JUWAIRIYYA Part 2
.
Jan motar su Haj Asiya ke da wuya mal Yau ya fita shima bayan sun gama shawara da maikoko. Bakin titi yaje ya tari mota sai wani kauye. Boka Dillin yana ganinsa yace mugu dan masara yau kuma bayan wa kake son gani. Mal Yau ya zauna a inda ya saba idan tasa ta kawo shi yace yarinyar kanina ke neman ballo min ruwa kasan na fada maka tasan komai don ma kayi kokarin rike bakinta ne. Amma fa bata tsorona yanzu kada wata rana tayi magana. Sannan akwai yayar babarta kusan ita ce gatsnsu yanzu. Itama ina son a hada su duk a tada musu hankali. Tazo ta dauki Zuwairan sun tafi kano bikin yarta. Boka yayi dariyar mugunta yace indai wannan ce matsalar to an gama fadi wata idan akwai.
*************************
Ana bude gate din gidan Haj Asiya wani dadi ya rufe Ju. Ita dai tana son gidan mami kamar yadda yaranta da suma yan gidansu suke kiran Hajiyan. Bari uku ne a cikin tankamemen gidan. Daya na Alh Bashir mijin mamin sai na wansa Dr Umar sai kuma na babarsu Hajja a tsakiya. Mami tace Juwairiyya muje mu far gaida Hajja ko. Tace to Mami ai ni ina sonta tunda tana zuwa duba Baba. Mami tayi murmushi ita kam ta rasa yadda akayi yarinyar nan take son babanta haka. Suna shiga Ju taga 'ya'yan wan babansu Amal da take kusan saar su Fauza da Yasmin sun takurawa Hajja wai sai sun daura mata gwaggwaro da biki tunda bikin jikokinta biyu zaayi. ita kuma Hajja ta dage tana turewa abin ya ba Ju dariya tana kokarin karasawa gaban Hajjan su gaisa taji ta taka wani abu, kafin ta ankara ta juyu kuwa aka hankada ta ta fadi kada kanta ya bugu da hannun kujera. Tan take kowa hankalinsa ya dawo gare ta wanda ta taka kuwa cikin fushi ya tashi yace are you stupid? kina tafiya bakya kallon gabanki.
.
Hajja tace Asiya duba min goshin yarinyar nan. Kai Rayyan tun dazu nace ka tashi daga kwanciyar nan kayi hanya kaki. Ju kafin Mami ta taba ta ta shafa goshinta taga jini ai nan taķe ta manta da manya a gabanta tace kan uba ka fasa min goshi. Allah Ya isa, kazo ka kwanta kan hanya kuma ni ina jin na taka maka kafa niyata na juyu na baka hakuri. Mami ta daka mata tsawa tace ke Juwairiyya bana son rashin kunya. Ta juya ga Rayyan tace yi hakuri babban yaya. Sai a lokacin ya durkusa ya gaishe da mami sannan kafin ya fita yace ni dai Mami indai wannan ce mai aikin da zaa daukarwa Amal na mun yafe. Hajja tace kuga yaro mara kunya babar matar taka kake fadawa haka? To yarta ce itama.Mami tace Hajja ya zaki korar min da. Duk suka yi dariya sannan suka gaisa
******* ***************
Bayan anyi sallar azahar Ju da Amal sun cin abinci tare suna hira Mami ta fito daga daki ta zauna kan kujera tace Amal idan anyi laasar ki dauki Juwairiyya kuje ku gaida Dada. Tace to Mami amma motata tun safe Abdul zaije siyo min mai giyar ta makale sai dai mal Garba ya kaimu a taki. Mami tace na aike shi gidan mai turaren wuta. Abdul yace dazu naji Ya Rayyan yace zaije yau. Mami tace to ka fada masa akwai yan rakiya. Amma jira su gama cin abincin ka raka kanwarka ta gaida Umma. Sunje sun gaida Umma matar Baba Umaru har Ju ta zauna hira wajen su Fauza don ita Mami duk yaranta shida maza ne sai Amal ita kadai.
.
Bayan laasar sun fito zuwa gwangwazo gidan kakarsu babar su Mami wato Dada sai Ju ta hango Ya Rayyan tsaye jikin mota ai kuwa ta taba Amal tace yaya da wancan mutumin zamu je. Tace eh Ju tace shine fa don wulakanci yace min mai aiki. Amal ta kwashe da dariya tace kin dai rama ko. Tace a'a amma zan rama. Abdul autan mami wanda dashi zaa yace ke Ju shine angon fa. Ta zare ido tace angon wa yace na yaya Amal. Ju sai tayi tsit da baki har sukavkarasa mota. Suna shiga Amal tace Ya Rayyan shine ka kira kanwata mai aiki ko. Yana kokarin ribas da mota yace yi hakuri amarya ai ban sani ba.kanwar taki ce akwai baki kamar reza. Ju dai da tasan angon yayarta ne da tayi shiru da bakinta amma jin yace bakinta kamar reza yasa ta bata rai. Shi kuwa sai ya cigaba da cewa she talks alot, i could hear her voice from my room. To Ju taga abin kamar da rainin hankali wai ana magana da turanci a gabanta tace a ranta wallahi sai na rama. Ko yaya Rayyan kalli mudubin zai duba bayansa sai yayi ido hudu da Ju ita kuma tana lura da hakan da ya kallo sai ta murguda baki a haka har suka isa gidan Dada.
*********************
Kwanan Ju uku a gidan Mami amma duk gidan ya fara isarta. Sau biyu tun zuwants ta hadu da Ya Rayyan amma yana ganinta yake bata rai. Inda sabo ta saba da ganin mutanen da basa sonta a gidan baba Yau amma abinda yasa wannan ke damunta tausayin Yaya Amal take ace mutum irin wannan zata aura mara fara yadda take da son mutane. Yau gidan Hajja a cike yake da baki 'ya'yanta mata Hassana, Usaina da Habiba na duk sun zo saboda taron gaggawa da Hajja ta kira sati biyu kafin a fara biki. Babu kowa a falon sai yayanta maza da matansu sai matan da kuma Amal da Rayyan. Baba Umaru ne ya fara magana da tambayar yaran shin a falon nan akwai wanda ya taba baku shawarar auren juna? Suka ce a'a. Yace madalla. Ku kuka hada kanku sannan kuka sanar damu sai yanzu saura sati biyu auren ku Amal kice kin fasa. Amal wadda kanta a kasa yake tunda aka fara magana tace wallahi Baba idan na aure shi wani mugun abu zai same ni kila ma na mutu. Rayyan wanda ko daren jiya bayan sun gama hira sun dade kuma a waya abin sai ya zo masa wani iri don shi duk a tunaninsa irin nasihar nan aka zo yi musu. A firgice ya dago kai yace Amal what did you just say?. Mami tace na shiga uku Amal lafiyarki kuwa. Anti Usaina tace ni dai yau bayan asuba ta kira ni ta fada min tana kuka shiyasa nazo na sanar da yaya. Hajja tace zo nan Habiba dayake shine sunan Amal na gaskiya. Me ya hadaki da dan uwanki. .
.
Cikin kuka tace ba komai. Babanta wanda ya rasa abin fada ya dafe kai yayi shiru, Mami itama cikin kukan tace Alhaji kana jin abinda yarinyar nan take baka ce komai ba. Nan dai ya dago kai yace Rayyan kana son auren nan? Yace eh Abba amma ..... bai karasa magana ba Abba ya mike ya fita. Baa jima ba ya dawo tare da Sagir dansa da kuma Aliyu wanda yake bin Rayyan ya dubi yayansa yace ni dai indan har kun amince a daura auren nan yanzu naga iya gudun ruwanta. Ya dubi Amal yace uwata yau ba don abin nan na gida bane so kike ki mayar dani karamin mutum. Anti Hassana tace yaya Bashir abi maganar nan a hankali. Ta kalli Rayyan tace ka fada mana gaskiya me ya hada ku. Shi da jin abin nan yake kamar wani mummunan mafarki yace wallahi anti babu komai, Amal tace na gaya muku babu komai auren ne bana so.
.
Nan babanta ya kwada mata mari. Baba umaru yace meye haka Bashir ina wuri kana zartar da hukunci. Hajja kam kuka take sosai don tashin hankali ganin haka dai aka yi shawara akan a daura auren idan ma hure mata kunne ake sa yi maganin abin. A gabansu Abba Bashir ya bada duba dari a matsayin waliyin Rayyan shi kuma Baba Umaru ya karba sauran yaransu maza suka yi sheda. Sagir na gama addua Amal cikin wata irin murya kamar ta maza mara dadin sauraro tace kun daurawa kanku bala'i. Tana fadin haka ta fadi timmm a kasa. Nan da nan kowa yayi kanta cikin rudewa ana salati. Wai meke shirin faruwa a gidan Hajja ne daga zuwan Ju?
.
Sagir da Rayyan ne akan Amal suna kokarin dagata amma duk sun kasa. Baba Umaru yace wai me kuke jira ne ku dago ta akai ta dakin Hajja. Sagir yace Baba mun kasa fa. Nan dai hankali ya sake tashi Abba ya fita ya kira liman aka zo ana ta karatun Qur'ani da adduoi. Ju da sauran yaran da baa barsu sun shiga bangaren Hajja ba duk hankalinsu ya tashi don ko baa fada ba sun san ba lafiya yadda suka ga manya suna ta shige da fice. Sai bayan magriba Amal ta farka daga yanayin data shiga ta fara kuka. Anyi anyi tayi shiru abu ya gagara karshe dai gidan Marigayi Tafida Abubakar ranar baayi kwanan farinciki ba. Duk wannan tashin hankali Mami ko kadan batayi kuka ba don sai a yau ma ta kara yarda kuka rahama ga bawa. Asubar fari ta kira kanwarta Mariya a waya ta sanar da ita duk abinda ya faru, sai a lokacin mami tayi kuka tace mariya ban fadawa Dada ba.Mama tace karki damu in shaa Allah yau zan zo.
.
Bayan sun gama waya tayiwa Baban su Ju bayani shima hankalinsa ba karamin tashi yayi ba kuma yayi mats izinin tafiya. Mama ta barwa su Nafisa da babban yaya Najib sallahun yadda zasu kula da gidan da babansu kafin ta dawo. Fitarta ke da wuya wurin 7:30 na safe taci karo da Lawi dan baba Yau ko kallo bata ishe shi ba ya juya ya koma gida. Yana shiga yace da mahaifiyarsa naga ta fita amma ita da Ismail ne inajin tasha zasu. Har ya juya zai koma daki sai yaga yadda innar tasa ta washe baki. Yace wai inna meyasa tun jiya kika ce nasawa mutannen gidan can ido. Tayi murmushi har wawolunta na hakoran gaba ya bayyana tace kai dai jeka nagode. Da sauri maikoko ta shiga daki ta tashi malam Yau tace inajin fa abin ya tabbata don munafukar ta fita kuma inajin kano ta nufa. Yace ai kinsan aikinsa na kyau a hankali maji wane tashin hankalin ya tura mu.
**********************
Rayyan ba karamin damuwa ya shiga ba da gari ya waye ya shiga bangaren Abba suka gaisa da Mami da Mama wadda take ta sharar hawaye bayan ta ga yadda Amal ta ke ance tunda ta farfado haka ta kwana kuka ba sauti sai hawaye. Rayyan ya zauna a kasa yace Mami Abba ya tashi kuwa kafin yayi shiru Abban ya ce gani Rayyan sannan ya zauna suka gaisa da mama. Rayyan yace Abba ni dai idan babu damuwa ko warware auren nan zaayi don ta sami lafiya. Bazan taba samun kwanciyar hankali ba nasan nine silar ciwon nan. Abba yayi murmushi yace yaro kenan ai rayuwa ba haka take ba.
.
Ni bamu san Amal da lalurar aljanu ba amma wallahi bazan taba yi musu yadda suke so ba indai aure ne basa so tayi to sai dai suyi hakuri don Allah Yafi su. Zamu nema mata magani har Allah Ya bata lafiya. ka bar auren idan har sauki bai samu ba da kaina zan shige maka gaba kayi wani auren. Rayyan sai ya fara kuka kamar yaro wanda hakan yayi daidai da shigowar Ju falon tana ganin yana kuka tace yi hakuri zata sami lafiya in Allah Yarda. Takaici ne ya kama Rayyan ace sai a weakest moment dinsa yarinyar nan zata shigo harda wani bashi hakuri. Wasawasa yau sati biyu da fara ciwon Amal kullum zata fadi kamar sumammiya kuma tayi mugun nauyi idan ta farfado kuma sai kuka har cikin bacci tana hawaye. Da farko asibiti aka kaita tayi sati daya tasha allurai da drip amma duk a banza don ma asibitin na Baba Umaru ne so baa biyan kudin treatment. Hajja da Dada ne suka yanke shawarar a dawo da ita gida malamai suyi aikinsu. Mama dai kwananta goma a kano mami tace ta koma wudil kada abin ya zama rashin hankali ta bar yara da babansu shima kuma da tasa lalurar. A dole ta tafi don tasan hakan ne yafi dacewa amma kafin ta tafi mami ta roki alfarmar a bar mata Ju domin bata da waata mace ita take taimaka mata da ayyukan gida kafin su koma makaranta. Haka Ju ta zauna sai gashi cikin ikon Allah ita kadai Amal ke yarda ta taba ta ko malami ne yazo ita ke riko hannunta su fito falo don tuni aka barta a dakin Hajja. kullum safiya zata yi wa Mami shara da yan sauran ayyuka duk da akwai mai aiki. Idan ta gama zata je ta gaishe da Hajja ta bawa Amal abinci.
**********************
Kwana biyu ya rage Ju ta koma Wudil sai amal ta dena magana. Ana zaune zata yi fitsari ko kashi sai dai aji wari dole tasa dena fito da ita. Wannan kukan ya ragu amma ta dena magana sai nuni idan ta ga dama. Ranar da ta fara fitsari a zaune Mami tasha kuka don taga alama yarta ta zama nakashashshiya akayi akayi ta tashi a gyarata taki. Ju tana ganin haka itama sai kuka don babanta ne ya fadu mata a rai ita kuma Amal sai ta zata kwaikwayonta take ta tashi ta dawo kusa da ita, umma ce tayi mata signal da ta ja ta toilet ai kuwa akayi saa ta bita. Ju dai taga ikon Allah don Amal ki tayi kowa ya taba ta karshe dai ita ta gyara mata jiki.
.
Tun daga ranar wankin kashi da fitsarin Amal ya dawo gareta harda wanka domin duk wanda ya taba ta ba Ju ba to zata yini ta kwana kuka. A hankali Amal ta zama kamar yarinya karama Rayyan kam ra rabu da faraa tun ranar da ta fara ciwon don gani yake laifinsa ne. Malamai kam suna ta aikin magani da addua amma dama ciwo ke shiga farat daya sauki sai a hankali gashi aljanun da ake tunani sune a kanta sunki magana ma. Ranar da Ju zata tafi da sassafe umma ta buga kofar gidan mami don kwana tayi tunani. Lanti mai aiki ce ta bude mata sannan ta kira Mami. Bayan sun gaisa tace Asiya ina Abban yara shawara na kawo mana baki daya. Abba ya zauna shima sun gaisa da Umma tace to ni jiya hankalina ya tashi kan maganar komawar Juwairiyya gida. Ni dai indai da hali ku barni na roki Mariya ta barta a nan kafin Amal ta sami sauki. Kuna ganin irin artabun da ake da ita idan wani ya taba ta ba yar uwar ba. Na fadawa Baba yace muyi shawara tsakaninmu. Abba ya kalli Mami yace ya kika gani? Nasan yarinyar nan kawaici kawai tayi mana akan babanta.
.
Shin Ju zata yarda ta zauna a kano kuwa???
0 comments:
Post a Comment