Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron abokinsa, amininsa, kuma d'an uwansa dake xaune kujera me xaman banxa cikin motar, can dai ya ja tsaki ya girgixa kai, speaking calmly yace "Ni fa da ma ka canxa labarin nan naka Ahmad, in anyway ban ga amfaninsa ba..." Dariya abokin nasa Ahmad yyi yace "Toh ai ni yana da amfani gareni sosai tunda ina sonta and i want to marry her, look Captain don Allah ka cire son xuciya ka gaya min meye aibun Maryam let me know" Wanda ya kira da captain ya shafa lallausan gashin kansa yace "Kasan mene?" Kallonsa kawai Ahmad yake yana jiran jin abinda xai ce, Captain yace "Ina son ka sanar dani me yasa ku Hausawa baku da xancen da ya wuce na soyayya, ga dai abubuwan ilimi iri iri masu ma'ana da mutum xai karu da su duniya... Amma ku dai soyayya kadai ku ka sa a gaba, did u know that it's just of recent ina wani karatu nayi discovering cewar Airplane water is riddled with bacteria, not even that, jiya jiyan nan na gano cewar...." Ahmad dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Wannan kai da masu tunani irin naka ya shafa, what u are saying now will add no value to people like me gaskiya" Captain ya maida hankalinsa gaba daya kan tukin da yake, Ahmad yace "Duk sanda na kawo maka maganar Maryam you always have a way to get rid of the discussion ko me yasa?" Captain yace "Ohk you asked me of her flaws if i am not mistaken, right?" Ahmad yace "Yes so" Captain yace "To xaka ji ynxu.... first of all she is local, secondly she gat no qualities da xai sa ka makale mata dude, just imagine an undergraduate fa?? And worst of all she isn't even beautiful enough, ga dai big babes a garin da ka baro Abuja, sannan..... her hygiene is nothing to write home about, i mean nothing.... Shine ma babban damuwata ma ni" Da mamaki Ahmad ke kallonsa, da farko kasa ce masa komai yyi, can kuma yace "Wani rashin tsaftar kaga tayi??" Captain ya saci kallonsa yace "Oho, wataran xaka gani" Ahmad ya girgixa kai yace "You are talking off hook, Maryam tana da qualities din da ni nake so, I think that's all? Kuma dama kai idan baka son abu to fa baxa ka ta6a son abun ba, ka dingi discouraging mutum a kai kenan" Captain ya gyada masa kai yace "Ehh haka ne, plss close the chapter" Ahmad xai yi magana ya hango inda ake tuyar awara a gefen titi, da sauri yace "Captain plss ka d'an tsaya, I want to get this, na mance yaushe rabon inci awara, tun kafin in tafi Uk fa..." Captain ya d'an kalli wajen da ake tuyar awaran ya kara ma motarsa gudu yace "Allah ya kiyaye, domin na je dauko ka a railway station doesn't mean xa ka mayar da mu gantalallu a hayi.... Meye kuma awara?" Ahmad yace "Toh ka ajiye ni, ai bance sai ka xo ka daukeni a tasha ba dama, you offered to do so" Captain yyi kasa da murya yana rage gudunsa yace "Yanxu Ahmad kasan ta ynda suka yi processing abun nan da xaka ci? Hayi ne fa nan, ka bari kaje gida kasa ayi maka mana, ni Allah bana son locality din nan naka" Calmly Ahmad yace "Su 'yan hayin ba mutane bane Abuturrab?" Captain yace "Aa ba haka nake nufi ba, I mean... hygiene din, they don't value it, ka gane ai" Ahmad yace "Kai komai sai kace hygiene, to sannu sarkin 'yan tsafta, a haka kuma nake son in siya, ba ruwanka kuma" Captain bai kuma ce masa komai ba ganin wani waje da ake suyan yyi parking kafin ya karasa wajen yace "To sai ka sauka kaje ka siya, amma gaskiya you ain't worth being a Dr wllh, very careless Dr that looks down on Hygiene" Ahmad na hararansa yace "Ae ba dankali nace maka xan ci ba malam, Awara nace kuma nan dankali ake siyarwa" Captain ya kalli wajen masu tuyan yace "Toh ai ban san yanda Awaran yake ba, ba shi bane wnn din?" Ahmad yace "Ba shi bane" Captain ya ja motarsa yana tukin a nutse, can underneath his breath ya ja tsaki, Ahmad is just too local for his liking, Ahmad yace "I think ga wani wajen can" ta gefen wajen da ya nuna masa Captain ya gangara yyi parking yana kallon yarinyar dake tuyan awaran yana yamutsa fuska shi wnn ko yunwa xai kashesa xai iya cin abinda take yi kuwa, Ahmad ya bude motar ya sauka ya tafi gun ta, ita kadai ce xaune sai yara da almajirai dake tsaye suna jiran a siyar masu awara, Ahmad yace "Me awara nawa nawa ne awaran naki?" Ba tare da ta kallesa ba tace "Daya Ashirin" Ahmad ya buda ido ya rike waist dinsa yace "Ikon Allah, kamar dai muna fada da me awara irin wnn amsawan" Still bata kallesa ba ta ci gaba da sallaman yaran da ke gabanta, ta mota Captain ke kallonsu, shi dai Ahmad na tsaye bai sake ce mata komai ba ganin mood dinta, sai da ta sallami yaran gabanta ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa xa'a sa maka?" Ya daga kafada yace "Na dari biyar kawai" Tace "Baxai kai ba, sai dai in xaka jira a soya wani" Yace "Toh ba damuwa xan jira a mota" Daga haka ya juya ya nufi motar ya bude ya shiga yana kallon Captain da ya kauda kai da sauri yana kallon daya side din. Leda biyu tayi masa sannan ta hadasu gaba daya a wani ledan daban, yajin ma ta xuba masa a wani ledan snn ta mike ta nufi motar ta mika masa ta glass dake bude, amsa yyi yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Kamar dai an 6ata ma me awara rai" Ita dai bata ce masa komai ba, dubu biyu ya ciro a aljihunsa ya mika mata yace "Toh gashi" ta daga kai tana kallon kudin tace "Na dari biyar kace" Yace "Ehh sai ki rike sauran canjin ai ko" Ta sauke idonta kasa tace "Aa ka dai bani dari biyar din dai kawai" Ya bude ido yace "Dama ana maida hannun kyauta baya" ta girgixa masa kai tace "Ban san wa xance ya bani ba a gida" Cikin sanyin murya ta karasa maganan, yayi murmushi yace "Sai ki boye kayan ki" Daga haka ya saki kudin nan kasa yace "To sai anjima me awara, Allah ya kawo kasuwa" captain da ya ki kallonsu ya tada motar suka bar wajen. Sai da suka kusa fita titin hayi Ahmad yace "I imagine may be condition ne ya sa yarinyar tuyan awara a rana ko, the country is getting tougher and tougher for the less privileged everyday....." Captain dai bai ce masa komai ba, Ahmad yyi kasa da murya yace "On a serious note ina jin tausayin poor masses a kasar nan, yanxu banda situation me xai sa iyayenta su barta bakin titi tana wnn sana'a? Allah dai ya rufa ma kowa asiri" Still Captain bai ce masa komai ba har suka shigo Unguwan Sarki, yana kallon Ahmad yace "Mu je can gida ne kawai?" Ahmad ya gyara xama yace "Aa kai ni in ga Ummata tukun, da yamma xan shigo in sha Allah" Captain bai ce komai ba yyi driving har xuwa gidan kanwar Mum dinsa Hajiya Ramlah warce ita ce mahaifiyar Ahmad... A kofar gida yyi parking Ahmad na kallonsa yace "Baxa ka shigo ba?" Captain yace "Aa ni fa ko jiya na xo gidan nan" Ahmad yace "Sai dai idan Ummi ce ta aiko ka ba dai xuwan kanka ba" Captain ya shafa kansa yana xare manyan idanuwansa ya kasa cewa komai, Ahmad ya ta6e baki ya bude motar ya sauka, da sauri Captain na nuna masa ledan awaransa yace "Heyy ga kullinka ka mance min a mota" Juyowa Ahmad yyi ya jefa masa wani kallo ya dau ledan awaran ya nufi cikin gidansu, Captain ya bi sa da kallo yana murmushi, can ya kashe motar ya sauka ya bi bayansa walking slowly... Siyama ta sake yayanta da ta rungume ganin Captain da ya shigo parlon, tana murmushi tace "Yaya sannu da xuwa" Yace "How are you Siyama" tace "I'm fine" Yace "Ina su Maimuna?" Tace "Sun tafi islamiyya" Yace "Ke fa" Tace "Ka manta nace maka bani da lafiya jiya?" Yace "Ohhh ohk na tuna, Allah ya kara lafiya, Umma fa" Tace "She's in her room" Tuni Ahmad ya nufi dakin Mahaifiyarsa, Captain ya bi bayansa. Sai bayan Magrib Captain ya bar gidan tare da Ahmad xuwa nasu gidan a Malali, Babban gida ne duplex me wadatattcen tsakar gida.... Captain yyi parking a daya daga parking lot biyu dake katon compound din, suka sauka motar tare da Ahmad suka shiga ciki Ahmad na cewa "Amma Abba baya gari ko?" Captain yace "Ehh baya nan"
Zaune take a d'an karamin tsukakken tsakar gidan nasu da kwanon tuwonta a gaba sae dai ba ci take ba duk da kasancewar hannunta cikin kwanon, wata matashiya ce xaune cikin daya daga kananun dakuna uku dake D'an tsakar gidan hannunta rike da mafici tayi daurin kirji, xaune a tsakar gidan kan tabarma wani middle aged man ne da baxai wuce 58 ba, daga cikin dakin matar ke cewa "Munafuka algunguma kawai, sae ana magana tayi mukui ta ki cewa komai, a haka xaki kare cikin nukurci da bakin hali, banda haka uwar me ya ci min naira hamsin a kudina, ko da yake dama ae kin saba halin bera, sae dai na yau yayi min ciwooo tunda ko biyar ubanki bai kawo min yace gashi kiyi cefane ba, to a kan me??" Ita dai bata iya ta ce komai ba har lkcn hannunta na cikin kwanon tuwon ta kasa ci, mikewa matar tayi tana gyara daurin kirjin jikinta ta fito a fusace ta janye kwanon tuwon jin almajiri na bara tace "D'an malam shigo ka amsa" Malam Isuhu dake xaune saman tabarma yace "Ita kuma ta ci me Hansatu??" Wani kallo ta jefa masa tace "Sae ta ci wanda ka nemo aka girka yau" tana fadin haka ta juye ma almajiri ta ajiye kwanon tayi shigewarta daki, shi dai bai kuma cewa komai ba, a hankali ta mike ta dau kwanon ta kai wajen wanke wanke ta shiga hada kayan wanke wanken tsakar gidan, sae da ta gama gaba daya ta mike mahaifinta dake tsakar gidan har sannan ya fiddo hamsin a aljihunsa yace "Gashi ki je ko dankali soyayye ki siyo ki ci Jiddah" karasawa tayi ta amshi kudin da ladabi tace "Nagode Baba" bata rufe baki ba Hansatu ta fito da gudu ta warce kudin tana kallonsa da kyau tace "Saura dari hudu da hamsin kudin cefane na na yau" tana fadin haka ta kulle kudin bakin xaninta ta shige akurkin dakinta, Jiddah ta juya a hankali ta shiga dakinsu ba tare da ta yarda hawayen dake makale idonta ya xubo ba.
Washegari da safe wata dattijuwa da baxata haura 55 ba ta shigo wani babban daki ta kulle kofar tana kallon wanda ke kwance yyi rub da ciki saman gado, karasawa ciki tayi ta buga gadon, juyowa yyi da sauri ya mike xaune ganinta yace "Aunty ina kwana?" Tace "Jiya da daddare ina kaje har bayan isha baka shigo ba" yace "Aunty ina gidansu Ahmad fa, kuma tare ma muka dawo nan da shi na xata kin yi bacci shi yasa bamu shigo ba" Tace "Ohk, jiya Ahmad din ya dawo" Yace "Ehh" Tace "Ai na xata tadi kaje" D'an murmushi yyi yace "Tadi kuma Aunty... Ai tana Abuja" Tace "Atoh na sani ko ka kyallara ido ka ga wata ka watsa min kasa a ido??" Bai kuma ce mata komai ba sai murmushi da yayi, ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle kofar, mikewa tsaye yyi yana kallon agogo dake nuna karfe tara ya shiga bathroom. Kasancewar ranan asabar ce sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya fito daga dakinsa sanye cikin kananun kayan da suka matukar amsar sa, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon gaba daya, kanninsa mata ne xaune Main parlor din gidan, duk kallo daya suka yi masa suka dauke kai, bangaren Mahaifiyarsa ya nufa, Ramlah ta bi sa da kallo tace "Ummi ta fita fa" Ya juyo ya wuce side din Stepmum dinsa... A parlonta ya sameta tana yi ma autarta Aisha tsifa, yace "Xan je gidansu Ahmad Aunty" Tace "Breakfast din fa?" Yace "Ni nayi breakfast da asuba fa" tace "Oh ka dawo breakfast din asuban kenan" Yace "Ehh" tace "Kawata xata tafi Lagos ranan Monday daga kano shine nace kilan ma you will be piloting the plane...." Yace "In dai flight din safe ne" Tace "Na safen ne ma ina ji" Yace "Allah ya kai mu" Daga haka ya juya yace "Sai na dawo" yana fita parlon, Hajiya Amina da suke kira da Aunty ta kalli autarta tace "Me yasa baki gaida sa ba?" Aisha ta buda hannu tace "Wllh Aunty ranan ce mana yyi mu daina gaishesa a gidan nan idan yana nan, and he was serious about it" Aunty tace "Me ku ka yi masa?" Aisha tace "Babu komai, ranan Thursday da ya dawo duk muna parlor da su Aunty Safiyya muka gaishesa bai ce komai ba, muka sake gaishesa, har ya tafi ya dawo on a serious note yace mana kar mu sake gaishesa baya so, and since then no one is greeting him again and he is very comfortable with that" Aunty ta ta6e baki tace "Toh ai shkkn" A daki Abuturrab ya tadda Ahmad bayan ya isa gidansu, Abuturrab ya nufi window din dakin ya dage curtains din ya bude windon yace "Allow natural ventilation mana" Ahmad yyi dariya yace "Gaskiya ne bature, to kashe Ac din ko?" Abuturrab ya xauna yace "Aa bar shi, how are you?" Ahmad yace "Fine, ya su Ummi" Abuturrab yace "Cool" Ahmad yace "Are you flying on Thursday?" Abuturrab ya d'an yi shiru trying to recall his piloting schedules, kafin yace "Yea, Kano to Lagos, Then Lagos to Abuja, on Friday kuma Abuja to port harcourt" Ahmad yace "Ohk dama Maryam will be going back to schl Thursday I tot kana nan mu kai ta tare" Abuturrab ya ta6e baki yace "Ahmadu Bello?" Ahmad yace "Ehh" Abuturrab yace "Ka kai ta tasha ka sa ta a mota mana, kawai yarinya karama tayi ta juyaka" Hararansa Ahmad yyi, Abuturrab ya fiddo wayarsa dake ring yana duba me kiransa. Bude kofar dakin aka yi Maimuna ta shigo da tray dauke da warmer din danwake da tamarind drink a jug, ajiyewa tayi ta gaida Abuturrab da murmushi fuskarta yace "Ya kike Moon?" Tace "Alhmdllh, Yaya xan je Abuja fa" Yace "To sae ki xo in makala ki a jirgi ko?" Dariya tayi sosai tace "To ai shi sa na gaya maka" yyi murmushi bai ce mata komai ba, ta mike ta fita, bude warmer din Ahmad yyi, Abuturrab dake ta kallon danwaken warmer din yace "Ya ma abin nan da ka siya jiya a hayin Rigasa? Kamar shi nake gani a nan" Ahmad ya wara ido ido yyi dariya yace "Ohh wannan danwake ne, wancan kuma awara, kamar kuwa kasan yau ma xan je in siya, kaji dadin awaran nan kuwa? Gaskiya sun iya sosai, har Umma sai da ta ci, ni uku kawai naci su suka cinye sauran" Abuturrab ya dinga kallonsa da mamaki, can yace "Har komawa xaka yi kenan ka sake siya" Ahmad yace "Yes, I had intention dama" Abuturrab ya gyada kai bai sake ce masa komai ba. Har yamma Abuturrab na tare da cousin din nasa kuma abokinsa.... Su yi fada su shirya, duk bayan sati uku Ahmad ke shigowa kd yyi weekend daga Abuja don a can yake aiki as a medical Doctor, throughout weekend din kuma tare suke spending dinsa da Abuturrab idan shi ma yana garin, karfe biyar saura Ahmad ya mike yace "Captain mu je ka rakani mana pls" Captain ya kallesa yace "In raka ka ina?" Ahmad yace "Hayin Rigasa" Abuturrab yace "Aa sae dai Hayin banki, kaga malam mu fita tare kawai kayi hanyarka inyi nawa, don gida xan wuce yanxu in sha Allah" Ahmad yace "Ae ko baka isa ba, wllh sae ka rakani" Abuturrab ya dau wayarsa xae dau makullin motarsa Ahmad ya dauke yace "Sae ka tafi da kafa ai" kallonsa Abuturrab yyi, lkci daya ya wani hade rai, Ahmad ya fita dakin yana murmushi. Driving Ahmad yake yi, ya kalli Abuturrab dake xaune gefensa yace "Wai Aneesah fa?" Abuturrab ya gyara xama yace "She's good, baka ji muna waya daxu ba" Ahmad ya girgixa kai yace "Kai ynxu da gaske mace da idanuwanta suke a bude da sunan wayewa kake so Captain...." Abuturrab yace "Look at you, kai baka san wayayyun sun fi tsafta ba, ni fa I don't care.... As far as xata yi tsafta 100%, wllh ko haduwa da mace kazama ban son yi a rayuwata, sae inji gaba daya hankali na ya tashi, u know how sensitive I am...." Dariya Ahmad yyi yace "Ita Aneesar tana da irin tsaftar da kake so kenan" Abuturrab yace "Kai ma kasan da ba don haka ba da tuni ae na rabu da ita, kawai sae kaga mace ta ci kwalliya iya kwalliya ta fito amma just check inside, ni in dai mace na da tsafta ko kyanta bai fi 80% ba i will manage her..." Girgixa kai Ahmad yyi yana kallon titin gabansa, Abuturrab yace "Ba ga wajen danwaken can mun wuce ba" Ahmad bai san lkcn da yyi dariya ba yace "Aa D'an gyero ne ba danwake ba" Abuturrab dai bai ce masa komai ba da ya lura u turn yake son yi, dai dai gun awaran Ahmad yyi parking, wata yarinya ce da baxata wuce shekara sha daya ba xaune a wajen tana juya awaran cikin kasko, Ahmad na kallonta yace "Ina me awaran?" Yarinyar tace "Ta je dauko canji a gida shine tace in tsare mata, ae sunanta Aunty Jiddah, a gidansu Bibalo take..." Ahmad ya koma jikin motarsa yace "Gidan ba nisa?" Yarinya ta nuna masa wani rubabben layi dake gefensu tace "Can karshen layi ne, gidansu daya da Bibalo" Shi dai Abuturrab na xaune kujera me xaman banxa yana kallonsu, Yarinyar tace "Lah ga ta can xuwa" Duk suka kalli direction din da ta nuna, Tafe take fuskarta daure hannunta rike da yar karamin bokiti dake a rufe, wanda ke dauke da dafaffen awara, sanye take da hijab ruwan kasa da iyakarsa gwiwa duk man awaran da take tuya yayi staining Hijab din, Abuturrab ya d'an yi tsaki ya hade girar sama da ta kasa yana kallon titin gabansa, tana isowa yarinyar ta tashi tace "Aunty Jiddah gashi xa a siya a awara, da motarsu ma suka xo" Ahmad ya wara ido yace "Aunty Jiddah a bamu kalan na jiya" Ta daga kai ta kallesa tace "Na nawa?" Yyi murmushi yace "Yanda kika sa jiya" Bata ce komai ba ta durkusa ta sa masa awaran sannan ta mika masa ledan, dubu daya ya ciro ya mika mata, tana kallon kudin tace "Yanxu na kai kudi gida na amso canji, ka d'an yi hakuri sai in koma in dauko..." Ya juya ya kalli Abuturrab yace "Ko a siya maka kai ma Captain?" Kallon Abuturrab din tayi ita ma suka hada ido, yyi saurin dauke idonsa yaki cewa komai, Ahmad ya kalleta yace "Toh kinsan abinda xai faru me awara? ki ajiye canjin...." Da sauri tace "Aa ka jira in tafi in dawo ynxu" yace "To tsaya ki saurareni mana, ajiyewa xa ki yi gobe idan Allah ya kai mu na xo sai a bani awara na canjin" tace "Toh" murmushi yyi ya nufi mota rike da ledan awaran, sae da ya shiga motar ta ga ledan yajinsa bata sa masa ba ta mike da sauri tace "Kayi mantuwa" motar ta nufa tana mika ma Abuturrab ledan yajin, da mamaki yake kallonta kamar dai mugun abu take mika masa, yace "Kai!! kinga na siya abu a wajen ki ne?" wani kallon cikin ido tayi masa snn ta xaga ta mika ma Ahmad ta koma gun xamanta tana juya awaran kan wuta, Ahmad ya tada motar suka bar wajen yana hararan Abuturrab da ko a jikinsa. Jiddah na xaune a d'an dakalin kofar gidansu bayan isha, dawowarta kenan daga bakin titi ta gama tuyan dankali da take yi, ta ta takure waje daya cikin hijab din jikinta, wani matashi ne da baxae wuce shekara ashirin da tara ba xaune d'an nesa da ita, yace "Kin yi shiru Jiddah" Ta d'an kallesa tace "Nace babu wata matsala" yace "Kin tabbatar?" Ta gyada masa kai, yace "To ki ci gaba da hakuri kin ji.... In sha Allah idan....." Kamar daga sama suka ji muryar Hansai, ta rike kugu tana kallonsa da kyau tace "Ta ci gaba da hakurin gyatuminka?" Ya kalleta ya duka har kasa yace "Ina yini Baaba" Ta wani sha kunu tace "Da ban yini ba xaka gan ni algungumi?? Ta ci gaba da hakuri a saboda ana cutarta ko? Sannan ban rabaka da kofar gidan nan ba? Dama tun da naga yara sun shigo da kayan tallanta ita bata shigo ba nasan da walakin goro a miya, shine nace bari dai in leko in ga ikon Allah" shi dai bai ce komai ba ya sunkuyar da kansa, tuni Jiddah ta mike ta makale da bango gabanta na faduwa, Hansai ta cire takalmin kafarta ta jefa mata a mugun fusace tace "Wuce ciki munafuka kawai, dama ban rabaki da wnn yaron mara tarbiya ba, ni xa ki ja ma abun kunya a unguwar nan?" Da sauri Jiddah ta shige ciki Hansai ta kai mata dundu da karfi, sannan ta maida dubanta kansa tana huci tace "Wllh na sake ganin ka tare da yarinyata gidan gayun garin nan yyi mana kadan da ni da kai, idan kuma karya ne mu xuba da kai" Tana kai wa nan ta shige ciki ya mike a hankali ya bi ta da ido....
💖 Jiddatul~khair 💖✍🏻
*Ina me mika sakon ta'axiya xuwa ga Chamo bisa rashin mahaifinta da tayi, Allah ubangiji ya ji k'an sa ya gafarta masa, ya sa aljanna makoma, ya bada hakurin rashi, mu kuma Allah ubangiji ya kyautata namu Ameeeen*👏🏻
💖💖 *Jiddatul~khair*💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
2.....
Abuturrab na kwance saman gadon dakinsa yana rike da wayarsa, kunnensa sakale da earpiece, video call yake da wani matashin da baxai wuce sa ba, matashin na xaune cikin wani ubansun parlor yana cin apple, Abuturrab ya girgixa kai yana kallonsa yace "Look... I don't want to say anything about that.... idan Mummy na kusa ka bata mu gaisa" Matashin na taunar apple yace "It's already late, tayi bacci..." Abuturrab yace "It's late tunda baka son fita, so when are u coming to kd?" El-Basheer yace "Xa mu shigo kano tare da Mai martaba next week in sha Allah, probably ni xan karaso, amma sai kana nan" Abuturrab yace "In dai Friday ne ina nan in sha Allah" El-Basheer ya daga kafada yace "Ohk then" Abuturrab yace "Let me pick a call, sai da safe" El-Basheer ya gyara xamansa yana murmushi yace "The lady u don't want to talk about?" Katse call din Abuturrab yyi ya dau daya wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne hade da cewa "How u babe?"
Abuturrab ne xaune parlonsa a gidansa dake Abuja shigowarsa gidan kenan ko awa daya bai yi ba, kasancewar weather babu kyau yasa suka yi landing flight da suka yi piloting daga Lagos a Abuja a maimakon kano.... Grapes ne gabansa yana ci a hankali yana kallon wani action movie da ake yi a tv, bude kofar parlon aka yi, lkci daya ya daga kai, he was expecting no one other than Ahmad da ya sanar ma yana Abuja... Tsayinta matsakaici ne.... ita ba siririya ba ita ba mai jiki ba, ta karasa shigowa parlon ta kulle kofan tana kallonsa ta cire Nikab din fuskarta, fara ce sosai, kallonta shi ma yake, she looks so orderly from head to toe, tuni kamshinta ya baxa parlon, shi dai kallonta kawai yake ta nufesa da damuwa ta xauna gefensa tace "Why ain't you picking my call Captain?" Ya gyara xamansa yace "It wasn't long da muka sauka ai, na sa wayar a caji a can daki, how are you doing?" A hankali tace "I'm fine, ya gajiya?" Yace "Alhmdllh, where are u coming from?" Ta buda manyan idanuwanta tace "Home... kace min xaka sauka Abuja shi sa na samu na fito" ya shafa beard dinsa yace "Ahmad na hanya, bana son ya xo ya sameki nan, u know how he thinks" Ta langwabar da kai tace "Ohk, amma nace maka ina son muyi magana, ina ta bin ka yau kusan sati biyu kenan sai kace min you will be piloting today, u will be piloting tomorrow...." Da damuwa ta kare maganar, Ya kalli agogo yace "To ina jin ki yanxu, I'm sorry i forgot about that" Shiru tayi, ya kafeta da idanuwansa, sai kuma yyi murmushi ya kamo hannunta yace "Ina jin ki Aneesah" Tayi kasa da murya tace "Aliyu a gidanmu an takurani in fito da miji, kwanaki kuma na gaya maka baka ce komai ba, idan har da gaske kake kana sona what is hindering you pls?" Ya dauke idonsa daga kallonta, bayan few seconds yace "To a jira ki gama karatun mana ko? Ina ce saura kadan" Ta girgixa kai tace "Aa last week Abbana ya kara min magana, and he is very serious about it this time, don't u love me ne Aliyu?" Abuturrab ya xaro ido yace "Not at all Aneesah, kema kinsan ina sonki.... kar ki damu xa mu yi magana, yanxu ki tashi ki tafi kafin Ahmad ya xo..." Ta gyada masa kai sannan ta mike, mikewa yyi shi ma ya wuce daki ya dauko kudi ya mika mata kafin yace komai tace "Aa ni da motana na fito don't worry" Bai ce komai ba ya rakata har balcony snn ya amshi jakarta ya sa mata kudin yace "I know da mota kika xo, Chocolate din da ban kai maki ba last week sai ki siya, ba kudi ne me wani yawa ba" Murmushinta me kyau tayi, tayi kasa da muryarta tace "Thank you my Captain" ya kashe mata ido yace "C'mon babe.... Nikab din kuma na meye yau kika sa?" Tace "I just felt like" ya daga kafada yace "Alright sai mun yi waya" ta gyada masa kai ta nufi gate ya juya ya koma parlor, her neatness melt his heart always nd make him fall for her deeply. Wata dattijuwa ce xaune dakinta tare da yan mata biyu, aka bude kofar dakin duk suka daga kai, Dattijuwar na murmushi tace "Aa Abuturrab sannu da xuwa" ya karasa ciki yana murmushi shi ma, ya xauna sannan ya gaisheta da ladabi, tace "Ka dawo weekend kenan" yace "Ehh daxu muka sauka, ya karfin jikin Umma?" Tace "Alhmdllh na ji sauki yanxu" yace "Allah ya kara lfya" tace "Ameen" ledan hannunsa ya ajiye yace "Ahmad yace in taho maki da wannan" Tace "Kun hadu a Abujan kenan" Yace "Ehh kwana na biyu a can, weather babu kyau sai yau na samu muka bar Abujan xuwa kano, daga kano na biyo private jet" Umma tace "Toh Allah ubangiji ya tsare mana ku dai, Allah ya rabaka da sharrin kayan bature, haka kai kuma Allah yayi hanyar cin abincin ka" Amira tayi 'yar dariya tace "Kabu kabun jirgi Ya Abuturrab yake fa" Ta gefen ido ya kalleta bai ce komai ba, amma ya hade rai sosai, Umma tace "Ni dai Allah ya tsare min shi" a hankali yana kallon kanwar mahaifiyar tasa yace "Ameen Umma" Tace "Mun yi waya da Ahmad daxu nace masa wani awara da yake kawo min nake son ci wllh, gaba daya bani da appetite, yace kuma a hayi ake yi ko" Abuturrab ya d'an buda ido, sae kuma da sauri yace "Allah sarki, baxa a iya maki a gida ba Umma? Ae kamar yafi tsafta ayi a gida kawai" Tace "Aa da wahala, beside babu ma waken suyan a kasa, Hurairan da xata yi ma ta tafi garinsu daxu, kanninka kuma babu abinda suka iya gasu nan dai xaune, gwara kawai a siya a wajen ya fi, naga me kyau ne sosai ran da ya siyo ae" Abuturrab dai bai sake cewa komai ba, tace "Kuma yace ka san wajen, tare ma ku ke xuwa" Da sauri Abuturrab ya kalleta, lkci daya ya kirkiri murmushi yace "Anya xan gane kuwa Umma, a wani layi ne can cikin hayi fah, the place is very complicated" tace "Aa Aliyu na fa sanka sarai, ko baka sob xuwa ne, idan ma da gaske ne baka gane wajen ba ai kiran Ahmad din xaka yi ya sake maka kwatance" Bai ce komai ba amma lkci daya mood dinsa ya canxa har hakan ya kasa boyuwa a fuskarsa, sai dai bai bari ta lura ba, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna karfe biyar da few minutes, Umma tace "Ko kana da inda xaka je ne?" Ya d'an shafa kansa a hankali yace "Aa, bari in je in dawo" tace "To Allah yyi maka albarka" da kyar ya amsa da "Ameeen" snn ya mike ya fita, sosai ya hade rai bayan ya shiga motarsa, why will Ahmad tell her ya san wajen, ynxu kawai sai ya fara driving xuwa hayi wai yaje siyan awara why??? wani tsaki yyi ya tada motarsa ya bar compound din. Driving kawai Abuturrab ke yi har ya shigo hayi, he was very observant kar ya wuce inda ake suyan awaran, haka nan yake jin ransa na baci, wani ma ya gansa ya xata shi xai ci, U turn yyi ya samu waje yyi parking yana kallon yarinyar da ta mike xata shiga karamin layin nasu bayan ta sauke kaskon awaran kasa, almajirai uku ne tsaye gun da wasu yan mata biyu, Abuturrab ya dake yace "Kee" bata juyo ba don tafiyarta kawai take kuma da alama ma bata ji ba, Daya daga yan matan wajen tace "Bata ji ba, yanxu xata dawo, xata amso canji ne" Bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, bayan kusan minti biyar sai ga ta tana dawowa, kallonta yake har ta iso bakin titi, ta kalli motar sannan ta durkusa gun sana'arta, Yarinyar daxu tace "Ke jiddah jiranki ake xa a siyi awara" Sai snn ta daga kai suka hada ido da Abuturrab, ya hade giran sama da ta kasa yace "Nawa kike siyar da kayan siyarwar taki?" Tace "Wanda ya rage a nan bashi da yawa, amma ynxu xa a kawo daga gida...." Bai ce komai ba ya dauke kai, ta sallami mutanen dake tsaye a wajen, bata son komawa gida dauko danyen awaran Gwaggo Hansai ta sake koranta tace bata gama ba, kuma ta bar mata dukiyarta a titi almajirai su sace, Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motar yana kallon agogon wrist dinsa, wata yar tsohuwa ce ta xo wucewa da kullin icce a kanta, hannunta daya rike da yar leda, ta rike ha6a tana kallon jiddah tace "Har yanxu kaddararren awaran nan bai kare ba har na je inda xa ni na dawo? Ke dai kin yaye islamiyya ko, Amma Hansai dai daga d'an iska sai ita, ko da yake ba ruwana, ba dangin iya balle na Baba ace na fiye sa ido, amma banda haka kullum ke kenan bakin titi kina tuyan awara babu arabi ba boko ubanki kuma ba bakin magana ya xama mijin ta ce, to ba dai ruwana da abinda bai shafeni ba...." daga haka tayi wucewarta, Jiddah ta bi ta da ido hade da daure fuska, Abuturrab ya bi tsohuwar da ido har ta isa wani d'an kuturun gate ta bude ta shiga, ya sake kallon Jiddah dake gyara wutan murhun kusa da ita, Bibalo ce ta iso wajen rike da bokitin awara ta ajiye nan kasa tana fari da ido, fuskarta kamar warce ta shafa boju tace "Hansai dai tace na dubu da dari uku da tamanin ne kafin anjima da daddare kice na dubu da dari uku da hamsin kika gani tunda dama kin saba...." Ko kallonta Jiddah bata yi ba tayi wucewarta tana taunar cingam... Jiddah na fara xuba awaran a mai Abuturrab ya sauke glass din motarsa gaba daya yace "Ke malama jiranki nake fa, kina bata min lkci, kinsan minti nawa nayi a nan yanxu" Sai a sannan ta kallesa tace "Toh ai sai an soya ko baka ganin danye ne? Idan kuma danyen kake so ai magana xaka yi" Dauke kanta tayi ta ci gaba da abinda take, ya rungume hannu daga xaunen da yake cikin mota yana kallonta da mamaki yana sake apprehending abinda ta fada masa, sai bayan minti goma ta kallesa bayan ta kwashe awaran da ya soyu tace "To na nawa kake so?" Ya mata wani kallo yace "Me kika ce min daxu? Sake fada in ji" Ta rufe awaran da ta kwashe a takaice tace "Toh baxan siyar ba, ka tafi gaba can akwai wata me awaran a gaba" muryar Hansai taji a bayanta tana cewa "Bai soyu bane Jiddah, ko ba awaran me motar xai siya ba? Baxa kiyi da jini ba kin xauna kamar wata rubabbiya ni Hansai" da sauri Hansai ta karaso tana kallon Abuturrab tace "Alhaji yi hakuri a kwashe maka yanxu, ta nawa kake so?" Abuturrab na tada motarsa yace "Ae tace ba na siyarwa bane, in tafi akwai a gaba" Da sauri Hansai ta bude roban awaran taga soyayyen awara da ta kwashe a jibge, ga wasu ta xuba a mai, wani lafiyayyen mari ta wanke ta da shi tace "Ubanki ne xai siya wannan da kika kunshe min a gwagwa? Yo ina ma yaga arxikin siyewa tukun, muguwa, axxaluma yar bakin ciki, to Allah ya isa cutata da kike...." Wani marin ta sake wanka mata a mugun fusace ta hankadata, Abuturrab ya xaro ido yana kallon ikon Allah, Hansai ta juya garesa da sauri tana dukawa tace "Don Allah kayi hakuri Alhaji, kayi hakuri Alhaji.... wllh akwai na nawa kake so?" Kasa ce mata komai yyi, ya kalli Jiddah da ta mike tsaye tana shessheka ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta, Yace "Toh har ya kai ki mareta haka??" Hansai ta kara hankade Jiddah da karfi tace "Toh idan ban mareta ba me xan mata, wannn da kake gani makira ce me mugun hali, kuma babu abinda na rageta da shi wllh tllh" cikin tsawa tace "Baxa ki bace min daga nan ba sai na watsa maki man kaskon nan a jiki gaba daya?" Matsawa tayi daga wajen tana kuka sosai, Hansai ta kara turata tace "Muguwa bar min awarata xan karasa suyan, ki je wannan tulin wankin na tsakar gida ban son in xo in ga ko hankici a kasa, duk in samesu kan igiya da lema" Tafiya kawai Jiddah take bata ce komai ba tana kuka, Abuturrab dai dauke kansa yyi, Hansai ta marairaice murya tace "Kayi hakuri Alhaji nasan ta 6ata maka rai sosai, na nawa kake son awaran?" Yace "Dubu daya" da sauri ta shiga saka masa har ta gama sannan ta mike ta kai masa ya bata kudin ta risina ta amsa tana murmushi hade da godiya, bai ko kalleta ba ya ja motarsa ya bar wajen. Washegari Saturday Abuturrab da yamma ya shirya ya fito daga dakinsa, Umminsa ce xaune parlor da Stepmum dinsa, duk 'yan matan gidan sun tafi makaranta, Ummi ce ke magana Aunty na ta kallonta absentmindedly lkci lkci tana duba wayar hannunta, Ummi tace "Ai mu ma ba sonmu Allah ya fi yi a kansu ba, toh meye a ciki don ta shigo nan ta xauna?" Aunty tace "Haka dai kike ga babu komai a ciki, amma kina da labarin kudin cixo na makalewa jikin kaya kuwa?" Ummi tace "Gashi ai naji a bakin ki yau" Aunty na kallon Abuturrab tace "Kai ka ji fa Aliyu.... Musa me gyaran fulawa ne ya xo da matarsa da yara uku wai sun xo gaishemu daga kauye ina laifin parlan can na boys quarter da har sai sun xo nan don Allah, baka gansu ba wllh abun ba acewa komai, ni yanda kake da kyankyami ma nasan da kyar idan baka yi throw up ba, sai fa da nasa turaren wuta a parlorn ynxu...." Abuturrab ya d'an yi shiru, can kasan xuciyarsa yace for peace to reign.... Sai kuma ya dago kai a bayyana yace "To ai can din ya kamata suje dama ba nan ba Aunty" Wani kallo Ummi ta jefa masa, yayi murmushi yace "That's the fact mum, ita Aunty tsoron bedbugs take...." Aunty tace "Toh ita cewa tayi wai ba a kyauta ba, haka kawai a bada mana kudin cixo a parlor a cuce mu?" Ummi tace "Toh Allah ya baku sa'a, idan walakanta d'an Adam abun yi ne, ku ci gaba" Abuturrab ya shafa kansa ya nufi kofa, Aunty tace "Ina xa ka Captain?" Yace "Xanje wajen wani abokina he just arrived from New york...." Har ya fita parlon Ummi bata ce masa komai ba, yyi murmushi bayan ya shiga motarsa, ko ina ruwansa da 'yan kauye da suka xo da Aunty xata yi involving dinsa at d first place, girgixa kai yyi ya tada motar ya bar gidan, tafiyar kusan minti talatin yyi tunani iri iri na yawo a ransa, ba kasafai yake kwana da abu a ransa ba, infact it's very rare hakan ya same sa, amma jiya ya kwana da yarinya me awara a ransa, dalili kuwa he lead to her been maltreated, she was slapped severally because of him, he felt guilty shi ne ma yasa ya kasa samun nutsuwa a ransa, yana isa dai dai gun da take awaran ya tarar bbu kowa, alamar ba ayi awaran yau ba, yyi ta bin dirty unkept layin da kallo wanda ko mota ba lallai ya iya bi ba sbda gutters dake kwance ta ko ina, ji yyi kamar yyi amai, hankalinsa ya tashi sosai Bibalo ce ta xo wucewa fuskarta yau ma dai kamar warce tayi dambe da powder ga bakinta ya sha jan janbaki, lkci daya ya ganeta, ya sauka motarsa da sauri yana yamutse fuska yana kallonta yace "Yau babu abinda ku ke siyarwa ne?" Tayi fari da ido tana kallonsa tace "Ehh wllh, mijin kanwar babaarmu ne ya rasu yau da safe, tana can gidan mutuwar tace yau baxa ayi awaran ba" Yace "Ohk, ita warce take soyawan tana ina??" Ta wani yatsine fuska tace "Ohh wai Jiddah, tana can gida xata daura sanwan tuwon dawa, nima yanxu gidan mutuwar xa ni Baabarmu tace inje" yace "Ohkk, sai anjima" Tana murmushi tace "Toh sunana Bibalo kai fa?" Wayarsa ya ciro ya kara kunne snn ya koma cikin motarsa ya kulle, ta bi sa da ido sai bayan da yaga ta wuce snn ya bude motar ya tsirtar da yawu yana yamutsa fuska, ita kanta tsami take yi ga uwa uba warin gutter din anguwar, yaji gaba daya cikinsa ya fara hautsinewa, ya fi minti biyar xaune motar bayan ya cika Ac, har yaji ya dawo dai dai, wani yaro ya hango yana tafiya ya sauke glass ya kirasa, yaron ya xo, yana kallonsa yace "Wani gida ne ake awara a layin nan?" Yaron yace "Gidansu Bibalo ne" Ya sauko motar ya kulle sannan yace "Toh kai ni gidan" Nose mask ya sa a hanci bayan glass dake idonsa yana biye da yaron har suka isa kofar wani kuturun gida wanda shi dai ko dabbobi yake kiwo baxai sa su gidan nan ba don kilan Allah sai yayi ma dabbobin sakayya a kan ajiyesu da yyi a nan, gaba daya tsigar jikinsa tashi yake ga cikinsa da ya fara hautsinewa again, he have never been uncomfortable all his life kamar wannan moment din, yana kallon yaron da kyar yace "Shiga ka kira min me awaran" Ba musu yaron ya shiga, can sai gashi ya fito yace tana xuwa, ba a dau lkci ba sai gata ta fito, Hijab ne ta saka iya cinya sai xanin jikinta, gefen farin fuskarta duk bakin gawayi don wuta take rurawa, kallonsa kawai take alamar bata ganesa ba, ya sauke nose mask dinsa, ya cire glasses din idonsa, lkci daya gabanta ya fadi sosai bayan ta ganesa, hakan kuma bai hanata hade rai tana kallonsa ba duk da a tsorace take, shi ma dai cike da karfin hali yace "A xaton ki an mareki jiya sbda ni?" Kauda kai tayi, ya hade rai yace "Ki juyo ki kalleni ina maki magana" Ba tare da ta juyo ba tace "Ni dai ka rufa min asiri bance an mareni sbda kai ba, me ya sake kawo ka nan, in dai awara ne yau babu bamu yi ba" kallon yanda take maganan yake wanda komai ta fada sai dimples dinta ya lotsa, ta kallesa jin bai ce komai ba tace "Nace maka babu awara yau" Yace "Ohk dama sai kuna awara kenan kike wanka ki xauna bakin titi?" Ta wani xare ido tace "Ni nace maka banyi wanka ba??" Tana fadin haka ta kalli Hijab din jikinta wanda shima duk bakin gawayi ne hade da xaninta, slippers din kafarta ma duk ya tsufa, haka kawai ta ji kunya ya rufeta, ta 6ata rai tace "Ni sai kace nace ma banyi wanka ba, bayan girki nake yanxu" Bai tankata ba ya mayar da nose mask dinsa da glasses dinsa ya juya ya bar wajen ta bi sa da ido kamar me shirin kuka har ya kusa bakin titi snn ta juya a hankali ta koma cikin gidan nasu.
💖💖 *Jiddatul~ Khair*💖💖
_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
3.....
Karfe taran dare Jiddah ta fito tsakar gida ta xauna kan tabarman dake bakin kofar dakinsu, muryar Hansai ne ya kaurade d'an tsakar gidan tana ma mai gidanta isuhu masifan ita ta gaji da ciyar da shi, shi dai yana xaune baya cewa komai hakan yasa tayi ta daga murya wanda da kyar ba a jin ta a kofar gida, a hankali Jiddah ta mike ta sa takalminta ta fita gidan, wani karamin gida can karshen layinsu ta tafi, tana waige waige ta shiga zauren gidan sannan ta karasa ciki, Wata yar dattijuwa ce tsakar gidan xaune tana ma yara uku dake kwance kan tabarma fifita, Datijuwar tace "An gama tuyar kenan..." Jiddah ta kwance ha6ar xaninta ta ciro dubu biyu tace "Aa yau ai bamu yi ba Baabarmu taje gidan gaisuwa, Iyah ki ajiye min wannan Usman ne ya bani daxu mun hadu bakin titi naje auno waken suya, ki dau dari biyar, sai ki ajiye min dari biyar sai ki sa dubu dayan a asusun da nayi ma Abbana" Iyah tace "Kai Allah dai yyi ma yaron nan albarka, kwana biyu ma bai shigo ya gaisheni ba, ni da a shirye yake ai da ya fito kawai ko Allah xai yanke maki wnn shegen wahalan, kai ko da akwati daya yayi maki indai xai rabaki da Hansai yafi maki wllh, ba yace min a can cikin gari yake da iyayensa ba, nan kuma wajen kanwar babarsa yake xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai ta mike ta nufi kofa tace "Sai da safe Iyah kar baabarmu ta nemeni" Tana fadin haka ta fita da sauri kafin a lura bbu ita a can gida, Iyah ta girgixa kai tace "Allah sarki, tsakaninsa da Allah yake sonta wllh, tsorona daya makirar bakar matar can kada ta shiga ta fita ta raba su, tunda ga bibalo babu mashinshini har yanxu sai yawon unguwa unguwa take a hayi, kuma duk sa'annin juna ne, to dai bbu ruwana tunda babu dangin iya balle na baba"
Ahmad ya gama sa cover shoe dinsa yana kallon Abuturrab dake kwance kan 3 seater hannunsa rike da remote yace "Ya naga kamar duk ka damu in tafi ne Captain?" Abuturrab ya kike xaune yace "Ohh toh ka yi xamanka mana ina ruwana, dama don kace kana night duty ne yasa nake ta reminding dinka, naga it's almost 6, an kusa kiran magrib" Ahmad ya ta6e baki ya mike yace "Yaushe xa ku wuce kanon ne?" Abuturrab yace "Am off for someday kawai i just decided to be in Abuja for a while, may be on friday xan bi train in sha Allah" Ahmad yace "Ohh that's great nima friday nake son xuwa kadunan, rabona da kaduna ai an kwana biyu" Daga haka ya nufi kofa ya fita, yana fita gidan ko minti goma ba ayi ba Aneesah ta shigo, Abuturrab na kallonta yace "Sorry i kept u waiting kinsan Ahmad...." Ta karaso parlon tace "Yeah i understand..." Xaunawa tayi ta ajiye jakarta, ya dawo kusa da ita yace "Kwana uku xan yi a Abuja...." Ta wara ido tace "Har uku?" yace "Yea, ko baxa ki tayani xama ba?" Ta juya ido tace "Aa kaga Dad dinmu yana gari, sai dai in dinga xuwa Ina tafiya..." Ya jingina da kujera yace "No need inyi kwana uku kenan, gobe inyi tafiyata kaduna dama sbda ke na sauka Abuja" Ta marairaice masa tace "Haba dear, to kar ka damu i will try and be with u" Mikewa tayi tace "Me xan girka maka nasan har yanxu baka ci abinci ba" Yace "Just a cup of tea now, mun sha fruits tare da Ahmad" bude kofar aka yi duk suka juya lkci daya, Ahmad ne ya shigo parlon, kallo daya yyi masu ya nufi gun da ya mance wayarsa ya dauka, yana kallon Abuturrab yace "Shi yasa ka damu in tafi kenan" Aneesah dai daure fuska tayi, kamar baxata ce komai ba sai da ya nufi kofa tace "Ina yini?" Banxa yyi mata ya fita ya kulle kofar, Abuturrab ya shafa kansa, a hankali tace "But am afraid Captain..." Yace "You are afraid of what?" Komawa tayi ta xauna da damuwa tace "I think this is the 5th time da Ahmad ke ganina a gidanka, ina tsoron kada ya sa iyayenku su ki amincewa da aurenmu" Abuturrab yace "Ni xan xauna da ke ko wani, don kina xuwa gidana does that mean anything?" Ta girgixa kai bata dai ce komai ba, ya mike ya isa kusa da ita ya kamo hannunta yace "Cheer up dear, beside Ahmad will never do that, i know who he is" kallonsa tayi da manyan idanuwanta ya sakar mata lallausan murmushi ya kai hannu dogon hancinta yace "Basu san samun me tsafta irin ki yanxu sai mutum ya dage ba?" Murmushi kawai tayi yyi pecking cheeks dinta yace "Babu wanda xai raba mu in sha Allah" hanyar kitchen ta nufa ya bi ta da kallo. Suna fitowa train station suka nufi motar dake tsaye yana jiransu, Ahmad ya bude back seat yana kallon saurayin dake xaune driver seat yace "Sorry for keeping u waiting salem, mun hadu da wani abokinmu ne muka tsaya gaisawa" Salem na murmushi yace "Ina yini ya Ahmad" Ahmad yace "Lafiya lau, ya su Aunty" Salem yace "Lafiya kalau" Abuturrab ya xaga ya shiga front seat bayan ya gama wayar da yake yana kallon stepbrother din nasa yace "How are you" Salem yace "Fine, how was the journey?" Abuturrab yace "Cool" Driving din motar salem yyi suka fara tafiya, tunda suka hau saman titin hayi idon Abuturrab ke gefen hanya, Ta madubi ya kalli Ahmad dake danna wayarsa, da kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Yau baxa ka siyi awara ba kenan" Sai a sannan Ahmad ya dago kai ya kalli inda suke, ganin sun kusa wajen da yake siyan awaran yace "I had no intention but let me get it for Umma and my siblings" Abuturrab ya ta6e baki bai ce komai ba, Ahmad na kallon Salem yace "Kana wuce layin nan ka tsaya a layin gaba" Salem yyi parking dai dai inda Ahmad yace, Ido hudu Jiddah tayi da Abuturrab da sauri ta sunkuyar da kanta tana gyara hijab din jikinta, Ahmad ya bude motar ya sauka yana kallonta smiling broadly ya rungume hannunsa yace "Sannu me awara" Bata yarda ta kallesa ba tace "Ina yini" yace "Lafiya lau ya kasuwa?" Tace "Na nawa xa a sa maka?" Yace "Ki sa na dari biyar ko?" Satan kallon Abuturrab tayi suka sake hada ido ya dauke nasa idon yana kallon gefen hanya, ta gama sa awaran ta mike ta mika ma Ahmad, ya amsa yana kallonta, sae kuma ya juya ya kalli Abuturrab yace "Bani 1k wajenka I'm not with cash" Abuturrab bai ce komai ba, ita dai tana tsaye, can ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika ma Ahmad, Ahmad ya amso ya mika mata ta amsa ta koma ta durkusa xata dauko canji yace "Aa ki bari idan na xo sake siya, shkkn ba sai na sake bada kudi ba koh?" shiru tayi, lkci daya ta mike tace "Toh ai akwai canjinka dari biyar a wajena da ka siya ranan nan, ka tuna?" tana fadin haka ta mika masa dubu dayan, yace "Aa ni na manta..." Daga haka ya shiga mota yace ma Salem su tafi, da ido ta bi motar sannan ta koma ta xauna gun kaskon awaranta. Hansai ta rike ha6a tace "Yau naga ikon Allah, baxa ki fito ana jiranki ba Jiddah???" Sai kuma tana murmushi ta kalli Iliya dake xaune kan tabarma tace "Da yake bata yi la'asar ba kilan sllh ta fara, bari in shiga ciki dai" daga haka ta mike daga kan kujeran tsugunno da take ta shiga dakin, can taga Jiddah xaune kusa da ghana must go din kayansu tana kuka a hankali, Bude baki Hansai tayi tana kallonta, can ta karasa a mugun fusace ta fincikota ta bugata da bango murya can kasa tace "Don ubanki kina ji na kika kyaleni bawan Allah ya xo tun daxu yana jiranki? Saukansa fa kenan daga legas yace kuma anjima da daddare xa su bi tirelan kaya su koma" Cikin rawan murya hawaye na sauka idonta tace "Wllh Baabarmu bana sonsa, shaye shaye fa yake...." Bata rufe baki ba Hansai ta buge mata bakin da karfi ta rankwasheta ta hankadata bakin kofa tace "Fita kar in sumar da ke, yar bakin ciki kawai muguwa" Goge hawayenta tayi ta fita da sauri tana hadiye kukan dake son subce mata, Can nesa da tabarman ta xauna ta hade rai taki cewa komai, Iliya na murmushi da jajayen idonsa yace "Hauwa kuluwa kwandon kilishi..." Sosai ta kara hade rai, yace "To d'an kalleni mana farin cikin xuciyataa" wani harara ta xabga masa, yayi wani murmushin da lebensa da ya dafe saboda shaye shaye ga idanuwansa kamar garwashi, yace "Mun sauke wani kayan ne yau, amma mun yi lodi xa mu koma xuwa nan da bayan magariba" Ita dai ko kallonsa bata sake yi ba, ya ciro rafan 'yan ashirin ashirin guda biyu sababbi ya ajiye kusa da ita yace "Hansai tace Babanki ya bukaci in turo magabatana, to in sha Allahu ranan laraba xamu yo lodi daga lagos, ina dawowa kuma xan turo tsohona da yayansa, a nan take ma xa a bada sadaki a saka mana rana, don ni a shirye nake" Wasu hawaye suka kawo idon jiddah, ya mike yace "Kice ma Hansai na tafi sai Allah yayi mana dawowa" daga haka ya fita ta bi sa da kallo da dafaffen farin shaddan jikinsa, yana fita Hansai dake la6e tana sauraron duk abinda yace ta fito, dauke kudin tayi tace "Allah yayi masa albarka, ai iliya ba dai xuciya ba, ga masara can ya kawo mana rabin buhu, da wake xai yi kwano biyar wllh, Allah yayi masa albarka" tana gama fadin haka ta dau gyale ta fita gidan..... Jiddah ta hade kai tana kuka sosai, mikewa tayi ita ma ta fita gidan, ta shiga gidan iyah, Iyah ta dinga salati tana kallonta ganin yanda take kuka, duk lallashin duniyan nan tayi mata amma taki sauraronta balle tayi shiru, Iyah tace "Atoh bari in je in ci gaba da tankade gari na kawai" daga haka ta mike ta koma gun da take tankadenta ta xauna ta ci gaba, Da kyar Jiddah ta dago kanta bayan wani lkci tana share sauran hawayen idonta cikin rawar murya ta shiga gaya ma Iyah abinda ya faru, Iyah ta ajiye matankadin hannunta tace "To ubanki ya xama sususu shashasha kenan, banda haka meye mutum xai maida kansa kamar gunki, ko min wani irin asiri tayi masa ai bai ci ya xama kamar gunki haka ba, mutum kawai bai da amfani Allah na tuba, Hansai dai wllh baxata gama da duniya lafiya ba, me yasa bata ba ma Bibalo iliyasun ba, waye bai san iliya ba a garin nan, kawai don axxaluma ce ita ta dage sai ta hadaki da d'an gwangwan d'an shaye shaye? Ranan babu inda labari bai kai ba kan cewar Iliya ya mari mahaifinsa, ba ga uwarsa can a kana radd ba tana 6ara, kanninsa mata kuwa duk karuwanci suke kowa yasani ba wani boyayyen abu bane, ohh na shiga uku ni iyantama, kaiii Hansai da kyar taga annabin rahama, da tasan abun arxiki ne iliya wllh baxa ta so ki da shi ba sai dai Bibalo amma da yake tasan waye shi sai cusa maki shi take alallai adole...." Jiddah dai kuka kawai take, Iyah tace "To dai ba ruwana nawa ido tunda 'ya yana sun hanani shiga maganan da bai shafeni ba, barin ma na gidan Hansai matar da bata gaji mutunci ba" tana fadin haka ta tafi ta ci gaba da abinda take, a hankali Jiddah ta mike tana share idonta ta fita gidan kada Hansai ta koma taga bata nan.
Abuturrab na xaune parlon Umma tare da Ahmad suna cin abinci a tare, Umma dake xaune tana kallo tace "Toh ba dole ku yi shiru ba dama" murmushi kawai Abuturrab yyi, Ahmad yace "Ni xan kawo maki ita ai ta gaisheki Umma...." Umma ta katse sa tace "Ka kawo min wa?" Bai kuma cewa komai, Abuturrab yace "Warce xai aura wai Umma" Umma tace "Akwai wata da xai aura bayan Ramlah ban sani ba?" A tare suka kalleta, Ahmad dai ya ci gaba da cin abincin gabansa bai ce komai ba, Umma tace "Ban da dai ku yaran yanxu abinda ku ke hange daban gida bai koshi ba ai ba a kai waje ba, is there anything wrong with Ramlah da baxaka iya aure ba?" Still Ahmad bai ce komai ba, Umma tace "Ni baxan yi abinda xai cutar da kai ba, meye da Ramlan da baka sonta ka gaya min" Jin bashi da abun ce mata ta mike ta fita daga parlon, Abuturrab dai sai kallon Ahmad yake, bayan few seconds Ahmad ya dago ya kallesa, d'an murmushi kawai yyi ya ci gaba da cin abincinsa, calmly Abuturrab yace "I dont want to believe kayi ma Umma shiru ne saboda Ramlah kanwata ce" Ahmad ya d'an kallesa sai dai he was mute, Abuturrab ya girgixa kai yace "Don't be quiet because of me, coz if i were in ur shoes i wont keep quiet, baka son Ramlah ga warce kake so to meye na yin shiru? Abinda ake tunanin shi xai karfafa xumunci shi ke 6ata shi, meet Umma.... Pour out ur mind to her, tell her who u intend marrying" Murmushi kawai Ahmad yyi ya maida dubansa kan TV, mikewa Abuturrab yyi yace "Xan amsan ma Ummi drugs a pharmacy so i will be on my way now" Ahmad yace "Alright, anjima da daddare xan shigo in sha Allah" Abuturrab yace "Ok then" daga haka ya fita parlon, amma sai da ya fara shiga main parlor yyi ma kanwar Mahaifiyarsa sallama sannan ya fita gidan. Abuturrab na bedroom dinsa bayan magrib Ahmad ya shigo, Ramlah ce biye a bayansa hannunta rike da cup din shayi da xata kai ma yayanta kamar yanda ya sa ta, Ahmad ya xauna gefen gado, Abuturrab na kallon Ramlah bayan ta ajiye shayin yace "Aunty ta dawo?" Ta girgixa kai tace "Aa bata dawo ba" Yace "Ohk" Ta kalli Ahmad dake danna wayarsa tace "Ya Ahmad su Umma fa?" Ya kalleta yace "She is fine, ya school?" tace "Lafiya lau, ya su Siyama" Yace "Alhmdlh" tace "Kai ma in hado maka shayin?" Yace "Aa sai kace nine Abuturrab" Dariya tayi, Abuturrab dai bai ce masu komai ba, ta nufi kofa, bayan ta fita Abuturrab yace "Mun yi waya da El-Basheer daxu yana gaisheka" Ahmad yace "Oh Yarima, kwana biyu bamu yi magana da shi ba ma" Abuturrab yace "Xai shigo Kadunan amma may be kana Abuja lkcn" Ahmad yace "Allah sarki, Allah ya kawosa lfya" Abuturrab yace "Did u talk to Umma?" Ahmad yace "About what?" Abuturrab yace "Ohh har ka manta" Ahmad yyi murmushi yace "No i dont need to, tunda ga abinda Umma take so, in sha Allah hakan xa ayi" Abuturrab ya mike a fusace yace "What nonsense, why will u say so bayan kai ba son hakan kake ba" Ahmad yace "Tunda Umma tana so nima dole in so" Abuturrab yyi masa kallo yace "Why just speak like an illiterate now?" Ahmad yace "Wait Captain, is there anything wrong with Umma's choice?" Abuturrab yace "Yes tunda ba son choice din kake ba" Dariya Ahmad yyi yace "Mun ta6a magana da kai nace bana son Ramlah? Asali ma duk cikin cousins dina babu wanda muke shiri da irin Ramlah, Ramlah was kinda brought up in our home since she was 2, tunda takwaran Umma ce kuma rainonta ce ita shi yasa take son ta hadamu, fine if Ramlah is okay with that ni bani da damuwa" Tsaki Abuturrab yyi ya koma ya xauna, Can yace "Ita kuma Maryam din dama yaudaranta kake kenan?" Ahmad yace "Idan wani xai min wnn kallon banda kai Abuturrab, it's just that my Umma's choice is my choice" Abuturrab ya jawo wayarsa dake ring ganin Aneesah ke kiransa ya katse ya shiga kiranta, Ahmad ya mike yace "Bari in gaida Ummi" daga haka ya fita dakin....
07087865788✍🏻
💖💖Jiddatul~Khair💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
4......
Jiddah ce xaune kusa da Abbanta dake kwance tsakar gida saman tabarma da wani pillow da ya yakune, hawan jininsa ne ya tashi tun daren jiya, magunguna ne ajiye daga gefensa wanda da kudin da take tarawa wajen Iyah ta samu ta siyo masa magungunan, ko bi ta kan inda ta samo maganin Hansai dake ta yankan dafaffen awaranta bata yi ba, Sosai Abban nata ke jin jiki shi yasa duk hankalinta ya tashi, Hansai dai sai ta6e baki take, lkci lkci kuma tayi tsaki har ta gama abinda take yi ta mike tace "Yau ai sai ki xuba ruwa kasa ki sha tunda baxaki siyar min da awara ba kin wani makale kusa dashi wai bai da lafiya, to a duniyar nan yanxu wake da lafiya? Kowa ba lallaba kansa kawai yake yi ba, idan ka xauna ka fake da ciwo ai sai yunwa ta kar ka, ko da yake shi kwanciyar tasa ma da rashinta duk daya ai, Atoh duk daya mana tunda mace ce ke rike da gidan" Daga haka ta daura roban fentin dafaffen awaranta a kai da jarkan man gyada tace "Idan kinga dama in Bibalo ta dawo kice ta sameni bakin titi, tun safe ni ko ganin gilmawarta ban yi ba ko ina taje oho" kofa ta nufa da xaninta da yyi dukundukun xata fita, Jiddah ta goge hawayen dake makale idonta tana kallon Abbanta a hankali tace "Sannu Abba...." Bai iya yace mata komai ba, Hansai ta saka kai xata fita suka kusa cin karo da Iyah, Hansai ta koma baya tana washe baki tace "Sannu da xuwa Iyah" Iyah tace "Yauwa Hansatu, ya me jiki naji ance Isuhu bai ji dadi ba" Hansatu tace "Wllh da sauki kuwa, ga magungunan da na siya masa can ma, to ko kwayan hatsi bamu da shi a gidan shine nace Jiddah ta xauna tare da shi in fita in siyar da awaran nan, ba wata me yawa bace ta dubu uku ce kawai don dai a samu na cin abincin yau da gobe, kinga ai ba a xauna dukka ana jinya ba" Iyah tace "Gaskiya ne, Allah dai ya rufa asiri, yi maxa yamman ma tayi, Allah ya bada sa'a" Hansai tace "Ameen" Daga haka ta fita gidan, Iyah ta karasa ta dau kujeran tsugunno ta xauna tace "Sannu Isuhu" Da kyar ya gyada mata kai, Iyah ta rike ha6a tace "Farin mutum bafillatani duk ya kode kamar bai ta6a haske a rayuwarsa ba, Allah dai ya baka lafiya ya rabaka da cutan nan" Nan ma dai ya gyada mata kai, Iyah ta kalli Jiddah tace "Ya sha magungunan kuwa?" Jiddah ta gyada mata kai, Iyah tace "Toh Allah ya yaye masa" A hankali Jiddah tace "Ameen" Iyah ta bi d'an kuturun tsakar gidan wanda hansai ta mayar kamar na mahaukata da tarkacenta da kallo snn ta ta6e baki ta maida dubanta kansa tace "Amma kana ji na Isuhu" shi dai kallonta kawai yake yana numfashi da kyar, tace "Don muhammadurrasulillahi S.A.W.... ba a dai san gawan fari ba amma ka dubi Allah ka gaya ma wnn yarinya Jiddah inda dangin uwarta suke taje ta nemo su a fadin duniyar nan" Ya sauke numfashi da kyar muryarsa baya fita sosai yace "Iyah Mahaifiyar Hauwa 'yar Nijar ce...." Iyah tace "Kullum xancen ka kenan Mahaifiyarta yar Nijar ce, to a Nijar din bata da dangi ne Isuhu?" Ya sauke wani numfashin yace "Ni dai kowa yasan ni maraya ne ina almajiranci Uban gidana Alhaji Auwal ya daukeni ya rike kamar d'an sa sbda duk safiya xan wanke masa mota in share masa tsakar gida har ma in je masa aike, ni ban san garinsu Amina mahaifiyar Jiddah ba a Nijar din, ni dai tace min su 'yan Nijar ne, rana daya uwarta ta daukota suka dawo Nigeria wanda babu tantama kurciya aka mata, ko da suka dawo Nigeria basu walakanta ba don wata Hajiya ta amshe su hannu bibbiyu kakar Jiddah na masu aiki...." Iyah tace "To kai duk a ina kasan wannan labarin da ka kunshe ma cikin ka isuhu?" Yace "Mahaifiyar Jiddah ta bani labarin" Iyah tace "Toh ina ji" a hankali yace "A haka har Allah yayi haduwata da Mahaifiyar jiddah ranan naje kasuwa mai dakin uban gidana ta aikeni, ita kuma Jiddah Mahaifiyar ta aiketa, ban wani sha wahalan samun Mahaifiyar Jiddah ba sbda uban gidana ne ya tsaya min kan komai, a gidan da muka xauna wanda uban gidana ya kama mana haya a lkcn, muka hadu da Hansatu tana xuwa gun kanwar Mahaifiyarta, suka shaku sosai da Amina Mahaifiyar Jiddah duk da ko a lokacin Hansatu xata yi Shekara kusan talatin da wani abu amma bata ta6a aure ba, a lkcn kuma aurenmu ko shekara bai yi ba da Aminatu, ni dai nasan watarana na dawo daga kasuwa Amina ta sani gaba ai sai na auri Hansatu sun xauna tare yau Hansatu ta 6ata labarinta da irin tsananin da ake mata a gida duk don bata samu mijin aure ba kuma taji tausayinta sosai, wllh wllh Auren Hansatu kaddara ce daga Allah amma Amina ce sila, ta takurani, hatta iyayen gidana basu amince da auren ba a sannan, amma sbda son da nake ma Aminatu bana kuma son bacin ranta na lallabasu sai dai sun nuna min babu ruwansu a batun auren kuma babu biyar dinsu a auren, yawanci xannuwan da nayi ma Hansatu na lefe ma xannuwan Aminatu ce ta bani, kinji dalilin auren Hansatu, ni baxan ce sun yi xaman tashin hankali ba gaskiya don ko hakan ya faru Amina bata ta6a nuna min ba don har yau ban ga mace me hakurin Amina a duniya ba duk da xaman mu bai yi nisa ba don ta haifi Jiddah da shekara daya ta rasu, a lkcn Hansatu na da cikin Bibalo kin ji yanda rikon Jiddah ya koma gun Hansatu tun ba a yayeta ba, Uban gidana ya so Jiddah ta dawo wajensu bayan rasuwar Mahaifiyarta amma Hansatu ta saka mana kuka xa a rabata da jiddah, ita a bar mata ita xata raineta kamar yanda xata raini Habiba su taso tare, hatta Mahaifiyar Amina ta so amsan Jiddah bayan rasuwar 'yar ta, Amma Hansatu ta bi ta da dadin baki taki bata, ashe ita ma ba mai tsawon rai bace, don bayan rasuwan Amina da shekara uku ita ma ta rasu...." Jiddah dai kallon Abban nata kawai take don bai ta6a bata labarin nan ba sai yau, ta dai sha jin mutane na cewa Hansatu ba baabarta bace amma bata yrda sbda ita ta taso ta gani, Iyah sai girgixa kai take tana cewa "Allah me girma, ashe dai Hansatu baxata wanye lafiya da duniya ba... wuhuhu, Allahu akbar, To su iyayen gidan naka suna ina suka bar ka ka walakanta ka gantale haka, ai ko ba komai nasan sun ci moriyarka dai ba adadi" lkci daya Hawaye ya kawo idonsa yace "Hansatu ce dae ta rabamu, Alhaji Auwal ya bani kudi miliyan 2 in kai masa banki ban samu xuwa bankin a ranan ba sbda ruwan da aka yi kamar da bakin kwarya ina tsoron bin hanya da kudi haka, sae na dawo gida da kudin, Hansatu ta xare dubu dari biyu a ciki, kudi ko sama ko kasa, sbda Alhaji Auwal din yace bai yrda ba bayan na sanar masa 6atan kudin da naga bani da mafita, shine matar nan taje har gida ta ci masu mutunci ba na wasa ba, basu yi mata komai ba amma shine har yau, kudi kuma yace ya yafe min ya dai amshi sauran kudinsa, to kinji abinda ya faru... Wnn gidan ma da muke ciki ai shi ya siya min wllh, yau shekara bakwai kenan da ya bar kaduna suna Abuja da iyalansa" Iyah tayi tagumi tace "Yau naga tsinanniyar mata, dama ance ita ta talauta ka da ba haka kake ba, ilai ga magana ta fito...." Yace "Duk ta bi ta siyar min da filayena biyu da gonata daya, da wnn gidan kadai na tsira...." jiddah ta goge hawayen dake makale idonta duk jikinta yyi sanyi, Iyah tace "In sha Allahu xa mu ga karshenta kuwa, abinda Allah baya bacci, ynxu damuwata inda wnn yarinya jiddah xata samo danginta, to gidan da kakarta tayi aikatau a ina yake?" Yace "Wnn ai sun fi shekara sha biyar da barin kaduna, idan ko ba barin kaduna suka yi ba to sun sauya wani gidan ne don xuwana biyu duk akan haka amma aka sanar min sun tashi" Iyah tace "Abu ya lalace kuwa, banda haka ai baxata rasa basu labarin kanta da garinsu ba, kaga da ko su sai suyi ma jiddah hanyar xuwa dangin uwarta ita ma ta dawo mutum, amma ina mutum a nan ba dangi" girgixa kai kawai yyi, Iyah tace "Toh Allah ya rufa asiri, xaka ci tuwon masara da miyar kubewa in tafi in yi maka yanxu?" Jiddah tace "Xai ci iyah, tun safe bai ci komai ba sae kunu da ya sha" Mikewa Iyah tayi tace "Toh bari in je in hura gawayi yanxu ina da komai a gida, yanxun nan xan gama, to ae mayyar ba wani damuwa da rayuwarsa tayi ba, ehh Hansatu ba" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta ta ido har ta fita, murya can kasa yace "Kiyi ta hakuri kin ji Jiddah, wataran sai labari, nasan ban ta6a cutan wani tsawon rayuwata ba, ina fatan Allah ya dubi hakan, albarkacin hakan kada ya bari ki walakanta, Allah ya yanke maki wnn wahala da kike sha cikin gaggawa yayi maki abinda yafi alkhairi a rayuwarki, ina maki addu'an Allah ya baki hakuri da juriya da kauda kai irin na Mahaifiyarki Amina, kar ki kaga ana maki abubuwa ina shiru Jiddah, har gobe bani da kamar ki a duniya jiddah tun bayan rasuwar mahaifiyarki, Ban yi shiru a kan batun aurenki da wannan takadirin yaron da take ba, don har yanxu ban furta komai ba hakan ba yana nufin na aminta da auren bane, idan anyi duniya domin manzon Allah xaki auri mijin da xai kula dake yayi maki abubuwan da mu muka kasa maki, xaki auri wanda xai rike ki bisa gaskiya, wanda xai yanke maki wannan wahala da kike ciki in sha Allah" Hawaye ya shiga sakko mata ta kasa ce ma Abban nata komai, amma taji hankalinta ya kwanta sosai, da kyar ya ci gaba "In sha Allahu wannan takadirin ba mijin ki bane Jiddah..." ta gyada masa kai tana gyara masa kwanciyar kansa, ya lumshe ido yace "Tashi ki je kiyi wanke wanken da ta sa ki kar ta dawo kin ji" Ta goge idonta cikin sanyin murya tace "To Abbana Allah ya baka lafiya" Yace "Ameen Jiddah" Mikewa tayi ta tafi gun uban kwanukan da Hansai ta tula bakin kwararo k'uda sai fareti suke a kai, sbda yawan kwanukan sai kusan la'asar ta gama ta mike ta dau buta ta xuba ruwa jin ana kiran sllh ta ajiye inda Abbanta ke alwala ta koma kusa da shi ta durkusa tace "Abba ka daure ka tashi kayi alwala" Jin yyi shiru ta kai hannu jikinsa tace "Abba la'asar yyi...." hannunsa taga ya xamo kasa daga jikinsa, ta kamo hannun tace "Abba...." Shiru bai amsa ba, komin bacci ko rashin lafiya shi din ba me nauyin bacci bane, hakan yasa ta sake kiransa nan ma shiru, jijjigasa tayi taga dayan hannun ma ya xame, bata san lkcn da ta kwala wani ihu da karfi ba kan kace me mutane suka shigo gidan da sauri jikinta na rawa tace "Ku taimakeni Abbana yaki tashi" Wani makocinsu wanda har da shi ya shigo ya kai hannu jikinsa lkci daya ya saki salati yace "Isuhu ai rai yyi halinsa" Daga wnn Jiddah bata sake jin komai ba ta dai bude ido ta ganta kwance saman tabarma dare yyi ga mutane cike tsakar gidan. Bayan kwana uku, Jiddah na xaune tsakar gida da idonta da yyi bulu bulu ga wani rama da tayi don har sannan bata iya cin komai, Hansai sai faman yankan awara take tana cewa "Ke kadai aka ma mutuwa idan ba munafurci ba, Ita Bibalo ba ubanta ne ya rasu ba halan, munafuka kawai me neman suna, kin taso kin fita da kayan awara bakin titi ko sai na taso na nakada maki shegen duka, idan bamu yi awara ba yau ubanki xa mu kwakulo a kabari mu ci?" Hawaye kawai Jiddah take ta mike ta dau kaskon awara da coal pot da wasu kananun kayan ta fita xuwa bakin titi, Hansai tace "Ni wllh idan ba binsa kabarin kika yi ba bansan kina yi ba, bayan mutuwan da yyi ya bar ni da wahalan yi maki kayan aure duk da dai katifa da robobin kitchen kadai Allah xai hore min inyi maki, to ince me wnn wahalan da ya bar ni da shi, ina ta sintirin xuwa gidan Saude xaman makoki miji ya rasu ashe nima nawa na kan hanya xai tafi ya bar ni da wahala, to banda dai dama ya gaji da duniyar daga tashin hawan jini sai mutuwa Allah na tuba, shi dai yaji da munafurcinsa kawai dama ya gaji da duniyar ne, to ba dai ya mutun ba dai ai shkkn, yanxu ga aurenki dake ta karatowa ya gudu ya bar ni da wahala" A haka jiddah ta dawo ta sameta tana ta kumfar baki ta dau robon awaran ta fita, har sannan jiddah taki dawowa dai dai, gani take kamar mafarki take xata farka taga Abbanta bai rasu ba, har yau da aka yi uku abincin kirki ta kasa ci, don ma Iyah na tsareta sai ta sha kunu, banda tsine ma Hansai babu abinda yan anguwan ke yi ganin Jiddah bakin titi tana tuyan awara, daga mutuwar miji da kwana uku har ta ci gaba da awaranta wnn wani irin xuciya gareta, yawanci duk Jiddah ake tausayi don shkkn ta xama marainiya gaba da baya yanxu.... Abuturrab na kallon Ramlah dake yankan ma Umma Fruits yace "Umma ta ci abinci kuwa?" Ramlah tace "Aa bata wani ci ba, Amma Aunty Zainab taje gida xata yi mata tuwo yanxu" Ummi dake xaune kan farin kujera a ward din tace "Ga farfesun hanta ma da nayi mata bata ci ba" Abuturrab ya kalli Umma dake kwance da drip a hannunta yace "Umma ko a siyo maki awara?" Ta d'an yi shiru kafin a hankali tace "Toh Allah ya sa in iya ci, bana jin dadin komai a bakina" Ummi tace "Toh wannan ai dole ne Ramlah... Kawai daurewa xaki yi kici ko kadan sai kiji jikin ya maki kwari" Abuturrab yace "Toh bari in je in siyo maki yanxu" Daga haka ya fita, Slowly yake driving din har ya karasa hayi, dai dai u turn din wajen ya juya ya nemi waje yyi parking yana kallonta ta glass din motar, kanta a kasa tana juya awaran cikin man kaskon a hankali, ya sauke glass din motar yace "Ki bani awaran dari biyar" Dago kai tayi tana kallonsa, kallon idanuwanta da suka kumbura yyi, bata ce komai ba ta saka masa awaran yanda yace snn ta mike ta isa gun motar tana mika masa ledan, bai amsa ba yace "Kukan me kika yi haka??" Ta sauke idonta kasa, lkci daya xuciyarta yayi mata rauni wasu sabbin hawayen suka cika idonta, da mamaki yake kallonta, bata san lkcn da ta fashe da kuka sosai ba tace "Abbana ne ya rasu" Daga nan kuma kamar warce aka tunxura ta jingina da motar ta dinga rera masa kuka, a hankali underneath his breathe yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Kuka kawai take so painfully, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ya bude motar ya sakko ya xagayo yace "Yaushe ya rasu?" Cikin kuka sosai tace "Yau aka yi uku" Da mamaki yace "Shine kika fito suyan wannan abun" Cikin rauni tace "Baabarmu ce tace sai na fito" Dauke kansa yyi, can yace "Awaran na nawa ne gaba daya?" Ta juya ta kalli roban awaran cikin shessheka tace, wai na dubu biyar tace min" Ya girgixa kai bai ce komai ba, can ya juya ya bude motarsa, kudin da ya ciro xa ayi masa delivering eye glasses da yyi ordering online ya dauko a motar, kamar wanda ya tuna wani abu ya fasa fito da kudin a haka sai da ya saka a wani ledan turare snn ya juyo yana kallonta, har sannan kuka take sosai, ya mika mata ledan kudin yace "Gashi ki kai mata kice ance kada ki sake fitowa sai an kwana biyu" Kallon ledan ta dinga yi da yyi mata dishi dishi sbda hawayen idonta ya kamo hannunta ya mika mata ledan ya amshi ledan awaran ya saka a mota yace "Allah ya gafarta masa" daga haka ya xaga ya shiga motarsa ya tada ya bar wajen, share hawayen idonta tayi ta leka ledan taga dari biyar sababbi dal a rafe, sosai gabanta ya fadi, ta kasa kwakkwaran motsi, wani almajiri ne yace "Awaran ki na konewa" Da sauri ta juya ta sauke awaran, ta xauna xuciyarta na bugawa da karfi, muryar Hansai taji a bayanta, Hansai ta ajiye bokitin wani awaran tana cewa "Ta dari biyar ce wnn, gaba daya ya kama dubu biyar da dari biyar...." ganin awara ya kone a mai tayi tsit tana xare ido, lkci daya ta saki salati da karfi tace "Na shiga uku awaran kika kona min Jiddah???" A mugun tsorace Jiddah ta mika mata ledan kudin tace "Baabarmu wllh wani ne ya xo ya kawo min wnn wai in kai maki kar mu sake fitowa sai bayan kwana biyu...." Hansai ta karbi ledan tana duba ciki da sauri, xaro ido tayi tana kallon tulin kudin cikin ledan, lkci daya ta dinga bin anguwan da kallo, murya can kasa tace "Daga ina yake?" Jiddah ta buda hannu har sannan jikinta na rawa tace "Wllh ban sani ba" Hansai tace "Dauko jarkar man da roban awaran mu wuce gida ai ya kare ma" A haka Jiddah ta kwashi kayan awaran ta bi bayan Hansai dake tafiya da sauri da sauri, A bakin kofar dakin Hansai Jiddah ta makale tana kallonta tana ta faman kirgan kudi duk ta hada xufa, har ta gama kirgen tana xaro ido tace "Dubu dari a wannan marran ni Hansatu, Allah yyi ma bawan Allahn nan albarka, yanda ya taimaki marayu Allah ya taimakesa haka shi ma, kaiii a duniyar nan ma dai xaman wasu toshe hanyar alkhairi kawai yake, banda haka daga rasuwan Isuhu kamar daga sama Allah ya jefo bawan Allah ya bamu dubu dari cif cif, yaushe rabon inga dubu ashirin da idona ni Hansatu" Jiddah dai ta sunkuyar da kanta xuciyarta na mata xafi bata ce komai ba, Hansai tace "Maxa ki sa ruwa kiyi wanka kema ko kya ji dadin jikin ki, kinga dai mutuwar nan alkhairi ne garemu sai kiga Allah yyi ta bude mana hanyoyi iri iri, aa ni dai wllh gwara da ya bamu hanya mu san me muke ciki a duniyar, to da ya baki kudin sai yace maki me?" Cikin sanyin murya tace "Yace kar in sake fitowa sae bayan kwana biyu" Hansai ta fashe da kuka tace "To dama banda talauci me xai sa mijina ya mutu in fara awara a ranan da aka yi sadakan uku, ai sai dai talaucin dama" Ta kara rushewa da kuka tana matsar kwalla da bakin xaninta, juyawa jiddah tayi a hankali ta bar bakin kofar tana dada jin mutuwar mahaifinta kamar a mafarki wanda hakan yasa hawaye kawowa idonta.
*Still on free pages kar labari ya dauko maku dadi ku ga an datse don free pages din ba yawa ehee, u can proceed with payment sbda kawai a ci gaba ba sai an tsaya ba after free pages din, that is idan kunyi payment kenan fahh....*👌🏻
Tunda dai littafin me sunana ne wannan kunsan baxan gantalar da littafin ba, don haka kar kuyi fargaban komai ku ma baxan gantalar da xuciyoyin ku ba a gaskiya😹😹
Ping 07087865788 for payment details.
💖💖 Jiddatul Khair💖💖
_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
5.....
Alhaji Usman ne xaune parlonsa tare da Hajiya Hauwa, ya ajiye wayar hannunsa yace "Toh ke ya kika ga Madam?" Ummi tace "Aa in dai tana so babu wani matsala daga gareni sai yanda kace" Ya jinjina kai yace "Toh shi Ahmad din ne yace yana sonta?" Ummi tayi murmushi tace "Toh wannan kuma gaskiya i can't say Alhaji" Abba yace "Toh sai na fara magana da shi Ahmad din da Ramlah, don ke da kanwar nan taki na lura kanku kadai ku ka sani" Yana murmushi ya kare maganar, tayi 'yar dariya tace "Aa ai baxa ayi masu dole ba dama" Yace "Toh Allah yayi xabi mafi alkhairi dai" Ta amsa da Ameen. Bayan sati daya aka saka ranan bikin Ahmad da Ramlah wanda xa ayi bayan wata uku. Abuturrab na gidansa na Abuja tare da Ahmad da shigowarsa gidan kenan, banda kamshi bbu abinda ke tashi a gidan, ko ina so very neat and tidy kai kace da mace a gidan, Ahmad ya fito daga kitchen rike da cup din coffee yana juyawa da spoon yace "Matar gidan bata iso ba har yanxu kenan" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa, Ahmad yyi wani dariya yace "Ka gama yaudaran yar mutane daga karshe ka samu yar sweet sixteen ka aura abun ka" Abuturrab yace "Sai ince na auri me? Ashe xaka sha mamaki kenan idan kaga na auri Aneesah" Ahmad yace "Gaskiya don ban ta6a sawa a rai cewar xaka auri Aneesan nan ba, ku dai gama holewan ku tayi auren ta kayi naka" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba ya maida hankalinsa kan TV dake aiki, Ahmad ya nemi kujera ya xauna yace "To in har da gaske sonta kake da aure kayi magana mana a saka mana rana daya gaba daya" Abuturrab that is already getting pissed up yace "You dont have to tell me what to do with my life dude..." Dariya Ahmad yyi yace "Of course, especially in a case like this" Tsaki Abuturrab yayi ya mike ya dau wayarsa ya wuce daki ya bar masa parlon... Ahmad na gama shan coffee din ya mike ya bisa xuwa dakin, xaune ya samesa da wayarsa yana magana alamar video call yake, Abuturrab ya kallesa sannan yace "Toh gashi nan ya shigo sai ku gaisa" Ahmad yace "Waye?" Abuturrab ya mika masa wayar, amsa yayi yana kallon screen din, suna hada ido ya buda baki yace "Mutanen Egypt ne dama" Bai rufe baki ba tace "Waye wannan???" Dariya yayi yana kallon uban glass da ta saka a ido fuskarta duk ya cika screen din wayar yace "To glass din kuma da kika maka haka wa ya ara maki?" Ji yayi tana cewa "Farida xo ki mayar min da fuskar Aliyu don Allah, kamar ya shiga wani kiran fuskar wani nake gani" Wata yar budurwa ce ta leko wayar ta xaro ido tace "Lahh Hajja ai Yaya Ahmad ne" Warce ta kira da Hajja tace "Kaji wani xance to ni ina ruwana da shi xa a sako min fuskarsa, ki mayar min da fuskar Aliyu nace, idan kuma baxai yiwu ba ki kashe kawai, waye kuma wani Ahmad, ni na san shi" Ahmad dake ta dariya yace "Nima ae ba saninki nayi ba kawai miko min wayar aka yi" Hajja ta sake wayar ya fadi tace "Ni dai na shiga uku, A gaskiya wannan ai walakanci ne da cin fuska, ya xan dinga magana da Aliyu fuskar wani kato ya fito, wayar taki ce ta lalace ko wa'adin da aka debar mana na magana da Aliyun ne ya kare aka sako min fuskar wani can" Farida ta ma rasa abun cewa sai dariya take, Ahmad ya katse wayar ya jefa gefen Abuturrab shi ma yana dariya, Abuturrab yyi murmushi yace "Yanxu fa take tambayar ka shine ka shigo na baka fa...."
Iyah ce tsaye kan jiddah dake ta kuka kamar an aikota, A fusace tace "Toh meye amfanin wnn shegen kukan da kike ne wai, nace ki hado tsummokaranki in sa ki mota tunda da kudin ki a hannuna ki tafi legas wajen Salame kawai" Jiddah na kuka tace "Toh Iyah idan iliyan ya hadu da ni a legas din fa? Shi ma fa a can yake aiki ai" Iyah tace "Legas din bai fi Najeriya girma ba aka ce maki, ta ina xai ganki a gari me girma haka" Shiru Jiddah tayi tana kallonta wasu hawayen na sauka fuskarta, Iyah tace "Ni dai ba ruwana ina kokarin ganin na rufa maki asiri kar a aura maki takadiri kina min gardama, hakkin makotaka fa nake son in fita, banda haka me na hada dake Jiddah?? Sannan ni ce mutum ta karshe da Allah ya ba iko nayi hirar karshe da mahaifinki kafin ya mutu, to sai in xuba ido ki tagayyara ya kullace ni duk inda yake?" Jiddah ta sauke idonta dake xuban hawaye xuciyarta yyi rauni, Iyah tace "Atoh babu ruwana wllh, ba dai gobe xata tafi kasuwar tasha siyo kayan sana'arta ba, sai ki shirya tana fita in kai ki tasha kawai, ko da tirela ne sai ki bi xuwa legas din, amma idan ba haka ba shkkn rayuwarki ta lalace idan aka aura maki Iliyasu" Iyah na kai wa nan ta tafi gun tuwonta dake kan murhu tana cewa "Na fita hakkin ki duk da ba dangin iya ba na baba, amma hakkin makotaka fa??" Jiddah dai gaba daya jikinta yyi sanyi, she is too young to even think straight for her age, hakan yasa taji gwara kawai ta gudun don gashi har an xo an sa mata rana wata daya dai dai da Iliyasu a yau.
Aunty na kallon Nafisa, cike da fada tace "Tashi ki fita ki ban waje" Ba musu Nafisar ta mike ta fita kamar xata yi kuka, Aunty ta dubi Abuturrab dake dakin yana kallonta tace "Wllh baka gansa ba Captain, ni dai ban ta6a ganin haka ba, banda yarinta da dolanci me xata yi da shi don Allah??" Abuturrab na cin Apple din hannunsa yace "Meye da shi wai Aunty?" Cike da takaici Aunty tace "Don dai sai da yamma ka dawo jiya da ka gane ma idonka...." Yace "Aa ni a garin nan ma nayi sllhn juma'ah, private jet muka biyo daga kano, sha biyu da rabi ina kaduna..." tace "To a ina ka tsaya sai bayan la'asar ka dawo gida?" Yace "Muna tare da wasu abokanmu" Aunty tace "Shi yasa, ai da ka gansa wllh... Muna xaune fa jiya da safe kamar abun arxiki tace mana wai Salis yace xai xo bayan an sakko juma'ah mu gaisa, na xata abun arxiki ne har da sa masu aiki su tayata yi masa snacks iri iri wai ashe gantalalle xata kawo mana..." Abuturrab dake ta kallonta yace "Toh meye da shi baki fada min ba har yanxu" Tace "Toh kaga Captain tun daga bakin titi da kafa ya tako har nan, ashe ko motar ma bashi da, sai kaga wani yakunannen yadin da ya sa bbu gugan arxiki, kana ganinsa dai kaga 'ya yan ya ku bayi, ni ko a raina nace ko ina wannan yarinyar ta samo mutumin nan haka, ni wllh a bakin stairs na tsaya amsa gaisuwarsa ban yarda na karaso parlon ba" Abuturrab yyi murmushi ya kai Apple dinsa baki yace "Wani sana'a yake yi?" Wani kallo ta jefa masa tace "Sana'a, wa ke ta wani sana'arsa banda abun ka, ko ka mance da wannan saying din that goes thus... The way u dress will be the way u will be addressed??" Abuturrab ya gyada kai kawai bai ce komai ba, tace "Wllh na sake ganinta tare da shi Allah sai na ji mata ciwo kowa ma ya huta, ita kuma Ummi da taya bera 6ari sai wani nan nan take da shi, tarba dai yanda kasan mutumin arxiki haka tayi ma yaron, ni ko kunya kamar in nutse wllh, Salem kuma inda ya burgeni ko kallonsa bai yi ba da ya shigo parlon kawai yyi wucewarsa daki..." Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh Allah ya kyauta...." Tace "Ameen sai ka kirata and talk sense into her head... Ba ni xata kwaso ma abun kunya ba" Mikewa yayi, tayi saurin cewa "Captain ban kai ka kaje kaga filin da na siya ba ae" Yace "Xuwa gobe in sha Allah" tace "Lahadin xaka koma aikin?" Yace "Idan Allah ya yarda" Tace "Wancan satin kasa nayi maka tamarind drink baka dawo ba..." Ya shafa kansa yace "Wlh daya daga pilot din da xai yi piloting jirgi daga lagos xuwa port Harcourt bai ji dadi ba shine ni nayi, wnn satin ma ban yi niyyar dawowa ba coz i was so stressed out during the week" Tace "Gashi ko ka xo kadunan ba wani hutawa kake ba tunda ba xama kake gida ba" yyi murmushi kawai, tace "Sai kaji an sa ranan Ahmad da Ramlatu" Yace "So Abba told me" Tace "Atoh bai fi mata ba, yar uwarta ta tsaya kula ya ku bayin garin nan, Ahmad ai d'an gayu ne d'an boko ga hankali da nutsuwa duk da dai ni ba wani shiri muke da shi ba, though auren xumunci ne ma ai amma gwara hakan, Nafisa ma tace min ai tasan tsohuwar Budurwarsa Maryam islamiyyar su daya kafin ta canxa islamiyyan" Abuturrab ya nufi kofa yace "To Allah ya kyauta" Tace "Bayan an gama da na Ramlah sae a dawo naka da Aneesah ko?" Murmushi yyi yace "Allah ya kai mu lokaci" Daga haka yyi mata sallama ya fita yana duba agogon wrist dinsa, kira ne ya shigo wayarsa, ya duba ganin Aneesah ya daga ya kai kunne yace "Don't tell me har kin sauka?" Tace "God!!! Nima Don't tell me baka fito ba Captain" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ban dade da shigowa gida ba... But in few mins time xan karaso I'm sorry" Bai jira me xata ce ba ya katse wayar ya fita ya hau motarsa.... Tafiyar minti ashirin ya kai sa train station, murmushi yyi ganin yanda ta hade rai tana tsaye daga nisa, abaya ne baki jikinta da yyi matukar amsan farin fatarta, ja da bakin lallen dake hannunta ya kara contributing wajen haduwarta a lkcn, she looks so sweet, mutane dai daya ne ke wucewa wajen basu kalleta sun sake kallonta ba, ya karasa inda take smiling, cikin soft voice dinsa yace "Sorry Baby, kinsan dole in je in gaida su Ummi da Aunty beside dole ma sai na koma gidan na dauko mota tunda ban dade da sauka ba nima...." Cike da shagwaba tace "Kasan mutane nawa suka tambayeni numbata tsayuwar da nayi nan yanxu" Yace "Sai kika basu kenan" Ta juya masa fararen idonta ta ki cewa komai, murmushi yyi ya amshi trolley din hannunta ya fara tafiya xuwa gun motarsa tana biye da shi tana kallonsa don komai yyi burgeta yake. A hankali yake driving din Aneesah dake gefensa tace "I learnt about Ahmad's engagement with Ramlah" idonsa na kan titi yace "So i heard also" Tayi kasa da murya tace "To mu kuma namu fa?" Still bai kalleta ba yace "Xa ayi" Tace "Yaushe??" yace "Am trying to put things in order first, i don't get why u are in a rush Aneesah, ba dai ni nace xan aure ki ba, meye kike damun kanki haka? Do i look like a liar or do my words sounds deceptive?" Ta kai hannunta kan nasa cikin sanyin murya tace "I just can't imagine loosing u My Captain, i just can't...." Yace "Keep ur mind at rest Neesah, i am all urs and urs alone" Yana fadin haka ya sakar mata murmushinsa dake kara narkar da xuciyarta, dai dai nan kuma ya kai layinsu Jiddah, yau bata awara a bakin titin don babu alamar ma ta fito, sai dai mutane ne cike fal a d'an layin nasu, a hankali yake driving din yana kallon cikin layin, Aneesah dake kallon direction din ita ma tace "What's happening there, ko anyi rasuwa ne?" kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Ko in sauke journalist taje ta gano mana???" Dariya tayi tace "Oops a wnn local area din xanyi journalism dina Captain? Haba this is so disgusting..." Tana magana tana yamutse fuska, shi dai bai ce komai ba yana ci gaba da driving dinsa, can gidan Kanwar babanta ya ajiyeta a unguwar sarki, bayan ya yi mata few shopping na kayan ciye ciye, ta sauka motar bayan yyi parking tana kallonsa, shi ma ya sauko ya fiddo mata da trolley dinta ya kai bakin gate din ya ajiye, ta dau ledan shopping din da yyi mata tana kallonsa bayan ya dawo cikin sanyin muryarta tace "Thank you My Captain, plss ka daure ka xo anjima da daddare mu yi hira..." Ya kashe mata ido yace "Ohk babe...." Daga haka ya shiga motarsa yyi reverse ta bi sa da kallo har ya fita layin tana sake jin wutan sonsa na ruruwa a xuciyarta. Abuturrab na komawa gida yyi parking nan kofar gidansu ya shiga ciki yyi alwala snn ya fito ya shiga masallaci don ana ta kiran magrib, bayan an idar ya fito masallacin ya shiga motarsa ya xauna yana danna wayarsa, ajiye wayan yyi yana kallon flowers dake xagaye kofar gidan nasu trying to imagine the meaning of the crowd they saw earlier a layin yarinyar nan me awara, did someone die again, tunanin hakan ya sa ya tada motarsa ya bar layin, yana isa yyi parking bakin titi ya dau nose mask dinsa a motar ya saka snn ya bude motar ya sauka, ashe da daddare sana'a ake yi sosai bakin titin layin, just like sauran layukan anguwan gaba daya, daga me soya wancan sai me soya wannan, masu siyar da gyada, rake, abubuwan ci na gargajiya dai yawa... A hankali yake tafiya cikin layin yana yatsine fuska, he is even afraid kada allergy ya je ya kamasa cos he is so sensitive to anything Filth,... har dai ya kai dai dai kofar gidan da yaron nan ya ta6a kai sa a matsayin gidansu yarinyar, tsaye yyi yana bin duk wajen da kallo, ginin block ne sai dai ko plaster babu, sannan gidan karami ne sosai, duk gidajen layin haka suke, banda gida daya da ya d'an darasu girma shi ma da kadan wato gidan Iyah, wata yarinya ce ke tafe ko takalmi bbu a kafarta, ya bi ta da kallo yace "Baby...." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Xo in aike ki cikin gidan nan" Yarinyar da baxata wuce shekara shidda ba ta dawo tace "Gidansu Bibalo?" Yace "Ehh, shiga kice ana kiran me awara a ciki" Da gudu yarinyar ta shiga, babu kowa tsakar gidan don Hansai ko minti biyar ba ayi da fitarta ba, ta shiga makota, Bibalo kuma tun la'asar rabonta da gidan, yarinyar ta kutsa kai cikin dakin su Bibalo tana kallon Jiddah dake kwance ta takure waje daya kan yakunannen katifarsu da Bibalo, tace "Wai ana sallama a waje" Da sauri Jiddah ta mike xaune da idanuwanta da suka yi jajir, duk da tasan Hansai ta fita gidan don sai da ta bar mata sallahun bakar magana ma kafin ta fita amma hakan bai hana xuciyarta dinga bugawa ba jin abinda yarinyar tace, A tunaninta saurayinta ne Usman ya xo, kilan ya ji abinda ke faruwa ne, da kyar dai ta lallaba ta mike ta cire Hijab din jikinta ta dau wankakke dake a linke ta saka, sanyi take ji sosai don xaxxabi ne jikinta, ta fito dakin ta sa takalminta tana tafiya kamar iska xai kadeta ta fito kofar gidan, babu haske sosai wajen hakan yasa ta dinga kallon mutumin dake tsaye da fararen kaya ya juya baya, gani tayi ba Usman bane don wnn yafi Usman tsayi, ta bi layin da kallo tana kara tsoron kada Hansai ta dawo ta tarda ita a waje bayan an yi mata iyaka da wajen daga daxu da yamma, da kyar tace "Wa kake nema?" Sai a snn ya juyo ya sauke mask din fuskarsa yana kallonta, ta xaro ido tsoronta ya tsananta, haka xaxxabinta ma taji yana neman fin na da, don sanyi sosai ya dinga shigarta, kallonta ya shiga yi daga sama har kasa, rasa abin cewa tayi daga karshe ta jingina da bangon gidan, still looking at her yace "Baki da lafiya ne?" Ta gyada masa kai, lkci daya hawaye ya kawo idonta, bin layin ya sake yi da kallo, can yace "Baki sha magani ba?" Hawayen dake makale idonta ya silalo kasa ta girgixa masa kai tace "Babu maganin" yace "Ke da waye a cikin gidan?" Tace "Ni kadai ce, Baabarmu ta fita yanxu" Shiru yyi kamar me naxari sai kuma ya kalli inda motarsa yake yace "Akwai asibiti a nan anguwar?" Ta gyada masa kai tana nuna masa tace "A layin can gaba" Yace "Mu je" Da mamaki take kallonsa tace "Ina?" Ya wani hade rai yace "Mu tafi can din nace" ta marairaice cikin rawar murya tace "Baabarmu tace idan na sake fitowa ko nan bakin kofa sai ta kasheni wllh" Shiru yyi na few seconds kafin yace "Saboda me?" Tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace "An sa min rana" Daga sama har kasa ya sake kallonta snn yace "Da wa?" Ta fashe da kuka tace "Da iliya" tana fadin haka kamar an tunxurata ta dinga rera kuka, yace "Ohk, amma bai san baki da lafiya bane bai kawo maki magani ba" Bata basa amsa ba sai kukan da take yi sosai, yace "Mu je" ganin ta ki motsawa ya daure fuska sosai yace "Ke kinsan daga inda nake?" Ta shiga goge idonta bata ce komai ba, yace "Mu tafi nace" A hankali ta fara goge idonta, ganin ya fara tafiya ta bi bayansa gabanta na faduwa tana waige waige har suka kusa bakin titi ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta don duk maxaunin bakin titin nan babu wanda bai santa ba, ya bude mata back seat, xuciyarta ya dinga bugawa da karfi ta tsaya tana kallonsa, ya sauke nose mask dinsa yace "Kina 6ata min lkci" A hankali tace "Baabarmu xata....." Wani kallo yyi mata yace "Nace ki shiga malama" shiga motar tayi a tsorace, ya rufe sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver ya tada motar, sai da ya hau saman titi yace "Ina asibitin yake?" Layi uku dake gaba da nasu ta nuna masa ya shiga layin suna isa yaga irin asibitin yyi parking yana kare ma wajen kallo, kafin yace "Nan din ne asibitin?" Kai kawai ta gyada masa, ya ja tsaki ya tada motarsa yayi reverse ya bar wajen, ta dinga kallonsa gabanta na faduwa, wani asibiti a cikin gari ya kai ta, yana parking haraban asibitin ba tare da ya juya gareta ba yace "Sauka" kalle kallen motar ta dinga yi alamar bata ma san ta ina xata bude ba, ya sauka ya xagayo ya bude motar, sauka tayi ya rufe motarsa, ganin yanda ta tsaya ya dake yace "Mu je" he sounds so pissed off, Ba musu ta bi bayansa har cikin asibitin, nan take ya yankar mata kati, ba a dau lkci ba nurse din ta sanar masa xa su iya shiga gun likita, yana daga xaune ya nuna mata office din likitan yace ta shiga ta gaya masa duk abinda ke damunta, Jiddah ta mike gabanta na faduwa tana kallonsa a hankali tace "Ai tsoro nake ji" ya hade rai a d'an tsawace yace "Tsoron likitan sbda xai cinye ki?" Sunkuyar da kanta tayi, yace "Juya ki shiga" a hankali ta juya ta nufi office din likitan da ya nuna mata, kamar me tsoron kofar ta murda ta shiga, sai a sannan ya mike ya bi bayanta xuwa cikin office din, tana xaune ta takure waje daya likitan na cewa ta kwantar da hankalinta ta nutsu, ganin ya shigo sai taji hankalinta ya kwanta, ya ja kujera ya xauna suka gaisa da likitan, likitan na kallonta yace "Me ke damun ki?" Cikin sanyin murya tace "Kai na ke min ciwo, ina jin xaxxabi, kuma ina ganin jiri...." Mikewa yayi ya dawo kusa da ita yana duba idonta da wani d'an abu kamar fitila a hannunsa, Abuturrab dai na xaune yana dubansu har likitan ya gama gwaje gwajensa snn ya koma ya xauna yana kallon Abuturrab yace "Xa ayi mata test, though symptoms din na malaria ne, but it's good ayi test din sannan kuma .... Is she ur sister?" Abuturrab ya d'an kalleta sannan a hankali yace "Yea" Likitan yace "Me ke damunta haka, yar yarinya da ita na ga Bp dinta ya hau" sake kallonta Abuturrab yyi, likitan na kallonta yace "Kina da damuwa ne 'yan mata, idan ma baxa ki gaya ma d'an uwanki ba ni ki gaya min" Sunkuyar da kanta tayi lkci daya hawaye ya kawo idonta, Abuturrab yace "Dont worry Dr i will talk to her about that, ynxu dai idan ba damuwa kawai a hada mata drugs if there is need for injection ayi mata ba sai an yi mata test din ba cos i guess it will take up to 40mins kafin result din ya fito mu kuma a kan hanya muke" Likitan yace "Toh shkkn babu damuwa" daga haka ya fara rubuce rubuce yana gamawa ya mika ma Abuturrab ya amsa snn ya mike yyi masa godiya, ganin har sannan bata mike ba yace "Mu je" Mikewa tayi yana gaba tana biye da shi har suka fita office din, wajen bada allura Abuturrab ya ga abinda bai ta6a gani ba, don kememe taki yarda ta dinga rusa masu kuka a asibitin tana rokansu, hakan yasa ya koma office din likitan yasa ya rubuta magunguna kawai gaba daya ya biya bill din sannan suka fita asibitin, har sannan shesshekan kuka take, ya bude front seat ya hade rai yana kallonta a hankali ta shiga ya kulle sannan ya xaga ya shiga maxaunin driver, sai da suka fita asibitin yace "Kin ci abinci?" Girgixa masa kai tayi tace "Baabarmu ta ba almajiri nawa" Ya dinga nanata sunan da ta kira a ransa, wai Baabarta, girgixa kai yyi cikin ransa still yace ba dai baabarki ba, gidan wani cin abinci ya tsaya ya siya mata abinci sai malt guda biyu da bottle water, yana shigowa motar ya ajiye mata, kallon ledan ta dinga yi, can ta bude ta ciro malts din ta ajiye gefe tace "Ban iya sha ba" Yace "Sai me?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tambayarki nake" a hankali tace "Ban iya shan lemo ba ni" Bai kuma ce mata komai ba, sai da suka shigo titin hayi yace "Taron me naga aka yi a layinku daxu da yamma?" Shiru tayi sai kuma ta kallesa a hankali tace "Baabarmu ce take dukana" Da mamaki yace "Saboda me?" Ta share hawayen da ya kawo idonta tace "Dama Iyah ce tace xata sa ni a motar tirela in gudu legas don kar a min aure da Iliya, shine sai na gaya ma wata kawata da muke xuwa makarantar dare tare da ita da, don gobe Iyah tace xata kai ni tasha, sai kawata taje ta gaya ma baabarta shine baabarta ta xo ta gaya ma Baabarmu, shine Baabarmu ta dinga dukana wai xata kasheni, duk aka taru a layin...." Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Shi dai sauraronta kawai yake yi, bayan few seconds yace "Wacece Ita warce tace xata sa ki mota ki tafi lagos?" Cikin rawar murya tace "Wata tsohuwa ce a layinmu ana ce mata Iyah...." Ya kalleta yace "Har yanxu xa ki tafi lagos din kenan don kar a maki auren?" Ta girgixa masa kai hawaye na sauka idonta tace "Aa baxan je ba amma xan kashe kai na" Bai ta6a expecting jin hakan daga bakinta ba, yyi parking yana kallonta da mamaki yace "Xa ki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Da me xaki kashe kan naki?" Cikin rawar murya tace "Piya piya xan siya in sha" Bai san lkcn da ya bude baki ba yana kallonta ganin she is so damn serious, da wani expression yake kallonta ganin she is truly depressed and frustrated, tana goge hawayen dake xuba idonta tace "Dama ae Abbana ma ya tafi ya bar ni, ba sai in bi sa ba" ya kwantar da murya yace "Amma kina xuwa islamiyya kuwa?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Na daina tun da dadewa, tun sanda muka fara sana'a" Yace "Toh saboda xa a maki aure kike son kashe kanki?" Ta gyada masa kai, sai kuma ta hade kanta da gwiwa ta fashe da matsanancin kuka tace "Shaye shaye fa iliya ke yi, kuma har kwaya yana sha shine Babarmu take son in auresa...." Kallonta kawai yake, can yace "To wa kika ta6a ganin ya kashe kansa sbda xa ayi masa aure da wanda baya so?" Tana shessheka tace "Akwai wata ma ai ta kashe kanta a nan hayi" yace "Shine ke ma xaki kashe kanki?" Ta gyada masa kai, yace "Toh duk sanda kika shirya ki min magana ni da kaina xan kawo maki piya piyan, kin ji ni?" Ta dago tana kallonsa tace "Toh ai ni na shirya" yace "Yaushe?" Da kyar tace "Yau da daddare nake son in sha" yace "Aa kinga ni sai yau na sani, ki bari ko xuwa jibi xan kawo maki" tana shessheka sae kuma ta sakar masa kuka tace "Yayi min nisa" Yace "Ya sunanki?" Tana kallonsa da hawaye idanuwanta tace "Jiddah" Ya d'an yi shiru, bayan few seconds yace "Jiddah.... shekaranki nawa??" Cikin sanyin murya tace "Babaarmu tace sha bakwai" yace "Toh ki jira sai na kawo maki da kaina, kar ki kuskura ki siya da kanki, kin ji me nace maki?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ki yi min alkawari xa ki jirani" Tace "Nayi" yace "Kina komawa gida ynxu ki ci abinci ki sha maganin ki ai nurse din ta nuna maki ynda xa ki sha" Ta gyada masa kai, tada motar yyi ya ci gaba da driving dinsa gaba daya yana kara naxarin xancenta.
07087865788✍🏻
💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖
_By Khaleesat Haiydar_✍🏻
6.....
Suna kusa layinsu cikin sanyin murya tace "Toh me xan ce ma Baabarmu idan ta dawo, wllh har dukana xata yi" Bai ce komai ba yyi parking d'an nesa da layin snn ya d'an kalleta yace "Amma ba Baabar da ta haife ki ba ko..." Ta girgixa masa kai a hankali tace "Abbana yace ita ta rasu tun ina yar karama" ganin hawaye idonta ya dauke kai bayan few seconds yace "Allah ya gafarta mata" Ta sunkuyar da kanta ta amsa da Ameen, yace "Sai kice mata saurayin da xaki aura ne ya xo kika fito" Ta marairaice tace "Ai yana legas bai dawo ba" Yace "Kwanaki da na baki kudi ki bata don kar ki sake fitowa bakin titi, kin sake fitowa?" Ta girgixa kai tace "Aa bamu sake yin awaran ba sai shekaranjiya ta fara" bai ce komai ba ya tada motarsa ganin ya fara tafiya ta kallesa da sauri tace "Ina kuma xaka kai ni?" Bai bata amsa ba ganin wani shago da ake cire kudi ta Pos ya tsaya sannan ya sauka motar, without taking much time ya dawo ya shiga motar.... Dai dai layin nasu ya sake parking ya ciro kudi a aljihu yace "Gashi ki kai mata yanxu ma" Kallon kudin ta dinga yi, sannan ta kallesa tace "Ince wa?" Yace "Kice wani ya bata" Amsan kudin tayi gabanta na faduwa, yace "Me nace kiyi idan kin koma gida yanxu?" tace "Kace in bata wai in ji wani" Yace "Kafin wannan" Ta d'an yi shiru sannan tace "Kace in ci abinci in sha magani" Ya d'an daure fuska yace "To sauka" yana fadin haka ya bude mata motar ba tare da ya yarda ya ta6a ta ba, ta sauka, yace "Kulle min mota" Ba musu tayi yanda yace sannan yayi wucewarsa without looking at her, sai a sannan bugun xuciyarta ya tsananta, ta fara tafiya a hankali xuwa cikin layinsu, ta fi minti biyu bakin xaurensu ta kasa shiga, daga karshe ta kutsa kai ciki, tuni hawaye ya fara sauka idonta tana jiran jin saukan duka, sai dai me... Har sannan Hansai bata dawo ba balle Bibalo, gidan babu kowa, dakinsu ta shiga duk da akwai wutan nepa amma kamar ko da yaushe wutan is very low, xaunawa tayi ta ajiye ledan hannunta sannan ta boye kudin cikin ghana must go dinta, a hankali ta bude take away din abincin ta ga shinkafa da katon kaza, ta xaro ido, ita yaushe rabon da ta ci shinkafa balle wata kaza, shinkafa sai suyi kusan sati uku ma basu ci ba daga tuwon masara sai taliya 'yar Hausa ko garin rogo, Kaza kuma dama ranan sllh ne kadai Hansai ke bata kai da kafafuwan ko kuma wuya, yau kuma ga kaza kato a gabanta har da shinkafa, kasa cin abincin tayi tana ta kallonsa, tunawa da tayi Hansai na iya dawowa yanxu ko Bibalo yasa ta xaro ido, a hankali ta fara cin abincin, sbda a tsorace take ta kasa nutsuwa ta ci abincin, ta dai ci wanda xata iya ci, jin almajiri na bara ta mike da sauri ta fita da abincin da ta kunshe a ledansa ta mika ma almajirin ta dawo ciki, ta fi minti daya tana kallon magungunan, kafin ta fito da su tana kallo, ganinsu kadai taji xuciyarta ya fara tashi ta mayar da su da sauri ta cusa a ghana must go, duk ciwon da xata yi bata shan ko d'an paracetamol da Abbanta ke siyo mata lkcn da yake da rai, Hansai kuma ko kasheta ciwo xai yi bata ta6a cewa ta sha magani, muryar Bibalo ta ji tana kiran Uwarta tun daga bakin Zaure hakan yasa ta boye goran ruwan da ta sha ta rage, snn ta kwanta ta rufe idonta. Washegari da asuba jiddah ta kasa tashi kamar yanda ta saba, duk karfe biyar dama take tashi ta fita ta debo ruwa a borehole ta cika jarkunan tsakar gidan da ma bokiti, ganin gari ya fara haske Hansai ta leko dakin tace "Yau naga walakanci, Jiddah kece kwance har yanxu baki fito ba, uban wa xai debo ruwan yau? Bibalo me ciwon kirji ko ni xan fita debo ruwan?" Bibalo dake kwance tana bacci ta gyara kwanciyarta hade da rufe har fuskarta da xanin gadonsu, Jiddah ta dago da kyar muryata na rawa tace "Baabarmu kaina ke min ciwo sosai, idan na tashi juwa nake gani" Hansai tace "To a rayuwar nan yanxu waye baya fama da ciwon kai, ko digon ruwan alwala fa babu a gidan nan, ni kike son in fita in debo ko Bibalo da ba cikakkiyar lafiya gareta ba" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai tace "Ai ko daurewa xa ki yi ki mike ki debo ko bokiti uku ne, gida idan babu ruwa ai ba magana" Daga haka ta juya ta fita tana cewa "Idan ma xaki rufa ka kanki asiri ga bishiyar gwanda da mangwara can ki tsinko ganyayyekin su ki hura icce ki dafa ki sha kiyi wanka don sile na baxanyi amfani da shi wajen siyo maki magani ba" Da kyar jiddah ta mike tana dafa bango ta fita, ta dau bokiti, d'an makotansu ne ya taimaka ya kawo mata ruwan har kai uku gidan, ta dawo da kyar ko tafiyan bata iyawa ta shige daki ta kwanta ko ina na jikinta na mata ciwo... Har karfe goma na safe tana kwance, Hansai ta shigo dakin cike da masifa sosai tace "Ke ni fa babu ruwana ki tashi kiyi ta kanki ki tsinko abinda nace ki dafa uban waye xaki daura ma wahala bayan na ciyar da ke da nake yi" Jiddah ta mike ko ina na jikinta na rawa sbda sanyi, tace "Xan yi" tana magana ta jawo ghana must go dinta ta fiddo kudin jiya ta mika ma Hansai tace "Jiya wani ya kawo wai a baki" Hansai ta xaro ido tana kallon kudin ta karba tace "wani kuma? A ina kika gansa?" Tace "Aikawa yayi in xo, ina xuwa yace in baki" Hansai ta xauna gefen gado ta fashe da kuka tace "Amma gaskiya isuhu ya tare mana abubuwa da yawa a duniyar nan sanda yake raye, to da ya baki sai yace me??" Jiddah ta koma ta kwanta tana fidda numfashi da kyar tace "Cewa yyi in baki kawai" Shiru Hansai tayi tana kirga kudin har ta gama taga dubu talatin cif, ta kalli Jiddah da sauri tace "Ko dai mutumin da ya ta6a baki kwanaki ki kawo min kada mu fito sana'a?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh don girman Allah duk ranan da ya sake dawowa kice masa ya shigo in masa godiya" Jiddah bata iya ta bata amsa ba, Hansai ta mike murna fal cikinta tana murmushi ta nufi kofa tana cewa "In dai haka ne duk wani nawa amma banda Bibalo ya mutu a duniyar nan mana, daga mutuwa sai billowan alkhairi ta ko ina? Ashe dama akwai sauran mutanen kirki a duniya ban sani ba" Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta.
Ummi na kallon Abuturrab tace "Ina kuma xaka da yamman nan kana ganin hadari?" Yace "Aa ni ba nisa xan yi ba, nan governor road xan je" tace "Ahmad din har ya tafi ne?" Yace "Aa tare xa mu fita da shi amma xai dawo" Tace "Toh Allah ya tsare, ka siyo min tsire while coming back" Yace "Alright, in sha Allah" Daga haka ya fita dakin nata ya dawo main parlor, Ahmad na xaune yana jiran sa, Ganinsa ya mike ya nufi kofa, bin bayansa Abuturrab yyi wayarsa ya fara ring, dubawa yyi yaga Aunty ke kiransa, ya daga ya kai kunne, wara ido yyi yace "Aunty yanxu ai xan dawo..." Murmushi yyi yana kallon wayar don har ta katse, juyawa yyi ya koma bangare Stepmum din tasa, Ahmad ya ta6e baki, a parlonta ya sameta, yace "Ba nisa fa xanyi Aunty" ta hade rai tace "Shine ni baxa ka min sallama ba amma ai naga ka shiga gun uwarka?" Yace "Toh kiyi hakuri" Yana fadin haka ya jefa ma stepsis dinsa dake xaune parlon wani kallo sanin ita xata gaya mata, Aunty tace "Toh me Ummin tace maka da ta kira ka?" Yace "Nothing kawai tace in taho mata da tsire while coming back" Tace "Toh nima ka taho min da tsiren" yyi murmushi yace "Toh" Daga haka yace "Sai na dawo" ya fita dakin. Yana driving ya d'an kalli Ahmad dake danna wayarsa yace "A ina xaka sauka?" Ahmad ya kallesa yace "Kai ina xa ka???" Abuturrab yace "Bakin ruwa, nan by pass" Da mamaki Ahmad yace "Me zaka je yi a bakin ruwa Captain?" Ya gyara xama yace "Xan amshi sako gun wani frnd dina ne, he is coming from Abuja kuma kano xai wuce, so yace min ya shigo kd yanxu mu hadu by pass in amshi sakon" Ahmad yace "Ohk, drop me home" Abuturrab ya nufi gidansu yyi parking bakin gate, Ahmad ya sauka yace "Sunday din xaka tafi kano?" Abuturrab yace "In sha Allah" Ahmad yace "Alright... Sai da safe" Daga haka ya shiga ciki, Abuturrab yayi reverse ya bar layin. Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kan hanya bayan ya iso bakin ruwa, jinginar da kansa yyi jikin kujeran da yake xaune yana tunanin wanda ya sani wanda bai yi aure ba that he can do anything possible to see him married to this girl that is ready and wanting to kill her self, driver din Abbansa ko wata uku ba ayi da yyi aure ba, who again? Wani senior cleaner ne a Airport din kano ya fado masa, Guy din na da hankali... a Diploma holder, ga shi da mutunta mutane, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ganin ya kusa samun solution, and he will try all possible means sai Mu'axxam ya auri yarinyar nan, wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa na relieve, driving ya ci gaba da yi, yana isa u-turn ya dau hanyar Hayi, kamar ko da yaushe parking yyi a bakin layin yana kallon cikin layin, nose mask dinsa ya saka da glasses din ido sannan ya sauka motar ya fara tafiya, calmly yake tafiyar har ya isa kofar gidan, wani yaro ya tura ya kira masa jiddah cikin gidan, Hansai na xaune tsakar gida tana cin shinkafa da wake da mai da yaji da salak wanda rabon da su ci shinkafar tun rasuwan Mai gidan nata, tana kallon yaron tace "Lawali daga ina haka?" Yace "Wani ke kiran jiddah a waje" Hansai tace "Jiddah kuma?" Jiddah dake kwance xaxxabi ya ci karfinta ta bude jajayen idanuwanta da sauri gabanta yyi wani mugun faduwa ta mike xaune, Hansai ta kakkabe guntun shinkafar hannunta a samiran cinyarta tace "Waye shi? Kuma daga ina?" Yaron yace "Wani dogo ne ya sa gilashi da takunkumi a hanci, ya sa fararen kaya" Hansai ta mike da sauri tana leka dakinsu Jiddah tace "Ke tashi, kaddai me kawo min kudin nan ne?" Jiddah ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa tace "Ban sani ba" Hansai tace "To ai kuwa daurewa xa kiyi ki tashi ki saka hijabi ki fita ki ga waye, kika sani ko shi din ne wani kudin ya kawo yau ma" Kasa ci gaba da tsayuwa tayi duk ynda ta so yin hakan, Hansai tace "Yau naga tsiya, baxa ki daure ki tashi ba kamar ba mace ba Jiddah??" Jiddah ta dafa gadon ta kara daurewa ta tashi, Hansai ta warware Hijab dinta dake ajiye a linke kan jaka ta mika mata tace "Sa ki fita maxa maxa ki ga waye" da kanta ta sa mata hijab din, jiddah ta fita dakin, Hansai ta xauna gefen gado tana addu'an Allah ya sa shi din ne, kuma wani kudin xai bada yau ma, jiddah na fita kofar gidan ya juyo yana kallonta, durkusawa tayi nan kasa ta kasa ci gaba da tsayuwa, ya dinga mata wani kallo yace "Jikin bai maki sauki ba?" hawaye ya shiga sauka idonta, kana ganinta kasan tana jin jiki, yace "Kin sha magungunan nan kuwa?" Kin cewa komai tayi, Ya hade rai da d'an tsawa yace "Tambayar ki nake" Ta fashe da kuka a hankali ta kara jingina da bango tace "Ni amai xanyi idan na sha" Da mamaki ya dinga kallonta, Hansai dai na ta tsaye tsakar gida tana jiran ganin shigowar jiddah, jin shiru shiru ta nufo xauren cikin sanda tana leko waje, hada ido suka yi da Abuturrab, ta sunkuyar da kanta da sauri tana d'an kame kame tace "Sannu da xuwa Alhaji.... Ae da ta fito maka da tabarma ko" kallonta kawai Abuturrab ke yi daga sama har kasa, can yace "ina wuni" Hansai ta rutsuna tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa, ko xaka shigo daga ciki...." Yana kallon jiddah yace "Ya mai jikin?" Hansai ta marairaice tace "Wllh da sauki kenan xa a ce, kuma fa ta sha magunguna amma shiru har yanxu" yace "Toh bari mu je asibiti" Hansai tace "Kai Alhaji da dai a je chemist kar hidiman yyi yawa, ga chemist can bayan mu" yace "Aa xa a je asibitin kawai" Hansai tace "Toh shkkn Alhaji, daure ki tashi Jiddan Mama, sannu... Ga dai ana shan maganin kamar ba a sha" tana fadin haka ta dagota, Abuturrab na kallon Hansai yace "Motata na bakin titi" Hansai ta kwance dankwalin kanta ta rufe jikinta da shi tace "Toh bari mu je can din" tana rike da jiddah suka isa bakin titin ya bude back seat ta saka jiddah ciki, mutanen layin sae kallonsu suke, Abuturrab na kallonta yace "Ina 'yar uwarta mu tafi tare" Hansai tace "Au wai Bibalo, ai kuwa bata anguwar nan yanxu haka, ko in shiga mu je ni?" Ya kalleta daga sama har kasa sannan yace "Yanxu xa mu dawo in sha Allah, ba sai kin je ba" tace "Atoh dama ae bai ma kamata in bi ku ba, toh Allah ya kiyaye Alhaji, a dawo lafiya" xagawa yyi ya shiga driver seat ya tada motar ya bar wajen Hansai sai washe baki take tana daga masa hannu, sai kuma ta hade rai tana kallon 'yan layin da suka xuba mata ido da kallo tace "To wai lafiya wannan shegen kallo haka??" Tsaki ta ja ta juya ta fara wucewa tana cewa "Jama'ah baxa su ji da talaucin da yyi masu katutu ba sai shegen sa ido da neman abun fade, to d'an uwanmu ne daga Habuja sai kowa yyi ta kansa haka kuma" Abuturrab na hawan saman titi ya kalli Jiddah ta madubi yace "Wato baki sha maganin jiya ba??" Shiru tayi bata ce komai ba, ya hade rai yace "Ki bude baki kiyi min magana ina tambayarki" kai kawai ta gyada masa, yace "Me yasa baki sha ba?" Kamar xata yi kuka tace "Nace maka amai xan yi idan na sha" Yace "To xa mu je su maki alluran yanxu ai" Ta mike xaune da kyar tace "Aa ni bana son allura" Wani kallo ya wurga mata, tayi shiru bata sake cewa komai ba.... Sai kusan karfe taran dare Abuturrab ya dawo da ita bakin layin nasu, yau ma da ledan take away din abincin da ya siya mata, ya sauko motar ya xaga ya bude mata side din da take xaune, da kyar ta sauko motar da wasu ledan magungunan daban da aka kara bata a asibitin da ledan abinci, ya rufe motarsa, har ya xaga xai shiga maxaunin driver ya sa hannu aljihu ya ciro dubu goma ya dawo ya bata yace "Sai ki ba Baabar taku" daga haka ya shiga motar yayi wucewarsa, da kyar ta dinga jan kafa har ta isa gida, Hansai na xaune da Bibalo dake cin abinci, ganin ta shigo Hansai ta mike a xabure tace "Me ya baki?" Jiddah ta mika mata duk ledojin hannunta da kudin sannan ta xauna nan bakin kofa ta jingina da bango kanta na juya mata, Hansai ta kirga kudin ganin dubu goma ne tace "Toh ya baxai bani dubu goma ba bayan kudi ya kare a shegun magungunanki, munafuka kawai, ciwo kalilan duk ta bi ta langwabe ma mutane kamar kyanwa, kuma da ganin asibitin me tsada xai kai ki, to Allah ya isa wllh...." Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta ja tsaki ta shiga fiddo magungunan a fusace tana kyabe baki, can ta watsa mata su tace "Abun takaicin ma asaran kudinsa kawai yyi, ke din ce xaki sha ma mutane magani" watsa mata ledan magungunan tayi gaba daya sannan ta bude dayan ledan ganin shinkafa da dunkulelen kaza ta murmusa tace "Allah sarki bawan Allah" Tuni Bibalo ta tura kwanon gabanta ta dawo kusa da uwarta, Hansai tace "Toh bai saka da lemo ba sai ruwan gora?" Jiddah dai bata ce komai ba, Hansai da Bibalo suka shiga cin abincin kamar mayunwata, sai da suka kusa cinyewa ta kallo jiddah tace "Au, to ai ba mu sam mata ba" kwanon abincin da Bibalo ke ci ta jawo, tana kallon guntun shinkafar da Bibala ta rage ta debi na take away din loma biyu ta yarfa a kai, sannan ta dau tsoka me K'ashi, sai da ta ta66atar ta kwaye tsokan sannan ta saka k'ashin a kwanon ta tura ma Jiddah tace "Gashi kema" Jiddah dai bata ce komai ba, suka cinye nama da abincin tass sannan Hansai ta maka uban gyatsa ta mike ta shige daki tana cewa "Bibalo ke da yar yabi sai ku bibbi gobe ku kai cingam da sweet din sa ranan da aka yi, har yau ba a ba jama'a ba" Bibalo ta mike ta bi bayan uwarta tana cewa "Yo ai cingam din kwali daya ya rage..." Jiddah ta jingina da bango hawaye ya kawo idonta a hankali tace "Kuma bai kawo min piya piyan ba" Washegari lahadi Abuturrab ya fito gida misalin karfe sha daya na safe, Waya ne kare kunnensa yana driving a hankali don bai fita layinsu ba, girgixa kai yyi yace "No kai dai ka samu adaidaita ni na riga da na fito da mota, sai ka fadi inda xan sameka" Murmushi yayi bayan few seconds yace "Okay then, tunda kasan hospital din ba sai ka tafi ba" Yana fadin haka ya katse wayar hannunsa. Dai dai inda suka yi xai dau Ahmad yyi parking yana jiransa, bayan kusan minti goma Ahmad ya iso wajen da adaidaita ya shiga motar yana kallon Abuturrab yace "Amma ba yau xaka bar kaduna ba Captain" Abuturrab yace "probably.... Akwai abinda xan yi yau din" Ahmad yace "Ni train xan bi in sha Allah yau xan koma Abuja..." Abuturrab bai ce komai ba har suka isa wani hospital domin duba wani frnd dinsu da aka yi admitting, fruits iri iri suka siya masa a hanyarsu ta xuwa wajen, suna shiga ward din da yake suka tarar da abokansu hudu su ma sun xo dubiya, bayan an gaisa, wani frnd dinsu Umar na kallon Abuturrab cike da tsokana yace "Captain ko dai a hayin rigasa kake gini ne? Or probably neman aure...." Da mamaki Abuturrab ke kallonsa har ma da sauran abokansu, Ahmad yayi dariya yace "Haka yace maka Umar?" Umar ya gyara xamansa yace "To for the past 4 days kullum sai na ga motarsa a hayi" Abuturrab ya xaro ido yace "Ni kuwa?" Umar yace "Kai mana, yawanci kana ta daya side din nake ganinka, kai akwai ranan da ma na kiraka ina jin ka bar wayar a mota and u didn't even follow my miss call" Abuturrab yace "Subhanallah on a serious note ban lura ba...." Umar yace "To airport xa a bude mana a hayi ne kullum muke ganin Captain a can" Murmushin yake kawai Abuturrab yyi yana kallon Nasir dake kwance da drip a hannunsa yace "Barrister guda a gadon hospital, so how are u feeling now?" Nasir ya jefa masa wani kallo yace "Kai ma baka wuce a kwantar da kai gadon asibitin ba ai" Dariya kawai Abuturrab yyi, sun fi minti ashirin a dakin suna labarin duniya, daga karshe Ahmad ya sanar masu xa su koma bayan sun ma Nasir addu'an samun lfya, a tare suka fito da Umar daga ward din don shi ma wucewa xai yi, Abuturrab ya d'an kalli Ahmad dake bayansa suna magana da wani abokinsu da ya fito rakasu, ya kalli Umar da har ya kusa fita reception din hospital, ya kara pace dinsa har ya isa gunsa yace "Kai me kake xuwa yi hayi har kake ganina?" Umar yyi murmushi yace "A can fa Mahaifiyata take, so kusan kullum nakan je can din" Abuturrab yace "Ohhh Allah sarki..." Umar yace "To kai wajen wa kake xuwa?" Abuturrab ya d'an shafa kansa ya saci kallon Ahmad dake tahowa yace "Aboki nayi nima a can din" daga haka ya fiddo wayarsa ya d'an yi gaba kamar xai yi answering call don bai son Umar ya ci gaba da maganan gaban Ahmad. Abuturrab yana kallon Ahmad bayan sun hau saman titi yace "Gida xan sauke ka?" Ahmad yace "Yeah..." Driving kawai Abuturrab ke yi, Ahmad dake kallonsa yace "Wajen wa kake xuwa a hayi Captain?" Abuturrab ya kallesa da sauri cos the question came unexpected, ya dake yace "Ka yarda da Umar kenan, he was just pulling my leg idan ba dai a train station ba ya gan ni wa gareni a hayi da xanje? Wa na sani a hayi? Kawai dai idan mun hadu dole sai ya tsokane ni ne..." Ahmad na gyara xama yace "To na sani ko budurwa kayi a can baka sanar min ba kake boye min, ai idan tayi tsami ma ji" Wani kallo Abuturrab ya jefa masa yace "In rasa inda xanyi budurwa sai anguwar nan???" Ahmad na kallonsa da mamaki yace "Meye da su 'yan anguwan, ba mutane bane su din? Or sai da aka halicceka specially sannan aka halicce su aka ce maka? What's wrong with u Abuturrab? Why do u sometimes behave like...." Abuturrab yace "Illiterate right?" Ahmad yace "Of course" Abuturrab yace "Fine, but do not forget everyone is entitled to his or her opinion, ra'ayinka daban ra'ayina daban, kai xaka iya budurwa a can infact har ma ka aureta ku xauna a can din, it's ur opinion, ni kuma last thing da baxanyi ba kenan a rayuwata, and this is my opinion, so stay entitled to urs, and i stay entitle to mine also" Ahmad yace "Baxa ka iya aure a can ba sbda kafi su a wajen Allah ko??" Abuturrab yyi masa wani shegen kallo yace "Wai Ahmad ance maka ni kai ne?? Ni fa ina da class ina da taste, as in i am far beyond that ka daina yi min irin wannan maganan bana so wllh" Ahmad yyi d'an murmushi bai kuma ce masa komai ba, Abuturrab yyi tsaki yace "Haka kawai sai kace kowa sai ya bi ra'ayinka, kai mace ko min kazantarta da locality dinta xaka iya aurenta ku xauna lafiya, ni kuwa it's a big No for me, bana walakanta 'yan adam kai shaida ne, sannan kasan ko kai baka kaini tausayin d'an Adam ba, idan naga mutum na cikin damuwa ko wani yanayi more especially mace ina bakin kokarin ganin nayi duk abinda xan iya yi ko a ina ne kuwa, even with my last card i can help, amma sai ka dinga hadani da su kana wasu maganganu marasu ma'ana" Ahmad bai kuma ce masa komai ba har suka iso gidansu, Abuturrab yyi parking, Ahmad ya juya yana kallonsa still bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ya rufe masa motarsa, tsaki Abuturrab yyi, yyi reverse ya bar layin kallon agogonsa dake nuna masa sha biyu da rabi yyi ya nufi gida kawai....
07087865788....✍🏻 Almost done with free pages
💖💖 *Jiddatul Khair*💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
7.....
Fitowa Hansai tayi tsakar gida jin ana sallama, ganin aminyarta Zulai ta ce "Aa ashe Zulai ce, shigo daga ciki mana" Zulai tace "Ina ta addu'ar Allah ya sa in sameki wllh" Hansai tayi dariya tace "Ai ko kin ci sa'a, don yanxu haka shiri nake xan fita kasuwar tasha in saro kayan sana'ata" Zulai ta rike ha6a tace "Kin fara wani sana'ar ne banda awara?" Hansai tayi shewa tace "Ai ni na kwan biyu ma banyi awarar ba, amma kilan idan na fita yau dai in siyo har da waken suyan, yanxu su maggi, kubewa, kuka, daddawa... Kai duk dai mahadin miya da kika sani nake siyarwa, ko kwana hudu ban yi da farawa ba, sannan ina sa ran fara dillalanci kwanan nan" Zulai dake ta kallonta tace "Ikon Allahhh..." Hansai ta shiga d'an dakinta tana murmushi, Zulai na biye da ita a baya, bayan sun xauna Zulai tace "To ina yaran?" Hansai tace "Bibalo yanxun nan ta shiga makota, Ita kuma warcan gantalalliyar na can kwance wai ba lafiya" Zulai tace "To Hansai wani labari dai nake ji a gari, shine nace bari dai in sa6o gyale in taho..." Hansai ta gyara xama tana kallonta tace "Me ke faruwa? Wani labarin kika ji?" Zulai tayi kasa da murya tace "Yawo ake da ke wai bayan an kawo gaisuwan wannan yarinya jiddah har an saka rana kina turata gun wani me katuwar mota kullum sai ya xo kofar gidan nan, meye gaskiyan lamarin nan?" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tayi mici mici da ido tace "Amma dai Allah ya tsine ma duk wani me sa ido a duniya, da yaushe da yaushe na turata gun me mota? Yau naga lalacewa, Jiya ne fa bata da lafiya shine ya siyo mata magunguna, kai ni Hansatu jama'a basu da gadonka amma suna da gadon maganarka..." Zulai tace "To waye shi me motar ma dai tukun" Hansai na huci ta lafto wani uban ashar tace "Duk wanda ya fasa sa min ido bai haifu cikin uwarsa ba a garin nan, tunda isuhu ya rasuwa wani shege ne ya ta6a kawo min kwayar masara balle shinkafa ko man kulli yace gashi ki ci kanki Hansai?? kawai sai don bawan Allah ya ga muna cikin matsatsi da yanayin rayuwa yana xuwa yana taimaka mana domin Allah sai a sa mana ido a hau mana bakin ciki da hassada a anguwa? Ni wllh ji nake kamar in siyar da gidan nan in bar gantalallen anguwar nan ko xan samu ci gaba" Zulai tace "Ke ni duk ba wannan ba tsoho ne mutumin nan ko yaro?" Hansai ta ja tsaki tana gyara xama tana huci tace "D'an yaro ne fa Zulai, ina jin ma saurayi ne bai ta6a aure ba, baki gansa ba bawan Allah wllh...." Zulai tace "Gun jiddar yake xuwa?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Waye kuma jiddah? ita a wa xai xo wajenta? kema dai da wani xance wllh, xuwa fa yake idan yaga tana tuyar awara bakin titi ya mika mata kudade masu yawa ta kawo mana, ai ya san halin da muke ciki, d'an gayu ne fa sai kin gansa me kuma xai yi da wata jiddah kamar warce uwarsa tace masa je ka ka gani?? Haba Zulai, wllh da kyar ma idan ba daga Habuja yake xuwa ba don d'an gaye ne" Zulai ta d'an leka waje a hankali tace "Bacci jiddar take?" Hansai tace "Oho...." Daga haka ta mike ta fita, bude labulen dakinsu jiddah tayi ganinta a kwance tace "Wannan shegen kwanciyar baxai fissheki ba idan xa ki tashi ki kwashi bokitai ki fita gashi can an kawo famfo bakin titi ki jido mana ruwa ko na alwala ina jin babu a gidan nan, tun safe kin wani makale daki a kwance kamar ruwa" daga haka ta fice daga dakin ta koma nata, jiddah ta mike xaune daga kan darduman da take a kwance bayan tayi sllhn azahar, duk da jikin nata ya mata sauki, amma idan ta tashi jiri take gani ga yunwa dake dawainiya da ita, tun safe kunu kadai ta sha kosan da aka siyo ma bata ga idonsa ba balle a bata ta ci, sai da Jiddah ta bar gidan da bokitai sannan Zulai ta rike kunnenta daya tace "Anya ba son jiddah mutumin nan yake ba kuwa Hansai, banda haka hidimar uban me xai maku, ku da ku ke gida, ga almajirai can a titi, ga gidajen marayu a gari" Hansai tayi kasake, sae kuma tace "Sonta kuma? Ta ina xai so ta Zulai, babban mutum ne fa, kudi yake bata ta kawo min mu kula da kanmu tun bayan mutuwar Isuhu fa...." Zulai tayi wani murmushi irin na boss tace "Lallai Hansai, ashe har ynxu da sauran ki, to wllh da kyar idan ba sonta yake ba me yasa bai mika ma Bibalo ta kawo kudin ba sai Jiddar" Hansai tayi tsaki tace "To Bibalo sana'a take min a bakin titi da xai ganta ya bata? Ai sai dai Jiddar dake bakin titi kullum" Zulai tace "To wllh ki farka daga wnn baccin da kike, kada ki kuskura ki bada kofar da xai shigo da wani batu bayan ihsanin da yake maku, idan kuwa kika yrda to kina ruwa, ga dai Bibalo ai ita ya kamata a so tunda da gatan ta, amma har kika yarda ya shigo maki da wani batu kan Jiddah to kashin ki ya bushe kina ji kina gani Jiddah xata xama matar babban mutum...." Shiru Hansai tayi tana kallonta ko kiftawa babu da alamar xancen Zulai ya gigitata, Zulai tace "Atoh, kada ki kuskura wllh, ihsanin ma idan son samu ne kada ki sake amsa don a bisa dukkan alamu ya ga Jiddah ne ya kyasa, to jiddah kuma a wa Allah na tuba, yarinyar da ko dangin kirki bata da, kai ina ma ta gansu, ke fa kadai ce gatan ta a duniya, ba dangin uwa balle na uba, yau da xaki koreta sai dai ta bi duniya bata da wajen xuwa...." Hansai tace "Toh wai hauka nake yi ne Zulai, bayan an amshi gaisuwa gun Iliya so kike d'an iskan ya 6a66aka ma gidan nan wuta mu shiga uku? ai jiddah yanxu bata da maraba da matar aure, Iliya ya kawo komai sadaki kawai ya rage da daurin aure, shi ma ni ce na ja lkcn ai an sa ranan kusa kusa na daga" Zulai tace "Atoh, tun wuri sanar masa ya dawo ayi ayi auren kawai, kinga wannan mutumi kam dole ya komo ma Bibalo...." Hansai ta sharce wani xufa tace "Ni dadina da ke akwai hangen nesa wllh Zulai, kinga bbu wanda ya xo ya wayar min da kai banda ke ina nan ina ta haukana, bari in sa a kira min Iliyan dama sbda kudin katifar da xan siya mata ya sa nake ta jan auren naki yrda a sa sati biyu kamar yanda ya bukata, amma tunda haka ne kuma ga wnn bawan Allah ya bamu kudade masu tsoka kema har na cire maki dubu biyu a ciki, sai ki rakani kawai gobe ko tsohuwar katifa ce in siya mata da 'yar robobin aikin gida" Zulai tace "Shkkn kuwa" kasa karasawa cikin compound din Jiddah tayi da bokitin ruwa a kanta jin abinda su Hansai ke cewa, ta fi minti uku tsaye duk tana sauraronsu Zulai tace "Idan kin kirasa kice yace a sa bikin sati biyu kawai kin shirya a wuce wajen" Hansai tace "In sha Allahu haka xan yi" A hankali Jiddah ta karaso ciki ta juye ruwan kanta duk suka yi tsit, ta juya ta fita tsakar gidan lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita dai bata ji xancensu na farko ba amma daga inda suke cewa xa su ce Iliya ya dawo ayi auren ta tsinci maganar su. Bayan ta fito ta so shiga gidan Iyah amma sbda irin warning din da Hansai tayi mata yasa bata shiga ba, inda xata shiga tayi kukanta me isarta take nema, a haka ta dinga jan kafa har ta isa inda pampon yake ta jingina da bangon wani gida tana share hawayen dake makale idonta, ko yaushe xai kawo mata piya piyan da yace xai kawo mata, ji tayi baxata iya jiransa ba kuma, gwara kawai ta siya da kanta duk da kudin da ya rage mata yanxu bai wuce dari biyu ba tunda Hansai ta rabata da Usman dinta ta karfi da yaji, don kuwa wanke kafa tayi ta tafi har gidansu can cikin gari ta sanar ma iyayensa su ja ma d'an su kunne ya fita harkar 'yar ta jiddah don an sa mata rana, tun daga sannan kuma rabonta da Usman. Washegari da sassafe Hansai ta fita xuwa gidan Zulai don daga can xasu wuce kasuwan dillalai yi ma Jiddah siyayyar aure, wata tsohuwar katifa ce da ko riga babu suka siya a farashi me sauki da pillow kwaya daya, sai robobin kitchen su ma duk tsofaffi, hatta wuka basu siya sabo ba sai tsoho, suka dai kwaso tarkacen da xa a iya kai ta gidan miji da shi, suna shirin barin kasuwan Zulai tace "To baki siya xanin gado ba" Hansai tace "Ina da wani a karkashin akwati xai yi shekara goma da ajiyesa sai in bata kawai, buta kuma ta tafi da na ubanta yana can ba amfani muke da shi ba" A barrow suka kima kayan suka dau hanyar gida. Tunda Jiddah taga siyayyar da suka yi wanda ke nuna cewar an kusa aurenta da Iliya hankalinta yyi mugun tashi, Hansai kuwa tuni tayi kiran Iliya da ya sanar mata sun ma kusa shigowa kaduna, bayan ta katse kiran tana kallon Zulai da wata kawarsu Dije da ta rakasu siyayya tace "Atoh ai shkkn, yace sun wuce Abuja, kun ga wannan karan kenan da matarsa xai koma legas din" Zulai tace "Ahh shkkn, Allah dai yasa ayi bikin da mu" Dije tace "Ameen, ai Hansai 'yar halaq ce, babu wanda yayi tunanin xata yi ma jiddah wannan abun arxikin, kowa gani yake tunda Malam Isuhu ya kwanta dama shkkn watsi xata yi da jiddah, sai gashi ta ba mara da kunya, kuma in sha Allahu baxa ki ta6e ba, kin cika yar halaq wllh" Hansai tayi murmushi tace "Toh Allah na tuba ko uban na da rai wllh ba samun hakan xata yi daga garesa ba, sai in idanuwansa xai kwakule ya siyar yyi mata kayan daki, uban me garesa banda wannan rubabben gidan, bashi da komai sai wahala wllh" Zulai ta kwashe da dariya tace "Allah dai ya ji kansa, gashi nan kin rufa masa asiri kin rufa ma 'yar sa asiri, kin mata abun arxiki" Washegari Hansai ta azalzali Iliya da kira nan ya sanar mata nan da kwana biyu xa su je can gidan kawun nata da ake xancen auren a wajensa tare da magabatansa sai a saka sati biyun da tace, amma fa ba shi da kudin sadaki a yanxu sai dai a biyosa bashi, Hansai tayi shiru tana sauraronsa, can tayi kasa da murya tace "Iliya da kudin sadakin fa nake son yi mata dinki tunda ba lefe xaka yi mata ba kace baka da halin yi...." Ya katse ta cikin fada yace "Gashi nan da duk kudin hannuna na siyo maki masara kwano 8 da gawayi, ko in siyar in kai kudin sadakin?" Da sauri tace "Aa to ai tunda kace idan ka samu xaka bada babu wani damuwa xan ma kawun nawa bayani, Allah yayi maka albarka, ai kowa yasan kai me xuciyar yi ne Iliya, to a ina xaka ajiye Jiddar?" Yace "Ehh akwai shago daya gaban gidan kakana sai ta xauna nan kafin in sama mata haya" Tace "Atoh shkkn, ni na xata legas din xaku wuce tare ince shkkn xaka rabani da Jiddah gaba daya" Yace "Aa nan xan bar ta, mu ma gareji muke kwana a legas din" Hansai ta xaro ido tace "Atoh Allah ya rufa asiri, tunda ga gida ka samar mata a nan din shkkn, Allah ya kai mu wannan rana dai" Yace "Ameen" daga haka ta katse wayar tace "Toh ba shkkn ba"
Abuturrab na kwance cikin resting cabin din jirgin da yayi piloting tare da Co-pilots dinsa daga lagos xuwa kano, ko minti talatin basu yi da alighting ba, idonsa a lumshe suke duk da ya rufe fuskarsa da hulan uniform dinsu na pilot dake jikinsa, tapping dinsa aka yi a kafa, ya xame hulan a hankali, Co-pilot dinsa ne tsaye kansa, pilot din yyi wani sigh yace "Done with the Secure Cockpit checklist.... Can we??" Abuturrab ya mike xaune yace "Alright..." Pilot din yace "Ain't you changing??" Abuturrab ya kalli uniform din jikinsa yace "Not at all" Jakunkunansu suka dauka suka sauka jirgin, sai da suka gaisa da incoming crew da suka hadu da sannan suka shiga cikin airport din. Driving Abuturrab ke yi cikin motarsa da yake bari a airport, hotel din da yake sauka yawanci idan yana kano ya nufa, duk da Abbansa na da gida nan kano wanda ke a kulle babu kowa ciki baya sauka gidan don baya son xama shi kadai shi yasa ma idan kwana ya kamasa a Abuja, it's either su kwana gidansa tare da Ahmad ko Aneesah ta xo tayasa xama, ya so tafiya kaduna yau amma bai samu flight me xuwa kaduna ba or even private jet, yana shiga hotel din ya karbi daki kamar yanda ya saba, wanka yyi ya sauya xuwa kananun kaya, yayi sllh sannan ya bude pepper soup din hanta da ya sa a kawo masa with cup of coffee, ya fara ci a hankali, ajiye spoon din hannunsa yyi tunawa da yayi bai samu Mu'axxam yayi masa magana ba a kan yarinyar nan ta Hayin rigasa, ya dafe kansa don shaff ya mance, tun a jirgi da ya tuna yake Allah Allah suyi alighting ya samesa da maganan, he can even go to d extent of taking all the marriage responsibilities in har Mu'axxam din yace bashi da hali, tsaki ya d'an yi don gobe da sassafe yake son driving xuwa kaduna baxai shiga airport din ba, a hankali ya ci gaba da shan pepper soup dinsa har ya ji ya ishesa sannan ya tashi ya shiga bandaki ya wanke bakinsa ya fito yayi kwanciyarsa. Washegari Saturday karfe goma saura Abuturrab ya shigo compound dinsu... Parking yyi kusa da motarsa da yake amfani da a kaduna, ya sauka sannan ya shiga ciki, part din Aunty ya fara nufa ya sameta parlonta tana breakfast, ganinsa tace "Daga ina haka kamar an jefoka captain?" ya xauna kasan lallausan carpet din parlon yana murmushi yace "Daga kano nake" tace "Ikon Allah welcome son..." Yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau ya hanya?" Yace "Alhmdlh" mikewa tayi tace "Let me get u breakfast" Bata jira cewarsa ba ta fita, sae gata ta dawo tare da mai aiki rike da tray din breakfast din, Mai aikin ta gaishesa sannan ta ajiye, ganin kallon da yake ma tray din Aunty tayi dariya tace "Taimaka min kawai tayi ta dauko flask din ba wai ita ta hada maka ba..." Bai ce komai ba ya dau cup dake a kife ya juya yana kallon ciki keenly kamar yana neman abu, Aunty tace "To yanxu da ba Aneesah bace budurwar ka ya xaka yi da wannan kyankyanin captain, yan matan yanxu da son jiki duk ya sa sun xama kazamai" Ba tare da ya kalli Aunty ba yace "Allah ya ga xuciyana shi sa bai hadani da mara tsaftar ba" Dariya kawai Aunty tayi tace "Jiya ma Aneesar ta kirani mun gaisa ashe ta koma Abuja" Yace "Ehh ta koma..." Tace "Idan ka gama sai ka ajiyeni U-rimi don Allah, driver baya nan kuma bana son driving" Yace "Alright" Yana gama breakfast din kuwa ya mike, tuni ta dauko mayafinta da yar jaka, yace "Salem fa?" Tace "Tun yaushe Salem ya koma makaranta" Abuturrab yace "Ohh yea mun yi chatting ya gaya min, but na manta" Sai da suka fita parlon ya tuna bai je gaida Umminsa ba, ya d'an buda ido yace "Aunty bari in shiga in gaida Ummi yanxu in fito" Ta d'an 6ata rai tace "Yanxun nan fa xaka ajiyeni ka juyo Captain, cikin mintuna kadan xaka dawo ai" Bai ce mata komai ba ta fara tafiya ya bi bayanta walking slowly. Abuturrab bai dawo gidan ba sai bayan la'asar tare da ita, tana rike da ledojin atamfofi da ta sa ya siya mata a gidan da suka je, ta nufi part dinta, shi kuma ya shiga bangaren Mahaifiyarsa, kanwarsa Ramlah kadai ce parlon tana shara yace "Ummi fa?" Tace "Ta fita tare da driver yanxu" Ya shafa kansa yace "Ohk..." Juyawa yyi xai fita tace "Shine baka shigo ka gaisheta ba kuma tun safe ka dawo yaya" Ya juya ya mata wani kallo yace "Yaushe na fara wasa da ke?" Shiru tayi bata ce komai ba, yyi kwafa ya fice daga parlon. Bedroom dinsa ya shiga, sai bayan da yyi wanka ya sauya kaya sannan ya fito main parlor rike da makullin motarsa, har xai fita ya nufi kitchen jin movement a ciki, Safiyya ce a kitchen din da Ramlah sai mai aiki da alama dinner suke dafawa, yace "Is there anything to eat here?" Safiyya ta kallesa tace "Aa ba a gama ba" Juyawa yayi ya fita daga kitchen din ya bar parlon gaba daya, sai da yayi sllhn magrib sannan ya bar anguwar... Parking Abuturrab yyi yana kallon cikin karamin layin da babu haske banda na wata, yara ne bakin wani tap suna ta diban ruwa suna wasa da ruwan, tun da yamma ya so xuwa amma sbda comment din Umar a kansa ranan a hospital yasa ya ki shigowa anguwar da yamman, ya sauke glass yana ta kallon yaran, da hannu yyi ma wani yaro cikin yaran alamar ya xo, yaron ya taho da sauri, dari biyar ya dauka cikin motar ya mika ma yaron yace "Kaje can gidan da ake siyar da awara ka kira min yarinyar dake siyar da awaran" Yaron ya ruga da gudu xuwa gidan, yana isa ya kutsa kai ya shiga, Hansai na xaune tsakar gida Bibalo na haska mata fitila tana daure busasshiyar kubewa a leda, Yaron yace "Ina wuni maman Bibalo" Hansai tace "Lafiya lau, me xaka siya?" Yace "Aa wani me mota ne yace in kirawo me awara" Hansai ta kalli Jiddah dake duke bakin kwaroron wanke wanke tana yi, Hansai tace "To ai kuwa xuwa xaki yi ki ji me ke tafe da shi, tunda yasan yanayin garin kilan wani alherin ya xo mana, ko kuma Bibalo ta je, yan sa idon anguwar nan sae su iya juya mana xance yanxu yanxun nan...." Jiddah dai bata dago ba ta ci gaba da abinda take yi, Mikewa Bibalo tayi da sauri ta ajiye fitilan hannunta tace "Bari in je ni" Mayafi ta figa ta fice daga gidan tana ce ma yaron taho ka nuna min inda yake, can bakin titi yaron ya nuna mata, Abuturrab ya dinga kallonta daga cikin motar, tun daga tafiyar ya gane ba jiddah bace har kuwa ta iso bakin titi, tsaye tayi jikin motar, ya sauko yana kallonta, tayi fari da ido tana wasa da mayafin kanta tace "Sannu da xuwa...." Yace "Ina 'yar uwar taki" ta buda ido sosai tace "Yo ae ta daina fitowa ynxu sbda bikinta sati me xuwa ne, kasan har iyayen iliya sun xo anyi komai yau..." Kallonta ya dinga yi ko kiftawa babu, tace "Idan wani abu ne gani ni ka bani in ji Baabarmu in kai mata" Ya dauke kai daga kallonta yace "Mu je xan ba Baabar taku da kaina" Da sauri ta shiga gaba yana biye da ita, sae wani rangwada take har suka iso kofar gidan, tace "Bari in je in mata magana" daga haka ta shige ciki, Hansai na ganinta tace "Me ya baki?" Bibalo tace "Yace ki je yana kofar gida" Da sauri Hansae ta figi gyale ta yafa ta fita kofar gida, dukawa tayi ta gaishesa ya sauke idonsa shi ma ya gaisheta, ta amsa cike da nutsuwa tace "Sannu da xuwa Alhaji"
07087865788✍🏻
💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖
_By Khaleesat Haiydar_📚✍🏻
8.....
Hansai ta shiga kame kame tace "Gashi babu ma wajen xama a nan Alhaji, ko xa ka shigo daga ciki a shimfida maka tabarma" Yace "Aa nagode, hakan ya isa..." Tana murmushi tace "Allah sarki... Da yake jiddar na daurayan kwanuka shine nace 'yar uwarta ta fito, jiki kam alhmdlh taji sauki sosai, duk ta shanye magungunan nata..." Abuturrab ya sauke idonsa kasa yace "Allah ya kara mana lafiya gaba daya" Hansai tace "Ameen, bari dai kawai in shiga in turo ta ku gaisa, ai yanxu nasan ta gama" daga haka ta shige gida ganin dai babu alamar Abuturrab xai bata komai, jiddah ta nufa da sauri, murya can kasa kasa tace "Tashi ki dau hijabinki ki saka ki fita yana nan kila ya fi gane ya baki, kada ki kuskura ku tsaya kofar gidan nan ki ja shi can karshen layi sbda yan sa ido, gashi iliya na gari, daga nan ma sai ki sanar masa bikin ki sati me xuwa ne idan Allah ya kai mu, kinga idan da akwai wani alkhairin da xai maki sai ya maki, kowa dai yasan ke marainiya ce ba uwa ba uba" Bibalo da ke tsaye kansu tana sauraron abinda suke cewa tace "To Baabarmu idan yaji xata yi aure fa kilan shkkn baxai sake dawowa ba, dama ba sbda awaran da take yi bakin titi bane yake tausaya mana yake bamu kudi?" Hansai tayi shiru, can tace "To kuma aure ae dole tayi abu saura sati daya dai har an gama komai, kawai ta gaya masa.. sannan ba ga ki ba, ai ke xaki ci gaba da yin awaran a bakin titi" Bibalo tace "Cabdijam, wllh baxan yi awara bakin titi ba kawayena da samarina na ganina, haka kawai?? sai dai ke ki dinga yin kayanki ni dai baxan yi ba, to ni ma ba sai a min auren ba kawai" Tana fadin haka ta shige daki tana gunguni, Hansai ta rike ha6a tace "Ikon Allah, yau naga jarababbiya, a maki aure? Duka nawa kike xa a maki aure, ita ma Jiddar ai don iliyan ya dade yana sonta ne kuma ya mana hidima ba kadan ba, ko so kike ya mana tijara yace sai mun biyasa? A gidan uban wa ma xan samu abun biyansa? ke kuma da nake da burin in samar maki makaranta cikin gari ki fara xuwa kya kawo xancen a maki aure, a can din sai kiga Allah ya hadaki da miji dai dai ke, nan banda yan kato da gora, da yan adaidaita sahu, ga leburori, ga yan gwangwan sai yan iskan anguwa, to waye sa'an auren ki duk cikinsu? Ai babu sa'an auren ki wllh, ke da kike matar babban mutum" Hansai ta kalli Jiddah da kanta ke kasa har lkcn tana sauraronta, ta hade rai tace "Baxa ki tashi kije ba kin bar bawan Allah tsaye a waje" Jiddah ta mike a hankali ta dauraye hannunta ta shiga daki ta dau Hijabinta ta sa, ta saka takalminta sannan ta fita Hansai ta bita da sauri murya can kasa kasa tana cewa "Ku bar kofar gidan ku je can bayan layi kada a samu me kai ma Iliya rahotu" Ita dai bata ce komai ba har ta fita, yana tsaye ya rungume hannayensa, a hankali ta karasa can jikin wani tsohon adaidaita da aka yi parking gaba da gidan nasu, ya bi ta da kallo sannan ya bi bayanta, jingina tayi da adaidaitan tana kallonsa cikin sanyin murya tace "Sakon da kace xaka kawo min fa?" Yayi shiru yana dubanta, ta fashe masa da kuka tace "Kasan baxa ka kawo min ba me yasa kace xaka kawo min?? Alkawari fa ka min" Ya rungume hannunsa yace "Ohk abinda kika ce xa ki sha??" Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace "Yaushe xa a daura maku auren?" Tace "Sati me xuwa, don girman Allah gobe ka kawo min, naje na tambaya a shago ance min ba dari biyu bane, kuma ni dari biyu gareni" Bude baki yayi yana kallonta da mamaki, can yace "Yaushe kika je kika tambaya?" Cikin rawar murya tace "Jiya" Ya sauke idonsa yace "To ai ni nace xan kawo maki ko? Kuma ban manta ba" Tace "Toh baka sake xuwa ba ai tun ranan" Yace "Toh gobe xan kawo maki" Ta gyada masa kai tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Sauke idonsa yyi kasa yace "Wa kika sani a kaduna bayan Baabar nan taku?" Ta girgixa masa kai a hankali tace "Ba kowa" Yace "Wa xai daura maki aure?" Cikin rawan murya tace "Kawu Jibril" yace "Waye shi?" Tace "Kawun Baabarmu ne shi" Shiru yyi na kusan minti daya sannan yace "Ki koma kice da Baabarku xan yi magana da ita" Juyawa tayi ta koma ciki, Hansai na xaune tsakar gida tana fifita tana jiranta, ganinta ta mike da sauri tace "Ya aka yi kika dade, nawa ya baki?" A hankali Jiddah tace "Yace xa ku yi magana da shi" Hansai ta hade rai tace "Bai baki komai ba?" Jiddah ta gyada mata kai, Hansai tace "Toh ba naje ba mun gaisa, maganar me kuma xa mu yi" Bibalo ta leko tace "Ke dai kije ki ji abinda xai ce maki kawai" Hansai ta nufi kofar gida da sauri, tana ganinsa ta sunkuyar da kai tana d'an murmushi tace "Cewa tayi kace xa mu yi magana ko?" Yace "Eh, yanxu take gaya min sati me xuwa xa ayi aurenta" Hansai tayi kasa da murya tace "Wllh kuwa, tun uban na da rai ya ci bashin da ya fi karfinmu, bamu da halin biya, to dai kusan auren biyan bashi ne, tunda mu dai bamu da kowa duniyar nan banda Allah, bamu da kowa bamu da komai sai rubabben gidan can, to ya xan yi??" Tana fadin haka ta fara matsar kwalla, kallonta kawai Abuturrab yake da mugun mamaki, can yace "Nawa ne kudin bashin?" Goge idonta ta dinga yi tana tunanin kudin da xata lafto, can dai tace "Dubu dari ne da ashirin wllh" Yace "Ina shi me kudin?" Nan fa hankalin Hansai ya tashi, cikin rawan baki tace "Ehh to ba garin yake ba, kawai sai dai a kai masa, noma kawai yake yi a nan amma ba d'an garin bane" Abuturrab yace "Ohk, shi ne xai aureta?" Tace "Ehh, Aa ba shi bane gaskiya, d'an sa xai aura ma, ehh babban d'an sa xai aura ma" Abuturrab yace "Ohk, dama akwai wani aiki ne da nake son in bata ta dinga yi, duk wata xa a dinga biyanta dubu dari biyu, kinga idan tayi aure baxai yiwu ba, naga kuma ta fi 'yar uwarta kwazo, dama tana farawa da wata biyu sai a kawo yar uwartata, kafin nan ita ta kware sai ta dinga sa 'yar uwar a hanya" tuni xufa ya fara keto ma Hansai tana kallonsa tace "Dubu dari biyu fa kace Alhaji?" yace "Ehh haka albashin yake, amma dai yanxu xan je in ciro kudi in bata sai ta kawo maki ki biya bashin... Xancen auren kuma sai a fasa shi" Hansai na share wani xufa da kyar tace "Toh ai shkkn Alhaji, Allah ubangiji ya kara maka girma da daukaka, yanda kake rufa mana asiri haka Allah xai rufa maka asiri kai ma" Yana kallonta yace "Ameen, amma kina ganin auren xai fasu idan aka biyasu bashin su?" Da sauri Hansai tace "Ba dole ba, dama ai sbda kudin ne suke son rabani da diyata" Yace "Toh xan je in ciro kudi yanxu..." Hansai tace "Toh turo maka ita xa ayi kuje tare?" Yace "Ehh" juyawa tayi da sauri ta koma ciki, Jiddah na daki ta hade kanta da gwiwa Hansai tace "Jiddah tashi xa ku je ya baki kudi ki kawo yanxu, duk abinda yace maki kar ki kuskura kice ba haka bane, komai yace kice masa ehh haka ne, kinji me nace??" Kallonta kawai Jiddah ke yi, Hansai ta hade rai tace "Baxa ki tashi ba an bar sa a tsaye" a hankali Jiddah ta mike ta fita dakin, yana nan tsaye ta samesa, Sai da ya kalleta sannan ya fara tafiya, bin bayansa tayi har suka isa bakin titi inda motarsa yake, Bank ya tafi a can cikin garin don cire kudi a Atm machine, ta bi sa da kallo bayan ya sauka motar, bayan wani lkci ya dawo ya shiga motar ya dau karamin leda ya xuba kudin a ciki ya ajiye, bayan few seconds yace "Tace auren biyan bashi xaki yi" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ba haka bane" ya kalleta da sauri yace "To ya ne?" Hawaye ya kawo idonta tace "Kawai aure take son yi min da iliya sbda yana kawo mata abubuwa daga legas idan xai dawo" Abuturrab yace "Shi a ina yake xaune a kaduna?" Tana share idonta tace "Nan hayi yake shi ma" Yace "Xa ki nuna min gidansu?" Ta d'an yi shiru kafin ta gyada masa kai, tada motar yayi suka bar wajen, sai da suka shigo hayi yace "Ina ne gidan nasu?" Tace "Can gaba ne amma hanyar bbu kyau mota baxai shiga ba kuma da akwai nisa, dole sai da adaidaita" Yace "Ohk..." Ta gyada masa kai kawai, dai dai layinsu ya tsaya, ta dinga jiran ya bude mata motar ganin bai bude ba ta kallesa, yace "Yanxu idan aka fasa auren naki xaki hakura da kashe kan naki?" Shiru tayi tana kallonsa, ya d'an hade rai ganin kallon da take masa yace "Ina sauraron ki?" Sunkuyar da kanta tayi tace "Ehh" bude mata motar yayi ya mika mata ledan kudin ta amsa, xata sauka yace "Jira" Komawa tayi ta xauna tana kallonsa, yace "Kin iya amfani da waya?" Ta kallesa sannan ta girgixa masa kai alamar A'a, kunna fitilan motar yyi ya dau pen da wani karamin jotter ya rubuta numbersa ya mika mata yana dubanta yace "Idan da akwai wani abu ki nemi me waya ki kirani" Ta gyada masa kai, yace "Sauka" Ba musu ta sauka motar ta rufe masa ta fara tafiya.... Hansai na ta xaune tsakar gida tana jiran shigowar jiddah, sauro duk ya cijeta sai soshe soshe take, ganin jiddah ta shigo ta mike da sauri tana kallon ledan hannunta ta karasa kusa da ita ta amshe ta bude.... xaro ido tayi tana kallon uban kudin ciki, Jiddah dai na tsaye sai kallonta take ita ma, daki Hansai ta shige da gudu duk ta rude don yan dari biyar biyar ne kudin shi sa yayi yawa, Jiddah ta juya a hankali xata shiga dakinsu kenan aka shigo gidan babu ko sallama, Iliya ne da abokansa biyu kamar an hankadosu sai muxurai suke, ya nufi Jiddah yana huci ya fixgota ya xabga mata wani wawan mari cikin katon muryarsa yace "Uban wa ya sauke ki a mota yanxu?" Hansai na jin muryarsa tayin sauri cusa ledan kudin can karkashen jakarta tana salati ta fito da gudu, wani marin ya sake wanka mata ya hadata da bango ya lafto wani uban ashar yace "Da kudin nawa a kanki kike bin kartin alhazan nan suke yawo dake cikin gari, dama an gaya min ban yarda ba sai gashi yau na gani da idona, idan baki fada min waye shi ba al-qur'an sai na sumar da ke yau...." Yana fadin haka ya kara kai mata hauri ya shakota, ihu kawai jiddah take, Hansai da jikinta ya dau rawa tace "Ji mana Iliya, wllh wllh wani abokin uban gidan babansu ne jin xata yi aure ya tafi yi mata siyayya ya bada gudunmawarsa...." Wani wawan mari xai kai mata ta kauce da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, kana ganinsa kasan a buge yake, Bibalo dai ta d'an windan dakinsu take leko su taki yarda ta fito bayan ta sakale dakin, Jiddah sai kichiniyar kwace kanta take amma ta kasa don ba rikon wasa yyi mata ba, Hansai ta nufi can bakin murhu jiki na rawa tace "Ka saurareni Iliya kada ka kashe min ita, wllh nace maka abokin wanda babansu yyi ma aiki ne a lkcn da yake raye, Jiddah ai ba haka take ba, jiddah kamilalla ce..." Sake Jiddah yayi ya juya yana kallon Hansai ya nufeta yana huci, wani ihu ta kwala tana cewa "Makota ku kawo mana dauki kar ya kashe mu...." Wani wawan naushi ya sauke mata a baki, tuni jiddah tayi waje a guje, daya daga abokan Iliya yace "Kai Iliya ta fice fahhh" iliya ya juya da sauri yace "Ku bi taaa" Duk suka fita da gudu, Iliya ya bi bayansu yana cewa daga nan kawai a kai min ita shagona, bikin banxa bikin hofi abinda har sadaki na biya naira duba sha uku, tinkiyar babata fa na dauke na siyar ko sani bata yi ba na biya sadakin, kawai a kai min amaryata..." Hansai dai tunda naushi ya sauka bakinta da ta fada cikin jerin bakaken tukwanen awaranta bata sake motsi ba sai 'yan idanuwa.... Jiddah na fita dama ta bayan layi ta xaga xuwa windon Iyah, a hankali ta dinga bubbuga windon jikinta na rawa tace "Iyah ni ce ki bude" Iyah tace "Aa ba ruwana an min iyaka da ke, ni da kika sa Hansai ta kusa cinna ma gidana wuta...." Wani ihu Jiddah ta fasa ganin Salmanu daya daga abokan Iliya, ya fixgo hannunta yace "Iliya gata na gano ta" Sai ga Iliya da gudu tare da Surajo, Iyah sai xare ido take jin ihun da jiddah ke yi, a haka Iliya ya ja ta xuwa adai daitan Surajo suka sa ta tsakiya Surajo ya hau adaidaitan ya tada, Iliya ya fiddo wukar aljihunsa yana nuna mata da jajayen idanuwansa yace "Al-qur'an idan baki rufan baki ba xan da6a maki wukar nan kowa ya huta" Tsit tayi jikinta na rawa hawaye na sauka idonta, can karshen kwalta suka kai ta, wani kuturun uncompleted house da Surajo ke ginawa, sbda rashin wajen kwana yake kwana a haka, Salmanu yace "Shikenan sai ku tare nan daren yau kafin gobe da safe Hansai taje tayi mata jere a shagon naka" Iliya yayi wani dariya ya sauka daga adaidaitan yana kallon Jiddah da ko kukan ta kasa sbda fargaba da shock, ya daure fuska yana kallonta da jajayen idonsa yace "Sauka mu shiga Amaryata ta kaina" Da kyar ta sauko daga adaidaitan ya tisa keyarta har cikin gidan wanda duk dogayen ciyayi ne, Surajo yace "To ko 'yar kifi da ruwan leda ba a siya mata ba ai" Iliya yace "Ai akwai wasu daren masu xuwa da yawa bayan wannan, idan bata ci yau ba xata ci gobe" Surajo yace "Da akwai lemo daya ma da na siyo da rana ban sha ba sai ka bata ta sha kawai" Dariya duk suka dinga kyalkyalewa da, Can jikin bango jiddah ta rakube kusa da yar katifar dake kwance a dakin da wani karamin fitila da bbu hasken kirki, ko siminti bbu a kasa, banda warin ta6a da wiwi bbu abinda dakin ke yi, ta runtse ido tana jin abubuwan kamar a mafarki, sallama su Surajo suka yi ma iliya suka fita dakin suna dariya suka yi masa sai da safe, Ya mike ya kulle kofar ya dawo ya xauna ya fiddo kwalin ta6arsa ya kunna ya fara xuka yana kallon Jiddah da ta takure ko ina na jikinta na rawa, yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri amaryata cikin bacin rai na bubbuge ki, raina ne ya baci ba kadan ba, kinsan idan raina ya baci bana ganin komai idona rufewa yake, har mutum ina iya kashewa, yo sau nawa ma aka yi hakan, kawai garbati ya ce min kusan kullum sai an xo an tafi dake an dawo a katuwar mota.... Shi ma shegen dake tafiya dake a motar ya ci sa'a bamu hadu ba wllh" Ita dai Jiddah bata ce komai ba jikinta sai bari yake, ya mike ya dawo kusa da ita ya xauna yana xukan hayakinsa yana murmushi ya rungumota kusa da shi, ta runtse ido xuciyarta na bugawa da sauri sauri, yace "Inji dai baki jin yunwa ko Amaryata?" Ta girgixa masa kai da sauri, ko kallonsa bata son yi kar ta saki ihun da take hadiyewa, ya wurgar da guntun taban hannunsa ya mike ya fara cire kayan jikinsa, Abuturrab ne ya fado mata, hawaye me xafi ya fara silalowa idonta, Bata san lkcn da ta fasa wani ihu a mugun tsorace ba ta rufe fuskarta da gwiwanta... Ya hade rai ya buga mata dundu a baya yace "Kee, ki kiyayeni fa, so kike ayi tunanin fyade xan maki bayan ke halaliya ta ce, dubu sha uku na biya jiya jiyan nan, har yanxu Babata bata san yanda aka yi da tinkiyarta ba, shine xaki kawo min iskanci, to idan xaki saki jiki ki saki, don muna nan da ke har sai an kira assalatu wllh...." Ta kallesa cikin dakiya amma muryarta na rawa tace "Fitsari xan yi" yyi murmushi yace "To ko ke fa, amaryata, ai gwara kawai ki saki jikin ki" Ya mike ya yace "Mu je in raka ki" Tashi yyi ya dagota xai cire Hijab din jikinta ta rike da sauri cikin rawar murya tace "Aa wllh sanyi nake ji" Bai saurareta ba ya cire Hijab din ya jefar kan gado ya nufi kofa ya bude yace "Mu je kiyi fitsarin" Ta bi sa da sauri jikinta na rawa, wani lungu ya nuna mata a jikin gidan, tun bata kai nan ba take jin zarni na tashi a wajen, yace "Kije kiyi ki dawo ki sha lemo kinji amarya" Ta gyada masa kai ta nufi wajen, komawa ciki yyi da sauri ya dau wandonsa ya laluba ciki ya fiddo wani karamin kwalba, sannan ya dau lemon coke dake ajiye a dakin ya bude, ya bude kwalban ya tsiyaya abinda ke ciki cikin lemon sannan ya rufe ya d'an jijjiga lemon ya sha kadan ya ajiye sauran, ya mayar da kwalban aljihunsa yana murmushi yace "Tass xa ki shanye lemon nan" xaunawa yyi gefen katifa yana jiranta, da sauri ya mike kamar wanda ya tuna abu ya nufi waje ya leka yace "Ke Jiddah, har yanxu baki yi fitsarin bane" A wangale ya ga d'an zinc din da aka yi kofa da shi na gidan, ya xaro ido ya fita da gudu yana kwala mata kira, gudu kawai Jiddah take wajajen da bbu kowa babu wasu gidaje sai ciyayi, sai da tayi gudu sosai taga wani me adaidaita ta tsayar da shi jikinta na rawa tace "Don girman Allah ka taimakeni wllh sato ni yayi, don Allah ka rufa min asiri ka taimakeni" Bata jira cewarsa ba ta shige adaidaitan don ya tsaya, shi ma mai adaidaitan duk a tsorace yake ya dinga gudu har suka shigo cikin mutane, har sannan Jiddah waige waige take gabanta na faduwa, sai da suka shigo hayi sosai sannan yace "Daga ina suka dauke ki?" Tace "Can cikin gari" Ya girgixa kai yace "Yanxu ina xa ki?" Shiru tayi don tasan tana komawa gida yanxu Iliya xai iya xuwa can gidan, da sauri tace "Cikin gari xan je don Allah" Dai dai kano road mai adaidaitan ya tsaya yace "To anguwan naku ba shi da sunana ne a cikin garin, ni fa nan ne iyakata?" Lkci daya hawaye ya kawo idonta ta bude tafin hannunta tana kallon takardan da Abuturrab ya bata daxu, har lkcn takardan na hannunta gam, ta kalli mai adaidaitan cikin sanyin murya tace "Don Allah kana da waya?" Yace "Ehh" tace "Toh ka taimaka ka kira min number nan don Allah" ya amshi takardan ya dau wayarsa ya kwashe lambar sannan yayi dialing, Abuturrab na xaune parlon Abbansa yana masa calculating din order din da Abban nasa yyi daga waje na kayan auren Ramlah wayarsa ya fara ring, Abba ya kallesa ganin ba daukan wayar xai yi ba yace "Pick ur call" hakan yasa Abuturrab ya dau wayar yana kallon number kafin ya daga ya kai kunne, Mai adaidaitan ya mika ma Jiddah wayar ta amsa ta kai kunne, calmly Abuturrab yace "Hello" Hawaye ya silalo idonta tace "Ni ce" Kallon Abbansa dake kallonsa yyi da sauri, sai kuma ya sauke kansa kasa yace "Ohk ina ji" Ta fashe da kuka sosai tace "Iliya ne ya xo ya daukeni wai saboda ya ganni a motarka...." Abuturrab ya dago da sauri yace "Xuwa ina?" Cikin kuka tace "Wai shi ba sai anyi biki ba tunda ya bada sadaki, nufinsa tarewa xan yi" Abuturrab ya saci kallon Abbansa ya rasa abinda xai ce, Abbansa dake lura da shi ya mike ya shiga bedroom dinsa, mikewa yyi da sauri ya nufi kofa ya bude ya fita yace "Kina ina yanxu?" Ta bi inda take da kallo tace "Mai adaidaitan yace min kano road ne" Abuturrab yace "Ba sa wayar" Mika ma mai adaidaitan wayar tayi ta shiga share hawayen da ya ki tsaya mata, Mai adaidaitan yace "Ehh a dai dai wajen muke ma" bayan few seconds mai adaidaitan yace "Toh shkkn xan jira in sha Allah" Daga haka ya katse wayar, Abuturrab ya koma parlon Abbansa, Ganin bai fito ba ya karasa bakin bedroom din yayi masa sallama, Fitowa Abba yyi, Abuturrab yayi kasa da kansa yace "Abba xan d'an je in dawo ynxu, wani abokina ne ya kirani and it's urgent" Abba yace "Alright sai ka dawo" Juyawa yayi ya fita daga parlon, ya tafi dakinsa ya dau makullin motarsa, jallabiya ne jikinsa ya fita a haka ya shiga motarsa ya bar compound din.....
07087865788✍🏻
💖💖 *Jiddatul Khair* 💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
9.....
Abuturrab yayi parking yana bin wajen da kallo ya dau wayarsa yayi dialing number da suka kirasa da shi, yana fara ring mai adaidaitan dake hira da wani me d'an kiosk a wajen ya daga, Abuturrab yace "Ka duba wani bakar mota a wajen da kace" Mai adaidaitan ya mike yana dube duben wajen, can ya hango motar Abuturrab ya kalli Jiddah dake xaune cikin adaidaitan har sannan ta takure waje daya yace "Ga sa can ya iso" Dago kai tayi da sauri sannan ta sauka daga cikin adaidaitan, tare suka tsallaka titi da shi xuwa daya side din ya nufi motar Abuturrab tana biye da shi a baya, Abuturrab ya bude motar ya sauko yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi sbda hawayen da ya kawo idonta, ya kalli mai adaidaitan ya ciro dubu biyu aljihunsa ya mika masa yace "Nagode" Mai adaidaitan ya amsa shi ma yyi masa godiya sannan ya tsallaka ya koma gun Napep dinsa, Ba tare da Abuturrab ya kalleta ba yace "Shiga" Ba musu ta shiga gaban motar, ya shiga maxaunin driver ya tada motar suka bar wajen, a hankali yake driving din yace "Bayan na tafi sai me ya faru?" A hankali ta fara basa labarin abinda ya faru bayan tafiyarsa babu abinda ta boye masa har karshe, ganin yanda take kuka ya kalleta yace "Ya maki wani abu ne?" Ta girgixa masa kai, rasa particular tunanin da xai yi yayi a lkcn, babban damuwarsa yanxu inda xai kai ta cikin daren nan, ya d'an kalleta yace "Yanxu babu wanda kika sani nan cikin gari?" Ta girgixa masa kai tace "Ba kowa" ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yana ci gaba da driving dinsa almost absentminded, parking yayi bakin gate din gidan, har Mai gadin ya mike xai bude gate ganin yayi parking a nan waje sai ya koma ya xauna, Abuturrab ya sauke glass ganin haka mai gadin ya sake tasowa da sauri ya nufosa yana murmushi cike da girmamawa yace "Barka dai ranka shi dade..." Abuturrab yace "Ya aikin?" Mai gadi yace "Alhmdlh, Baxa ka shiga ciki ba?" Abuturrab ya d'an shafa kai yace "A'a, wani d'an alfarma nake nema gun ka" Cike da natsuwa yace "Toh ina saurarenka yallabai" Abuturrab yace "Erm... Mai dakinka na nan ai?" Mai gadin yace "Ehh tana ciki wllh" Abuturrab ya kalli Jiddah yace "So nake don Allah ta d'an kwana nan wajen ku kafin gobe, amma kamar kuma hakan da takura tunda daki daya ne ko?" Da sauri Mai gadin yace "Inaa babu wani takura wllh ranka shi dade, ni ai ba baccin ma nake da daddare ba yawanci nan tsakar gida nake kwanciyata wllh, kar kaji komai" Abuturrab yace "Toh nagode, amma kada kace ma masu gidan na xo" Mai gadin yayi murmushi yace "Baxa ayi hakan ba ranka shi dade" Abuturrab ya juya yana kallon jiddah yace "Sauka, sai da safe..." Yana fadin haka ya bude mata motar, ta sauka a hankali, Mai gadin yace "Mu je ciki to...." tafiya ya fara yi ta bi bayansa sai da suka kusa gate din ta waiga ta kalli Abuturrab da ya bi su da kallo, dauke kai tayi ta bi mai gadin suka shiga cikin compound din, yayi wani sigh ya tada motarsa yayi reverse ya bar layin wani ajiyar xuciyar ya sake saukewa feeling a bit relieved. Har aka idar da sallan asuba Jiddah bacci take, matar mai gadin na idar da sallah ta d'an ta6ata tace "Ki tashi kiyi sallah lokaci yayi" a hankali Jiddah ta bude idonta ta mike xaune da sauri, daki ne babba gun katifar kadai ne suka yi demarcating da labule, yaronsu daya wanda ko yayesa ma ba ayi ba, jiddah ta mike matar ta nuna mata bandakinsu dake cikin dakin, tana fitowa matar ta bata hijab, bayan ta idar abun ka da bata saba komawa bacci ba ta kalli matar ta gaisheta sannan tace "Babu wani aikin da xa ayi?" Matar tayi murmushi tace "Aa babu, ki koma kiyi kwanciyar ki" Jiddah bata ce mata komai, amma duk yanda ta so komawa bacci bata iya ta koma ba don ta riga da ta saba da wahala, gari na wayewa ganin matar ta dau tsintsiya xata fara sharan daga nan inda suke xuwa bakin gate don gidan akwai me shara, jiddah ta amshi tsintsiyar, matar tace "Don Allah ki bari ki koma kiyi xamanki...." Murmushi kawai Jiddah tayi tace "Aa xan taya ki" Tana fadin haka ta fara sharan hakan yasa matar ta koma ciki don yi ma yaronta wanka tana yaba hankalin Jiddah, shi kuma mai gadin na can xaune waje, jiddah na cikin shara aka bude gate din gidan ta dago da sauri, sosai gabanta ya fadi ganin wanda ya shigo, a hankali ta juya tana ci gaba da sharanta, waya ne kare kunnensa ya katse wayar yace "Maman Abdallah kun tashi lafiya" Ba tare da ta bari ta kallesa ba a hankali tace "Ba ita bace" Ko rufe baki bata yi ba Maman Abdallah ta leko da fara'arta, cike da ladabi tace "Ba ita bace Dakta, bakuwa nayi, ina kwana" yana tafiya yace "Lafiya lau, Abdallah bai tashi ba?" Tace "Kaya nake sa masa ya tashi tun daxu" yace "To a gaida min shi" Tace "Xai ji Dakta" Entrance din gidan nasu ya nufa, Jiddah ta bi sa da kallo tana sharanta a hankali... Karfe takwas Maman Abdallah ta kalli Jidda bayan ta gama shiryawa cikin kayan da ta bata tace "Tunda kinyi wanka mu shiga daga ciki mu gaisa da 'yan gidan in amso mana kumallon mu, ko" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, Maman Abdallah ta goya d'anta tace "Tashi mu je, Hajiyar gidan ta tashi yanxu" A hankali Jiddah ta mike ta dau Hijabin matar ta sa sannan suka fita, Maman Abdallah ta bude kofar hade da sallama ta shiga ciki Jiddah na biye da ita, Xaunawa tayi kasa jiddah ma ta xauna kasa, Hajiya Ramlah dake parlon da murmushi fuskarta tace "Bakuwa kika yi Shafa" Maman Abdallah ta washe baki tace "Ehh wllh Hajiya, bakuwa nayi da yammacin jiya" Cike da ladabi ta risina tace "Ina kwana Hajiya" Umma tace "Lafiya lau kun tashi lafiya?" Maman Abdallah tace "Alhmdlh, su Maimuna da Siyama na ciki kenan" Umma tace "Suna ciki..." Jiddah na kallonta a hankali tace "Ina kwana?" Umma tace "Lafiya lau yan mata, sannu da xuwa.... ya sunanki?" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Jiddah" jin footstep ta dago tana kallon direction din, Ahmad ne ke sakkowa daga sama yana kallonta babu ko kiftawa, Umma tace "Ahh me babban suna ce ashe" Jiddah tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta, Umma tace "Maa sha Allah, sunan yayata gare ki, sannu da xuwa" Maman Abdallah dai sai washe baki take, Umma tace "Yar uwarki ce amma" Maman Abdallah ta sosa kai tace "Ehh kauyenmu daya" Ahmad dai sai kallon Jiddah yake, ita kuma taki yarda ta sake kallonsa, Maman Abdallah ta mike ta wuce kitchen don daukan kumallonsu, tana shiga ta dauka a inda mai aiki ta ajiye masu ta fito, Umma ta kira mai aikin tace "Tunda suna da bakuwa ki kara masu" Mai aikin ta amsa ta koma kitchen din, ba a dau lkci ba ta dawo ta mika ma maman Abdallah coolern, Cike da ladabi Maman Abdallah tace "Mun gode hajiya Allah ya kara girma" Umma tace "Ameen" Mikewa Jiddah tayi ta amshi warmer din a hannunta sbda Abdallah dake bayanta ita ma ta yi ma Umma godiya sannan suka fita, Ahmad dai ya bi ta da kallo.... He looks so confused, sak tayi masa kama da mai awaran hayi, wata xuciyar tace kawai kamanni ne me xai kawota cikin gari har cikin gidansu kuma, daga kafada yayi a ransa ya bar sa a cewar kamannin ne, ya nufi dining don yin breakfast. Karfe goma Abuturrab ya fito gida, driving yake yi with different thought in mind, wayarsa ne ya fara ring ya kalli wayar ganin Ahmad ke kiransa ya daga, Bayan sun gaisa Ahmad yace "Muna chatting kuma ka sauka" Abuturrab yace "Ehh i am driving now" Ahmad yace "To where?" Abuturrab yace "Aunty ta aikeni" Ahmad ya d'an ta6e baki yace "Ohk, wai ka dauki hutu ne naga baka koma gun aiki yau ba?" Abuturrab yace "Kai me ya dawo da kai during week day?" Ahmad yace "Wani taro xa mu yi nan kaduna, amma gobe xan koma ai, in sha Allah" Abuturrab yace "Ohk anjima xan shigo idan na dawo" Ahmad yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya ajiye, parking yyi inda ya saba parking din, ya sauka motar yana kallon layin dake cike da mutane, wani d'an saurayi dake fitowa daga layin ya kalla yace "Abokina me ke faruwa a nan?" Saurayin yace "Wata amarya ce saura sati bikinta aka nemeta aka rasa, wasu sunce angon ne ya dauketa, wasu kuma su ce uwar rikonta ta san inda take, ynxu dai ga shi angon na neman cinna ma gidan wuta wai sai an fito masa da matarsa, uwar rikon na can tana kuka da rantse rantse bata san inda take ba, jama'a kuma na ta dannan shi angon, da yake babu wanda bai san halinsa ba a unguwar nan, sai ya iya kona gidan, yanxu dai wajen yan sanda ko mai anguwa suke shirin xuwa" Abuturrab yace "Toh Allah ya kiyaye" Barin anguwar Abuturrab yayi, yana isa gidansu Ahmad yayi parking a waje, ya sauka motar gaisawa yayi da mai gadi dake xaune a waje sannan ya xauna kusa da shi murya can kasa yace "Kayi hakuri babu wani bayani na kawo maku yarinya..." Mai gadin ya katse sa da sauri yace "Babu komai ranka shi dade, kar ki ji komai wllh, xata iya xamanta har iya sanda xaman nata xai kare a nan, ni bani da matsala haka ma mai dakina.." Abuturrab ya sa hannu aljihu ya fiddo dubu biyar ya mika masa yace "Gashi ka rike wannan" Mai gadin ya girgixa kai yace "Aa kar mu yi haka da kai don Allah" Abuturrab ya ajiye masa kudin ya mike ya shiga gate din gidan, Babu kowa tsakar gidan ya kalli building din mai gadin sannan ya nufi main entrance din gidan. Kiran azahar ne ya sa shi fitowa tare da Ahmad xa su tafi masallaci, Jiddah na xaune compound din kan karamin kujera kusa da dakin mai gadin da ruwa cikin buta a gabanta tayi nisa tunanin da take, Har suka kusa isowa wajen Abuturrab kallonta yake haka ma Ahmad, kamar ance ta daga kai tayi ido hudu da su, sosai gabanta ya fadi ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara alwala da ruwan butan gabanta har suka fita compound din, sai a sannan Ahmad ya kalli Abuturrab yace "Don Allah wa yarinyar nan tayi maka kama da???" Abuturrab yace "Wacce yarinya?" Ahmad yace "Yarinyar da ke xaune a compound" Da mamaki Abuturrab yace "Ohh dama akwai yarinya xaune a compound din?" Wani kallo Ahmad ya jefa masa, Abuturrab ya daga shoulders dinsa yace "Banyi noticing ba" Ahmad yace Karya kake "Wllh" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba, Ahmad yace "Joke apart captain, bata yi maka kama da wannan yarinyar da muke siyan awara a wajenta a hayi ba" Abuturrab ya ta6e baki yace "Kai da kake kallonta kenan idan kaje siyan awaran, ni kam banda murhu babu abinda nake gani a wajen" yana fadin haka ya shige Masallaci kafin Ahmad ya sake ce masa komai, Ahmad ya bi bayansa kawai. Ko da suka fito masallacin Ahmad ya tsaya gaisawa da abokansa na layin, Abuturrab ya shiga compound din kawai, Jiddah na ta sauri tana kwashe kayan shanyan da Maman Abdallah ta shanya don garin akwai hadari, tun da ta kallesa sau daya ta dauke kai sai da ya iso dai dai inda take tace "Ina yini?" Bai amsa ba yace "Kina da wani matsala?" Ta girgixa masa kai, ganin haka ya ci gaba da tafiyarsa, dai dai nan Ahmad ya shigo compound din bata yadda ta kallesa ba har xai wuceta sai ya tsaya yace "Bakuwa muka yi yau a gidan ashe?" Taki yarda ta kallesa still, tayi kasa da murya tace "Ina yini" yayi murmushi yace "Lafiya lau, sannu da xuwa" Maman Abdallah ta leko tace "Dakta Abdallah fa boyewa yake idan yaji muryar ka" Ahmad yayi murmushi yace "Ae kice masa alluran ya kare" Ta kwashe da dariya tace "Lallai kam, shi dai ya tsorata da kai kawai Dakta" Ahmad yace "Ashe bakuwa muka yi gidan" Tace "Ehh wllh yar uwata ce daga kauyenmu ta xo jiya da yamma" Yace "Allah sarki, toh barkan ta da xuwa" Maman Abdallah tace "Ae ko dai Dakta, mun gode" Murmushi yayi ya ci gaba da tafiya a xuciyarsa ya kara gaskata cewa lallai kamanni ne kawai suka yi da me Awara a hayi, but the resemblance is so obvious even the dimples and large eyes, can balcony Abuturrab ya tsaya duk yana jin abinda suke fada, sai da ya iso Abuturrab yace "Kai dai baka abu da class Ahmad, meye na tsayawa hira da matar mai gadi pls?" Bai jira me xai ce ba yayi wucewarsa ciki, Ahmad ya girgixa kai kawai ya bi bayansa. Da yamma Mamam Abdallah ta ba jiddah kwanukansu ta kai can cikin gida sbda a ciki xa a sa masu abincin dare, Jiddah tace "Ta cikin parlon ake bi xuwa wajen girkin?" Maman Abdallah tace "Ehh inda muka je daxu ba, ynxu ma babu kowa gidan yaran duk sun tafi islamiyya, Hajiya nasan tana bangarenta yanxu haka, ai kinga dakin girkin da mai girki ta fito ta miko mana kumallo daxu da safe, nan xaki shiga, dakin ma ya kusa biyun wannan da muke ciki ae wllh" Jiddah ta mike ta dau babban samiran ta fita ta bar Maman Abdallah na linkin kaya, Babu kowa babban parlon kamar yanda Maman Abdallah tace, ko ina tsaf sae kamshin turaren wuta da ya kama parlon, Kasa karasawa can cikin parlon Jiddah tayi, tun da ta xo duniya bata ta6a ganin irin wannan parlon ba da ma komai na cikinsa, duk sai tsoro ya kamata, hanyar da taga Maman Abdallah ta bi daxu da safe ta bi ta d'an leka kofar da ta gani a bude ganin wasu mata biyu kuma har sun hada ido ta risina a hankali tace "Sannun ku da aiki" Duk suka amsa mata dayar tace "Shigo ki ajiye kwanon" Jiddah ta karasa kitchen din, ta kara masu sannu da aiki sannan ta ajiye kwanon, kanta a kasa tace "Me xa a kama maku?" Dayar matar tace "Aa babu komai 'yan mata, mun gode" Doguwar tace "Sae dai kawai wanke wanken dake cikin bahon wanke wanke, ba shi da yawa" Jiddah ta juya tana kallon sink da matar ke nuna mata, karasawa tayi wajen ta tsaya tana tunanin ta ya xata yi wanke wanke a takurarren waje haka sannan ta ina xa ta dinga xubar da ruwan wanke wanken, a hankali ta juya tana kallonsu tace "Ruwa da omo fa" Matar tace "Ga pampo a gabanki ki kunna, wannan roban kuma sabulun wanke wanke ne a ciki xaki matso ya fito"
Bayan magrib Abuturrab yyi parking inda ya sa6a parking ya sauka motarsa ya kulle da kafa ya karasa kofar gidansu Jiddah. Yaro ya aika ciki yayi masa sallama da mutanen cikin gidan, Hansai ce xaune tsakar gida da kawayenta biyu, Hansai ta sharbe majina tana matse hawayen kumburarren idonta tace "Wllh xai aika, waye bai san cewar shaye shaye Iliya yake ba, ni dai baxan kwana gidan nan ba yau gaskiya gwara in tafi wani wajen in kwana" Zulai tace "Aa nima dama ban bada shawaran ki kwana ba tunda ya furta sai ya kona gidan da kyar baxai aika ba" Ladi tace "Toh yanxu ina yarinyar nan ku ke tunanin xata tafi haka, wa gareta a duniyar ma gaba daya?" Hansai tace "Ai wannan magana ma bai taso ba, dolenta ta dawo duk inda ta tafi ta xo ta rabani da wannan mahaukacin mutumi, idan ya kona min gida gidan ubanwa xan koma kowa na ta kansa a rayuwar nan, dama gidan iyah nake ta tunanin ta shige amma duk dubawan da yan sanda suka yi a gidan babu ita babu alamarta" Kallon yaron da ya shigo suka yi gaba daya, yaron yace "Wai ana sallama a waje" Abuturrab ya daga kai bayan Hansai ta fito cikin gidan, ganinsa ta makale kofar xaure ta kasa karasowa, Ya karasa shi, yana dubanta yace "Ina yini?" Da kyar cikin rawar murya tace "Lafiya lau Alhaji, sannu da xuwa" kafin yace mata komai ta fashe da kuka tace "Muna cikin tashin hankali da alhini Alhaji" yana kallonta yace "Me ya faru?" Tana matsar kwalla tace "Tun jiya ake neman yarinyata har xuwa yanxu babu labarinta, ban san inda xan sa kaina ba xuciyata kamar ta fashe" Yayi shiru yana kallonta, ta sharbe majina tace "Shi kansa wanda ke da niyyar auren nata nan ya xo daxu da yamma ba irin tijaran da bai min ba har da ikirarin xai kona mana d'an gidan nan idan ba a fito masa da matarsa ba, wllh wllh bamu da masaniyar inda take, babban tashin hankalina ban san halin da take ciki ba yanxu" Yace "Yanxu ya ake ciki da shi wanda xai aureta din, baki basa kudin nasa bane?" Tace "Wllh yace baxai amsa ba, yanxu haka ma da kudin na tafi gun yan sanda na kai rahotu kasan sai an basu wani abu me d'an tsoka kafin su kula ka, sannan gidan radio da gidan talabijin duk na bi na rarraba masu kudin don su yi ta sanarwa har Allah ya bayyanata, yanxu maganar da nake maka ko dubu talatin ina jin kudin bai kai ba a ajiye a daki, 'ya ta bata fiye min komai ba a duniya?" Kallonta kawai Abuturrab yake bai ce komai ba, ta sake sharbe majina cikin rawar murya tace "In dai da wani taimakon da xaka mana yarinyar nan ta bayyana da wuri ka taimaka domin girman Allah Alhaji" Abuturrab yace "Ina shi madaurin auren nata?" Tace "Kawuna ne, tare da shi ma muke ta sintirin gidan radio da police station tun safe" Abuturrab yace "Ina son ki hadani da shi" Sosai gabanta ya fadi, yace "Yana da waya?" Da sauri tace "Aa bashi da shi, sai dai gobe in je in sanar masa, idan ka xo sai Bibalo ta kai ka" Abuturrab yace "Toh shkkn, nagode, sai goben" Daga haka ya juya ya bar wajen, ta bi sa da kallo gabanta na faduwa, da sauri ta koma ciki, Zulai tace "Waye hala?" Hansai ta share wani xufa da ya keto mata tace "Aa yan xuwa jaje ne, yanxu dai gidan Kawu Jibril xan tafi tare da Bibalo idan ya so sai mu kwana can kawai kada Iliya ya far mana cikin dare mu mutu" Ladi tace "Gaskiya kam, ku tafi can din kawai ku kwana, don kwana gidan nan ba karamin hatsari bane" Sai kusan karfe tara Hansai ta isa gidan kawun nata da Bibalo, Suna shiga d'an tsakar gidan yace "Me kuma kika xo yi nan kina neman ki ja min fitina Hansatu, ni nasan Iliya d'an daba ne amma bansan dabancin nasa ya kai haka ba, babu irin tijaran da iliya bai xo nan da tawagarsa sun min ba, in don dai shegiyar dubu ukun da kika bani ne cikin kudin sadakin yarinyar Allah ya kai mu gobe da safe in tafi in siyar da kaji na in baki kudinki, wannan tashin hankali har ina a kan dubu uku, wllh ban san tantirancin iliya ya kai har haka ba, to gaskiya baxai yiwu ba kuma ki fitar min daga gida kada ma yasan kina nan in shiga uku" Hansai ta fashe da kuka tace "Amma dai duk hatsin da yake kawo min ina dibar maka har rabin kwano wataran in kawo maka, har gawayi na sha cika maka leda me kayau kayau in kawo maka, kuma matsala ta samu sai ka rufe ido kace xaka koreni, cewa yayi fa xai kona gidanmu, idan na shashantar da batun ya babbake mu cikin dare fa?" Kawu Jibril yace "Toh ni cewa yayi xai ruguje gidan, ganinki ciki ai sai ya kara tunxurasa ya aikata hakan" Hansai na matsar kwalla tace "Yanxu duk ba wannan ba, dama wani Alhaji ne ya xo xai taimake mu kan lamarin da ganinsa babban mutum ne me fada aji, kuma tun mutuwar isuhu yake xuwa siyan awara ya mana ihisani, yanxu dai so yake ku hadu gobe a kan lamarin nan, don Allah ka sanar masa duk mun je gidan radio da gidajen talabijin din kaduna kai rahotu, dubu biyar xan baka kar kaji komai" Yace "Ina dubu biyar din?" Tace "Ba ni nace xan baka ba, fatanmu kawai ya taimakemu Allah ya bayyano mana da shegiyar yarinyar nan mu mika ma Iliya tsiyarsa ko ma sarara, don idan ba nemota aka yi ba aka damka ma Iliya bamu da sauran kwanciyar hankali wllh" Bata jira cewarsa ba ta shige dakin matarsa tana cewa "Lantana duk garin nan babu wanda bai xo min jajen abinda ke faruwa ba amma banda ke, ko ba komai ai sai ki ajiye duk wani tsiya dake tsakaninmu a matsayinki na musulma kixo ki jajanta min wannan musiba da ta sameni..."
07087865788....✍🏻 Start ur payment for the book because i am almost and almost done with free pages kar ku ji dippp an dakata💖
💖💖 *Jiddatul Khair**💖💖
_By khaleesat Haiydar_📚✍🏻
10....
Washegari da asuba bayan an idar da sllh Ahmad ya fito rike da karamar jakarsa, dakin Ummansa ya shiga ya gaisheta tace "Da asuba xaka tafi Ahmad?" Yace "Ehh kar nayi missing train din ne" Umma tace "To kun yi da drivern ya xo da asuba ne ko wa xai kai ka train station din??" Yace "Aa Abuturrab xai kai ni" Umma tace "Abuturrab kuma? yana garin ne? Lafiya bai koma aiki ba" Ahmad yace "Ehh satin nan yana nan yace min" Umma tace "Toh Allah ya tsare, kayi addu'a dai" Yace "Ameen Umma, in sha Allah" Har ya kai kofa tace "Har xaka tafi gashi ka mance da drugs din nawa" Juyowa yayi da sauri yace "Oops, kiyi hakuri Umma Abuturrab xai kawo maki anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya kai mu, Allah ya kiyaye hanya" sallama ya kara mata ya fita dakin, yana fita compound ya dau wayarsa ya shiga kiran Abuturrab, Abuturrab ya daga yace "Gani na shigo layin yanxu" Ahmad yace "Alright" Sai da suka yi nisa Abuturrab ya d'an kalli Ahmad yace "Medical report din da nace xaka min din fa?" Ahmad yace "Idan aka yi how will it reach you?" Abuturrab yace "The plane coming from Abuja to kano, xan yi ma pilot din magana abokina ne, sai ku hadu ka basa" Ahmad yace "Flight din karfe nawa ne?" Abuturrab yace "karfe uku" Ahmad ya tabe baki, Can ya kalli Abuturrab yace "Toh wai ma me ya hanaka komawa gun aiki kake neman medical report din karya Captain?" Abuturrab yace "That is none of ur interest, kai dai kawai kayi min medical report" Ahmad yace "Toh baxa ayi ba" Abuturrab bai kuma ce masa komai ba har suka iso Station din, Ahmad yace "Yauwa pls captain i will text some drugs now to you, na umma ne, xaka siya ka kai mata, i forgot to do so yesterday" Abuturrab yace "A hakan xan siya magani in kai mata? Kana ganin babu kaya jikina" Ahmad ya kallesa, Jallabiya ce milk color jikinsa, Ahmad yace "Shi kuma wannan bargo ne a jikinka kenan, beside ni bance da safe ba, wani pharmacy xaka samu a bude this early, kaga dole dai sai anjima" bude motar Ahmad yyi ya sauka yace "Thank you" Daga haka ya rufe motar ya shiga cikin tashan, Abuturrab ya bi sa da wani irin kallo, bayan few minutes ya ja motarsa ya bar wajen, Abuturrab ya na isa gida text din Ahmad na drugs din ya shigo, lkci daya alert din kudin drugs din ma ya shigo, tsaki Abuturrab yayi ya cire jallabiyan jikinsa ya shiga bathroom. Karfe goma saura Abuturrab ya fito dakinsa, bangaren step mum dinsa ya fara shiga ya gaisheta, tana gyara press dinta tace "Ina xuwa da sassafen nan haka, kai da nake tunanin ka dau hutu ne don ka huta" Yace "Xan je siya ma Umma drugs dinta ne" tace "Tohhh, Ahmad din fa?" Yace "Ya koma gun aiki" Tace "Toh nima ka siyo min Panadol night..." Yyi murmushi yace "Toh in sha Allah" Ya juya xai fita tace "Captain shiru shiru kuma baka turo abun ba, kada a siye wajen ne fa" Yace "Ehh ina son in sanar ma Ummi ne...." Da sauri tace "Sai ka sanar mata captain? Ina ce yanda ka dauketa haka ka daukeni?" Ya d'an yi shiru, sai kuma yyi murmushi yace "Toh nawa ne kika ce?" Tace "1.7m" yace "Toh xan tura in sha Allah" Tace "Yauwa ko kai fa, idan ka dawo anjima ka shigo da akwai wata maganan kuma" Yace "In sha Allah" daga haka ya fita, bangaren Ummi ya shiga, waya ne kare kunnenta, hakan yasa ya jingina da kofa ya jira har ta gama sannan ya risina ya gaisheta, tace "Lafiya lau..." yace "Jiya na shigo kin yi bacci" Tace "Ehh da wuri na kwanta" Yace "Ohk, sai na dawo" Daga haka ya fita dakin ta bi sa da ido. Abuturrab na shiga mota yayi ma Ahmad transfer din kudin da ya turo masa, sannan ya nufi wani babban pharmacy, ya siya duk drugs din, bai mance na Stepmum dinsa ba, ita ma ya siya mata pack har uku na drug din da tace sannan ya dau hanyar gidansu Ahmad, Sallama yyi bakin kofar parlon aka amsa masa sannan ya shiga, Umma na xaune parlon da Maman Abdallah dake xaune kasa Jiddah na gefenta alamar gaisheta suka shigo yi, daga kai Jiddah tayi suka hada ido da shi ta sunkuyar da kanta, karasowa cikin parlon yyi ya xauna yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau Aliyu, ashe kana garin" Kallonsa Jiddah tayi jin sunansa a karo na farko, ya shafa kai yace "Ehh ina nan Umma, ya karfin jiki?" Tace "Ah Alhmdlh sauki ya samu" Mikewa yayi ya karasa kusa da ita ya ajiye mata ledan maganin hannunsa yace "Ga drugs din naki Umma" tace "Toh nagode son, Allah yayi albarka" komawa yayi ya xauna yace "Ameen" tace "Ya su yaya?" Yace "Suna lafiya..." Tace "Toh a kawo maka breakfast?" Tana fadin haka ta mike, yace "Aa umma nayi breakfast a gida" Umma tace "Toh ga awara da Maman Abdallah da mai sunan yaya suka yi da safe, u will like it" Ya d'an kalli Jiddah da kanta ke kasa, Umma ta mike ta nufi kitchen, Abuturrab ya girgixa kai da sauri xai yi magana sai kuma yyi shiru ya sauke boyayyen ajiyar xuciya, Maman Abdallah na kallonsa da fara'a tace "Ina kwama abokin Dakta" Babu yabo babu fallasa yace "Lfya lau" Jiddah bata dago ba ita ma tace "Ina kwana" yace "Lafiya lau" Umma ta fito kitchen, sai ga mai aiki rike da karamin tray me dauke da awara da sauce da pepper soup din naman rago a rufe a wani warmer din, dinning ta kai ta ajiye, Umma na kallon Abuturrab tace "Gashi can a dining area son" Ya d'an yi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Ko a kawo maka nan?" Ya bi dining area din da kallo sannan yace "Ohk" Nan kusa da shi mai aikin ta kawo ta ajiye sannan ta wuce, Maman Abdallah ta mike cike da ladabi tace "To Hajiya xata maki gyaran ne yanxu??" Umma tace "Eh to, ko kuma ta bari gobe ai tana nan, ko ba kwana biyu ta xo yi maki ba?" Maman Abdallah tace "Tana nan tukun wllh Hajiya, don bata ma sa ranan tafiya ba" Umma tace "Toh shkkn gobe sai tayi min gyaran" Maman Abdallah tace "Toh shkkn Allah ya kai mu Hajiya" Mikewa tayi tana kallon Jiddah tace "Toh mu je gobe sai kiyi aikin ko" Umma tace "To ki bar ta tayi kallo mana, tunda ke ba kallo kike ba" Maman Abdallah tayi dariya tace "Ehh kuma haka ne, tunda xan je maki kasuwa yanxu, ina fita hijabi kawai xan sa in tafi dama" Umma tace "Toh ki bar mata Abdallah ko baxai xauna ba" Maman Abdallah tace "Baxai xauna ba Hajiya, kiwuya ya gallabesa ai" Umma tayi murmushi tace "Toh sai kun dawo" Ko kadan Jiddah bata so haka ba duk da ba wai tana da niyyar bin ta kasuwan bane saboda tsoron kada wani da ya santa ya ganta a hanya amma xaman parlon ma bata so, Umma na lura da ita taga alamar she isn't comfortable, hakan yasa tace "Ko kuma ku tafi kasuwan kawai tare kada ta xauna shiru" Maman Abdallah da har ta nufi kofa tace "Dama tare nayi niyyar xa mu je, da kika ce ta xauna tayi kallo ne yasa nima nace ta xauna Hajiya" Sosai gaban Jiddah ya fadi, Maman Abdallah tace "Toh taso mu tafi kasuwan" Abuturrab dake xaune parlon yana sauraronsu yace "Tunda kallo take yi ki bar ta tayi kallonta mana" Kallonsa Umma tayi da mamaki, that's very odd of him, shi mutanen cikin gida ma baya shiga sabgarsu yayi masu magana balle wanda bai hada komai da su ba, Jiddah ta dago kanta amma bata ce komai ba, Umma ta d'an yi murmushi tace "Toh tayi xamanta" Maman Abdallah ta fita parlon bayan ta ce ma Umma sai ta dawo, Mikewa Umma tayi ta tafi kitchen sae gata ta dawo da karamin flask da mug ta ajiye ma Abuturrab tace "Kilan ta manta ne bata kawo maka ba..." yayi murmushi yace "Nagode Umma" Tace "Kana son madara?" Ya girgixa mata kai, tace "Yauwa nayi tunanin hakan, Ahmad ma bai fiye shan madaran ba" Sama ta nufa tace "If u are done ina daki" Yace "Alright" Bayan few minutes da tafiyarta ya daga kai ya kalli Jiddah, kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta maimakon kallon da aka barta tayi a parlon, ya bude flask din gabansa ya xuba ruwan Lipton cikin mug, wanda ya xuba ko rabin mug din bai yi ba, sae kamshi ruwan shayin ke yi, Calmly yace "Baki da wani damuwa a inda kike?" Ta dago ta kallesa sannan ta girgixa kai, bayan few seconds a hankali tace "Sai dai Baabarmu xa tayi ta nemana a gida" Kallonta yayi a takaice yace "Toh a mayar da ke wajenta kenan?" Shiru tayi tana kallonsa, can ta sauke idonta cikin sanyin murya tace "Iliyan xai iya sake biyo ni, ita ma xata iya kai ni wajensa" Abuturrab ya hade rai yace "Shine kuma xaki ce min Baabarki xata nemeki?" Bata ce komai ba, ya fara shan shayin hannunsa a hankali, tv ya dinga kallo kafin murya can kasa yace "Amma idan aka sauya maki shi wanda xai aureki yanxu da wani daban xaki amince da auren?" Kallonsa take babu ko kiftawa, yace "Ko baxa ki amince ba?" a sanyaye tace "Toh ai ban san waye shi ba" yace "Toh ni nasan sa" Tace "Toh in dai baya shaye shaye" Ya dinga kallonta sannan yace "Kina dai son kiyi aure kenan dama?" Hawaye ne ya kawo idonta tace "Baabarmu ce ke son inyi auren, kuma ai ba makaranta nake xuwa ba kawai sana'a muke yi" Bai kuma ce mata komai ba ya ci gaba da shan shayinsa, ta goge hawayen idonta, ya d'an kalleta yace "Wanda xan hada ku baya shaye shaye" A hankali tace "Toh" bude warmer din awaran yayi yana kallo yana d'an yatsine fuska, sai kuma ya bude na pepper soup dinma, lkci daya duk ya rufesu yace "Ki dauka ki kai maku can ki ci" Da sauri ta kallesa tace "Aa mun ci namu ai, kai dai ka ci ai naka ne" Ganin babu spoon a wajen tace "Bari in kawo maka cokali" Tana fadin haka ta mike tayi hanyar kitchen ya bi ta da ido sannan ya sake kallon warmer din awaran, ba a dau lkci ba ta dawo ta iso kusa da shi ta durkusa ta ajiye spoon din, sai kuma tace "In xuba maka?" Bata jira yace komai ba ta fara dibar masa awaran a plate sannan ta mika masa, calmly yace "Kwashe su nace baxan ci ba" Sauke idonta tayi a hankali sannan ta juye ta mayar cikin warmer din ta dau tray din ta mike ta wuce kitchen. Tana fitowa ta nufi kofa xata fita ya bi ta fa kallo yace "Kee, ina xaki?" Ta juyo tace "Xan xauna a waje ne" Authoritatively yace "Dawo nan ki xauna" a hankali ta dawo parlon ta koma ta rakube inda take xaune da farko ta xauna, ya ci gaba da shan shayinsa har ya gama ya ajiye mug din ya kalli agogo dake nuna sha biyu saura, mikewa yayi ya nufi kofa ya fita parlon, sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Umma yace mata ya tafi. Yana cikin driving wayarsa ya fara ring, kallon wayar yayi ganin me kiransa ya nemi suitable place yayi parking sannan ya daga wayar, Daga daya bangaren aka ce "Captain da kansa barka da wuni..." Abuturrab yace "Ya kake Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Alhmdlh Oga, Kayi scarce kawai wannan satin, daxu nake tambayarka Umar ke cewa ai baka shigo ba satin nan baka jin dadi" Abuturrab yace "Ehh ina kaduna" Mu'axxam yace "Toh ya jikin Captain!" Abuturrab yace "Alhmdlh" Mu'axxam yace "To maa sha Allah ranka shi dade" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujeran motarsa a hankali yace "Kana ji na Mu'axxam?" Mu'axxam yace "Ina jin ka Oga" Abuturrab yace "Kana da mata ne?" Mu'axxam yayi dariya yace "Aa tukunna dai Oga Allah bai kawo lkcn ba" Abuturrab ya gyara xamansa yace "Ohk, wata yarinya na sama maka ko hakan yayi maka?" Mu'axxam yace "Ikon Allah, Oga ai baxa ka min xabin da xai cutar da ni ba nasani wllh" Abuturrab yace "To kar ka damu, in sha Allah xan maka duk wani abu da ya kamata na auren tunda nasan kilan ba wai ka shirya bane yanxu ae" Mu'axxam yace "Allah sarki Oga, amma wllh nayi farin ciki da wannan labarin naka, naji dadi sosai, dama tuntuni nake son yin auren amma babu halin yi sbda kasan komai yanxu tsada, shi kansa auren tsada, duk da iyayen nawa sun ma riga mu gidan gaskiya sai kanni da yayyi, da dangi, amma ginin da nake yi a kauyenmu shi ke cinye min kudi wllh...." Abuturrab yace "Babu damuwa, Allah xai rufa asiri, amma xuwa ranan alhamis ko Juma'ah ka dau leave din kwana biyu ka xo kaduna, a nan yarinyar take, but before then ma xa mu yi magana" Mu'axxam yace "In sha Allahu kuwa Oga, Allah ubangiji ya saka maka da alkhairi, ya biya maka bukatunka na alkhairi, ya ji kan iyaye da kakanni, wllh nayi farin ciki sosai Oga" Abuturrab yace "Maa sha Allah, xa mu yi magana" Daga haka ya katse wayar, wani ajiyar xuciya ya sauke... this is now almost settled saura mutanen Hayi kuma yanxu, tada motar yayi ya ci gaba da driving din nasa. Kawu Jibril sai muxurai yake daga inda yake xaune jin abinda Abuturrab ke cewa, Hansai ta marairaice tana wuri wuri da ido tace "Ni kuwa Alhaji sai nake ga fa kamar idan mun koma gun 'yan sandan nan maganar nan babba xata xama, Iliya fa bai bari mun yi baccin kirki ba daren jiya a gidan nan, ni har na sadakar jiya xan mutu, saboda ka sanar min da xuwanka yasa na koma can gida karfe goma nayi ta jiranka sai gashi ka xo bayan azahar sannan na kawo ka wajen kawun nawa" Abuturrab yace "Ae baraxanar da yake maku ne dalilin da yasa xa aje police station din yanxu ba wani abu ba..." Abokin Kawu Jibril dake xaune tare da su yace "Ni da xa aji ta nawa kawai a tafi wajen me unguwar yankin nan gaba daya, naga yana fada aji, idan abun ya gagaresa shi sai mu koma gun 'yan sanda don gaskiya wannan yaro Iliya d'an iska ne wllh, iyayensa ma ba isa suka yi da shi ba balle wani, amma gwara a fara sako mai anguwa a lamarin nan sannan ya kai mana gaban hukuma koko ya ku ka ga?" Hansai tace "Wallahi haka ma yafi, mu je aji ta bakin me anguwan tukunna" Kallonsu kawai Abuturrab yake with surprise, su fa ko damuwa da 6atan yarinyar basa yi, damuwarsu da tashin hankalinsu Iliya da ya sako su gaba, Kawu Jibril yace "Ko ya kace Alhaji??" D'an murmushi yayi yace "Ehh hakan yayi, aje wajen nasa" Hansai ta mike tana gyara takurarren mayafinta tace "Ba sai mun sha wahalan neman abun hawa ba da motarsa ya xo babba ce duk xata kwashe mu" Abuturrab bai ce komai ba ya mike shi ma duk suka bi bayansa xuwa kofar gida, sai bayan da suka shiga motar, Hansai tace "Ita Jiddah ganinta me sauki ne wllh, nasan tsoro ne yasa ta buya wani gun, amma ko ni daya sai in samota ai, bari dai a gama da tantirin nan" Ta madubi Abuturrab ya kalleta yace "Kinsan inda take kenan?" Da sauri Hansai tace "Aa amma nasan tana nan cikin hayi babu inda xata, kasanta da shige shige da yawace yawace tunda ba jin magana take ba, baxata rasa wanda xai boyeta ba na kwanakin nan kam" Abuturrab bai kuma cewa komai ba har dai suka isa gidan mai unguwar, xuwansu ya sa shi fitowa xuwa kan tabarmansa dake shimfide a waje da wasu dattijai uku ke xaune, Bayan an gaisa Kawu Jibril yace "Toh gashi dai mun xo gareka mai unguwa...." Sanin kawun nata bai iya magana ba yasa Hansai ta amshe bayan ta maka masa harara, ta marairaice tace "Mai unguwa muna cikin tashin hankali da fargaba wallahi, don a gaskiya bamu da wani tsaro xaman mu a hayi" Mai Anguwa yace "Ikon Allah, me ke faruwa? Har kin fita takaba ne Hansai?" Hansai ta sinne kai taki basa amsansa na karshe, Nan dai ta kwashe duk abinda ke faruwa karya da gaskiya ta sanar masa tana matsar kwalla da kyar, kallonta kawai Abuturrab ke yi da mamaki don maganganu da yawa ta canxa a kan yanda shi ta gaya masa, Mai Anguwa na jinjina kai yace "Ikon Allah Iliya dai guda, d'an gidan Malam Kabiru?" Hansai na shessheka tace "Shi wllh" Yace "Toh yanxu ke kin tabbata yarinyar na nan cikin garin nan, don lafiyarta shine babban abin dubawa yanxu..." Hansai tayi saurin cewa "Tana nan anguwar wllh Mai anguwa, ai nasan babu inda xata, kawai tsorata tayi yasa ta buya, yanxu idan na dage na kwalo mata kira xata fito wllh, kawai dai a gama da xancen yaron nan iliya tukun" Mai Anguwa ya girgixa kai yace "Toh yanxu xa a min kiran shi mahaifin Iliyan da shi kansa iliyan" Hansai ta xaro ido a mugun tsorace, Mai anguwan yace "Amma ke kika haifi yarinyar?" Hansai tace "Ehh 'ya ta ce" Yace "Yanxu ki rasa wanda xaki yarda ya nemi auren yar ki sai wannan takadirin Iliya? Waye bai san halinsa ba a garin nan, garin yaya har kika amince ya auri yar ki, duk uwa ta gari ai baxata so ma yar ta wannan yaro ba" Hansai ta fara matsar kwalla tace "Wallahi mahaifinta ya rasu, yarinyar nema take ta gagareni, baxan boye maka ba wllh bin maxa take, to shi nan rufa mana asiri yayi xai aureta, bayan haka kuma da tsohon bashi tsakaninsa da mahaifinta ina jin, kuma ni bani da halin biya gaskiya shi sa kawai na sadaukar ai ba a cire ran shiryuwar d'an mutum, ni ban cire ran shi ma xai shiryu ba sannan ai gwara shi kiriniya kawai yake yi, ita fa bin maxa take wllh, duk iya bakin kokarina kan yarinyar nan ya ci tura, tsoro nake kada ta jajibo min abun kunya shi sa da ya billo da xancen aurenta bani da yanda xan yi na hakura, don kowa tsoronta yake sbda halinta, sannan yana da xuciya yaron, me yi ne shi wllh" Sake baki mai Anguwa yyi yana kallonta, Abuturrab ma kallonta yake ko kiftawa babu with shock, ta sharce majina tace "Amma tunda abu ya xo da haka in da wani shawara da taimakon da xaka mana kawai kayi mai anguwa mun baka wuka da nama don a gaskiya muna cikin hatsari" Ya sauke wani ajiyar xuciya yace "Ikon Allah, to yanxu dai xan sa ayi kiran mahaifin yaron da shi kansa yaron sai a san abun yi, idan naga sulhun baxai yiwu ba sai kawai ku tafi wajen yan sanda su ma idan abun baxai sulhuntu a gunsu ba kotu xa su tura ku, amma abu me sauki a mayar ma yaron nan kudadensa ita kuma yarinya a nema mata mai hankali wanda yaji xai iya ya aureta...." Hansai ta fashe da kuka tace "Duk ba sai an kai ga haka ba wllh, Allah xai dubemu maganar ta mutu cikin ruwan sanyi, banda ta lalata rayuwarta idonta ya bude da maxa me xai sa in yi sha'awar yi mata aure bayan abinda xan kai ta da shi ma bani da shi, duka duka shekarta fa sha bakwai, har nawa take xan dage sai na mata aure banda ta lalace" Kawu Jibril dai ba baki sai idanuwa, sauran dattijan dake xaune gun sai kallon Hansai suke wasun su na tirr da ita a xuciya, don ko min lalacewar naka baxa hadasa da lalatattce ba da yayi fice a gari, Abuturrab ya d'an yi murmushi shi dai bai ce komai ba yana kara jinjina halin Hansai a ransa. Sai da suka yi la'asar Mahaifin iliya ya iso, sai ga iliya ma da abokansa yan daba irinsa sun iso wajen, Mai anguwa ya dakatar da abokan dake kokarin xaunawa kan takalmansu don tabarman ya cika yace "Ku yi hakuri yan samari kuyi jiransa ga benchi can" Suna gunguni suka bar wajen, Abuturrab ya kafe iliya da ido, ba lebbensa ba hatta fuskarsa ya dafe saboda xuke xuke.....
07087865788📚✍🏻
0 comments:
Post a Comment