu mayafi a jikinta seta kuma ta sako

Tana fitowa suka kama hanyan dialogue

Idan de da sabuwa akan ciwon Ameenah toh sun riga sun saba dan duk wata se an kara mata ruwa likita ya basu shawara ayi mata aure kawai
Harse an mata aure ciwon ze bari


Suna isa aka amsheta dayake sun riga sun saba kawai allora akayi mata sannan aka kara mata ruwa bayan 2hour ta farfadu
Tana tashe taga karin ruwa a hannunta tace an runa 
Mami ta juyo ta kalleta tace me aka runa 
Tace karin ruwa mana tayi murmushi tace ae ya kusan zuwa karshe

Tace me kika ce Mami tace noh bada ke nake bah ta tsaho zuwa bakin gadon tace ya jikin
Ameenah tace nifa na warke kawai a sallame ni dan wlh na tsana kanciyan asibiti

Tace an ma sallame mu dama jira ake ruwa ya kare se mu tafi gida 
Bayan yan mintuna ruwa ya karw sega Hakeem ya shigo yana dariyan mugunta yace Mami daman a barta a kara mata leda 20 ku zata kara kiba

Tace ae daman baka sona su kake na muto
Mami tace ae dakinga inda ya rude da kika su.........................
Bata karasa bah ya tushe mata baki yace tunda an sallame ta mu wuce kawai ku
Tayi murmushi tace toh 
Ameenah ta mike suka fito suka kama hanyan gida
[20:56, 15/12/2016] Tyetyelorh-❣: Suna isa suka tarar Abbah ya dawo yace daga ina kuke
Ameenah tayi huging dinshi tamai sannu da zuwa shima hakeem yayi mai sannu da zuwa ya amsa
Suka wuce daki
Mami ta kalla Abbah tace kasan wata yaxo daga asibiti muke 

Abbah yace ohh ni wannan ciwon
Mami tace ae insha Allah yaxo karshe 
Yace Allah sa tace ameen 
Ta kawo mashi abinci bayan yaci sukayi dan hira sannan tace bari taje dakin Ameenah shi kuma ya wuce dakinshi

Ita kuma Ameenah tana shiga dakinta tayi wanka tasa pad sannan tasa kayan bacci ta hau kan gado ta dauka ipad dinta tana kallon wani waka da ariana grande tayi a miami a stage

Mami ta shigo da plate a hannunta ta yanyanka kankana ta kawo mata
Da murna ta amsa tana ci se tace mata tanason ta bata number Ameerah da Fatye
Tace Mami me zakiyi dashi
Tace ina ruwanki kawi ki bani
Tayi tayi da ita ta bata amma taki bata
Seda tayi mata alkawarin abu sannan ta bata 
Tana amsa tayi mata seda safe sannan ta fita

Ita Ameenah se mamaki takeyi ko me Mami zatayi da number su

Mami tana fita parlor ta kira su tace gobe suzo su amsa kayan bridesmate dinda zasusa da bikin suka ce toh


WASHE GARI
 
Da sassafe taje kasuwa ta sayo masu wani pink cut-less me tsada kuwa yadi hudu da net da zasusa a kasan gown din sannan ta sayo masu golden head su hudu


Tana dawowa ta tarar da safieyarh sister adeel sannan safieyarh sister Ahmed sannan Ameerah da Fatye bst frndz dinta
Ta gansu a parlor da Ameenah ita duk mamaki takeyi 

Tana shigowa duk suka gaisheta safieyah ta amsa kayan hannunta 
Data zauna Ameerah sister Ahmed ta kawo mata ruwa me sanyi 
Tayi murmushi ta amsa 
Bayan tasha ta fito da kayan ta mika ma kowa nashi ta gayan masu tana san kuwa yayi style iri daya dan tasan Ameenah baza ta taba maganan bikin ba duk sukayi dariya
Sukayi mata godiya sosai
Ameenah ta hada fuska tana ta gunguni 
Mami ta tashi ta hau sama 
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Share this

WhatsApp
Email ThisBlogThis!Share to TwitterShare to Facebook
Newer Post Older Post Home

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts

  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 11 to 20
    Tunda aka bud'e mana muka fito hadimansa sukayo caa akan mu, kowanne k'ok'arin nuna farincikin sa yake ga Galadima.     Casuke A...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 31 to 40
    Na dad'e ina barci kafin Na tashi, nayi mamakin ganina ni kad'ai, bansan time d'in da Galadima ya ficeba, sakkowa nayi daga gado...
  • RAINA KAMA Book 1 Page 1 to 10
    RAINA KAMA......!!♦_*                _{Kaga gayya}_          *_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_* *_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._* πŸ‘‰πŸ»1⃣      *Matsanan ...
  • RAINA KAMA BOOK 2 Page 21 to 30
    Yanda ya rik'e hannun yasani fad'in “please yalla6ai akwai zafi fa”.         Sassauta rik'on yayi, ya sauke ajiyar zuciya, murya...
  • BARIKI AUREN SOJA Page 51 to 60
    Motocine guda shida aka ajiye musu sababbi dal suna sheki ta tsakiyar tasha Adon balloon kana gani Kasan motar AMARYA ce ta fito tareda su ...
  • KASUWANCI NA Page 61 to 70
    Ameer kasa jurewa yayi gaba daya jikinsa ya fara rawa,tunawa Meenat tayi ba Muharraminta bane sai ta dan matsa kamar zata fada kasa ta wayan...
  • KASUWANCI NA Page 31 to 40
       A kunyace na Zauna a daya daga cikin kujerun palon nima sannan nace Ina yini kazo lfy,cike da fara'a ya amsa lafiya Alhmdllh Madam, d...
  • UMURNIN IYAYE Page 51 to 60
    Suna isa asibitin emergency ward aka shiga dashi  Wani kujera suka zauna akai Hakeem yana shafa bayan Mami a hanakali yana bata hakuri shim...
  • UMMU AYMANA Part 6
      *UMMU AYMANA PART 6* Suna isa Asibitin likitoci suka rufu akanta,wanda da taimakon Allah bata jimaba ta farfaΙ—o se kuka takeyi,prince kasa...
  • MACIJINE SHI Page 31 to 40
    _________________Kai tsaye part Γ‰—in nanny Adeeb ya nufa da fattu,suna zuwa kuwa nanny ta gyara ko ina sai Γ†™amshi ke tashi,dakin fattu suka...

Categories

  • 'YA'YA DA KUDI 1-END (8)
  • 'YA'YA MATA 1-END (9)
  • 'YAR BOKO 1-END (6)
  • 'YAR FULANI 1-END (14)
  • 'YAR GIDAN TSOHUWA 1-END (6)
  • 'YAR JAMI'A (9)
  • 'YAR MAFIYA 1-END (6)
  • 'YAR TALAKAWA 1-END (7)
  • AGOLA 1-END (17)
  • AKIDATA BOOK 2 Page 45 -End (11)
  • ANAL 1-END (12)
  • ANTIN YARA 1-END (6)
  • AUREN JARI 1-END (9)
  • BAKAR MACE 1-END (3)
  • BARIKI AUREN SOJA 1-End (8)
  • BINTU 1-END (7)
  • CIN AMANA KO FANSA 1-END (10)
  • CIWON IDANUNA 1-END (7)
  • CIWON IDANUNA AUDIO (2)
  • DAGA TAIMAKO 1-END (5)
  • DAKON SO 1-END (4)
  • DAMA TA BIYU 1-END (13)
  • DR BOBBY 1-END (11)
  • DUBU CIKAR MAI CARBI 1-END (7)
  • FULANI 1-END (11)
  • GURBIN IDO 1-END (1)
  • HADIN ALLAH 1-END (8)
  • HIBBAH 1-END (4)
  • INA ZAN GANSHI 1-END (7)
  • INAYA 1-END (9)
  • JIDDARTIL KHAIR 1-End (1)
  • JIHADI 1-END (10)
  • JUWAIRIYYA 1-END (7)
  • JUYAYI PAGE 1-END (6)
  • KASUWANCI NA Page 1-End (1)
  • MACIJINE SHI 1-END (1)
  • MAH NOOR 1-END (5)
  • MAIMOON 1-END (10)
  • MAKARANTAR KWANA 1-END (5)
  • MAKAUNIYAR KADDARA 1-END (10)
  • MATAR ALI 1-END (10)
  • MIWASMITI 1-END (8)
  • MOTAR KWADAYI 1-END (4)
  • NAMIJI BAYA KADAN 1-END (16)
  • NI AYS NAKE SO 1-END (16)
  • RAINA KAMA 1-END (1)
  • RAYUWATA 1-END (6)
  • SHIMFIDAR MIJINA 1-END (3)
  • SONE AJALINA 1-END (5)
  • SURBAJO 1-END (14)
  • TUDUN DAFAWA 1-END (4)
  • TUZURU 1-END (6)
  • UMAR KO FARUUQ 1-END (5)
  • UMMU AYMANA 1-END (8)
  • UMURNIN IYAYE 1-END (7)
  • WAMINAL HOOB 1-END (9)
  • YAN MATAN ZAMANI 1-END (6)
  • ZAYN MALIK 1-END (10)
  • ZUCIYA KOWA DA IRIN TASA 1 (10)
  • ZUMA SAI DA WUTA PAGE 1-END (7)

Social Plugin

  • facebook
  • twitter
  • instagram
  • youtube

Hausa novels 2023

Search This Blog

Powered by Blogger.

Blog Archive

  • July 2023 (7)
  • June 2023 (65)
  • April 2023 (33)
  • March 2023 (132)
  • January 2020 (10)
  • December 2017 (62)
  • November 2017 (33)
  • October 2017 (38)
  • September 2017 (39)
  • August 2017 (75)

Report Abuse

Total Pageviews

Copyright © 2023 To Hausa novels 2023 | Powered By WwW.aysnovel.com.ng
Design By Aysha Adam | Theme By WwW.aysnovel.com.ng | Distributed By Aysha Adam