har yakai sai da ya cire rigar sa, ganin cinnakun basu fita ba daga k'arshe ya tub'e wandon sa ya , yashiga kakkab'a ya koma daga shi sai gajeren wando."
Can saiga cinnaku suna fad'owa d'aya bayan d'aya."
tsaye yayi ya kasa magana yana sauke ajiyar zuciya,d'aya bayan d'aya
Yakasa d'aga ido ya dubi d'alibansa saboda kunya domin ya fahimci cewa duk shairin dijama ne."
Dijama tayi tsaye tana kallonshi tana dariya, ya dubeta da kyau cikin b'akin ciki da jin haushinta yace " dijama kitafi gida nakoreki karki k'ara zuwanmin mkrnta,
Ta b'arkewa da dariya had'ida rik'e ciki tana nunanshi tace
"toh saimi Dan ka Koreni,
ainaga kai kafara zagina ni kuma narama,
Harda yimin gorin ilimi, kuma ai naga shi ilimi Allah ke badashi nima ba Dan ya manta daniba,
Kuma ai naga itama 'yartaka jakace bata San komiba sai jakanci,kuma doluwa ce,
Idan ina da kwanyar kifi ita kuma kwanyar kwad'd'i ke gareta,
Ta k'are maganar had'ida mur gud'a baki, tayi tafiyarta."
Sai da tayi nisa da tafiya snn ta waigo a lokacin malma yana k'ok'arin maida kayan jikinsa tace "kuma sai naci uban Larai idan muka had'u rafi,
Tunda ka koreni, daga makarantarka, sann ta juya rik'e da Allonta, tayi tafiyarta."
Koda ta isa gida tana gunguni,
Tsohuwa ke tmbayarta lfy?
Meya dawo da ke gida ynzun?"
Idonta ya cika da hawaye tashiga fad'awa tsohuwa abunda yafaru tun daga farko hark'arshe saboda dijama duk rashin jinta bata k'arya."
Tsohuwa taja bakinta tayi shuru na minti goma, sannan tanisa tace "toh zauna kihuta, gaskiya dijama banji dad'in korarki da malam d'ahiru yayi ba."
To yanzu yazanyi? An koroki a mktantar boko, gashi yanxun islamiyar ma ankoroki.
gashi kuma ke ba k'ok'ariba,
allonki sai yayi wata ukku bakiyi wankiba, haka boko baki ganewa, to ni yanzun miye mafita?"
Dijama tayi shuru sai zarar ido takeyi Can taja dogon nishi tace
"yauwa tsohuwa tunda kinga baganewa nakeyi ba shawara kawai ki sanyani makarantar koyon sak'e sak'e, watak'ila a can nafara ganewa kinga saina koyi sak'a
dama nafison can."
Mahmud dake tsaye yana jinsu tun shigowarta me zaiyi inba dariyaba,
Yace kinko kawo shawara mai kyau, tunda da keda kwad'o bakuda wani banbanci,
Bako mai a k'wak'walwarki sai rashin kunya da gidadanci,
babu abunda kika iya, sai k'auyanci da jakanci takwalla me kan kifi me idanun mujiya." Idan har ba canxa hali kikayiba mki gama yawon makarantuba."
Murgud'a baki tayi cike da jin haushin kala mansa tace "sai naga ai kamar gado nayi a wurinka tunda kamarmu d'aya da kai."
Kuma k'wak'walwarmu d'aya,
kaga kuwa gareka na gada, yayi saurin ja da baya
yace wah?"
Ni ?Allah ya tsaren Dake."
Yana fad'ar hakan yayi waje abinsa domin ida yabiye mata zata hasalashi Dan yasan dijama badai bakiba."
Ai kuwa tsohuwa ta hau masifa, tana fad'in "da kake ce mata kwanyar kifi gareta ai dai 'yar uwarka CE, kuma jininka CE, ni dai bansan irin tsanar da kake yiwa dijamaba."
Mahmud baima San tsohuwa na masifaba yayi ficewarsa abunshi."
tafiya yakeyi yana dariyar dijama saboda rashin kunya da tayi mata yawa akai ita da kanta tasan bata gane karatu, kai Allah dai ya kyauta."
Yana shanye kwanan gidansu, bai ankaraba yaji ankwad'a masa sanda akai, waiga warda da zaiyi wa zaigani, Buba ne da yaransa sun zagayeshi suna shan taba."
Cike da mmki Mahmud yake kallonsu, zai bud'a baki yayi masu mgna suka kuma yunkurin kuma buga masa sandar a karo na biyu,
Hannunsa ya kara suka yashiga jujuwa yaron Buba ya yarb'ar dashi gefe d'aya,
nanfa danbe yakaure tsakaninsu."
Nanfa Mahmud ya shiga dukansu, baji ba gani
,duk suka zube warwas wasu kuma suka tsere a guje,
Daga cikin masu gudun harda Buba😅
D'aya daga cikinsu daya daku ya kasa iya gudu, Mahmud ya shak'o wuyanshi ya mak'areshi, yashiga tmbyarsa, "waye yasanya Ku?" Menamaku kukeso kuga bayana?"
Jinkinsa na rawa yace dijama ce tasanyamu."
"what dijama?" Yace cike da mamaki,
yanzu dijama bayan rashin kunya harda ta'addaci takeyi?"
Ya wurgar dashi gefe d'aya yayi tafiyarshi, zuciyarsa cike da bak'in ciki d mmki."
Haka ya koma gida Rigarsa rataye a kafad'arsa,
Yana shiga cikin gidan, ya ta rar da dijama tsakar gida zaune,
Tana ganinsa ta tashi da gudu ta tafad'a d'akin tsohuwa.
Baibi ta kantaba yayi shige warsa d'akinsa, yashiga har had'a kayansa, cikin akwati.
Saida ya d'auki komai nashi. Ya tallabo akwatinsa yafito."
Lokaci da yafito janye da akwati, yayi dai dai da fitowar
Tsohuwa daga band'aki ta dubeshi cike da mmki tace "Mamuda lafiya?" Ina zakaje da akwati?"
Mahmud ya dubi tsohuwa yace "gida zantafi tunda naga har anfara turomin "yan iska su dakeni
,watara na maganin b'era za a sanya min a abinci domin naci na mutu,
Dan haka tsohuwa kinga tafiyata sai wani lokacin."
Ya kai dubansa ga dijama dake zatsaye a bakin k'ofar d'aki, ta marairaice fuska,
duk bataji dad'in tafiyar da yace zaiyiba
, yace " toh meye kuma na tsayawa kina kallona?"
Zaki turosu ne su kuma tareni a hanya?",
.
Bata tanka masaba illah ta kuma sunkuyar da kanta k'asa,
, tashiga tunanin kaddai ace Buba sanyawa yayi aka daki yaya Mahmud."
Bai kuma bi takan kowaba ya Yakama hanya yayi tafiyarsa." Tsohuwa ta bishi da Addu'ar Allah ya tsareshi ya saukeshi lfy."
bayan fitarsa tsohuwa ta dubi dijama da kyau,
taga ba gaskiya a fuskarta tace dijama me ke faruwa da mahmud?"
Bata b'oyewa tsohuwa ko maiba tashiga bata lbr abunda yafaru."
Aikuwa tsohuwa tashiga yiwa dijama fad'a ta inda take shiga batanan take fitaba, fad'a takeyi sosai kamar ta daketa,
dijama bata tankaba illah turo baki takeyi."
*******************
*The following day*
Tsohuwa takira dijama domin ta aiketa,
Tafiya takeyi tana rawa a kan hannya tana d'an karkad'a k'ugunta,
Ta k'ofar gidansu Buba tabi inda suke zama suna majalisa,
ta hangosu ta d'aure fuska tayi kamar bata gansuba,
Sai da tazo daf dasu abokanansa sukace Baba ga mutuniyar can,
yana ganin takawo daf dasu ya wangame bakin sa da ya kunbura yayi suntum, yasha duka wurin mahmud."
yayi saurin tashi ya shiga gabanta yana fad'in "dijama ta sai ina hakan?" Ta d'aga kai ta dubeshi taga yanda labbansa suka sundume kamar ganda,
Bata San lkcin da ta tuntsire da dariya ba, tana nuna bakinsa da hannu, tana kuma dariya."
Muzanta Buba yayi,
Yashiga kallon kansa,
yaga metake yiwa dariya?"
Fahimta yayi da bakinshi take yiwa dariya ya, farajin haushi, amma kuma sai ya waske."
Ta kuma karkace kai tana kallonshi had'ida ya motsa fuska, kamar ba ita bace ke dariya yanzun,
Tace wai dama kai ragone?" Ina taurin naka yake wanda kake tsoratar da mutanen garin nan?"
Shin wai meyasa harka bari yaya mahmud yaji maka ciwo, lallema amma dai buba kabani mmki,
Ta kuma kallonshi ta tuntsire da dariya tace " toh Allah ya tsare gaba kaga tafiyata", ta barshi nan tsaye
Ta rab'ashi ta wuce, me abokansa zasuyi inba dariyaba, da suka tuna da gudun dasukaga yayi jiya."
Sukace gskya "oga munfaji kunya jiya wai ya akai hkan ta faru? Musamman kai oga duk kafimu gudu a nan take kashanye kwana,
Nanfa yafara k'uluwa. Ya dubesu ya doka masu tsawa idonsa sunrik'e zuwa launin ja."
Dijama nayin nisa snn tawaigo ta kallesa taga yana nan a inda ta barshi tsaye,
ta kuma b'arkewa da dariya ta d'aga murya ynda zaijita tace "amma dai Buba Kai wawa ne wlh da mace zatasanya kaci duka hka, tunda ma Nagano kai ragone na rantse bazan aurekaba, tun wuri ka nemi matar aure amma ba dijamaba ehe, tana kaiwa nan ta zuba a guje ta b'ace masa."
Aikuwa Buba ya k'ulu iya k'uluwa yashiga zage2, yana d'aga anda yana kirarinsu na 'yan tauri,
Had'ida borin kunya."
"Karya kike dijama na rantse da Allah Indai ina numfashi a garin nan bawani Wanda ya isa ya aureki saini, saini Buba na dijama yar gidan tsohuwa."
*wacece dijama*?" Waye Mahmud?"
Muje zuwa yanzun lbr yake ba'ayi komai ba."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
7⃣
Mahaifin Mahmud da mahaifin Dijama Hassan da Husaini ne,
Hakan suka tashi a tare duk abunda zasuyi a tare sukeyinsa, har sha'awa suke bawa mutanen k'auyen Tofa dake cikin k'aramar hukumar Kano."
Hassan da Husaini sun taso cikin so da k'auna da kulawa a wurin mahaifansu, Malam Adamu da Hadiza,
Wanda a yanzun jikokinsu suka canxa masu suna suka mayar dasu tsohuwa da Kaka
Babu wani Abu dake raba Hassan da Husaini,
ako da yaushe suna tare da juna, a cewarsu a yanda suka fito tare sun d'aukarwa Kansu Alk'awarin baxasu tab'a rabewa ba."
Tun haihuwar Hassan da Hussaini tsohohuwa bata kuma k'ara samun haihuwa ba, wannan dalilin yasa suka d'auki son duniyar nan suka d'orashi a Kansu."
K'auyen Tofa k'auye ne mai tattare da Ni'ima da wadatuwa. Da kuma yalwar makarantun boka dana islama."
Wannan dalilin yasa mlm Adamu ya tashi tsaye tsayen daka domin ganin Hassan da Husaini sun samu ilimi boko dana Islama, kasan cewar mlm Adamu manomi ne, akwaishi da wadatar zuci, da son yaga ya wadatar da iyalinshi batareda sun gani a wani gidan ba."
Hakan kuwa akayi suntashi cikin hazak'a da k'ok'ari Wanda gaba d'aya k'auyen na Tofa, suna Alfahari dasu, suka zama abun sha'awa da kwatance."
Akwana a tashi har suka kammala karatunsu na _secondary_ har suka tafi Jami'ar Bayaro _university_ dake cikin garin Kano."
Shigarsu jami'a ra'ayinsu yarafa banbanta a wurin karatu domin Hassan _Business_ yakeson karanta, shi kuma husaini _mass_ _communication_ yake son ya karanta."
Hakan suka Amincewa junansu amma kuma duk da hakan a cikin mkrantar a tare suke kwana a tare sukecin abinci,
idan har ba saninsu kayiba bzaka tattace Waye hassan ba waye husainiba."
Hakan sukayi karantunsu cikin Aminci da soyayyar juna tare da taimakon mahaifinsu har sukayi masters."
Allah ya taimakeso suka fito da sakamako mai kyau,
Nan take har rugogowar d'aukarsu aiki akeyi."
Hassan aiki baya gabansa yafi ganewa kasuwanci domin tun kafin takardunsu su fito har ya bud'a d'an karamin shago a k'ofar gidansu yana sayarda atamfofi da shamdodi da takalma, wadda yin hakan harda taimakakon mahaifin nasu."
Wani babban kamfani ne na sarrafa motoci, dake cikin garin Kano a can Hassan yasamu aiki inda ya samu matsayin manager campanin za'a dinga yimashi Albashi mai tsoka." murna a wurin mahaifan nasu da kuma d'an uwan nashi Husaini abun ba'a mgna
Bayan kwana biyu da faruwar hakan, garin Lagos suka d'auki Husaini aiki a gidan TV na garin Lagos, inda shima suka bashi babban muk'ami."
Hmmmm Hassan Husaina sunyi bak'in ciki sosai da rashin samun aikin da basuyiba a gari d'aya, inda suka buga Kansu da k'asa sukace sun fasa yin aikin indai ba gari d'aya suka samuba.".
Tsohuwa da Kaka suka Shiga lallashinsu suna basu hak'uri a kan cewa rabuwar aikinsu ai bashine rabuwarsu ba, kuma ai ba'a can zasu dawwamaba."
Da kyar a ka samu suka hak'ura had'ida yiwa junansu Addu'a."
Ranar da zasu fara tafiya wurin aiki, ko wannensu ya shirya kayanshi a akwatinsa,
sunja wuri d'aya sun zauna suka rungume junansu ko wanne idonshi ya cika da hawayen rabuwar da zasuyi."
Tsohuwa da Kaka dake tsaye a tsakar gida suna jiran sufito surakasu, sukaji shuru basuda niyar fitowa, kai tsaye suka shiga d'akin, suka ta tarar dasu a zaune rungume da juna suna hawaye."
Sukansu saida suka tausaya masu ganin cewa tunda aka haifesu basu tab'a rabuwaba,
A yanxun shekara Ashirin da bakwai kenan sai yanzun da girmasu lokaci d'aya zasu rabu tabbas dole suyi kukan rabuwa."
Hakan suka shiga lallashinsu da ban baki da komai sannan suka lallab'asu had'ida yi masu rakiya suna d'agawa junansu hannu sukatafi."
Tsohuwa da Kaka sunyi kewar tafiyar tasu, sai dai daga k'arshe suka bisu da Addu'a Neman dacewa."
Wata d'aya da tafiyarsu suka shiga aiki gadan gadan baji bagani, kuma sun tsare gskiyarsu da Amana,
Kullu suna kiran junansu a waya ko kuma su hau charting suna fira cike da kewar junansu."
albashinsu na farko suka shigo garin na Tofa suka shiga rarrabawa tsofafin garin da masara k'arfi."
Sukayiwa tsohuwa gyaran gida aka mayar mata da ginin zamani, Kaka yacika da murna da farin ciki, suka wadata fahaifan nasu snn daga k'arshe suka koma wurin aikinsu."
Bayan shekara d'aya da fara aikin Nasu, ba laifi kud'i sun zauna masu a rayuwa babu abunda suka nema suka rasa, Kaka ya tayar masu da fitina akan cewa zamansu a hakan ya isa,
Ya kamata kowanne daga cikinsu ya nemi mata domin yayi aure, ko zasu ga jikokonsu tun suna da rayuwa."
Suka amsa gaba d'ayansu da to." daman abunda suke jira kenan."
Bayan wata biyu da yimasu maganar dukansu suka nemo matar aure a garin da suke aiki,
Hassan ya nemo auren Hajara, Husaini kuma ya Nemo auren Bilkisu."
Saida suka turawa junansu photo nan yan matansu dukansu sukayiwa juna sambarka da dacen da sukayi sannan suka isarwa da Kaka umurnin sa."
Kaka da tsohuwa sunji dad'i sosai sunyi murna, cikin sati d'aya aka tsaida magana aka sanya ranar bikin nasu nan da wata d'aya masu zuwa."
Akwana tashi lokacin bikinsu yayi aka shiga hidimar biki gadan gadan, in da Hassan ya k'era k'aton gida naji da gani a cikin garin kano,
Shima Husaini hakan,
gida iri d'aya sukayi duk abunda ke akwai gidan hassan akwaishi gidan Husaini gari kawai ya babbanta Hassan a kano husaini a lagos."
Ansha shagalin biki anyi taron bikin da ba'a tab'ayin irinsaba a cikin k'auyen na Tofa."
Ko wannansu Amaryarshi ta tare a gidansa."
Hmmmmm."
Bayan wata tara da aurensu matar Hassan ta haihu ta haifi d'anta namiji mai kama da Husaini sak👌🏻 mmki kowa yakeyi sai. Sai dai ba abun mmki bane kasancewa jini d'aya ne."
Murna Husaini yashigayi dajin labari, tun kafin ya iso yasanyawa yaro suna *Mahmud* Hassan yaji dad'i sosai domin shi a kullum farin cikin husaini shine nashi. Kuma duk abunda yakeso shima shi yakeso."
Shekarar Mahmud Uku aduniya aka Haifa mashi k'anwa aka Sanya mata suna Asma'u."
Har a lokacin matar Husaini ko b'atan wata bata tab'ayiba."
Ta d'auki damuwar duniyar nan ta d'orata a kanta, inda shi kuma Husaini sai dai ya dinga Addu"a, Allah yabashi mai Albarka idan lokaci yayi."
Wanda a wannan lokacin Hassan kud'i sun zauna mashi ya daina aikin kamfani yashiga harkar siyasa gadan gadan."
Shima Husaini hakan ta kasance a gareshi yazama babban d'an jarida a garin lagos wanda akeji dashi, kud'i sun zauna masu."
Bayan matar Hassan ta yaye Asma'u ta kuma samun wani cikin ta haifi d'anta namiji aka sanya mashi suna Adamu wato sunan Kaka kenan suna kiranshi da Khalil."
Wasa wasa sai da sukayi shekara goma sha uku da Aure sannan Allah yabawa matar Husaini ciki, Wanda yayi dai dai da kuma samun cikin matar hassan haihuwa ta hud'u."
Samun cikin Bilkisu matar Husaini ba k'aramin murna sukayi ba gaba d'aya family musamman Hassan, da yakeji tamkar matarsa ce keda cikin."
Haka sukaci gaba da renon cikinsu har ya kai watan haihuwa, ta haifi 'yarta macce sak Hassan,
Masu karatu kusan dai Hassan da Husaini kamarsu d'aya idanba saninsu kayiba bazaka iya tattace d'ayansuba."
Hassan yayi mata hud'uba yasanya mata suna Nana Khadija wato sunan tsohuwa kenan, inda tsohuwa taji dad'in wannan kara da akayi mata aka sanya sunanta, amma kuma ta shinfid'a sharad'in cewa baza'a canza mata sunaba akirata da ainahin sunanta Nana khadija."
Hakan akayi domin bin umurnita, ba'a canxa mata sunaba da sunanta kowa ke kiranta, amma bnda mahaifan nata sai dai suka dinga kiranta da Ummie." Inda tsohuwa take kiranta da deejamah."
Tunda akazo da Mahmud wurin bikin sunan Nana khadija, yaji yana sonta musamman da duk wanda ya gansu ake cewa kamarsu d'aya a lokacin mahmud yana da shekara goma sha d'aya."
Idan zai kwanta barci dole sai a kusa da ita yake kwantawa. Wnn abun bak'aramin dad'i yayi wa mahaifan nasuba."
Bayan haihuwar khadija da sati d'aya matar hassan ta kuma haihuwa ta haifi 'ya mace aka sanya mata suna Fateemah."
Bilkisu tayi Arba'in d'in Nana Khadija cike da k'oshin lafiya, dijama tayi kyau harta gaji sak kamannunta suka dinga komawa na mahaifinta."
Shiri sukeyi zasuzo Kano yawon Arba'in domin ya d'auk'i huto a wurin aikinsa."
Sun shirya tsaf cikin Shiga ta Alfarma, anyiwa Deejamah kwanliya tayi kyau tana sab'e a kafad'ar mahaifiyarta, Husaini yana janye da a kwati yana k'ok'arin sanyashi a but,
Bayan ya shirya komai suka shiga mota yajasu suka d'auki hnyar kano."
Tafiya sukeyi suna yiwa 'yarsu wasa cike da so da k'auna,
Suna kaf da kawowa Husaini yana yawa da Hassan kan cewa gasunan sun kusan kawowa, domin sai sunfara tsayawa cikin kano wurin hassan idan sukayi kwana biyu sai su wuce Tofa wurin tsohuwa idan suka gama kwanakin da zasuyi sai su dawo gida."
Yana cikin waya da hassan saigani sukayi mai mota ya gifta masu ta gabansu ya daki motarsu,
Tayar motar husaini ta fita ya yanki daji babu abunda sukeyi sai Addu'a domin kuwa yayita k'ok'arin ya tsayar da motar amma yakasa."
Saida takai gindin wani k'aton icce, ta daki icce gaba d'aya motar takife,
Wadda yyi ddai da zuwan mutanen da abun ya faru a gabansu suka biyo bayansu domin ceto rywarsu."
K'ok'arin tsiratar da rayuwarsu aka shigayi, da kyar aka samu a ka fito dasu a k'ark'ashin motar wanda a lokacin ko wannensu baya motsi Allah ya karb'i rayuwar bayinsa."
Cikin ikon Allah Nana khadija ko kwarzane batayiba, koda aka cirota a motar sai wasa takeyi da hannunta alamar tana cikin k'oshin lfy."
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
*9*
Gudu takeyi tana ihu,
Buba na biye da ita.
Samarin Antyn lantana ne, suka hangota tana tik'ar gudu suma suka dafo mata dama jiranta sukeyi sunada haushinta."
Tana ganinsu suma sun biyota, ta kuma k'ara gudu tana fad'in wayyo jama'a kufito Ku taimakeni 'yan fashi da makami."
Wani tsoho a kan kekensa yana tafiya yanajin hka yasaki keken ya xuba da gudu ya nemi ma b'oya."
Matan Aure sai kama d'iyansu sukeyi suna rufewa a d'aki suna Addu'oi domin a tunaninsu 'yan fashin ne suka shigo cikin garin."
Dantijawan garin da samaru suna ganin su Buba na gudu tareda dijama,
sun d'auka 'yan fashin sukeyiwa gudu, ai kuwa har 'yan rigaggen gudu sukeyi suna shigewa gida had'ida rufo k'ofa da sanya sakata."
Duk inda dijama ta gifta tana ihu su Buba na biye da ita suna Neman kamata,
Jin ihunta tana fad'in wayyo 'yan fashi da makami, jama'a kufito Ku taimakeni
Kowa ta Kansa yakeyi baya tsayawa saurarenta."
Da kyar tasamu ta kawo gida, tana shiga gida ta mayar da k'ofa ta rufe ta sanya sakata,
Ihun takeyi bakinta yak'i yayi shuru tana fad'in "wayyo tsohuwa 'yan fashi da makami."
A razane Abba ya mik'e tsaye cike da tashin hankali da tsoro ya tallabi Kaka yashigar dashi d'aki,
Tuni tsohuwa ta kai d'aki zaninta a hannu daga ita sai dogon siket, saura kad'an tayi tuntub'e ta fad'a wurin tashi."
D'aki d'aya suka shige suka rufe ko wannensu sai zarar ido yakeyi."
Can sukaji ana dukan k'ofar waje da k'arfi kamar za'a cire k'ofar.'
Jikin tsohuwa ya soma rawa tana kallon Abba tana cewa "yanxun Hassan ya zamuyi?" Karfa su shigo su kashemu."
Abba yace "kwantar da hankalinki tsohuwa baxasu kashemuba,
jin haushina d'aya na baro bindigata a cikin mota."
Kaka kuma ya sunkuyar da kai sai salati yakeyi yana addu'a jikinsa sai rawa yakeyi'
Dukan k'ofa akeyi ba girma ba arziki, tsohuwa ta dinga rawar jiki zanenta a hannunta takasa d'aurawa sai addu'a takeyi idan tasaki wannan ta kwaso wannan."
Dijama ta dubi tsohuwa ta dubi kaka ta rik'e ciki tashiga kwasar dariya, tana nunasu da hannu."
Tsohuwa na ganin hakan ta fara tunanin ko dijamace ta janyo fitina a waje ba 'yan fashin bane."
Tsohuwa tace Hassan ina ganin ba 'yan fashibane dijama ta janyo mana fitina."
Abba yayi saurin waigawa ya dubi dijama da sai dariya takeyi idan ta dubi tsohuwa da kaka.
"Yace dijama suwaye ne? Mekikayi masu?"
Turo baki tayi tace Abba su Buba ne, bata k'arasa maganarba sukaji dukan k'ofar yayi yawa, kamar harda hayaniyar mutane a wajen,
Sai a lokacin Kaka yayi magana yace "ai saikatashi kafita kaji abunda ke faruwa,
Indai wann hatsabibiyar yarinyarce wata rana sai ta janyo mana mgnar da za'a cinnawa gidan nan wuta duk mu k'une gaba d'aya
Yana gama mgnar ya wurgawa dijama harara ya d'aga sandarsa ya zungureta mata k'afa da ita."
Abba ya mik'e da Sauri ya bud'e k'ofa yafita,
Bbu abunda tsohuwa takeyi sai wurgawa dijama harara domin yau ta kaita bango."
Abba yana fita yaga mutane jimjim a k'ofar gida, babba da yaro, tsofaffi da samari,
kowa sai fad'in Albarkacin bakinsa yakeyi a kan dijama,
a gefe d'aya tawagarsu Buba ce da makamai a hannunsu,
d'aya gefen kuma samarin Antyn Lantanane suma rik'e da makamai, rik'e baki yayi yacika da mmki."
Suna ganin fitowarshi sukayi saurin ajiye makamansu suka zube k'asa suna gaida shi."
Bai tambayi abunda ke faruwaba Dan yaji duk abunda suke fad'i, illah yashiga basu hak'uri, tare da rarraba masu kud'i."
Wani dantijo yagani zaune wuri d'aya ya rafka tagumi, kowa yana zuwa karb'ar Kud'i shi yana zaune wuri d'aya baya da niyar motsawa,daga inda yake,
Abba ya isa kusa gareshi yace "Baba lfy meya faru?" Ko wanine bashi da lfy a cikin iyalinka."
Dantijon ya dubi Abba yace "Alhaji dama ciwon ne ai da sauk'i."
Abba yace "Baba meke faruwa?"
Ina kan keke na ina tafiya yarinyar wurinka tadinga ihu tana fad'in 'yan fashi da makami, bansan lokacin da nasaki keken hannuna naba,
wurin intsiratar da kaina,
Kafin in ankara ansace mun keke, kuma wlh Alhaji shi kad'ai na mallaka shine kaddarata."
Abba ya lallasheshi had'ida kirga kud'i masu yawa wad'anda sukafi na keken yabashi had'ida bashi hak'uri,
Hakan Abba yayi bawa mutane hak'uri yana yimasu Alheri suna wucewa daga ciki kuwa harda Buba da yaranshi da saurayin Antyn lantana."
Harda wani magidanci wurin gudun 'yan fashi bai saniba ya ture 'yarshi ta karye a hannu, bai ankaraba saida yaji ance ba yan fashin bane snn ya fahimci Ashe ya karye 'yarshi a hannu."
Shima Abba yabashi hak'uri had'ida bashi kud'i masu yawa da zai nemarwa yarshi magani harta warke."
Sann Abba ya juya yashiga gida yanata mmkin hatsabibanci irin na dijama,
Dijama ta rakub'e wuri d'aya sai zarar ido takeyi tsohuwa sai faman fad'a take mata kamar ta daketa."
Abba shima yashiga yimata fad'a kamar ya doketa abunda bai tab'a yi mataba tunda aka haifeta,
Kaka dake zaune gefe d'aya yace "gwara da Allah yasa ka nan a gaban idonka hakan ta faru,
Kullum a rana d'aya sai sama da mutum goma sunkawo k'ararta tsohuwa ke tare mata,bata son ganin b'acin ranta."
Amma tunda ynxun ka ganewa idonka sai ka d'auki mataki, akai,
Ga ganta nan Ko mkranta bata zuwa gaba d'aya makarantar biyu Arabic da boko duk ankorota, saboda hatsabibancinta gata bata gane komai sai fitina da rashin kunya. Yakai k'arshen maganarshi yana zungura mata sandar hannunshi."
Tsohuwa bata tanka masuba saima taja bakinta tayi shuru, domin yau itama dijama ta kaita bango."
Abba yayi kyaran murya ya dubi tsohuwa yace "inna kiyi hak'uri kibani dijama natafi da ita na nema mata ilimi Wanda zatayi dogaro da kanta tazama abar Alfahari a cikin Al'umma, yin hkan shi zai Sanya mana natsuwa a zuciyarmu ganin mun rik'e marainiyar Allah tsakani da Allah."
Kaka yayi karaf yace "aikuwa wlh da ka taimakemu ka taimaki mutanen garin nan mundun katafi da dijama kabar garin nan da ita,
ni wlh wani lkcin idan na tsaya ina tunanin inda dijama ta gado wnn halin nata sai inkasa tunano kowa a cikin zuri'armu, ina ganin wata k'ila a can cikin dangin mahaifiyarta tayi gadon wnn halin."
Tsohuwa tace "nidai ya isa haka malam kamata yayi kadinga yiwa dijama Addu'a ba aibatataba."
Kaka yace "ni Sam bana aibata dijama a kullum Addu'a ta d'aya Allah ya shirya mana ita, yabamu ikon rik'e amarta da Allah ya d'ora mana a kai."
Abba ya katse zancan da yace "to Ummie tashi kishiga ciki ki had'o kayanki mutafi marece yafara."
Tana murna tana tsalle zataje birni. Ta tashi tashiga d'aki ta fara had'a kayanta."
Tsohuwa bata son tafiyar dijama dan dai ba yanda zatayi ne, dole ta hak'ura tabari za'a tafi da ita."
Sai da ta shirya kayanta tsaf a jaka ta tallabo jakar tana dariya tana jin dad'i, ta fito."
Abba har ya kammala shirinsa ya fito had'ida yiwa su tsohuwa sallama dijama na gabansa Jakarta a hannunta suka nufi hanyar waje,
Tsohuwa dai Addu'a take masu Wanda takejin kanta duk ba dad'i an d'auke Mata dijamarta."
Kaka kuma saboda dad'i kamar ya zuba ruwa a k'asa yashi, domin yasan yau idan ya kwanta barci ba bak'ocin da zai tayar dashi domin kawo shedun dijama."
Har mota suka rakasu, suna yimasu add'o'i."
Mutanene cimjim gaban motar k'awayen dijama suna bangwana, Abba ya bud'a mota yashiga dijama itama tashiga gidan gaba sai wasar baki takeyi tana dariya tana d'agawa su suwaiba hannu."
Murmushi Abba yayi ya kunna mota ya fara tafiya, Dijama ta lek'o ta k'ofar marfin mota tace "suwaiba idan kukaje gonar Audu wurin satar gwaiba,
idan kukaga Buba kuce masa natafi birni amma zandawo don saina rama abunda yayi mun."
Abba yace Ummie na wai meye hkan? Ki zauna dai dai mana karda kiji ciwo."
Snn tayi saurin gyara zamanta Abba yaja mota
Yatafi yana dariyarta, suka d'auki hnyar kano."
_dijama a birni ikon Allah🤔_
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMA*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_😅)
Writing
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
8⃣
Hassan dake waya da Husaini yanajinsa yana kalmar shahada a waya,
gaba d'aya hankalinsa ya tashi ya fito da saurin shi baibi ta kan kowaba ya shiga motarshi yajata da k'arfi ya mik'i hanya,
ya nufi wurin da yaji Husaini yace masa ya kawo."
Cikin minti talatin ya isa wurin ya d'aga wayarsa ya shiga kiran wayar husaini, d'aya daga cikin wad'anda suka kawo masu taimakon gaggawa, ya d'aga wayar yashiga yiwa Hassan bayanin abunda ya faru, ya shaida mashi da cewa gasunan Asibity, Had'ida yimashi kwatancen asibity dasuke."
Cikin tashin hankali Hassan yanufi Asibity idonsa yana zubar da hawaye kamar macce."
A Gaban gawarsu yake dur'kushe yana kuka yana jijjiga Husaini yana fad'in "Husaini katashi don Allah karka mutu kabarni rayuwata idan babu kai bnga amfaninta ba,
kai kad'ai ne d'an uwana jinina Wanda nake shawara dashi husaini katashi."
Kuka yakeyi sosai kamar ya d'auke numfashi yana jijjigar gawar Husaini."
Mutanen wurin suka tallabeshi suka bar wurin dashi ana bashi hkr,
Snn dga k'arshe yakira mahaifan Bilkisu da sauri suka zo, snn ya kira Kaka da tsohuwa, a tare sukazo asibity aka d'auki gawarsu aka nufi Kano da su gidan Hassan akayi masu wanka da sutura aka kaisu gidansu na gskiya."
A nan gidan Hassan akayi amsar gaisuwa,
Inda Dijama tana rungume a hannun tsohuwa tana bata madara."
Hassan yayita lallashin tsohuwa akan ta amince tabari Hajara taci gaba da shayar dasu tareda fateema,
Amma tsohuwa ta kafe tace "sam bazai yiwoba, kuma da anyi sadakar bakwai zatayi tafiyarta gida, tare da dijama tazata tafi Dan bazata bartaba."
Hankalin Hassan ya kuma tashi, ya shiga rok'on tsohuwa akan ta amince ta bar masa dijama zai kula da ita ya had'ata da 'ya'yanshi yanda bazata tab'ayin maraiciba."
Tsohuwa tace "Sam bazai yiwoba, itama ita zata dinga gani a gabanta tana jin sanyi tana d'ebe mata kewar Husaini da tarasa."
Hakan akayi bayan sadakar bakwai ta harhad'a kayanta ta goya Dijama zata tafi, direba yana jiranta."
Hassan da iyanlansa suka yomata rakiya, ko wannensu idonshi cike da hawaye domin ji sukeyi mutuwar Husaini ta kuma dawo masu sabuwa."
Mahmud kuka yakeyi sosai yana birgima yarik'e tsohuwa yana fad'in bazataje masa da dijamarsaba."
Kuka yakeyi sosai kowa ya tausaya masa, tsohuwa tace a had'o masa kayanshi sutafi tare idan hutunsu na mkranta ya k'are sai aje a d'aukoshi, tun da daman hutun makaranta sukeyi."
Haka kuwa akayi, aka had'awa Mahmud kayansa yana murna yana dariya, sukayi masu rakiya zuwa mota direba yazasu suka d'auki hanyar Tofa."
Wnn shine dalilin zaman dijama a wurin tsohuwa a cikin k'auyen tofa."
Tsohuwa bata son jin kukan dijama bata son ganin b'acin ranta,
Haka mahmud da zarar akayi masu hutun mkranta zai tsira fita a kan dole sai ankawoshi wurin tsohuwa yaga dijamarsa."
Itama dijama tun tana k'arama da zarar Mahmud yazo hutu,
bata kuma yarda da kowa sai mahmud a tare sukecin abinci a tare suke kwana, idan tayi kashi shike wanke mata, shike mata wanka,
zarar hutunsu ya k'are Idan direba yazo d'aukarshi, da kuka da komai suke rabuwa,
Tsohuwa tana jijjinawa wannan shak'uwa tasu, haka shima Abbah wato Hassan kenan shima yana jijjinawa wann soyayyar tasu."
Wnn dalilin ne yasa mahmud duk lokacin da suka samu hutu baya iya zama garin kano sai dai yatahowarsa Tofa yayi zamansa saboda dijama, har zuwa yanzun da girma yazo masa ya mallaki hnkalin kansa yashiga jami'a a yanzun yana zangonshi na k'arshe a dgree d'insa."
Tun tashin dijama a rayuwa babu abunda ta nema ta rasa, domin tsohuwa da Kaka da muhmud basu da wani buri da yawuce a koda yaushe su farantawa marainiya, basa son ganin kukanta."
Abba shike d'auke da karatunda da duk wani Abu da yashafi rayuwata, tunda tsohuwa ta kafe a kan cewa baxata bashi itaba, amma shi har ga Allah yaso ya d'auki dijama ya had'ata da yaranshi yabata gata Wanda yin hkan shi zai sanyashi ako da yaushe zai dinga ganin kamar Hussainin shi yana nan bai mutuba."
Tun tashin Mahmud shi mutum ne mai son a girmama shi, baya d'aukar raini a gida ko a waje,
K'annansa su fateema da zarar yashigo a gida kowa yake kama Kansa, idan ba hakan ba da zarar sunyi abunda ba dai dai ba a nan take zai hukuntasu. Ya azzabtar dasu yayi tafiyarsa."
Wnn dalilin ne yasa yaji ya tsani dijama saboda rashin jinta, gata bata gane karatu,
Kuma bata ganin girmanshi kwata kwata ta rainashi raininda ba Wanda ya tab'a yi mashi irinshi."
Tsohuwa bata ganin laifinta duk rashin kunyar da zatayi jan maganar da zatayi a waje tsohuwa bata ganin laifinta,
Wann dalilin yasa a rayuwarshi yaji ya tsaneta basa shiri kwata kwata.wani lokaci Sai ya d'auki niyar cewa bazai k'ara zuwa Tofa hutuba saboda rashin kunyar dijama,
Amma da zarar anyi masu hutun ko na kwana biyu ne baya iyawa sai yazo Tofa yayi hutunsa snn ya koma."
Kamar ynzun da Hutu yazo yayi, bai iyar da kammala hutun nashiba, ta had'ashi dasu Buba, ya tattara kayansa ya koma warsa gida Wanda tsohuwa tacika da mmki."
*Wnn kenan mudawo labari*
***************
Mahmud na komawa gida, kowa ya cika da mmki dan ganin hutunsu bai k'areba ya dawo."
Abba ne yakirashi a falonsa yana tare da momy mahaifiyarsu yashiga tmbayar sa, lafiya me yadawo dashi bayan ba hakan ya sababa hutunsu bai k'areba?"
Murmushi yayi ya sunkuyar da kansa yace " Ba komai Abba hakan nan kawai nadawo babu abunda ya faru."
Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "ina fatan kowa yana lafiya?"
Ya 'yata Ummie ina fatan tana cikin k'oshin lfy?"
Murmushi mahmud ya k'ak'aro yace kowa lfy Abba. Kaka ne kawai yake fama da ciwon k'afa, amma kuma yaji sauk'i sosai."
Abba yace subahanallahi!!! Ai kuwa zanje cikin _weekend_ d'in nan nadiboshi,
Momy tace "Allah yabashi lafiya."
Suka amsa da "Amin gaba d'ayansu."
Snn Abba yayi kyaran murya yadubi mahmud da kyau yace "dama ko baka dawoba zankira ka, a waya nace kadawo, domin Alhaji Atiku commonden d'in sojoji wnn abokin nawa yayo mun waya a kan cewa anfitarda form na sojoji ya d'aukar maka d'aya,
Saika had'a takardunka katafi Abuja cikin satin nan zakuyi jarabawa Allah yabada sa'a yasa a dace."
Suka Amsa da Amin."
Sannan Mahmud yayi masu sallama ya fito yanufi d'akinshi yana kuma jin haushin dijama a ranshi."
**************
Dijama zaune a kusa da tsohuwa tana turo baki, tsohuwa nayi mata fad'a akan ta fara gajiya da halinta kullum saita janyo mata fad'a da fitina a mak'ota."
Ta mik'a mata kud'i tace "gashi kitafi gidan jummai ki kai mata kud'in zubi, dan Allah dijama karki tsaya kuma karki kula kowa a hnya kiyi tafiyarki."
Mik'ewa tsaye tayi had'ida turo baki tana gun guni, sannan ta karb'i kud'in ta fita."
Tana tafiyarta cikin natsuwa abunda bata tab'a yiba, k'awayenta su lantana tagani sunfito daga rafi, suka had'a baki suna mata magana suna cewa "dijama 'yar gidan tsohuwa sai ina?"
Bata tsaya ta kulasuba sai dai ta nuna masu da hannu tana tafiya tace "Tsohuwa ta aikeni gidan jummai nakai kud'in zubi, batajira taji amsarsu ba, tayi tafiyarta, sab'anin da, da sai ta tsaya sunyi jan magana snn kowa ya kama gabansa."
Mmki suka shiga yi ko meyasamu dijama?"
Lantana tace ko dai batada lafiya ne?"
Suka had'a baki sukace lafiyarta k'alau akwai dai abunda ke damunta."
Sukace "Allah ya kyauta gaba d'ayansu sannan sukayi tafiyarsu."
Dijama anfara jin mgnar tsohuwa kenan, hnmmm Bari dai mugani."
Tana gafda da zata shiga gidan jummai mai adashi, taci karo da Antyn lantana wadda tabata takarda ta kaiwa yaya Mahmud,
ta sha gabanta tana fad'in "yawwa dijama shine nabaki sak'o ki kaiwa yayanki d'an birni shine baki bashiba kika yaga."
Bata tanka mata ba, sai ma k'ok'ari takeyi tabi ta gefenta ta wuce, ta kuma tarar gabanta, tana d'auke da k'waryar da tayo nik'an dawa a kanta,
Tacewa dijama "wani sabon iskanci kika samo wadda idan ana yimaki mgna kidinga kyale mutane, taciyo kwalar rigar dijama."
A rayuwar dijama babu abunda ta tsana irin a rik'e mata kwalar riga, cike dajin haushi ta dubeta tace "lallai ma Antynnan harda wani rigemun riga, bakisan ina ragamaki bane a k'auyen nan saboda lantana amma yau zakisan kowacece dijama."
Ta duk'a kamar wadda wani abun nata ya fad'i a k'asa zata d'auka,
Tasanya hannunta ta yaye k'afar Antyn lantana, sai gata tafad'i k'asa dab'as kwaryar nik'an dawa ta rabe biyu, nik'an ya zube k'asa
Ta rik'e k'ungunta tana fad'in "wayyo Allah nashiga uku K'uguna dijama kin lahantani."
Me dijama zatayi idan ba dariya ba, tace "dankinga ina ragamaki, lallai ma Antyn nan to ba tsoronki nkejiba, ni bana tsoron kowa a garin nan ki kiyaye ehe."
Babu abunda antyn lantana takeyi sai kuka da murje2 sboda masifar rad'ad'in da k'ugunta yake mata."
Dijama nayi mata dariya, ta rab'ata zata wuce, saiga samarin Antyn lantana sunbiyo ta wurin, zasu wuce
Ganinta sukayi zaune a k'asa warwas dafe da k'ugu tana kuka tana fad'in wayyo dijama kin lahantani wayyo k'uguna."
Dijama na ganinsu taja da baya ta koma hanyar gida, ta arce da gudu, basu ankaraba sai ganinta sukayi tana gudu kamar filfilwa ta kusan shanye kwanar gidansu." Dijama ba dai guduba kamar mai Aljanun gudu."
Saurayin Antyn lantana yace "nayi Alk'awarin tunda dijama tashigo gonata saina saita mata hankali A garin nan."
Yashiga taimakon budurwanshi ya mik'ar da ita tsaye ya rakata yarakata har k'ofar gida sannan ya juya ya tafi."
Dijama na shanye kwana gidansu sai hango motar Abban kano tayi a jiye a k'ofar gidansu, murna tashigayi tun daga nesa ta dinga stalle Tana "Abba oyoyo."
Kai tsaye taje kan jikinshi ta fad'a tana dariya tana murna ganinshi domin Abban kano yana sonta sosai,
Murna yayi da ganinta yashiga shafar bayanta yana fad'in "Iye Ummie na ta girma, kina nan kina karatu kuwa?"
Taji gabanta ya fad'i domin Abba baya wasa idan akazo fagen karatu."
Tayi saurin kauda maganar da cewa "Abba ina su fateemah?"
Yayi dariya yace sunanan lfyrsu glau, suna gaisheku."
Anan suka shiga shirya Kaka domin a d'aukeshi a tafi dashi asibity dake cikin garin domin a kuma diba mashi lfyar k'afarshi."
Alhmdulillah anyi mashi aune aune angano ciwon k'afar da sauk'i, aka rubuta mashi magani Abba yasawo mashi sann suka dawo gida."
Anan Abba yace zai kwana sai gobe idan yaga ynda jikin Kaka ya kwana snn sai yatafi gida ko da marecene yatashi safiyar _Monday_ a garin kano."
Tun zuwansa garin bai hutaba, mutane ne cingim a k'ofar gidan tsofaffi da samari,
Abba sai rarraba masu kud'i yakeyi suna godiya tare da sanya mashi Albarka."
Abba mutum ne mai taimako da tausayi, wannan dalilin ne yasa mutanen cikin garin tofa suke mutuntashi da darajashi."
Washe garin ranar lahadi da safe, misalin k'arfe goma na safe,
Abba yana stakar gida zaune, tsohuwa na gefensa d'aya gefensa Kaka ne zaune da sandarsa gefensa a jiye, Abba yana b'are mashi ayaba yana bashi yanaci had'ida sanya mashi Albarka."
Dijama na cikin d'aki zaune ta fito daga wanka tana tsara kwanliya." Fuskarta tasha kwalli da jambaki da hoda."
Tsohuwa tashiga kiran sunanta tana fad'in "dijama kiyi Sauri Ki shirya kizo na aikeki gidan kuluwa ki kaimata tsarabarda bbnki yazo da ita."
To dijama tace had'ida mik'ewa tsaye ta d'auki kayanta tasanya
Snn ta fito."
Tsohuwa ta mik'a mata Leda cike da ayaba da lemu tace "ungo ki kai mata kuma Dan Allah karki tsaya a kan hanya."
Tace "to." Ta karb'a had'ida fita, Abba ya dubita yayi murmushi yace "Ummie ba dai wayoba."
Tsohuwa tayi dariya,
Kaka kuma yace "hmmm yaja bakinshi yayi shuru."
Bayan ta dawo aiken datsohuwa tsohuwa tayi mata tana tafiyarta a hanya tana wak'a tana rawa, tana d'an karkad'a k'ugunta."
Wazata gani Buba tagani a gabanta yana wasar Baki yana fad'in dijamata kinyi kyau wnn kwanliya hkan."
Bakin buba ta kalla inda har ynzun bai iyar da warkewa ba daga kumburin da yayi."
Batasan lokacin da dariya ta sub'uce mata ba,
Ta dubeshi tana dariya tace "Wai amma dai Yaya mahmud ya iya duka."
Wai kai Buba kana aikin me harya kumbura baka Baki, ta kuma shek'ewa da dariya, ta dubeshi
Tace a hkan kake cewa zaka aureni. Allah ya tsaran da auren ragon mutum kamarka,
Ni nafison na aure jarumin namiji mai firgita 'yan maxa, amma kai ai macce ne."
Ta rab'ashi ta wuce tana dariya,
Buba yaji haushi ya k'ulu iya k'uluwa, idonsa ya canza launi zuwa ja, ya zunduma ashar, Wanda yasa dijama saurin juyowa da sauri tana kallonsa."
Yace "duk son da nake maki dijama yau bazai hana naci ...... Ya zunduba wani kalar shar ya dafawa dijama da saurinshi cikin hushi."
Dijama na ganin hakan ta zuba da gudu ai kuwa buba ya dafa mata, da yaranshi."
Gudu takeyi tana kuwa tana fad'in "wayyo Allah jama'a kutaimakeni 'yan fashi wayyo Allah 'yan fashi.da makami"
[28/04, 20:51] Sadiya Aliyu Fbk: 🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar gidan tsohuwa_ )😅
Written
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)
0 comments:
Post a Comment