Hajja tana nan tayi gaho da baki tana sauraren Ameer yazo suyi maganar komawa wajen Malamai tunda yanzu taga ya shiga jikinmu sosai zai iya aikata komai,Abbi sai Haushin Hajja yake ji ta hanasu aikata nasu ita kuma ta kasa komai ta biyewa wani Ameer.
Na dan Dade a tsaye ina tunanin me zance masa sai da na gaji nace gashi Yarima ya bamu,juyowa yayi yana daga kwancen,kudin na mika masa tare da bude masa ledar kayan zakin iri iri,a hankali yace ki basu kuje ya kyauta,To ka kirashi ka mishi godiya,Ba musu ya jawo faskekiyar wayarsa ya dannawa Yarima kira bugu biyu ya dauka suka fara suruntunsu na abokai naji Yarima yace to ya zamu shirya mata Plan din,Aayan yayi dariya tare da cewa ka bari sai mun hadu zanzo gobe ko jibi idan na samu time,ok anyway shaa cewar Yarima,Aayan yace dazu Ashe har wani wahala kayi na kudi da Sweets tnx, ban son Godiya Malam Good night I forget to tell u gobe Umma na zasu dawo tare da Abba, good to hear that sai nazo nayi missing girkin Umma tun muna London,Yarima yana dariyar Jin dadi yace ga matarka nan tafi ma Umma iyawa,Uhm gaskiya ne Night nan suka yi Sallama,ni kuwa na kuma jin ance ya plan dinmu a kanta nasan ma nice kawai na kara Jin haushi,Na kumbura kamar zan fashe da kuka,Kallo na yayi yaga yanda nayi a ransa yace to fa wannan na kasa gane meke kanta,ni kuwa Harda Haushin yace yayi missing girkin Babar Yarima wato nawa ni ba dadi bai dameshi ba har girkin wata yake tunawa yafi nawa ma wani haushi ya turnuke zuciyata naci gaba da tsaiwa a kansa rike da kudin tare da ledar kayan da Yarima ya bamu.
Kallo na ya karayi yaga kamar zance na shiga uku na lalace na hada girar sama data kasa na cokalo lips gaba kadan nake jira kuma na tsaya masa a kai, light ya kashe ba tare da yace min komai ba nima ban motsa ba kamar me gadinsa haka nake tsaye gefen bed din, mun dauki lokaci a haka yaga dai ko matsawa naki yi nan ya kara kunna light haske ya mamaye dakin,inda nake haka nake, kallona ya sake kare min ni kuma tunani nakeyi ba a sona ni ban san tsakin da Naja ya fito fili ba,a fusace ya Mike tare da dirowa daga saman bed sai da na firgita,ban kara tsurewa ba sai da naga ya zaro wata wayar wuta doguwa ya nufo inda nake da gudu na watsar da kayan na fice da shegen gudun da rabon nayi irinsa tun ranar dana je guess house Hon Chairman neman tallafi.
Dariya ma abin ya bashi dama gwadawa yayi yaga karshen rashin kunya, ban tsaya ba sai dai Su Meenat suka ji na banko musu kofa tare da fadawa Kansu,da gudu suka Mike daga baccinsu suka yi waje can Palo da gudu basuyi tunanin nice ba sabo da tunaninsu ai can nake kwana,Dariya suka bani na fito ina ce musu kai nice fa,Meenat ta manta ni yayarta ce sai da ta dura min ashar daga baya tace yi hakuri wlh na tsorata kin bani haushi muka dinga dariya Ma'eesha harda bige kafa da jikin Bed, ganinsu da kayan bacci nace ku koma Bedroom kar Aayan ya fito ya ganku a haka,Ko kunya kishinki yayi yawa cewar Ma'eesha,nace ae naji dai,suna shiga kafin na shiga suka banke kofarsu tare da Sa key wai sai daí na nemi wajen kwana.
Ni kuma tsoro nakeji na kwana ni kadai ban saba ba,lallabawa nayi na koma dakin Aayan kamar munafuka ko wacce taje yin sata haka nake sanda kamar Soja ana kwanton yaki,a hankali na tura kofar dakin Allah ya taimakeni ya kashe light ya kwanta saman Bed Amma ba bacci yake ba tunani na yakeyi gaba daya ya kasa bacci yanzu na gama sangartashi tare muke bacci idan bana kusa matsala ce a gareshi kasa bacci yake.
Lallabawa nayi yana tunaninsa baiji motsina ba har na hau saman Bed din gefe daya can na kwanta a hankali ina dauke numfashi na, nayi shuru kamar ansa wata na'ura me jawo ruhin mutum zuwa na dayan haka nakeji,gashi a kusa dani Na kasa sukuni burina na rungumeshi mu kwanta yanda muka saba,idan na taba shi kuma ina tsoro kar ya mike da fushi ya zaneni,Shi kuwa ya lula tunanina kamar yaje ya dakko ni,ji yake ma me yasa ya koreni gwara ai ina dakin ko banza ya dinga jin motsina.
A hankali nake matsawa kamar ana jana ban san sanda zuciyata ta Gaza hakura ba,idan na matsa sau daya sai na huta dan kar yaji,ji yayi kamar abu na motsi a bayansa ya firgita shima,ya kara ji ana matsowa,Sandarewa yayi gaskiya aljanune suke shafar mutum a gidan nan,shima gashi sunzo masa,na kara zakudawa kamar tsutsa,a bin yaji yayi yawa kawai ya kunna Haske dal ya haske dakin,ni kuwa Sabo da tsoro har Hawaye ne ya zubo min nasan zanji jiki yau dukana zaiyi,waje daya na dunkule a saman Bed din,wani farin ciki ne ya mamaye masa zuciya Amma bai nuna ko Alama ba, ba tare da yace komai ba ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kashe light again ya matsa can karshen Bed ya kwanta wai kar ma na taba masa jiki bayan yana so.
Juye juye na farayi ina wash cikina wayyo,bai kulani ba har na gaji nace bani da lfy fa,ya min banza,nace da gaske nake fa,shuru nan ma,nace ba karya kasan bana karya fa,nan bai ce min komai ba,nace ita dai Duniya da ake ganinta ba matabbata bace,wa ya sani ma ko Bazan kai gobe ba,ko jibi ma ba lallai na rayu ba wa ya sani ma,yau in kaine gobe ba kaine ba,duk wannan abin watakila ma Baza mu kara yi ba a duniya,mene abin fushi da juna,ni ba cewa nayi sai an soni ba,ni bance ace ana sona ba,ai ba a so dole,maybe ma idan an fada din ba lallai ayi soyayyar ba mutuwa tazo ta riski mutum,ni dan anmin shuru ina ruwana bana gaba da mutum,kuma bana rike mutum a raina kamar zuciyar Fir'auna ni ba haka nake ba ana yi min abu nake mantawa na mai da komai ba komai ba Sabo da Duniya ai ba kanwata bace Meenat ko Ma'eesha bare ta daga min kafa,Ina maganata yana jina yana dariya a boye, muryarsa naji yace ina ruwana to sai me kuma,a raina nace iyye lallai ta tabbata baya so na na gama wannan tunatarwa ta mutuwa Amma ko a jikinsa nama mutu kenan,nace to in Allah ya yarda Bazan mutu ba sai naga Yayan jikokina da tattaba kunne idan an tsaneni a harbe ni,shuru ya min kamar bacci yakeyi,nace Hmm ba komai Watarana ana kallo a gidan nan zan shanye fiya fiya ko Blitch na wanke toilet,Yace ke kika huta da duniya mu ina ruwanmu, bakin ciki ya kamani nace Allah sai na ma yanke gashina,yace kinwa kanki ke zaki daina kyau ki koma Horror me ruwanmu,nace hmm za a gani ai dai ko Allah ya kaimu gobe,naji yace ga almakashi ma yanzu zan baki idan kina so, na rasa ma me zance nace to in ba tsoro ba ace na tafi gidanmu na bar gidan nan a gani,Dariya yake a ransa,muryarsa naji yace target nake hada miki first,nan take na tabbatarwa kaina maganar nan gaskiya ce ni ake hadawa plan shi da Yarima suna so suga bayana,ni kuma sonsa ya min yawa,ban sanda na fara kuka a hankali ba,Yaji da gaske Kukan kuwa nakeyi kuma da gaske ba na wasa bane wannan,Juyowa yayi ya kara juyawa tare da cewa Hawayenki ne zai kare ki koma na jini, ina shesheka nace da...dama...Hawaye na ka..rewa?Yace sosai ma sai Jini ya biyo baya.
Da Sauri na goge hawayena na daina Kukan nace kar naje jinina ya fito,sai kuma Hawayen ya zubo na goge da Sauri ina ta gogewa yana zubowa na fara yaki tsayawa wayyo jinina na kara wani Kukan nace wlh yaki dainawa,yace shike nan anjima kadan sai Jini saukar min a Bed kar ki shafa min a Bed,na Tsorata da gaske,yace kai kamar ma jinin ne yanzu ai gashi nan ya fada yana kallon idona ina kukan Kar jinina ya fito ta ido,Ya zanyi ni na furta da muryar kuka,
yace badan halinki ba matso na hure miki yanzu Zai tsaya Hawayen kafin jini yazo,da Sauri na matsa jikinsa ya daurani a samansa sosai kamar shine katifar tawa,fuskata a saman tasa ya gwale min ido yana Hure min ido,ni kuma jina a jikinsa ban san ma hawayen ya tsaya ba tuni,sai nayi tunanin da gaske shine ya tsaida hawayen,yace to ya daina saukar min a jiki, nace kai dan Allah daga dan hawa, ki koma wajenki ko na rama nima,jin haka nace wayo zan ma a raina,na ki sauka kuwa sai ma kara gyara kwanciyata da nayi a kansa,shima wani dadi yakeji yana godewa Allah,amma sai ya nuna na takura masa sai na bar masa jiki,saman Bed ya maidani shi kuma ya haye min jiki kamar yanda nayi Amma bai sake min nauyinsa ba,tunani na nice na iya shanye nauyinsa,nace ashe ma baka da nauyi kalli yanda na iya daukanka, dan munafunci irin nasa sai yayi wani likimo yana ta faman mutsu mutsu a kaina yana jin dadinsa Amma wai sai yace a'a ni kin dameni sai mutsu mutsu kikeyi,nace Allah kaine kake motsawa,sai ya sa cinyarsa ko da hannunsa ta dabara ya girgiza min jiki sai yace ke mene haka wai baki da karfi sai wani sukur sukur kikeyi duk abinki sai na rama abinda kika min, nace wlh kaine kake motsi fa baka gani wai? Ba wani nan ni me zaisa na motsa, yasa hannu ta dabara ya zame min rigata kasa Amma sai ya dinga masifa ke abin naki har ya kai haka?to duk abinda zakiyi ko tsirara zakiyi Bazan hakura ba sai na rama, Allah kaine ka cire min ai ina jinka,nan ya dinga masifa wai ba shi bane nayi masa sharri ina ji ina gani sai shuru nayi masa,can naji ya bankaro min kirji tare da manneni a kirjinsa da Sauri nace ka gani ko gashi nan wlh Allah kaine nan kake matseni sai kace wani nice gashi na kamaka,dariya yakeyi a boye yace a'a kawai dai kice min kin lalace yanzu haka kuma kika koma yarinya dake Amma kina son dadi kema,nayi fushi tare da cewa yaushe nace ma ina so duk kabi ka makalkalemin jiki zaka ce nice,ki fadi gaskiya yarinya ya furta tare da cewa juya bayanki bana son yanda kike bankaro min kirji haka bari na karasa ramawa a bayanki Allah yasa naga kinmin wani abu kuma zaneki zanyi, Nan kuma ni har ga Allah dadin abinda yake min nakeji bana so ma a daina ko kadan,har haushinsa naji yace na juya baya a raina nace bari nima na kala masa sharri kawai na masa wayo naji dadina.
Na juya baya na tare da kifa cikina uban Hips da tudun mazaunai na kara yin sama dasu kamar zasu tashi sama🤣 Aayan dadi ya kamashi a ransa duk ya zauce ya birkice abin ya sha masa kai,Sai da yasa hannayensa ta kasan cikina ya rungumo dukiyar Fulanina,da Sauri na lumshe ido na Gaza gane a ina nake ma,maganar naji can sama kamar irin da nisa tsaka ninmu haka nake Jinta,yace me ya kawo wannan abubuwan hannuna kuma? Ko kulashi banyi ba lokacin maganarsa gida biyu nake Jinta,iri biyu take tashi a kunnena bana ganewa ni kamar na sha barasa shi kanshi gani nayi ya rabu gida wajen biyar ban san wanne Aayan na gaske ciki ba.
Wasu irin abu yake min a bayana masu nauyi da Wuyar fassara mun gama fita daga hayyacinmu niko ban san sanda na zake ba na koma ina masa abubuwa masu nauyi mun manta inda muke ko wannenmu yana jiyar da dan uwansa dadi marar misaltuwa,mun rabu da kayan jikinmu kaf ba tare da mun sani ba,Aayan ya kai kololuwa yau yaji bazai iya jurewa ba ya kamata ace yau ya gwada babbar harka,a hankali da kyar ya iya magana cikin dishewar murya tana rawa yace Babyna ki yarda yau muyi pls mu gwada ko za a samu Baby mu Haifa,Haushi ya kamani wato dan a samu da ma za ayi badan yana so na ba,nan naji gaba daya na dawo hayyacina ban nuna naji Haushin maganarsa ba nasan halinsa da mugun zuciya sai nace a'a ni bana so yanzun nan kace nice nake takura ma ina taba ma jiki, yaushene zaki daina wannan kuruciyar taki?bakya ganewa wai? Ke fa Matata ce mene idan munyi ai abin jin dadi ne ma,ga lada kuma mu Haifi danmu,a raina nace wai bazai ce yana so na ba ni ban yarda da wannan ba kawai ya min ciki ya juya min baya,gwara yasan daraja ta tukun ni ban gama yarda dashi ba kuma naji me suke Plan a kaina Bazan yarda ba,da ace dai banji hirarsu ba to ko dan na faranta masa zan yarda ya gwada ko dan mu tantance lafiyarsa ta samu ko a'a, a fili nace a'a ni bana so daga auren Business ai kai kace banda wannan , dadin aure Bazan sani ba Amma yanzu kuma kace sai naji dadin ni bana so, cike da marairaicewa yace baki san Allah yana canja komai ba? Pls ki bari muyi,na makale kafadata kamar zanyi Kuka,so kike na mutu? Baki san yanda nake ji ba baki da Imani?Nace ae ni dama bani da Imani bani da tausayi haka nake ni haka Allah ya yoni, Ok to Hakkin auren fa? Kin san dai ba wani Kasuwanci a aure ko wasa a cikinsa da gaske akeyinsa Ki bari mu sauke wannan hakkin,ni dai a'a ban yarda ba,aure fa da kike gani ba haka kawai ake yinsa ba,Sai da Allah ya saka dokoki tare da ka'idoji sannan ya gindaya sharudai ba wai kawai abinda kaga dama zaka yi ba,dole abinda Allah yace shi za ayi ba wai ra'ayin mutum ake bi ba dokokin Allah ne,wanda yanzu musulmai abinda sukeyi kenan aure ba a yinsa yanda Allah yace tare da bin dokokin Allah sai kawai abinda naga dama shi zanyi,shima mijin abinda yaga dama zaiyi shi yasa auren baya karko,idan ma yayi karko sai kaga ma'auratan basa jin dadin auren sam Sai fada yau fari gobe baki,kullum cikin bacin rai,daga mutum yayi aure 1yr tayi yawa zaka ji ana Complain both Maza da matan,bakin cikin da suke sha yafi farin cikin yawa,me ya jawo wannan? Sabo da ba a bin abinda Allah yace,ba aiki da fadar Allah abinda kowa yaga dama yakeyi a gidan auren,ya kamata Alumma musulmai Maza da mata mu san me mukeyi a aure wlh ba haka kawai akeyi ba,sai da bin dokokin Allah dake cikin tsarin aure Amma kowa sai ka rantse ma ba Allah ne ya tsara sharudai a Cikin aure ba yanda naga dama,ko yaga dama,ko taga dama shi mukeyi a daure a nemi sani sannan ayi aiki dashi sannan komai zai tafi dai dai.
Haka Aayan ya dinga min nasiha da wa'azi akan me Allah ya tsara a zaman Aure,nasan gaskiya ne kuma nima na sani sannan ina da burin aikata komai Insha'allah Amma a wannan bangaren Bazan iya ba yanzu bayan ina kokonto akan Aayan ba wani so na yake ba,kuma haka ma zan yarda ba wani gyara etc nima wlh kamar yanda Amare masu gata sukeyi nima haka zanyi nan gaba da Izinin Allah,ba irin salon da bai billo min ba,tare da rokona har ma wa'azin naki yarda,nayi tunanin Zaiyi fushi ya daina kulani sai naji akasin haka yace sha zamanki na fita hakkinki Bazan miki dole ko na takura ki ba, Allah ya ganar dake gaskiya,Dariya nayi nace Ameen kayi hakuri dan Allah sai nan gaba,ba komai karki damu ci gaba da dariyarki yanzu na tabbatar da Imaninki kadan ne ashe da gaske ne?Dan Kar ma yayi tunanin zan ji tausayinsa na canja shawara sabo da kuruciya ban san a me zai kalleni ba da Sauri nace ai ni haka aka haifeni bani Da tausayi ko kadan,yace Allah?Nace Imani ko digo bani dashi ni ko me mutum zaiyi ba ruwana,ya gane dalilina na fadan haka Amma sai ya fuske yace uhmm lallai kice ke ko dan mutuncin nan babu,gani nake nifa na gama birgewa nace ko na digo banda shi ni ai kowa ya sanni ni akan mutunci ma ko a Unguwarmu ba a shedata,Aayan yace kin birgeni ai yafi hakan,ban san kawai biye min yayi ba yana ganina yarinya me kuruciya, da yawa yanzu mata da Maza sunfi so a yabesu ba ta Kalma me dadi ba,basa ma so ace wance me hakuri ce,me mutunci,me hankali,ko wane Allah Sarki ba ruwansa da duniya etc, anfi so aji ana wance ai shegiya ce,wance bata ji ai bata da kunya,ko Wane Allah yayi shege anan,wane tsinanne ne, ai shegiya wance bata da mutunci tana birgeni,bata dagawa kowa kafa sai kaga a haka wai dadi ake ji har ana kara zakewa ana kara goga iya shege dan ayi suna a shedar banza, muyi kokari mu samu shedar arziki ta kirki a ko ina muka shiga.
Aayan a ransa shi yasan ba haka nake ba ina da Imani da tausayina sai yace to karasa ladanki karki gwada min halin wannan Lalatacciyar unguwar taku tunda baza ki bani Babban ba karasa min sauran yar Mufeen Ammah ,tausayinsa dama nake ta faman ji sosai sai da na zage na tsundumashi a nishadi tare da faranta masa yaji shi fes kuma inda yaji haushi yau ma ya kara Releasing a banza naki yarda ayi.
A hankali ya rada min a ina kika iya abubuwa haka? Murmushi nayi tare da rufe ido na sabo da kunya,nace karantawa nakeyi a wani littafi Sai watarana zan fada ma,to Kunji Readers wani sirrin zamu ji inda Mufee ta iya abubuwa na birge me gida a Bed,Aayan kuwa kullum mamaki yake yanda akayi Mufeeda ta iya abubuwa haka wanda bashi ya koya mata ba,kuma bai nuna mata ba,gasu gingima gingima ba kowacce kwararriya ce ta iya irinsu ba,yanda kuma take iya sarrafa shi gata yarinya abin yana daure masa kai,yasan kuma matarsa bata san Namiji ba ko kiss a kansa ta sanshi,wasu ma suna da aure ko sun san Maza tun awaje Amma basu iya sarrafa namiji yadda yakamata ba,kuma ba updated bane su kullum abunda suka sani shike nan ba canji,ba a ci gaba da samo new zafafa ana juyawa me gida Brain,iya style dinki ya gama saninsa a daina bacci Hausawa a daina tsayawa ana ci baya kullum maimakon ayi gaba,a dage a nemi Ilmi akan komai,a san abubuwa wanda zaki garara a wajen megida,a daina kunya ana cutar kai, Aayan ya tabbatar Mufeeda ta gama dashi gani yake ma ko wata ya aura baza ta iya gigitashi haka ba,baza ta iya da shi ba sai Mufee yar yarinya me zukar Fura.
Kara makalkaleni yayi yana shafa gashina har bacci ya kwashe mu me dadi da nauyi.
Nina fara farkawa washe gari da Safe ban iya janye jikina a nasa ba sai a hankali na zauna kusa dashi ina karewa suffarsa hadaddiya kallo a raina ina Allah yayi baiwa a nan Bazan iya rabuwa da shi ba, wani sonsa ke kara ratsani ina kallon yanda jikinsa ke sheki,komai sumul lumi ban san sanda nace a hankali Allah ya barmu tare ya sa maka sona kamar yanda nake sonka,sumarsa taci kudi me santsi da laushi na kalla tare da shafata a hankali na zare hannuna tare da jinjina kyai a raina nace Allah me baiwa.
Ina zaune sai naga ya juya tare da shafo gefen da nake da Alama ni yake nema jin bana wajen ne yasa ya bude idonsa a hankali ya sauke su a kaina tar dasu,wani shock naji har raina da bargo na,Murmushi ya sakar min nima na maida masa tare da gyara rigata da na maida jikina,da hannu ya yafito ni wai na matso ba musu na matsa jikinsa, kissing din bakina ya fara,lokacin na tabbatar mun cika masu Tsabta wanda dole nayi respecting dinsa shima dole yayi respecting dina ta wajen tsafta a ko ina,sabo da sai mutum ya cika me Tsabta ta gasken gaske ne zai tashi daga baci kaji bakinsa bai canja ba babu wani wari ko wani canji,mata sai dai an dage mijinki yaji ko daga bacci kika tashi zai iya yin kissing dinki babu wani fargaba ko zai ji wani abu daban,zai kara girmamaki ya kara sonki yasan lallai kin hadu a Tsabta, a dinga shan abubuwa masu wanke dirty na ciki sannan Brush atleast sau biyu Safe dare,sai kuma ki siyi aswaki kina yi duk time din da kika ci wani abu ko haka kawai ma,Ana wanke Harshe da can ciki wajen makogwaro,Ana amfani da gawayi toothpaste tare da gishiri,ko toothpaste da lalle, Baking Powder da Lemon tsami sai toothpaste,kullum da Safe ki samu ruwa me zafi rau rau a hada da gishiri kina kuskure bakinki dashi, a tabbatar ana yawan cin Fruits,ko lemon tsami da zuma a zuba a ruwa me dan zafi ko dumi 1 cup kullum zai wanke miki dirty ciki ba ruwanki da wari ya fito daga cikinki,na baki kuma ga yanda zaki tsaftasheshi,a dage ana samun matsala ta nan mata.
Shima idan bai sani ba bayayi a dinga ganar dashi cikin dabara,ki dinga bashi yana yi ta sigar dabara.
Aayan yasan lallai yayi dacen mata me Tsabtar gaske ko ba turare a jikinki baza aji wani ordor a jikinki ba matukar kina tsafta yanda ya dace.
Zamewa nayi daga jikinsa tare da cewa ko Brush banyi ba fa,to so what? Ya furta yana kallona kamar maye, Ni na fara shiga toilet Sabo da ya fini dadewa wajen wanka,wanka nayi tare da Brush na fito shi kuma ya shiga,mun kusa makara da Sauri na shirya tare da tayar da Sallah ina idarwa ya fito shima ya fara tasa,munyi azkhar sosai sannan na cire Hijab dina tare da busar da gashi na na gyara shi Neat na maida kayan bacci na,shima haka sai muka koma bacci.
Ma'eesha ce ta shirya mana Breakfast,sai 11am na bar dakin Aayan na koma namu tare da sake sabon wanka na cakare cikin Shadda Dark Brown yar gaske dinkin zamani doguwar riga,Na kafe dauri kowa yasan na gama haduwa kamar Balarabiya,Meenat tana schl zana exam,Maeesha sai koda irin kyan danayi takeyi kamar wata Hajiya haka na fito na zauna a Dining ina jiran Aayan.
Kamshi naji ya cika sashin ba tare da na juya ba nasan ma waye wani sanyin dadi naji a raina ban ma san Sanda na juya na kalleshi ba cikin 3qtr da riga yayi matukar bala'in kyan da ban ma sanshi dashi ba sai yau, Na kalleshi kamar nace kayi kyau sai na fasa kar ya rainani,Shima yana ta kallona da kyar kamar dole yace u look Good,tnx nace tare da fari da idona ina wani wanashi warrr,bai san sanda yayi dariya ba yace naga wannan,Na kara waresu na lumshesu,murmushi yayi tare da cewa wannan ma na karba, na kara juya idona suka kalli up and down,Nice One yace dariya nayi tare da rufe idona da tafin hannuna yace wannan ma ba laifi na kara kyalkyalewa da dariya tare da fara zuba masa abincin.
Ameer ne gaban Hajja yana zaune tana tambayashi to Ameer yaushe zamu je ne wajen malaman karfa muyi sakaci,dan karta gane yace ah Hajja ai na gama shiga jikinsu ni dama Umarninki nake jira muje kawai Saturday ko Sunday ba matsala,Hajja tana ta murna tana yawwa yanzu naji magana bana kauna na bude ido naga yaran nan a gidan nan,wlh bana kaunarsu,babu wata mace dana tsana a duk matan da Aayan ya aura sama da wannan,nema take ma ta rusa min kan zuria ta,abinda na dade ina ginawa take nema ta rusa,Ameer yace gaskiya dai nima bakiga yanda nake jin haushin shiga part dinsu ba,ba a son raina ba,bana so ko kadan basu da kunya,Hajja tace ai babbar cikin itace duk shegiyar ita ke juya komai Mufeeda ba,Ameer yaji haushin zagin Mufee da Hajja tayi Amma ya danne sai yace a'a Hajja ai ta tsakiyar data karshe Meenat da Ma'eesha sune shegun,Hajja taja tsaki jibi wani suna na Aljanu malam,tun daga sunan ma kasan na aljanune wai Ma'eesha,Dariya Ameer yayi yace Hajja kenan ni na matsu ma muje a gama da yaran nan baki daya,Hajja tace Allah ya kaimu asabar sammako za muyi asubanci da wuri.
Ranar Asabar da wuri Hajja ta shirya tsaf ta nufi wajen Ameer, ta fara buga masa kofa yasan itace kawai sai ya koma kalar me cuta ya kwanta kamar me cuta ya fara numfarfashi kamar zai mutu,Hajja taji shuru ba a bude ba nan take ta tura kofar da kanta,ai ta hango Ameer na murkususu da Sauri ta shiga tana lfy dan nan ina can ina shiri ashe kana cikin wahala me ya sameka?ta furta kamar zatayi Kuka tana girgiza shi,Da kyar Ameer yace Hajja.....ba...na...boye..miki...komai...aure...nake...so...ciwon...sha'awa ne...Ya motsa...Me yasa baka fada min ba tuntuni idan ka mutu ka barni ya zanyi tashi muje asibiti,Ameer yace Nasha magani Likita ya kawo dazu yanzu zai daina,Hajja tace ai ko dole ayi maka aure ko da Sajeeda ne,Ni wlh idan aka bani Sajeeda sai dai ciwon ya kasheni bari zanyi ya kashe ni Bazan iya yin komai da wannan ba,Hajja tace to kwantar da hankalinka sannu kaji,mu bar tafiyar sai wani satin idan Allah ya kaimu,Allah baka lfy kaji,Ameer a ransa murna yake yace Ameen yana jin dadi an fasa zuwa.
AsmaBaffa
[1/21, 11:08 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
86-90
Official
By
AsmaBaffa
AGAS, MMN HUSNA,AMINA AMINU, Mom Ammar page dinku ne domin jin dadinku.
Ameer yana ta rashin lafiyar karya sai Sunday yace ya warke da yamma ya feso uban Wanka sai part dinmu lokacin kawata Nawwara sarkin son jin Gulma da munafunci tazo min ziyara nasan badan Allah tazo ba,ganin kwakwaf tazo taje ta samu labarin fesawa,Kuma Alhmdllh taga gida iya gida,yau ta tabbatar da gaske gidan kudi nake aure ba abinda ban bata taci ba na jin dadi munyi mata babbar sauka, taci kwalliyarta ta masu rufin asiri tayi kyau kuwa ba karya, muna Hira a palo ta dameni sai ta gano Cikin Bedrooms nace to muje na rakata ko ina ta gani banda dakin Aayan,wai sai tace to dakin mijin naki fa ko duk yanda muke dake baza ki barni na gano kayan alatun ciki ba? Shuru nayi mata,tace kefa Amaryace gidan Amarya nazo gani kinga kuwa dole na ga ko ina,Nasan gulma ce kawai Allah kiyashemu mu abinda akeyi kenan yanzu.
Murmushi nayi nace banda dakin mijina ko baya nan baza ki gani ba bare yanzu da bacci yake ma,ina laifi da na nuna miki sauran me kike so ki gani?
Tabe baki tayi tare da cewa a hankali zamu shiga na kalla bazai tashi ba ta ya zai san mun shiga ma tunda bacci yake,Hmm Nawwara kenan ki hakura haka yafiye miki Bazan bari ki jawo ya tashi daga bacci ba,bai dade da farawa ba ma da kyar na samu ma ya kwanta Sabo da ya huta jiya bamu samu munyi bacci da wuri ba shine kuma zan bari a tasar min shi,ke a hankalinki ya dace ki shigarwa mace har dakin miji? Bada ni ba,Nawwara tace yaushe kika koma haka Mufeeda? Dariya nayi kawai na jata muka koma kasa nan muka hango Ameer ya shigo yana zaune,Ameer lfy kwana biyu kuwa? Murmushi yayi tare da cewa ai baku da kirki kunga shuru ko ku nemeni,Nawwara ta gaisa shi ya amsa tare da dauke kai can gefe,Nawwara sai gyara riga take tana kara bude mayafi tare da karairaya don kawai ta birge Ameer yace yana sonta itama ta shigo gidan kudi Amma ko kallo bata ishe shi ba, waye wannan fa?Nawwara ta tambaya, cousin din mijina,tace ok,muna haka sai ga Aayan yana sakkowa daga samansa yaci uban wankan Wani danyen yard Fari kar yanda ya hadu ba a magana ma,wani kishi ya soke ni bana so Nawwara ta ganshi kar taji tana sonsa nasan duk wacce taga Aayan sai taso ace shine mijinta,Aayan kuma shima bana so ya ganta Sabo da tayi kwalliya harda jambaki kar ya kyasa shine nake kishi sosai.
Nan take na bata rai kamar na boye Nawwara Amma ba hali,mikewa nayi da Sauri na Isa gabansa,Murmushi ya sakar min tare da cewa zanje wajen Daddy ne sai na fita wajen Yarima akwai wani abu da zamu tattauna a kai,Baki na turo gaba ina shagwaba ni...to wai me zaku tattauna? Kallo na kawai yayi ya share maganar yana kokarin wucewa,Nace dan Allah zamu je Saloon anjima,na aiki Drivers din gidan nan basa nan gaba daya kowa da inda na aikeshi, sai muje a Napep ko Ameer ya kaimu,a'a ke baza ki fita ba fa yace Direct,na marairaice pls kaji,ki ebi kudi ki bawa su Meenat Ameer ya kaisu Amma banda ke, ki wanke naki a gida mana, ina nuna kaina ni din?Yace kefa din,ya wuce zai fita bai ma kula ko da bakuwa ba har ina murna sai ji nayi Nawwar tayi shishigi tace Ina yini, lfy Alhmdllh ya furta da fara'a tare da tambayata frnd dinki ce? Nace ae tare muka taso a unguwa daya sunanta Nawwara,yace Ok thts Good Amma kina gani zan fita baki fada min ba,da Sauri na share zancen ina jin Haushi ana kalle min Aayan dina nace Zaka biya Office ne? Me zai kaini Office yanzu kuma,a dawo lfy Allah ya kaika ya dawo da kai lfy,yace Ameen kafin ya karasa na bude masa kofa kawai Sauri nake ya bar gidan Nawwara kar ta ganshi,yana fita na rufe kofar sannan na kalli Ameer nace Ameer Saurayi mijin yan mata,masu tashe da ji da kai,Allah ya hadaka da mata ta gari zukekiya Amma da ta sha kallon wanka da iyayi,Dariyar jin dadi Ameer yayi yau Ina yabonsa da kaina sai yace haba Aunty ai mijikinki ya fini,nace daga shi sai kai kusan irin halinku daya,wlh ya fini dan mijinki ne ba kya ganin laifinsa,nace uhmm to me kake so na baka kaci yau? tuwon danyar shinkafa miyar Kubewa danya da kifi Amma sai dare,Nace ka gani ko na fada ma irin halayenku daya da Mijina,Nawwara tana zaune tayi shuru sai tunanin Aayan take ya gama Tafiya da zuciyarta gaskiya zata dage da zuwa wajena kullum ko Aayan zai so ta ya kara ta biyu da ita ta shigo itama ta kwace gidan,ko hannunka ya rike ai ka dace wannan,cin Amanar Mata bama kawai a aureshi ba kawai a shigo a kwace gidan,a kori uwar gida ko a wulakantata su kuma su zama sune a gaba.
Ameer ka kai min su Meenat Saloon mana dan Allah,Ameer ya turo baki Amma Aunty kin san Meenat bata girmama ni ko dama Ma'eesha ce Amma wannan sai girman kai bana son kulata ni dai,kayi hakuri ka jira yanzu Meenat Zata dawo sai ku wuce Ma'eesha tana daki,kasan ina ji da kannena nafi so kullum na gansu sun hadu,Ameer yace ai ku dama Hadaddu ne Aunty,amma in kana da kyau ka kara da wanka.
Muna hira har dai Meenat ta dawo tana cin abinci nace su shirya,dama sun dameni zasu je Saloon,kudi na basu Ameer yace haba Aunty ina wajen sai kin basu kudi ina da kudi,Meenat tace mu dai a bamu kudinmu Sis Sabo da tsaro, na basu kuwa,tana karba ta Radawa Ma'eesha kinga munyi cuwa cuwa mun samu na kashewa mu kara a schl,shi kuma ya biya mana na Saloon babu ko sisinmu,Ameer yaji Me Meenat take fadawa Ma'eesha.
Ya kaisu hadadden wajen Saloon tare dashi suka shiga yaki fita wai sai yaga kalar gashinsu kamar na Maza ne ko dogo ne yanda zai musu dariya da kyau, Meenat ta zauna tare da warware gashinta Ameer ya dinga mamakin tsayinsa kamar na larabawa,haka Ma'eesha ma yace Allah ya taimakeku kuna da gashi yau da sai na dauki pics nayi status a social media,Meenat tayi dariya tare da cewa ta Allah ba taka ba to yaro,nine yaron Amma kin san na girmeki nesa ba kusa ba ma kuwa,Maeesha tace kaine ma Kwaja karewar girma nan suka fara dariyar Kwaja,yace zanje na dawo kafin a gama muku,Meenat tace a taho mana da me zafi tare da Me sanyi,fada kawai tayi sai ko gashi ana gama musu ya dawo,suna shiga mota suka ga Take away guda Wajen biyar wai duk nasu ne har Nima da nake gida,Gasassun Kifi da chips,sai Hanta lafiyayya taji hadi,ga su ice cream da yogourt.
Suna shigowa lokacin Nawwara ta min Sallama ta tafi har kudi na ebo cikin na Aayan na bata Dubu biyar da kayan kwalliya iri iri ta dinga murna tana godiya,ni kuwa Zama nayi na fara tunanin irin kyautar da nayi mata kamar wacce tazo da asiri na bata kudi masu Uban yawa haka kuma wai harda kayan kwalliya ma.
Su Meenat ne suka gyara min gidan ni kuma nayi girkin na shirya komai a Dining sannan na Shiga wanka ina tunanin Aayan yanzu suna can suna Hada min plan a raina nace duk kuyi Ku gama zaku San dani kuke zancen,yau ba Sallah nake ba shi yasa kwalliyar da nayi har da Nail paint nasa a farcena sky Blue nayi wani red wani Blue ba karamin kyau yayi min ba,nasa wando tight 3qtr me kyau baki,sai rigata Sky blue ta hadu gashina yasha gyara sai kyalli da kamshi nake ta ko ina ka rantse Balarabiya ce ni,na fito tare da Shiryawa Meenat Abincin Ameer a wani kwando me kyau nace ta kaiwa Ameer can part dinsu sabo da shi yace bazai dawo ba na bayar a kai masa abincin.
Meenat ta karba ba musu ta fita me aiki ce ta nuna mata ta shiga part dinsu su uku Mazan Ameer,Khaleel tare Mujaheed gaishesu tayi sannan ta ajiye a gaban Ameer tace ya Ameer gashi inji Sis,Yace na gode,ita kuma ta juyo zata dawo,Khaleel Kansu ya daure sai mamakin Ameer su ke yanzu abin nasa har ya kai haka? Gaskiya zasu fadawa Abbi me yake shirin faruwa kuma fa dasu aka cinye abincin nawa.
Sajeeda taga lokacin da Meenat ta shiga ta fito daga part din su Ameer shike nan ta dinga fesawa cewar Meenat bin maza takeyi abin har part din su Ameer,da sauri ta shiga sabo da kishi ta samu Ameer ai wlh Allah ya Toni asirinka dama abinda kakeyi kenan,to sai kowa yaji macuci yanzu har ajinka ya zube da zaka nemi wannan?ai gwara ko me kake so kazo wajena.
Khaleel da Mujaheed suka Mike tare da basu waje,Ameer ko kallonta baiyi ba har ta gama masifarta,yace ai ta fiki daraja da mutunci a idona ta kuma fiki class,asararriya me rabawa mazan waje,ke kike haka shi yasa kike tunanin haka kowa yake irinki,Sajeeda ta rushe da kuka tare da ficewa da Sauri.
Washe gari Sayyah kawata ce ta min waya zasu zo min ziyara tare da wasu kawayenmu yan Schl Mardiyya da Islaha,So nake Aayan ya bar gidan kafin suzo kar ma su ganshi wata ta soshi,5pm suka ce zasu zo ni kuma 4pm ina yin Sallah na bar kitchen na shiga wani Palo da nasan Aayan yana can sunyi wani meeting da abokan kasuwancinsa,Nasan ba kowa yanzu shi kadai ne,yana zaune ya baje yana cike wasu takaddun Office,Sallama nayi masa a hankali tare da Zama kusa dashi har muna gogar juna nace sannu da aiki,lemo ya kurba sannan yace Yawwa har kin gama aikin? A'a wai yau baza ka fita ba har yamma tayi? Tabe baki yayi tare da cewa no,nace yau fa Tuesday guda ai ya dace ace mutum yana aiki,Yau bazan iya fita bane shi yasa,Shuru nayi can na kara cewa gaskiya kana hutawa da yawa baka fiye fita ba jiya ma fa baka fita ba sai yamma liss,yau ma hakan take ai sai yamma zan fita,gashina na gyara na gaba nace yau muna tare kenan har dare? Bironsa ya ajiye sannan ya kalleni sosai yace korata kike?so kike na fita kenan anya kuwa kina da gaskiya tsakanin jiya da yau,jiya ma fa har murna kike na fita,a'a ni bance ka fita ba tambaya nayi na Mike zan bar palon ya riko min riga na koma na zauna amma sai nace aiki fa nakeyi kasan zanyi baki, je ki karasa aikin to,mikewa nayi na fita,har na rufe kofar na kara budewa a hankali tare da leko da kaina muka hada Ido na washe baki tare da cewa to ko zaka koma Bedroom dinka zan gyara nan? Wai wayo zan masa kar ya fito yace zaije samansa bakina su ganshi, ban san me kike nufi ba zo ki kwashi papers din sai na koma can din,Da murna nazo na kwaso masa ina bayansa yana cewa mutum da gidansa sai yanda akayi dashi ya zanyi,ina dariya har muka je Bedroom din na ajiye masa komai tare da cewa asha aiki lfy ranka ya Dade,murmushi ya saki yasan dana ce Ranka ya dade ko Yanlabai wayo na shirya masa wai zan masa.
Sai da na gama shirya lafiyayyan girki kala Hudu ga kayan Sha iri iri ko ina na gyara sai kamshi ke tashi,wanka na fada na tsantsara kwalliyata cikin fitted gown black and Silver,gogorona Silver na daurashi dan dagwas,sarka da abun hannu duka silver color wow ga red jambaki na saki gashi yalala.
Ina fesa turaruka naji sallamarsu suna knocking, fita nayi tare da bude musu su uku Sayyah,Mardiyya da Islaha yar gidan Wata babbar lauya, idanu suka zuba min yanda suka ganni kamar wata Queen,nan suka hau yabon kyauna Sayyah tace shegiyar kin ganki kuwa muna ganinki a Uniform muna rudewa Ashe kinfi ma haka gaskiya mijinki yayi dace ya huta,Mardiyya tace zai kwashi harkoki,dariya mukayi gaba daya nace kufa baku da mutunci,Islaha sarkin jiji da kai,bata kawa sai da me kudi,nima ganin mijin da nake aure masu kudi ne yasa ta biyo su dan ta tabbatarwa idonta,ta kuma taba ganin Aayan a TV tana sonsa sosai shine yanzu ta samu hanyar da zata ganshi face to face ko zata dace ni ko ban sani ba.
Zama mukayi a Palo suna kalle kalle duk sun Zama yan kauye suna kallon haduwa,Maeesha na kwalawa kira,yau sabo da na kara kankaro girmana bance Ma'eesha ba wai nima fa na Zama yar gayu sai da nayi zaman Hajiyoyi a kujera irin me ji da Hutu da Naira sannan na wani Kebe baki tare da cewa Angel...sai ga Ma'eesha ta fito da Headphone a kunnenta tana Jin waka cikin English wear riga da skert tayi kyau, da fara'a tare da ladabi ta gaishesu suka amsa Sayyah tace Ma'eesha ko,Marrdiyya tace gaskiya kuna da kyau Mufeeda,nace tnx Dear, Islaha kuwa sai wani cin magani take tana yanga sai danna waya take,tana kishi da bakin ciki.
Angel kawo musu ruwa,Maeesha ta cika musu gabansu da kayan abinci dana Sha iri iri,nace to ya akayi Frnds Gist me mene News?
Sayyah dama itace muke so close tace bari mu fara cin abincin Amarya muji ko kin iya,Nace ai kema kin sani yarinya,muna ta hira sosai banda Islaha,ko abincin taki ci sabo da bakin ciki,mu kuwa bamu San meke ranta ba ko ta kanta bamu bi ba.
Kamar Aayan yasan yau kankaro girma na da mutunci na nakeyi gaban Frnds,lekowa yayi ta sama tare da dafa jikin Karfen steps din sannan yace Baby ina kika sa min Envelop din nan,bana so frnds su gane min shi,amma munafuka Islaha tana Jin murya tasan shine da sauri kamar wata engine haka ta daga kai kamar kadangare tana ta faman kallonsa,wani haushinta na naji kamar na koreta daga gidana, gani nayi zai sakko kasa kuma yasha wanka da alama fita zaiyi, nace bari nazo na dauko ma,ina yauki da kisisina muka hadu dashi a steps,su Sayyah kallo kawai suke Sha,a gabansa na tsaya ina murmushi kamar zan shige jikinsa na zura hannayena na rungumo bayansa amma bamu hada jiki ba,kyakyawar fuskata yake karewa kallo da idanunsa masu kyau,hannu na zare tare da saka hannuna cikin nasa nace muje ka gani,ba musu ya Bini tare da zame gannunsa,ina gaba yana bayana ya daura hannayensa biyu a waist dina sai kare musu kallo yake har muka shiga Bedroom.
Islaha kasa kallon tayi sabo da bakin ciki,Sayyah da Mardiyya kuwa kunya suka ji lallai Ashe suna ganina yarinya ba ruwana da duniya Ashe haka nake sai kuskus sukeyi suna dariya,Islaha na zabga musu Harara.
Muna shiga yace na fasa fita ni duk ya wani birkice min,nace dan Allah? da ka kyauta dama a raina bana so ya fita su ganshi,yace amma sai dai in zaki zo mu kwanta,baki nayi kaga ai bazan kwanta suna Palo ba ka bari sai dare,to bazan zauna ni daya ba bari na fita,ba yanda zanyi dole na barshi ya fita tunda ina da bako,kallona yakeyi kamar zai hadiyeni kinyi kyau shine sai da zaki baki kika yi wannan kwalliyar su kika yiwa? Wani idan ya shigo fa ko Ameer,dadi ne ya kamani ko dai ya fara kishina,nace ai kasan dai ina yi kullum iri iri sai wannan kadai zaka ce tafi kyau?, bafa nufina kinyi wani kyau can da yawa ba,kin danyi dai kyau kadan,addini kuma ai baice kiwa wani ya gani ba sai Muharrami ba nufina wani abu ba is just tht na tunatar dake addi ne.
Murnata ta koma ciki haushi naji,kawai nace tnx na dakko masa Envelop da ya nema nayi waje abina ko saurararsa ban kara yi ba.
Ina fita muka dora hirarmu sai gashi ya fito zai fita,Sayyah tace ina wuni? Sai lokacin ya gane da mutane a palon,Amsawa yayi kawai da fara'a ya kara gaba,zumbur muka ga Islaha ta Mike wai ita gida zata tafi,Sayyah tace amma kin San haka ne yasa kika ce Muzo ki kawo mu a motarki? Sai Ku hau Napep ni na gaji tafiya zanyi,Nace ki Bari Driver na zai kaiku ga motoci a gidan nan sai kun Zaba,gaba tayi tare da cewa sai mun hadu a schl.
Sauri take ta cimma Aayan dan ta samu dama amma karaf sai suka ci karo da Ameer zai shigo part dinmu,karo sukayi da kai,dama tun asali kun San yan gidan basu da mutunci ko wanne bako ne babu me kulaka,yana dagowa yaga tayi ma gaba abinta,cikin zafin nama ya jawo rigarta baya tare da wanke ta da mari are u Mad zaki buga min wannan katon kan naki ki wuce baki da hankali,Hawaye ne ya zubo mata ba Marin ne ya dameta ba irin asarar da ya jawo mata bata ga Aayan ba sai fitar motocinsa taji.
Kyaleshi tayi ta wuce shima ya kara gaba yana takaici,Tana yin gaba ta hadu da Su Haneefa,Sajeeda tare da sauran yan matan,Gefe su Khaleel ne ke buga game,Tazo wucewa Haneefa tazo daukan Ball dinsu sai ta sata a kafa ta saita kan Islaha ta buga mata da karfi sai ga Islaha Tim a kasa nan ta saki Kuka baki ya fashe,su Khaleel da sauran suka dauki shewa da dariya,Bata kula su ba a tsorace da gudu ta fada yar karamar motarta ta bar gidan a gigice dama gidan idan rashin kunyarka bata kai karshe ba to baza ka iya shiga ka fita lafiya ba.
Bayan sallar Isha nasa Driver ya maida su tare da kudi ko wacce Dubu biyar kuma a kudin Aayan nake shiga kawai na ebo na basu tunda ni ba wasu kudi nake kashewa ba kuma ba baki nake ba yana dawowa nake fada masa na ebi kaza yace ba damuwa sabo da yasan ina da hankalina.
Aayan baya fita ya dade a waje ko wanne time daga aiki sai gida ko masallaci,Hankalina ya tashi Meenat bata dawo ba tunda ta tafi schl zana Exam,Kuma 4 zuwa 5pm take dawowa Normally amma gashi har bayan Isha bata dawo ba yau.
Ma'eesha tace Sis Meenat fa ya zamuyi Innalillahi har yau bata dawo ba,hankalinmu ya tashi sosai har na fara kuka ma ni ganin har Aayan naji shigowar motocinsa amma Meenat shuru,Kuka nake sharba ko sace Meenat akayi wayyo,Aayan yana shigowa yaga muna kuka yace lfy? Nace Meenat bata dawo ba tun safe har baki na sun tafi gashi mun kira mutane da dama har schl mate wai sunce ta taho gida,ina zata tsaya dan Allah idan ba saceta akayi ba,Aayan yace zata dawo ne ai mene na kuka bari ki gani,Aayan ya dinga bige bige waya ba labarin Meenat,Kawarta Husna na kira nace dan Allah da kuka tashi ko kinga Meenat sanda ta hau Napep ko Taxi? Husna tace wlh wani me Napep muka gani Anty yayi parking a bakin schl da yawa student sunje zasu hau yaki daukan kowa amma Meenat ganin yamma nayi taje tace ko zai kaita gida ba musu yace tazo su tafi yanzu Anty bata dawo ba? Ina kuka nace bata dawo ba wlh Husna an sace Meenat.
Shi kanshi Aayan jikinsa yayi Sanyi ya rasa me ma zaiyi,amma baya so ya nuna mana kar hankalinmu ya kara tashi sai ma lallashinmu da yakeyi,Muna haka sai ga Ameer ya shigo shima yace lfy? Nace Meenat Babu ta bata an saceta ina kuka na bashi labari,shuru yayi tare da Zama a kujera yace maybe wani tayiwa rashin kunya ya saceta,nace zata aikata gaba daya haka muke ba a taka mu muyi shuru sai mun rama bama daukan raini.
Ameer yana ta tunani sai kuma ya Mike yace Zo muje Ma'eesha mu bincika wani waje muji,da sauri ta maka Hijab ta bishi tana Hawaye, mota suka shiga ya figa da sauri,suna tafiya ya kira wayar Sameera Yar daba bugu daya ta dauka tare da cewa Hello waye? Ameer yace Driver din Rabiu Rabson ne yace na nemeki akwai Deal,Sameera ta kyakyace da dariya tare da cewa shege Rabson Ashe yasan dama ina nemansa,zo Ku dauki karamar shegiyar nan gata an kawo min ita har gida wlh sai sun gane cewa ba a ja damu,Ameer ya kara kumbura Murya ta yan daba yace kadan daga aikinki ice ko akwai kudi karfa ki mana yawa,tace ai ko nawa ne zan kashe akan wannan yarinyar yanzu ma nasa a sauya mata kamanni.
Ameer yace wanne gidan kuke yanzu?gidan karshen layin nan can dajin da ka sani na wajen gari nan Sameera ta gwada gidan,Nan take Ameer ya kashe waya ya kira wani cikin yaran Sameera ya kara tabbatar masa nan ne gidan,yan Sanda ya saita da komai suka nufi gidan.
Suna zuwa yan Sanda na labe Ma'eesha ta cika da mamakin Ameer yanda yake abu kamar babban soja ko Dan sanda,gashi da basirar gano matsalar abu har ya iya yin tunanin Sameera ce zata iya aikata haka,zauna a mota Ameer yacewa Ma'eesha shi kuma ya shiga gidan,ta kan me gadi yan Sanda suka fara Damkewa sannan suka shiga,Sameera na Zaune ta hakimce a saman kujera ga kartin Maza sun zagaye Meenat,mutum daya a ciki ne yake dukan Meenat duk ya fasa mata jiki da katuwar bulalar wire ta Wutar Nepa.
Meenat sai kuka takeyi Sameera tace sai ta bata hakuri ita kuma tace akan ta bata hakuri gwara a kasheta.
Yan Sanda tare da Ameer ne suka fado dakin, Meenat tana ganin Ameer shi kadai ta sani ta Mike da gudu ta fada jikinsa tare da kankameshi, Ameer yana tsaye kikam ya kasa komai,yan Sanda suka kama su Sameera da yaranta gaba daya aka hankada keyarsu,Sameera ta kalli Ameer tare da cewa u r smart zan dawo kanka sai na fito.
Ko kulata baiyi ba ya dauki Meenat kamar jaririya sabo da sun mata rauni da yawa zata bata masa lokaci, suna tafiya yace ki min shuru ni ko na jefar dake,Meenat da iya shege sai tayi Murmushi tana share hawaye ta kara wani kwantar da kanta a kirjinsa,yace anji jiki me laushi da kamshi dallah tashi da badan Anty Mufee ba bazan zo ba,a hankali tace Na dai gode yaron kirki,nine yaron naki? Shuru tayi,Maeesha tana mota ta hangosu ta danji haushi a ranta kishi tana son Ameer amma kuma ta tuna ai yar uwarta ce ko Ameer din take so ma zata barwa Meenat shi kuma ma ai ga jikinta da rauni taimako ne,
Sai murna takeyi ta fita da gudu,Ya sa Meenat a bayan mota sannan yaja sai asibiti,ya hana a fada min ina ta faman Kuka na Aayan yana lallashi,Anyiwa Meenat abinda suka dace a asibiti sannan suka taho gida,sai ganinsu nayi gaba daya Meenat na dingisa kafa,murna wajena da Hamdala ba a magana,Gaba daya muka zauna a Palo,Maeesha ta bamu labarin komai sai godiya mukewa Ameer har Aayan,Aayan yace ya akayi ka gane Sameera ce? Ameer yace tunda muka je Birthday party naji furucinta nasan sai ta aikata,ina jin ba Meenat nayi tunanin itace sabo da sunyi fada a wurin party Aayan yace sunyi ma da Wannan marar jin ya furta yana dungure min keya.
Na dinga tsinewa Sameera kuwa,Meenat tace to sarkin Mita yau kwana za ayi ba bacci kina nanata zancen nan,ai kuwa Ameer har ya tafi idan na tuno sai nace Ohhh ke duniya Allah dai ya tsinewa Sameera,Aayan yace addua zaki mata,bazan bata bakina ba nace,Meenat sun kwanta nima munyi shirin bacci ina kusa da Aayan yana zaune Saman Bed yana danna waya, nace Hmm Amma Sameera Allah ya wadaran Halinta,kallona yayi yamin shuru har ya gama abinda yake yace kwanta ki daina damuna da wata Sameera,nace Allah ai Sameerance yar Iska ta bani haushi na kwanta a jikinsa,munyi shuru har bacci ya fara tafiya dani na tuna nace Wai Sameera tana da iyaye,tsaki yaja ya juya min baya,juyowa ya sakeyi tare da rungumeni ya fara Romancing dina na zare hannunsa daga jikina tare da cewa kyaleni naji da jimamin abinda ya Dameni Sameera Allah ya kwaso jarabar duniya data lahira ya.....bakinsa baji cikin nawa,Na kwace baki na nace inba sai naci uban Sameera ba Allah ya....Ni ba Uban Sameera ba dai cewar Aayan,sai na tuna me yake nufi nayi shuru duk yanda yaso na bashi dama mu Sha murje murjenmu naki yarda ni jimami nakeyi,muryarsa naji cike da haushi yace Allah ya isa tsakanina da Sameera tazo kawai ta Rusa min Harka,Dariya nayi tare da cewa kaima ka dawo hanya ke nan? Yace yau kwana zanyi ina kwashewa Sameera Albarka ta cuceni.
Zancen muka Dena amma ya hanani sakewa da tabe tabe ban san sanda na mika wuya ba muka Sha romancing dinmu cikin nishadi da jin dadi.
Kwana biyar tsakani yaune kuma Hajja ta tasa keyar Ameer suka tafi karbo magani dole ba yanda zaiyi gudun kar ta gane ya bita sai da suka gama zagayensu dama duk ta sanar musu a waya an hada komai, duk wajen Malamin da suka je sai Ameer yace Malam to kuma me zamuyi wannan magani ya karye ko munyi aiki dashi bazai ci ba?ya dace mu sani gudun kar mu bata rawar mu da tsalle,Hajja har murna take Ameer me kaifin basira ne,bata San so yake duk ya karya maganin ya watsar dasu ba,bai so ya kona kar azo wani abu kuma ya samu Su Mufee,gwara komai da ilmi.
sai da suka huce gajiyar Hanya tace to Ameer gasu ka tafi dasu duk nayi ma bayani yanda zakayi amfani dasu,dana abinci,dana sawa a cikin pillow,kasan gado,da wanda zaka samu ka yafa mata a jiki ba tare da ta gane ba,Ameer yace an gama ya wuce da magunguna,cikin dare duka ya fito dasu wani Malamin yace ana musu fitsari sun karye,nan Ameer ya fada toilet ya tsula musu fitsari ,wasu Kuma akace idan aka kona etc duk yabi yayi musu yanda Malam yace in anyi baza suyi amfani ba sun karye, sannan ya juye komai a toilet yayi Flowshing gaba daya suka tafi.
Kwana biyu tsakani ya samu Hajja yana murna yace aiki ya kammala na gama komai sai saurare,Hajja tace badai su kamaka ba ko?yace haba ai na girmi tunaninsu.
Kusan kullum sai na je na gaisar da Daddy haka Su Meenat ma, yau ma na shiga Bedroom din Aayan domin mu kwanta na tadda suna waya da Yarima,Aayan yana dariya da gani a raina nace ta mugunta ce wannan, sai naji yace Saura kadan da kanta zata San inda ta nufa ai komai ya tabbata na gane ta gama fadawa sai kuma yanda zan tarwatsa komai,baki na bude a boye na kara danne kirjina sabo da tsorata da nayi ba Shakka ni suke nufi, wani kuka yazo min a raina nace sai an sakeni,yana gama wayar kamar me Aljanu na fada kansa Saman Bed ina kuka sosai na fara cizonsa da yakushi ina kuka nace sai an sakeni wlh bazan zauna ba,yana kokarin cireni a jikinsa ya kasa,Mari ya kwada min har biyu wanda yasa nan take na dawo haayyacina amma ban daina kukan ba,kallo na kawai yakeyi da mamaki bai San me ke damuna ba,shi yasan bai min komai ba,ni kuwa kukana nakeyi,ya kasa cewa komai duk nasa fatarsa tayi jajir inda na yakusa da cizo,jikina yayi Sanyi kuma naga ban kyauta ba,da alama na bata masa rai matuka Allah sarki ina son mijina ni dai Bana fata a sakeni bacin Raine kawai da zuciyar banza me kai mutum ta baro sai an aikata ayi dana sani marar amfani,Shesheka nakeyi naga ya Mike tare da cewa miko biro da takarda a fusace,Nan take jikina ya fara bari ina addua kar ya sakeni,a hankali na kalleshi shima ni yake kallo,nace Dan Allah karka sakeni kaji? Tsaki yaja yace kawo min nace ko,nace dan Allah ni dai dan Allah pls na fasa wlh kuskurene ina son Aurena,Yace ni ance miki mahaukacine ko yaro ne irinki da zakice nayi abu ba tunani nayi,dakko min biro nace ko ya daka min tsawa,jiki na bari nace gashi na dakko na mika masa kuma na rungumeshi tare da dabaibayeshi ta ko ina,a hankali nace in dai akan na yakushe ka ne kayi hakuri bari na biyaka fatarka,Toilet na nufa ya Bini da kallo kawai,ruwa me Zafi a bowl tare da dan towel karami fari na dakko,ban kulashi ba na cire masa riga tare da kwantar dashi tunda yana daga Zaune, yana kallon ikon Allah na gasa masa jiki,yace kin gama?nace ae,yace to kawo min takardar da biron a rude na fara ina ina da soshe soshe na kashe light duf na cire kayana duka na shige masa jikinsa gaba daya na sukurkutashi,yace ba abinda kike nufi zan rubuta ba fa abu zanyi Jotting na Office nace ni gobe kayi banda yau,Sai salo nake masa,yace fada min me yake damunki?idan baza ki fada ba kuma fitar min a room,cike da shagwaba na sanar masa komai da na naji suna fada,Dariya ya dinga yi tare da cewa amma ke anyi sakarai,kin jawo na mareki A banza, to a kan Business muke magana wanda ya hadamu da wata take shirin damfarar mu wai zata mana wayo mu kuma mun fita wayon shine fa kawai,dariyar jin dadi nayi nace budurwa ce ko bazawara? Yace Bazawara ce mene? Hmm ba komai dan Allah tana da kyau? Yace ae mana sosai,baki na tabe jikina yayi Sanyi nace nifa?Ina da kyau? Dariya shima yayi sosai yace ae kina da shi mana,nace hm yaudara dai ko,am serious ya furta nace taya zaka ce tana da kyau nima kace ina dashi ai daya zaka dauka.
Kina da kyau to,nan ma nace ban yarda ba na fara ja da baya zan Mike na bar room din,ya fisgoni na fado jikinsa yace banda Negative thinking Baby ya hade bakina da nasa yana min zafafan kisses idon na lumshe ina mayar masa da martani tare da bashi hakurin abinda na masa shima yace kin jawo na mareki am so sorry,kumatuna na shafa cike da shagwaba nace amma na Maru wlh da zafi kayi min
AsmaBaffa
[1/24, 8:17 PM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
91-95
Official
By
AsmaBaffa
HAFSAT KHAIRAN, NAFEESAT UMAR,CATTY,SUBYUSMAN10 jinjina gareku tare da gaisuwa me tarin yawa ina godiya da Sharhi.
Page na HADIZA MUKTAR yar albarka ina godiya.
Dariya Aayan yayi kadan tare da cewa bakya jine sai kin Sa mutum ya zaneki kin jawo yanzu Bazan taba yafewa Hannuna ba, ba wani nan dama ka saba Marina tun farko ba Imani ka min Dukan tsiya kamar nayi accident da mota ko ina muka hadu sai ka Mareni bai ma dace ace na kulaka ba shine Sabo da banyi ma tunani ba na aureka, Murmushi yayi tare da cewa na daina to ko me zakiyi as from today hannuna bazai taba jikinki da niyyar duka ba,sai da niyyar me to? Romancing,Caring etc ya furta wai dole bazai ce love ba shi, har yau ban gamsu ba ni nafi so a dinga cewa ana sona Amma sai na hakura nayi shuru.
Na manta ban fada ma ba na bawa bakina kudi da kayan kwalliya cikin wanda ka siya mana sai an siyo min wasu na bayar da nawa Sababbin, nawa kika basu,nace hm nayi Barna fa ni kaina naji kyautar nan da nayi har tunani nakeyi ban kyauta ba kayi hakuri Dan Allah dubu goma na kwasar maka,murmushi yayi yace me yasa kika basu har goma bayan ke nasan baza ki iya kashewa kanki goman ba? Hmm kawai naje ne naga kudin naka sunyi yawa wlh gasu a jere a jere suka birgeni naji nima yau so nake na kankaro mutunci na, na zama Hajjaju kawai shine na irga na basu,amma fa a schl suna koya min abubuwa sosai kuma ko me nake so suna min musamman Sayyah,ina wannan rigunan baccin dana dinga sawa masu kyau har kala biyar ka tuna su? Yace ae na gane to Maman Sayyah ce ta bani su da naje gidan,shine na basu dubu biyar biyar ita da Mardiyya,Badan Allah kika basu ba ke nan? Dan ki kankaro mutuncinki kika ce,kin basu kuma kina jimami kina tunanin kyautar da kikayi bata dace ba dama baki basu ba,kinga ba lada kenan kuma Sabo da suna miki kema shine kika rama musu,ba haka ake kyauta ba,iya wacce kikayi niyya ita zakiyi kuma da zuciya daya kisa Iklassi dan Allah kawai ba wani tayi min bari na mata ko ki Bada ki koma kina tinanin kudinki dama baki bayar ba,kinga ba lada sai ma ko Zunubi,kuma 10k ma tayi kadan nayi tunanin ma sunfi haka,amma abinda bana so shine indai kaya ne ni na siya miki to bana so baki amfani dasu ba ki bayar wata tayi,ke na siyawa ke nake so kiyi kwalliya dasu Sabo da ina so naje na siyo da hannuna wasu ma baki san tsadarsu ba shi yasa,idan kina son kyauta to ki karbi kudi wajena kije kisiyo ki ajiye duk wacce zaki bawa ki bata a naki,wanda na siya miki sai in kinyi amfani dasu ko na canja miki new sai ki bayar da wanda kike amfani dasu, haka akeyi ba a daukan kayan miji da ya siyo ki masa kwalliya ko amfani baki dashi ki dauke ki bawa wasu in kina haka Bazan kara bari Frnds dinki su zo.
Mata wasu don son gwaninta sai miji ya siyo miki kaya dan ki masa kwalliya ki birgeshi sai a dinga gayyato Frnds ana basu maza basa Jin dadin hakan.
Sai kuma tambayata yaushe kika je gidan su Sayyah ban san zancenba baki fada min ba? Jikina yayi sanyi nace daga schl rannan mun tashi frnds da yawa suka ce ba nisa daga schl zuwa gidan su Sayyah zasu je gaida Mamanta shine nima na bisu muka tafi tare,su basu da aure ai?ae duk yan mata ne,ke kuma fa? Ina da aure mana, sai akace miki matsayinku daya yanzu? Zaman kanki kikeyi da zaki je wani wajen ban sani ba? Da kika dawo baki fada min ba mala'iku na tsine miki,shi yasa mazaje da yawa basa so matansu suyi aiki ko makaranta idan sun aure su sai a fake da wajen aiki ko schl ayi ta yawo mara amfani,wasu ma daga can suke samun hanyar bin malamai da bokaye ko tarbiyyarsu ta lalace yanzu badan Allah ya kawo zancen ba baza ki fada min ba kenan? Kuka na fara yi masa to kayi hakuri Bazan sake ba tunanina ba wani abu bane,Shi yasa har kasuwa na raka wasu ma daga schl,munje gidajen wasu ma siyo wasu abubuwan da yawa Ban fada ma ba kayi hakuri na daina,kishi ne ya kama Aayan harda kasuwa ma gidajen mutane Maza nata kallonki kamar budurwa? A rude nace ai ban kula su ba Allah duk da yawa sun tareni wai suna sona nace ina da aure,Aayan takaici ya kara rufeshi ana gane masa mata wasu sunji muryarta ma yace daga yau ko an koma schl kin daina zuwa tunda bakya jin magana ni bana son irin wannan, kuka na nakeyi nace ni me nayi to dan Allah? Kayi hakuri Bazan kara ba daga schl wlh sai gida, na yafe miki ai Amma karki sake ki san kina da aure bana son irin shirmen nan na student,kamar an matse bakikin ki gashi kinzo kin fada min ana miki fada ki fara wani kuka,
nace to yanzu duk abinda kaine ka siya min kar na bawa kowa? No ba haka nake nufi ba,sai kinmin kwalliya dashi sosai idan na canja miki wasu sai kwashe sauran ki bayar tht's what I mean, na gane Insha'allah ba matsala,dama kana son kwalliyar tawa ne? A'a kawai dai ke kiyi kyau,wani haushi ma naji kawai nayi shuru har bacci ya kwashemu.
Sati biyu tsakani Meenat ta gama Exam tare da Ma'eesha suka shirya zasu tafi can kauyen Ammah wajen dangi za suyi sati daya daga can su Wuce Maiduguri nan dangin Abba za suyi sati daya, na hada musu goma ta arziki tare da Driver suka tafi abinsu,ni kuwa ina gida tare da Aayan,sai Ameer da yake dan shigowa idan yaga dama bai son yazo yaga muna tare da Aayan kunya yake ji,na tambayi Aayan ya bani kudi na fara zuwa gidan su Sayyah wajen Mum dinta gyaran jiki,haka take gyaran tana bani kayan tsumi,duk na kara cikowa skin dina sai sheki,santsi tare da kyalli ga uban laushi.
Nawwara ta min waya zata zo min again nace bana gida munyi Tafiya bana so tazo,amma Sabo da naci yau Saturday ina kitchen Aayan ya ce na mishi Shawarma na gane yana son Kalar tawa,knocking naji sai da na leka ta yar kafa naga Nawwara ce,abin ya daure min kai to uban me tazo yi nace mata bana nan ana dole ne,komawa nayi kitchen naki budewa tayi ta danna Door Bell shuru.
Khaleel yazo wucewa ta wajen ya ganta a tsaye tsawa ya buga mata wanda ta kusa sumewa uban me kike mana a gida kamar na ubanki anki bude miki ki tafi mana kin cika mana gida Nonsense,jiki na rawa Nawwara ta kama gabanta,Haneefa tana kallonta ta saman Bene tunaninta daga wajena take zata tafi shine taji Haushi an fara cika musu gida da baki,Sajeeda ma tana wajen suna kallo akwai ruwa a hannun Sajeeda roba guda ta dakko zata sha sai ta fasa sha ta saita kan Nawwara ji kake Gaf zafi ya ratsa Nawwara tunaninta Bom ne ya fashe ta kurma ihu ta fadi kasa tana Bom...Bom...ta mike da kyar tana faduwa tana tashi da Rarrafe ta Isa bakin gate,Haushi ya kama masu gadi ta ruda su tana Bom tsawa suka buga mata tare da turata waje suka jefar kamar wanki suka kulle kofa.
Nawwara tana karasawa gida ta fada Toilet tare da barkewa da zawo ga gefen gashinta ya fashe.
Na gama hada masa Shawarma na shirya komai a tire na wuce Bedroom dinsa zan kai masa na bude zan shiga kenan Naji Aayan yana amsa gaisuwa da Alama da mace suke waya da Sauri na shiga Amma sai naji yaci gaba da wayarsa, kwana biyu kiyi Hakuri Ban kira naji ya kike zama a kasar ba,Da Sauri na zauna a gefensa tare da gwara kaina da nasa na jonesu waje daya wai so nake naji Muryar macen ko Budurwa ce Amma bana jin komai,Ya matsa nima na kara matsawa jikinsa,ya matsa na kara matsawa again,kasar akwai dadi yana Murmushi harda wani Ladabi yakeyi na musamman ina jinshi ya gama wayar sannan yace min Allah ya shuryeki nace Ameen ina turo baki idan wayar gaskiya ce a fadi sunan wacce ake waya da ita Mana aji,yace to yar Us ce Sarkin zargi, wa kake dashi a can me jin Hausa na furta nayi kicin kicin,ki bari zata zo Soon kasar nan zan kawo miki ita idan tazo sai ki fada mata haka in kin Isa, baki na turo tare da cewa ni mutunci gareni an cema Allah bata Isa ta zo nan gidan ba ko wace sai na balla yarinya,murmushi ya saki tare da cewa ai ni zan tare mata fadan,da kai zan hada ai sai na mayar mata da fuska ta koma baya,keyarta ta dawo itace fuskarta,Dariya yayi yace Allah ya kaimu dan baki san wace ba shi yasa, ki shirya min kayana zanyi tafiya,gaba na ya fadi rass nace ina zaka je?Us daga can zan wuce Saudiya,Hawaye na fara tare da turo baki cike da shagwaba nace yanzu ni kadai zaku bari? Amma kasan Tsoro nake ji ko ni kadai ban iya zama a gidan nan,Ga Ameer nan zai dinga zuwa yana tayaki Hira Amma da dare kuma sai dai ki kwana ke daya,Yarima na jirana tare za mu tafi zanyi 2-3wks, ganin kamar bai damu dani ba nima kawai na share shi nace a dawo lfy bari na hada ma kayan, zuciya ta a jagule gaskiya baya so na ya kasa sanar dani zai Tafiya sai yau da zai tafi kuma ko ajikinsa irin bai damu da rabuwa dani ba,Allah ya gani nayi kokari na da zan iya,da ace bana sonsa da tuni na fita daga harkarsa Amma zuciyata ta kasa hakura dashi na rasa me yake damuna gaba daya,shi kuwa shawarmarsa ma yake ta ci ko a jikinsa dama Already naga yayi shiri tare da hadewa cikin kana nan kaya.
Harda goge yar kwallata ina hada masa kayansa na gama komai tsab yanda ya dace na ajiye a gabansa, yana cin abincinsa na dauki paper da Biro nayi dan dogon rubu a takardar me Santayana mutum zuciya amma fa ba na love ba,na adduar Tafiya sannan na Sa a tsakiyar kayansa ba tare da ya sani ba.
Yana gama ci ya mike yana kara shiryawa ni kuma na sauka kasa ina palo a zaune saman kujera duk raina a bace yake kadan nake jira sai gashi ya sakko cikin shiri ya kalleni tare da zuwa gabana ya zauna a gefe na jikinmu na Gugan na juna a hankali yace zan tafi Baby, ban san sanda na zabga masa uwar harara ba nace Ina ruwana to ni na nasan da wata tafiyarka ne,Kallona yayi tare da cewa shirya mu tafi tare am serious wlh i wl be missing you is Better na tafi dake,Harara na kara watsa masa ae ai dole kace haka tunda zaka tabe min jiki to Bazan je ba,ba Us ba ko birnin Sin ne Ban zuwa,Har fa Germany? ban san sanda nace Allah yasa Agadaz zamu je hhh ya dinga dariya in bake shashasha ba kin taba ganin inda Agadaz tafi Germany zaki Hada Niger da Germany ne,ina turo baki nace to ko Birkinafaso ce ehe,Dariya yayi yace ke ana maganar Europe kina kawo África,nace to ko Egyft ce harda Morocco kai ko Algeria ce,nan ma yana ta dariya,yace to Saudiyya fa? Nace ko Qudus ce,dan Allah shirya a yau za miki komai mu wuce bana son bana ganinki kusa dani,uhm sai kayi kuma zancen kake so Karuwa taji me Wa'azi tace aiki ne bai isheka ba, Marairaice min yayi sai da nayi mamakinsa kamar wanda ke so na da yawa, wai sai kuma naji tausayinsa Amma na rantse Bazan bishi ba,nace ni Bazan je ba fa,wai harda jin haushina ya juya tare da fara Tafiya,nace Aayan... Juyowa yayi nace zo pls,tunaninsa zance zan bishi ya dawo nace nasan me kake so a jikina tattaba ka tafi abinka kaji,wani haushina yaji me nake nufi?au tunanina ma jikina yake so shi yasa yake taba ni etc Amma tunda haka nake tunanina zai nuna min,tsaki yaja ya juya abinsa,nace a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya ayi addua me yawa Sabo jirgi zaka shiga ba dabara ga wanda aka kwashewa kafafu kasan duk wanda aka kwashewa kafafu kana sama to dabara ta kare sai du'ai,dariyarsa ya danne kawai yayi gaba,Yana fita Ameer ya shigo nasa Katon Hijab dina,jefi jefi muke hira yana ta bani labarin yan matansu da suke yaudara muna dariya, gaskiya Anty gidan ba dadi Ba Maeesha da wannan yarinyar da na sani ma na bisu munje tare naga Kauyen,Bani Address na bisu Allah zanje,Ni kuwa ya ban mamaki kawai dai na bashi Address din, tun daga Lokacin Ameer yacewa Abbi da Hajja tare da yan gidan kaf wai ya tafi Abuja interview Zai nemi Visa a wani Embassy idan ya samu,Hajja tace bazai tafi a mota ba Amma yace a mota zai je,Nufinsa tunda Rimin Gado zai bi su Meenat sai ya kaisu a mota har Airport su shige jirgi sai Maiduguri gaba daya har da shi,Hajja ta damu ita bazai je har Abuja a mota ba sai a jirgi haka ya hakura Driver ya kaishi har Airport,Driver na Tafiya ya shige Napep har inda zai hau motar Rimin Gado ya shiga Drop fyalleliyar mota karama ya biya kudi shi kadai har Cikin kauyen Rimin Gado can rugar fulani.
Da tambaya ya gane gidan da su Meenat suka sauka yan fulani sukace yan matan Larabawa yan birni ga gidan can,Ameer sai wani make jiki yake yana karkabe kayansa tare da tabe baki yana kyankyami wai,a kofar gidan ya tura yaro wai Meenat da Ma'eesha suzo inji Ameer dan Birni,Meenat ce ta fito kofar gidan tasha Atamfa riga da Zani me style tayi kyau,tasha mamaki ganin Ameer ne da gaske to ko lfy ko Mufee ce wani abu ya sameta Meenat ta tambaya da tsoro a fuskarta, kin wani tareni da tambaya zuwa nayi naga kauyenku to Anty ce ta bani Address bakwa gida duk ba dadi shine nazo,Murmushi Meenat tayi tare da cewa kayi Kokari bari na fadawa Inna to,
Wajen Inna tsohuwa tazo ta sanar mata,Inna tace to kuma sai ki barshi a waje gidan tsohuwa ne kice ya shigo,Maeesha ce ta fita tana dariya tace lallai ya Ameer kayi Kokari ina motarka?ke zan mareki ko wacce sai tambayar tsiya,shugo to ciki,Ameer yabi Bayan Meenat suka shiga gidan,komai na kara ne dakuna Uku irin na ruga,Tsohuwar yayar Ammah ce ita kadai ce a gidan sai jikanta babba kuma ya tafi kiwo can wani daji sai shekara ta zagayo zai dawo gida tare da shanunsu.
Gidan Babba ne me dan fadi tare da katuwar bishiya a tsakar gidan,yasha shara tsaf dashi,Ameer da Ladabi ya gaisar da Inna,da Fara'a ta Amsa sannan tace to ajiye kayan naka ga dakin da zaka zauna can,ke Meenatu kai masa kayansa,Meenat ta rakashi dakin tabarma ce katuwa sai katifa yar siririya dai dai mutum daya ko juyi sai daí ka mike sannan ka juya,Ameer ya dinga dariyar katifar tare da cewa sai kace ta jarirai wannan har katifa ce,ni Yanzu ya zan iya kwana a nan kato dani? Daki yasha tsafta dai ba laifi Amma katifar nan gaskiya kice ta canja min wata,Meenat da Sauri ta sa Hannu tare da toshe masa baki tare da cewa rufa mana asiri kunnenta kamar micijiji yake masifaffiya ce wlh ta gaske bar ganinta haka kunyi faran faran yanzu tayi mana tatas a gidan nan.
Hannunta ya janye a saman bakinsa tare da cewa ke baki da kunya ni kamata zaki toshewa baki kamar yaronki kato dani,ni gaskiya ki fada mata ta canja min katifa,Ai ko karaf a kunnen Inna sai muryarta suka ji tace Iyyeeeeeee... Kai kake bani kudin?ko jikana yana gari ai bazai canja ma katifa ba,duk girman wannan makekiyar katifar yo ni Allah na tuba duk ranar dana kwana a saman ta kasa Sallar asuba nakeyi,har makara nakeyi sai rana ta fito nake tashi Sabo da laushi da girmanta,ba karamin daraja mutum nake Ba zan barshi ya kwanta saman wannan katifar tawa,ai wlh ko su Meenatu basu Isa ba,amma zaka nuna min kai dan birni ko kinibibinka ne? Murmushi Ameer yayi jin yanda take ta mita tana yabon katifar da take duk ta jeme duk ta side tudun babu Sabo da taci duniya ta gaji gata siririya ta gaske,Ameer ya fito wajen Inna yace Inna ta dakina da nake bacci a birni sai tayi girman tsakar gidan nan gaba daya,kinga Bed dina kuwa like...Hannu Inna ta daga masa kaji shakiyin yaro yo ko Sarki ne ina zai samu katifa kamar girman tsakar gidan nan in ba karyarku ta yan boko ba,sai dai ka shiga gidan Radio a Sa zancenka a labarin nishadi na tatsuniya Amma ba a wajena ba baza ka samu karbuwa ba
Dariya Ameer yayi tare da cewa dan kawai baki sanni bane Inna kalli fatata fa kalli kyauna, me yasa kasan da haka baka Sako gadon naka a mota ka taho dashi ba karka dameni kaje kayi wanka ga abinci miyar harda Naman Zabo,Maeesha sai dariya suke har suka kai masa ruwan wanka bayi,yaga bayi ba rufi ba komai fayau ko murfin kofa babu gashi na kara da Ameer ya fito tare da cewa shi ya fasa wankan Tafiya gida zaiyi kar dare yayi masa bazai iya amfani da toilet dinsu ba,Toilet ce kadai zata koreshi daga kauyen,rokonsa sukayi yamma Liss yayi Manage zuwa gobe sai ya tafi,ya shiga haka ba yanda ya iya kayansa ma daya cire sai ta saman katangar ya mikawa Meenat ta rike masa su,
Ya mike yana wanka jikinsa duk kumfa wata yar fulani da kwaryar nono ta bayan gidan zata wuce sukayi ido hudu da ita ta kalleshi ya kalleta Amma iya kansa zuwa kirjinsa take iya hangowa ta wajen gidan,Ameer yaga taki dauke idonta ya ware mata hannu alamar zagi dakuwa yace karbi wannan kan Uwarki,bata gane ba ta tsaya tace me kace yace baki gane ba? Hakan nana yana ware mata yatsu wai yaren mutan kauyen ya mata na zagi Haka nanan,Tace ni yace a'a ubanki nake nufi baza ki bar nan ba sai na fito na fasa miki baki,Yar fulani tace yo ni ina ruwana da kai dan zanje tallana, ko tsirara na kalleka me zai firgitani,Kaga naga kalar ta Iro,Nasan ta Ja'e,har gaisawa na kanyi data Lawalli duk ranar kasuwa iya kaci kace ta wani fara ta wani ba to duk cikinsu ta Ja'e ce Baka wuluk me zaka bude min ido dashi ta ja tsaki tayi gaba,Ameer ya zaro ido waje tare da bude baki yana mamaki yace Ana iya shege a kauye ba kunya ba komai,ana cewa yan Fulani masu kunya etc ashe duk karyace, ya kwalawa Meenat kira ta bashi kayansa nan ma sai kanta ta sadda kasa sabo da kunya kar ta hango kirjinsa.
a gaggauce ya karasa wankansa ya karbi kayansa ya fito,Abincin ma ba dadi kasa ci yayi yace shi wlh gobe zai tafi da Safe,Gari na wayewa ko karya wa yace bazai yi ba,dama tun jiya ya karbi number din me motar da ya kawoshi jiya yace ya dawo gobe da sassafe ya daukeshi,Me mota yaji yanda ya samu kudi da Sauri ya Amsa, ai kuwa 8am sai gashi yazo daukan Ameer back to Cikin Gari,Ameer da murna ya dauki jakarsa tare da basu kudi da yawa har Inna sai godiya take tana Sa masa albarka, ya musu Sallama Meenat da Ma'eesha har mota suka rakashi ya shiga yana musu gwalo ta Glass suna dariya sai gida.
Yana dawowa Yace wai ya fasa Interview din ne shi yasa ya dawo ya bincika yaji bazai yuwu ba,Hajja sai murna take ya dawo lfy, toilet ya fada ya dinga dirzar jikinsa ya dade sannan ya fito ya shirya sosai ya nufo Part dinmu.
Ina kitchen ina Hada Chips na ganshi,Na dinga dariya naji abinda ya koroshi,nace ai kyaleka kawai nayi,Gaskiya Anty baku dace da Ruga ba ina sam kauyen baiyi ba,Abinci na zuba masa ya dinga ci Sabo da ya kwaso yunwa,yana ci yana bani labarin irin wahalar da yasha,Anty toilet ba rooping bare kofa ina Bazan iya ba, yasu Meenat fa? Ameer yace sunfi kyau acan,a kauyen zasu fi kyau Ameer? Ameer yace sosai Anty baki ga Meenat ba har wasu kumatu takeyi,Ina ta dariya nace to ko dai ita zan baka? Ameer yace wannan Masifaffiyar ai sai ta kashe ni ma gaba daya.
Yau kwana biyar da tafiyar Aayan kenan da kyar nake bacci tunaninsa ya Addabi zuciyata,na ma rasa inda zan Sa kaina gaba daya duniyar bata min dadi kullum ni kadai gashi yace Bazan fita ko ina ba, sai gyaran jiki da nake zuwa, tunda ya tafi bai kirani a waya ba nima ban nemeshi ba Amma ko bacci bana iya yinsa sosai Sabo da tunaninsa, Shima can Aayan hakan take baya iya komai sai tunanina,Yarima ya gama gane Aayan so ne kawai ya kamashi,ya kasa nutsuwa,baya iya bacci,abinda ya kaisu ma ya kasa komai,har Zazzabi yakeyi cikin dare na rashina kusa dashi.
Ameer ne kadai yake debe min kewa idan yazo muyi hirar ya tafi,idan ina bukatar abu shi zan bawa kudi nace ya siyo min Amma bazai taba karbar kudin ba da kudinsa zai siyo min komai me tsada da kyau, kullum idan ya dawo daga Office sai ya shigo kuma bai taba nuna min ko sona yake ba,ko wani abu na banza bai taba shiga tsakaninmu ba,mutuntani yakeyi yana bani girma na yanda ya kamata,
Shi Ameer ma tuni ya tuba da son Matar wani tunda yaji wani Wa'azi me Zafi,yaga ina bai kyauta ba,nan take ya fara Istigifari ga Allah ya cire komai a ransa,kawai ganin mutunci na yake dana Aayan sosai,sai kannena yanda suka daukeshi kamar dan Uwansu.
Idan ta kama watarana ko kitchen ya shiga idan yaga wanke wanke banyi ba sai ya tsaya ya wanke min ya gyara min kitchen sannan ya tafiyarsa,hakan yasa abinci sai kalar da yake so nake mishi ance ka kyautatawa me kyautata ma.yau da dare ina bacci wayata ta shiga Ruri ina ganin Number ce ta kasar waje naki dagawa nasan Aayan ne,kullum haka yake min har sai da muka kwashe kwana Uku kullum sai ya kirani yafi a irga Amma bana daga masa waya,har ya cika sati yana kirana kullum kuma bana dagawa.
Muna haka dashi katsam da yamma nasha wanka na cikin doguwar riga Ready made ina palo gidan yasha gyara littafin Hausa nake karantawa a wayata ina ta dariya ni kadai ashe Bell nata kara banji ba sai gani nayi an turo kofar a hankali har ya shigo ban sani ba,sai kamshinsa naji kawai ya cika wajen,da Sauri na daga kaina sama da Sauri ido hudu muka yi ba karamin Kyau yayi ba cikin kana nan kayan ya hadu karshe, Sallamar na Amsa kwarjini yasa na kasa yi masa abinda nayi Niyya,wani dadi,Sanyi,farin ciki,sonsa ya kara shiga jikina gaba daya na wani diririce,nace sannu da zuwa ka dawo lfy?kai da kace 2 to 3 wks zakayi Amma yau Sati daya ka dawo lfy? Harara ya watsa min tare da zama gefena muna gogar juna yace Baki da kirki Mufeeda,bani wayarki ya furta tare da fisgewa yaga Number ta kasar waje da ya kirani da ita har Saving nayi da sunansa Amma naki dagawa,kallona yayi yace kin ma san nine kika ki dagawa saima Saving da kikayi kin kyauta.
Kallonsa nayi nace kayi hakuri,kin hanani yin abinda ya kaini gashi dole na dawo me zaki fada min,Yaushe na hanaka? Yatsuna ya rike ya fara wasa dasu yana mirzasu ina ji har na fara jin wani canji a jikina,Gaba daya naji wani yarrr,shi kuwa har idonsa ya canja,ban san sanda na rungumeshi ba, mun dauki lokaci ya kankame ni a jikinsa sosai Nace ina zuwa na mike tare da nufar kitchen,
Da kallo ya bini kamar zai hadiyeni Sabo da canjin da ya gani a jikina komai nawa kara canjawa nake na kara cikowa,ga kyau dana kara ina sheki, lemukan dana hada na fruits na kawo masa tare da Dambum naman Kaza da nayi na ajiye a gabansa tare da zuba masa lemo a glass cup na bashi a nutse, yana kallona yana sha abinsa ni kuwa shuru na masa tare da dauke kaina har ya gama ya mike tare da da cewa bari nayi wanka naga bakiyi Missing dina ba,shuru nayi masa,yace sabo dake fa na dawo,a raina har ga Allah dadi nake ji marar adadi baya misaltuwa Amma a fili nayi masa banza sai ma turo Lips dana shiga yi.
Mikewa yayi yana murmushi yaja akwatinsa yayi samansa tare da shiga wanka yana tunanin canja masa da nakeyi kwana biyu bayan bai min komai ba.
Su Abbi da Hajja sun sawa Ameer ido a boye ba tare da kowa ya sani ba sun gano cewar karya kawai Ameer yakeyi ashe soyayya yakeyi da Kanwata Meenat,sun gama tabbatarwa ne lokacin da suka Sa CID daya ya dinga bin bayansa har lokacin da ya bisu Kauye ya dawo kuma,tare da Sauran bincikensu,nan take Hajja ta fusata me tsanani haka su Abbi ma,Abbi yace kyale shi zanyi maganinsu gaba daya Har Ameer din,Hajja tace Yaro ya maidani sakara lallai bai san wace ni ba idan na gano cewar mutum ya munafunce ni,wlh wlh nasan Malamaina basa karya Amma dan Iskan yaron nan nasan shine ya lalata komai,kuma ba shakka shi yasa yan fashi suka tare mu kwanaki tare da amshe maganin da muka karbo,Amma kyaleshi zai san ni yayiwa haka kuma sai ya auri Sajeeda.
Abbi yace abu na farko da zamu ladabtar dashi shine mu kwace aikinsa da na bashi a Company na,da mota sannan muce ya bar mana gidan gaba daya,kuma nasan basa shiri da Aayan bare yace zai taimakeshi,Abbi Sani yace ai ko suna shiri da Aayan kasan shi Aayan bai shiga sabgar mu bare zuriarmu,sabo da haka bazai taimakeshi ba.
Bayan sun gama shawara suka nemo Ameer ba mutunci suka masa tatas yana basu hakuri yana Abbi kai fa Mahaifina ne amma kamar baka so na? Abbi yace nafi son uwata da kai dan Iska ajiye min mukullin motar dana sai ma,amma ai da kudina na siya,Mari Hajja ta watsa masa a dalilin wa ka samu kudin aikin ai shi ya baka har ka siyi motar,Abbi yace na kwace aikin ma kuma ka bar gidan nan Banga Amfaninka ba baka bina baka bin uwata har ita zaka yaudara? Abbi bani da kamar ku fa bani da inda yafi nan ina kake so naje? Abbi yace part din nan kasan dai namu ne to kaje wajen ubanka Aayan ya baka inda yafi nan,Umman Ameer ma tana kuka tace kayiwa kanka wlh ba ruwana,kasan dai danginmu kaf talakawa ne baza su iya rike ka ba bare nace kaje can kai ka jawowa kanka kuma kasan Aayan bazai saurareka ba,Abbin America Baban Aayan kaine ka fara masa rashin kunya ko kulaka baya yi ka san da haka,kuma ka sani nan gaba zasu ce ka dawo gida kasan ba a ja dasu dole ka dawo kuma lokacin zasu daura ma aure da Sajeeda.
Ameer takaici ya kamashi yasan dama ko dansu ne na cikinsu basu da imani idan ya musu laifi horo me tsanani suke masa, ya shiga part dinsu ya kwaso kayansa da dan yawa ya fito yana jan trolley dinsa idonsa Jajir ya fito lokacin zan shiga mota zanje Gidan gyaran jiki,tunda na hangoshi nasan ba lfy.
Su Abbi duk sun leko ta saman Bene suna kallonsa yanda zai kare,Sai suka ga na fito da Sauri har wajen Ameer nace Kanina lfy?Ina zaka je haka? Murmushin karfin Hali ya kakalo tare da cewa Abuja Abbi ya aikeni,wlh ban yarda ba Ameer da gani ba lfy kuma nasan bazai wuce a kan kana shigowa part dinmu suka ce ka bar gidan ba nasan tsab zasu horeka ta haka baka ji maganarsu ba,shuru yayi min,nace haka ne ko? a hankali yace ae hakane Abbi ya kwace aikina da motata, to amma ai iya part dinsu zaka bari tunda gidan ba nasu bane su kadai ko?kai ya daga min gwanin tausayi,nace muje ga Bedrooms da yawa a part dinmu sai ka Zaba ma fa ka dawo namu,Anty kina ganin ya Aayan zai yarda? Kuri na nayi nace ai sai abinda nace a gidan nan ka kaddara nawa ne ma,Dariya yayi kawai ya biyo ni su Abbi suna kallo ta sama baki bude.
Muna shiga na bashi Bedroom daya me kyau a kasa Kusa da na su Meenat,yace ki fara fadawa Ya Aayan nace yana Office zan masa waya karka damu,Bari naje gidan gyaran jiki yanzu zan dawo akwai komai a kitchen idan kana so na fita abina na barshi ciki yana Hamdala ga Allah.
Waya nayiwa Aayan na sanar masa komai yace ba Matsala alfarmarki ce Baby baki da damuwa komai kikayi nasan ba matsala I trust u,kuma nasan Ameer baya shirme irin na sauran na yarda dashi bazai yi abinda zai sabawa Shari'a ba da matata ko wata. murmushi nayi nace na gode.
AsmaBaffa
[1/27, 11:26 AM] Asmabaffa: 🌖🌖🌖🌖
🌖🌖🌖🌖
KASUWANCI NA
96-100
Official
AsmaBaffa
MEENAL AMFAL and MMN ADNAN ths page is for u tnx
MMN AMATULLAH Ina turo gaisuwa me tarin yawa.
REAL MAMAN WALEEDA jinjina da godiya Littafin yana Sweet yanda kika fara Lfy Allah ya baki ikon gamawa lfy tare da mu masu karatu,Allah ya kara Basira.
Kuyi Hakuri Fans yan ASMABAFFA FANS CLUB ne suka ce sun bani hutu na kwana biyu weekend na huta ba laifi na bane su suka jawo muku,kuma ko yau suka ce na huta zan huta😅
Na wuce gidan su Sayyah inda Mum dinta ke koya min yanda ake kula da miji etc sannan ta fara min Gyaran jiki ina shan na tsumi,sai wurin Magrib nayiwa Driver waya yazo daukana muka tafi gida Sayyah sai tsiya take min an kusa gamawa Aayan ya kwashi harka, ina dawowa na Iske Aayan da Ameer suna hira a palo kamar wa da kani na jini da Alama wata muhimmiyar magana sukeyi ta sirri, Ameer yace sannu da zuwa Anty nace yawwa ya hutu,Ya Aayan nace tare da daga masa hannu zan wuce Bedroom ya yafito ni da hannu ina karasawa ya miko ko min kumatu nasan me yake nufi cut nabashi kiss a kumatu na wuce, duk da cewa tunda yayi Tafiya ya dawo bama wani shiri dashi dan Romancing dinma da mukeyi ya daina taba jikina ko da wasa akan nace jikina yake so shine zai nuna min ba jiki na yake so ba,da dare da kyar muke iya bacci Sabo da mun saba idan mun kwanta muna yin abubuwa masu dadi tare da shiga rai,ina ta faman gyaran jiki Amma baya nuna min komai ko irin nayi kyau ko Ya rude a akaina abin yana kona min rai Amma ai ni na jawo.
Wanka nayi tare da shiryawa cikin wasu arnayen kana nan kayan da ya kawo min daga tafiyar da yayi,nayi kyau na fitar asiri sai Hijab na Sa har kasa Sabo da Ameer,Kitchen na shiga na fara shirya mana abincin Dare kamshin girkina ya cika gidan.
Ameer kuwa tuni Aayan ya bashi mota guda fyalleliya yana shiga su Abbi sai mamaki sukeyi,Daddy kusan kullum sai naje na gaisar da shi mun sha hira abinmu in ta bashi labarin mu,Sameera yar daba dukansu tare da yaranta an yanke musu hukuncin a gidan kaso na watanni 8 Sabo da Sameera me kudi ce ta basu cin hanci maimakon na shekaru sai na watanni kuma a hakan ma sunce baza suyi 8 mnths ba wata daya ma za a sakesu Sabo cin hancin da ta basu,kasar nan ba gaskiya a cikinta, Aayan kaji wai 8mnths kacal za suyi nace masa ina tura baki,yace Hmm bana son halaka ne da sai na Bada kudin wanda yafi nata a barta a ciki to Allah ya hana cin hanci da me karba da me bayarwa akwai ranar da Allah zaiyi maganinta gaba daya,Amma in kina so a bayar hakan to? Nace ae a bayar kawai dan ubanta ai akan gaskiya ne,a Bada kudin a tabbatar musu da hukunci me tsanani,Kanwata guda da aka bar min Amana nice kamar Uwarsu fa ai wlh Bazan yarda ba da Ammah na da rai kake jin zata yi alfahari dani Na karasa ina zare masa idanu kamar shine Sameeran,Dariya yayi yace to ke mene tunda Allah yasa ta fito lfy? Bazan yarda ba sam kamar kudin ubana haka nake fada Bazan yarda ba dole na tsaya a tabbatar da gaskiya a sharia ka bani kudin Kasuwanci na sai na biya dashi a tabbatar da anci uban Sameera a gidan kaso,yace za a baki tsigai,nace ae a bani kuma dole muje da kai ka wuce gaba ayi komai da kai,yace an gama Uwata, da kansa yaje ya kashe case din ya biya kudi masu mugun yawa aka canjawa su Sameera shekaru Har uku ba tare da nasan anyi ba,sai da ya dawo ya sanar min,nace kash Uku kacal? Laifin Kidnapping tare da niyyar kisan rai? Uku fa ai wlh ba a ci uban Sameera ba sam baza ta koyi darasi ba,sai kace kasar turai da suke da Imani,a Nigeria muke fa inda ba Imani ba a dauki dan Adam da daraja ba,Dariya ya dinga yi to so kike a kasheta wai ko ba a kashe ta ba nafi so ta tsufa a prison,sai gashinta yayi fari tass lokacin na kusa aurar da yan biyun da zan Haifa nan gaba yan mata,Aayan ya bude baki dama har yan biyu kike so ki Haifa?Nace ae Insha'allah su dinga min girki kullum,Aayan yace sai ki dage ki haifo su ai,Wai Ya Aayan ta ina ake Haihuwa kuwa? Yace ta cibi zaki ga ta bude kawai jariri ya fado,dariya nayi nace ba wahala ashe ma.yana ta min dariya yana tunani Allah yasa ya warke ya yi maganin gaba daya.
Bayan na gama girkin daren nawa Ameer yau bai dawo da wuri ba daga ni sai Aayan muka ci,. 8pm nayi shirin bacci da komai a dakinsa shi kuma naga yana ta cin kwalliya kamar ranar daurin aurensa sai fesa turaruka yake faman yi,nace ina zaka je? Yace wajen yarinyar nan ta Us ce tazo kuma a Hotel ta sauka ba dadi Budurwa kamarta ta zauna a Hotel ai ba mutunci ko kawai zanje dakko ta ne ta zauna damu kafin ta koma.
Kamar ana zuba min ruwan zafi haka naji a zuciyata,ji nayi kamar zanyi hauka gaba daya hankalina baya jikina Sabo da tsananin kishi,nace idan an Isa Allah ya dau raina yau ba sai gobe ba, nace Wayyo Jama'a ga Kwarto,Ameer ya dawo yana kasa yana juyowa ina ta ihun Kwarto a sama,shi dai yasan Aayan yana gida Amma yace bari ya gani kar ko wani ne daban da Sauri ya karaso Saman yace Anty Mufeeda lfy waye,Aayan ne ya fito cikin shirinsa yace kyaleta jeka kuruciyarta ce ta motsa,Ameer yana dariya yace Ya Aayan kaine kenan Kwarton Aayan yace ae fa gani,Ameer ya juya yayi tafiyarsa yana dariya a ransa yace Mufeeda itama irin yan fulanin garinsu ce kenan,Ni dai ko a jikina na fara kuka yana daukan Agogo zai fita na dakko Jambaki da Sauri na bude shi na dinga shafa masa a rigar ta ko ina na jefar da jambakin na kama rigar na dirje lips dina da ita kalar pink jambaki ga wancen Red,yace kinyi ta banzan dole zanje ya bude kofa kenan na jawo rigarsa ta baya,ina ta uban nishi ina Hawaye,hakan baza ta kaini ba na tsuguna na kwaso kafafunsa Amma ko motsi baiyi ba,sai ya biye min ya tsaya don yaga me zanyi masa tunda Hannunsa nake ta ja da karfi,sai ya biyoni tunanina ni nake jansa ta karfi ina nishi na jawoshi har Jikin Bed,ya tsaya kuwa,nace kwanta to dan Allah kaji ina ta kukana,yaki kwanciya na kara mikewa na danna shi kan Bed ta karfi,nan ma gani nake ai karfi nane ya kwanta sharab,yana kokarin mikewa na fada kansa na kwanta daf daf tare da rufa mana bargo tare nace ka dubi girman Allah ka kwanta,Sabo da me? Aljanune suka ce kar na barka ka fita kana fita zaka samu matsala,a lokacin kuma da Aayan yake son fita lokacin Abbi ya barbada masa Wani garin magani a kofar fita wajen part dinmu suna jira ya taka wajen,mu harga Allah bamu san da wannan ba kishi na ne yasa na hanashi fita.
Sai da Abbi Sani ya Kira Aayan a waya wai ya fita yanzu ga abokan Daddy nan sunzo duba Daddy daga Abuja kuma karya yake burinsu kawai suga Aayan ya taka maganin kafin gari ya waye,idan har gari ya waye to ya karye maganin ko an taka bazai yi ba,shine suka rasa yanda zasuyi ya fito suka hada abin da Wai Bakin Daddy sun san yanda yake kaunar Daddy dinsa.
Ta inda Allah ya tsare Aayan sai a ransa yace bari ya tsokaneni yaji shine yace ai wajen wata zaije,ni kuma uwar kishi shine sai da nasan yanda zanyi na hana fitar ta dole,a hankali na kai bakina zan masa kiss yace karki taba ni,why? Kince Sabo da jikinki nake taba ki so na daina taba ki,to Sabo da me kake tabani? Fadi gaskiya naji? Murmushi ya saki sannan yace Do not judge a person by their looks or the things they have. You do not love some one for their appearance or their nice cloths but because of their personality, their thoughts etc u have to Understand kinji?
Shuru nayi ina jin dadi yaci gaba Sometimes people don’t tell you how they truly feel about you but they will always show you so pay attention ki gane ba sai ance kullum ana sonki ba kamar yarinya ku yan mata haka kuke.
Baki na turo tare da cewa ni dai duk da yanzu ina jin turanci kayi min da Hausa yafi shigata sosai kai turancinka na turawa kakeyi duk a harde, murmushi yayi yace Ok ku mata sai kuyi shekara yafi goma tare da mutum yana ta nuna muku yana sonku Amma wai in dai bai ce i love u ba to kawai ba sonku yake ba,wani ma sai ayi ta cewa ai kawana ne,kuma in ka sake kana gani zata auri wani ta barka,sai kace daga baya ina sonki tace me yasa baka fada min da wuri ba bayan duk abubuwan da ka nuna mata na zallar so ne.
Murmushi nayi nace uhm munfi so muji gar da gar, kumatuna yaja da dan karfi sai da nayi kara sannan yace I LOVE YOU......I DO REALLY LOVE YOU,I NEED U,I LOVE EVERYTHING ABT U,U ARE MY SOULMATE BABYNA ya karasa furtawa tare da hade bakinmu waje daya yana sha,Dadin da nake ji ya wuce a fade shi,nan take na kara kankameshi,naji yana nema ya zarce nace bari nayi fitsari,a hankali ya sakeni na shiga toilet,na kulle tare da jingina da jikin kofar ina sauke numfashi da ajiyar zuciya bakina yaki rufuwa Sabo da murna,dama Sabo da kar ya gano ni yasa na gudo toilet Sabo da nayi murnata ni kadai,harda tsalle da murna ina yarfe hannun dadi,sai da na dade ina murna sannan na hade rai na fito daga toilet irin ko a jikina bana murna, gefensa na kwanta ya kalleni tare da saka hannunsa cikin nawa Baki ce komai ba Baby, akan me fa na furta ina yanga,do u love me too? Yatsina fuska nayi tare da cewa sai nayi tunani na duba naga ko ka dace,Murmushi kawai yayi tare lumshe ido ya jawo ni jikinsa Amma Sabo da iya shege sai na ja baya kadan tare da kwace jikina.
Shima bai takura min ba ya kyaleni kawai tare da daukan wayarsa dake uban ruri sunan Abbi ne a jiki,sai yanzu ya tuna Abbi ke neman Sa yaje tarbo Bakin Daddy,amma abin mamaki baki daga Abuja su rasa lokacin zuwa sai dare kawai dai yace gani nan yanzu su jirani,Abbi yana ta masifa ka wulakanta mutane Sabo da kai ga me kudi ko to kayi gaggawar fitowa,burinsu ya fito ya taka maganinsu,Ni kawai ban yarda da fitarsa ba kishi nake ko wayo zai min macece da yace daga U.S take,nan take na fashe da kuka ganin ya mike da gaske fita zaiyi, a hankali yace mene ne? Ni..Allah ba inda zaka fita,Indai ka fita Bazan kara tayaka kwana ba kawai baka so na,mirmushinsa me tsada yayi tare da cewa kina jin yanda Abbi ke fada bakin Daddy suna jira na kiyi hakuri naje naga ko su waye mana,Yanzu wasu bakin kirki ne da Dare haka ni Dai Allah baza kaje ba na sani ko wajen budurwarka zaka je.
Hakura yayi kawai da fita Sabo da yaga da gaske tunanina yana da budurwa gudun Zargi sai yace Ok na fasa to,murna na fara yi tare da kashe wayoyinsa gaba daya na ajiye gefe,shi kuma yana zaune gefen Bed na zagayo ta bayansa tare da Zura hannayena ta cikinsa na rungumeshi gaba daya a jikina,bai san sanda ya lumshe ido ba jin yanda Albarkatun kirjina suka sauka a bayansa,Kasa jurewa yayi ya juyo tare da matsane a kirjinsa gaba daya kamar zai fasa min Kashi, gaba daya ya tafi dani ban san sanda na biye masa ba alhalin nace na daina yarda yana taba min jiki yanzu sai na bashi wahala Amma sai gashi na kasa jurewa,har mamakin kaina nakeyi yanda nake da Feeling me karfi kan Aayan bana jurewa.
Da Zafi zafi muke Sarrafa juna kowa na nuna kwarewarsa Har Aayan ya dauki Hanyar Cinma burinsa Amma sai kawai sha'awarsa ta tsaya cak ya gagara komai,ni kuwa dama gyaran jikin da nayi nace shike nan na hakura ya samu abinda yake so Sabo da son kudi na bana so nayi asarar kudin gyaran jikina gwara ko mutuwa zanyi kawai ya Mori kudinsa tunda dama danshi nayi gyaran idan ba ayi ba ai na rafka asara tare da bata lokacina.
Kallonsa nayi da tausayi sosai Sabo da yana da sha'awar abin Amma kuma bazai iya ba wannan Masifa ce,sai dai yayi ta shan wahala,shuru kawai naga yayi ya fada dogon tunani,Nace Man ya akayi ne? Har yau baka warke ba ko? Kai kawai ya daga min,da kyar yace min am so sorry na kasa baki hakkinki shi yasa bana son auren nan,amma kiyi hakuri idan kinga da matsala ko zaki shiga wani Hali tunda ban san ranar warkewa ta ba ki fada min duk da ina sonki nasan da kyar idan zan rayu babu ke zan iya hakura, Hawayen tausayinsa ne ya ziraro min nan take nayi Sauri na rufe masa baki nace karka kara ambata in Bazan iya ba zamu iya rabuwa ka daina ba kai ka daurawa kanka ba Allah ne kuma watarana zaka warke,kayi hakuri itace Kaddararmu ba shi nake so a tare da kai ba wlh ko shekara nawa zakayi a duniya zan iya hakura mu zauna tare,Allah idan har kaji ni Mufeeda nace ka sawwake min ko mu rabu ko zan bar gidan nan abu na farko da zaka min kawai ka kaini gidan malamai masu Rukiyya kawai ba kalau nake Ba ko Aljanu sun shafe ni ko an min asiri kaji na rantse.
Ka daina damuwa ko kasawa kanka tunani, na gode Baby Na gode yake ta maimaitawa I love u so much My wife,yanzu in naji kince mu rabu ko zaki barni na...da Sauri na karasa ka kaini Ruqiyya wajen Malamai kawai asiri aka yi mana,Dariya yayi kadan tare da kara kankameni a jikinsa.
Can kuwa su Abbi suna ta faman kiran Aayan a kashe ma wayar,Abbi yace iyyeeeeeee ehhh lallai yaron nan fa ya fara tsallake iyaka dan muna daga kafa ne kawai idan mukayi sake muna jiran Hajja to lokaci zai kure mana,da gani yar iskar matarsa ce ta hanashi fitowa wlh bazai wuce ita bace,Abbi Sani yace dama naga Alama yanzu sai abinda tace Gwara mu fara maganin shegiya,akwai Maganinta Hanifa ko Sajeeda zan bawa aikin su zuba mata a abinci inda da kanta zata bar gidan a nemeta a rasa taje can tayi ta garari a duniya.
Abbi yayi dariya sannan yace ai har kannenta kar a bari su dawo tunda sun tafi dangin ubansu to su zauna can ko su Bita ita Mufeedan su karata can,da banyi niyyar kulata ba Amma yau ta shiga gonarmu,Washe gari da Safe Saturday Ameer yana Bedroom muma haka na hada mana break na shirya a Dining na koma ina taya Aayan shiryawa Sajeeda ta samu yanda zatayi ta bude kofar ta shigo a hankali tare da kallon gefe da gefe ta tabbatar ba kowa a wajen sannan da Sauri ta karasa saman Dining ta bude duk kalolin abincin dana shirya ko wanne ta barbada garin maganin sannan ta rufe a hankali ta juya zata tafi duf Numfashinta ya dauke na wasu dakiku sakamakon ganin Ameer da tayi tsaye a bayanta ya harde hannaye a kirjinsa,yana mata wani wulakantaccen kallo.
Nan take jikinta ya fara mazari, ba zato taji mahaukacin Mari ta ko ina,zafi ya hada ta kamar an dosana mata wuta a fuska,Fisgo wata waya yayi ya fara tafkarta yana Ball da ita,tun tana neman agaji har ta garara,ni kuwa munji kamar hayaniya amma hankalinmu bai kawo ba,Ameer ne ya samu Kwalaba ya fasa tayi cako cako ya jawo Sajeeda kiiii har palo ya zauna saman Kujera,Fuskarta ya rike da karfi tare da dagata,tana kuka tana bashi hakuri tasan Ameer bashi da Imani zai iya yankar jikinta da Kwalaba,kamar me aski ya fara karta mata Kwalaba tun daga goshi jini na tsatsafowa,Sai yanzu muka fito nan muka hango irin muguntar da Ameer ke aikatawa,Aayan ne yayi magana da karfi Ameer me ya faru wannan wanne irin rashin Imani ne?
Gashin Sajeeda ya fisga da karfi tare da cewa confess dan uwarki,nan take Sajeeda tana kuka ta fara tonawa kanta asiri da Abinda Abbi ya sata aikatawa,Ni Mufeeda Salati na fara nace Ameer hada da kirjinta duk ka karce shege a Zane mata ko ina,Aayan yace no..Ameer kyaleta taje mun godewa Allah ma haka tunda ya nuna mana,baki na turo nace ni dai baza a barta ba sai an cire mata farcen kafa na Babban yatsa ta karfi zan tsige shi,Aayan yace ba a nan gidan ba ke tashi ki tafi,tana mikewa na damkota tare da yarda ta kasa Aiko Sajeeda ta fini karfi kawai sai ta rufeni da Duka sosai na koma neman a taimakeni,Aayan yace au Sajeeda naji tausayinki an barki shine zaki dukar min Mata to na fasa,Sajeeda da fuska duk zanen Kwalaba da jini tace ae din tare da gallawa Aayan Harara kafin ta maida idonta ya kafeta da Mari hagu da dama tare da bude kofa yayi short da ita waje ya maida kofar ya rufe,Ameer yace na fada ma basu da kunya.
Nace ai wlh sai naci ubanta idan na kamata sai na karya mata hakori sai na tsoma mata yatsa a ruwan zafi, dariya Aayan yayi yace ai tafi karfinki gashi zata ji miki rauni a banza nan nace ai kyaleta nayi kawai Amma mu fada a wajenmu harda na siyarwa dan Babanta. Kwashe abincin nayi gaba daya na juye a leda na kai Dustbin Ameer ya fita dasu waje,haka na dan dafa mana saukakakken abinci abincin mu me dadi muka karya,s ai mita nakeyi na hana kowa sakewa.
Tunda Hajja da Abbi suka ga abinda aka Yiwa Sajeeda suka shirya Tafiya can kasar Kudu cikin wani kauye wajen Babban sabon bokan da aka basu lbr anyi,
Har wanda ya basu labarin bokan gaba daya da shi aka shirya yayi musu Rakiya banda Hajja ta dai ce Abbi yayi komai.
A jirgi suka sauka a Enugu daga nan suka dauki Taxi wai ya kaisu wani daji ko a garin Enugu tsoron bin hanyar Dajin akeyi Sabo da matsafa sunyi yawa a dajin, Driver yayi ta Maza yana Tafiya dasu yana tsoro ko yan yankan kaine,yana Tafiya yana jan tsaki yana Chaiiiiii Alaji,suna jinsa har dai ya kaisu dai dai inda zasu dan shiga dajin da kafa mota ko machine basa shiga sai da kafa,Suka sauka tare da bashi kudi yace Alaji always making juju Money,go and Meet ur Malam is Better than to visit ths land wooo, u have to be very careful with ths place,ahhh see me see troble because of Money so people can do anything in ths world they can even kill them self,Abbi yace Abeg carry ur Wahala and Go stupid Taxi Man,shi dai me Taxi ya figi motarsa bayan ya gama surutunsa.
Dan cikin dajin suka shiga kadan sannan Me Rakiya yace anzo wajen,Abbi yace ya sunansa kace? Mutumin yace sunansa SHAKYLGANCY sai kace dan India cewar Abbi,ai a india ya koyi har kar nan Alhaji cewar me Rakiya.
Suna zuwa wajen anyi Ado da komai Red Abbi yace Shakylgancy.....Shakylgancy.....Sai ga Shakylgancy bugul ya bayyana kamar Aljani wani me mummunar suffa,Cikin harshen turanci Abbi ya koro baya nansa,Shakylgancy ya kece da daria sannan yace shima cikin turancinsa yace 1million Amma baza a biyashi sisi ba sai in magani yayi suka ce Shakylgancy baza mu iya dawowa nan ba karbi kudi kawai ko yayi ko baiyi ba karbi kawai zamu dinga contacting dinka a waya idan ta kama dole nayi kokari mu dawo,Shakylgancy ya washe hakoransa tare da wani hancinsa kato kamar tattasai ya karbi kudi yace suje zasu ga aiki.
Bayan su Abbi sun fito gefen titi tare da Dan Rakiya suna neman Taxi wata mota ta yan Mafiya matsafa ta shararo da gudun tsiya dan Rakiyar su Abbi shine a gefen titi motar na zuwa tayi gaba dashi ta markadeshi a titin fit kansa ya dinga gare gare kamar Ball a saman titi,su Abbi sunyi mutukar firgita shi da Abbi Sani nan suka ga fa an kashe banza motar ko slow down bata yi ba,aiko su Abbi suka take da gudu suma suka mike titi sambal suna ta yi kamar yan tseren gudu basu san sanda suka watsar da takalma tare da babbar rigarsu ba,dama Abbin Sajeeda cewa yayi suje sun wakilceshi shi tsoron zuwa kudu yake yi tunda watarana a Crossriver akasace wani a gaban sa shike nan ya firgita.
Sai da su Abbi suka yi Nisa sannan suka samu Taxi da kyar ta kaisu Har airport a Hanya suka siyi Sababbin takalma Amma Sabo da rashin Imani ko Jimamin Mutuwar abokin Rakiyar tasu basu yi ba sai Abbi da yayi karfin halin daukan hoton gawar a waya Sabo da ya nunawa iyalansu gashi wancen talaka ne shi da iyalansa Amma an mutu a shirka,nan ba aci ba can ba a ci ba,a kiyaye talaka ka lallaba kanka ka samu a Aljanna.
Yau ni kuwa shirye shirye mukeyi Su Meenat zasu dawo daga Maiduguri Ameer yafi mu Zumudi wurin Magrib sai gasu kuwa da kaya Niki Niki sun shigo sai murna lokacin Yarima yazo sun finta tare da Aayan,sai hira mukeyi muka ci muka sha,Ameer yace Duk kunfi kyau a Kauyen Rimin Gado har kumatu kuka yi,Meenat tace ai baka kyauta ba tunda ka wani gudo,yana dariya yace tab ina wani zan iya zama a wannan garin toilet ce tashin hankali ana kallonka a waje,ga wata katifa kamar ta jariri,dariya mukayi gaba daya muna haka sai ga Aayan tare da Yarima,Yarima yana ganin Ma'eesha wani sanyi ya fara ratsa shi ita kuwa Ma'eesha kunyarsa takeji kwarjini yake mata wata uwar signa ya mata da ido ai ko Nan take gaban Ma'eesha ya fadi rass Sabo da lokacin Ma'eesha ta cire Ameer dama shakuwace Sabo da yawan mu'amula da sukeyi ganin kuma kamar shi wata mace bata gabansa yasa tace ke Ma'eesha shafawa kanki ruwa,
Ma'eesha tana Satar kallon Yarima ta gaisheshi ya amsa cike da fara'a, duk ta kasa sukuni ni kuwa ina gefen Aayan nayi shuru na lula tunanin asara da zata hau kaina kwanan nan na gama kashe kudin gyaran jiki mijin bai mora ba,danni a kan ayi asarar kudin nan gwara na kusa mutuwa na farfado kawai.
a hankali Aayan yace ya akayi? Ya rada min a kunne,ajiyar zuciya na sauke nace kai dai bari kawai asarar kudade nake ta yi kwanan nan,ina ta zuba adashin da ba a dauka,Aayan bai gane me nake nufi ba yace ke na rasa inda kika gado son kudi haka wacce asara kikayi na biya ki? Nace baza ka gane ba a bar zancen Amma ko ka biyani Bazan iya daina tunaninsu ba,tunda har yau me kayan ma bai yabe su ba ko da baki yace kayan nan sunyi sun kuma hadu etc ba a ce min kala ba bare naji dadi da kwarin gwiwar karbar asarar danayi tunda bai samu damar siyan kayan ba.
Aayan iya tunaninsa ya kasa ganewa me nake nufi wani kuma waye wani?to Business sukeyi? Nan fa kishi ya cika shi tab yasan zata iya indai Mufeeda ce zata iya, Yarima Ya rasa inda zai saka kansa dama yake jira kawai su dan kebe da Ma'eesha ya karbi Number ta kullum cikin tunaninta yakeyi,Sai ko Ya mike yace zan tafi Aayan sai mun hadu,Aayan yace bari na rakaka,a'a zauna ban son Rakiyar Katon Gardi ni Ma'eesha kawata ce zata rakani,Dariya mukayi gaba daya Ameer yace da Alama Ya Yarima girma ya fadi ka fada akan yar wannan yarinyar,Meenat tace Ss1 kawai fa,Ma'eesha ta harari Meenat tace Gwara dai ni ko a hanya duk mutanen kirki ke tareni suce suna so ke kuwa fa Kwaja,Fela etc ku bari na dawo wlh na fasa rufa miki asiri dama kince kar na fada na yarda to na fasa Bari na dawo na baku latest a Maiduguri da Rimin Gado,Ameer dama kadan yake jira yace muna jira Sauri yau wlh komai dare bazan kwanta ba sai naji.
Aayan yana Dariya yace gaskiya a rufa mata asiri,Meenat tayi mukus tasan yau Tata ta kare,Yarima ya dan jima yana jan Ma'eesha da hira sama sama duk shima akwai ji da kai bai fiya magana ba Number dinta ya karba ya bata tasa sannan ya bata kudi taki karba,babu yanda baiyi ba Amma taki karba nan ta kara birgeshi sosai.
To yan mata pls a rage nuna zalama wajen Saurayi ko idan kika ga mutum ya fiye yi miki kyauta dan Allah watarana ki dinga jayayya kice baza ki karba ba ko da kina so ki dan dinga kai zuciya nesa sai ki kara birgeshi,sai masu jarabar Rokon Samari abu kawai yan mata Direct kice yi min Kaza ko bani Kaza ko yaushe kuma ba kunya ba komai wlh ba tarbiya ce ba,kina zubarwa kanki mutunci da na iyayenki a dinga daga kafa ana hakuri da yanayi na Babu ba har ayi ta roke roke ba, ko ina wasu zakiji suna wancen ina ba yar manya bace Bazan iya ba na tsani me roko etc.
Ma'eesha na dawowa Ameer yace matso nan Hajiyata ki bamu mu musha,Meenat tace Sis Mufee kin gansu ko,Mufeeda tace nima baza kunne nayi yarinya, Babbar banza cewar Aayan,dukan wasa na danyi masa kadan tare da kwanciya a cinyarsa , Ma'eesha tace kai Allah ya bawa Meenat farin jini samari iri iri tun daga Rimin gado yan fulani suka dinga cika kofar gida.
Farko mun fita siyo pure water muka hadu da wani zai je kiwo da shanunsa ya tare mu yana washe baki idan kun ganshi abin dariya yana busa hayakin wiwi Yace hooai Yan Birni aradu wagga Bingel tana Burgeni, wannan ke nake so ya nuna Meenat tare da cewa Sunana TSITO, nan muka fara dariya jin sunansa Ma'eesha tace in kun ganshi wlh yaci sunansa Tsito wani siriri ne kamar a busheshi gwara Kwaja ma yana da Katon ciki Amma Tsito shi ba dan cikin ma,Meenat tace to Dan Uwarki ai Tsito yafi Kwaja lfy da ganin cikin Kwaja ai na cuta ne,kuma Tsito kyakyawa ne,Ameer yace mu dai ba ruwanmu Tsito muka sani,Ina dariya nace karki kara zagar mana Uwa akan kice dan Uwarki gwara kice dan Ubanki Better,Make min baki Aayan yayi shi Abban shine ba a so ba kyau,baki na turo cike da shagwaba nace da zafi fa...Zan rama ne.
Ma'eesha tace Daga Tsito kuma sai NA AGWAGWAJI shi kuwa a yan fulanin ma dan Daba ne duk wanda yaga Meenat tayi masa magana sai ya farfasa masa jiki,Ameer yace kice dan karamin yaki ta hada,Meenat tace Allah ya bani ya zakuyi dani ehe,Dariya muka dinga yi Jin har Dan karamin Saniya Na Agwaji ya bawa Meenat tana can gidan Inna an daureta za a sata cikin Shanu ana kiwata mata ita,Nace Business Sabo Sarkin Kasuwanci cewar Aayan jin yanda nake ta murna Meenat ta samo Saniya zata girma ta Haifo yayanta.
Ma'eesha tace Arzikin Meenat bai tsaya a nan ba kullum samarinta suna hanyar kawo mana kaji da zabbi muna yankawa mu sha farfesu iri iri,Na ciji yatsa nace me yasa kika cinye a ciki banzaye maimakon ku siyar ku tara kudin ku kawo min ko dankunnen Gold na siya muku dan karami,Aayan ya kalleni baki bude yace da kudin kajin? Nace of Course.
Ameer yace inye to wannan buhun kayan naku fa? Ma'eesha tace duk Samarin kauye ne suka tara mana su danyar Gyada,gero,wake etc,A Maiduguri kuwa samarin Meenat harda Conductors na mota,yan Napep etc me dubu daya me dubu biyu haka muka cinye musu kudi,Nace to ke kuma fa in haka ne kece me bakin jini,Meenat tace tsakani da Allah duk wani me kudi indai kinga rantsatsiyar mota ta tsaya to ba shakka wajen Ma'eesha aka zo zance,ni dai Meenat ina ga asiri akayi min daga me kaji sai me Saniya,gyada da gero tare dasu waken Suya hhhh muka dinga dariya,Aayan yace sorry Sis zaki samu wanda yafi kowa kudi kuma na gari kema,ni kuwa nace Meenat haka Allah yake lamarinsa ni kam Ruwa ta sha aradu,Rankwashi Aayan ya zuba min,Ameer yace ni wlh ji nayi gwara haka ita ba iyayi ba dama Allah yasan manufar jaki shi yasa ya hanashi kaho.
Meenat ta gaji da abinda Ameer yake mata ta mike cike da shagwaba tayi kansa wai zata kwala masa spoon ya mike suka fara zagaya mu a palon muna zaune, sai da na gaji nace Meenat kun damemu can u stop ths Nonsense pls? Meenat tace ai kuna jinsa abinda yake ce min kun kasa yi masa fada,Maeesha ce abar duka ai ba Ameer ba tunda ita ta fada mana,Haushi Meenat taji ta jefar da spoon din tayi Bedroom abinta .
0 comments:
Post a Comment